Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 107
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 107: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 107. Alhamdullahi da asuba garas…
4,438 words
Alhamdullahi da asuba garas Maanal ta farka. Gashi ma sun makara salla dan AA yau ya jima bai kwanta ba yanata aiki. Ana yin sallamma a masallaci Maanal na buɗe idanunta. Akansa ta sauke dan yana kwance ne kusa da ita sosai kansu a filo ɗaya. Yanda fuskarsa take a haɗe sai abin ya bata dariya. A zuciyarta tace (a cikin barci ma miskilanci ake Namijin duniya) a zahiri kam yatsarta ta saka akan lips ɗinsa ta shiga zagayawa a hankali. Fin minti ɗaya kafin idanunsa su fara motsawa, sai kuma ya kawo hannu ya riƙe nata da take zagaya masa a lips. Murmushi ta saki, sai kuma cikin raɗa tace, “Baby open your eyes”. Kamar mai controlling nasa da remote a hankali ya buɗe idanun a kanta. Sun kaɗe sun kumburo irin na mai barci. Yanda take kallonsa lips ɗinta a cikin baki tana ɗan murmushi ya sashi yin yanayin kamar ɗan shagwaɓe fuska. Murmushi ta sake sakar masa tana jan hancinsa. Sai kuma ta kama kumatunsa ta ɗan matsa bakin yay kamar na yara na shagwaɓa “ALLAH shagwaɓa na maka ƙyau. Look at your face, just like a baby doll”. “No, I'm not! You're the baby doll, note me”. Ya faɗa a hankali yana tura lips. Murmushi ta sake saki mai faɗi tana shigewa jikinsa sosai. Ta ce, “Nima na girma ba baby bace, kai ne dai baby na tunda kana.......” sai kuma ta matsar da bakinta kusa da kunnensa ta ƙarasa raɗa masa sauran maganar. Murmushi ya saki har haƙoransa na bayyana, yana motsawa ta zille daga jikinsa, kafin ya cafkota harta dire a gadon tana dariya. Binta yay da kallo yana murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa har lokacin da murmushin dai a fuskarsa. Agogo ya kalla, har shida tayi, ya ɗan waro idanu yana sakkowa da ambaton, “Suhanallahi, haka muka makara yau ”. Bayi ya nufa agurguje, dan a duniya wucewar lokacin salla na ɗagama AA hankali. Yana ƙoƙarin shiga Maanal na ƙoƙarin fitowa, ta bashi hanya ya shiga sannan ta fito. Jiranshi tai ya fito yay musu jam'i. Sai da suka idar ya ɗan samu nutsuwa, amma yanata istigafari da ƙwacewar lokacin sallar. Jikinsa Maanal ta kwanto tana faɗin, “Good morning Bestie”. Sai da ya duƙo ya sumbaci lips ɗinta sannan ya amsa da “Barka da safiya Zuciyar Ajwaad. Yaya jikin?”. Cikin ɗan girgiza kai ta ce, “Ni lafiyata lau, kawai barcin nan dana ɗorama kaina ne dan jiya banyi ba ya nema zame min ƙalli-ƙalalla. Amma zan dage na daina, shiyyasa bana son sabama kaina abu sai kaga ya zamar min jidali idan ina son dainawa”. Murmushin gefen baki ya ɗan sakar mata yana shafa kanta. Muryarsa da sanyi-sanyi ya ce, “Anya zaki iya kuwa Basty, wannan fa nada banbanci da na baya”. Sai da ta ɗan zuba masa idon mamaki sannan ta ce, “Miya banbanta su. Naga dai duk barci sunansa barci”. “Uhmm kumafa haka ne gaskiya. Amma wannan ya shiga jikinki da yawa daina shi da alama sai ansha yaƙi kin san barcin cizon sauro daban ne”. “Uhm-uhm ni ka daina min fatan tsiya. Kuma babu sauron daya cizan”. “Tom na bari”. Ya faɗa yana mikewa da ita zuwa saman gado. Tana buɗe baki zatai magana yace, “Karma kice komai, yau babu wani kitchen da zaki shiga da safen nan. Nima zanci duk abinda aka girka a gidan gaba ɗaya oya sleep”. Baki ta tura masa tana ɓata fuska. Ya ce, “Naji dai”. Ganin zatai magana kawai ya rufe bakin nata da nashi. Tun yanayi kamar wasa har kiɗan ya canja salo, ya ɗaukesu cancak zuwa wata duniyar....
______★
A lokacin da duk waɗan can ɓangarorin ke more duniyarsu anan ɓangaren Mamy ta kwana ne cikin wani irin damuwa da takaici. Dan ko barcin kirki bata samu ba. Ƙullawa kawai take da kwancewa akan yanda zata taro abubuwa dake ƙwace mata. Rashin barcin ya saka mata nauyin jiki har akai sallar asuba tana ji ta kasa tashi, sai da gari yay haske kusan shida da rabi ta taƙarƙara da ƙyar ta tashi tai wanka tayo alwala. Zata kabbara salla taga wayarta na ring, kamar zata ɗauka sai dai ta danne tai sallar sannan. Tana idarwa dai-dai ana sake kira, ta jawo tana kallon baƙuwar lamba, kamar zata share dai sai kuma ta ɗaga. Muguwar dariyar Sille ta wani daki kunneta. Da sauri ta janye wayar gabanta na faɗuwa, ta kashe kuma ta kasa. Daga can cike da isgili da iskanci irin na tsagerun mutane Sille ya ce, “Matar Darma kuɗi nake so. Wanda kika bada sun ƙare kin san hannun barnata kuɗi gareni, abinka da babban yaro mai yammata buhu-buhu. Yanzu ma 10m nake so”. Wani irin harzuƙa Mamy tayi da faɗin, “Baka da hankali ma”. “Niko nake da hankali Kamila, tunda hakkina da kika kasa saukewa nake ci, wlhy na baki nan da sha biyun rana zuwa ƙarfe ɗaya idan banji alert ba zanzo da kaina ne har gidan na amsa”. Ƙitt ya yanke kiran...........✍️
ALLAH ya rabamu da mummunar ƙaddara😆🙏
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣5️⃣
______________
.........Murmushi Aunty tayi da girgiza kai, cikin rashin damuwa ta ce, “Wanda dai kika haifa mata ɗinne, kika kuma ɗauka da hannunki kika bata a gaban shaidu halak malak. Kika kumayi alƙawarin wannan ƙyautar bazata taɓa tashi ba har abada. Ni kinga tafiyata, ya kamata dai kima kanki faɗa akan ƴan uwan nan namu kamar yanda na baki shawara, idan ba haka ba bayan ƴaƴan har muma dangin naki sai kin rasamu ɗaya bayan ɗaya dan zuciya nason mai ƙyautata mata”. Daga haka tai ficewarta. Idan ana suman zaune to yau shi Mamy tayi kalaman Aunty na jijjiga mata zuciya. Yaushe lalacewar tata takai haka da Aunty ke datsa mata irin wannan maganganun babu ko risinawa. Eh lallai da alama ta fara sakaci da kanta, shiyyasa itama Nana yanzu take kunno mata wasu baƙin ɗabi'u, jiya fa ƙiri da muzu ta tafi ta tare a sashen ƴarta kota kanta batabi ba, yau kuma ga aunty na gaya mata magana akan Fateema da ƴan uwansu.....
(😆Kamil-mil ta malam Aliyu Darma kenan😜)
_______★
Matuƙar jin jiki Ameerah tayi a hannun Babban Yaya, kuka kam tasha har sai da muryarta ta dushe. Shi kuma yanata aikin lallashi da kalamai masu taushi da sanya mata albarka. Makarar da suka nema yi ya sashi barinta ya gyara jikinsa ya tafi sallar asuba. Ana idarwa bai tsaya ya haɗu da kowa a yaran nan ba dama su Abah ya baro massallacin. Sai da ya haɗa tea a kitchen ya hau sama ya ɗakko magani sannan ya koma ɗakin Ameerah. Barcin wahala ya ɗauketa yanzu kam, dan haka cikin lallashi ya shiga tada ita. Da shagwaɓar kuka ta farka masa, shi dai yanata ban baki da lallaɓa. Sai da tai shiru yay ƙoƙarin miƙar da ita dan taimaka mata tace ita bata so ya kira mata Maanal. Shiru yay yana kallonta a karo na farko, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin, “Bazai yiwu ba My Soha, karfa ki manta Lilly autarmu ce, taya zan yarda tazo taga wannan ɗanyan aiki da yayanta ya tafka. Adai yi haƙuri a tausaya min komai kike so zan miki. Gwara-gwara ma kice in kira miki Aunty Majdiya ko Aunty Siyama”. Kafaɗa ta maƙe ta ce, “Uhm-uhm ni ina jin kunyarsu gaskiya”. “To nima ina jin kunyar Lilly gaskiya. To kawai ki bari ni da nai aika-aikata nai aiki na ba shike nan ba. Amma kiran Lilly ai akwai ƙura babba”. Rigima ta cigaba da masa, ya cigaba da lalaɓata shima, tare da nuna mata agogo lokacin salla na sake nisa. Dole ta yarda yay mata dukkan abinda ya dace, ya gasata yanda ya kamata dama batai zaton zai iya ba sannan ya ɗakkota har kan abin salla. Shi ya saka mata riga da hijjab tai sallar, zata kwanta a wajen ya riƙeta a jikinsa ya bata tea ɗin nan tasha ya bata magani. Sake ɗaukarta yay ya maida a saman gadon daya canjawa bedsheet, ya kwanta shima ya sakata a jikinsa yana raɗa mata, “Oya sleep” a cikin kunne. Ajiyar zuciya kawai ta saki dan tasan dai itama tana buƙatar barcin sosai tunda bai barsu sunyi ba sam, a hankali ta lumshe idanu. Shi ko yana shafa kanta a hankali a haka shima barcin yay awon gaba da su su duka biyun zukatansu cike da nutsuwa da ƙaunar juna mai ban mamaki......
Hummm su Babban Yaya🤭na daiyi shiru kawai🏃😂 ______★
Yaya Fawzan kam da aka garƙame a cell barcinsa gaba ɗaya mafarkin Najma ne, koda ya farka da asubahi sai yaga wayam babu Nibras a ɗakin. Ƙwafa yayi cike da jin zafi a ƙasan zuciyarsa ya sakko a gadon. Sai kuma gata ta fito daga bayi alamar wanka tayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Ta wuce tana ƴar dariyar mugunta duk da itama ranta a ƙuntace yake har kuka tayi bayan yayi barci, dan wayar da yayi da Najma jiya da dare a gabanta ta tsaya mata a zuciya. Badan karma yaga gazawarta ba data buɗe masa ƙofar tun daren, amma koba komai gara su kwana a ƙuntacen su duka, ƙofar ta buɗe ta fice gaba ɗaya a dakin tana waƙa. Guntun murmushi ya saki yana mai cije lips, a fili ya furta, “Anjima kaɗan zakiyi kuka yarinya. Kukan jiya da daren ma da kikai ina jinki”. Bathroom ya shiga, dole yay wanka kafin shirin massalaci. Koda ya sakko ɗakin Najma ya nufa, jin ƙofar a rufe sai yay knocking. Cikin mayen barci Najma ta taso ta buɗe masa, ya ɗan zuba mata idanu ganin yanda kayan barcin suka kwanta a jikinta suka mata ƙyau. Kauda kansa yay, cike da kulawa ya shafa fuskarta da faɗin, “Sorry Love na tashe ki ko, lokacin salla yayi ne”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma a ta furta, “Thanks you Yaya”. Cikin yanayin muryar barci. Aiko sai da tsigar jikin maza ta tashi. Ya dai dake yace, “Nazo na taimaka miki kiyi alwalar? Naga kamar akwai barci a idonki”. Kanta ta girgiza masa, sai kuma ta ɗan kallesa ta maida kanta ta duƙar. “A'a Yaya kaje massalacin ka zan iya. Aina tashi”. “Kin tabbatar ”. Nan ma kan ta jinjina masa. Ya ce, “To oya, aimin addu'a fa ALLAH ya bani ƴan uku masu kama da ƴar Zaria”. Fuskarta da murmushi tace, “In sha ALLAHU, amma masu kama da ɗan Darma nafi so nikam”. Shima sai ya murmusa yana rufe mata ƙofar ya wuce massalaci. Koda ya dawo kai tsaye ɗakin nata ya nufa, ya sameta a kan sallaya tana azkar. Sai ya zauna a bakin gadon shima yana tashi. Koda ya idar ya fahimci itama ta idar cike da kulawa yace, “Taso mu kwanta barci nake ji sosai Love”. Gaban Najma ya faɗi, amma dai ta daure ta miƙe. Batare data cire hijjab ɗin ba taje gabansa ta rissina tana gaisheshi. Maimakon amsawa sai ya kamota ta hawo saman gadon, ya zame mata hijjabin ya kwantar da ita a jikinsa ya rungume. Cikin kunnenta ya ce, “Love bafa haka ake gaida miji ba.” murmushi tayi mai sanyi ta ce, “To kayi hakuri zan gyara”. Idanunsa ya lumshe, yana jin daɗin yanda komai yace bata masa musu. Sun daɗe shiru na wani lokaci, kafin ya lalubo lips ɗinta ya haɗe da nashi. A tsorace take matuƙa, amma batai masa musu ba ta barshi yay yanda yake so. Har ya haƙura ya barta dan kansa ya rungumeta kawai, a hankali ya fara sauke numfashi alamar barci ya ɗaukesa. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ranta fal farin ciki yau gata a jikin Yaya Fawzan. Rayuwa kenan, watanni biyar da suka wuce ko a tunani bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tsakaninsu da Yayunsu girmamawace da kyautatawa. Sunama juna ƙauna irin ta yan uwan taka, amma a yanzu jitake Yaya Fawzan shine duniyarta, shine farin cikin ta. Kaunarsa take matuƙa a ƙarƙashin zuciyarta. Fatanta ALLAH ya bata ikon faranta masa, ya kuma bashi ikon sauke hakkin su. Nibras ta faɗo mata a rai, sai kawai ta kauda tunaninta ta gyara kwanciya a jikinsa itama barcin yay gaba da ita.....
________★
Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna kam al'amari ne babba ya faru. Ammie da Hajiya Basariyya duk suna nan Abuja wajen biki. Yaran Hajiya Basariyya suna Zaria suma basu koma Kaduna ba. Hakama Daddy tun ranar ɗaurin aure daya taho da Hameed da Waleed basu koma Kaduna ba ya zauna yin wani aiki da da Yaya Yazeed ne keyinsa. Shigowar wannan matsalar tashi kuwa duk ya saki abubuwan ya tare a jikin Nazeera. Sai abinda tace yayi yake yi. Shiyyasa Daddyn ya dakata yin aikin Hameed na taimaka masa duk da yaron sai yanzu ne yake js2 a Secondary. Amma da yake yana da kwazo da fahimtar abubuwa sai Daddyn ke sashi yana taimaka masa da ƙananun abubuwa. Hajiya Yaya ita kaɗai ce a gidan sai ƴaƴanta. Sai Nazeerah da Yaya Yazeed da sai ma ka jima bakaji motsinsu ba. Tunda Daddy yabar gari mijin Sabuwa biye yake da shi, dan haka shima anan yake nasa shiri. Yau kuma daya kammala komai yay kiran Yazeed a waya. Lokacin yana ɗan barcinsa da Nazeerah ta barsa yi da ƙyar, dan jarababbiya ce ta bugawa a jarida. Shi kuma gashi ALLAH bai yosa mai yawan damuwa ba. Indai ya samu ya biya buƙatarsa dan kwana biyu uku ma sai ayi bai nema ba. Amma ita babu fashi babu ɗaga ƙafa. Kuma dole yay mata yanda take so babu abinda ya shalleta da baya ra'ayi. Wayar ta katse aka sake kira, cikin haushi Nazeerah ta ɗauka da nufin kashewa sai taga sunan Babanta. Aiko wani irin duka ta ɗakama Yazeed ya farka a firgice. Harara ta watsa masa tare da jefa masa wayar tana faɗin, “Kaifa wani lokacin wawa ne, to ihu zaka mana da”. A jiyar zuciya ya sauke. A ƙasan ransa yana jin zafin zagin data masa, amma a zahiri sai yace, “Kiyi haƙuri na tsorata ne.” Tsaki taja ta maida kanta ta kwanta, cike da wulaƙanci tace, “Tashi kaje can falo ka amsa bazaka daman ba anan barci zanyi. Shima Daddy ya wani kama kiran mutane a cikin dare suna hutawarsu. Mtsowww ”. taja tsaki. Jallabiya Yazeed ya ɗauka ya sanya, sannan ya fita dai-dai kiran baban Nazeera ɗin na sake shigowa. Cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya shiga gaisheshi harda duƙunnawa kamar yana a gabansa. Daga can baban Nazeera ya amsa cike da isa, kafin cikin bada umarni ya ce, “Yazeed kana jina”..........✍️

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣6️⃣
______________
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍
‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah! MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!
Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido
Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya. Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.
Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.
Tambaya/Booking: WhatsApp: 08062991549 Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge. Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
__________
.........Murmushi Aunty tayi da girgiza kai, cikin rashin damuwa ta ce, “Wanda dai kika haifa mata ɗinne, kika kuma ɗauka da hannunki kika bata a gaban shaidu halak malak. Kika kumayi alƙawarin wannan ƙyautar bazata taɓa tashi ba har abada. Ni kinga tafiyata, ya kamata dai kima kanki faɗa akan ƴan uwan nan namu kamar yanda na baki shawara, idan ba haka ba bayan ƴaƴan har muma dangin naki sai kin rasamu ɗaya bayan ɗaya dan zuciya nason mai ƙyautata mata”. Daga haka tai ficewarta. Idan ana suman zaune to yau shi Mamy tayi kalaman Aunty na jijjiga mata zuciya. Yaushe lalacewar tata takai haka da Aunty ke datsa mata irin wannan maganganun babu ko risinawa. Eh lallai da alama ta fara sakaci da kanta, shiyyasa itama Nana yanzu take kunno mata wasu baƙin ɗabi'u, jiya fa ƙiri da muzu ta tafi ta tare a sashen ƴarta kota kanta batabi ba, yau kuma ga aunty na gaya mata magana akan Fateema da ƴan uwansu.....
(😆Kamil-mil ta malam Aliyu Darma kenan😜)
_______★
Matuƙar jin jiki Ameerah tayi a hannun Babban Yaya, kuka kam tasha har sai da muryarta ta dushe. Shi kuma yanata aikin lallashi da kalamai masu taushi da sanya mata albarka. Makarar da suka nema yi ya sashi barinta ya gyara jikinsa ya tafi sallar asuba. Ana idarwa bai tsaya ya haɗu da kowa a yaran nan ba dama su Abah ya baro massallacin. Sai da ya haɗa tea a kitchen ya hau sama ya ɗakko magani sannan ya koma ɗakin Ameerah. Barcin wahala ya ɗauketa yanzu kam, dan haka cikin lallashi ya shiga tada ita. Da shagwaɓar kuka ta farka masa, shi dai yanata ban baki da lallaɓa. Sai da tai shiru yay ƙoƙarin miƙar da ita dan taimaka mata tace ita bata so ya kira mata Maanal. Shiru yay yana kallonta a karo na farko, sai kuma yay ɗan murmushi da faɗin, “Bazai yiwu ba My Soha, karfa ki manta Lilly autarmu ce, taya zan yarda tazo taga wannan ɗanyan aiki da yayanta ya tafka. Adai yi haƙuri a tausaya min komai kike so zan miki. Gwara-gwara ma kice in kira miki Aunty Majdiya ko Aunty Siyama”. Kafaɗa ta maƙe ta ce, “Uhm-uhm ni ina jin kunyarsu gaskiya”. “To nima ina jin kunyar Lilly gaskiya. To kawai ki bari ni da nai aika-aikata nai aiki na ba shike nan ba. Amma kiran Lilly ai akwai ƙura babba”. Rigima ta cigaba da masa, ya cigaba da lalaɓata shima, tare da nuna mata agogo lokacin salla na sake nisa. Dole ta yarda yay mata dukkan abinda ya dace, ya gasata yanda ya kamata dama batai zaton zai iya ba sannan ya ɗakkota har kan abin salla. Shi ya saka mata riga da hijjab tai sallar, zata kwanta a wajen ya riƙeta a jikinsa ya bata tea ɗin nan tasha ya bata magani. Sake ɗaukarta yay ya maida a saman gadon daya canjawa bedsheet, ya kwanta shima ya sakata a jikinsa yana raɗa mata, “Oya sleep” a cikin kunne. Ajiyar zuciya kawai ta saki dan tasan dai itama tana buƙatar barcin sosai tunda bai barsu sunyi ba sam, a hankali ta lumshe idanu. Shi ko yana shafa kanta a hankali a haka shima barcin yay awon gaba da su su duka biyun zukatansu cike da nutsuwa da ƙaunar juna mai ban mamaki......
Hummm su Babban Yaya🤭na daiyi shiru kawai🏃😂 ______★
Yaya Fawzan kam da aka garƙame a cell barcinsa gaba ɗaya mafarkin Najma ne, koda ya farka da asubahi sai yaga wayam babu Nibras a ɗakin. Ƙwafa yayi cike da jin zafi a ƙasan zuciyarsa ya sakko a gadon. Sai kuma gata ta fito daga bayi alamar wanka tayo. Kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Ta wuce tana ƴar dariyar mugunta duk da itama ranta a ƙuntace yake har kuka tayi bayan yayi barci, dan wayar da yayi da Najma jiya da dare a gabanta ta tsaya mata a zuciya. Badan karma yaga gazawarta ba data buɗe masa ƙofar tun daren, amma koba komai gara su kwana a ƙuntacen su duka, ƙofar ta buɗe ta fice gaba ɗaya a dakin tana waƙa. Guntun murmushi ya saki yana mai cije lips, a fili ya furta, “Anjima kaɗan zakiyi kuka yarinya. Kukan jiya da daren ma da kikai ina jinki”. Bathroom ya shiga, dole yay wanka kafin shirin massalaci. Koda ya sakko ɗakin Najma ya nufa, jin ƙofar a rufe sai yay knocking. Cikin mayen barci Najma ta taso ta buɗe masa, ya ɗan zuba mata idanu ganin yanda kayan barcin suka kwanta a jikinta suka mata ƙyau. Kauda kansa yay, cike da kulawa ya shafa fuskarta da faɗin, “Sorry Love na tashe ki ko, lokacin salla yayi ne”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma a ta furta, “Thanks you Yaya”. Cikin yanayin muryar barci. Aiko sai da tsigar jikin maza ta tashi. Ya dai dake yace, “Nazo na taimaka miki kiyi alwalar? Naga kamar akwai barci a idonki”. Kanta ta girgiza masa, sai kuma ta ɗan kallesa ta maida kanta ta duƙar. “A'a Yaya kaje massalacin ka zan iya. Aina tashi”. “Kin tabbatar ”. Nan ma kan ta jinjina masa. Ya ce, “To oya, aimin addu'a fa ALLAH ya bani ƴan uku masu kama da ƴar Zaria”. Fuskarta da murmushi tace, “In sha ALLAHU, amma masu kama da ɗan Darma nafi so nikam”. Shima sai ya murmusa yana rufe mata ƙofar ya wuce massalaci. Koda ya dawo kai tsaye ɗakin nata ya nufa, ya sameta a kan sallaya tana azkar. Sai ya zauna a bakin gadon shima yana tashi. Koda ya idar ya fahimci itama ta idar cike da kulawa yace, “Taso mu kwanta barci nake ji sosai Love”. Gaban Najma ya faɗi, amma dai ta daure ta miƙe. Batare data cire hijjab ɗin ba taje gabansa ta rissina tana gaisheshi. Maimakon amsawa sai ya kamota ta hawo saman gadon, ya zame mata hijjabin ya kwantar da ita a jikinsa ya rungume. Cikin kunnenta ya ce, “Love bafa haka ake gaida miji ba.” murmushi tayi mai sanyi ta ce, “To kayi hakuri zan gyara”. Idanunsa ya lumshe, yana jin daɗin yanda komai yace bata masa musu. Sun daɗe shiru na wani lokaci, kafin ya lalubo lips ɗinta ya haɗe da nashi. A tsorace take matuƙa, amma batai masa musu ba ta barshi yay yanda yake so. Har ya haƙura ya barta dan kansa ya rungumeta kawai, a hankali ya fara sauke numfashi alamar barci ya ɗaukesa. Itama sai ta sauke ajiyar zuciya ranta fal farin ciki yau gata a jikin Yaya Fawzan. Rayuwa kenan, watanni biyar da suka wuce ko a tunani bata taɓa kawo hakan a ranta ba, tsakaninsu da Yayunsu girmamawace da kyautatawa. Sunama juna ƙauna irin ta yan uwan taka, amma a yanzu jitake Yaya Fawzan shine duniyarta, shine farin cikin ta. Kaunarsa take matuƙa a ƙarƙashin zuciyarta. Fatanta ALLAH ya bata ikon faranta masa, ya kuma bashi ikon sauke hakkin su. Nibras ta faɗo mata a rai, sai kawai ta kauda tunaninta ta gyara kwanciya a jikinsa itama barcin yay gaba da ita.....
________★
Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna kam al'amari ne babba ya faru. Ammie da Hajiya Basariyya duk suna nan Abuja wajen biki. Yaran Hajiya Basariyya suna Zaria suma basu koma Kaduna ba. Hakama Daddy tun ranar ɗaurin aure daya taho da Hameed da Waleed basu koma Kaduna ba ya zauna yin wani aiki da da Yaya Yazeed ne keyinsa. Shigowar wannan matsalar tashi kuwa duk ya saki abubuwan ya tare a jikin Nazeera. Sai abinda tace yayi yake yi. Shiyyasa Daddyn ya dakata yin aikin Hameed na taimaka masa duk da yaron sai yanzu ne yake js2 a Secondary. Amma da yake yana da kwazo da fahimtar abubuwa sai Daddyn ke sashi yana taimaka masa da ƙananun abubuwa. Hajiya Yaya ita kaɗai ce a gidan sai ƴaƴanta. Sai Nazeerah da Yaya Yazeed da sai ma ka jima bakaji motsinsu ba. Tunda Daddy yabar gari mijin Sabuwa biye yake da shi, dan haka shima anan yake nasa shiri. Yau kuma daya kammala komai yay kiran Yazeed a waya. Lokacin yana ɗan barcinsa da Nazeerah ta barsa yi da ƙyar, dan jarababbiya ce ta bugawa a jarida. Shi kuma gashi ALLAH bai yosa mai yawan damuwa ba. Indai ya samu ya biya buƙatarsa dan kwana biyu uku ma sai ayi bai nema ba. Amma ita babu fashi babu ɗaga ƙafa. Kuma dole yay mata yanda take so babu abinda ya shalleta da baya ra'ayi. Wayar ta katse aka sake kira, cikin haushi Nazeerah ta ɗauka da nufin kashewa sai taga sunan Babanta. Aiko wani irin duka ta ɗakama Yazeed ya farka a firgice. Harara ta watsa masa tare da jefa masa wayar tana faɗin, “Kaifa wani lokacin wawa ne, to ihu zaka mana da”. A jiyar zuciya ya sauke. A ƙasan ransa yana jin zafin zagin data masa, amma a zahiri sai yace, “Kiyi haƙuri na tsorata ne.” Tsaki taja ta maida kanta ta kwanta, cike da wulaƙanci tace, “Tashi kaje can falo ka amsa bazaka daman ba anan barci zanyi. Shima Daddy ya wani kama kiran mutane a cikin dare suna hutawarsu. Mtsowww ”. taja tsaki. Jallabiya Yazeed ya ɗauka ya sanya, sannan ya fita dai-dai kiran baban Nazeera ɗin na sake shigowa. Cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya shiga gaisheshi harda duƙunnawa kamar yana a gabansa. Daga can baban Nazeera ya amsa cike da isa, kafin cikin bada umarni ya ce, “Yazeed kana jina”..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣7️⃣
______________