Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 114
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 114: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 114. “Tashi muje dan ubanki, wlhy…
4,197 words
“Tashi muje dan ubanki, wlhy bazaki kwana a gidan nan ba”. Kuka Nibras ta sakarma Yayanta mai maganar, shiko ya haɗe girar sama data ƙasa yana mata kallo mai kaɗa hanjin ciki. Tsawa ya sake daka mata, ta diro a saman gadon da take kwance. Dan tun safen data iso gidan ta samu Momynta bata gida wai sunje jihar Nasarawa gaisuwar wani abokin aikinta daya rasu ta shigo bedroom ɗin ta kwanta taci kukanta, rashin barcin daren da bata samu ba ya ɗauketa a haka, bata tashi farkawa ba sai 2. Shine mai aikinsu ta kawo mata abinci tace bazata ci ba, ta zauna tana lallashin ta da yake babbar mace ce tun ma Nibras ɗin na ƙarama take aiki a gidan. Da ƙyar ta samu Nibras ɗin ta ɗan ci, tana fita ta koma ta kwanta batare da neman salla ba, shine har zuwa yanzu da akai la'asar bata fito ɗin ba Yayanta na biyu yazo gidan mai aikin tasu ke sanar masa halin da Nibras ɗin ke ciki. Shi dama bai cika biyema taɓarar Nibras ɗin koda yaushe ba, shiyyasa take shakkarsa, shine yayanta na biyu. Koda yazo yana tambayarta kukan rashin mutuncin ta sanya masa tana gaya masa abinda Yaya Fawzan ya mata harda abinda itama tayi, daga ƙarshe ta zagi Fawzan ɗin. Aiko ya buge bakinta da ƙarfin gaske har sai da ya fashe. Kafin ya shiga zaginta shima yana faɗin, “Mijin naki kike zagi? Mijin naki ne abin zagi saboda ya ƙara aure. To ke wacece da kika isa haramta masa abinda ALLAH ya hallata masa dan ubanki. Ko an gaya miki duk wani iskancin da kike masa yana ƙyaleki bamu sani bane, ai dama mun zuba muku ido ke da Mom ɗin muga iya gudun ruwanku. Wlhy kaɗan ma yay miki, idan nine sai na lakaɗa miki shegen duka a daren kuma bazaki kwana min a gida ba. Shashasha kawai mara wayo. Kin tashi ko sai na karyaki”. Cikin kuka sosai ta ce, “Amma Yaya ko kishina baka ji, na gama gaya maka abinda yay min kace na tashi na koma dan kaga Mom bata gid....” Bata ƙarasa ba ya sake kaima bakinta duka. Cikin ƙanƙanin lokaci ya sake hayewa da kumburi, itako ta ƙara ƙarfin kukanta. Belt yay ƙoƙarin fara zarewa daga jikinsa, da gudu ta dirgo a gadon ta kama akwatinta taja ta fice ko ɗan kwali babu a kanta, sai shine ya ɗiba mata ya bita da su. Motarsa ta shiga, ya kuma hanata kuka yaja suka bar gidan. Kai tsaye gidan Darma ya nufa, suna gab da isowa aka fara yayyafi, lokacin da AA ke shigewa sashensu lokacin motar yayan Nibras ke shigowa gidan. Da ga shi har Nibras ɗin kuma duk sunga AA ɗin, shine dai bai gansu ba dan hankalinsa ba'a kansu yake ba sam. Yayan Nibras bai fita a mota ba yay kiran Yaya Fawzan, lokacin yana rungume da Najma yana mata wayo, kamar bazai ɗaga ba ya dai amsa wayar dan Najma ce ta miƙo masa, cikin ɓata fuska ya ɗaga yana kaiwa kunnensa batare daya nutsu yaga ma waye ba. Sai da Yayan Nibras ɗin yay masa sallama sannan ya amsa yana ciro wayar a kunne yaga sunansa. Maidawa yay suka gaisa. Yayan Nibras yace gasu a gidan cikin mota shi da Nibras, idan ba damuwa zasu shigo ciki. Fawzan da sai ɗazun nan bayan la'asar yake farga da babu Nibras a gidan cikin ɗan furzar da iska yace, “Bismilla ku shigo”. Daga haka ya yanke kiran. Ganin yanda yay wani ciɗin da fuska yana kwanciya rigingine yasa Najma zuba masa ido, sai kuma cikin sanyin murya tare da kai hannunta saman jikinsa a kunyace ta ce, “Yaya miya faru ne?”. Shiru yay na ɗan sakanni, kafin ya jiyo yana kallonta da idanunsa dake cike da soyayyarta, ganin damuwa a fuskarta itama sai ya gyara tashi ya murmusa yana mai jan hancinta kaɗan. “Soyayyar love ce ta ƙara ƙaruwa a zuciyar Yayanta mana”. Murmushi ta saki yanda yake da zolaya na sake birgeta.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣2️⃣
______________
........Murmushi kawai AA yay yana shafa bayan Maanal dake rusa masa kuka bil haƙƙi, sai da tafi mintuna biyu tana yi sannan ya ɗago fuskarta ya riƙe cikin tafukan hannunsa duka biyu. Kallonta yake sosai kamar yau ya fara ganinta, itako idanu a rufe tana kukanta kai kace saƙon mutuwar Babu aka kawo mata. Cikin wata irin murya mai fita da sanyi da kauri kaɗan, ainahin silent voice na masu aji da ƙarfin tasirin soyayya ya motsa lips a hankali ya furta, “I'm sorry”. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan tare da sake maida voice ɗin nashi can cikin maƙoshi, oily eyes ɗinsa na sake narkewa a kallonta ya sake furta, “Please for give me. Kin san in har ba kukan shagwaɓa kike min ba duk duniya babu abinda ke ɗaga min hankali irin hawayenki Besty, kece idanun Ajwaad kuma kece zuciyarsa. Sannan tattausar muryarki ce kawai kesa na jini a cikakken namiji. Why zaki dinga karya min zuciya da kukan ki. Ki gaya min laifina zan hukunta miki kaina duk da ina ji a raina na san laifin”. “Ni ka daina yaudarata da daɗin bakinka, dan kasan bana taɓa iya samun nutsuwa da sukuni na awa guda batare da jin muryarka ba shiyyasa kake yarfani da hakan. Na kiraka 10 miss call plus amma kaƙi ɗaga min, idan kace baka gani ba da farko saboda uziri tsakanin kiran da yanzu awa nawa? Ni zaka yarfa Besty, ni Maanal ni zaka ma wannan abun saboda na gundirek.....” “Noooo! Please Babie, ki daina faɗar haka, har abada bana jin ke dai zanji gundira dake koda na awa guda ne. Sai dai bazan miki gardamar samun saɓani na yau da kullum a tsakaninmu ba, wannan kuma normal ne ga ma'aurata Besty. Ire-iren abinda ya faru yau kuma shike kawo shi, dole ne ɗaya ya aikata wani abu ma ɗaya a bisa kuskure ko saɓani ko wani dalili, idan yayi uziri sai a samu maslaha. So Please kimin uzirin kema, duk da nasan a wannan gaɓar ni ne da laifi, amma ina da dalili, naje Kaduna ne, dan kar kisan ina can shiyyasa ban ɗaga ba nasan zaki iya saka min rigimar sai kinje shiyyasa kuma na ɓoye miki”. Tunda ya ambaci Kaduna hawayenta suka tsaya cak. Ta wani sake zuba masa idanunta kamar zata cinyeshi da su. Da yasan maganar kadunar nan zata hasalata ma fiye da laifin farkon da yayi shiru. Haba tayi mamakin ganin ya saka manyan kaya batare da takurawarta ba, wai mi ake ɓoye mata ne? Ta fa tambayesa Ammie tunda suka tashi amma yace mata ai tana wajen Daddy, sai tai zaton can gidan Daddy tunda tasan sukan sauka idan sun shigo Abujan. Shiyyasa ko tambayar Oum batai ba dan tana jin nauyin hakan, da kuma taga kayan Ammie a ɗakin Oum sai ta sake yarda da maganarsa. Ashe ba haka bane, amma sai ta danne idanun nata na kallonsa ta ce, “Wajen wa?”. AA bai iya ƙarya ba, idan ma ya kwatanta yi da wuri ake gano shi. Kuma Maanal da Oum sunfi kowa saurin harbo shi. Idanu ya lumshe a hankali ya sake buɗewa, sai ya ɗan cije lips kaɗan ya ce, “Wajen Ammie”. “Ammie! Dama ba gaskiya bane da kace min tana wajen Daddy? Mi kake ɓoye min? Miyasa Ammie batace min ta koma Kaduna ba ɗazun da mukai waya? Kuma ina ƙyautata zaton kana tare da ita a lokacin ma?”. “Karki damu zaki sani. Fara taimaka min nayi wanka dai Please”. Baki ta tura masa zata bar kusa da shi ya riƙeta da ƙyau, sai kawai ya sake rungumeta sosai suna sauke ajiyar zuciya a tare.” daga haka dai ya lallaɓata ya ƙarasa taje mata gashin ya ɗaure mata shi, yana dariya a zuciyarsa da mamakin irin wannan saurin fushi da kuka, kodan ba damuwa yay da harkar mutane ba shiyyasa yake mamakin dama haka matan keyi idan suna da ciki. Abu kaɗan a tujareka aita zuba maka rigima, idan kace kaima hawa zakai kamar su tuni rayuka zasu ɓaci, dole kake dake zuciyarka ka sassauta koda kaji taka zuciyar ta hasala dan a wannan gaɓar ƙwarai da gaske su ɗin abin tausayi ne, kulawa da soyayyar miji kawai sukafi buƙata. ALLAH ya sakama iyaye da alkairi, sai yaji yana sake yima Mamy addu'ar samun sanyin zuciya akan tata damuwar, tare da yima Oum ta gamawa da rayuwa lafiya. Dan Mamy tasha wahalar rainon cikinsu da haihuwa, Oum kuma ta ƙarasa sauran wahalhalun raino zuwa tarbiyya har girma... Daga wanka aka tsaya wanke juna, balle yanda ake zabga ruwan sama dole ne ma'aurata su ji matuƙar jin kwanciyar hankalin yanayin tare da soyayya mai nagarta.....
______★
A wannan gaɓar Mamy ce can a sashenta ita kaɗai kamar mayya, sai su Haule dake ƙasa da bata ganinsu sai in waya ta kira tace su kawo mata wani abun. Yau gaba ɗaya ta cinye yinin ne cikin tunane-tunane da ƙulle-ƙullen abubuwa daban-daban. Musamman akan al'amarin Sille dana Oum. Sai kuma ga kira ta samu daga wanda ta sanya aiki dai-dai ruwan nan na sauka tana daga jikin bedroom ɗinta tana kallon compound ɗin gidan da motar AA data shigo. Sai da ya gama shigewa sashensu sannan ta saki labulen ta maida hankalinta ga wayar yanda ya kamata. Daga can ya ce, “Hajiya kina saurarena kuwa?”. A dake ta ce, “Eh”. Yaja fasali da fara mata bayani dalla-dalla. “Tabbas bincike ya tabbatar min sunan shi wannan mai zuwa wajen naki Junaid ne, kuma sunan mahaifinsa kenan shima Junaid. Kuma tabbas yana raye bai mutu ba.....” Wani irin sakin wayar Mamy tayi a ƙasa jikinta na rawa. Batare data farga tama yadda wayar a ƙasa ba ta ce, “Junaid na raye?”. Kasancewar a hans-free wayar take raɗam wancan yaji, bai kumayi ƙasa a gwiwa ba ya ce, “Kwarai da gaske yana raye. Dan shine ma ya raini yaron a Lagos na tsawon shekaru, kafin ya sake dawowa gida bayan an fidda rai yana a raye, tunda tsahon shekarun nan duk an fidda rai ya rasu ne sakamakon ɓacewarsa ɓat ta lokaci guda. Wanda duk ya gaya min ya kuma tabbatar min da babu wani abinda ba haka yake ba, saboda shine da idonsa yaga Junaid ɗin a Lagos har yazo gida ya sanarma iyayensa, bama su gaskatashi ba da farko sai da suka haɗa shi da wani yaje ya ganshi ya tabbatar da shine ɗin sannan. Bayan hakkane shi Junaid ɗin ma ya dawo gidan......” Iya wannan bayanin kawai Mamy ta iya ji a cikin kunnenta, daga haka ta sulale ƙasa jagwab, ba suma tayi ba idanunta biyu amma komai ya tsaya cakk a jikinta hatta da jinta, sai wani shuuuiii duniyar ke mata kamar irin an kunna redio ɗin nan anƙi dacewa da tashar ƙwarai......
________★
Tunda Fawzan ya fito shi kansa Yayan Nibras ya fahimci ya samu natsuwa da kwanciyar hankali, dan sai wani irin glowing yake ƙyawunsa ya sake fitowa matuƙa alamar angwanci. Ko kallon Nibras Fawzan baiyi ba, ya zauna yana bama Yayanta hannu suka gaisa cikin mutunta juna dan shi kaf yayunta yana darajasu, hasalima ta wani ɓangaren yana haƙuri da halinta ne saboda su. Basu da yawan damuwa, duk da soyayyar da suke mata matuƙa suna mutuntashi da girmamashi da kiyaye haƙƙoƙinsa na miji a gareta. Suna cikin gaisawar ne Najma ta fito sanye cikin dogon hijjab har ƙasa. Dan Yaya Fawzan ɗin ya sanar mata baƙone harma da alaƙar, shiyyasa ta daure ta taso ta fito. Cikin girmamawa tama Yayan Nibras ɗin sannu da zuwa, shiko ya amsa mata da kulawa, bata zauna ba ta wuce kitchen, babu jimawa sai gata da ruwa da shayi data dafa ma Yaya Fawzan ɗin ɗazun bayan la'asar sakamakon ganin hadari, to bata kai ga bashi ba saboda yaje ya kanainayeta a ɗakin. Sai kayan gara irinsu alkaki, cin-cin da sauransu. A table ta ajiye, tsakkiyarsu shi da Yaya Fawzan ɗin, sannan ta zuba shayin ta miƙama mijinta shi kuma ta ajiye a saitinsa tana faɗin, “Yaya bismillah ga shayi maganin sanyi”. Murmushi sosai Yayan Nibras yayi, yarinyar na wani irin birgesa, eh lallai dole miji yaji ya daina son ƙanwarsu kam, irin wannan mar'atussaliha haka. Najma da bata san yana yi ba ta zauna tana gaisheshi, ya ko amsa mata tare da mata murnar aure, yay musu addu'ar zaman lafiya da zuri'a masu albarka. Kan Najma a ƙasa ta kasa amsawa dan kunya, daga ƙarshe tama miƙe zata bar musu wajen Yayan Nibras ɗin ya ce, “Kiyi haƙuri idan ba damuwa ki zauna. Dan nazo ne wajenku ke da mijinki”. Babu jayayya Najma ta juyo sai dai bata zauna ɗin ba ta tsaya tana kallon Yaya Fawzan alamar jiran umarninsa. ALLAH sarki Yaya F. Sai yaji wani irin sanyi da nutsuwa na ratsa masa gaɓɓai. Zuciyarsa na wani irin narkewa yay salon nasu na gado, wato lumshe idanu da buɗewa a kanta ya jinjina mata kai alamar amince mata. Sai itama ta lumshe masa nata idanun alamar godiya taje ta zauna. Ai sai yayan Nibras yay sumar zaune yana kallon tsagwaron girmama juna da soyayya mai natsuwa, tausayin ƙanwarsa da gaba ɗaya yake tamkar tazarar kudu da arewa tsakanin halayenta dana wannan amarya ya sake kamashi. Dan ya tabbatar ko yanzu tace zata gyara ta riga tayi loosing. Jiba fa gaishe da Fawzan ɗin ma batai ba, shi ko ko kallon inda take baiyi ba, sai ma ka rantse bai ganta ba a wajen..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣3️⃣
______________
........Shigowar Haule ce ta taimaki Mamy, ita ta kamata da ƙyar ta hau da ita a saman gado bayan ta bata ruwa tasha, kamar hawayenta jira suke Haule ta fita suka fara zuba sharrr, karo na farko kenan da duk fara wannan kai-kawon da badaƙala hawaye suka zuba a idanun Mamy kamar haka. Zuciyarta ta daɗe kafin tai babban motsi a cikin ƙirjinta. Tama rasa yanda zata fassara al'amarin. Junaid fa yana raye, Junaid dai Junaid data gama rufe babin rayuwarsa gaba ɗaya kuma tayi imani da hakan. Tayama za'ace mata Junaid yana raye? Sannan wannan yaron wai ɗan nan ne data haifa ita kaɗai bayan ta raini cikinsa ita kaɗai, taje ta yarda shi cikin tsakiyar dare ita kaɗai. Mi rayuwa take son nuna mata ne a wannan gaɓar? Mi tarihi yake son dawo mata da shi ne? Wane waiwaye ake son bayanta tayi a lokacin da tagama yarda tayi gaba, gaba irin na har abadan. A yanzu fa itace matar Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Fadeel Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Fawzan Aliyu Abubakar Darma, mahaifiyar Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Jiga-jigan murahu uku fa gareta, tare da basamudiyar tukunya a samansu. Hakan na nufin yanzu a kan gaɓar yin GUDU DA WAIWAYE zata kasance? Sai wasu hawayen sharrr-sharrr. A hankali ta lumshe idanunta dake tsaye ƙyam suna kallon zanen haɗaɗɗen pop ɗin rufin ɗakin, tamkar ana tariyar film tuninta ya fara komawa baya-baya harya tsaya cak a inda take buƙatar ganinsa... (Idan masu karatu basu manta ba mun tsaya a tunanin Mamy na waccan ranar dai-dai inda Junaid ke matsayin malamin su....) _____Matuƙar gundura da halayyar Uncle Junaid ƴan ajinsu sunyi, dan haka sukai gangamin kai ƙararsa wajen principal. Sai dai maimakon su ciwo nasara ɗan karen duka suka ciwo. Wannan abu da akai musu ya ƙona ransu matuƙa, dan haka manyan ƴan iskan cikinsu irinsu Kamila da ire-iren ƙawayenta da samarinta suka haɗa meeting a wajen makaranta domin maganin Uncle Junaid. Sai dai basu samo hanyar da zasu aiwatar da shirin nasu cikin sauƙi ba, dan sun aminta koda an gane sune bayan sun aiwatar ɗin ba damuwarsa bace, iyaka dai ace za'a koresu ai daga makarantar. Sun haɗa tsahon kwana uku suna neman hanayar data dace, sai a ranar alhamis ɗin ƙarshen sati wani a cikinsu ya samo mafita. Kamar yanda suka saba bayan an tashi sun fito zasu tafi gida suka wuce inda suke haɗa meeting ɗinsu. Wanda ya samo mafitar ya zayyane musu komai, babu wanda ya musa hakan yay musu ɗari bisa ɗari, dan kuwa basu da wata hanya idan ba wata a cikin matan ta ƙulla soyayya da Uncle Junaid ɗin ba. Dan haka a cikin su Kamila akace wacece zatayi?. Da farko duk shiru sukayi, sai zuwa can wanda ya kawo shawarar yace, “Babu wadda zata dace da wannan aikin sai Amila (Haka suke kiran Kamila a lokacin) dan itace keda innocent face da bazata tona ma kanta asiri ba, kuma sai yafi aminta da ita sosai, bakwa ganin yanda dama yake ƙoƙarin son ganin ta gane karatu a duk sanda yayi”. Anan ne wanda ke matsayin saurayin Kamila yace bai yarda ba, aka kaɗa dambu taliya yace bai fa yarda ba, har abin yaso zame musu rikici aka tashi baran-baran babu wata matsaya. Har aka dawo hutun ƙarshen mako babu dai-daito, satin ma ya kusa ƙarewa, tsautsayi yasa ranar juma'a Uncle Junaid ya basu assignment ya kuma tabbatar musu duk wanda baiyi ba zai sha mamaki. Bako suyin ba dan gadara, aiko ranar Monday ya amsa, da yake shima muguntar ya shirya saboda ya tsani yaran dan basu da kunya a cikin ajin ya duba assignment ɗin nasu yay amfani da period ɗinsa gaba ɗaya, ya kuma amshi ta malamin da zai shigo next. Haka ya zage ƙwanji yaci uban wanda basuyi ba daga mazan har matan, babu abinda ya dame shi da ƙanƙantar shekarunsu, dan a lokacin kaf ɗinsu basu wuce 15+ ba. Sai da ya jigatasu iya jigatawa da punishment, musamman ƴan group ɗin su Kamila sannan ya barsu, tare da basu suspension na sati biyu. A cikin wannan suspension ne suka ƙulla yanda Kamila zata shiga jikinsa dan saurayinta ya amince, itama kuma ta amince. Dan haka sai gasu sun dawo makaranta ranar da suspension ɗin ya ƙare kowa da iyayensa, sai dai Kamila ita ɗaya tazo ta zabga ƙarya wai babanta yayi tafiya shida mamanta kakarta kuma bata da lafiya. Har za'a sake komar da ita sai cikin iyayen sauran ya hana, yace ai ɗa na kowane shi ya wakilci baban nata, tunda har tai hankali ma ta dawo ai Alhamdullah. Wannan shine mafarin dawowar su makaranta, suka kuma nuna sun nutsu saboda nasihar da akai musu iyaye da malamai, idan Uncle Junaid ya shigo zakaga sun bashi dukkan hankalinsu, duk aikin daya bayar na aji ko na gida basa lattin yi koda baiyi dai-dai ba, a haka Kamila ke saka wasiƙar soyayya ma a nata littafin ma Uncle Junaid. Bai taɓa nuna mata yasan tanayi ba, duk da kuwa yana ganin wasiƙun kuma yana karantawa. Har sai da ya kammala hidimar ƙasarsa lokacin zasu shiga ss2, basu san ya kusa gamawa ba sam, aiko sunyi baƙin ciki sosai musamman Kamila dan a wannan gaɓar fa da gaske ita ta fara jin son Uncle Junaid ɗinne. Aiko haka ta rubuta masa wasiƙa mai ban tausayi ta bayar aka kai masa, ta kuma tabbatar masa in har yabar makarantar itama ta barta kenan. A karo na farko daya saka aka kira masa ita kenan, koda taje ta samesa a ƙasan bishiya da yake zaune tana duƙawa gabansa sai ta fara kuka. Tsayawa yay kawai yana kallonta na tsawon lokaci, kafin zuwa can yay kiran cikakken sunanta. Kanta a ƙasa ta amsa masa. Sake kiran sunanta yay a karo na biyu, yanzu kam sai ta ɗago tana kallonsa. Shima kallon nata yake a cikin ido, kuma sosai yaga soyayyar da take masan, sai yay murmushi da faɗin, “Kamila shekararki nawa?”. “Sha biyar da wata bakwai”. “Miyasa kike sona?”. Shiru tai na tsawon lokaci tana wasa da yatsun hannunta. Kafin a hankali tace, “Zan gaya maka gaskiya, amma dan ALLAH kada kayi amfani da hakan kace bazaka soni ba ko zaka hukunta ƴan uwana.....” “Karki damu ina saurarenki, na miki alƙawarin kuma bazanyi komai ba, idan kuma har na gamsu zan amshi soyayyarki”. Cikin farin ciki matuƙa da jin kalamansa ta warware masa komai na shirinsu, ta kuma rantse masa ita sonshi take a yanzu da gaske. Ko karatu yace ta bari a yanzu zata bari suyi aure”. Shi dariyama ta bashi sosai. Shi yana shekara ashirin da huɗu a lokacin ita tana sha biyar da wata bakwai take maganar aure. Yo a gidansu yace ma aure yake so ai maybe sai an zanesa tsaf, dan ƙa'idar babansu sai ka gama karatu kayi hidamar ƙasa ka fara aiki da kasuwa, ka kuma cika shekara talatin ciss a duniya sannan ake maka aure. Amma yayunsa biyu hakan, kuma sun girmesa sosai, a yanzu hakan ma akwai mata biyu a tsakaninsu. Amma zai amsheta dan zatai masa amfani. Ya amshi soyayyar ta, ya kuma bata ƙaramar waya yace ta ɓoye zaiyi magana da ita idan ta koma gida kafin ya samu lokaci yazo gidansu. Tayi murna da hakan sai dai maganar zuwa gida ta tayar mata da hankali, dan tana tsoron kar yaje gidansu yaga ita ba ƴar kowa bace ya canja shawara. (Wlhy ƴan uwa mu kiyayi raina tushenmu. Dan an haifeka a ƙauye, ko iyayenka talakawa ne, ko sunada wata nakasa ta jiki kama dinga jin inama basu bane iyayenka, ko kaita ƙoƙarin hidden wannan ni'imar da ALLAH ya baka kuskurene. UBANGIJI ya fimu sanin abinda ya dace damu, haihuwarka a birni ko gidan masu kuɗi ba shine nasarar rayuwa ba, babbar nasarar nagartattun iyaye da zasu baka tarbiyyar da wataran zaki fito cikin birnin kifi wanda aka haifa a ciki komai, ko ka fito cikin gidan talakawan, kafi wanda aka haifa gidan arziƙin komai. Ku koma tarihi mana, suwaye ANNABAWAN mu. Yo ko a wannan duniyar kabi silsilar su masu arziƙi zaka samu a asali ai talakawane kuma suna da ƙauye, hakama wanda aka haifa a cikin birni, kai su kansu biranen fa da ai ƙauyuka ne, yau da gobe ce ta maidasu birane. Maida hankalinki wajen samun dawwamamen birni da yafi ko ina ƙawa da ni'ima wato aljanna dan shi wannan na duniyar na zaman ɗan lokaci ne, shi wannan arziƙin da muke fafutukar nema wasu ta hanyar halak wasu ta hanyar haram rana ɗaya zai zama tamkar bamuyi ba. A DUK YANDA UBANGIJI yayimu mu gode masa muyi alfahari da wannan NI'IMAR sai ya ƙara mana da wadda ta fita tunda ba biyansa muke ba balle muce ya mana yanda bama buƙata. Yau ina fir'auna, mi mulkinsa da izza ta amfana masa? Ina Qaruna, mi dukiyarsa da alfaharin arziƙi ya tsinana masa. Ina mutanen Annabi Luɗu, mi saɓonsu ya amfana musu. Ina jiga-jigan tsinannun kafiran makka irin su Abu lahab, mi gadararsu da rigima da son ƙuntata MANZON ALLAH ya tsinana musu. Idan zamu zama na ƙwarai mu zama, dan babu mai tayaki kwanciyar kabari ko amsar sakamakon hisabinka a ranar sakamako. Hasalima masu taya maka ka aikata ɓarnar kai da su tsine-tsine zaku dingama juna, to miya amfanin alaƙar da ba'a gina domin ALLAH ba. Miye ribar ɓata lokaci a burge wanin da bai isa baka ko hanaka ba. Yanda aka haliccesa kaima halittarka akayi. Duniya gidan kashe ahu ce, yanda kaga kasuwa na cika a hankali kowa ya tafi idan dare yayi haka wannan duniyar zata kasance. Riƙe da gaskiya, sai UBANGIJI ya riƙe maka kaima). Wannan bada waya itace tsushen komai tsakanin ta da Junaid, daga nan kuma komai ya fara. Farawar da take tunanin ta kawo ƙarshenta a wata gaɓar samun yanci da cigaban rayuwar da shine sanadinta duk da ba'ayita ta hanya mai ƙyau ba. Sai gashi komai na ƙoƙarin canjawa, bayan data juyama baya da yaƙini da yarda na ƙoƙarin komawa gabanta. Gaban nata ma a gaɓar da take ƙoƙarin tsayawa da ƙafafunta..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣4️⃣
______________