Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 115

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 115

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 115: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 115. ..........Da gidan Chalawa…

3,817 words

..........Da gidan Chalawa Sabuwa gidansu ta wuce tana kuma wiwi take sanar da iyayensu abinda ke faruwa. Wai Chalawa yasa ƴan sanda sun tafi da Nazeefa da Yazeed wai sune sukai musu sata. Suma zancen ya girgizasu, sai dai basuce mata komai ba. Hasalima mahaifiyarsu catai ina ruwansu. Suje can su ƙarata ita da ƴar uwar tata. Yanda basu tanka ba a na baya yanzun ma babu ruwansu. Baban kuwa cayay tabar masa gida, idan ba haka ba zai ɓata mata rai. Haka ta baro gidan kuwa dan suna tsoron Mamansu bata da wasa, yanzu ne ma da tsufa ya kamata wasu abubuwan take kallo ta kauda kai. Amma jajirtacciya uwa ce mai tsayayyen ra'ayi akan zuri'arta. Kawai dai ko yaya sai ka samu fanɗararre a cikin ƴaƴa, to su kamar ma Sabuwar ce fandararriyar dan Hajiya Yaya iyakar tujararta a gidan mijinta ne, shima sai da akai mata kishiyoyi... Daga nan gidan police station ta wuce inda take tunanin an kai su Nazeefa, sai dai kai tsaye suka nuna mata bama su san case ɗin ba. Ta buƙaci ganin dpo sukace baya nan. Can sai ga kofur Hamza, tai masa magana tana kuka da faɗin ai sune sukaje suka kamasu yace shi baima taɓa ganinta ba sai yanzu. Wannan abu ya rikitama Sabuwa hankali. Ta dinga rantsuwa da kuka tana tabbatar da Kofur Hamza ne shiko yay mirsisi, sauran ƴan uwansa ma suka goya masa baya wai shi bama ya gari ai yanzu ya dawo. Neman haukata Sabuwa suke, dan haka ta ɗauka waya tana kiran mijinta amma fin sau goma bai amsa ba. Sai zuciyarta ta sake dagule wa. Har wani bishi-bishi take gani sanda ta baro ofishin ƴan sandan, dan tana matuƙar so da ƙaunar Nazeefa. Koda ta iso gida bata samu mijin nata ba, dan mai aikinta ma tace ai tunda suka fita tare bai dawo ba. Wannan abu ya sake ƙona mata zuciya da ruhi, sai kawai ta zauna a ƙasa a falo ta zuba uban tagumi....

★A lokacin da take nan tana damuwa da halin da ƴarta take ciki, a ɓangaren Mabera shi yana can yana kai-kawon lissafin yanda aikinsa zai tafi dai-dai. Dan kuwa tafiya da Yazeed da Nazeefa, shigowar ɗan gidan Darma a harƙallar gaba ɗaya ya gama ƙwaɓa masa shirinsa. Dole ya sake sabon lissafi gudun kar yay gaggawa, ka da kuma yayi garaje. Domin shi kaɗai yasan miya gani a cikin idanun wannan hatsabibin yaron ɗan gidan Darma, tabbas yasan barewa bazatai gudu ɗanta yay rarrafe ba. Sannan wannan yaron shi ake kira da ɗan gado har ya zarta. Bafa a banza ya ɓiyema ganin Aliyu Darma ba na tsawon shekaru. Duk da a yanzu next shirinsa shine bayyana a gabansa ai ba irin wannan yake shirin yi ba... Tun a ranar ɗaurin auren Yazeed da Nazeefa da yaci karo da fuskar Darma da zaratan mazajen yaransa uku zagaye da shi hankalinsa yay matuƙar tashi, dan ya rasa ta ina alaƙar ta ƙullu a tsakanin Chalawa da Darma, dan a kaf sanin da yay masu na tsahon shekaru babu wata alaƙasa, sai ta business data ɗan ƙullu watanni da suka wuce, wanda sarai yasan Chalawan ya jima yana bibiya kafin ya samu hakan. Sai daya zurfafa bincike ya gano amaryar Chalawa ce igiyar zaren ƙulluwar alaƙar, abinda bai taɓa zuwa masa a lissafi ba, duk da kuwa yana biye da komai na rayuwar gidan Darma. An kuma bashi ƙafa ne a dalilin komawar amaryar Chalawa ƙauye da yaranta, daga haka yay tunanin komai ya ƙare ata ɓangarenta kamar yanda ɗansa ya tabbatar masa ashe-ashe ba haka bane ba.. shigowar kira a wayarsa ya katse masa tunani, ya ciro wayar yana dubawa, ɗansa ne, kuma zuciyarsa. Dagawa yay, tare da faɗin, “Son”. “Yea Baa. Ykk?”. Yaron ya faɗa daga can. Mabera yay gajeran tsaki da faɗin, “Bana lafiya Son, dan wasana ake shirin buɗe min”. “Wanene da wannan gangancin. Halan bai san ka mallaki ɗan zaki ba?”. “Tabbas bai sani ba, dan cikin ƙwaryar kawai ya sani, ainahin kalarta zanenta ya ɓoye masa, musamman daya kasance an bita da fenti”. “Ai ko lokaci yayi da za'a kankare fentin, domin yasan da ainahin ƙwaryar da ake kai masa niƙan tuwo”. “Karka damu wannan aiki na ne, idan ina buƙatar shawara dama dole zan taɓoka.” “Haka ne Baa, nima ma kira ka ne akan matar can. Ta saka bincike akan ni da kai, yau kuma na tabbatar zuwa yanzu amsoshinta sun risketa”. Wata shegiyar dariya Mabera ya kwashe da ita, kafin ya ce, “Miyasa baka gaya min ba?”. “Saboda ba wani mai muhimmanci bane ba Baa, ai kai sarki ne ba kowane tarkace bane ya kamata yazo kunnen ka”. “ALLAH yay maka albarka ɗan Baabansa. Yanzu yaya ake ciki?”. “Nasa an bata dai-dai da abinda take buƙata, dan ina son mu tafi step 2. Sannan yaron nan na gaji da ganinsa yana yawo akan ƙafafunsa Ra'iz a cikin kujerar guragu, ya kamata shima ya ƙarfi nasa hisabin. Amma kafin hakan ina son shima na ɗan tatsesa kuɗaɗe akan video ɗin dana taɓa ɗauka shi da tsuntsuwarsa”. “Kayi komai ba komai ɗan babansa, sai dai nima fa ya shigo tawagata a wannan tsarin”. “What! AA Darma ɗin?”. “Tabbas yarona, yanzu haka nasan ya iso Abuja. Na shafa'a cewa yanzu surukin Chalawa ne, yana auren agolansa”. “Hummm Baa! Bana gaya maka yaron nan ƙwallon shege bane kana ganin bazai kai ubansa ba, na rantse maka duk gidan Darma babu hatsabibi irinsa. Kasan yanzu haka akwai wasa a tsakaninsa da Sen.. Kaugama, yanzu haka suna akan shiri kansa suma, shiyyasa nake son fara aiwatar da nawa kafin su”. “Kaugama! Kai wannan jini na Darma akwai ɓare-ɓare. Mi kuma ya haɗashi da Kaugama?”. “Kamar dai akan tsuntsuwar yarinyar nan ne, kasan shegen jinta yake kamar wata hurul-ayni.” Ɗan jimm Mabera yayi cikin nazari, sai kuma zuwa can ya ce, “Son in ko hakane bari kada kayi wani motsi zan shigo Abuja a week ɗin nan mu haɗu. Dan kamar zaifi dacewa ka taka yarinyar nan a matsayin tsanin shiga gidan Darma kafin na iso”. “Ko Baa?”. “Yes! Yes ɗan Baa”. “Ba damuwa yanda kace haka za'ai, sai ka shigo”. Daga haka suka yanke wayar Mabera na wani murmushi. Yaji daɗin wannan tattaunawar tasu matuƙa dan kamar ta bashi mafita ne akan tashi cakwakiyar.......

________★

Har magrib ana zabga ruwa, dan salla ma su AA duk a gida sukayi ta. Oum ma sai ta waya ta masa sannu da zuwa. Hakama Abah, ya kira Mamy bata ɗaga ba. Sai Yaya Fawzan da Babban Yaya suma kowa yana sashensa. Bayan sunyi sallar isha'i har lokacin dai Maanal na ɗan fushinta dan bata gama sakin jiki ba. Cikin kujera ta koma ta zauna tana shan tsamiyan biri da Ammie ta sako mata a kaya, sai waya a hannunta tana latse-latse, sai dai hankalinta na kan AA ne dake zaune a inda sukai salla har yanzu ya jingina da table ɗin jikin gado kansa a sama idanunsa a lumshe alamar tunani yake yi. Yanda baya iya jurar ganinta a damuwa itama hakane gareta, yanda suke jin junansu a zuciya al'amarine mai girma da fushi baya dogon zangon musu tasiri. Wayar ta ajiye ta miƙe riƙe da bowl ɗin tsamiyar burin. Har takai zaune a kusa da shi bai motsa ba, bai kuma buɗe idanun ba, ta zuba masa ido na fin minti guda kafin ta ɗan kaɗa masa hannunta a fuska amma ko motsi. Sai zuciyarta ta motsa da ƙarfi, duk abinda kaga ya saka AA a zurfin tunni irin haka to lallai bamai sauƙi bane ba. Tashi tai a wajen ta koma ta saman gadon ta kwanta rufda ciki ta saita fuskokinsu a waje guda. Lips ɗinta ta kai saman goshinsa mai ɗauke da tabon salla ta sumbaci tabon sallar, sai kuma ta kama fuskar tasa da tafukanta duk biyu tana hura masa iska a saman idanunsa. Tunda ta sumbacesa ya dawo hayyacinsa, yanda take hura masa iskar ya sashi sakin ajiyar zuciya a hankali sai kuma ya buɗe idanun slowly suma. A haka yake kallonta itama tana kallonsa, cikin raɗa ta ce, “Mike damun mijin Maanal Giro”. Sai da ya lumshe idanun ya sake buɗe a kanta sannan shima ya kai hannu ya shafi tata fuskar a haka. Cikin wata irin murya mai kasala da fitar sauti can ciki, yana kallon cikin idanunta ya ce, “Ƙaunarta mana, fishinta na sakani jin kamar an barni a duniyar nan ni kaɗai a cikinta.” “Haka nake ji a duk lokacin da naga damuwa a tare da kai Besty, kana kusa da Bestyn ka har kake iya zaman yin tunanin damuwa ba tare da ita ba. Kodai ba Bestyn bace ba”. Ta ƙare maganar da ɗan tura baki gaba. Murmushi ya saki mai sanyi a karo na farko, zuciyarsa na wani irin sanyi, gajiyarsa na warwarewa. Cikin sake tausasa murya ya ce, “Zo nan”. Babu musu ta sauka a gadon ta koma inda yake. Shi ko yana binta da kallo harta kai zaune. Zamewa yay ya kwantar da kansa a cinyarta tare da harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya zuba mata lumsassun idanunsa..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣5️⃣

______________

.........A gaba ɗaya wannan dare Mamy bata rintsa ba. Ta tsara abubuwa masu yawan gaske dan ta fahimci in har tayi sakacin da Junaid ya cimmata komai bazata ribantu da shi ba a wahalar zaman gidan Darma na shekaru kusan talatin da takwas. Ya zama dole ya tsira da komai koda ƴaƴanta ne da dukiyarsu. Batun jira yanzu babu shi, dan bazata iya ba sam. To wane ma jira zatayi? Mi kuma zata jira? Waɗanda Fateema ta aurama ƴaƴanta su haihu ko mi? Impossible, a wannan gaɓar dolene tai fito na fito da Fateema. Tana idar da sallar asuba da hijjabin da tai sallar ta fito. Kai da kaga Mamy kasan bata da isashen lafiya, dan ta rame sosai tayi duhu. Tasan ko a sashen Abah Fateema ta kwana a ɗakinta take sallar asuba. Dan haka kai tsaye sashen Oum ta nufa ta baya. Har yanzu garin ana yaff-yaff saboda ruwan da aka kwana anayi a daren jiya. Babu kowa a falon, hatta su Inte na ɗakinsu basu fito ba dan akwai sauran safiya. Kai tsaye sama ta haura, ta sama ƙofar hanyar upstairs ɗin key saboda karma cikin yaran wani yazo ya katse mata abinda tai niyyar yi. Falon sama ɗin ma shiru, ta wani taɓe baki tana ƙarasawa gaban ɗakin bedroom ɗin Oum tai knocking. Oum na zaune na karatun Alkur'ani, a zatonta ma cikin su AA ne, kai tsaye tace, “Shigo”. Sallamar Mamy ta saka Oum ɗagowa, dan tayi mamaki ƙwarai da gaske, amma sai ta ture mamakin gefe fuskarta da murmushi ta ce, “Oh ai nazata cikin yarane fa”. “Hummm” Kawai Mamy tace mata tana kaiwa zaune cikin sofa. Oum dai da yanayin Mamyn ya ɗan bata mamaki ta ajiye Alkur'anin ta maida hankali a kanta. Tace mata ina kwana. Nan ma Mamy bata amsa ba, maimakon amsawar ma sai cewa tai, “Magana nazo miyi Fateema”. Kwarai da gaske sai da zuciyar Oum ta harba, amma saita ambaci sunan ALLAH fuskarta da murmushi ta ce, “Ba damuwa Mamy ina jinki”. Sake tsume fuska Mamy tayi dan bama tason Oum ta ɗauka da wasa tazo. Cikin dakewa kuma kai tsaye ta ce, “Fateema nazo ne na gaya miki ina buƙatar YARANA su dawo hannuna”. Ɗan jimm Oum tayi, dan wlhy sai ma taji ta kasa fahimtar wane yaran, zuwa can ta ce, “Kiyi haƙuri Mamy wlhy ban fahimta ba, wane yaran?”. Wata dariyar iskanci Mamy tayi a karo na farko tana ma Oum wani kallon kinma haukace. “Lallai Fateema wato wane yaran? Akwai wasu yara ne a hannunki nawa bayan su Fadeel. Waɗan nan ai jikokina zan kirasu ba yarana ba”. Tai maganar tana nuna su Naufal dake barci a gadon Oum. Kallon su Naufal ɗin itama Oum tayi na ɗan sakanni, sai kuma tai murmushi tare da juyowa ta fuskanci Mamyn. Cikin nutsuwarta, kuma fuskarta a sake kamar yanda take mata magana tun ɗazun ta ce, “Mamy mike faruwa? Mi kuke ɓiye min ke da Aban yara?”. Duk da Mamy bata san mi Abah ke ɓiyema Oum ɗin ba, dan kawai ta ƙona mata zuciya sai cewa tai, “Wannan tsakanina da mijina ne, ya kuma tabbatar miki baki da hurumin shiga ciki tunda ya ɓoye miki. Yanzu ina miki maganar ƴaƴana ne, Fadeel, Fawzan, Ajwaad. Ina son ki bani yarana, duk abinda yake nasu a wajenki ki tattaro ki bani. Kin taɓa ɗaukar ciki, kin ɗanɗana haihuwa kin san ciwo da zafinsu, ya kamata ki fahimci na miki ƙoƙari”. Hawaye ne suka cikama Oum ido amma sai ta shayesu tama saki murmushi. Batace komai ba ta miƙe, a zaton Mamy Oum zata ɗauka mata abubuwan su AA ne, ta rakata da harara. Amma mi sai taji ta buɗe ƙofar toilet ta shiga ta maida ta rufe. Mamy ta zubama ƙofar bayin ido. Tun tana ƙirga sakanni ta koma mintina, sai da Oum taci fin mintina ashirin sannan ta fito, a mamakin Mamyn wanka ma tayo. Wani irin hasala da zafi zuciyarta ta shiga yi, cikin tsananin ɓacin rai ta ce, “Fateema! Amma dai kin san zan iya wulaƙantaki da rayuwarki akan waɗan nan ƴaƴan ko?. To ina mai baki shawara da gargaɗi mai ƙarfi, daga nan zuwa kwana uku rak ina son dukiyar yarana da su ɗin su dawo hannuna. Idan ba hakaba, ko minene ya biyo baya kiyi kuka da kanki”. Ta miƙe ta fice, tare da bugo ƙofar har sai da Oum ta runtse ido, su Naufal suka farka. Murmushi Oum ta saki mai sanyi, zuciyarta na cigaba da ambaton ALLAH...

Dai-dai Mamy na fitowa a sashen Oum Maanal ke isowa, cikin fushi take dan ta taho kawo ma Oum ƙarar AA ne yace bazataje aiki ba. Ta kalla Mamy da ko ganinta babu lallai tayi, yanda take a fusace yay matuƙar bata mamaki. Karo na farko gabanta ya faɗi saboda abinda zuciyarta ta ayyana mata Mamyn taje ƙila tama Oum. Cikin sauri ta ƙarasa shigewa sashen. Da bibbiyu ta dinga haɗa steps ɗin harta iso ƙofar ɗakin Oum. Knocking tayi, Oum ta bata iznin shiga duk da bata san wanene ba. Ganin fuskar Oum da murmushi tana magana da su Naufal ya saka Maanal sauke wata wawuyar ajiyar zuciya. Oum ta ce, “Ni Fateema Baby lafiya irin wannan sauke ajiyar zuciya. Zonan naji miya faru”. Ƙarasowa Maanal tai ta zauna kusa da Oum ɗin ta rungumeta, a shagwaɓe tace, “Ba komai Oum mafarkinki kawai nayi”. Sosai Oum tai murmushi da shafa kan Maanal ɗin. Ta ce, “Oh Baby mafarki ai ba gaskiya bane. Kinyi addu'a dai ko?”. Kai Maanal ta jinjina mata. Sannan ta ce, “Oum I love you, ALLAH ya sakamu aljanna muyita ganinki. Ina ƙaunarki Oum.” Hawaye ne suka cikama Oum idanu sosai, tasa yatsa ta ɗaukesu batare data bari Maanal ta gani ba. Sai ta sake rungumeta sosai a jikinta, “ALLAH yay miki albarka ƴar Oum. Ina sha ALLAHU mu ƴan aljanna ne.” “In sha ALLAHU”. Maanal ta sake faɗa. Dai-dai nan AA yay knocking da sallama, Maanal ta kalla ƙofar sai kuma ta kalla Oum tai murmushi, ta ce, “Oum bari na ɓoye kice banzo ba”. Kai Oum ta jinjina mata tana Murmushi, Maanal ta kalla su Naufal ta ce, “Duk wanda yace ma Uncle ina nan na fasa zuwa yawo da shi weekend.” Kai suma suka jinjina mata, ta tashi ta shige closet ta ɓuya. Oum kuma tace ma AA ya shigo. Jallabiya ce a jikinsa, ta kuwa yimasa ƙyau kamar Balaraben Sudan. Sai da ya ɗan bi ɗakin da kallo kafin ya zauna kusa da Oum ya bata side hug. Cike da ƙauna da kulawa ya ce, “Oumna I love you ina kwana”. “I love you too Babyn Oum. Ka tashi lafiya ya Babyna?”. Dan jimmm yayi kafin yace, “Lafiya lau Oum, amma batazo nan ba?”. Oum dake danne dariya ta ce, “Tace maka zata zo nan ne?”. “Aiki nace bazataje ba shine tace zata kai ƙarata wajen Abanta da Oum, nasan kuma bazataje sashen Abah yanzu da safen nan ba. Amma nasan mizanyi, dama Kaduna zan koma yau bari naje nai sauri na shirya kafin ta koma”. “ALLAH ya kamata to”. Manaal ta faɗa tana fitowa baki a kumbure. Mi Oum zatai ba dariya ba. AA ma da ƙyar yake danne tashi dariyar. Dama da biyu ya faɗi zancen zuwa kadunar dan yana jin ƙamshinta a ɗakin yasan ɓoyewa tayi. Tashi yay ya fice yana mata gwalo, ta bishi. Oum dake dariya ta ce, “ALLAH ya shiryeku”. Sai kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya. Dan ɗan shigowar tasu gaba ɗaya sai taji nauyin da zuciyarta tayi ya sauka gaba ɗaya, wani farin ciki ya baibayeta....

ALLAH sarki Oum ai duk yanda wani yaso ƙuntata maka idan ALLAH bai amince ba sai yayi ta banza.

________★

Mamy na sashenta tana zaman jiran taji ance ga Oum can ta faɗi jininta ya hau ko zuciya na neman bugawa amma shiru kake ji. Harma yaran suka shigo gaisheta, Maanal da AA cikin shirin office. Kallo ɗaya AA ya mata yasan tana cikin damuwa. Amma saboda Maanal yay shiru. Ita kanta Maanal ɗin ta fahimci hakan. Sai abin ya rabu mata biyu. Gashi dai taga Mamy ta fito a sashen Oum ɗazun cikin ɓacin ran da har yanzu shine a fiskarta, ta shiga kuma ta samu Oum cikin nutsuwarta kamar ko yaushe. Mike faruwa ne? Tana buƙatar yin magana da RK. Hakama Najma tunda su suna gida. Suko su Babban Yaya da yake ba fitar zasuyi ba ma bataga idonsu ba sai kusan goma. Hakama su Ameerah. Su Nuratu kam yanzu ko sashenta basa kallo. Abinda ma ya rikita mata lissafi ya hargitsa mata zuciya kusan sha biyun rana ta fito da shirin zuwa gidan Hajiya Turai kawai taga Nuratu da Saheeba sun nufi sashen Oum, kuma sun ganta dan har haɗa ido tayi da Saheeba amma ta watsar da ita kamar bata ganta ba, da wannan ƙumar zuciyar ta shiga mota ta fita a gidan, dama saboda zancen su zataje gidan Hajiya Turai. Bama tasan Nana na nan ba har yanzu bata koma Kano ba..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣3️⃣6️⃣

______________

..........Abinda ya faru a gidan Daddy ya saka Baban Sageer shirya musu zuwa Kaduna domin yin jaje. Harda Huznah kuma. Za kuma su barta ne anan Kaduna ɗin kamar yanda Baba ya bama Sageer ɗin shawara. Ba haka yaso ba, amma bazai iya jayayya da iyayensa ba. A yau da zasu tafi yaga uban kayan data haɗa sai abin ya bashi mamaki. Dan haka ya tambayeta kayan duk na miye. Kasancewar ta gama shiryama zuciyarta komai sai cemasa tai akwai kayan da zata bama ƙannenta ne da bata sakawa yanzu saboda sun mata kaɗan. Dan cikin ƙiba yake sakata yanzu sosai. Gashi ya fito abinsa daka ganta kaga mai ciki. Abin ya sosa masa zuciya, harya kasa haƙuri yace su ƙannensa kashi sukai mata shiyyasa bazata basu ba. Shiru tai batace komai ba, shima sai bai sake magana ba. Sai da suka gama shirin ya ɗaukar mata kayan suka fito. Su kansu iyayensa da sukaga kayan tafiyar tata sai da sukai mamaki, amma dai babu wanda yace komai. Haka suka ɗauki hanyar Kaduna. Kasancewar tafiyar safiya sukai sosai dan yau zasu juya sun iso da wuri. Daddy ya gayama Ammie zuwan nasu, baiwar ALLAH haka ta zage ta haɗa musu abinci wadatacce ita da su Amrah dan yanzu dai kam sun maida sashen Ammie wajen zuwansu. Yauma Daddy nacewa suje su taya su Ammie girki za'ai baƙi har rige-rigen fitowa suke. Daddy yay murmushi, ƙaunar Ammie na sake girma a zuciyarsa. Gashi dai ta canja masa mugayen halayen yaransa da ƙyaƙyƙyawan halinta. A sashen Hajiya Yaya aka saukesu, suma baƙin kansu mamakin duniya ya cika su ganin tarbar da suka samu yau a sashen Hajiya Yaya. Matar data tsanesu idan suka zo gidan ko gaisuwarsu da ƙyar take amsawa. Ga abinci an shirya musu na musamman dan can Ammie tasa aka shirya abincin, kai tsarin tarar tasu ma itace tacema Daddy can ya kamata a sauke su dan Hajiya Yaya itace babba. Daddy yaso ya doje dan yasan ƙiyayyar da Hajiya Yaya da Basariyya kema danginsa saboda suna talakawa. Amma Ammie ta dage. Sai kuma gashi Alhamdullah Hajiya Yaya ta bama kowa mamaki. Dan yau harda tsokanar Baba Sani mahaifin Sageer irin dai wasan ƙanin miji. An kuma gaisa cikin mutunta juna suka jajanta abinda ya faru. Tare da yin addu'ar ALLAH ya kawo iyakar komai. Suma dai yaran sunzo sun gaishesu cikin girma da arziƙi, abinda bai taɓa faruwa ba. Shi kansa Sageer lamarin ya matuƙar girgizashi. Dan a nan gidan ya zauna sanda yake karatu a ABU. Wlhy ko kallo bai ishi yaran gidan ba, a lokacin ba'a auro Ammie ba. Abinci ma sai ya haɗa wata uku baici na gidan ba, dan inba sashen Daddy yaje ba irin an kawo masa ɗin nan ya sashi suci tare bashi da kwano a gidan, ko kuma idan Yazeed na gida nan ne kullum zai samu ya ci tare da shi idan an kawo masa, wani lokacin ma Hajiya Yaya tace baza'a kawo ba yaje can yaci. Amma yau wai sune suke zuwa gaida iyayen sa da shi cikin girmamawa. Ganin Hajiya Basariyya bata shigo ba har fin awa guda da zuwansu dan Daddy ma bai san harda Huznah ba, dan haka ya aika Salima yace ta gaya mata batasan anyi baƙi bane. Caraf Waleed ya ce, “Daddy hada Aunty Huznah fa”. Harararsa Ammie tayi, ya duƙar da kansa. Daddy dake kallon komai ya jinjina kansa da faɗin, “Hadda Huznahr amma ta shige sashen uwarta bata nema kowa ba?”. Cikin sauri Ammie ta ce, “A mata uziri tayi kewar gida kaiko Daddynsu. Watanni kusan biyar ai ba wasa ba”. Shiru kawai Daddy yayi, dan yasan Ammien ta faɗi hakanne kawai dan hanashi yin faɗa.....

Readers Also Read