Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 124
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 124: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 124. Daga Abuja su Mabera Kaduna…
3,385 words
Daga Abuja su Mabera Kaduna suka nufa. Ransu fes musamman ma Sille dake jin burinsa na duniya ya kusan cika. Dan an raini zuciyarsa ne da ƙiyayyar Kamila tun yana a tsumman goyo, dan haka ya girma da burin ɗaukar fansa a kanta. Sun iso cikin Kaduna huɗu ta wuce, sarai Mabera na ganin kiran Sabuwa amma yaƙi ɗagawa saboda hankalinsu ya tashi da ganin cikin ƙanƙanin lokaci labarin kidnapping ɗin ahalin Aliyu Darma ya karaɗe ko'ina na media. Abin ya basu mamaki, dan yanda suka tsara komai basuyi tunanin hakan ba. A ganinsu ko za'a farga da abinda ya faru sai irin zuwa gobe ɗin nan haka. Amma sai gashi ko awa biyar ba'a cika ba al'amarin ya fito. Wanene ya buɗe musu aiki haka ne?. Sun riga sun shigo Kaduna, dan haka babu ɓata lokaci suka wuce gida da taimakon Sille suka tattara komai daya shafesa mai muhimmanci da nata ita kanta sannan ya rubuta takarda ya ajiye mata suka fice dan basu da isashen lokaci. Sake ɗaukar hanyar Abuja sukayi, gudu na tashin hankali Sille yake yi, lokacin da magrib tayi sun iso dikko junction. Hanyar Niger state. Hanyar suka ɗauka suka nausa, sannan suka ɗauki hanyar cikin jejin lambata sosai. Ashe tafiya ce mai zurfi sosai, dan basu iso inda aka ajiye su Abah ba sai bayan isha'i... Zuwa lokacin yaran su sun kunna fitulu, dan akwai sola babba a wajen, babu mai neman salla balle su taimaki su Abah da aka zube a ƙasan bishiya suyi. Su su AA ma allurar da akai musu ta bugar da su sun kama barci tuni. Sille na gama faka motar yaran sukai musu caaa, kowa na musu barka da isowa. Cike da isa suke amsawa, musamman Mabera dake bin su Abah da kallon ɗaɗɗaya. Ya sauke idonsa akan Mamy, sai kawai ya kwashe da wata shegiyar dariya. Takowa ya shiga yi har inda take yasa ƙafa ya shureta a wulaƙance. Bata ko kalleshi ba, hasalima bata ɗaga kanta dake duƙe ba. Dama kuma tunda aka kawosu wajen ta koma gefe ta ware kanta, gaba ɗaya ta riga ta tsargu, cin zarafin da Junaid yay mata a Darma House gaban kowa shi da Sille dafa mata zuciya yake matuƙa. Zuciyarta har raya mata take ta kashe kanta kawai, sai dai idan ta tuna Abah yaci gubar data saka masa a abinci sai taji babu amfanin hakan, wannan baƙin cikin da tashin hankalin na lokaci ne ƙalilan komai zai wuce. Musamman data tuna alluranta na jikinta da zataima su Junaid na guba.... “Oh wai yau kuma kin zama Saliha ne Kamila”. Sille ya faɗa cike da iskanci. Dariya suka sakeyi da ubansa, ita dai bata ko motsa ba balle ta kulasu. Sille ne ya shureta a karo na biyu, tare da mata tsawa. “K dalla tashi ki haɗa wuta ga gawayi can ki samun ruwan wanka”. Yanzu kam dole Kamila ta ɗago tana kallonsa idanunta cike da hawaye, Sille ya zuba mata kallo mai firgitarwa tare da jan kunamar bindigar hannunsa ya ɗanata. “Ko bazaki tashi ba sai na fasa miki ƙoƙon gwiwar ƙafa ne”. Shaaaa hawaye suka gangaroma Mamy, ta kalli sashen Oum da Abah suke taga ita suke kallo, haka ma su Maanal. Nana kuwa kamar ma tana murmushi ne duk da Saheeba dake fama da kanta barcin wahala ya ɗauketa na jikinta. Sai kawai taji ta gama muzanta, ta gama ƙasƙanta. Dole kuma ta tashi dan ta tabbatar Sille zai iya aikata mata abinda ya faɗa ɗin. Mabera daya kai zaune a kujerar da aka kawo masa ko'a jikinsa ya maida dubansa ga Abah yana faɗin, “Kar kaga ina cin uban matarka kaji haushina My Darma, dan baka san abinda tai min bane ba. Kai kanka data samu dama sai ta aikata maka irin wanda tai min ɗin. Bamu da wani isasshen lokacin ɓatawa anan dan mu ba masu zama bane ba. Nan da kwana biyu kacal zamu bar ƙasar nida ɗana. Dan haka Darma kana da zaɓi biyu zuwa uku. Bayan na baka labarin alaƙata da Kamila da sanar dakai ainahin wacece ita zaka biya diyya da maƙudan kuɗaɗe masu yawan gaske kai da zuri'arka dan nasan kuɗi ba matsalarku bace. Kuɗi nake so BALIDAN kuɗi da zasu wadatar da ni ni da ƴaƴana biyu a rayuwar turai kar ƙarshen numfashi mu. Nasan dai ka fahimceni. Na uku dole ka bani ƙaramin ɗanka na huce dukkan takaicina a kansa na ramawa ɗana abinda ya aikata masa a shekarun baya saboda waccan fitsararriyar matar tasa...” ya nuna Maanal. Harararsa Maanal tayi babu tsoro babu shakka. Ta yamutse fuska da taɓe baki ta watsar da banza. Murmushin takaici Mabera yayi da faɗin, “Zan gyara miki zama yarinya. Zan kuma koya miki tarbiyya da yanda ake girmama na gaba....” “Ka fara koyama kanka mana. Kuma Besty da Abah sunfi ƙarfinka wlhy, kadai ji da wadda kace kana da alaƙa da it.....” Bata rufe baki ba wani ya kawo mata duka da bakin bindiga Abah ya kare. Da sauri Oum ta riƙota jikinta itama. A nutse Abah ya kalli Mabera dake dariya. “Junaid ka kawo mu nan ne dan ka illatamu, ko ka kawomu nan dan biyan buƙatunka? Na rantse maka da ALLAH, idan wani abu ya samar min yara bazan taɓa na yafe maka ba”. “Amma kaga rashin kunyar da take min ai”. “Kazo da siffar da za'ai maka hakanne ai”. “Oh kana goya mata baya kenan Aliyu”. “Kai ba goyon bayan naka ɗan kake yi ba”. “Shike nan ni banda lokacin yin sa'insa da kai yanzu. Amma ina baka shawara ka kimtsa bakunan surukanka da ƴaƴanka idan sun tashi in har kana buƙatar dukanku kubar wajen nan da rai da kuma lafiyar jikinku. Idan ba haka ba waɗan nan fusatattun karnukan nawa basa jira. Su sha yanzu magani yanzu ne idan aka taɓani, kar kaga yanzu ta tsallake. Na baka daga nan zuwa safiyar gobe idan ka yarda da sharruɗɗana zamuyi komai mu gama a goben. Dan na faɗa maka banda isashen lokaci. Kai ku tattara su ku kaisu ciki, a haɗe min su a ɗaki guda...” Daga haka ya miƙe yabar wajen. Su kuma yaranshi suka zo suka zagaye su cikin tsawa suna faɗin su tashi. Su Nuratu ne farko tashi, suka kakkama Saheeba. Abah da gaba ɗaya zuciya ta kumeshi ambaton ALLAH kawai yake a zuciya shi da Oum ya jinjina ma su Ameerah da sukaƙi motsawa kai ganin su Abah ma basu motsa ba. Tashi sukayi suma, haka aka sakasu gaba zuwa cikin gidan. Ashe ƙaton gaske ne, akwai mutane kuma a cikin gidan zaune alamar suma kidnapping ɗinsu akayi, jikinsu yayi dauɗa sosai, wasu a rame, wasu ma ciwo ya ci su ya cinye. Bayin ALLAH kallonsu Abah kawai suke har aka shige dasu ɗaki, a zukatansu ayyanawa suke waɗan nan dai ƙila manya ne shiyyasa ba'a kawosu cikinsu ba. Daga ganin mutanen kuma dama dai kasan suna tare da jin daɗi, duk da darene ba wani sosai suke iya tantancesu ba. Ɗakin dai ginin ƙasa ne kuma rufin ƙasa. Ko daɓen ƙasa babu ƙasace rubuɗi zube jajir, sai dai akwai hasken sola har anan. Haka suka zazzauna. Sai ga su Babban Yaya an kawo, babu tausayi haka suka dinga sakinsu a ƙasa. Baiwar ALLAH Oum sai idanu ta runtse hawaye na sakko mata. Abah kam idanu ya zubama zaratan mazajen ƴaƴansa abin alfaharinsa. Manya-manyan bread guda kusan goma cikin yaran nasu wani ya kawo ya watso musu, sai ledar ruwa ɗaya. Cike da wulaƙanci ya bisu da kallo a yatsine yana faɗin, “Wannan karramawar oga ce, badan haka ba wlhy yanda na tsani masu kuɗin ƙasar nan tuwon ƙasa zakuci, ni ne nan zan ma tuƙa muku shi da hannuna yan iska ɓarayin kuɗaɗen mu. Kum tsare komai kun tare ko ina daga ku sai ƴayanku da jikoki”. Karo na farko Abah yay murmushi, dan harga ALLAH tausayi yaron ya bashi, dudu bazai wuce shekaru ashirin da huɗu ba. Sam baiga laifinsa ba, dan abinda ya faɗa gaskiya ne, sannan kuma maybe bai san su ɗin su wanene ba, dan a Nigeria kawai idan kayi kuɗi sunanka ɓarawon gwamnati a wajen wanda bashi da su. Alhalin kuma ba haka bane ba........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣5️⃣7️⃣
______________
.........Tabbas a rayuwa shi alkairi danƙo ne, baka kuma gane masoyi na ƙwarai sai a gaɓar da wata jarabawa ta rayuwa ta sameka. Hakama baka gane alkairi ga marashi rahama ce da jin ƙai sai a gaɓar da kake cikin wani bala'i na rayuwa. Shiyyasa ko yaya mu kasance masu alkairi ga wanda basu da ƙarfi ko basu kaimu ƙarfi ba. Idan kina da dubu biyar daure kiyi alkairi kona ɗari biyar ne zakiga ribarsa koda ba'a lokacin da kikayi ba. Tabbas shuka alkairi da ahalin Abah keyi da shi kansa a wannan gaɓar sai ya zam suna girbarsa ne da addu'oin bayin ALLAH akan halin da suke ciki. Dan ta ko'ina addu'oin fatan kuɓuta daga azzalumai ake musu. Masu saukar Alkur'ani nayi musamman makarantun da suka tallafawa da alkairansu. Gaba ɗaya media labarin ɗaukesu ya danne na shagalin bikin salla. Haka ahalinsu sun duƙufa addu'oi a wannan dare. Idan akace maka wani yayi barci to sai dai ƙaramin yaro, amma mazansu da matansu sunyi kwanan zaune ne agaban UBANGIJI suna kuka da fatan kuɓutar ƴan uwansu. Yayinda jami'an tsaro suma basu zauna ba. Dan shugaban ƙasa da kansa ya kira IG hankali tashe ya bashi umarnin amsar case ɗin. Kowa yasan yanda AA Darma keda kima da mutunci a idon shugaban ƙasa, hakama mahaifinsa. Dan haka wannan ba wani sabon abu bane ba ko abin mamaki. A ganin mutane ma wannan shine halaccin da shugaban ƙasar zai nuna ga ahalin Darma gaba ɗaya dana Kashim Kura dan sun taka rawar gani akan hawansa mulki ƙwarai da gaske ta ƙarƙashin ƙasa da dukiyarsu. Duk da ba kowa yasan hakan ba dan a zahiri babu wani ahalin Darma dake da alaƙa da siyasa. Shi kansa AA da aka bama muƙami a gwamnatin kowa na ganin yanda yake wasarere da shi da masa ɗaukar kashin kaji....
______★
Dukkan wani motsin dake faruwa a cikin gari waɗanda suka tallafawa Mabera a aikin saboda nasu dalilan suna isar masa da saƙo. Abin zai baka mamaki idan akace maka kuma a wasu manyan jiga-jigan ƙasar ne. Yawancinsu kuma haushinsu akan AA da Abah ne. Sai Yaya Fawzan dake harkar kwangila shima ta wani fannin haushin ya shafesa. Shi babban Yaya nasa abokan hamayyar na wajen aiki basu isa shiga cikin jiga-jigan azzaluman ba shiyyasa babu yanda suka iya da shi. Kusan misalin ƙarfe biyun dare Mabera ne a ɗakin kusa da nasu Abah zaune yana karanta sakwannin da aka tura masa game da halin da ake ciki, ƙasa tako ina ta ɗauka talakawa da manyan dake jikin su Abah. Yanda masu turo sakwanin ke jinjina girman al'amarin haka Mabera ke jinjina wa. Ƙaramar waya ya ɗauka ya haɗa sim card a ciki ya saka battery ya lalubo layin wani abokinsa da shima keda hannu a cikin aikin. Bugu biyu aka ɗaga. “Humm kai barci ma kake yi ni ina nan cikin jaje sauro na cinyeni lallai Kaugama”. Cike da kasalar jiki wanda aka kira Kaugama ya ce, “Bazaka gane ba, tun ɗazun nake jiran kiranka amma shiru, bakaga saƙona bane”. “Na gani, kasan sai da na koma Kaduna na tattaro komatsaina, dan ina gamawa da su gobe zuwa jibi zan bi ta Niger na wuce. Sai ku kuma ku ɗora da naku.” “Oh wai kana akan bakanka kenan?”. “Kaima kasan bana magana biyu Kaugama. A nawa tsarin kuma dukiyar Darma kawai nake hari sai rama abinda ɗansa yayma nawa ɗan, da. Shi na rama wanda yay min tuni. Itako Kamila dama zan ɗauketa ne ba'anan zan horata ba. Kaga manufarmu ta banbanta”. “Haka ne. To yanzu ya ake ciki?”. “Komai na tafiya anan normal, dan zuwa gobe zan zauna da su, zan kuma ajiye musu tabon da dole zasu bani kuɗaɗen dana buƙata da wuri. Na gama magana da Lawwali yanzu haka a shirye yake can bakin border yana jiran isata”. “Okay shike nan, muma dai anan normal ne, dan basu gano bakin zaren ba har yanzu. Sunata dai buge-bugen tudun dafawa. Kasan babbar dabarar da mukai shine lalata camaras ɗin nan. Sai dai ka kula sosai, dan yanzu duk wani mai TAKUN SAƘA da su za'a hau bincika, shiyyasa kaga na bada ƙafa na bar ƙasar tun satin daya gabata.” “Karka wani damu, dan ni babu wani mahaluki da zai ce inada alaƙa da Darma ta zahiri.” “Hakan yayi na barka lafiya. Zamu cigaba da tura maka kowane motsi na yanayin da ake ciki”....
_____★
A lokacin da Mabera ke waccan wayar anan su Abah sun duƙufa ne kaima UBANGIJI kukansu, dan ruwan da aka kawo musu ya taimaka musu ƙwarai da gaske sai suka kama alwala da shi. Babu wanda yabi takan bread ɗin nan sai Nana da su Naufal da suke kukan yunwa. Cikin amincin ALLAH gabannin asuba suma su AA suka farka, sai masu ibadar suka ƙaru, dan suma duk da rashin ƙarfin jiki da suka tashi da shi basu biye ba suka fuskanci UBANGIJI, dan a wannan gaɓar shine kawai zai kuɓutar da su a halin da suke ciki. Ba kansu suke ji ba, matansu da yaransu ne damuwar, ga Saheeba da itama ta farka a gigice da zubar jini. Hankalinsu ya tashi matuƙa, Nana kuka Nuratu kuka. Da wannan tashin hankalin suka wayi gari. Dan tabbas in har Saheeba bata samu taimakon gaggawa ba komai zai iya faruwa da ita. Tsabar iskanci irin na Mabera koda kukan su Nana daya ishesu ya sashi leƙowa kallo ɗaya yay musu ya watsar zai koma da baya. A bazata yaji Abah ya furta, “Na amince da dukkan sharaɗin ka. Amma kukai yarinyar nan asibiti ko ku nemo mai kula da ita”. Ba Mabera kawai ba, hatta su Oum kallon mamaki suke ma Abah, shi mutum ne mai sauƙin kai a zahiri, amma Abah akwai kafiya da dagiya, shi kansa Mabera sanin wannan halin nasa da yayi ne ya sashi kafa waɗan nan sharuɗɗan da bai yaɓa tunanin Abah zai amince da su cikin sauƙi haka ba. Oum zatai magana Abah ya hanata. Shi ko Mabera dariya ya shiga tuntsurawa. Sai kuma ya ɗan tsagaita yana faɗin, “Anya My Darma ba wani abu kake shiryawa ba kuwa. Kai ne zaka amince haka cikin sauƙi. Kai ban yarda da kai ba wlhy”. Kallonsa Abah yay cikin ido, sai kuma yayi murmushi mai ciwo. “Junaid ke nan, kai kasanni ai, kuma kasan abinda zan iya tun kafin kazo nan damu. Amma ka sani zan iya sadaukarwa saboda zuri'ata, ciki harda RAYUWATA...” A matuƙar gigice kowa yake kallon Abah. Mabera kam dariya ya sake sanyawa, sai kuma ya taɓe baki da faɗin, “Wannan kai ya shafa, yarana zasu zo su fita da ita, kuma sai ku karya ku fito domin fara zartar da shari'a”. Babu wanda ya kulashi balle tanka masa. Yana barin wajen baifi da mintuna biyar ba wasu ƙartai suka zo zasu ɗauki Saheeba. Babban Yaya ya motsa da niyyar yin magana duk da bashi da wani ƙarfi Abah ya riƙeshi ya hana. Dole ya haƙura suka ɗauketa suka fice. Nana zata bisu sukai mata tsawa, hakama Anum. Oum dake hawaye ta ce, “Gadanga miyasa zaka amince musu? Idan zaka iya basu dukiya kenan zaka iya sallama musu su cutar da Ajwaad kamar yanda suka faɗa?”. Shiru Abah yay mata kamar bai ji ba. Su Babban Yaya da basu fahimci zancen ba sukace, “Oum mike faruwa? Wane irin sharaɗi ya kafama Abah akan Ajwaad?”. Kuka Oum ta sake fashewa da shi, ta shiga zayyane musu komai da Mabera ya faɗa a jiya da dare suna barci. Cikin zafin rai Yaya Fawzan ya ce, “Miyasa zaka amince masa Abah?”. “Hakan da yay shine dai-dai Yaya Fawzan. Ko kuna son ita Saheeban ta rasa rayuwarta. A yanzu rayuwarta ce mai muhimmanci fiye da komai.” “Amma kasan wannan ALADEN mutumin zai iya aikata komai daya faɗa ko Ajwaad”. Cewar babban Yaya a fusace shima. Murmushi AA yayi idonsa akan Maanal dake barci, sai kuma ya lumshesu ya buɗe akan Babban Yaya da Yaya Fawzan. Ya maida kan Abah da kansa ke ƙasa. “Yaya na fiku sanin mutumin nan ƙwarai da gaske. Na san kuma zai iya yin fiye da abinda yama faɗa. Karku damu ALLAH na tare damu ai.” Kafin wani a cikinsu ya sake cewa wani abu Sille da yaransu suka zo fita da su. Har yanzu jikin su AA Baida wani ƙarfi, dan sai da ma aka kamasu. Da alama allurar zatai kwanaki a jikinsu kafin ta sake su. Gaba ɗayansu tsaye sukai suna kallon Mamy daketa aikin girka abinci a waje cikin rana kuma ƙatuwar tukunya, dama tun jiya Oum ke tambayar ina take Abah yay mata shiru. Duk kuma inda ta motsa yaran Mabera na biye da ita da bindigu. Duk tayi wani irin wujiga-wujiga dare ɗaya kacal, kai daga gani kasan ubanta take ci a hannun su Sille. Basu AA ba hatta Oum zuciyarta tafasa take da halin da Mamy ke ciki, haka aka kaisu ƙasan watsa bishiya da Mabera ke zaune a kujera kamar wani sarki ana faman danna masa ƙafafu. Yasa laptop a gaba yana kallon Film sai dariya yake yi kamar mahaukaci. Ga kayan ciye-ciye an baje masa. Gefensa Sille ne zaune shima yana haɗa bindiga yana zuƙar sigari. Komai basu ce musu ba har sai da Mamy ta gama uban girkin nan ta zuzzubama yaransu. Tsabar yanda ta jigata layi take kamar zata faɗi, haka suka rakota wajen inuwar. Amma tsabar mugunta sai Sille cewa yay ta koma rana tai kneeling. Ai wani irin zaburowa AA yayi sai dai bashi da ƙarfin tashi, Abah ma ya riƙeshi yana girgiza masa kai. Sille dake kallon AA yay dariya da faɗin, “Kai fa na lura ɗaukar kanka kake wani tsagera ne. Karka manta kai ƙanina ne na uku, ko shi wannan Fadeel ɗin dole yabini balle kai haihuwar taliya. Dama ka shanye fushinka dan ba amfani zai maka ba anan, ko an gaya maka a banza muka saka kuɗi muka sayi allurar da mukai muku hahhhaaha”. Lips kawai AA ya cije, tsabar yanda zuciyarsa ke hasala sai ga hawaye sun cika masa ido. Mabera da duk ke saurarensu ya kashe laptop ɗin yana gyara zama da kallon AA, kamar ba shi ba a dake ya ce, “Ajwaad ka daina damun kanka da yanayin da kake ganin wannan matar, dan wlhy a yanzu idan ka gama jin wacece ita sai kafin sauran ƴan uwanka tsanarta. Ban sani ba ko mahaifinku ya taɓa faɗa muku alaƙata da shi. In ma baiyi hakan ba ni yanzu zan faɗa muku dan zakufi fahimtar abinda nake son ku fahimta a wannan shari'ar.” “Sunana Junaid Abubakar Mabera. A......” Maganar ta maƙale a maƙoshinsa sakamakon isowar yaronsa a guje har yana faɗuwa. A tare Mabera da Sille suka miƙe, Sille ya daka masa tsawa. “Are you Mad?!!”. “Sir akwai matsala, an YANKA TA TASHI, an kama su Bakure da matar nan mai zubar da jini, yanzu haka shi ya gudu amma sun bishi yace muyi takamm...” Wani murmushi Abah ya saki, yayinda Mabera ya rikice, a tsawace ya ce, “A saka kowa a mota yanzun nan...........”✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣5️⃣8️⃣
______________