Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 126

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 126

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 126: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 126. ........“Duk abinda Junaid ya…

3,246 words

........“Duk abinda Junaid ya faɗa game da haɗuwarmu haka ne, shi malaminmu ne, kuma nice na sameshi nace ina son shi. Bayan ya amince min yabar makarantar mu, ya kuma hanani ni na bari kamar yanda nai niyya, shine ya cigaba da ɗaukar ɗawainiyar makarantar tawa, ya kuma fara saya min kaya irin na ƴammata. Dan yaje har gidanmu ya nuna kansa ga mahaifina da kakata a matsayin malaminmu ne shi, tausayina ya sashi son taimaka min. Hakan da yayi ya tayar min da hankali ya kuma bani haushi, dan haka naje na samu ƙawata na gaya mata komai. Sai tace min anya kuwa Uncle Junaid na sona. Taya munyi maganar soyayya zai je gidan mu yace tausayina yake ji. Nace mata nima abinda ya rikitani kenan. Sai tace naje na samesa na tambayeshi dalilinsa nayin hakan. Na yarda da shawararta, naje nai zaman jiran zuwansa dan gidanmu yake zuwa bai taɓa yarda mun haɗu a wani waje bayan nan ɗin ba. Amma sai shiru-shiru bai zo ba har sati guda, hankalina ya tashi na shiga damuwa har kakata ta fahimta dan ko abinci bana ci na kirki, ta tsareni da tambaya sai na gaya mata gaskiya, shine take min bayanin ai Babana ne ya hanashi zuwa, dan bai yarda da alaƙar daba ta neman aure ba tsakanin namiji da mace. Idan har sona yake ance ya turo, amma saɓanin haka baba yace yayi haƙuri. Ni kaɗai nasan halin dana shiga da jin wannan mummunan labari, dan a lokacin wlhy ji nake idan ban auri Junaid ba kamar zan iya rasa rayuwata ma gaba ɗaya. Haka naje ina kuka da bama Babana haƙuri, amma sai yaƙi ma saurarena. Wannan shine sanadin fara neman gidan su Junaid ta hanyar malam mu da nasan sunyi huɗɗa tare. Da ƙyar malam Yusufa ya gaya min, ranar weekend muka ɗauki ƙafa ni da ƙawata sai anguwarsu. Kamar yanda Malam Yusufa ya gaya mana gidansu ba ɓoyayye bane a anguwar muna tambaya kuwa aka nuna mana. Sai dai mun kasa shiga ni da ƙawata. Dan bamu san idan munje mi zamu ce ba, sannan ma babu lallai a barmu dan gidan harda maigadi. Muna a wajen muna shawarta yanda zamuyi cikin sa'a sai ga Junaid ya fito. Ba ƙaramin rikicewa yay da ganinmu ba, ya shiga yimana faɗan miyasa zamu biyoshi gida, bamu da hankali ne. Ƙawata ce kawai ke ƙoƙarin bashi haƙuri da masa bayani, amma ni nayi shiru. Koramu yay yace muje gida zai zo ya sameni. Sai lokacin nai magana. Na tabbatar masa idan da har bai zo ba zan dawo kuma har cikin gidan sai na shiga. Yace zaima zo. Haka muka tafi gida bamu zanta komai da shi ba. A ranar bai zo ba, sai washe gari da yamma ƙawata tazo ta kirani gidansu, da farko nace ban zuwa dan damuwar rashin zuwansa ta sakani a wani hali, sai da ta sanar min shine yazo sannan na tashi da rawar jiki na bita. Ko kakata dake tambayar lafiya ina zamu ban kulata ba. Baƙaramin farin ciki nayi da ganinsa ba, bayan mun gaisa nai masa ƙofarin abinda yaje yace ma baba. Sai yay min bayanin shi yayi hakane saboda ya fahimci baba aurar dani yake sonyi, shi kuma karatu yake son nayi sai zuwa nan gaba muyu maganar aure dan a gidansu a yanzu baza'a masa aure ba sai nan gaba. Na fahimceshi na kuma amince, naji zuciyata tayi sanyi. A wannan zaman ne yace min zamu dinga haɗuwa gidan Malam Yusufa dake quarters ɗin malamai cikin makaranta, amma lokaci-lokaci zai dinga zuwa yana gaida baba kodan hidimar karatuna da yake son cigaba da ɗauka. A take na amince da hakan, dan haka duk juma'a muke haɗuwa a cikin makarantar mu, gaisuwa ce kawai ke haɗamu sai kuma ya duba litattafaina yay min gyara akan abinda ya gani ba daidai ba. Baya min wani hirar soyayya sam, ni kuma abinda nake so kenan dan haka abin ya fara damuna. Na samu ƙawata akan ta bani shawara. Ta girmeni sosai, dan asali ba ƙawata bace ƙawar Auntyna ce, bayan barinsu ƙasar sai bata daina zuwa gidanmu ba sai kawai muka ƙulle. Ita tana talla dan haka idannunta a buɗe suke sosai ta fini buɗewar ido. Koda na gaya mata halin da muke ciki ni da Junaid sai tace dani gaskiya akwai matsala, kuma tabbas wataran zan iya neman Junaid na rasa a rayuwata. Dan ta fahimci ba sona yake ba tausayina kawai yake yi. Amma da zan yarda da wata shawara data bani, dan itace kawai zata riƙe min Junaid ya kasa kuɓucewa daga hannuna harna samu damar aurensa. Balle gashi dan masu kuɗi. Cikin rashin damuwa nace ta faɗa min ko minene zanyi. Tace kin tabbatar? Nace kwarai ma kuwa. Tsaff ta zauna ta zayyane min komai, na tsorata matuƙa, nace mata idan yaki fa?. Tace lallai baki da wayo, an gaya miki akwai namijin da zaki bama kanki a wannan zamanin yaki, balle ma shi yace gidansu ba aure za'ayi masa yanzu ba, yaga kinzo kin nuna masa wannan kulawar ai da gudu zai amsa kuma zakisha tattali. Nace idan ya gudu fa? Tace ta ina zai gudun? Aike yanzu indai hakan ta faru kin gama samun makamar riƙeshi gam-gam wlhy, koda yayi yunkurin hakan sai ki masa barazana da cewar zakije ki sanar a gidansu. Ke harma ki dinga masa ƙaryar kina da ciki. Amma kije kiyi tunani dai.” “Sosai hankalina ya rabu biyu da zancen nata. Ban tsaida zuciyata waje guda ba har sai da na sake tuntuɓar Junaid akan aure ya nema ɓata min rai sannan. Sai kawai na yarda da maganarta, dan haka ta koya min duk yanda zan masa. Banyi kasa a gwiwa ba na aiwatar, sai dai me, ƙiri-ƙiri Junaid ya nuna min baima gane inda na dosa ba. Daga ƙarshe ma ya kakkaɓe rigarsa yay gaba. Ban sake ganinsa ba har sati biyu, nan kuma na tada hankalina na samu Malam Yusufa da wasiƙa nace ya bashi. Itama ƙawata na sameta da batun yanda mukai har ina mata kukan cewar zata rabani da shi. Dariya kawai tayi tace ke wlhy Kamila zai dawo, kawai yana latsaki ne, amma ina da dabara ta biyu, dan wlhy in har ba wannan hanyar kikabi ba na tabbatar miki wannan Junaid ɗin ba aurenki zai yi ba, kawai yana lallaɓawa ne ku rabu. Hankalina ya tashi, nanfa na dameta akan ta gaya min ya zanyi. Tace na bata kwana biyu. Kwana biyun na bata, ranar data cika dai-dai da kwanakin takutaha, kun san dai ranar a kano abubuwa akeyi sosai na shagali, da wannan damar muka fita zuwa anguwar su Junaid, kaya rigi-rigi a hannunmu na abinci da kunun zaƙi da kawar tawa ta haɗama saurayinta nima ta ɗiba min wai na kaima Junaid. Na kuma tabbatar yasha kunun zaƙin dan ta saka kwaya a ciki. Nace mata miye amfanin kwayar? Tace itace zata sakashi yin abinda muke so ko baiyi niyya ba. Daga nan an wuce wajen sai yanda kikayi da Junaid wlhy. Zan iya cewa maganarta ta tabbata, dan yau ma mun sami Junaid ne a gida, sai dai maigadinsu mukaima bayanin cewa mu ɗalibansa ne munzo kawo masa abincin takutaha ne. Anan gate ya barmu yaje yay kiranshi, sai ko gashi ya fito. Koda ya gammu sai da ya nuna mamaki ya kuma ɓata rai, amma sai ya dake. Bayan mun gaisheshi ya koma cikin gida yace mu jirashi anan, bai wani jima ba sai gashi ya dawo da mukullin mota. Yace mu shiga, ni na shiga gaba ƙawata a baya. Nayi zaton gida zai kaimu sai naga ya kawomu wata anguwa ne mai sabbin gine-gine. Ya samu waje yay parking sai ga wani da zai iya kaiwa sa'anshi ya fito, yace mana abokinsa ne. Bayan mun gaisa abokin nashi ya shiga damu cikin gidan, gidan sabo ne yace mana na yayansa ne da zai yi aure nan da sati guda.” “Abokin nan nasa ne ya min nasiha ya kuma gaya min gaskiya akan gidansu Junaid bazasu barshi yay aure ba yanzu. Amma idan zanyi hakuri nayi karatu kamar yanda ya faɗa min tun farko nan gaba sai aje matakin auren. Yace min na daina damun kaina komai nada lokaci, sannan na daina zuwa gidansu inba hakaba yayunsa ko babansu wani ya ganni za'a bata masa rai ne sosai.. sosai raina yake a dagule, na dinga kuka suna lallashina, da kyar na nuna na amince da abinda suka faɗan. Dan haka ƙawata da abokin nasa suka fita suka bamu waje wai zai sake lallashina. A wannan barin namu ne na bashi abincin dana kawo masa, dan zuciyata ta gama aminta da batun ƙawata dole fa sai nayi hakan ne zan samu Junaid. Idan ba haka ba ina ji ina gani ɗan masu kuɗi zai suɓuce min. Da farko yaƙi cin abincin, sai da na nuna fushina sannan ya yarda mukaci tare. Daga kuma shan wannan kunun zaƙi ne komai ya faru.....” kuka ya sarƙeta. Zuciyoyin su Babban yaya kuwa wani irin rarrabewa suke gida bibbiyu, babu abinda suke sai ambaton addu'a. Yaya Fawzan daya kasa jurewa ya ce, “Abah bama buƙatar wannan labarin a barshi...”........✍️

Gaisuwa da fatan alkairi gareku baki ɗaya 😘😘😘😘

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣1️⃣

______________

........“Baku isa ba, sai an kaishi har ƙarshe. Dan haka oya Kamila muje”. Sille ya faɗa yana nuna Mamy da bindiga. Hawaye ta share tare da zufar dake cigaba da jiƙe mata jiki ta cigaba da faɗin, “Junaid yamin fyaɗe.....” “Kodai kin min fyaɗe dan uwarki! Shegiya mubafuka, idan baki gyara maganarki ba kin faɗi gaskiya wlhy zan harbeki ne nima. Iya ƙoƙarina nayi na son kaucewa ban taɓaki ba amma da yake ke shaiɗaniya ce sai da kika samun abu nasha na aikata hakan”. Mabera ya faɗa a fusace. Mamy ta cigaba da faɗin, “Shike nan naji ni na saka maka ka aikata. Maimakon ni nayi kuka akan abinda ya faru duk da wahalar dana sha shine ke kuka sosai da zagina, ya tsareni sai na faɗa masa abinda na zuba a abincin nan. Da farko naƙi, sai da naga yana neman kasheni na sanar masa komai. Nasha maruka a hannunsa, na kuma sha zagi, ya kuma tabbatar min har abada mun rabu kenan. Sai lokacin na fara kuka da roƙonsa. Da ƙyar na samu yace ya haƙura. Koda abokinsa da ƙawata suka dawo sukaga halin da muke ciki bai ɓoyema abokin nashi komai ba. Shima abokin nashi ya girgiza, ya kumayi mamaki sosai musamman da yake kallona ƴar ƙarama babu jikin kirki. Bayan dai ka-ce-na-ce abokin nasa da kanshi ya fita ya samo min magunguna nasha, ƙawata ta taimaka min na gyara jikina a gidan tanata nuna min karna wani damu nasara tamu ce. Wannan abinda ya farun shine tushen komai, kuma shine mafari. Dan bayan jiyyar kwanaki dana sha batare da barin kakata ta fahimci komai ba saboda magani da nake sha da taimakon da ƙawata ke bani cikin dabaru na warke sarai, abinda kuma ya sake bani mamaki Junaid ya koma zuwa gidanmu, tun Baba na ɗaure masa harya saki jiki ya haƙura. Abinda na lura da shi Junaid na kaffa-kaffa da nine kada na faɗama su baba abinda ya faru tsakanina da shi, aiko saina samu na firgitashi, haka yake ɗaukata muje super market ya kaso min kuɗi ni da su Baba. Kawai bayan wata biyu dayin hakan sai yazo min da buƙatar irin wancan al'amarin daya faru, ban masa musu ba na bashi kaina. Nasha wahala a karo na biyun ma amma na daure sosai. Shi ko yayta lallaɓani da min alƙawari kala-kala. Wannan shine ya sake fasan kai na ƙara ji na gama damƙe Junaid a hannu. Sai dai me na daina ganin period ɗina tun daga yi na biyun nan. Na kasa samun koda ƙawata da batun, sai dai na tambayeta mike saka jinin mutum ya daina zuwa duk wata. Sai tace ciki ne. Nice bana gani? Da sauri nace mata a'a wlhy, naji makwafciyarmu ne na hirar jiya ni kuma sai abin ya ban mamaki shiyyasa na tambaya. Da alama ta yarda, dan bata sake min maganar ba nima ban sake mata ba. Sai dai hankalina a tashe yake dan hakan dai na fahimci ana nufin cikine da ni. Ga kakata ta fara ƙannanun magana akan tunda na kusa gama makaranta ya kamata na fitar da miji haka nan. Babana ma ya hau ya zauna akan batun. Tsoron sake yima Junaid magana nake yi akan aure tunda ya gaya min gaskiyarsa, amma yanda suka matsa min dole nai yunƙurin yin hakan. A mamakina wannan karon baiko musa min ba yace ya yarda zamuyi aure, amma akwai wani aiki da zai sakani na watannin da basu wuce biyar ba kacal. Dan haka zai samu Baba da batun cewa zai aureni amma mahaifinsa baya nan a bashi lokaci har ya dawo. Ko damuwar jin wane aikine zan masa banyi ba na amince. Haka kuwa ya samu Baba ya tsarashi, mukai sa'a kuwa ya amince. Wannan ne ya bani damar yin jarabawar ssce ɗina batare da matsawarsu akan batun aure ba. Ga ciki maƙale a jikina na rasa wazan tunkara da batunsa tsakanin ƙawata da Junaid, balle zuwa wajen likita nama tabbatar shi ɗin ne ko kuwa. Kwatsam a ranar da mukai final exam ɗinmu na dawo gida da murnar kammala Secondary na tarar da anguwarmu a cike taf da mutane anata hayaniya. Da ƙyar na kukkutsa na shiga ainahin inda hayaniyar take sai na samu ƙawata shimfiɗe a ƙasa ga ƴan sanda da babanta da mamanta zaune gabanta sunata kuka. Hankalina yayi masifar tashi na tambayi wani ɗan anguwarmu dake kusa da ni sai yace min iyayentane suka gane tana da cikin shege shine suka kamata da duka akan sai ta faɗi wanene yay mata, da ƙyar aka ƙwaceta a hannunsu sai ma akaga ta rasu. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka maka rana. Ban san sanda na nufi gida ba saboda gudawa dake neman zubomin. Wannan al'amari yayi matuƙar tayar min da hankali, dan har aka tafi da iyayen ƙawata ita kuma aka binneta da fin sati biyu ban dawo dai-dai ba. Sai dai faruwar hakan ta sakani sake yin gum da bakina akan abinda nake tunani a kaina nima game da ciki, sai dai na tasa rayuwar Junaid gaba akan batun aure. Dan a shirmena lokacin cikin zai cigaba da ɓuya har muyi aure kafin na haifeshi. Saboda wani magani dana amsa a hannun masu tallar magani, masu faɗin sunci dubu sai ceto ɗin nan. Haka na saka maganin nan gaba naita sha a ɓoye wai ciki zai kwanta har nayi aure, dan a lokacin ni sam ban kawo wani batun zubar da shi ba, dan zubar da ciki ba abu ne mai sauƙi ba sai da kuɗi sosai kuma bamma san ina zamuje nayi hakan ba tunda bayan ƙawata data rasu ba wani ya taɓa sanin halin da nake ciki ba, dama itace ke nuna min hanya yanzu kuma babu ita. Iyayenta ma ance an kaisu prison. Matsawar da naima Junaid yasa jarabawarmu na fitowa ban san yaya akai ba ya shiga ya fita wajen babansa aka nema min jami'a, bayan iyayensa sun kawo kuɗin aure na. (Ashe ba iyayensa bane hayarsu yayi) Sai dai a lokacin mu duk bamu sani ba, shi kuma baba ganin har iyayensa sunzo gida babu gardama ya yarda zan fara makaranta.” “Ana gobe zan fara zuwa makaranta Junaid yazo gidanmu ya ɗaukeni wai zai min siyayya, a wannan fita ce ya sanar min ainahin aikin dazan masa. Ya nuna min hoton Fateema. Yace Kamila wannan sunanta Fateema Abubakar Ishaq Darma. Kamar yanda zaki shiga makaranta gobe itama gobe zata fara zuwa. Ƙanwar abokina ce. Ina son ki shiga jikinta ku zama ƙawaye aminai na gaske. Cike da mamaki nace masa duk akan mi zan yi hakan, daga ganinta ƴar masu kuɗice irinka Junaid, kodai budurwarka ce?. Tsaki yayi da faɗin kefa shashashace wani lokacin, yanzu nake gaya miki kanwar abokina ce. Ainahin aikin kuma ba'a kanta bane akan abokin nawa ne, sannan banda wata alaƙar soyayya da ita wlhy. Kin dai ji na rantse miki. Kawai ina son mu takata ne a matsayin tsani samun kuɗaɗen aurenmu, dan babana ya rantse tunda aure nake so bazai min komai ba na auren sai dai nayi da kaina, yasan bani da inda zan samu kudin nayi shiyyasa yace hakan. Kinga dole na haƙura, ni kuma a wannan gaɓar wlhy bazan iya haƙura ba sai na aureki, dan kin ɗanɗana min zumar da ban san haka take ba. Sannan ina son aurenmu ya zama aure na musamman da kowa zai san kin auri wanda ya isa. Ki nunama ƙawayenki kin wuce da su na har abada. Tabbas maganganun Junaid sunyi tasiri matuƙa a zuciyata, saboda bani da burin daya wuce ace muma gidanmu munyi kuɗi, mamana da ƴan uwana da suka gudu suka barni saboda talauci suzo su samu na wucesu fintinkau, dan haka ko musu banyi ba na amince masa. Matuƙar farin ciki ya nuna min da amincewata da kalamai masu daɗi na soyayya da suka sake zurmani a ramin. Washe gari na fara shiga makaranta, kuma Junaid ya kaini, sai dai bamu haɗu da Fateema ba. Da aka tashi na koma gida, da daddare da Junaid yazo hira na faɗa masa sai yace kada na damu wai batajin daɗi ne shiyyasa amma gobe zatazo. Washe gari ma nata jiran shigowarta amma shiru har malami ya shigar mana aji, harna fidda rai da zuwanta kawai sai gata. Cikin sauri na ɗan fiddo hoton da Junaid ya bani dake cikin jakata na kalla. Ita ce kuwa, dan har ma tafi ƙyau a zahiri fiye da hoton. Kawai sai zuciyata ta shiga raya min anya ba yaudarata Junaid keyi ba sonta yake yi. Taya za'ace wannan ƙyaƙyawar budurwar da wani manufa ta kuɗi kawai zai ce na raɓe ta. To amma ya rantse min ai, da kuma son nata yake tunda yace yayanta abokinsa ne danmi zai zo ta wajena. Ina wannan tunanin har ta ƙaraso inda nake ban sani ba, sai da ta taɓani na dawo firgigit, tai min murmushi na mayar mata, ta buƙaci zama kusa da ni da gudu na matsa mata kuwa ta zauna zuciyata fes komai yazo min da sauƙi. Wannan shine mafarin alaƙata da Fateema. Junaid na cigaba da tsara min mataki-matakin zama da ita har naci galaba a kanta..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣2️⃣

______________

Readers Also Read