Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 144

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 144

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 144: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 144. .........A nan gida ma an gama…

4,444 words

.........A nan gida ma an gama zanama Maanal kwalliya ta dukan zukatan maƙiya. Didi ta bata wani ubansun lass da aka saya da kuɗi masu nauyi sky blue da kwalliyar peach a jiki. Skirt ne da helf bubu, ya bala'in jin stones. Ɗauri akai mata daya zauna fem, sannan akabi kunnenta zuwa hannuwa da wuya da muguwar sarƙar gold ɗin kayan da Oum ta kawo. Da masu karatu zasuji nauyin kuɗin sarƙar nan sai sunce (Bilyn Abdull ta fara zuba mana ƙwayayen ƙarya🥱. To kawai mubar komai a rufe ni kaɗai na sani🤣🏃🏼‍♀️). Ba mai kwalliya ba hatta ƴan uwanta tsayawa kawai yau sukai suna kallon ƴar ƙanwar tasu. Ita kanta Maanal data kalli kanta a mirror sai da hawaye suka cika mata idanu. Rayuwa kenan, kai dai an haifeka amma baka san wanene kai a shekarun girma da hankali ba. ALLAH dai yasa mu dace. Amma musani an haifeki a ƙauye ko gidan talauci ba shike nuna ALLAH bazai ɗaukaka ba watarana, ko al'umma su dinga ji a ransu baka isa ka kai haka ba. Waye kai da, miye-miye hassada a bayyane mtsowww!!. Takalman ta masu ƙaracin tudu da suka zauna da shigar tata aka bata ga saka, sai dan siririn gyalenta a gefen kafaɗa. Wlhy ko maƙiyi yaga Maanal a yau sai ya haɗiyi yawu balle mu masoyanta. Hajiya Shuwa tazo ta sake tirareta da ƙamshi na musamman. Daga haka suka sakko ƙasa aka sake gyara saman dan ba'a so kowa ya hau musu can sirrinsu ne, shiyasa ma su Amal suka gyara mata bedroom ɗaya a ƙasa da zata zauna har taro ya tashi. Da su Zeezah da Aneesa ta fara karo, wanda isowarsu kenan daga Kaduna. Wani kalar ihun farin cikin ganin Juna suka saki. Rabonta da su ko'a waya tun kafin su bar ƙasar. Sai kuma ga ƴan Giro an kwasosu daga masaukinsu, dan wasu ne anan da aka bari kawai su uku suka kwana. Ana haka tawagar yaran gidan su Ammie suma suka iso. Abu kamar wasa sai ga zuri'ar Nene itama, sai kuma ga ƴan uwan Hajiya Yaya. Lallai su twin's sunyi gishi. Kowa ya kalli Maanal sai ya ambaci masha ALLAH. Hajiya Yaya da Nene da Hajiya Shuwa da Hajiya Majdiya ne tsaye akan komai ta nan ɓangaren ta. Sai su Ameerah, Najma, Amaal, Shahidah dasu Aneesa suka fuskanci shirya wajen da za'ayi walima dan anan cikin gidan ne. Tacan ɓangaren Oum ma ahalin Darma sunata nasu ƙoƙarin. Gaba ɗaya sai ya zam babu mai kallon sashen Mamy balle tunawa da ita, haka su Saheeba sun zama kamar an waresu ma. Balle Nibras da ita zuciyarta ma ta gama dagargajewa. Jitake kamar ma tabar gidan idan an gama sunan sai ta dawo. Duk wanda yazo yay cigiyar yara ace suna tare da babansu a wajen walima. Sai ƙarfe ɗaya da kusan rabi ana shirin fara walimar mata mazan ke shigowa. Mamakin ganin gidan sukai taff, dan kamar wasa bikin suna dai yayi mugun yin armashi. Lokacin da idon AA ke sauka akan Maanal sai ya tsaya cak, ya subahannallah matarsa duniyar ƙyau ce da cikar kamala da ƙyawun haiba. Bai sani ba ko tsananin ƙaunar da yakema yarinyar nan ce yasa yake ganinta da tazara mai yawa tsakaninta da sauran mata? Shifa magana ta ALLAH idan har Maanal na waje kallon sauran matan wajen yake kamar mata maza (😲🤕 AA ka fita idonmu🙄). Ba AA kawai ke kallon Maanal ba, itama kallonsa take yi cike da shauƙi da ƙauna mai girma. Sai da Yaya Fawzan ya zunguresa cike da neman magana ya ce, “Kai malam kula kada ka yadda min yaro ƙasa fa”. Dariya mutane suka sanya. A hankali Maanal ta kauda kanta tana murmushi itama. A wani irin slowly AA ya lumshe idanunsa masu hasken madarar nan tamkar an zuba oil a ciki. Ya ɗan furzar da iska da sake buɗe idanun a hankali sannan ya kai ɗayan hannunsa ya gyara gilashin idonsa. Yaya Fawzan dai yasa hannu ya amshe Muhammad dake hannun AA ya haɗa da Ahmad dake a wajensa. Ba kunya ba tsoron ALLAH AA ya taka zuwa inda Maanal take kawai ya rungumeta. Ihu sosai yaran matan wajen suka saka. Sai hasken camaras a kansu dan abin nasu ya burge mutane. Maanal kam cike da kunya ta kifa kanta a ƙirjinsa kawai tana murmushi. Kawai sai ganin Babban Yaya akai yazo yana liƙa musu sabbin dubu-dubu. Ya subahannallah ihu mai ƙarfi irin na shewar mata waje ya sake ɗauka. Wata zaƙaƙura a cikin ƴan Giro ta dage ta callara guɗa. Najma da Ameerah kam mp suka ɗakko kawai suka saka musu waƙar nan ta Halifa sk ɗorayi. Tana ƙarewa suka sa Idan gagangar so ta doku ta shamsiyya sidi, ya rabbi, AA bai damu da jin waƙa ba sam daga na turancin har na hausar, amma a yau ji yay jikinsa na wani tsuma tamkar randa aka fara saka waƙar baza na daina kuka ba ta Halifa sk a wajen taron MAWAAD. Maanal kanta hawaye taji na bin idanunta, a hankali ya ɗago fuskarta yana kallon hawayen, shima idanunsa sun gama kaɗewa jikinsa na tsuma, tsigar jikinsa tashi take kwarai da gaske. Wato mutane na cewa akwai kiɗan gado dake saka mutum taka rawa ko bai niyyar ba, to fa yau ya yarda akwai kiɗan soyayya mai susuta jiki da jini harma da ɓargon jiki ga ma'abota soyayya. Ji yay kamar kowa ya mutu a duniya daga shi sai Maanal kawai ke numfashi a ciki, bai ma san ya wani irin kai harshe ya fara lashe hawayen ba. (Ihuuuuuuu huh huh kai nima sai na ɗan wlhy🤣. Na shiga tamanin Abdull yau ka dawo gidan nan babu zaman lafiya sai mun saka gangar so ka lashen hawayena. Yo hauka ake dazan bari kaina yayi murfi. Aradun ALLAH tsumin soyayya ta ya tashi a wajen nan ALLAH kasa mu da mazanmu duk ƴan aljanna ne😌❤️❤️❤️❤️❤️🥳🥳🥳🥳). Abu ya girma, ba Babban Yaya ba sai kawai dangin nan suka rufesu da liƙi babu mai kwasa. (Tab duƙewa nai naita ɗibar ƴan dubu-dubu, ina ruwana da wani nuna capacity a gidan masu akwai😌😎). Mamy da Uwangale ta fiddo da ƙarfin tsiya mutuwar zaune tayi kawai tana kallon abinda yafi ƙarfinta, zuciyarta sai tsitsinkewa take yi. Balle data hango Abah da Oum suma sunama su AA liƙi ana musu. Kai daga gani kasan suma waƙar gangar so ɗin ta doku a zukatansu, don tsoffin nan wani kalan kallon juna suke kamar zasu cinye kansu. Jikin Mamy na ɓari ta danna buttom ɗin jikin wheelchiar ɗinta zata koma ciki Uwangale ta balla mata hararrar data sakata taka birki da sauri. Mugun tsoron Uwangale take kamar ranta, tsoron da zata iya rantsewa bata taɓa jinsa ma wani ba. Wani lokacin har tunani take anya Uwangale mutum ce kuwa? Dan al'amarin fa yana da girman gaske a tsakaninsu. Haka dole ta tsaya tana sharar hawaye, data duƙar da kai kuma Uwangale ta daddage ta bata azababben mintsini, dole ta koma kallonsu. Haka aka raƙashe a gabanta sosai, dan abin kamar wasa sai gashi ya bada armashi. Aka fara zuba hotuna, can Oum ta hango Mamy, ai da sauri tazo inda take da kanta ta tura keken nata zuwa wajen taron aka fara hotunan da ita a haka, ALLAH ya sota ma Aunty ta takura mata ta saka kayan arziƙi, da baƙarmin ƙasƙantuwa zatai ba a wajen. Ko kallo bata ishi Abah ba, haka danginsa kaf babu wanda ya nuna yasan da fitowar Mamyn, badai zasuyi magana ba kodan darajar ƴaƴanta. Amma ita kanta tasan bata da daraja da mutunci a family ɗin Darma yanzu hatta a wajen ƙananan yara. Sai da ta gwammaci inama bata fito ba, dan tayi mugun jin abin ya taɓa mata zuciya. Ko hoto za'ayi bamai yarda ya jinginu da jikinta sai Maanal da Oum ke ƙoƙarin mata hakan. Kiran sallar la'asar yasa kowa ya wuce yin salla. Mazan suka fita mata suka shige ciki. Bayan kowa ya kammala aka kimtsa aka sake fitowa. Maijego ta sake sabon ado da wani azababbiyar atamfa lass data amsa sunanta ta ci kuka kuɗinta. Itama dai stones work ɗin aka zuba mata na ala tsine uwar mai ƙarya. Ta zauna ɗas a jikin Autar Ammie, ga wani ubansun diamond sarƙa da agogo da abin hannu, zobba da AA da kansa ya saka mata su. Shima yayi wanka ya canja shiga dan suma sunce zasu zauna ayi walimar dasu, sai dai can gefe aka shirya musu nasu kujerun a runfar motoci. Yaran ma an sake musu shiga ta alfarma. Daga haka aka sake ƴan hotuna a nutse sannan akai zaman walima dan malamar da aka ɗakko harta zauna. Yanzu ma tsabar mugunta Uwangale sai da ta fito da Mamy. Haka Babban Yaya ya koro su Saheeba bayan ya gama zagesu ciki da bai ita da Nuratu. Itama Nibras da ƙawarta tazo Yaya Fawzan korosu yayi wajen walimar. Ƙawar sai wani kwarkwasa take masa. Zuciyarta na sake narkewa akansa, a tsakanin nan gaba ɗaya hankalinta nakan Yaya Fawzan, shiyyasa a yau ta gama ƙudira ɗora Nibras akan keken ɓera game da AA ta kuma yo mata shiri na musamman, dan gwara tai sanadin kaɗata waje ta samu ta shigo daga ciki kada son Fawzan ya halaka ta. Ta gyara zama zata fara ɗora Nibras ɗin akan abinda zatai game da AA Yaya Fawzan ya shigo, dole ta haƙura sai an tashi a walimar nan sannan. An fara gabatar da addu'a mai ratsa jiki ga maijego da yara da babansu. Sannan kankanin da ƴan uwa da abokan arziƙi. Malama ta gyara zama ta fara zuba lecture akan wacece uwa..........✍️204

.........Bayan an ragargaza bayani akan wacece uwa da haƙƙokinta aka ƴaƴa, aka koma wanene uba da haƙƙoƙinsa akan ƴaƴa. Sannan aka koma kan ƴaƴa da haƙƙoƙin iyaye a kansu. Duk wanda yace jikinsa baiyi sanyi ba a wajen nan yayi ƙarya. Sai irinsu Mamy da zuciyar kawai ke ci da wuta na rasawa daga tasu kyautar, dan kafin a tashi a wajen zazzaɓi ya rufeta. Anci ansha daga kayan daɗi nau'i daban-daban. Dan bayan abincin da aka shirya daga ɓangaren gidan Darma su kansu su Ammie sun shiryo nasu abincin, haka ma Hajiya Shuwa. Aiko naman kaji dai yaci ubansa a wannan walima. Dan ɗaya-ɗaya aka dinga bamu😎, ku tambayi ƴan Arewabooks da ƴan discussion house sunyi wadaƙa gwargwadon iko. Su o'e harda zubawa a jaka ina kallo. Amma zan rufa asiri bazan faɗa ba🤭😂. Yo nima mai gulmar sai da na ɗiboma Abdull, wa zaiga banza ya ƙyale yo jama'ata😆🤌. Lemo ko ba'a batun ƙananan ƙwari su coc.. fanta haba mun girmesu. Kwali muka dinga buɗewa da kwalaban non alcohol zunduma-zunduma. Harda su fruits fresh na saukar da abinci ga wanda sukaci yay musu yawa. Kowa ba wajen zamansa za'azo a ajiye maka souvenirs ɗinka mai ɗauke da hoton hannun AA dana Maanal cikin juna. Sai Babie da Naufal da suka fito masha ALLAH. Sai sunan Anum a ƙasa itama da hotonta. A ciki akwai kayan suna da agogon bango dana hannu daga kamfanin Maawad. Yo yau ranar balantiya da agogone can naga mutanena ana washe baki za'a saka agogon mawaad wannan shekarar. Lokacin da Najma ke ma mutane godiya da fatan komawa gidajensu lafiya tace akwai tambayoyi da wasu suka rubuto suna son dan ALLAH a amsa musu maijego ko angon jego daga Maawad Company. Dariya aka ɗan sanya, amma kowa ya ƙagu yaji tambayar. Najma dake murmushi itama ta ce, “Tambaya ta farko daga ma'aikatan kamfanin Maawad, sun ce dan ALLAH suna son boss ya gaya musu minene ma'anar MAWAAD yau, sun taɓa tambaya a shekarun baya yace idan lokaci yayi zai gaya musu, to a yanzu suna fatan ace lokacin yayi Please”. Karo na farko da AA ya saki murmushi mai laushi da narkar da zuciya. Ya ɗan kalli sashen da ma'aikatansa suke maza da matansu dan yasan su Zaharadeen ne da wannan gulmar, yaran nan sun sashi gama da yawa fa, kafin ya kalla Maanal dake kallonsa itama. Murmushi suka sakarma juna, sai kuma ya miƙe anutsensa, cikin takun san nan na isa da ƙasaita da nutsuwar rashin garaje ya je inda Najma take. Cike da girmamawa ta miƙa masa mic ɗin. Ya amsa da kulawa kafin ya gyara tsaiwarsa ta izza dake narke zukatan mata, ido suka haɗa da CFO. Sai yaga kamar hawaye na neman zubo mata. Kauda kai tayi da sauri dan haka shima ya kauda nashi a nutse ya maida kan Mamy da ke kallonsa kamar zata cinye. A hankali ya lumshesu ya sake ɗaukewa daga kanta itama. Babu wani ɗar ko shakka ya ce, “Lallai na cancanci a tuna min wannan alƙawari na tsawon shekaru. Kuma dole na cikashi a yau kodan sake jaddada godiyata ga UBANGIJI daya kaini zuwa wannan rana dana gama fidda rai da sallamawar zuwanta. Kai tsaye sunan kamfanin MAWAAD dai sunaye biyu ne a waje guda, kamar yanda UBANGIJI ya tabbatar da masu sunayen a yanzu haka a jini guda. Ma:-Manaal take nufi. Waad-Ajwaad ne. Dan haka idan muka ɗauki farkon sunan Maanal, muka haɗa dana Ajwaad a ƙarshe shine zai bamu MAWAAD. Yanda sunayen suke haɗe haka kamfanin mallakin masu sunayen ne su biyu. Wato Besty na kenan. Ba Maawad Company kawai ba, komai na Ajwaad na Maanal ne, a dukkan abinda nake da shi a duniya sunanta da nawa ne a jiki, kuma haka za'a cigaba da gani har abada in sha ALLAHU”. Wani irin tsitstsinkewa jinin Maanal ya shiga yi, yayinda Oum, Abah, Babban Yaya, Yaya Fawzan ke wani irin murmushin farin ciki duk da sun san da hakan dan komai zai yi saiya sanar musu, Mamy ce kawai yake ɓoyewa saboda ta nuna ƙiyayyar Maanal a fili garesa tuni. Ai kam yanzu ma jitai numfashinta na riƙewa. Dan ba ƙaramin girgiza zuciyarta wannan bayani na AA yayi ba. Kamfanin nasa daya sha wahala, yake narke da dukiya zai ce nasu ne su biyu, babbar bala'i wlhy yau dole ƙura ta tashi a gidan nan bashi yiyuwa bari ƴan sunan su gama su tafi. Sauran mutane kam sai ƙus-ƙus akeyi, masu farin ciki nayi, masu al'ajabi nayi, masu hassada nayi. Najma ta sake amsar mic AA zai koma ya zauna ta ce, “Yaya ba'a gama ba fa”. Harararta ya ɗan yi sannan ya dawo ya tsaya, tana ƴar dariya ta ce, “Tambaya ta gaba ta ce (Ko zuwa nan gaba Boss AA Darma zai iya ƙara auren wata matar?)”. Kai tsaye ya kalli inda AS yake, shima yasan shine ya rubuto ta, AS kuwa yay ƙasa da kai yana dariya. Lips AA ya cije a hankali sannan ya ce, “Har abada, in sha ALLAHU, in ALLAH ya yarda babu ƙaddarar sake aure a rayuwar Ajwaad Aliyu Abubakar Darma. Ta farko yayi kuma ta ƙarshe, ina nufin ya auri AUTAR MATA Maanal Habib Umar Giro. Ina fata da addu'ar ko mutuwa tazo ta ɗaukeni da ita. Dan idan na ƙara aure ma ai kishi zan dingayi da amaryar nima, to nayina Besty na kishiya kunga ko dole na tayata kishi, idan amarya ta mata wani abu mu haɗu mu lakaɗa mata duka kunga laifina ƙawatace fa, aminiyata, maganin ayi ai kar ma a fara ko” ya zubama Manaal idanunsa da suka kaɗe, itama kallonsa take yi kamar zasu cinye juna. Sai kuma a hankali ta duƙar da kanta hawayen na sauka akan hannunta. Shima kan nasa ya kauda gefe yana miƙama Najma mic. Ta ce, “Yaya tambaya ta ƙarshe. (Yaushe ka fara son Maanal?).” Yanzun kam sai da ya saki murmushi da ya bama kowa mamaki. Ya kalla Maanal sannan ya juya ya kalli Babban Yaya, Abah, da Yaya Fawzan. Sai suma kawai suka shiga yi masa murmushi. Cikin dan laɓe baki yace, “Wato yarinyar nan tun tana da shekara biyar kacal bata cika ta shida ba ta mamaye zuciyar Ajwaad a kallo ɗaya, a lokacin da Ajwaad baima gama sanin kanshi ba shi kansa. Kai Oumna ma bata gama rainona ba fa, amma zuciyata da rigima harta zaɓo uwar ƴaƴa....” Miza'ai ba dariya ba. Shima murmushi yake har haƙoransa na bayyana, abinda mutane zasu iya rantsuwar da yawansu basu taɓa gani ba sai yau ɗin. Ya cigaba da faɗin, “Abinda ya fara riƙe zuciyata da ita da taga chocolate a hannuna ba wani ɗan basarwa yarinyar nan ta ce, “Kai tsammin mana”. Yay maganar cikin kwaikwayon muryar Maanal a wancan lokacin. Miza'ai in ba dariya ba, itako ta shagwaɓe fuska tana kallonsa. Shima fuskarsa da murmushin ya cigaba da faɗin, “Nafa mata shiru amma ƴar rigimar nan sai ta sake kallona gata a hannun Babu ta kirani marowaci. Kujifa ni da abuna, an taɓa ƙyauta dole ne? Abah ya ɗauki wasu ya bata a mota amma bata barni ba ta cigaba da min tsiwa harda gwalo. Bayan hakan fitinarta da jan faɗa, tsiwa, da rashin tsaro yasa naji a raina na samu ƙawar wasa, duk da fa na bata shekara ɗai-ɗai har fin takwas bata raga min nima, kai komai na Maanal sonshi nake, hatta fushi idan tayi narkani yake, wlhy a duk sanda tai min nisa zuciyata bugawa take, bugu mai ƙarfi da saka ƙirji a razani, da ace jarabawata shine rasata wlhy nima nasan bazan iya cigaba da rayuwa ba. Dan shekarun da suka gittama rayuwarmu ta sigar jarabawa ni nasan nayi tsahon rai ne kawai da hope ɗin watarana zata dawo, wata rana komai zai zama labari, jarabawace domin na sake sanin muhimmancin ta a rayuwata. Dan haka ku tayani da addu'a, ku tayani da addu'ar cigaba da sonta da ƙaunarta har ƙarshen numfashina, ku tayani da addu'ar mu mutu tare kamar yanda muka rayu a tare. Al'amarin wannan yarinyar da kuke gani mai girma ne a zuciyata, matuƙar girma a gangar jiki da ruhina, wlhy zan iya rantsuwar nafi Majnoon jin shauƙin so da yarda dashi akan Maanal fiye da yanda yayi akan lailah, nafi romeo jin abinda yaji akan juliat. Idan kuma har sun yarda suma sune a yankinsu da ƙabilarsu, nima na yarda irinsu ne a yankina da ƙabilata.......” Ya kasa cigaba da faɗa saboda wani irin rungumesa da Maanal tayi babu zato. Dan zuciyarta ta kangare, kalamansa neman zautata sukeyi, kassara mata dukkan garkuwar jiki suke. Rufe mata ido suke, mantar da ita suke bafa su kaɗai bane a wajen. Ai babu musu ya rungumeta tsamm a jikinsa shima. Tafi sosai wajen ya ɗauka. Malama ita kanta abin ya ratsata ya kuma birgeta. Waɗan nan sune irin mazan da addini ke alfahari da su, sune irin mazan da iyaye ke farin cikin samuwa ga ƴaƴansu. Da sune irin mazanmu a ƙasar hausa da mata bazasu taɓa sake kiran namiji da suna ba ɗan goyo bane. Da mata sun sallama matuƙar sallamawar da ko kwanciya suke maza na takasu bazasu taɓa su damu ba. Wata mace ba sauke nauyin gida kona hakkin kwanciya kawai taƙe buƙata ba. Tana son soyayya, tattali, kulawa, riritawa, adanawa, tana son taga namiji ya sallama gaba ɗaya a kanta. Wlhy idan har zata samu haka ko aure mijin yace zai ƙasa zakaga bata damu ba, to ta samu abinda take buƙata mizai ɓata mata rai a kishin wata da zata shigo kuma. Wasu dama ai rashin samun ingantaccen zaman ne da rayuwar aure ke saka zukatansu Zafafa a kishi da tsanar kishiya. Kiga ke baki gama wadatuwa ba wata ta shigo an sake raba abinda kike samu biyu ke da ita. ALLAH dai ya ganar da irin waɗan nan mazan kawai damu ma matan dan munada ƴan balaja'u muma ai. Idan ɓera da sata daddawa ma da warinta ALLAH dai ya ƙyauta kawai. Taro ya tashi lafiya, masu tafiya gidajensu sun wuce, masu kwana suka fara haramar salla. Malama tasha ƙyautar galleliyar mota daga Abah, su Babban Yaya suka cikata da kuɗi. Kayan suna sai da aka cika mata booth da su ita da muƙarrabanta. Ƴan Giro ma an kwashesu zuwa masaukinsu, sai zuwa jibi zasu tafi idan ALLAH ya kaimu. Zuwa gobe su Babu zasuga likita. Suma ƴan uwan Hajiya Yaya sun koma gidan su Ammie............✍️205

..........Su Aneesa, Amaal da su Madeena ne kawai suka kwana anan tare da Maanal. Washe gari sukai suyar nama raguna huɗune dama, sai naman sa domin ƙara afkin naman. Dan haka aikin bawai su kaɗai sukayi ba dan anan babu ruwansu da wani dangin amarya dangin miji. To ai family guda ma su Ammie da su Oum suke ɗaukar kansu. Duk bidirin da ake Maanal na ɗaki kwance tana barcin gajiya, yaran ko na sashen Abah tare da su AA. Sai wuraren 12 take tashi. Lokacin sun kusa kammalawa Oum ta shigo ma dan suna tattauna yanda za'a haɗa souvenirs na ƴan Giro da zasu wuce gobe idan ALLAH ya kaimu. Sai na ƴan uwan Hajiya Yaya da aka haɗa yanzu za'aje a kai musu dan zasu bi train zuwa 3 na yamma su koma Kaduna. Ƴan Kano kam sai zuwa jibi in sha ALLAHU rabbi. Cike da tsokana irin ta sako Amal ke kallon Maanal data fito, tana sanye da simple gown datai mata ƙyau, kai baka ce itace ta haihu ba sai ma wani ƙyau take fatanta na glowing saboda gyaran Hajiya Shuwa. Dan yau ma sunyi na safe saura na yamma. Itace ma tace tai kwanciyarta kada ta fito wajen masu aikin naman nan. “Hummm ƴar gatan Yaya AA, kina can kina barci abinki mu muna nan muna fama ko?”. Baki Maanal ta tura, sai kuma ta matsa jikin Oum ta rungumeta tana faɗin, “Oum kin ganta ko”. Oum dake murmushi ta shafa kanta tace, “Ƙyaleta kinji Baby na. Ai gwara da kika sha barcinki kika huta. Jiya an baki wahala sosai”. Murmushi Maanal tayi tana ma Amaal gwalo, ita kuma tana hararta sai ga AA ya shigo da Ahmad sarkin kuka kenan. Oum ce ta amshesa cike da so da ƙauna tana faɗin, “Oh oh oga rigima kenan, kai dai kaf halin tsohonka Fawzan na kuka ka iya shi. Kodai yunwa yake ji?”. Tai maganar tana kallon AA dake kallon Maanal, duk yau basu ga juna ba, dan da sassafe ya fita sai yanzu yake dawowa gidan yayi meeting a fadar shugaban ƙasa da wasu mutanensa. A hankali cikin nutsuwa da maganar nan tasa ƙasa-ƙasa ya ce, “Maybe Oum, dan Abah yace tun ɗazun suke a wajensa. Amma shi wannan boss ɗin ko ba yunwa ma akwai rigima ai.” Oum tace, “Sai fa boss ɗin, Baby zauna ki bashi abincinsa.”. Baki Maanal ta turo, sai dai yanda AA ya tsareta da idanu sai ta kasa cewa komai ta zauna Oum na saka mata shi a jiki. Zama AA yay a hannun kujerar da ta zauna yana kallon su, sai ga Ameerah ta shigo. Gaishe shi tayi, ya amsa da kulawa yana faɗin, “Ameerah samo min tea a kitchen ɗin nan naku”. Da to ta amsa tana juyawa, Maanal ta ɗago tana kallonsa tana yamutsa fuska saboda Ahmad dake shan abinci, bata san randa zata saba da feeding ɗin nan ba ita kam. A sanyaye ta ce, “Bakaci abinci ba?”. Shima yana wani kallonta a narke ya ce, “Baki bani ba Besty, yanzu baƙya tani sai yaranki ai a gidan nan”. “Kai Besty ban san sharri, amma Didi fa tace an shirya maka abinci a sama”. Hannu ya kai yana gyara hular Ahmad dake zamewa, sai kuma ya ɗan kalleta da faɗin, “Ai ban shigo nan ɗin bane sai yanzu. Bari kawai nasha tea ɗin, saina haura na ɗan watsa ruwa naga idan zan iya ci. Zanje muje asibiti da su Babu ma”. Tana ƙoƙarin yin magana da kai hannu fuskarsa ta cire zare daya ke akan gashin sajensa Ameerah ta dawo da tea ɗin. Amsa yay yana faɗin, “Thamks” a maƙoshi, ta jinjina masa kai da kallon Maanal. “Madam a kawo tea ɗin kema?”. Zatai magana AA ya ce, “Barta wannan zai ishemu kaɗan zan sha”. Kai kawai Ameerah ta jinjina ta wuce, sai ya kai kofin bakin Maanal. Yana sha yana bata cike da kulawa su CFO sukai sallama. Bashi da alamar tashi sai ma damar shigowa ya basu, Maanal ta gyara Ahmad dan bata son a gani mata jiki. Turus CFO da ƙawayenta suka tsaya suna kallonsu. Sai kuma ta ƙaƙaro murmushi da faɗin, “Ashema kana gida Sir”. AA da zuwan nasu ya bashi mamaki tunda yasan jiya tazo wajen walima a dake ya amsa yana kai kofin tea a bakin Maanal, itama ta sha abinta dan zuwa yanzu ta fahimci take-taken matar sarai akan mijinta. Zama sukayi ƙawayen nata suma fa AA ya tafi dasu, hakama Maanal ɗin so cute da ita kamar ba ita ta haihu ba. Ji wata soyayya mai narke jiki tea ɗin ma sai miji ya bata tabɗin. Sun gaisa AA ya amsa sau ɗaya ya basar, sai Maanal ce ma ta ɗan sake musu, sai kuma gasu Najma sun kawo musu ruwa da lemo da nama. Barka sukayi da ALLAH ya raya, CFO tai musu bayanin ƙawayenta ne sunzo ta nan street ɗin shine tace suzo su musu barka. Godiya Maanal tayi, dai-dai AA na miƙewa da jan hancin Maanal kaɗan yace, “Kin shanye min tea”. Murmushi tayi tana kallonsa a narke ta ce, “Kaine fa ka bani”. Gefen fuskarta ya sumbata ya amshi Ahmad daya gama yama koma barci yana faɗin, “Yana iya dake. My Kiddo zamuje ka taya Abiee wanka tunda Ommy tace jego take”. Ya wani kashema Maanal ido ɗaya yay wucewarsa. Murmushi kawai tayi da girgiza kai. Su CFO suka rakashi da kallo kamar mayu. Duk da CFO na aiki a Maawad babu wani sabo bayan na gaisuwa tsakaninta da Maanal. Yanzu ma sai ta kasa sakewa da su. Suko sun wani baje juna hira da cin kayan da aka kawo musu. Kusan mintuna arba'in sai ga AA ya fito tsaff da shi yayi wanka sai uban ƙamshi yake yi, inda Maanal take yazo ya miƙa mata lins na hannu, babu musu ta amsa ta saka masa. Ya wani duƙo ta saka masa hula tamkar sun manta da su CFO. Fuskarsa ya bata ta masa kiss shima yay mata sannan yace, “Ki kula min da kanki da twin's sai na dawo”. Kai ta jinjina masa tana murmushi tace, “ALLAH ya tsare min kai da tsarewarsa, ya baka kariya da ƙarfin ikonsa.” “Amin my everything”. Ya faɗa yana sake kissing lips nata sannan ya wuce. Ai zuciyar CFO sai taji tana harmutsawa. Bai ko kallesu ba ya wuce ciki-ciki yana faɗin, “Thanks”. Hawaye sosai suka cika zuciyar CFO, Dan kwallin data saka dai da'alama yabi iska. Tunda ko haɗa ido basuyi dashi ba. Kuma malamin daya bata ya tabbatar mata in dai basu haɗa ido da AA a yau ba gaskiya bazata taɓa samunsa ba har abada. Ganin tana share hawaye ƙawayenta suka lallaɓata sukai ma Maanal sallama suka tafi, dan suma dai sun san sai haƙuri kuma ƙawarsu ta rasa.....

_________★

Readers Also Read