Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 145

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 145

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 145: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 145. AA da kansa yaje har masaukin…

3,708 words

AA da kansa yaje har masaukin ƴan Giro ya ɗauki su Babu yakai asibiti. Sailu da Babu gwaje-gwaje akai musu da sake bada magunguna. Gwaggo ce akai ma sabon gwaji. Babu wani kai-kawo result ya nuna ta ɗauka itama. Duk da ta jima da sallamawa sai da tai kuka sosai, sai Ammie data samesu a asibitin ce ke lallashinta. RK dai ya zauna ya sake basu shawarwari da sauransu. Aka ɗan saka musu drip su duka sannan suka shiga office ɗin RK dan yace zasuyi magana. Result ɗin Mamy ya ciro ya bashi na gwajin HIV. Bayan ya duba zuciyarsa na wani kalar rawa ya ɗago yana kallon RK. Da ɗan rawar lips ya ce, “Uncle HIV fa?”. “Nima irin wannan yanayin na shiga da Dr Hamaad ya kawo min result. Haka na sake mata sabon gwaji amma still dai abu guda ya bamu. Na ma rasa inda zan kamo lamarin Ajwaad. Amma babu wanda ya sani gaskiya har ita, dama ina son ku dawo ne suma Yaya da Aunty muyi musu gwajin ko zamu samo bakin zaren”. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un AA ke maimaitawa kawai hannunsa dafe da kansa. RK ya taso cike da kulawa ya ta zauna a kujerar dake facing wadda yake zaune. Ya ce, “Ajwaad calm down, itafa rayuwa gaba ɗayanta jarabawa ce. Yanda mukai haƙuri dana baya yanzu ma haka zamuyi kaji.” AA ya ɗan murmusa kaɗan, idanunsa da suka kaɗe ya ɗan zubama RK. Sai kuma ya furzar da iska kaɗan. “Rafeeq bana fatan ace Oum da Abah suna da wannan ciwon suma. Rashinsa kuma zai sakani a wasiwasi mai girma na ina Mamy ta samoshi”. “Bana tunanin ta mummunar hanya, dan zan gaya maka gaskiya na jima ina bibiyar Aunty Kamila ban taɓa samunta da makamancin abinda zai iya sawa ta samu ba. Kayi haƙuri ɓoye maka abubuwa da nayi.......” Gaba ɗaya ya zayyane masa komai daya sani tun ɗan zamansu a Paris, har su suka dawo Nigeria suka barsu acan. Bai gama fahimtar komai ba sai bayan kawo Maanal Mawaad Company, a lokacin daya kaita gidansu ya gane komai na alaƙarsu. Tun a lokacin ya shirya barin rayuwarta, ya fara koyama kansa haƙuri da ita, duk da zuciyarta taƙi amsa saboda da gaske sonta yake har takai ya sallama gaba ɗaya ranar da tazo gidan Shahidah da motarsa. Sai kuma randa ya sameta a asibiti yaji maganganu su a ɗakin jiyyarta. Yaja numfashi da cigaba da faɗin, “Nata tunanin ta yanda zan gyara komai auren ya koma kanka amma ban san yaya zan yi ba, kuma bana son gaya ma kowa tunda Yaya ya gargaɗeni. Kawai randa naje Kano dan musu maganar kai kuɗi na samu Aunty Kamila taje tayi magana da Abbu da Baba Sardauna, sai kawai nai amfani da damar na zauna da Mah-mah”........✍️206

........“Ban ɓoyema Mah-mah komai akan abinda na sani ba, itama hankalinta ya tashi ta tabbatar min bazata taɓa yarda a aurama Maanal wani idan ba kai ba. Dan haka ta samu Abbu suka kirani muka tattauna sosai a daren muka samu baba Sardauna. Shima yayi mamakin jin cewar anga su Maanal amma baku gaya masa ba, amma sai yay muku uziri tunda ga yanda abin yazo. A wannan zaman muka tsara komai da maganar ɓoye maka saboda kada aunty Kamila ta biyo ta wani wajen ta hanaka auren tunda ba'asan ainahin abinda ya faru a wancan karon ba. Amma yanda ta nuna a zuwan datai Kanon tafi damuwa da a aura maka Nuratu sai duk muka sha jinin jikinmu da ita. Shine dalilin rufe komai sai da aka ɗaura aurenku kowa ya sani harda ku da su Yaya ma. Hatta riƙe Maanal da Yaya yayi ya hanata tarewa harda gudunmawar Baba a ciki, dan shi yace ayi hakan saboda aja zancen bikinka da Nuratu sam baya son haɗinku tarbiyyar yarinyar batai masa ba. Baya son kuma ya nunama Aunty Kamila ta biyo ta wani hanyar ta tursasaka aurenta matsayinta na uwa. So a taƙaice magana ta ALLAH ban taɓa kamata da wani abu mara ƙyau ba. Sai dai yanzu zamuyi wannan gwajin yanzu, daga nan sai mu tafi mataki na gaba dan dole sai munga results ɗin da zamu samu a kansu suma”. Kai kawai AA ya iya jin jina masa. RK ya shiga masa nasiha da kwantar masa da hankali. Dan yasan halinsa sarai....

Koda ya koma gida bai gayama kowa komai ba, yama samu ƴan Giro sunzo musu sallama dan asubanci zasuyi. Dama dasu Gwaggo ya wuce gidan. An haɗa musu shatara ta arziƙi ma kayan suna harda turamen zani da dubu ashirin-ashirin aka saka musu. Babban Yaya da Yaya Fawzan ne kuma suka bada kuɗaɗen. Oum zannuwa. Sai kayan suna na musamman, nama kam ƙaton botiki aka cika musu harma wanda basu zo ba suma da kayan sunansu. Itama Maanal da su Amaal kuɗaɗe da abubuwa suka haɗa musu sosai. Sun yima Babu ɗinkuna suka saka masa kudi masu yawa a account. Sai dare sosai suka wuce masaukinsu bayan anyi sallama. Washe gari sunayin sallar asuba suka wuce Haƙila harda kukanta, dan shi Sule yana nan an barshi za'a kaishi Rehab a fara treating ɗinsa akan batun shaye-shaye, AA nason ya gyara rayuwar yaron da ikon ALLAH a maidashi makaranta tunda kwata-kwata fa yanzu yake 15years da wasu watanni....

Suma su Amaal sun kammala komai daya dace zuwa azhar suka wuce gidan Shahidah. Maanal harda kukanta, dan kowa ya wuce ba'a barta da kowa ba sai yarinya ƙarama da zata dinga tayata da raino da ta saka aka taho mata da ita daga Giro. Sai Meeno data dawo nan gaba ɗaya tunda ta dage. Dama basu wuce ba sai da suka gyara mata ko'ina, dan haka komai neet Najma da Ameerah ma dake fama da kansu sun shigo sun ƙara gyara abinda ya dace, daga nan sukai zaman tayata hira data ɗauke mata hankali ta bata nutsuwa. Twin's ba wani zama suke a wajenta ba, sai idan suna kukan abinci ne ma ake kawo mata su. Suna sashen Oum da Abah wajen dangi.....

_________★

Da dare matuƙar gajiyar da Maanal tayi yasa da wuri tai barci, dan yaran ma sai Oum ce data shigo da su tai musu shirin barci aka kwantar da su bayan sunsha madara sunyi nak. Oum tai musu addu'a ta koma sashen ta dan sunata hirarsu da ƴan uwa ne tunda suma gobe in sha ALLAHU zasu wuce. Gashi idan an haɗu sam ba'ason a rabu, shiyasa duk daren tafiyar sai kiga an kusan kwana ana hira, ko Kano sukaje hakace ke faruwa suma. Meeno da Nafisa suna sashen Najma tare da sa'oinsu dake can. AA bai shigo ba suna tare da ƴan uwa ana shan hira suma. Da wannan damar Nibras data gama yankema kanta shawara a yau bisa tunzurawar ƙawarta ta lallaɓo ta shigo sashen. Kwana biyun nan duk ta gama lura da yanda ake haɗama AA abinci, sai tayi amfani da hakan itama ta shiga neman fruits salad da taji yana faɗa a haɗa masa ɗazun. Wanda Najma ta haɗa masa kuma ta manta shaf bata kai ɗakinsa ba ta ajiye a kitchen na sama a fridge dan ita ko Ameerah ke bashi abinci tunda aka fara shagalin sunan nan ko Amaal, yau Amaal sun wuce, Ameerah bata jin daɗi tunda tai sallar magrib ma bata sake fitowa ba tana a bargo. Ita kuma Najma hirar dangi ta saka ta mantawa dan AA ɗin da kansa yace ta haɗa masa fruits salad ɗin ma kafin su wuce nasu sashen dan yaji Maanal na cewa da tayi isha'i zata kwanta yau ta gaji. Koda ta kammala sai takai fridge na sama ta ajiye masa, ta dafa tea shima a flaks ta ajiye ta wuce nata sashen. A kitchen ɗin ƙasa ta fara dubawa, ganin bata ganshi ba ta haura sama tana ta waige-waige da fatan kar wani ya shigo, amma duk da haka sai da ta leƙa bedroom ɗin Maanal taga tana barci sosai ita da yaran fitila ma a kashe sannan ta koma ƙaramin kitchen dake a saman nasu ta buɗe fridge sai ko gashi ta gani. Murmushi tayi sosai, ta fiddo bowl ɗin ta ajiye, ta ciro abinda ke cikin kimono ɗinta ta warware takardan sai ga ƙwaya ƙanana har biyu. Abu ga samu ta daka su tana murmushi sannan ta zuba ta motse. Tray ta ɗauka ta haɗa masa komai ta saka akai ta ɗauki tray ɗin ta wuce bedroom ɗinsa. Yau ne karo na farko data taɓa shigowa bedroom ɗin tun bayan aurensa da Maanal. Ɗakin ya haɗu dan komai an canja shi. Sai ƙamshi mai daɗi da taji ɗakin Maanal nayi ke tashi anan ɗin ma. Baki ta taɓe cike da kishi ta ajiye komai ta fita. Kawai sai taji ƙamshinsa kamar yana hawowa saman. Da sauri ta shige kitchen ta kashe fitilar..

AA da barci ya ciwo idonsa ya baro hiran yana gama haurowa yaji ƙamshin turaren daba na Maanal ba, amma da yake gidan da mutane sai bai wani saka komai a ransa ba duk da ya ɗan ji mamaki tunda yasan Maanal bata bari a hawo mata sama, yana kuma jin daɗin wannan respect ɗin nata. Ɗakin da take ya fara shiga, ganin yanda suke barci ita da yaran yay murmushi kawai, a ransa yana raya kamar wadda tasha wani abu. Kissing na yaran yaje yayi itama haka, sannan ya fito dan wanka kawai zai yi ya dawo nan tare da iyalinsa zai kwana babu ruwansa da wani batun jego can. Koda ya shiga ɗakinsa kaya ya cire ya wuce wanka, sai da ya fito ma yake lura da tray ɗin nan. Ajiyar zuciya ya sauke yana zama da bathrobe a jikinsa ya buɗe bowl na fruits salad ɗin. Kamar ma zai haƙura da shan sai kuma fruits ɗin suka birgesa, dan exactly yanda Maanal ke haɗa masa ne, ya tabbatar koba itace ta haɗa ba ita ta gayama su Najma yanda zasuyi. Ko kawowar ma ya zata itace ta kawo masa, har yana ƙananun magana wai yanzu bata gashi sai ta yara. Haka dai ya ɗauka ya fara sha, sai kuma yay masa daɗi ya kuma sake yarda ita ta haɗa dan abincin Oum da Maanal ko a wani gida aka bashi sai ya banbance. Yasha sosai sannan yay shirin barci, ya ɗan zauna yana taɓa aiki kaɗan tea na kusa da shi bai dai zuba ba yana son fruits ɗin ya sauka. Sai mi zai faru kawai cikinsa ya fara ƙullewa. Wani barci ya fara cin ƙarfinsa. Tunfa yana jin zai daure harya kashe laptop ɗin yakai kwance batare daya sha tea ɗin ba dama a gado yake zauna. Kamar wasa barci mai ƙarfi yay gaba da shi, ga wata irin sha'awa na damunsa har a cikin barcin, jikinsa kuma yay masa nauyin daya kasa tashi ya je ɗakin Maanal yaga ko zai iya rage zafi koda bai samu mai gaba ɗaya ba. Amma ina kamar an dannesa da dutsina tsabar halin daya tsinta kanshi. Zuwa can kuma barcin ya tafi da shi gaba ɗaya ya koma mafarki...

Najma na kitchen abinta a kujeran work table tanata chart da ƙawarta dake ƙara tsara mata komai da yanda zata yi. Sai faman jin daɗi take da sakin murmushi. Gaba ɗaya ta kasa tunanin idan ta tashi mata fa ga gida cike da mutane. Abinda kawai take dubawa ai ta bugar da Maanal itama. Dan abu ta zuba mata a shayi da tasha da yamma batare da sanin kowa ba. Saboda shayin na musamman ne da Hajiya Shuwa ke dafa mata tana sha akai-akai ita kaɗai. Ganin lokaci yaja ta miƙe a hankali ta buɗe ƙofar bayan ta sake fiddo mayataccen turaren da ƙawar tata ta kawo mata ta mulke jikinta da shi yanda ya kamata. Ai sai taji kamar ana ingizata da remote. Eh tana son AA sosai, amma bata taɓa tsarama zuciyarta bin wata hanya dan ya kwanta da ita ba. Sai da ƙawarta nan tata ta fara kwaɗaita mata al'amarin. Da farko ma bata amsa ba dan tana jin tsoro, musamman data san wanene AA ɗin. Sai da ƙawar tata ta bata turaren nan ta shaƙa sai taji ta amince ɗari bisa ɗari. Cike da ƙwarin gwiwa na mallakar AA a yau ta tura ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. A kwai haske mara ƙarfi, hakan ya bata damar ganinsa kwance a gado yayi rufda ciki. Murmushi ta saki zuciyarta na ingizata, ta cire kimono ɗin jikinta ta yar, figigiyar rigar barcinta ta bayyana. Itama cirewa tai ta yar, ta koma haihuwar tsohuwarta sannan ta nufi gadon.........✍️

207

.........Cikin barci kawai AA yaji an kwanta masa a jiki. Dan bayansa ta haye ta kwanta rufda ciki itama. Sai wani sakin azababben ajiyar zuciya take yi da sauri-sauri, ta ƙanƙameshi hawaye na fita daga idonta a guje. ALLAH tana son AA, mahaukacin so ma da bata taɓama kowa ba a duniya. Bata tabbatar da hakan ba sai yanzu da take jinta a jikinsa. Kissing ɗin fuskarsa ta farayi zuwa kai da wuya da gadon baya a haukace, dama a buƙace take matuƙa da gayaran data sha. Kuma tunda suka dawo taƙi yarda da Yaya Fawzan kwata-kwata. Shima kuma bai nema ba dan yanzu kam ya gama ajiye ta inda ya dace da ita. Lokaci kawai yake jira. Tun AA najin al'amurin kamar mafarki harya farka. Hannu ya kai ya jawota a bayansa ya sauketa gefensa. A tunaninsa Maanal ce, dan mafarki ta yake yi, sai dai ƙamshin sam bai masa kama da nata ba, hannu ya kai jikinta nan ma sai yaji ba ita bace ba. Dan wlhy ko a wane irin yanayin zai iya gane matarsa. Hannunsa Nibras data gama haukacewa ta kama zata kai ƙirjinta ya janye. Cikin mayen magani dana masifaffiyar sha'awar da yake ji ya buɗe idanunsa da ƙyar, luuu ya kalla Nibras ya lumshe su, kamar wanda ke aiki da magic sai brain nashi ta sake hasko masa fuskar, da sauri ya buɗe idanun again dai-dai tana matsowa zata shige masa jiki. Babu shiri ya turata da ƙarfi, sai kuma ya tashi zaune yana dafe kansa dake sara masa na ciwo. Da ƙyar ya iya kai hannu ya kunna fitilar ɗakin haske ya gauraye ko'ina. Ya fisgi goran ruwa dake gefen gadon a bed side drawer ya ɓalle murfin ya juye a fuskarsa duk da sanyin da ruwan ke da shi bai damu ba. Dai-dai Nibras na sake matsowa tana hawaye da faɗin, “Dan ALLAH ka biya min buƙatata ko sau ɗaya ne. Sonka nake AA so mai tsanani da zai iya kasheni wlhy.......” wani irin hankaɗawa yay mata ta bala'i sai da ta wantsala ƙasa. Duk da jikinsa yayi week sosai haka ya ƙarfafa kansa ya miƙe, dan maganar da tayi ya fahimci wacece. Wani kalar tsatstsagewa zuciyarsa ta shiga yi. Ko ci kanka baice mata ba ya nufi ƙofa zai fita. Kawai ta tashi da gudu ta riga shi isa ta zare key ɗin jiki. Baya son yay mata magana, baya son kuma ya kalleta dan haka ya juya kawai zai je closet ya ɗauka wani key ɗin. Amma ƴar shegiyar nan ta taho a guje ta rungumeshi ta baya tana sakin kuka da cigaba da roƙonsa. Zuciyar AA ta gama zuwa maƙoshi, bai ma san ya fisgota a bayan nashi ba ya bugata da kujera ba. Ta saki wata kalar wahalliyar ƙara. Baibi takan ta ba ya wuce ya ɗauki wayarsa. Da ƙyar ya iya gano sunan Yaya Fawzan dan ko gani bayayi da ƙyau.....

★Kiran AA na shigima Yaya Fawzan dai-dai ya fito ɗakin Nibras yana mamakin ina taje kuma. Zuwansa na uku kenan bata nan shi kuma yana son ya amshi keys ɗin sashen ne data kwashe tun waccan ranar, sun rasa inda na ɗakinsa yake shi da Najma tun ɗazun. Shigowar kiran na AA ya saka shi dakatawa ya ɗaga. Koda ya kai kunne yanda yaji muryarsa sai da gabansa ya faɗi. A ɗan rikice yace, “Auta baka da lafiya ne?”. Da ƙyar AA yace, “Lafiyata ƙalau Yaya, ina son ka saki matarka yanzun nan, sannan ka tattaro min su Abah kuzo sashena”. Cikin mamaki da ruɗewa Fawzan Yace, “Wace irin magana ce wannan Auta, wace matar tawa?”. A fusace AA yace jakar da aka aura maka ta farko, dan igiyar aurenka ce kawai zata zama shamakin hanani abinda nayi niyyar yi yau. Tsinketa ne kawai zai bani dama dan itace kawai tai mata GARKUWA a waje na. Dan haka ina roƙonka dan girman ALLAH ka saketa koda itace alfarma ta ƙarshe da zakai min a duniya”. Rawa kawai jikin Fawzan ya kamayi, shi mutum ne da sam baya son tashin hankali. Amma zuciyarsa ta gama haska masa akwai babbar matsala, dan yasan wanene Ajwaad. Ajiyar zuciya ya sauke mai ƙarfi batare da sake yin wani dogon nazari ba ya ce, “Ajwaad raina fansa akan ku zuri'ata. Duk da ban san mike faruwa ba bazan tambaye ka ba, na saki Nibras saki ɗaya, saki biyu, saki.....” “Ya isa Yaya hakan ma ya wadatar. Nagode da wannan alfarmar. Saura dan girman ALLAH ka tattaro min su Abah yanzun nan”. Kafin ma Fawzan yace wani abu AA ya yanke kiran. Dai-dai Nibras na rarrafowa inda yake ta riƙe ƙafarsa tana kukan wahala da cigaba da roƙonsa ko sau ɗaya yayi amfani da ita, idan ba haka ba mutuwa zatayi wlhy. Hankaɗeta yay da ƙafar yabi takan hannunta ya wuce closet ɗinsa bai damu da ihun wahalar data saki ba. Wani tafkeken belt ɗinsa na ainahin fata ya ɗakko a inda suke a tsare cikin drawer na glass dake tsakiyar closet ɗin, harda su link na hannu, agoguna, da glasses. Gashi kamar a buge amma yana jin ƙarfi kaɗan, ko yaya mace da namiji ma ba ɗaya suke ba balle AA kallo ɗaya zakai masa kasan ko mazan ne a gabansa mai kada shi sai ya shirya. Wani irin zubama Nibras belt ɗin nan ya shiga yi. Ta fasa gigitacciyar ƙara mai ihu tana miƙewa, ina ya sake lafta mata yana taɗeta da ƙafa ta zube ƙasa. A duniya ya tsani yaga ana dukan mace, amma wlhy yau sai ya kakkarya wannan ƴar iskar ta yanda bazata sake moruwa ba a rayuwarta wannan alƙawarinsa ne. Dukanta yake babu tausayi ko ragi, a kallo ɗaya zaka fahimci sam baya cikin hankalinsa ma saboda fushi, AA akwai zuciya, kafin yayi fushi irin haka ne akan daɗe dan sai an kaishi maƙura, amma idan fa ya birkice ɗin nan bayaji baya gani sam.....

Cikin barci Maanal take jiyo ihu, ta buɗe idanu a hankali, wani ihu da Nibras ta kwaɗa mai gigitarwa ya sata zabura ta tashi zaune. Dan gadon yaran dake gefenta ta kalla, har sun tashi suma dan Muhammad ma da baida yawan kuka harya fara ƙunƙuni. Kasancewar bango ɗaya ne tsakanin ɗakin nata dana AA tana jin yanda ake buga ƙofar da bangon kansa, ai dole ta fasa ɗaukar Muhammad datai niyya ta fita da sauri, har tana buge wajen cs ɗinta sai da ta dafe wajan da hannu. Tabbas anan ɗin ne, kuma ɗakin AA, mace kuma yake duka. Maanal ta jima bataga abinda ya ɗaga mata hankali irin yau ba, wacece haka a ɗakin mijinta har yana duka. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ƙofar tai ƙoƙarin buɗewa amma a rufe gam, ta shiga bugawa tana kiran sunansa amma ina, sai ma Nibras da jin muryar Maanal ɗin ya saka shiga ƙwala kiran sunanta tana faɗin, “Na shiga uku Maanal ki taimakeni zai kasheni, wlhy kasheni zai yi Maanal..” Gigicewa Maanal ta sake yi tana jijjiga ƙofar, tama rasa miyya kamata tayi, key ne ya faɗo mata, da ɗan gudu ta koma ɗakinta wajen cs ɗinta na mata zafi saboda ta buge shi. Kasancewar ta san inda suke ɗakkowa kawai tai, ga twins sun rikice da kuka na bala'i amma batabi takansu ba ta sake ficewa, idannunta sun mata nauyi, barci take ji saboda abinda suka bugar da ita da shi, tsabar ƙarfin jini ne kawai kuma da yake ta kwanta da wuri barcin ya ragu mata sosai. Yanda hannunta ke rawa da ƙyar take iya gwada keys ɗin, a lokacin ne su Abah ke shigowa sashen. Tun daga ƙasa ihun Nibras ya ratsa su, da gudu suke rige-rigen hawowa steps ɗin. Dai-dai Maanal ta samu key ɗin ya shiga ta murza. Tana tura ƙofar suna ƙarasa hawowa. Da rarrafe Nibras ke fitowa a ɗakin duk ya fasa mata jiki da belt, danma ta samu ta hmmka kimono ɗinta da ƙyar ta rufe jikinta da anyi abin kunya. Cigaba da dukanta AA yake a hakan ma, Maanal na ƙokarin masa magana amma ko ganinta bayayi, su Abah da suka hawo kuma duk wanda yay yi ƙurin zuwa ceton Nibras sai Yaya Fawzan ya riƙeshi ya hana. Oum na kuka da kiran sunan AA amma baya jinta. Ga Maanal ɗin ma na kuka tana hanashi, ƙarshe dai ta shiga tsakkiyarsa da Nibras cikin matuƙar ƙaraji tace, “Ajwaad!! Wai mi kake yi haka?! Matar Yayanka ce fa!” sai kuma cikin sanyin muryar kuka ta cigaba da faɗin, “Dan ALLAH kayi haƙuri kada ka kasheta kasa kanka a masifa muma ka saka mu...” Cikin rufewar idanu da matsanancin fushi ya ce, “Tashi min a gana kona haɗa dake kema!!”. “Ka haɗa dani ɗin, nace ka haɗa dani ɗin, sai me idan ka haɗa dani, mace kake ma irin wannan dukan kamar ka samu ƙato”. “An mata ɗin, wlhy idan baki tashi min a gaba ba zan mareki kema. Kuma dukan wannan jakar jahilar yanzu ma na fara!!”. Hannu ya ɗaga zai maretan kuwa, dan idon AA a rufe yake halin yanzu baya gane komai. Ita kuma sarkin taurin kai ta tsaya masa ɗin ya mara. Yana gab da sauke hannun nasa a fuskarta Yaya Fawzan yazo ya riƙeshi. “Haba Ajwaad Bestyn taka zaka daka?”. “Tunda bata da kunya bakinta ya iya tsiwa sai me idan na daketa Yaya, tasan mi banzar nan tamun da zatazo tana bani umarnin abinda zanyi ita kuma”. Cike da tsiwa Maanal ta buɗe baki zata sake magana Yaya Fawzan ya mata tsawa. “Yima mutane shiru Lilly, stupid, kika ƙara magana zan ɓata miki rai”. Shiru Maanal tayi, dai-dai nan suka ji dariyar Nibras da babu wanda ya kula tabar wajan hankalin kowa ya koma ga rikicin AA da Maanal. Da sauri duk suka juya saboda dariyar tata da kukan twins. Ai babu wanda bai waro idanu ba.........✍️208

Readers Also Read