Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 146
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 146: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 146. .......Nibras da gaba ɗaya…
3,376 words
.......Nibras da gaba ɗaya kamar wadda ta haukace ta nufi wajen ƙarfen da glass da akai adon upstairs ɗin ta tsaya, cikin bushewar zuciya ga jini na zuba mata a inda ya jijji mata ciwo amma tana dariya, tace, “Ajwaad bani ka daka ba? To wlhy kaima sai ka ɗanɗana raɗaɗin wannan dukan a jikinka dan sai na kashe waɗan nan shegun yaran, sai dai ka sake mata cikin wasu ta haifo maka. Mugu azzalumi, kuma sonka bazan daina faɗar inayi ba ko za'a kasheni. Komai tsahon shekaru kuma sai na amfana da wannan lafiyayyen jikin naka, sai na ɗanɗanaka Ajwaad wlhy”. Babu wanda kalaman Nibras basu gigita ba a falon. Yaya Fawzan ya ɗan lumshe idanunsa yana kauda kai, wlhy ba kishin AA yake ba, nadamar auren Nibras na tsahon shekaru yake ji a zuciyarsa. A fusace AA ya nufeta, Babban Yaya ya riƙesa, Abah da gaba ɗaya zuciyarsa ke bugawa daga shi har Oum murya a sanyaye ya kira sunan Nibras. Amma sai cikin tsawa catai, “Abah ka barni, ka ƙyaleni bashi yace ya iya mugunta da taurin zuciya ba, shekara nawa ina nuna masa abinda ya dace yana wani basar dani shi mai taurin kai, to zan kashe yaran, ba shike nan ba naga ta ɗanyen kai. Idan kuma yana son rayuwarsu sai ya zaɓa amsar soyayyata ko su mutu....” A fusace AA ya ce, “Wlhy kema da sai na kashe ki, na kashe uwarki da kaf zuri'ar gidanku. Idan kuma ke kin cika ƴar halak ce ki kashe su mana!!”. Ƙoƙarin kuwa watsa su tayi downstairs, ai da sauri Maanal ta zube ƙasa tai kneeling tana kuka da roƙonta, hakama Oum kukan takeyi. Dai-dai nan su Umma suka shigo, dan a gabansu Fawzan ya kirata a waya, sai tace musu tana zuwa. Jin shiru sosai gashi ta fita a ruɗe ya sakasu aiko Rufaidah ta duba, sai ta koma a rikice take sanar dasu babu lafiya gidan fa a sashen AA. Shine suka taho, sai ga su Saheeba ma da Ameerah, dan yanda Babban Yaya ya fito suma ya rikitasu, Najma ma haka jin shiru ga yanda Yaya Fawzan ya fita yasa ta fito. Saheeba uwar gulma ta kira Nuratu dake sashen Mamy tace su fito gida babu lafiya. Uwangale muguwa tana zuwa taga mike faruwa ta koma ta cicciɓi mamy tasa a wheelchiar ɗinta ta turota suka taho sashen AA Tsoro kuma ya hanata magana ga barci a idonta. Ganin fa al'amarin babba ne Umma tai kiran su RK dake sashen baƙi a waya. Sosai ake lallashin Nibras ga ƴan biyu na kuka na tashin hankali saboda riƙon mugunta datai musu. Amma taƙi sauraren kowa wai wlhy sai AA yace yana sonta sannan. Shi kuma yace sai dai ta mutu. Humm ahalin Darma basu taɓa ganin masifa makamanciyar wannan ba a dukkan abubuwan da suka faru da su a rayuwarsu. Wannan wane irin shaiɗanci ne kuma? Anya brain na Nibras yana lafiya kuwa. Shegiya shiru-shiru da ita ashe sheɗaniya ce mai zaman kanta. RK ya fahimci zuciyar Nibras fa a bushe take, sai kawai yace a samo katifa asa a ƙasan, hakan kuwa akayi, saman ya fara haurawa cikin ƙaraji tace, “Wlhy duk wanda ya hawo upstairs ɗin nan a cikinku sai na saki yaran nan ƙasa sun ragargaje”. Cak RK ya tsaya a step na biyu daya taka, sai kuma ya kalleta da ƙyau yana jingina da bango. Ya ce, “Nibras ke musulma ce anya kuwa?”. “A'a bamagujiya ce”. Ta bashi amsa a gadarance. “Da alamar hakan”. Ya faɗa cikin jinjina kansa. Alama yay ma Babba yaya dake ta saitin inda yake ya cigaba da jan Nibras da magana. Ita kuma tana mayar masa cikin zafi, Abah na riƙe da AA dan jikinsa tsuma yake kawai, burinsa ya kama Nibras ya ɓalla ɓas kawai. Oum na rungume da Maanal dake durƙushe tana kuka sosai ga wajen cs ɗinta na mata azaba, tana jin kukan yaranta har cikin ranta. Yaya Fawzan kam ya kifa kansa ne a kafaɗar Abah ta ɗayan gefen shima yayi shiru. Karaf idon Nibras ya hango mata alamar da RK kema Babban Yaya da hannu, da sauri ta juya tana kallon Babban Yaya, ta ce, “Wlhy idan kuna son yaran nan kada wanda yazo inda nake”. Tsayar da babban Yaya daya fara fusata shima Abah yayi, sannan ya dubi Nibras cike da lallashi ya ce, “Daughter Please ki saurareni, yaran nan basu ne suka miki laifi ba, kiji tausayinsu kinji. Kalla yanda suke kuka, kalla yanda mahaifiyarsu ke kuka.....” “Abah kukan daɗi take yi ai, ita ba tana jinta wata shegiya ba, ta mamaye zuciyar Ajwaad ta hana shi kallon kowacce mace. To itama tana da zaɓi, kodai ta saka mijinta yace yana sona, kota rasa ƴaƴanta. Dan haka Maanal tunda sai kin bashi umarni yake ji bismillah”. Tai maganar tana yima yaran wani mugun ruƙo daya saka su tsagewa da sabon kuka. Rawa sosai jikin Maanal yake, tsabar yanda ta ruɗe batama san tabar jikin Oum ta koma gaban AA ba tai kneeling. Tana kuka mai ban tausayi, ta ce, “Yaya Ajwaad dan ALLAH, dan girman ALLAH kace kana sonta karta kashe min yara. Ka tausaya min Besty”. A zafafe ya ce, “Har abada! Nace ina son wannan dabbar, ki barta idan ta isa ta kashe su mana”. A fusace Maanal ta miƙe tsaye, cikin rufewar ido da ƙaraji ta ce, “Saboda baka san zafin haihuwar ba, baka san wahalar ɗaukar ciki ba. Kalla-kalla yanda take azabtar min da yara ƴan kwanaki goma sha uku kacal a duniya amma kake faɗin har abada ka faɗa mata kalma ɗaya. Anya kana da tausayi Ajwaad? Wane irin busashiyar zuciya ce wanna.....” Ta ƙasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙe ta. Wani irin zafi kalamanta suke masa a zuciya, kodan zuciyar tashi a sama take dama, sannan yanda tayi sai yake ganin kamar ma babu kishinsa a ranta, rashin kishi kuwa na nuna babu soyayya. Eh bai san zafin haihuwa da rainon ciki ba, amma duk raɗa ɗin da taji yayi imani da ALLAH ko baiji kwatankwacin nata ba shima ya azabtu ai, saboda koda can idan ciwon kai tayi sai yaji a jikinsa balle rainon gudan jininsa. Wani kalar zuba mata idanunsa da suka ƙara kaɗewa yayi sosai, cikin ƙunar rai har furucinsa na nuna wa ya ce, “Saboda baƙya so na da ƙaunata har kike biyema wata wawuya na amsa ina sonta bayan kin san minene matsayinta a wajena, Maanal saboda baƙya kishi n......” “So!! kishi!!? Har wani maganar kishi da so kake a wannan gaɓar Ajwaad, to naji bana sonka, bana kishin naka ƴaƴana kawai na sani, kuma wlhy idan aka kashe min su a dalilin taurin kan ka sai na barka na har abada!!!”. “To ki barni mana, idan kin barni sai me?? Na ce sai me??? Zan mutu ne??”. Yanda yake maganar yana wani irin turata zaka san AA baya cikin hayyacinsa kamar yanda itama ta fita a nata hayyacin. Gaba ɗaya Oum sai ta ƙara ruɗewa, haka ma su Abah, wannan wace irin masifa ce kamar waɗan da asiri ke ci. Magana Abah da Oum ke musu amma basa jinsu. Maanal tsiwa, AA zuciya. Sai da Babban Yaya abin ya kaishi bango yay musu tsawa. Cikin nunasu da yatsa ya ce, “Duk wanda ya sake magana a cikinku ALLAH sai na mareshi. Wane shirmene wannan? Kanku kuke son kunnawa fitina kome? Ga abinda ke da muhimmanci amma kuna neman ɗaukar wata hanyar ma daban ya rabbi.” Cikin kuka Maanal ta ce, “Yaya so yake ta kashe min su, kawai yace yana sonta ta bani yarana shine abu mai wahala. Wlhy ta kashesu nima mutuwa zanyi”. Sai kuma ta matsa da sauri tai kneeling tana fuskantar Nibras tana roƙonta cikin haɗe hannaye da kuka. Babu ko ɗar Nibras da ranta ke mata fes da yanda suke fitina ta taɓe baki da faɗin, “Kima daina wlhalar da kanki Maanal, rayuwar ƴaƴanki ko mijinki yace yana sona, yanda kuma ya saka aka sakan kema wlhy sai ya sake ki sannan zan bada yaran nan”. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wlhy kan Maanal neman bugawa yake yi. Ga cikinta na zafi, kanta na juya mata alamar jininta ya haura sama. Yuuuu duhu ya fara mamayeta, kawai sai jinta sukai ƙasa yiffff. Ai Alhaji AA ne ya fara zabura kanta, sai Abah da Oum. Shima Yaya Fawzan da Babban Yaya suka sanya salati. Da wannan damar RK ya fara jan ra'ayin Nibras da baƙar magana. Aiko sai hankalinta ya rabu biyu, kan Maanal da Yaya Fawzan ya ɗakko ruwa za'a zubawa, da RK da take zagin, babban Yaya na matsawa a hankali a hankali har ya zo bayanta, a bazata ya damƙe yaran, ai ko sai ta shiga kokawa da shi, shima bai san ya wanke mata fuska da mari ba, babu arziƙi ta saki yaran, dai-dai AA na miƙewa ya maida Maanal jikin Oum sai ihun Nibras kawai suka ji ya wani ɗauketa da mari. Hankalin RK da Babban Yaya nakan yaran, Yaya Fawzan da su Oum na kan Maanal, su Umma na ƙasa, ai ko ALLAH ya sake bama AA dama yajata ƙiyyy yay kitchen da ita, ihu take na neman ceto, dai-dai nan sauran mazan suka nufoshi dan amsarta kawai ya danna ƙofar kitchen ɗin ya saka key. Ya kuwa ɗora daga inda ya tsaya a jibgar Nibras. Gaba ɗaya hankalin kowa ya ƙara tashi, wasu suna dukan ƙofa ana kiran sunan AA kar ya kasheta ya saka kansa a masifa amma ina baya ma ji........✍️209
...........Tun suna jiyo kukan Nibras har suka bari, sai da ya sumar da ita sannan ya buɗe ƙofar ya jawota ƙeyyyy kamar kayan wanki, duk wanda yazo zai tareshi kawai sai dai ta hankaɗa shi gefe, sai dai kaji mutum teemmm a ƙasa. Dai-dai inda ta tsaya dasu twin's yazo kawai ya ɗagata cak ya wantsala ta tayi ƙasan down stairs, dan kwashe mata ƙafafu AA yay ya hankaɗata ta wajen. Gigitaccen ihun data saka ne ya farfaɗo da Maanal, gaba ɗaya suma suka miƙe akai kan AA wasu na rige-rigen sauka downstairs. Shiko ko a jikinsa sai ma wani irin zubewa da yay zaune ya jingina da glass ɗin wajen ya zauna kansa a duƙe irin na matsanancin mutum a baƙar zuciyar nan kawai sai ga hawaye. AA fa akwai zuciya ta bala'i, kawai idan baka taɓo abinda zakaga zuciyar bane ba sai ka ɗauka mai rangwame ne miskilancin kawai ya iya. Da gudu Maanal data zabura tayi wajen, ta inda yake tazo ta leƙa ƙasan, sai kuma ta ɗago ganin Nibras wanwar a downstairs ɗin, kodan idonta a birkice suke bama ta gane akan mi Nibras ɗin ta faɗa ba, zabura tai zata bar wajen AA ya riƙe hannunta batare daya ɗago ba. Tai ƙoƙarin fisgewa kawai ya fisgota ta faɗa jikinsa. Sai kawai ya ƙanƙameta....
A downstairs kam tuni su Umma sun kai ƙasa. Hajiya Majdiya ta saka yatsarta a hancin Nibras da sam bata numfashi. A ruɗe ta ɗago, dai-dai itama Mah-mah na saka hannunta a wuyan Nibras ɗin. Ta ce, “Da ranta suma tayi ku bani ruwa.”. A guje aka kawo ruwa aka sheƙa mata, a gigice ta fasa wani ihu, sai kuma ta kasa cigaba saboda wahala da yanda illahirin jikinta ya amsa. Tabbas badan ALLAH ya taƙaita al'amarin akwai katifa da aka sanya ba babu abinda zai hana ɗayan biyu faruwa. Kodai Nibras ta mutu, ko ta karairaye, kota samu matsalar laka. A hankan ma wani gigitaccen ihu ta sake saki da aka motsata sai kuma tayi ɗiff alamar ta sake suma. A sama kam kowa hankalinsa nakan twins. Yaga kayan jikin su twins kawai Babban Yaya da Yaya Fawzan sukayi dan basu da haƙurin zaman cirewa. Suka shiga dudduba yaran RK da su Oum na tayasu, Muhammad ne yaji ciwo a hannu, shiyyasa kukansa ma yafi na Ahmad yau. RK dake ɗan matsa hannun yaran na sake saka kuka yace, “Yaji ciwo a hannu, bara na duba wake asibiti ta ɓangaren ƙashi sai yazo yanzu a duba su kar yay tsami”. Sai lokacin suka sakko ƙasa suma, dan falon sama bai kai girman na ƙasan ba yayi musu kaɗan. Mamy da a karo na farko taji wani irin nauyi a ƙirjinta tana zaune a wheelchiar ɗinta ta zubama Nibras idanu kawai, batace tana son su twins ba saboda daga jikin Maanal suka fito, amma wlhy jitai zuciyarta ta mata nauyi da abinda Nibras tai musu. Sanda AA ke magana cikin ƙarajin nan jininta tsitstsinkewa ya dinga yi, da gaske fa tana son AA, kai tana son yaranta ma fa, karo na farko zuciyarta motsawa take da shauƙi mai girma akansu dakan mahaifinsu da take ƙoƙarin ganin ta danne a tsakanin nan. A sama kuwa AA da Manaal ne kawai suka rage. Dan tunda ya jawota jikinsa ya matseta ya wani lumshe ido sai furzar da huci yake akai-akai kawai ya kife kansa a jikinta, itama bata da ƙarfin ƙwace kanta dan azabar da take ji a wajen cs ɗinta. Cikinta ma ya ƙulle. Babban Yaya na tsaye a hanyar benen dan in har suka bar wajen dukansu AA ya tashi ba suma ba ko mutuwa Nibras tayi kanta zai sake yi. Idanunsa idan ya buɗe sai in kana da juriya da jarumta ne zaka iya cigaba da kallonsu saboda yanda suka kaɗe suka juye gaba ɗaya. AA fa akwai masifar nacin faɗa, yanda kasan kurma haka yake a naci faɗansa baya mutuwa. Shiyasa ko zamanin Maanal ta takalo faɗa ya tafi ramako kwana da kwanaki yake yana bibiyar yaro shiyasa ake tsoron faɗansa... Nauyin da Maanal tai masa a jiki da wani irin fisga da numfashinta yayi ne ya ɗaga masa hankali, ya ɗagota da sauri yana kallon ta, ina ta sake sumewa fa, girgizata ya shiga yi yana kiran sunanta, hakan yasa babban Yaya matsowa da sauri inda suke, akan hannun Maanal idonsa ya fara sauka ta dafe wajen cs ɗinta har jini ya fasa kayan barcinta ya nuna a hannunta. Hankali tashe ya ce, “Jini kuma?”. Da sauri AA ya kallesa, babban yaya ya nuna masa hannun Maanal, cikin sauri ya kama hannun ya ɗaga, jinin ne kam tabbas, rigar ya janye jikinsa na ɓari, tabas wajen ne kuwa ke jini. Ai sai ya fasa ƙara sosai yana miƙewa da ita, su Oum na ƙoƙarin dawowa saman ya sauka da ita. Da sauri Babban Yaya dake biye dasu ya musu bayani. RK yace, “Ai kawai muje asibiti”. Ai kafin ma su fito AA ya saka Maanal a mota, ALLAH yaso key na hannun drivern Abah dan motarsa ce. A tsawace ya ƙwala kiran sunan Drivern, sai gashi da gudu dan su basu san mike faruwa ba. Gaba suka yi, aka bisu da su twins da Nibras. Sannan mazan ne kawai suka bisu ance matan su zauna tunda dare ne, duk da ma asuba ta gabato, dan kusan uku da arba'in lokacin. Haka suka haƙura dole badan sun so ba......
_________★
Anan Kano kam rayuwa ta ladabtar da Huznah. Dan horon da Sageer yay mata yayi matuƙar tasiri a kanta, duk da shima dai ya wahalu kwarai da gaske saboda mutum ne mai yawan buƙata. Duk wanda yaga Huznah a yanzu dole ta bashi tausayi, ta canja matuƙar canjawa ta maida al'amarin ta ga UBANGIJI. Kullum cikin sallar dare take, karatun Alkur'ani da sadaka. Duk abinda Sageer ke so tana ƙoƙarin yi masa, duk wanda baya so tana ƙoƙarin kiyaye wa. Abubuwa da bata iya ba haka ta dinga binciken online class's tana shiga domin koya. Sai ga Huznah yanzu harda ƙulla ƙawance da maƙotamsu su Zubaidah. Yayar Zubaidah bata da matsala sam, haka ta amsheta hannu biyu bata nuna mata komai ba kuma data musu a baya. Sai ma ƙoƙarin jan Huznah take a jikinta kamar ƙanwarta. Ta canja alƙarta da ƴan gidansu gaba ɗaya. Ƙannensa su Khadijah da wanda ke gidan aure har wanda suke uba ɗaya yanzu jansu take a jikinta. Haka zatayi abinci duk juma'a yaji nama ko kifi ƙular Baba daban ƙular ƴan gidan daban taje ta yini ana wasa ana dariya tana taya surukan nata ayyuka duk da suna hanata sai yamma idan ya tashi aiki yaje ya ɗauketa su wuce gida. Yan Abuja ma haka take kiran Hajiya Yaya da Ammie ta gaishesu. Suma hakan yana saka su a farin ciki, dama tsakaninta da ƴan uwanta yanzu normal ne, har su Shahidah da Amaal kira take, har Manaal ma tama barka. Waɗan nan canje-canjen da Sageer ya gani a tare da ita ya sashi fara sakkowa shima. Da wannan damar tayi amfani wajen bashi haƙuri da neman gafararsa, tun tanayi baya tanka mata harya fahimci da gasken take komai ya wuce. Sai kawai ya haƙura suka shirya, ranar dai taci ƙaniyarta a wajen maza, dan sai da ta gwammaci kiɗa da karatu. Kwana biyu yana biyan bashin sa tayi laushi sosai a hannunsa kafin ya ɗauketa sukaje shopping ya kaso musu kuɗaɗe ita da Fodio ɗinsa. Sannan yay mata batun aiki da aka samar mata. Farin cikin sosai tayi tana rungumesa. Yay murmushi da sumbatar kumatunta yana lakace hancin Fodio dake gefensu. “Babana kaga mamanka zata karyani ko”. Huznah tai murmushi da faɗin, “Babansa dai zai ƙare min ruwan jiki”. “A to tunda haka ne zona ƙarasa ƙarar da shi sai muje asibiti a ƙara mana wani”. Zillewa tai tana dariya, sai da ta shige kitchen ta leƙo tai masa gwalo. Sassanyan murmushi ya saki yana mai lumshe idanu da buɗewa. Finally Huznah ta zama Sageer, Sageer ya zama Huznah. ALLAH ya cigaba da basu zaman lafiya da haƙuri da juna. A tsakanin nan kam har ya fusata aure zai ƙara amma yanzu ya haƙura. Babu batun kishiya, zai tsaya tsayin daka su gina rayuwarsu kodan mahaifiyarta tasan dan ka aurama ƴarka talaka ba shike nufin watarana bazasuyi arziƙin ba, ba shike nufin bazasu samu farin cikin rayuwa ba, ba shike nufin aurensu bashi da darajar kaiwa na auren kai kuɗi ba. Tun daga wannan lokacin farin ciki mai girma ya wanzu a gidan man Sageer. Matuƙar gatanta Huznah yake, da safe su shirya su tafi aiki tare bayan sun ajiye Fodio a gida wajen mamansu da abincinsa. Bayan sun taso su biyo su ɗaukesa su dawo gidansu, su raba dare suna kashe juna da soyayya da ƙauna. Basu zauna a haka ba ya fiddo musu hanyoyin kasuwanci, dan haka suka dinga sayen atamfofi, yadika, sarƙoƙin da takalma suna kaiwa wajen aikinsu, karshen wata idan an ɗauki albashi a haɗa musu kuɗinsu. Abin kamar wasa sai ga shi har da bags, veils, da wasu abubuwan ma duk suna kawowa. A'a basai suka fara planing buɗe shago ba anan anguwarsu koda ƙarami ne, aiko sai UBANGIJI ya sanya musu hannu shago ya tabbata. Kafin kace mi *_FODIO COLLECTION_* ya zama wani abu. Hakan ya saka Daddy farin ciki ya ƙara musu jari mai nauyi, sai kawai suka sake buɗe wani shagon ma da wajen kiwon kaji. Huznah kuma aka ɗan fara amaye-amaye. Hankalinta zai tashi ga yaro bata yaye ba man Sageer yace karta wani damu yana son kayansa. Dole itama ta kwantar da hankalinta, ta kuma fahimci ta samu cikin nan ne lokacin da suka shirya akan faɗansu ya dinga mata punishment. Abin ma sai ya dinga bata dariya, shi kansa data ɗakko masa labarin dariyar ya dinga yi da tsokanarta. Ta rungumeshi tana ɓoye fuskarta a jikinsa dan taji kunya..........✍️
😂Haka duniya take dama. Huznah dai ta bamu kunya ta kanainaye man Sageer ɗinta. To wlhy ƴammata izna a gareku, Kinga auren talakan nan ko auren dole da kike ganin iyaye sun miki dan sun zaɓa miji, wulaƙanta namiji dan yazo gunki bashi da ko sisi ko gidansu bai kai naku gidan kuɗi ba, rufawa kanki asiri ki barma UBANGIJI zaɓi, wataran sai kiga komai tamkar mafarki kamar yanda Huznah ta gani a yau. Bada kuɗi kawai ake samun farin ciki ba. Bamu ce ki auri wanda baida abinyi ba, a'a wannan kuma ganganci ne hajiyata. Mai neman nakansa muke magana, ba ƴan zaman kan layi ana irga motoci ba da rantsuwar sai na sayi irinta nan gaba. Koda zaman kashe wandon zai sayi irintan ban sani ma ɗan ƙaniya ba. Duk abinda kikaga bai zo hannunki ba to ki yarda ba alkairi bane a gareki sai ki zauna lafiya. ALLAH ya tsaya mana akan dukkan al'amuran mu, talakan dai wataran shike zama Dangote 🥰🥰🥰😘👍.210