Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 35
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 35: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 35. .........Bayan yin hakan kamar…
4,428 words
.........Bayan yin hakan kamar Fateema ta haƙura tabar Aliyu, zuwa wani lokaci kuma saita dawo da zancen. A wannan gaɓar ma sunyi rikici sosai da har ya kaisa ga kai ƙararta ga Baba Sardauna da Ummu. Dole sukai zama dasu domin sasanta rikicin. Sai dai a wannan sasanci ma bawai Fateema tabar wannan rikici bane, dan ko'a gaban su Baba Sardauna tace tana akan bakanta. Shima yace yana akan bakansa. Fateema ta cigaba da naci da takurama Aliyu akan batun aure da yaƙin son fahimtar da su Baba Sardauna dalilinta. Tun kowa bai fahimceta ba har aka fara goya mata baya. Musamman da taga su Baba Sardauna kamar basa so sai ta shirya tai tafiyarta gidan Kakanninta wato Alhaji Lawan mahaifin Kasheem Kura. Sai da ta bari hankalin Aliyu yay masifar tashi sannan ta bayyana kanta bisa tasota gaba da Baba Lawan ɗin yay suka zo gidan Baba Sardauna. A wannan zamane suka tattauna sosai Baba Lawan ya nuna musu Fateema ta fisu gaskiya, ya kuma kawo hujjoji da dole suka amsa kodan kasancewarsa Uba ga harsu su Baba Sardauna ɗin. Duk da haka har a lokacin shifa Aliyu bai gamsu ba. Amma baice komai ba. Sanin halinsa yasa anan Fateema tace ayita ta ƙare dan karma yace ya fasa. Ya zaɓa a ƴaƴan dangi duk wadda tai masa in ma a gefe ne ma duk taji ta gani. Ai ko a fusace Aliyu ya balbaleta da cewar shi bai son kowa. Ita da tace taji ta gani sai ta kawo matar tunda ita zai aurowa dan ita ta damu. Dariya kawai su Baba Sardauna sukayi, dan sun tabbatar fa Aliyu bai ƙaunar batun ƙara auren nan sam. Aiko Fateema bata gusa ba tace to ga ƙawarta aminiyarta Kamila, tasan halinta tasan tushenta ta kuma yarda da tarbiyyarta. Wani mugun kallo Aliyu ya watsa mata kuwa. Itama ta murguɗa masa baki ta ɗauke kanta dan zuciyata ta gama rufewa ita dai kawai Aliyu yay aure su samu yara ace nasu ne. Anan ma Aliyu yaso tirjewa. Amma sai su Baba Sardauna sukaita lallashinsa da ƙarfafashi. Badan yaso ba ya amsa kawai. Ammafa suna komawa sashensu ya balbale Fateema da faɗa itako ta masa banza. Ita dai tunda burinta ya cika yaje yayta yi. Anyi haka da sati ɗaya Fateema ta shirya taje har gida ta tunkari Kamila da zancen. Ruɗewa Kamilar tayi. “Haba Fateema wace irin maganace wannan. Shin kina zargin ina son MIJINKI ne komi?.....” Hannu Fateema tai saurin ɗaga mata. “Kinga Kamila kada ki sauya min magana. Ni ban taɓa zarginki da koda kwatankwacin hakan ba. Hakama mijina nasan wanene shi, dalilin ƙara auren ne kawai ya taso masa. Kamila da'aje a auro wadda ban san halinta ba tazo ta rabani da shi ba gwara wadda na sani nasan halinta tasan nawa ba. Ina sonshi Kamila so mai tsanani, bazan so wadda zata zo ta cutar damu ba, domin maganar aure fa ake ba hutu ko zaman wucin gadi ba. A gaba ɗaya na hanga na hango kece kawai halayenki sukai min dai-dai da rayuwar mijina. Na kuma tabbatar miki zai soki kamar yanda yake sona in sha ALLAHU in har kin cigaba da zama akan ƙyawawan halayenki. Ba tallarki nai masa ba, haka kema ba tallarsa nake miki ba. Cancantar kasancewar mu a inuwa guda mu uku kawai na hango. Ki taimaken Kamila kada kice a'a, dan cewar a'a ɗinki na nufin wata da ban sani ba zata shigo min gida. Bai zama lallai ta kasance mai ƙyawun zuciya irinki ba. Maybe ta rabani da shi, maybe ta maidani gefe maimakon farina ya koma ganin baƙina da kasawata. Amma ke fa. A tsahon shekaru uku da muke tare ina jinki tamkar jinina, tamkar wata twin sister ɗina da muka tashi tare muka girma tare. Dan ALLAH ki tausaya min, ki auresa kizo ki haifa mana yara mu haɗu mu rungumesu tare. Mu rainesu tare, mu basu tarbiyya tare, su tashi a tskaninmu tare. Ba'a auro wadda kota haifi ƴaƴan zasufi ƙarfina ba, su ringa min kallon matar uba ba uwa ba. Please na roƙeki”. Kuka ya sarƙe Fateema. Itama Kamila kukan takeyi, sun jima a haka kafin Fateema ta miƙe ta tafi, tare da bata damar yanke hukunci....
To bayan dai kai ruwa rana da faɗi tashi, da kace nace da ƙyar dai Kamila ta amince bisa tsayawar ƴan uwanta biyu da suka dawo Nigeria a lokacin tare da mahaifiyarsu. Sosai farin ciki Fateema ta nuna da amincewar Kamila, taje har gida tai godiya. Anan ne suka fara sanin juna da sauran ƴan uwan Kamila da kuma mahaifiyarta da a yanzu itama take ƴakin neman komawarta ga mahaifin su Kamila ɗin. An fara shigi da fici akan auren Aliyu da Kamila, sai dai shi ango ya tare gabas ya tare yamma akan shi babu ruwansa. Da ƙyar ma ya amince yaje yaga Kamila a gidansu sau biyu. Dai-dai da lefe da sadaki duk Fateema ta biya. Dan kaf Family ɗin Baffa Ishaq Darma nada kuɗaɗensu a asusun bankuna tun daga manya har yara. Kamar yanda Fateema ta buƙata babu wanda ya saka mata hannu a hidimar wannan aure itace tai komai da kuɗaɗen asusun bankinta. Sai abincin taron biki ne da abubuwan da suka biyo baya Baba Sardauna ya sauke mata akan dole ba dan taso ba. Haka dai aka ɗaura Auren Aliyu da Kamila. A kuma lokacin ne Baba Sardauna ya bama Aliyu gidan zama, dan yace yakamata shima ya koma nashi da iyalinsa yabar gidan gandu. Hakan baima Aliyu ba, amma baya iya musu dole ya amsa. A sabon gida aka kai amarya Kamila, ita kuma Fateema tace sai bayan kamar wata guda zata tare. Da kanta taima ango rakkiya gidan amarya. Sai kuma bayan ta koma gida taci kuka harta godema ALLAH. Daga baya kuma ta maida komai ga ALLAH taita sallolinta harta samu natsuwa zuciyata tai fayau kamar ba ita ba. Sai ma walwalarta ta ninku a safiyar ranar. Har Aliyu da yazo gidan ya nuna jin haishin yanda ya ganta cikin farin cikinta. Wai ai bata kishinsa ta masa auren dole. Bayan dariya kawai bata kulashi ba ita dai. Tunda dai taci nasara sai fatan kuma ALLAH ya azurtasu da abinda ake nema... To da farko dai zaman Aliyu da Kamila babu wani armashi. Dan bai taɓa kulata a shimfiɗa ba. Baya sakar mata fuska. Baya zama suyi hira. Takurar Fateema ma ke sakashi zaman gidan amaryar da cin abincinta dan yasan idan yaje can wajenta ba bashi zatai ba. Gashi ta saka masa takunkumin bayan sati ɗaya ta ƙara masa sati uku wata guda zai yi a wajen amarya. Su Umma kuma sun goya mata baya. Hakan kuwa dole ya cika wata gudan nan a wajen Kamila sannan Fateema ta tare a gidan, har lokacin kuma bai taɓa kusantar Kamila ba. Itako Kamila hankalinta a tashe yake, dan bata tabbatar tana son Aliyu so mai tsananin gaske ba sai a yanzu da suka zama ma'aurata. Yanda yake mata, ko duk motsinsa Fateema dai yasa ta fara jin kishin Fateema mai tsananin gaske a zuciyarta. A ganinta ba'ai mata adalci ba. Idan ance Fateema tasa aka aurota to ai dama bawa baya wuce ƙaddarasa. Tun ran gini tun dan zane. Koda sawar Fateema koda rashin sawa dama ALLAH ya ƙaddara sai Aliyu ya ta zama mijinta. Wannan zafin kishi daya fara taso mata yasa ta tunkari mahaifiyarta da ƴan uwanta da batun, maimakon su tausheta su lallasheta su kuma sai suka fara ɗorata a hanya mara ɓillewa. Aiko ta mitsithtsike ido ta nunama Aliyu bafa zata yarda ba. Dan yanzu matsayinta ɗaya da Fateemar da yake damun mutane da batunta. Tofa wannan abu ya tayar ma Aliyu da hankali, yo tunkan aje ko'ina kenan ma. Tab ɗin jan inji mata, ai dole yayma tufƙar hanci. Nan fa ya zauna ya warware Kamila tsaf da rashin mutunci, yo har a gayama bafillace zuciya da baƙar magana. Uwar watsi sukai yace taje gida za taga aike. Hankalinta ya tashi sai kuma duk ta gigice. Ita ina taga ƙafar tafiya gida tabar wannan daular da kowa ke mata barka da arziƙin shigowa. Sannan ma auren sati uku kawai ai wannan abun kunya ne da ko'a mafarki bata fatansa. Dole fa ta zubar da makaman yaƙi ta shiga neman afuwa da rusar kuka da ban haƙuri tana tabbatar da sharrin shaiɗan ne. Hakan ma bai saurareta ba, yace saifa ta tafi. Haka kuwa dole ta tafi gida batare da kowa ya sani a dangin Aliyu ba. Amma sai dai me, a ranar iyayenta suka maidota, suka kuma duƙufa bama Aliyu haƙuri suma da tabbatar masa ƙuriciyace ke damun Kamilar kawai. Amma yay mata afuwa ko Fateema kada ya bari tasan wannan al'amarin dan ALLAH. Suka kuma masa alƙawarin canjawar Kamilar fiye da yanda yake buƙata. Badan dai Aliyu yaso ba wannan wuta ta mutu a haka. Sai dai kuma ya sharɗanta ma Kamila sharuɗai masu tsauri game da Fateema in har tana son cigaba da rayuwa a cikinsu. dole kuwa ta amsa da hannu bibbiyu tayi biyya. Sai dai kuma acan ƙasa ta ɗauke karatun uwarta da ƴan uwanta tsaf. A haka Fateema ta tare gidan itama. Da gaske Kamila ta kwantar da kai fiye da zaton Aliyu. Tana bin shariɗɗansa sau da ƙafa. Bawai shariɗɗansa kawai ba, da gaske Fateema mugun kwarjini take mata, dan matar nada wata irin baiwa da nagarta mai ban mamaki. Ga ƙyaƙyƙyawar zuciyar zama da kowa da gaskiya. Sai dai bata son raini, bata son munafunci da wulaƙanci. Wannan abinda Kamila ta sani ne tuni, dan haka ta shirya yaƙar Fateema da su har ma da Aliyu. Sannu a hankali kuwa suka fara tasiri, dan duk wata hanya ta gwaji Aliyu yabi akan Kamila game da zamansu bai kamata da kowane laifi ba. Sai ma yanda take bin Fateeman ya fara saka masa jin nutsuwar zama da ita. A gefe kuma ga Fateema kullum damuwarta da fatanta taga Kamila da ciki. To tsakanin mace da namiji kwance a ɗaki ɗaya sai ALLAH, yau da gobe kuma bata bar kowa ba. Dan sannu a hankali dai Kamila taci nasara akan Aliyu cikin dabaru da kissa irin na mata ya maidata cikakkaiyar mace. UBANGIJI kuma mai hikima da yin yanda yaso a lokacin da yaso ba'a rufa wata biyu da Kasancewar tasu a ƙarƙashin inuwa ɗaya ba sai ga Kamila ta fara laulayin ciki. Ya rabba zokuga murna ga Fateema. Sai ma ka ɗauka itace da cikin. Gaba ɗaya ta kwashe kulawarta kacokan ta maida kan Kamila. Hatta shi kansa Aliyun yanzu ba wani yana samun lokacinta bane, har ya fara kishi da hakan sai da ta zauna ta lallashesa. Bawai baya farin ciki da cikin da Kamila ta samu bane, a'a yana dannewa saboda baya son ko yaya zuciyar Fateemansa ta sosu. Dan haka ya barma zuciyarsa nasa farin ciki ita ya bari take nata a bayyane dama zuciya. A haka kwanci tashi ALLAH ya sauko Kamila lafiya, ta haifo ɗanta namiji mai tsananin kamanni da Aliyu da Fateema tamkar sunyi kaki, dan in baka sani ba kazo saika ma ɗauka Fateeman ce ta haifi yaron. Wannan shine ƙalubale na biyu daya sake girgiza Kamila da ahalinta, sai dai sun shanye a cikinsu suma sunata fatan alkairi. Sai ma ɗaukar jinjiri da Kamila tayi domin sake samun fada ga Aliyu tun a randa ta haifesa ta damƙawa Fateema tare da alƙawarin mallaka mata shi na har abada. Ta kuma sake maimaitawa a gaban Baba Sardauna da Umma da dukkan ahalin Aliyu da nata ahalin. Ranar kuka sosai Fateema tayi da sake jin ƙaunar Kamila. Tana ji a ranta lallai batayi zaɓen tumun dare ba. Hakama Aliyu wata sabuwar soyayyar Kamila ce yaji ta soki ƙahon zuciyarsa tayi tasiri a ciki tare da mamaye komai. Duk wanda zai so Fateeman sa to har abada zai dawwama shima kam yana sonshi da ƙaunarsa ne. Haka dangin Aliyu da Fateema ma suka zo aka haɗu akasha shagalin suna yaro yaci suna Fadeel (Babban yaya 😂👍). Bayan shan shagalin suna aka bar masu ɗansu. Gaba ɗaya Fadeel a ƙarƙashin kulawar Fateema yake. In dai ka ganshi a hannun Kamila to lallai za'a bashi abincinsa ne. Sai ko dare yayin yin barci. Amma dukkan wahalhalu na raino da kulawa Fateema ce. Kai hatta daren ma yana fara kai watanni shida ya koma kwana hannun Fateeman. Dan ALLAH yayisa bamai fitina ba. Tama kai ba wani ya damu da shan nn bane ba.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣8️⃣
______________
.........Fadeel da kansa ya yaye kansa. Dan wata irin shaƙuwace a tsakaninsa da Fateema da ita yakema kallon uwa ta haƙiƙa ba mahaifiyarsa ba. Yayinda Fateema ke nuna masa wata irin soyayya mai girma da ko ɗan data haifa a cikinta iyaka kenan. Son Fadeel take da zuciya ɗaya, so irin wanda koda wasa bata taɓa kawoma ranta ba itace mahaifiyarsa ba balle tunanin cuta masa. A haka suka kammala karatunsu. A lokacin Fadeel nada shekara uku, har lokacin kuma Kamila bata sake samun wani cikin ba. Sai kuma ta ɗan shiga damuwa. Idan Aliyu yayi magana saita nuna masa tana son haihuwar domin cikama Fateema burinta. Sotake ta cikama Fateema ɗaki da ƴaƴa ta yanda zata kwaranye mata ƙishirwar su. Idan ta faɗi hakan na saka Aliyu sake jin ƙaunarta mai yawan gaske. Sai dai kuma a zuciyar Kamila sam wannan ba shine gaskiya ba, tana faɗar ne domin sake farautar zuciyar Aliyu kawai, so take ya sota fiye da soyayyar da yake iƙirarin yima Fateema, so kuma take ta haihun ta yanda zata mallake komai daga garesa, dan ta san dai komansa nata ne tunda itace mai haihuwa. To ALLAH bai sake kawo haihuwar nan ba sai da Fadeel ya shiga shekara ta huɗu sai ga wani cikin. Zo kafa murna da farin ciki a wajen Fateema (Oum) kamar yanda Fadeel ke kiranta yanzu. Kamila kuma (Mamy) Aliyu (Abah). Hakama dangi nata mata fatan alheri musamman ta ɓangarenta. Fatansu shine ta sake haihuwar namiji, haka itama kanta wannan shine fatan nata. Ga Oum da Abah kuwa basu da wani zaɓi, duk abinda ALLAH ya bada so suke yi. A haka dai ciki ya shiga watan haihuwa, ranar na zuwa ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ɗanta namiji again. Ya ALLAH burin Mamy da zuri'arta ya cika, dan sun san ta kuma gama kama gida da mai gida. Ga Abah yayi murna ya kumayi kukan tausayin Oum a ɓoye kamar yanda yake yi a ɓoye tun haihuwar Fadeel. Ga Oum kuwa ko'a jikinta, dan ko sau ɗaya bata taɓa jin hassadar Mamy ba akan tazo ta haihu a gidan ita bazata haihu ba. Ita tun bayan kukan samuwar ƙaddararta bata sake zama ta damu kanta da tunanin shike nan bazata haihu ba, balle saka kanta a damuwa. Tuni ta fawwalama UBANGIJI komai, ta kuma amshi jarabawarta da hannu biyu, kullum cikin godema ALLAH take. Tayi imanin maybe haihuwar ba alkairi bace a gareta shiyyasa UBANGIJI ya jarabceta da yankewarta da wuri. Kuma ai ba sai ka haifi ƴaƴa da cikinka bane suke zame maka ƴaƴa, ɗa na kowa ne, maybe ma bazaka amfani wanda ka haifa ba sai na wani, nakan kuma wani ya amfana. Wannan yasa bata taɓa jin wani ƙaiƙayin hassada ga haihuwar Mamy ba. Dan zuciyarta duk ɗaya take ɗauka... Kwana biyu da wannan haihuwa Mamy ta fahimci kamar Abah bai murna da haihuwar ba, sai hankalinta ya fara tashi, da dare ya shigo mata sai da safe ta daure cikin damuwa take masa tambaya. Ya jima shiru kafin ya kai zaune tare da ɗaukar jaririn ya rungume a jikinsa. Cikin kulawa ya ce, “Kamila ba farin cikine bana yi ba. Nama fi kowa farin ciki kuma ina cikin godiyar UBANGIJI daya bani abinda arziƙina ko ilimina baya badawa balle tarin dangi da nasabarsu. Zuciyata ce kawai, zuciyata ce ke tsananin tausayin Fateema. Kamila Fateema MATAR ƘWARAI CE RABIN ADDINI, ke shaida ce akan ta da ƙyawawan halayenta a ɗan rayuwar da kikai da ita ta ƙawance har zuwa ta zaman gidan nan. Munci buruka da yawa tsakanina da Fateema akan ƴaƴanmu, sai dai ashe ba haka UBANGIJI ya ƙaddara mana ba. ALLAH sarki Fateema baiwar ALLAH, koda wasa koda ganganci ban taɓa ganin damuwa ko jin ƙyashin samuwar haihuwa daga wata ba ita ba a gidan nan......” Takaici da zafin da zuciyar Mamy keyi akan kalamansa na yabo ga Oum ya sata saurin katsesa ta hanyar faɗin, “Dan ALLAH ka daina faɗin Fateema bata haihu ba, ka daina raba ɗayan biyu akan yaran nan da Fateema. Tabbas ni ce nai rainon cikinsu da naƙudar su kawai, amma tun kafin suzo duniya mallakin Fateema ne. Ka shaida ni Kamila kamar yanda na mallaka ma Fateema Fadeel da alƙawarin bazan taɓa canja hakan ba koda a kan fuskata shima wannan jinjiri ɗan kwana biyu na mallakashi ga Fateema har abada. Da zarar na yayesa ta ɗauka nata ne, kai in ma zata sha wani abu ne ta shayar da shi da kanta ni tama amshesa yau ikonta ne”. Hawayen ɗaci da tiririn fitar kalamanta da iyakar bakinta suke banda zuciyarta suka shiga silalo mata.... Tabbas kamalanta ratsa ɓargo da zuciyar Abah suka dinga yi, har bai san ya jawota jikinsa ya rungume taba, sai jera mata addu'oi yake hawaye na zuba masa shima. Sosai ƙaunarta mai yawa take sake samun gurbi a dukkanin jinin jikinsa bawai a tsokar zuciyarsa kawai ba. Baiyi ƙwairon baki ba ya shiga jera mata kalamai masu nauyin gaske da ta jima tana ƙishirwar jinsu da buƙatar saurare daga garesa. Shi ɗin dai shi Aliyu da tun a haɗuwar farko ta kamu da soyayyarsa. Duk da so da ƙaunar da takema ƴaƴanta guda biyu masu tsananin kamanni da shi ta gwammace ta sadaukar koda na wuccin gadi ne domin samunsa shi da zuciyarsa gaba ɗaya. Daga baya sai tayi haƙin ƙwatar ƴaƴanta a tsakaninta da Fateema. Dan tabbas wannan ƙyautar duk biyu a iya fatar bakinta take bawai a zuciyarta ba. Amma ta fahimci dolen dole sai ta yita kafin ta samu zuciyar mijinta da dukkan kulawarsa fiye da wadda yakema Fateema. Dan haka zatai dauriya da juriya na wani lokaci... Haka kuwa akayi, shima jinjiri da yaci sunan Fawzan Mamy ta tabbatar a gaban kowa ta mallakawa Oum har abada. A wannan gaɓar kam Oum kukan da tai har sai da ta dinga bama kowa tausayi, dan kuka ne na farin ciki da dukkan jin ƙauna dake fita tun daga zuciya. Ita kanta batama san inda zata ajiye martaba da kimar Mamy ba zuciyarta. Ƴan uwan Mamy kam da mahaifiyarta sun balbaleta da masifa da nuna mata kuskurenta. Amma sai tayi murmushi kawai tana mai kallonsu... “Ku daina min kallon wawuya sarai nasan abinda nake yi. Amma bazaku gane ba sai a nan gaba kaɗan. Domin kuwa fatsa na jefa a kogi tare da ƙananun kifaye a jikin fatsar dan samun damar shaƙo manyan kifaye mamiyo. Har yanzu baku san wanene Aliyu akan Fateema ba....” “Oh ke a naki haukan kina nufin duk kinyi hakan ne dan samunsa da matarsa?”. “Tabbas hakane Mama, dan ta hakan ne kawai zan mallaki Aliyu da komai nasa, ta hakanne Aliyu zai bani dukkan yarda da aminci. Ta hakanne zan saka Fateema a kwalba na rufe rufewa ta har abada. Daga ƙarshe na dawo da ƴaƴana hannuna cikin sauƙi. Shiyyasa ma na sake tabbatar mata a gabanku a gaban Aliyu, a gaban dangisa haihuwata ma ta gaba mallakar Fateema ce. Zan bata ƴaƴa uku kafin wanda zasu biyo bawa su amsa sunan nawa....” “To idan kuma haihuwar ta tsaya miki daga ukun kuma fa Yaya?”. Autar su ce tai tambayar. Kallonta Kamila tayi da murmushi. Sai kuma ta dafata da faɗin, “Humm Gambo kenan, ina ji a jikina sai nayi haihuwa ɗai-ɗai har goma anan gidan, dan na sadaukar da uku kuwa ai ba komai bane, bama sadaukarwa bace ba ajiyar ce. AJIYA A DUHUn da FATEEMA bata sani ba. Dan komai daran daɗewa sai ƴaƴana sun dawo gareni a gabar da Fateema ke murna da jin alfaharin zata amfana. Zan bata fili ne a yanzu ta gama min wahala da su iya iyawarta, ni kuma na mora kayana a lokacin girmansu”. Murmushi kawai Gambo tayi dan ita kam ta gamsu da bayanin Kamila, yayinda yayarta da mahaifiyarsu kawai suka girgiza kawuna, dan suna ji a ransu lallai Kamila ta tafka babban kuskure. Kuskuren da bazata fahimci kuskure tayi ba sai anan gaba.... To koma dai yaya ne Mamy ta cigaba da shayar da Fawzan shima, yayinda komai nashi ke'a hannun Oum, shan nn kawai ke kawosa tamkar yanda akai da Fadeel. Shi Fawzan ba kamar Fadeel ba, ba yaye kansa yay ba, yana da shekara ɗaya Mamy ta sake samun ciki, wannan shine dalilin yayesa gudun samun matsala. Nan ma Abah da Oum suka cigaba da kula da ita da kaffa-kaffa, dan wannan cikin ma sai yafi bata wahala fiye da na Fadeel da Fawzan. Ga cikin da tsirfar tsiya, yana son wancan baya son wannan. Tun yana watanni biyar yay wani irin girma na tsiya kai kace tagwaye ko ƴan uku ta ɗauka, dan Oum da Abah har tsokanarta suke akan wannan karan kodai ƴan uku ne ko twins. Murmushi kawai take yi akan batun, amma a can cikin ranta tana ma kanta fatan hakan itama. A lokacin da cikin ya shiga watanni bakwai sai wahalar ta ninku matuƙa. Har takai bata iyama kanta komai sai da taimakon Oum da Aba. A haka aka shiga watan haihuwa da ƙyar, har ALLAH ya kawo ranar haihuwar. Ansha gumurzu, gumurzu na haƙiƙa dan kwananta biyu akan gwiwa kafin a na uku ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan karan ma dai namiji ne sargaɗeɗe mai kamanni da ƴan uwansa, sai dai shi ya ɗan ɗakko duhun fatar Mamy saɓanin Fadeel da Fawzan dake farare tarr dasu tamkar mahaifinsu da Oum. Jaririn nan ƙato ne na gaske, dan bayan fiddosa hatta ma'aikatan asibitin zuwa kallonsa suke da mamaki. Haka dai aka sallamesu suka koma gida, a wannan karon ma dangi tako ina sun cika gida anata huɗar arziƙi. Ƙalubale na farko akan wannan haihuwar shine tunda Mamy ta ɗaura idonta akan jinjiri wata kalar ƙaunarsa mai zafi data bambanta data ƴan uwansa ta shigeta. Ƙalubale na biyu tun a asibiti yaƙi kama nn. Ƙalubale na uku Abah da kansa suna dawowa gida gaban ƴan uwanta da nasa ya sake tisama kowa alƙawarin Mamy na ranar haihuwar Fawzan akan mallakama Oum wannan ɗan ma a karo na uku, dan haka ya sake tabbatar musu wannan alƙawari na nan daram bai canja ba. Sai dai suyima Mamy addu'a kuma da fatan alkairin ALLAH ya kawo ƴaƴa na gaba da suma zasu kasance matsayin nata mallakin. Ƙalubale na huɗu shawarar da Umma ta bada akan tunda jinjiri yaƙi kama maman Kamila bazai yiwu a barshi a haka ba fa sai a koma asibiti, koda aka koma asibitin sai likitoci suka fahimci fa akwai matsala ne, matsalar canjawar kalar nn Mamy daga fari zuwa yellow, dole suka shiga binciken ainahin matsalar, suka kuma bada shawarar sai dai a shayar da yaron madara gudun kada a shiga hakkinsa, dama gashi yanata kukan yunwa. Ita kuma aka ɗorata akan magani da tabbatar musu in sha ALLAHU komai zai wuce ta samu lafiya kamar ba'ai ba. Jin haka sai Umma tace baza'a bashi wata madara ba Oum ce zata sha magani ta shayar da shi. Baba Sardauna ya yarda da wannan shawara ta matarsa, hakama Abah da sauran dangi. Dan haka mahaifin Oum wato Dr Kasheem Kura da kansa ya aikoma Mamy ingatattun magunguna tun daga Paris da zai bata ruwan nn. Dan su basu zo ba a lokacin babu jimawa da sake haihuwar matarsa (Maryam kenan mahaifiyar Oum ina fatan kuna fahimta). Itama ta samu ɗa namiji cikin na huɗu da yaci sunan Rafeeq. Oum bataje ba saboda yanayin da Mamy ke ciki a lokacin. Cikin amincin UBANGIJI Oum nashan magani kuwa sai ga ruwan nn mai ƙyau. Aiko ta hau shayar da jinjirinta da yaci suna Ajwaad. Yayinda aka bar Mamy da jiyyar zuciya da kukan ɓoye. Gashi kuma babu yanda ta iya, dan ita dai tai alƙawarin nan babu wanda ya tirsasata, a zahiri kuma taƙi nuna ma kowa damuwarta saboda neman soyayyar Abah da take ganin saita wannan hanyar kawai zata iya samunta. Ita dai Oum ranta fes, ƴaƴanta uku cif sun kammala, tsakaninta da UBANGIJI sai godiya. Sai kuma aminiyarta Kamila da har abada take jin a ranta bata da kamarta a wannan duniyar idan ka cire iyayenta da iyayen riƙonta da mijinta. Ƙaunar yaran nan uku take da zuciya ɗaya, da iya gaskiyarta. Bata taɓa jin ƙaiƙayin cewar ba itace ta haifesu ba. Kai ita mantawama take da ba itan ce ta haifesun ba. Dan a zahirance dai Mamy kawaici take yi. Bata taɓa jingina kanta da yaran koda wasa. Sai ta faki ido ta dinga aibanta Oum a zuciya, gefe ga tsananin kishinta da take ji da hassadar finta komai na rayuwa da tayi. Wanda ada can iyakar kishin soyayyar mijinta Aliyu kawai take ji. Amma bayan auren data sake fahimtar wacece Oum a wajen Aliyu da nasarorin rayuwa dana iyayenta ke da shi sai hassadar hakan ta shigeta. (Wannan hassadar al'adace kamar a zukatan matanmu akan kishiya. Ya rabba ALLAH ka yaye mana hassada dan mugun dafi ce mai kassara rayuwa da cigaban cikinta)........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣9️⃣
______________