Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 36

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 36

Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 36: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 36. .........To rayuwa fa ta fara…

4,351 words

.........To rayuwa fa ta fara shuɗawa. Abubuwa da yawa nata faruwa. Ciki harda yaye Ajwaad da Oum tayi bayan cikarsa shekara biyu cif yana sha daga jikinta. Tuni ta sanyama Ajwaad Auta, tunda dai Mamy da kanta ta tabbatar da iya gejin abinda zata bata kenan haihuwa ta gaba tata ce. Autancin ko yabi Ajwaad tun da ƙarancin shekaru. Dan ALLAH yayisa irin yaran nan masu tsananin ƙulafucin iyaye. Sam baya ƙaunar koda wasan wasa Oum tayi nesa da shi. Wani lokacin ko toilet ta shiga yana ƙofar bayi yana jiranta har saita kammala abinda take ta fito. Idan zataje wajen Abah kuwa a ranar girkinta sai fa da wayo da dabara idan ta tabbatar barcinsa yayi zurfi can cikin dare. Wani lokacin kuma dashi dole take tafiya ta kwantar da shi a falo ko in barcin nasa yay nisa ta maidosa cikin ƴan uwansa. Akowane motsinsa shi dai Oum ce. Gashi da shegen ƙiwa tun yana watanni biyar zuwa shida baya yarda da kowa sai Oum sai Fadeel idan yaso. Amma ko Abah da Mamy basu isa taɓashi ba ya hau ihu yana bin Oum da kallo yana kuka. Sanda ya cika shakara ɗaya da wasu watanni kuwa idan ka takura sai ka ɗaukesa cizo zakasha ta yanda dole ka saukesa ya koma wajen uwarsa. In ma anguwa suka fita bai yarda wani yako taɓasa daga jikin Oum. Baba Sardauna ne ma ke ɗan samun wannan alfarmar shima ana ɗan yarda da shi saboda yana bashi irin chocolates ɗin da yake so. A haka ya cika shekara huɗu aka saka shi a makaranta kamar sauran ƴan uwansa. Duk da su an sakasu tun suna da shekara uku-uku, shiko ƙulafucin uwa ya hanashi. A yanzun ma dai badaƙala ake sha dan baya ƙaunar zaman makarantar, yata kuka kenan da kiran Oum! Oum! Shi akaisa wajen Oum ɗin sa. Shi gida zaije wajen Oumyn sa. Karatu yaƙiyi ya hana sauran yara yi. Duk wanda ya nuna kulawarsa da son rarrashinsa ya danƙarama yaro cizo sai an rabasu da ƙyar. Ganin haka yasa makarantar suka bada shawarar a ƙara masa lokaci ya ƙara wayo, dan inma ba hakaba bafa karatun zai yi ba. Dole su Oum suka yarda da hakan, amma tana ƙoƙarin masa a gida ita da Fadeel musamman na ɓangaren addini. Gashi kuma da ƙwaƙwalwa Masha ALLAH. Sai da Ajwaad ya cika shekara bakwai a duniya sannan Mamy ta sake samun ciki, a lokacin yana zaman makaranta da ƙyar dan yana a nursery 2 ma. A islamiyya kuwa Alhamdullah ya tashi da ƙwazon karatu kamar sauran ƴan uwansa biyu. A wannan karon abinda ya fara tadama Mamy hankali kamar Abah bai damu da cikinta ba kamar ukun can na farko, sai Oum ce ma ke dama-dama da ita da bata kulawa. Idan tai magana yace to mikuma ya rage shida keda uku rigis, ai sai fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya sauketa lafiya. Wannan furuci nashi na cimata zuciya, amma haka take dannewa ta maida abin wasa. A haka ta shiga watan haihuwa, a kuma lokacin Abah ya fara musu gini dan yace wannan gidan ya musu kaɗan ga zuri'a suna tarawa. A wata juma'a Mamy ta sauka lafiya ƴan biyu duk maza. Musalta muku irin farin cikin da wannan ahali suka shiga a wannan karon ma ɓata lokaci ne. Anyi shagalin suna kamar yanda akai na baya, duk da Mamy taso ace na wannan karon yafi na bayan armashi kodan biyu data santalo. Haka dai suna ya tashi lafiya yara sukaci sunan Hassan da Hussain. Dan tace bata son a canja mata suna a barsu da nasu. Duk da a wannan karon Mamy batace ta mallakama Oum su ƴan biyu ba bata fasa yin hidima a gareta da jinjirayen ba kamar yanda ta saba. Dan har takai Ajwaad na nuna kishinsa a fili, sai dai suyita masa dariya kawai. Bayan yaye su ƴan biyu da wata uku Hussain ya fara laulayin haƙora, ya dinga gudawa irin na haƙora mai wahalarwa. Abin ALLAH kwana biyu kacal a wannan halin UBANGIJI ya ɗauke abinsa. Duk da rasuwar yaro ce ta girgiza wannan ahali, dan daga Oum har Mamy kuka rurus sai Abah ne ke lallashinsu, da ƙyar suka haƙura suka sabarma kansu da rashinsa. Sai kuma tunda Hussain ya rasu shima Hassan lafiya ta masa ƙaranci. UBANGIJI mai rahama da jin ƙai shima bai cika kwana arba'in ba yabi ɗan uwansa. Ai neman zautuwa Mamy tayi, da ƙyar ake tausarta. Sai dai kuma babu yanda ta iya da hukuncin ALLAH. Tun bayan rasa ƴan biyu ko ɓatan wata Mamy bata sake yi ba. Har suka tare asabon gidansu da a yanzu suke ciki wanda ke maƙwaftaka da nasu Maanal. Zuwa yanzu tsanar Oum Mamy keji mai zafi a ranta, amma a zahiri bazaka taɓa fahimtar hakan ba, gefe ga uwarta da ƴan uwanta dake zugata. Ba Oum kawai ba, hatta duk wanda Oum ke huɗɗa da shi Mamy ta tsanesa. Dan haka bata taɓa son Ammie da su Maanal ba. Amma koda wasan wasa bata taɓa nunawa a koda fuskarta ba. Sai ma nunawa take kamar tanama Oum kawaici musamman akan tarayyar Maanal da Ajwaad dake a bayyane ga kowa. Ita ko Oum soyayya takema Mamy ta gaskiya da kuma zuciya ɗaya, jin girmanta take da kimarta ta yanda zuciyarta koda hasashe bata taɓa kallon munininta ba. Kai a yanzu koda Abah yazo yace da Oum ga munin Mamy to tabbas bazata amince ba. Ta bata matuƙar yarda da gaskiya ta yanda bata ko jin wani ɓurɓushin kishita a ranta. Kai sam bama ta mata kallon kishiya sai ƴar uwa. Hatta da sirrinta bata taɓa canjawa daga yanda take sanar mata ba a sanda suna amintaka da ƙawance. Komai buɗema Mamy take da zuciya ɗaya ta nema shawara. Kuma a cikin ƴan uwanta kaf babu wanda ya taɓa kallon illar hakan dan suma yarda ɗaya suka bama Mamy saboda ɗunbin hallaci da yakana da dattakon data nuna ga Oum ɗin. Lallai Mamy ta samu fada da soyayya tako ina daga zuri'ar Baffa Ishaq Darma. Yarda suke mata ta gaskiya, basa taɓa banbantata a matsayin bare a cikinsu, basa taɓa banbantata tsakaninta da Oum dake matsayin tasu. Kai sai suyi mata abu basu yima Oum ba musamman ma mahaifinta Dr Kasheem Kura. Dan shi yakance Mamy itace ƴarsa. Oum kuwa ta Baba Sardauna ce. Itama a zahiri ta riƙe dukkanin abinda zasu kalleta da wannan mutuncin, duk da zuciyarta cike take da shirin maido da ƴaƴanta gareta komai tsahon lokaci da rayuwa zata bata. Hakama duk damar data samu daga Abah da yarda bata gamsar da ita ba, kullum cikin sake harin ninkin baninkin ɗinta take yi. Duk da kuwa ta wawashi kaso mafi girma daga soyayyar tasa. Dan tun fara girman su Fadeel Oum ta sake sallama mata Abah ɗin kaso saba'in cikin ɗari, ita kuma yake riƙe da talatin cike da kawaici da dattakonta. A yanzu ko tafiya Abah zai yi da ita ne. Idan wani abu ya taso kai tsaye Oum zatace yaje suyi da Mamy ita bazata iya yin nesa da yaranta ba. Tun abin na bama Abah haushi har ya haƙura ya sallama dan ya fahimci mai raba Fateema da ƴaƴan nan nata sai dai ALLAH. Musamman Autan ta uban ƴan ƙalata da ƙulafucin uwa. Duk da Oum bata taɓa fitowa ta sanar ma yaran ainahin mahaifiyarsu ba tana nuna musu girma da darajan Mamy a garesu. Kullum cikin cusa masu soyayyarta take a zukatan yaran cike da hikima. Tana ƙawata musu girma da kimar Mamy a zukatansu. Tun abin baya tasiri a ransu harya fara. A hankali Fadeel da Fawzan suka ɗan fahimci wani abu kaɗan bamai yawa ba. Sai dai hakan bai taɓa canja musu Oum ɗinsu a matsayin da suke kallonta ba. Ita dai suka sani, ita kuma suke kallo da matsayi irin na uwa da mahaifiya. Amma suna girmama Mamy da bata hakkinta da mata soyayya kamar yanda Oum ta koyar da su take ma kan koyar da su ɗin. Shi dai oga Ajwaad Auta Oum ɗinsa kawai ya sani. Shi uban kowama ya mutu har liman in dai za'a bar masa Oum ɗinsa. Farin cikinsa ce ita, sannan duniyarsace. Bai haɗa soyayyarta data kowa ba a duniya... Wannan halin na Ajwaad na cima Mamy rai matuƙa, dan ALLAH ya jarabceta da soyayyar Ajwaad fiye da duk sauran yaranta. Ƙaunar yaron take har ƙarƙashin zuciyarta. Ga shi kuma hankalinsa san baya a kanta yana akan maƙiyarta ne. Shiyyasa take sake jin ninkuwar zafin Oum ɗin matuƙa. Gashi ta fahimci itama Oum ɗin tanama Ajwaad wata irin soyayya mai girman gaske. Hakan na nufin bayan Aliyu sun sake yin tarayya akan abu guda kenan. Wato soyayyar AJWAAD ALIYU ABUBAKAR DARMA...

_MUN SAKE DAWOWA DAI CIKIN LABARIN RAYUWAR AJWAAD DA MAANAL DATA GABATA🙏😀_

*GIRO:-* A Giro dai an ɗaura auren Babu da amaryarsa Safarah. Safarah yarinya ƙyaƙyƙyawa mai busashen ido. Dan cikakkiyar ƴar tallace a tashoshin motoci na yankin ƙauyen Giro da cikin Suru. Musamman a ranakun kasuwanni. Kai har cikin Kebbi idan ta kama suna zuwa kawo kayan sayarwa ita da ƙawayenta. Gwaggo ta zaɓama Babu ita ne dan a cewarta itace dai-dai da Asiya. Anko sha biki, dan su Ammie sun sha kallo. Bajinta sosai Gwaggo tayi a bikin dan dabbobinta har goma ta saka a kasuwa. Bayan tarewar amarya a nan dai gidan ɗakin dake a tsakanin Gwaggo da Ammie ango yasha bidiri. Dan Babu dai kura ne ba'a bashi ajiyar nama. Duk da ma dai abin bai masa armashi ba saboda samun Safarah ba'a cikakkiyar budurwa ba ita dai. Amma tsabar iya bariki na yarinyar nan da dudu shekarunta goma sha tara ne a duniya sai ta dinga zumbuɗa masa ihu da kururuwa ita a dole tana shan wahala. Wannan ihu ya tadama Ammie hankali, bawai akan kishi ba, duk da bazatace bata kishin mijin nata ba. A'a saboda su Shahidah ne. Dan takai yaran nan sai da suka farka a barci suma. Yayinda itama kanta Gwaggo data fito tsakar gida a wannan tsohon dare take faman kiran sunan Babu da gargaɗinsa akan wai yabi Safarah a hankali, ya dai san yarinyar ƙarama ga mutuncinta ta kawo. Wannan abu shine ya taru ya saka Ammie kuka dan su Amaal nata jera mata tambaya akan ko mi ya samu amaryar haka. Sai dai bata kula yaran ba, daga ƙarshe ma ta musu tsawa suka kwanta. A ranta dai tana sake godema ALLAH da su Abah suka wuce da Maanal. Dan tabbas kaɗan daga aikinta tama fita itama koda safe ta tsare Babu ɗin da tambayoyi. Wannan kuka da amarya tasha da ihun iskanci yasa kowa ya yarda ta kawo mutuncinta. Shi ko Babu tai masa ɗaurin goro dan bashi da damar musawa. Ga wata irin kunya da nauyin Ammie da ALLAH ya jarabceshi da ita. Dan ƙiri-ƙiri ya kasa yarda ya haɗa ido da ita a wannan yinin baki ɗaya. Ko hanya suka haɗa duk sai ya daburce. Itako Ammie ta dake abunta ko'a fuska bata nuna masa ba. Amma a dare na biyu saita tura Amaal da Shahidah kwana ɗakin Zainabu ɗaya daga cikin matan gidan, kasancewar tasan mijinta baya gari. Dan gara ta nesanta yaranta da shiyyar gaba ɗaya kafin su fahimci abinda ke faruwa. Aiko Ammie tayi dabara, dan daren yau ɗin ma bata canja zani ba. Sai da Safara tayi duk iya yinta ta hillaci Babu ya kasance da ita. Gashi dama ta ɗirki magunguna shima an ɗirka masa ta hanyar abinci. Ai sai ihun ya zama nasu su biyu yau ita da shi. Kai jama'a wannan iskanci dami yay kama haka. Cewar Gwaggo cikin mitar son yin barcin da suka hanata. Amma da safe ko'a fuska bata nuna ba saima kulawa take bama amarya ta musamman dan Ammie taji haushi. Sai kuma Ammien ta tabbatar mata ita ɗin ƴar halak ce dan bata nuna damuwarta ba koda a fuska. Kasancewar daren jiya ta kwana salla da karatun Alqur'ani sai ta tashi sakayau zuciyarta cike mamaye da farin ciki. Musamman daya kasance da safe ta kira Oum a waya sun sha hirarsu harda Maanal dake ta faman bata labaran daɗin da Oum da Bestyn ke ciyar da ita. Shi kansa Babu ɗin sai yanayin na Ammie ya sake jefa shi a ƙaulani da ɗunbin kunyarta da shakkarta ma..........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖7️⃣0️⃣

______________

..........“Ni bazan je ba barci nake ji”. Maanal ta faɗa tana ture hannun Ajwaad dake ƙoƙarin sauketa a saman gadonsa. Dan ɗakin ta shiga ta masa uwar ɓarna a wadrobe ɗinsa da duk abubuwansa. Ɗakin nasu ne su uku amma a tsare yake, kowa da sashen kayansa da abubuwansa da kuma ɗan gadonsa. Maanal kan shiga ɗakin amma bata taɓa komai na Fawzan da Babban Yaya sai na Ajwaad. Yau kamar abin arziƙi suna tare a ɗakin suna duk wani assignment ɗin da aka basu na islamiyya kasancewar zuwa gobe zasu koma. Sai Mamy tai kiran Ajwaad ta aikesa kai mata markaɗen alale da zatayi a gidan yau matsayin abincin rana. Wannan dama Maanal ta samu ta canja akalar assignment ɗin nasu ta koma zane-zanenta na fama. Dan tana son zane-zane sosai tun bata kai haka ba. Kai a makaranta makinta dabanne akan subject ɗin ma saboda yanda tai matuƙar ƙwarewa. Ko aiki aka basu awannan fanin hatta Ajwaad itace ke masa kai har su Fawzan bata suke da su Shahidah. Tana cikin zane-zanen ta ajiye ta sauka a gadon inda take ta koma masa bincike a kaya wai tana neman colours wanda take amfani da su sun fara bushewa basa mata da ƙyau. Daga haka ta ɓige da ɓarnarta tai kaca-kaca da komai. Tana jin zai shigo ta haye gadonsa da sauri tai likimo ita adole barci ma take yi. Shi ko tsaye yay kawai yana kallon fallasar datai masa da kayayyaki. Amma sai baice komai ba ya ƙarasa saman gadon ya ɗagota yana faɗin, “Tashi kije ɗakin Oum tana kiranki.” Shine ta ƙwaɓe fuska da faɗin itafa bazataje ba barci ma take ji. Shiru yay yana kallonta, sai kuma ya saki hannun nata ya koma kan kayansa ya fara tattarewa yana maida komai inda yake. Dan shifa duk da ƙarancin shekarunsa komai nasa akan tsari yake da tsafta. Dan Ajwaad sam baya ƙaunar ƙazanta. Shiyyasa komai nashi a tsaftace a killace yake. Yana tsaka da maida kayan kuma sai ta sakko ta dawo wajensa tana masa surutu da nuna masa zanen agogon da tayi. Harara ya zuba mata ya ɗauke kansa. Ita kuma ta tsaya tana kallonsa kawai. Sai kuma ta kumbura baki da jefa masa book ɗin ta fice tana kuka wai ita babu ruwanta da shi kada ya sake mata magana kuma. Baiko kulata ba sai da ya kammala maida komai har books ɗin nasu dake baje a gadonsa ya gyara gadon sannan ya ɗauka book ɗin data jefa masan. Shiru yay yana kallon zanen agogon da tayi, yayi matuƙar ƙyau tamkar ka saka hannu ka cirosa. Sai yaga ya banbanta masa da duk abinda ta taɓa zanawa kodan bata taɓa zana agogon bane sai yau oho. Samun kansa yay da buɗe box ɗin da yake adana muhimman abubuwansa ya saka shi ciki ya maida ya rufe. Daga haka ya shiga bayinsu dake a ɗakin yay wanka ya canja kayansa sannan ya fito..

Wannan zanen agogon shine tushe kuma sila na ginuwar buri mai girma a zuciyar Ajwaad game da Maanal akan harkar zane-zane musamman agogo....

____________★

Sosai Giro tama Ammie zafi, zafi mai tsanani ita da yaranta. Dan haka ta roƙi Baabu komawa Kano. Da farko ya turza, saboda gwaggo ta sakashi a ɗaki ta kitsa masa cewar yabar Ammie ta cigaba da zama anan Giro. Itako a karo na farko tattara kayanta tsaf dana yaranta washe gari ya fita shi da amaryar tasa da Gwaggo zuwa can gidansu wai babanta babu lafiya ta baro Giro bisa taimakon Baba Haruna. Taso ta kwana a kabbi. Sai dai rashin mukulli dan yana a hannunsa yasa haka suka fallo hanya. Cikin amincin UBANGIJI suka iso cikin Kano kusan tara na dare. Sai da suka shiga gida ta kira Oum ta sanar mata. Sosai Oum tayi mamaki, amma sai ta ture mamakin ta kwantar da Maanal datai barci a jikinta ta fita. Kitchen ta shiga ta haɗa musu abinci sannan ta kira Abah a waya Fawzan ya mata rakiya. Sosai hankalin Oum ya tashi da ganin yanda duk Ammie ta rame ta lalace. Gashi suna haɗa ido kawai Ammie ta sakar mata kuka. Jiki na rawa ta ajiye abincin ta rungumeta tana lallashi. Sai da tayi kukan sosai sannan Oum tace ta tashi tai wanka. Wankan duk sukayi sukaci abinci, sannan Oum da Fawzan suka koma gida. Damuwa fal kan Oum. Washe gari rijib Ammie ta tashi da ciwo, dole suka wuce asibiti. Aiko aka basu gado dan likitocin sun tabbatar da jininta ya hau sama matuƙa. Sai da Ammie tayi kwanaki huɗu sannan aka sallemta suka dawo gida. Washe gari cikon na huɗu sai ga Baabu da amarya sun iso. Ammie batayi mamaki ba, kuma batace komai ba, duk da taga da wani wutar bala'i da rashin mutunci yazo garin. Dan babu kunya ya rufeta da zagi harda mari wai ta taho bada izninsa ba, ta raina masa mahaifiya miye-miye. Ko ci kanka batace da shi ba, hakan sai ya dake hasalashi ya fara nemo hanyar da zai musguna mata ta mangantu ya juye mata abinda ke a ransa. Ɗaki uku ne kacal a gidan, nata, nashi, sai na yara. Haka ya murje ido yace ta koma na yaran ita amarya ta zauna a nata. Ammie ta ce wannan ne kuma bai isa ba. Dan ita ba wulaƙantacciya bace, ba gori ba gidan nan mallakinta ne idan ya manta tunda da kuɗinta aka sayeshi. To dama fa ta samu, haka Baabu ya dinga zuba tijara har sai da Abah yazo ya fiddashi a gidan aka samu masalaha. Daga ƙarshe dai dole amarya ta zauna a ɗakin shi. Tun wannan dawowa komai ya canja, canji mai ban mamaki daga ma'auratan dama gidan kansa. Musamman daga Baabu. Hatta ƴaƴansa yanzu ja baya suke da shi, dan abu kaɗan zakayi ya hauka da zagi. Ranar ma ƴar lelen tashi Maanal har duka taci, aiko ta haɗa inata-inata ta koma gidan Abah. Tafi sati bata shigowa gidan nasu kafin ta saki jiki kuma ta manta bisa tirsasawar Ajwaad ta koma shigowa. Ga amarya dai babu wata matsala. Ta kwantar da kanta yana fahimtar komai daki-daki kamar babu komai. Sai dare ta ishesu da ihu ita da miji. Wannan abu shine mafi girma tadama Ammie hankali, dole ta maida kwanan su Shahidah gidansu su Oum gaba ɗaya. Dama yanzu batun miji Ammie bata da shi a gidan, Baabu yana tare da amaryarsa tunda suka dawo. Sai da suka cika wata ɗaya cif sai gashi da takarda wai ya saki Ammie saki ɗaya. Murmushi kawai Ammie tayi da faɗin, “ALLAH yasa haka shi yafi alkairi, amma kuma babu inda zanje. Zan zauna na cigaba da rainon ƴaƴana har lokacin aurensu sai dai kai ka bar min gidan tunda dama nawa ne”. Wannan furuci nata shine ya kawo tashin hankali, tashin hankalin da dole sai da Abah da Oum suka shiga yanzu ma. Da ƙyar dai aka sasanta bayan Abah ya nusar dashi illar abinda yake shirin aikatawa. Shine fa ya maida Ammie. Haka aka cigaba da haƙuri Ammie bata da miji, bata taɓa tada kai ta kallesa ba har tsawon shekara biyu. (Kenan dai tun da amarya ta tare😭) Ko'a fuska Ammie bata nuna masa damuwarta, karatunta kawai take na Islamiyya da take zuwa da kula da tarbiyyar yaranta da sana'arta. Dan takai yanzu ma itace ke ciyar da kanta. Zuwa yanzu su Maanal fa an shiga secondary, Dan suna aji biyu ma duk da da ƙyar suka amsheta saboda sunce tayi ƙarama da yawa, yayinda Shahidah ke shirin kammalawa ita da Fawzan, babban yaya kuwa ya wuce ƙasar Saudiya karatu. Amarya bata shiga sabgar Ammie, itama bata shiga tata, dan a zahiri bata da matsala da ita sai da Babu, sai dai tushen matsalar daga gare ta ne tazama macijin sari ka noƙe ne kawai. Har lokacin kuma dai babu ciki, sai da ta shiga shekara ta uku sai ga ciki, nan fa su Babu aka shiga murna da addu'ar haihuwar ɗa namiji. Ita dai Ammie ko tari bata musu ba, duk taɓarar iskancin da amarya keyi bata nuna tasan suna numfashi a gidan ba ma. Sai da ciki ya shiga wata biyar sannan ya ɗauketa suka wuce Giro, dawowar da basu sake yi ba sai da ta haihu akasha shagalin suna a Giro dan buri ya cika an haifi Namiji. Ashe duk wannan abun da ake Baabu na cikin Kano, tunda ya kai amarya gida Gwaggo ta sharɗanta masa hanashi komawa wajen Ammie wai har sai in matarsa ta haihu. Ammie bata taɓa sanin haka ba sai bayan dawowarsu da jinjiri da Gwaggo, wai itama ta dawo nan Kano da zama, ashe aure dai ya ƙare tsakaninta da Baba Haruna duk kuma akan Ammie ne, dan bayan tahowar su Ammie a wancan karon ansha fitina Baba Haruna ya saki Gwaggo shine fa ta ɗau alwashin yanda ya saketa itama sai an saki Ammie, idan kuwa ma ba'a saketan ba sai ta ɗanɗana fiye da abinda itama ta ɗanɗana. Wannan duk shine tushen matsalar da suke ciki a yanzu shiyyasa Amarya data san komai ta koma gefe ta nutsu tana shan kallo dan tace faɗan na manya ne ba nata bane. Dawowar Gwaggo Kano ba ƙaramin tashin hankali su Ammie suka shiga ba ita da yaranta. Musamman Maanal mai bakin tsiwa datai matuƙar tsanar Gwaggo, kuma a zahiri take nunawa bata ɓoyewa. Yayinda Gwaggo itama ta tsani Maanal fiye da su Shahidah, ta kuma tsani Ajwaad, dan shima a dalilin ƙin Maanal da su Ammie daya ga Gwaggo nayi ƙuru-ƙuru ya sashi tsanar matar, dan sam Ajwaad baya son mugu da mugunta. Rayuwa tayi tsanani wa Ammie, uwar miji, da miji da kishiya sun saka rayuwarta gaba data ƴaƴanta. Shekaru kusan huɗu bata kwanciya da miji, baya shiga ɗakinta. Yanzu kuma haihuwar namiji tasa kullum cikin aibanta mata yara suke da shegantasu, dan akwai randa Baabu da bakinsa yace yana tantanamar ma su Shahidah ƴaƴansa ne. Wannan abu ya girgiza Ammie, ya sakata kuka mai tsanani da sake jin sabuwar kewar iyayenta data rasa. Amma ya zatai, haka ta haƙura ta share hawayenta ta barma ALLAH komai. A wajen Oum da Abah kawai take samun sauƙi da soyayya da ƙauna ita da yaranta. Kammala secondary ɗin Shahidah yasa Abah tada zancen aurenta da Fadeel. Dan yace za'a fara nasu, ita kuma Amaal sai Fwazan ya kammala. A ɗan tsukun Fadeel yazo gida hutu, dama can shi da Shahidah tuni sun ƙulle, dan haka aka saka ranar aurensu ya koma saudia. Bayan komawar tasa Shima Fwazan ya shiga lallaɓa Oum akan kawai a haɗe nasa dana Amaal lokaci ɗaya dana Babban Yaya, sai su tafi jami'ar tare. Dan shi rashin ƙyawun result daya samu yasa dole ya ƙara shekara ɗaya a ƙasa sai da ya canja ssce ɗinsa duka. Duk da a lokacin ita Amaal na ss2 sai yace kawai tayi exam ɗin itama su wuce tare. Oum ta tunkari Abah da zancen, yay shiru yana nazari, sai zuwa can yace ta bashi lokaci zai yi magana da Baabu, kuma zai kira Baba Haruna a waya....

____________★

Kamar yanda suka saba tashi sallar asubahi kullum yauma hakanne. Saida Fwazan ya fara yo alwala sannan babban yaya ya shiga. Ajwaad shine ƙarshe, sai wani ciccin magani yake. Ya girma sosai a tsaye, dan a yanzu shi da mutuniyar tasa suna js3 ne. Suna shirin tafiya ss. Shekarun girma sun gama bayyana mai, dan har wani ɗan tsigin gemu ya ajiye (kamar jelar tsatso inji Ibro.😂 ALLAH ya gafarta masa da iyayenmu baki ɗaya 🙏). Yanda yake tafiya kamar mara laka a jiki ya saka Fawzan sarkin tsokana faɗin, “Wai na Lilly kodai barcin nan bai isheka bane ba?”. Harrarsa kawai ya ɗanyi ya wuce abinsa, dama Fawzan tsokana, Ajwaad miskilanci. Haka suke kullum, sai ya ƙuresa ne yake tanka masa. Juyawa Fawzan yay ga babban yaya dake canja kayansa zuwa jallabiya, shi kam tako ina ya zama cikakken saurayi, ga cikar kamala da nutsuwa ta sake baibayesa, duk da shima Fawzan ɗin tsokanar ce kawai, amma a nutsensa yake. Har sun kammala shiryawa yau ma Ajwaad na cikin bayi, babban yaya ya dubi fawzan da faɗin, “Wai mike damun auta ne yanzu?. Da babu wanda ya kaishi himma shirin fita sallar asuba, amma tunda nazo garin nan naga sai mun fita yake fitowa”. Murmushi Fawzan yayi da ɗan sosa kai, sai kuma ya ɗage kafaɗa da faɗin, “Maybe yana wani uzirin ne”. “Kamar ya?”. Shiru Fawzan yayi saboda fitowar Ajwaad daga bayin a tunaninsa sun fita ɗin. Turus ya tsaya yana kallonsu, suma duk sai suka zuba masa ido........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖7️⃣1️⃣

______________

Readers Also Read