Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 47
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 47: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 47. Salla suka fara gabatarwa saboda…
4,341 words
Salla suka fara gabatarwa saboda gudun fitar lokacinta. Kafin a cika musu gaba da abinci kala-kala. Kan Ammie dai a matuƙar ɗaure yake da ganin sanayya tsakanin Hajiya Majdiya da su Oum. Daga ƙarshe dai ta kasa haƙuri ta magantu. Dariya Hajiya Majdiya tayi, kafin ta warwarema Ammie komai. Matuƙar mamaki da al'ajab ne ya nema kashe Ammie, ta dinga raba ido tsakanin Hajiya Majdiya da Oum. A lallai tabbas bata san ƙannen Oum ba a fuska a tarayyarsu har suka rabu, saboda lokacin su suna ƙasar waje, amma tasan labarinsu, tana jin kuma tana ambatar ƙanwarta datai aure amma tana acan kasar wajen mijin kuma na nan Nigeria saboda yanada mata biyu a Zaria amma yana zuwa can wajenta dan yana kasuwanci a ƙasashen ƙetare. Cikin kasa daurewa Ammie ta ce, “Aunty! Dama Maman Najma ce kike yawan bani labari da mijinta ke Zaria amma ita tana can Paris”. “Tabbas itace Asiya. Shekara shida kenan da dawowarta Nigeria har ma da su Abbu. Dan yanzu haka su suna Kano ne”. “Ikon ALLAH kenan, shekaru biyar kenan muna tare amma bamu san akwai muhimmiyar alaƙar data taɓa haɗa ƙaddararmu ba. A lokuta da dama wasu al'amura na Maman Najma kan so sakani a ruɗani wlhy. Dan sai kita dawo min cikin idanu duk da bakwa kama ko kaɗan a fuska.” “Gaskiya ne bama kama da Majdiya da Rafeeq sam. Garama Sulaiman shi kam da kin gansa zaki san akwai alaƙa. Mu kamar mun kwaso Mah-mah ne. Itako Majdiya da Rafeeq Abbu. Wai ni naga kowa banda Baby na fa, ko bata zo bikin bane?”. Murmushi Ammie tayi. “Tazo, suna tare da su Najma Nene ta aikesu.....” Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammie. Ganin Daddy ya sata ɗauka batare data ƙarasa maganar ba. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar tana kallon Oum. “Aunty dama harda su Yaya kuke tare?”. “Ai mu duka gidan ne ba'a bar kowa ba. Halan har an ɗaura auren?”. “Eh an ɗaura harma sun shigo. Amma inaga su basu ƙarasa wajen walima bane ba. Dan yace gasu nan a hanya a shirya musu abinci a sashensa.” “Oh oh ji son bama mutane wahala. Maimakon su ci acan kamar kowa”. Mamy ce mai maganar. Dariya Ammie tayi, da faɗin, “Babu wata wahala Mamy, hakan ai shine dai-dai suzo na gansu shekara nawa”. Daga haka Ammie ta fice. Da wani shegen hararar ƙasan ido Mamy ta bita, sai ko karaf a idon Hajiya Majdiya. Mamaki sosai ya kama Hajiya Majdiya dan abu ne da basu taɓa gani ga Mamy ba. To kodai sunada matsala ne da Hajiya Asiyan? Kai to amma a dukkan labarin da Oum ta bata na alaƙa da tarayyarsu babu wani saɓani ai, hasalima Mamy bata da yawan shiga sabgar mutane. To kodai idonta ne ya gane mata ba daidai ba? Kai to gaskiya hakanne. Da wannan tunanin ta saki zancen a ranta suka cigaba da hirarsu.....
★ Har cikin gida motar su AA ta shigo dan suna biye da Daddy ne. Yanzu kam Fawzan ne ke driving ɗin. AA na gefensa Abah da Babban yaya na baya. A kusan tare duk sukai ƙoƙarin fitowa. Hakan yayi daidai da fitowar su Huznah daga sashensu. Cak taja wani kalar wawan birki. Itama dai cikin kwalliya take, sai dai ɗan kwalinta a hannu ta yana siririn veil a kanta. Tare take da wasu ƴammata guda biyu. Sai wata dake biye da su da makeup box a hannunta, da alama dai kwalliya zatayima Huznah ɗin. Dan su sauran biyun da kwaliyarsu raɗam a fuska. Bakinta har harɗewa yake wajen ambaton “AA Darma! A gidanmu?”. Duk kallonta ƙawayen nata sukai, wadda ke'a gefen haggunta ta ce, “AA Darma naki da kuka haɗu a Abuja lokacin bikin Yaseerah?”. Bata iya ta bama ƙawar tata amsa ba. Jiki na rawa ta juya sashensu da sassarfa. Wani iri zallo zuciyarta keyi kamar zata fasa mata ƙirji ta fito. Hajiya Basariyya na falo tsakkiyar ƙawayenta su Maman Yaseerah Huznah ta faɗo musu. Tama manta a cikin taron mutane suke. Yanda take ƙwala kiran “Ummy! Ummy!” yasa Hajiya Basariyya miƙewa zaram. Tareta tayi tare da girgizata tana faɗin, “K Huznah lafiyarki kuwa? Wane irin kirane wannan? Jibafa yanda kike shigowa kamar wadda aka biyo.” “Ummy AA Darma fa na gani a gidan nan”. Rasama inda Hajiya Basariyya zata kamo AA Darma tayi. Ta ce, “Waye kuma AA Darma?.” “Ummy AA Darma ɗin ne baki sani ba? Mijin da zan aura na Abuja”. Ai sosai Hajiya Basariyya ta waro idanu waje, hakama Maman Yaseerah zaram ta taso inda suke. Hannun Huznah ɗin ta kama sukai cikin bedroom, Hajiya Basariyya ta take musu baya. “K Huznah nutsu, da gaske kike kuwa”. “Wlhy da gaske nake Mamah.” “Tab ɗin jan, eh lallai malam yayi gaskiya. Hakan na nufin aiki yayi kenan”. Maman Yaseerah ta faɗa tana kallon Hajiya Basariyya.......
_In dai da gaske aikin nan yaci nima ai arakani wajen malamin nan zai min aiki akan makaranta AJIYA A DUHU musamman ƴan Discussion House da ƴan AREWABOOKS ina son a musu ASIRI su fara son Uncle RK🥱🥱🥱🤪🏃🏃🤣👍_
__________★
A yayinda haɗuwa ta kasance tsakanin AA Darma da Huznah, Ammie da Oum acan Kaduna. Anan Kano RK ne tare da Alhaji ƙarami yayansa da Abbu mahaifinsu suka kai ziyara gidan Baba Sardauna. Ƙyaƙyƙyawan bafilatanin dattijo mai tarin cikar kamala data addini. Anga jiya anga yau ana fatan ganin gobe. A yanzu shine uba kuma jigo da gaba ɗaya ahalin Baffa Ishaq Darma ke kallo a matsayi na kamar mahaifi. Shine garkuwa kuma shine alƙali mai tsawatarwa da zartarwa akan a tsakanin wannan zuri'a. Hakama matarsa ta karɓi wannan girma bisa ga bashi dukkan goyan baya ta hanyar amincewa ita ɗaya daga cikin wannan zuri'ar ce ba matar ɗa dake kallonsu a matsayin dangin miji ba. Dan bata da abin cewa ga wannan zuri'a sai godiya da fatan alkairi. Ita kanta mantawama take ba daga tsatsonsu ta fito ba. Baba Sardauna ya girmi Abbu sosai, dan sai dai suyi sa'anni da Baba Umar mahaifin Abah kenan. Ga kuma girma irin na matsayin yayan mata a tsakaninsu. Harara Baba Sardauna ya makama RK bayan ya gama amsa gaisuwar Alhaji Ƙarami. “Ni bazan amsa gaisuwarka ba ai Rafeeq. Dan lokaci kaɗan ma ya rage kai da wannan ɗan naka Ajwaad da Najeeb na sakaku a ɗaki na zane ciki da bai sannan nakai hotunanku massallaci ko za'a samu mai taimakonmu ya baku matan aure koda guragu ne. Kun wani ajiye gemunan ƙarya kamar na ALLAH. Ku yanzu dan ALLAH Moddibo da Saleem basa birgeku, da ƙananun shekarunsu amma yaran bibbiyu....” “Ayi haƙuri Baba a mana afuwa. In sha ALLAHU zamuyi”. “Haka kullum kuke faɗa. Har gara kai ma kana bada haƙuri da nuna zakayi, amma waɗan can biyun inaga sai mun haɗa da roƙon ALLAH dan da alama akwai iska marasa san aure a tare da su”. Abbu dake murmushi ya ce, “Ai kaima dai ka faɗa Yaya. Ni wlhy canai idan suka wuce wannan shekarar kawai a samu wanda suka dace a aura musu sai dai akai musu ɗakunansu, ba sai suyi yacce zasuyi da su ba”. “Shawara mai ƙyau wlhy Kasheem. Dama jiya-jiyan nan muke maganar nan da Kamila da tazo. Sai kuma ga Khadijah ta kira waya Itama tana mun complaine akan Raihana da Nuwaira.” “To ai sai asan mafita kawai Yaya, duk da shi yazo da nasa batun ne yanzu haka wai acewarsa. Ni kasan ba kama zancensu nake ba su ukun nan dan munafukan bakinsu ɗaya da kake gani. Najeeb da Ajwaad da Rafeeq ba, ALLAH kaɗai zasu gaya min akan aure na yarda dasu”. Dariya Alhaji Ƙarami yay da faɗin, “Kai Abbu, ALLAH kun kasa fahimtarsu ne kawai.....” “Ohhh yanzu na gane, Sulaiman kuke ɗaure musu ƙugu kenan ku yayun nasu”. “A'a wlhy Baba. A dai yi haƙuri, in sha ALLAHU wannan karon komai ma yazo ƙarshe. Ina kuma goyon bayanku dan muma ba son zaman nasu muke haka ba”. “To Alhamdullah ai haka muke son ji”. Cewar Baba Sardauna yana gyara zama. Sai kuma ya kafe RK da tunda ya duƙar da kai bai ɗago ba. Cike da kulawa ya ce, “Ɗan nema, zonan naji ɗuminka, dama kwana biyu nayi kewarka kaje ka maƙale a Abuja wajen ɗan uwanka”. Murmushi RK yayi, tare da miƙewa ya isa gaban Baba Sardauna, zai zauna ƙasa ya kamashi ya zaunar a kusa da shi, tare da ɗan rungumesa. “Fitinanne wai ni kake jin kunya kuma?”. Dariya RK ya fashe da ita, hakama Alhaji ƙarami da Abbu. Aifa nan baki ya buɗe aka shiga gaisuwa. Sai kuma hira ta ɓalle. Suna cikin hirar sai ga Baba Umar. Shima dai nutsatstsen mutum mai cike da kamala. Dan zasuyi shekaru ɗaya da Abbu. Shi mutum ne da baida yawan magana. Dan duk cikinsu ya fisu haƙuri. Bazaka taɓa cewa ya haifi kamar Abah ba, abinka da ana jin daɗi. Sosai suka tattauna akan al'amarin dake damunsu na rashin auren RK, AA, da Najeeb daya kasance ƙani ga Abah. Shima dai yaƙi auren, har ga ƙannensa biyu sunyi har da yara. Shine ƙani na uku a wajen Abah, sai Saleem da Moddibo sannan matar Alhaji ƙarami data kasance Auta. Shi yama girmi su AA ɗin. Sosai Baba Sardauna da Baba Umar suka ji daɗin kawo matar aure da RK yayi. Sun kuma tabbatar da babu wasa a satin nan zasuje Kaduna nema masa aurenta. AA da Najeeb kuwa su zasu zaɓa musu matan aure dan ayi bikin rana ɗaya dana RK ɗin. A wani irin farin ciki mara misali RK ya tsinta kansa. Har ji yay ya ƙagara su baro gidan Baba Sardauna dan ya samu ya kira Maanal ya sanar mata wannan albishir, duk da yasan suna a cikin biki yau. Kasa haƙuri yayi tun suna a gidan ya tura mata daddaɗan text massage, Dan basu baro gidan Baba Sardauna ɗin ba sai da sukai sallar isha'i a massallacin ƙofar gidansa. Suna ƙoƙarin fitowa kuma sai ga Hussain yazo gidan tare da matarsa da yaransa biyu shima. Nanfa kuma aka sake zaman sabuwar gaisuwa, dan RK da Hussain ɗin sun jima ba'a haɗu ba. Ƙarshe dai sai goma suka baro gidan. Sanda suka iso har Mah-mah da Rufaidah da yara sun gaji da jiransu sunci abincinsu. Suna a falo suna hira, yara kuwa sun tafi sun kwanta. A rayuwar Mah-mah da Rufaidah sam babu surukuta, zama ake irin na uwa da ƴa. Dole rayuwar gidan su Rafeeq tai matuƙar birgeka, dan rayuwace mai cike da so da ƙaunar juna. Babu munafunci, babu makirci. Kowa na ƙoƙarin bama ɗan uwansa hakkinsa dai-dai gwargwado. Zama Abbu da Alhaji ƙarami sukai anan falo wajen Mah-mah, yayinda RK yay sashensa dan burinsa kawai yay kiran Maanal ya mata albishir........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣1️⃣
______________
........A falon Daddy akama su AA masauki, kafin Daddyn ya ɗaga waya yay kiran Ammie akan a kawo musu abinci. Da to Ammie ta amsa masa, tare da ajiye wayar suka cigaba da haɗa abincin ita da su Shahidah da Hajiya Majdiya. Hakan kuma yayi dai-dai da shigowar su Maanal, Amrah, Najma, Aneesah, Zezaah (ƙawayen Maanal kenan na sarvese). Dole ne matasan ƴammatan kai musu kallo ɗaya ka ƙara. Dan babu wacce batai ƙyau cikin tata shigar ba. Taku suke cike da nutsuwa sun kamo kuloli na waina masa da Ammie tasa akayi a gidan Nene, yayinda Almajirai uku ke biye da su da wasu kulolin manya da sukafi biyun da suka kamo. Gaishe da mutanen dake a falon sukayi sannan suka ƙarasa kitchen inda akace musu su Ammie na nan. “Kai yaran nan ALLAH yay muku albarka, kamar kun san yanzu nake tunanin kiranku”. Ammie ta faɗa tana kallonsu. Amsa mata duk sukayi da Amin. Maanal ta matsa jikinta ta rungumeta. Kallonta tai da mamaki. “Lafiyarki kuwa Maanal?”. Fuska ta ɗan ɓata, sai kuma ta kamo hannun Ammie ta ɗora a saman ƙirjinta dai-dai saitin zuciyarta. Kamar zatai kuka ta ce, “Ammie zuciyata ce ke bugawa da sauri, gabana kuma nata faɗuwa. Sai nake jin kamar wani abu babba na kusanto ni”. Shiru Ammie kawai tai tana kallonta. Itama zuciyar tata na raunana. Dan bata raba ɗayan biyu kasancewar Ajwaad a gidan nan ya sakata jin hakan. Ya rabba wannan wace irin tarayya ce haka?. Amma dai bari tai mata tambaya. Fuskar Maanal ɗin ta shafa, cike da kulawa ta ce, “Dama yana miki haka?”. Kai ta girgiza ma Ammien tana sake narke mata a jiki. Ammie ta sauke ajiyar zuciya, tare da shafa mata kai ta ce, “Kairan in sha ALLAH kinji my babie”. Kai ta ɗagama Ammien sannan ta saketa saboda umarnin da Hajiya Majdiya ta basu na ɗaukar abincin da aka shirya su kai sashen Daddy. Manaal da Najma ne a gaba, sai dai Najma ɗin ma ta gota Maanal, dan itace ta fara shiga falon da sallama Maanal biye da bayanta. Da wani irin sauri Najma ce ta tsaya cak tana mai waro idanunta da faɗin, “Lah wa nake gani kamar su Yaya Fawzan da Yaya AA? Abah! Babban Yaya”. Da wani kalar sauri itama Maanal ɗin ta tsaya, hakama su Amrah duk suka tsaya suna kallon inda Najma ɗin ke kallo, sai ma ta ajiye kular hannunta ta nufi inda suke cike da mamaki da farin ciki. Ba ƙaramin girgiza zuciyar Maanal tayi ba, dan nata idanun akan AA ɗin suka fara sauka. Kamar shima kuma ance ya kalletan sai nasa idanun a kanta. Da sauri ta janye nata zuciyarta na zallo. Cikin ƙarfin hali ta maida su akan Abah da ya furta, “Finaly yau dai gani ga Autan Oum”. Ƙasa Maanal tayi da kanta tana murmushi, sai kuma ta cigaba da takowa cikin falon ta ajiye kayan hannunta inda su Amrah suka ajiye, gaban Abah taje ta durƙusa, har cikin ranta itama tana jin daɗin ganinsa. Abah ubane da bazata taɓa mantawa ba a rayuwarta. Ya nuna mata dukkan gata da soyayyar da ko ita ɗin a cikin ahalinsa ta fito iyaka kenan. Shiyyasa har gobe shine uba mafi kima da daraja da take kallo a cikin idannunta. Hatta da babu sunan mahaifi kawai yake amsawa a zuciyarta. Amma uba na gaske da bugun ƙirji a nunama duniya Abah ne farko. Cikin rawar murya alamar tahowar kuka ta shiga gaishe shi. Shima a mamakin duk wanda ke'a falon idanun Abahn cike suke da ƙwalla. Amma sai yay jarumtar sakin murmushi tare da kai hannunsa ya kamo nata. Kamar abinda take jira kenan hawayen suka shiga rige-rigen sakkowa. “My daughter nima so kike nayi kukan?”. Ya faɗa cikin taushin murya da kulawa. Kanta ta girgiza masa. Kafin ta share hawayenta ta ɗago ta ɗan kallesa. Murmushi ya sakar mata, itama sai tayi murmushin. “Abah nayi kewarka matuƙa”. Ta faɗa a hankali. Gefe ya kauda kansa, yasa babban yatsarsa ya ɗauke guntun hawayen daya ciko masa idanu shima. Har cikin ransa yana ƙaunar yarinyar, ɗaukarta yake tamkar yaransa guda uku daya mallaka a duniya. Sake juyowa yayi gareta da murmushin dai. “Nima nayi kewarki Maanal. Bantaɓa kwana na tashi babu ke a zuciyata ba. A kullum ina ji a raina akwai wani giɓi da babu a cikin ƴaƴana. ALLAH yay miki albarka, ya kare rayuwarki, ya azurtaki da farin ciki mara yankewa. Ya rabbi kasa iyakar jarabawar kasancewa a nesa da juna da mukai kenan.” Jiki a sanyaye kowa dake a falon ya amsa. Yayinda kan AA ke a ƙasa babu mai ganin fuskarsa balle yanayinsa. Gaishe da su su Aneesah sukayi suka fita, sai Najma da Manaal dake gaban Abah suna magana ƙasa-ƙasa da kowa baya ji. Dan hatta Daddy dake a kusa da su baya jin mi suke faɗa. Dai-dai nan Huznah ta shigo hannunta ɗauke da babban basket an shiryo abinci, sai yara biyu biye da ita da kayan ruwa da lemuka. Gaba ɗaya hankalinta akan AA da kansa ke ƙasa har yanzu yana latse-latsen waya. Babu ko kunyar mahaifinta dake a falon kanta tsaye gaban AA ɗin ta nufa ta dire basket ɗin, murya can ƙasa cike da iyayi ta ce, “Barka da zuwa gidanmu Sweetheart”. Ɗan jimm AA yay zuciyarsa na kai da kawon wai da shi ake ko wa? Ga shi kamar yasan muryar. Sake yin magana da tayi ya sashi ɗagowa a karo na farko, manyan idanunsa da suka ɗan kaɗe ba kamar sanda ya shigo gidan ba da suke fari tas ya zuba mata. Harga ALLAH yayi mamakin ganinta anan ɗin, amma sai ya dake ya wani kalar janye idanunsa ya maida akan wayarsa. Duk da zuciyar tata ta raunana da salon nasa haka ta dake tare da basarwa ta juyo tana kallon sauran mutanen falon. Karon farko gabanta ya faɗi sakamakon saukar idonta akan Abah, ya ALLAH, wlhy batasan harda mahaifinsa ba, ai da ta kama kanta. Ita tsabar ganinsa ya firgitata duk zatonta abokansa ne ma. Zaram ta miƙe daga gaban AA ɗin ta nufi inda Abah yake. Sai da ta watsama Maanal dake mata kallon mamaki harara sannan ta durƙusa cike da girmamawa tana gaishe da Abah. Amsa mata yay cike da kulawa dan kamannin Daddy a bayyane suke gareta. Ya tambayeta sunanta ta gaya masa tana faman sinne kai wai ita taji kunya. Kafin ta juya tana gaishe da su Babban Yaya. Ta gane Fawzan dan haka bayan gaisuwar ta tambayesa ina Oum da Mamy. Fawzan da al'amarin yarinyar ya ɗaurema kai ya bata amsa cikin dauriya. “Su Oum na tare da Ammie”. Zaram kuwa ta miƙe da faɗin, “Lah ai ban sani ba”. Kafin wani ya samu damar magana har ta fice. Tsabar mamaki daya lulluɓe Daddy ya saka shi suman zaune ya kasa magana. Sai kuma Huznah ɗin na fita Hajiya Basariyya da Maman Yaseerah suka shigo da sallama. Shi Abah ba wani sanin Maman Yaseerah yayi ba, duk da kuwa ƙanwarsa na matsayin kishiyarta. Koda suka gaishesu ya amsa ne da tunanin duka matan Daddy ne, dan kamanin Huznah yafi fitowa a fuskar Hajiya Basariyya. Fuskar Maman Yaseerah da murmushi ta ce, “To wai ni ina surukin namu anan?”. Karan farko Daddy daya kasa daurewa ya ce, “Suruki kuma?”. “Eh mana Alhaji. Ai baƙin Huznah ne, nazatama har sun sanar maka, shine muke maka batunsa kwanaki, har mukace ka shirya za'a kawo kuɗi kace a jinkirta a gama na Yazeed ko. Kamar AA naji tana ambatonsa da shi ita Huznahr”. Wani irin ɗagowa AA yayi ya kalla Hajiya Basariyya mai maganar, yayinda Abah da su Babban Yaya duk suke kallonsa su kuma. Shi ko Daddy Hajiya Basariyya ya zubama idanun kawai. Sai falon yay shiru akama rasa mai iya yin magana. Wani irin takaici ne ya gama turniƙe AA, jiyay bazai iya daurewa ba, dan haka ya buɗe baki a fusace zai yi magana, amma sai Babban Yaya dake kusa da shi ya kama hannunsa ya riƙe. Dole yay shiru, tare da haɗiye maganar. Tsaf Daddy ya lura da abinda ke faruwa. Dan haka a dake ya cema su Hajiya Basariyya, “Okay naji, kuje zasuci abinci tukunna”. Baki Hajiya Basariyya ta sake buɗewa zatai magana Daddy ya harareta, dole ta haɗiye. Suna fitowa Maman Yaseerah ta ce, “Kada ki wani damu shirin nan namu fa ya hau, kin san Malam akwai iya tsara abu”. “Anya kuwa Aminiya, kina ganin yanda yaron ke kallon mutane babu ɗigon sassauci, wlhy sai yanzu na fahimci abinda Huznah ke sanar min a kansa. Lallai da ganinsa zai yi baƙin taurin kai.” “Karki wani damu da taurin kansa, zamu bi dashi ne tsaf ya mata biyayya kamar babu gobe. Yanzu dai kawai muyi yaƙin shigarta gidan. Ammafa ni ina mamakin munene alaƙarsu da Asiya ne haka wai?”. “Nima wlhy ina son sanin wannan dangantar, amma ki bari, akwai ta hanyar da zan bincika”.
★A ɓangaren Huznah ma tana can sashen Ammie, hatta Mamy tayi mamakin ganinta, amma sai ta basar. Cike da ladabin daya bama Ammie da su Amaal mamaki take gaishesu, sai wani sissinkuy da kai take. Ita Oum ma bata wani maida hankali a kanta ba, hirarsu suke da Maanal dake jikinta kwance. Dan itama tun shigar su Hajiya Basariyya falon Daddy ta baro can. Saheeba dai da Nibras harara suketa antayama Huznah a kaikaice, dama kuma basu tanka ba koda tai gaisuwa. Bayan ficewarta cike da takaici Huznah tai tsaki da faɗin, “Ya akai tasan nan? Ko biyomu tayi ne? Nifa ban san ballagazanci wlhy. Yo ko mata sun ƙare mi Yaya Ajwaad zai yi da ita, balle ma yanada matarsa a hannu. Ai wlhy inaga sai Nuratu ta sake mata wani sabon zanen a fuska zata kiyayi mata saurayi”. Da mamaki Oum ta ce, “Ban gane ba, ke ina kika san wannan ɗin Saheeba?”. Batare da Saheeba ta kula kallon gargaɗin da Mamy ke mata ba ta ce, “Oum itace fa wadda sukai faɗa akan Yaya Ajwaad da Nuratu a Abuja”. “Ikon ALLAH, ai ni ban ganeta ba sam wlhy. To ya akai tasan nan ɗin?”. Amaal da Shaheeda da Ammie mamaki ya gama kashesu, Maanal kam yi tai kamar bata ji mi suke tattaunawa ba. Sai ma karanta saƙon da ya shigo mata a waya take wanda AA ne kuma ya turoshi akan tazo, amma ta masa reply da a (anƙi ɗin). Amaal ce ta bama Oum amsa da, “Oum ai anan gidan take, ɗiyar matar tsakkiyar gidan nan ce”. “Oh shiyyasa na ganta a gidan Shahidah kenan. To ALLAH ya rufa mana asiri ”. Da Amin kowa ya amsa aka saki zancen. Bayan sun kammala cin abinci ne Ammie da Oum da Hajiya Majdiya da Mamy sai Amaal, Shahidah da Maanal suka nufi sashen Daddy da yay kiran Ammie a waya. Sun samu suma sun kammala cin abinci, dan haka akai zaman gaisawa cike da mutunta juna. Abah nata tsokanar su Amaal. Dan yanda sukai jiki suka zama manyan mata ya bashi mamaki. Hakama yaransu da su Waleed duk suna zagaye da shi yanata sanya musu albarka da musu wasan jika da kaka. Sai da ya gama tsokanarsu yaran suka fito suka bar su Ammie can. Da wannan damar Abah yay amfani wajen bama Ammie haƙuri da neman gafararta akan abinda ya faru a baya. Ya ɗora da faɗin,..........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣2️⃣
______________
........“Nasan zakuyita mamaki akan rashin bin bayanku da bamuyi ba a wancan lokacin, a randa kuka wuce a ranar Fateema jikinta ya rikice matuƙa, dan yanke jiki tai ta faɗi, dole muka wuce da ita asibiti, amma sai suka turomu Abuja dan al'amarin nata banbane, paralysis na neman kamata. Tashin hankali yasa bamu tsaya Abujan ba kawai muka fara shirin fita da ita waje da tunanin bazamu daɗe ba zamu dawo sannan gwaggo ta huce, ashe wasa farin girki, dan shima Ajwaad sai ciwo mai ban tashin hankali ya samesa, ga depression. A haka suna cikin jiyyar su duka biyun Fateema ta matsa ni da Fadeel muka taho Nigeria domin ku, kai tsaye kuma Giro muka nufa, amma sai muka samu cewar wai ai suma sun wayi gari kun gudu, kuma an sanar dasu a majiya mai ƙarfi kuna dangin mamanki ba kuma a ƙasar suke ba. Bamu da wani dalilin ƙin yarda da su, dan haka muka juya muka koma. Amma Fateema naji tace ƙaryane, baki da wani dangi a ƙetaran Nigeria, ta sake tada hankalinta har takai jikinta dana Ajwaad yayi rikicewa mai ban tsoro, dan Ajwaad akwai daren da ma har mun gama yarda ya rasu, sai kuma ya farfaɗo gabannin asuba. Sai da akaita tausarta tare da mata alƙawarin a hankali zanta bincikenku sannan, muka maida hankali akan Ajwaad kuma. A lokacin ne kuma aka bani ambassador, shiyyasa bamu dawo Nigeria ba, amma inata ƙoƙarina batare data sani ba akan neman ku. Sai dai kuma ALLAH bai ƙaddara ba sai a dalilin samuwar aikin Maanal a kamfanin Ajwaad ta dalilin Rafeeq. Dan ALLAH mu yafi juna Asiya, mu ɗauka dukkan abinda ya faru ƙaddararmu ce babu mai canjata. Mu dawo da zumincinmu tamkar a baya can.” Hawayen dake gudu a fuskarta Ammie ta share. Ta ce, “Babu komai Yaya komai ya wuce. Ni dama ban taɓa ƙullatarku ba wlhy. Sannan ban san ma Maanal a ina take aiki ba dan basu sanar min ba. Da tun kafin kuzo nan ma nice zanzo gareku, ban dan Rafeeq nada alaƙa da ku ba shi da Maman Najma. ALLAH ne kuma bai ƙaddara haɗuwar tamu ba shiyyasa, tunda gamu tare da Majdiya fin shekara huɗu”. “Ikon ALLAH ai yafi gaban wasa. Wannan wata hikima ce ga UBANGIJI mai ɓoye al'amura ta yanda yaso, a kuma inda yaso. Shi kuma yasan dalilin yin hakan garemu”.. Haka ne. Kowa ya faɗa cikin jinjina kai....
_________★
Da yamma sosai su Abah sukai shirin wucewa, sai dai fa Oum tace suje ita sai gobe in sha ALLAHU. Jin haka AA yace shima ya fasa, ƙafar babarsa ƙafarsa. Wani irin takaici ne ya turniƙe zuciyar Mamy, dan haka kawai take ji a ranta wani abun Oum ke son ƙullawa. Sai kawai catai ai itama kuwa tana nan ɗin. Sam babu wanda ya kawo komai a ransa a tsakanin Oum da Ammie, sai AA ne yay wani iri. Daga baya kuma yace to kawai shi bari ya bisu. Yana ganin hararar da Mamy ke masa amma ya basar. Nibras kam wani sanyi taji a ranta, dan har hankalinta ya tashi da zaman AA a tsakiyar kuraye biyu da take kallo. Wato Maanal da Huzna😂, yayinda Huznah da keta dama-dama da AA ɗin taji kamar tayi kuka. Haka dai babu yanda ta iya suka wuce. Dama Maanal ko'a kwalar rigarta, sai ma hirarsu suke da Fawzan....