Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 61
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 61: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 61. ★ Ya jima tsaye a inda ta barshi…
4,302 words
★ Ya jima tsaye a inda ta barshi yana kallonta, kafin ya tako shima a inda taken. Kujerar dake facing ɗinta ya zauna, batare da yace mata komai ba ya zuba mata idanunsa kawai hannayensa duka harɗe a ƙirjinsa. Yanda ya zuba mata idanun nasa masu kaifi ya sakata daburcewa ta daina fahimtar abinda ma ta fara karantawa. Amma a zahiri bazaka taɓa tunanin a rikicen take ba dan ta maze ƙwarai da gaske kamar bata san da shi a wajen ba. Dai-dai nan kiran Oum ya shigo wayarsa. Kasancewar ringing ɗinta na musamman ne ya saka shi dakatawa daga faɗar abinda yay niyya ma Maanal. Wayar ya ciro daga aljihu yana gyara zamansa da ƙyau. Sai dai idanun nasa har yanzu a kanta tamkar ya samu television ɗin kallo. Cike da tsokana ya furta, “Assalamu alaikum uwargidan Abah har a ALJANNA”. Murmushi Oum tayi daga can. Cike da jin shauƙin ƙaunar Autan nata tace, “ALLAH to ya tabbatar Autan Oum ɗinsa, sannan tare da ku Bestyn bestynsa.” Murmushi AA yayi mai faɗi, sai kuma ya ɗan saci kallon Maanal a miskilensa ya furta, “Shike nan dai Oumna kin rama 1-1 kawai.” Dariya sosai Oum tayi, sai kuma ta ce, “Dama zance kazo kaci abinci gamu nan zuwa tare da Abahn ku zaici abincin tare damu”. “I'm so happy, Oum! gamu nan”. Daga haka ya yanke batare da Oum ta fahimci inda (gamu nan) ɗinsa ta dosa ba. Yana ajiye wayar ya zare book ɗin Maanal tare da ɗaukar kwalin popcorn ɗin nata da goran ruwan ya ce, “Oya let's go Oum na kira”. Komai bata kawo a ranta ba ta miƙe kawai. A jere suka fito duk da ba wata hira suke ba. Sai da sukazo fitowa ne cike da neman magana ya gwargwaɗa mata magana a kunne. Da sauri tai gaba zata barsa saboda kunya, yayinda murmushi ya ɗan ƙawata fuskarta batare data shirya hakan ba. Shima murmushin yake yi dan haka kawai murmushin nata ya saka shi jin nishaɗi. Ai cak Abah da Oum dake fitowa daga sashensa suka tsaya. Galala Abah ya saki baki yana binsu da kallo, yayinda Oum ta gimtse dariyar dake neman suɓuce mata da ƙyar. Suna tsaye kamar gumaka AA da Maanal suka shige sashen Oum batare da su sun ma farga da su ba. Gyaran murya Oum tayi kaɗan, hakan ne yasa Abah maido da idanunsa kanta, harrarta yayi. Daƙyar ya iya gimtse dariyar tayi gaba tana faɗin, “let's go tunda gasu can.” bata jira cewarsa ba tai gaba tana murmushin data kasa riƙewa. Suna zuwa ƙofar sashen Oum Maanal ta zame tai hanyar baya ta kitchen ita adole bata son a gansu tare da AA. Bata san wanda take gudun su gansun ba sun riga sun gansu. Samun su Inte na haɗa abincin da zasu kai dining sai kawai ta shiga tayasu. AA kam daya shige shi kaɗai dariya ma ta bashi. A ransa yace (Magulmaciya, kina so kina kaiwa kasuwa). Fawzan kawai ya samu a falon yana kallo. Zama yay kusa da shi. Fawzan ya dubesa da ƙyau, sai kuma ya ɗan matsa da fuskarsa yana shinshina shi. Harararsa AA ɗin yayi, ciki-ciki ya ce, “Miye?”. Da ƙyar Fawzan ya gimtse dariyar dake cinsa, cikin ɗaure fuska shima kamar yanda AA ɗin yayi ya ce, “Yada tsarguwa haka Malam, ka bari na gama tantancewa mana. Naji ne kana ƙamshi kamar na turaren Lilly.” Irin ɗan waro idon nan AA ɗin yayi, ya ce, “Kai yaya Fawzan ido ka koma samin?”. “Oh da mikake tunani? Kasan dai bazan bari aci amanar Abah ba. Kuma zanma ƙanwata garkuwa”. Rasa ma abin cewa AA yay, sai kawai ya zubama Ya Fawzan ɗin ƙasaitattun idanunsa. Sosai Fawzan ya kwashe da dariya, dan yasan ya gama kaishi maƙura kenan. Ai idan kaga Auta ya rasa abin faɗa to yakai maƙura kenan... A haka Oum da Abah suka shigo suka samesu. Gaishesu sukayi, suka amsa Oum na faɗin, “A'a ina Baby na kuma?”. Fawzan ne ya bata amsa da, “Ai tunda na shigo ban gantaba Oum, maybe tana sama ko?”. Kai Oum ta jinjina tana jiran AA ya bada amsa, amma ya basar abinsa tamkarma baijisu ba. Sosai shima Abah ke satar kallon AA ta gefen ido ransa fal mamakin, dai-dai nan Maanal da su Inte suka fito a kitchen. Dariya taso kama Oum, amma ta danne da ƙyar idonta akan Maanal ta ce, “Oh ashe kina kitchen Auta”. Kai Maanal ɗin ta jinjina tana murmushi da satar kallon AA daketa latsa waya kanshi kwance a kafaɗar Fawzan hankalinsa kwance like baima san mike faruwa ba. Juyawa tai tana gaida Abah dayay Zuru yana kallonsu su duka. A ransa ko faɗi yake (Aiko zakuci ƙaniyarku ku duka) a zahiri kam amsawa yay cike da kulawa. Daga haka suka ɗunguma dining cin abinci.....
A nutse suke cin abincin, yayinda Oum da Abah ke ɗan hira Fawzan kuma da Maanal. AA kam hankalinsa nakan waya komi yake oho masa. Abincin ma bawani ya maida hankali bane a cinsa. Wayar Oum ta zare daga hannun nasa, yako kalleta a shagwaɓe. Harararsa tayi tare da nuna masa abinci tana faɗin, “Ni tunda ka tashi ciwon nan kake neman maida abinci abokin gabarka Auta. Oya maza yanzu naga plate ɗin nan, in ba haka ba ɗura zan maka”. Dariya Fawzan yayi, Maanal ma ta kasa riƙe nata murmushin saboda ganin yanda AA ɗin yay da fuska. A dai-dai nan Mamy ta shigo sashen da sallama. Gaisheta Fawzan yayi bayan duk sun amsa mata sallama, tare da faɗin, “Naje sashen yaran nan sukace kina wanka”. Cikin danne takaici Mamy ta ce, “Eh sun faɗa min”. Ledar hannunta ta ajiye a gaban AA da tunda ta shigo ya maida hankalinsa ga cin abincinsa. Maanal kam sai satar kallon Mamyn take bayan ta gaisheta itama. Ajiye ledar ya saka AA ɗagowa ya kalleta a karo na farko, hakama su Abah kallon ledar suke. Murmushi ta ƙawata fuskarta da shi, tare da juyawa tana kallon Oum. “Bara na aiki ɗanki gidan Aunty tunda dai yaji sauƙi, na manta shaf har drivers ɗin gidan sun tafi gashi da sassafe zasu wuce lagos”. Fuskar Oum babu wani damuwa ta ce, “Eh ya kamata kam a kai mata su a daren nan. Auta sai ka maida hankali ka gama ko kar dare yayi, duk da dai kai ba tsoron fitar daren kake ba”. Kansa kawai ya jinjina batare da yayi magana ba. Dan shi yasan babu wani saƙo. Mamyn ce ta kafa masa sharaɗin zuwa yaga Nuratu ya kuma bata kayan da zata bashi yace inji shi wai Ramadan basket. Zama Mamyn tayi suka cigaba da hira da Oum da Abah, sai kawai AA ɗin ya miƙe badan ya kammala cin abincin ba, dan zuciyarsa gaba ɗaya jinta yake a ƙuntace, amma miƙewar da zai yi suka haɗa ido da Maanal sai wata dabara ta faɗo masa. Guntun murmushin iya shege yayi, cike da shagwaɓa ya dubi Abah. “Abah dan ALLAH ka bani aron ƴarka ta rakani tsoro nake ji”. Atare gaba ɗayansu suka ɗago suna kallonsa, ya sake narke fuska kamar zai yi kuka. “ALLAH Abah da gaske nake”. Ai kasa daurewa Fawzan da Oum sukai suka sanya dariya. Abah kansa da ƙyar yake iya danne tasa dake neman kufcewa. Maanal kam baki da hanci tama saki tana kallonsa, yayinda Mamy ta cika tayi fam fa takaici har hakan ya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Cikin dariya Oum ta ce, “Please Abansu a taimaka mana, ai bazasu daɗe ba yanzu zasu dawo”. Fawzan ma yace, “Abah ayi haƙuri ta rakashi kada yay mana kuka ko kura ta cinyeshi a hanya dan tsoro. Kasan Besty da Besty duk tsanani tare suke zuwa aika”. Kai Abah ya girgiza, tare da faɗin, “ALLAH ya shiryeka Ajwaad. Jiba yanda ka wani ɓata fuska like zakama mutane kuka. Shike nan kuje, amma ina nan ina jiran dawowarku, idan kuka daɗe kwanakin zan ƙara”. “Thanks You sweet Abah”. AA ya faɗa a hankali. Nan ma kan Aban ya girgiza kawai, yayinda Oum ke faɗin, “Baby tashi ku tafi kinji”. Ji Maanal tayi kamar ta nutse dan kunya. Duk da kuwa a shekarun baya hakan ba komai bane a tsakaninsu. Dan ko tana gidansu aka aikesa zaije yace tazo ta rakashi kida cikin anguwa ne. Haka itama idan aka aiketa ko yana gida agaban su Abah ɗin zatazo tace masa (Besty zoka rakani aika) amma sai yau gashi tana jin hakan kamar sabon abu. Sarai AA na lure da mugun kallon da Mamy ke masa, amma ya fuske abinsa, sai ma nufar sama da yay ganin Maanal na niyyar warware ƙaramin veil ɗin kanta alamar da shi zatama fita take nufi. Da kallo duk suka bisa, Fawzan kuwa na masa tsokanar daya saba da kirari. Babu jimawa ya dawo da mayafin da yafi na kan nata da ke kamar na yara dan na Abaya ne. Wanda ya miƙa mata ɗin ta kalla, sai kuma ta ɗan tura baki gaba. Wancan ta cire ta amshi na hannun nata ta sanya, zata nufi saman itama ta maida Oum tace ta kawo kuje kawai kar dare yayi. Oum ɗin ta ba, shi kuma ya ɗauka ledar Mamy da takaici ke neman bombing mata zuciya suka fice..........✍️
_Abah da kasan kura kaba ajiyar nama da baka bayar ba😂🥱_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. 🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣
______________
.......Wata Nurse da Sageer ya kira anan anguwarsu na tsaka da duba Huznah kiran Hajiya Basariyya ya shigo wayarta. Kasancewar yana a kusa da ita shi ya kai hannu ya ɗauka dan ita ana mata ƙarin ruwa ne. Shine ya fara yin sallama, dan haka Hajiya Basariyya tai ɗib daga ƙoƙarin maganar da tai niyyar yi. Da ƙyar ta iya amsa masa gaisuwar da yake mata. Kafin ya ƙara cewa wani abu ta yanke kiran. Murmushi kawai yayi baice komai ba. A ransa kam dariyar ƙeta yake da faɗin (Mama ai sai kuma haƙuri, ƙiyayya ta ƙare tunda ruwa ya gauraya da jini). A zahiri kam murmushi yayi kawai....
Wani irin malolon baƙin ciki ne ya sake tokare zuciyar Hajiya Basariyya. Dan ita kam abin ya zame mata goma da goma. Tana yaƙin ganin ta koma ɗakinta kafin Hajiya Yaya ta koma, Daddy kuma ya saki Asiya a randa ta koma dan alwashine sai tayi maganin Asiya a wannan gaɓar ga kuma batun Huznah da shima suketa faɗi tashin ganin wannan auren ya rabe tazo ta auri AA sun fiddo waccan shegiyar agolan daga ciki mai ƙwacen saurayi. Ita kuma sakaran tayi sakaci wannan matsiyacin ya kwace ɗan mutuncin. Zaune takai a bakin gadon ɗakin da take zaune a gidan yayanta, ɗakin da saida akai uban rikici matansa suka bari ta zauna duk da kuwa ɗakin baƙi ne. Kayayyakin data amso a Zaria tare da Maman Yaseerah take bi da kallo. Haɗi ne sosai tayoma mutane guda biyar. Daddy, Asiya, Hajiya Yaya, sai mijin Huznah da AA. Kuma duk ana son ta aiwatar da su daga nan zuwa gobe, shiyyasa ma tai kiran Huznah dan taji yaya za'ai nata ya iso a goben itama ta aiwatar, ko Sageer na yawo da ubansa ko sai ya saketa da hannunsa. Dan sunan maganin KANWA UWAR GAMI. Amma shine tantirin ya ɗauka mata waya.. Bumm!! Bumm!!! Bumm!!! Bugun ƙofar ɗakin da take aka shiga yi da masifar ƙarfi, a zabure ta miƙe tana yayimar kayan ta tura ƙasan gado, kafin ta mirza idonta ta nufi ƙofa kamar mai barci. Dan bata raba ɗayan biyu yayanta ne matansa sunkai ƙararta saboda yau ta zagesu tas wai suna saka mata nama biyu a abinci, duk naman dake gidan saboda an rainata ace biyu ne kawai kasonta... Tana gama buɗe ƙofar wani kakkauran mari ya ratsa mata kumatu. Da bala'in sauri da rawar jiki ta dafe fuskar da hannaye biyu gaba ɗaya. Bai dubi girman shekarunta ba ya sake wanketa dana biyu. Shi dama mutum ne mai zafi sosai. Ai yanzu kam ihu ta ƙwala dan azaba ta koma cikin ɗakin a guje. Bayanta yabi, ta maƙure jikin bango tana hawayen azaba a matuƙar gigice. Cikin wata irin tsawa mai kaɗa hanji ya ce, “Ina kukaje yau dan ubanki?”. Hawaye na ziraro mata ta ce, “Babu inda naje fa yaya, matanka sun haɗani dakai saboda su munafukai ne. Wankin kai da kitso fa naje kuma na gaya maka ka bani kuɗin da kanka”. “To mara mutunci, aiba maraina wayon naki bane ba ni da idona na ganki tare da Alhaji Usman a Zaria. Ko zakice min kitson acan akeyi?”. Sosai jikinta ya fara rawa na haƙiƙa kam yanzu, zuciyarta kamar zata faɗo cikin in-ina tace, “Yaya Zaria kuma?..” “Oh ƙarya nai miki kenan? Wlhy Basariyya ki shiga hankalinki a gidan nan. Wato har yanzu baki daina biye-biyen bokayeba ko? Shike nan karki fasa ki cigaba da yi, ki kuma haɗa inaki-inaki gobe kawu na Katsina zaizo ku tafi tare. Ki koma can wajensa dan ni bazan iya ba...” Wani irin gigitaccen ihu ta sanya tana roƙonsa ya taimaketa bazata iya zama gidan kawun nasu ba. Ko kallonta baiyi ba ya fice abinsa. Tashin hankali matuƙa Hajiya Basariyya ta shiga a wannan dare. Dan wlhy bazata iya zama gidan kawu Manu ba. A ƙauye yake bama cikin birnin katsinar ba, ita wlhy ko ruwan gidan bata iya sha idan sukaje gaisheshi na yini ɗaya saboda kiwon dabbobinsa na tsiya. Gashi masifaffe hakama matarsa, kuma su duka ƴan uwansu ne dan auren zuminci ne shida matar tasa. Tun babansu na da rai ake fama da shi ya baro ƙauyen amma yaƙi. Mahaifinsu kansa tsoronsa yake ji balle su, dan mutum ne azababbe na bugawa a kalanda, ga tsauri dan komai na gidansa da doka akeyinsa. Kuka sosai taci, daga ƙarshe ta yanke shawarar yin asubanci ta gudu. ALLAH gara ta koma gidan mijinta duk ma bala'in da za'ai ayi bazata fito ba koda Daddy zai daketa kuwa. Kayanta ta shiga haɗawa, tsaf ta kammala ta ajiye komai a ƙofar ɗakin, sauran kuma ta ajiyesu akan daga baya zata turo su Madeena yaranta su ɗaukar mata. Ko barcin kirki kuwa batayi ba, huɗu na bugawa zabar ta miƙe dama ba wani barcin kirki tai ba, a gurguje ta shiga bayi ta kimtsa ta fito, ta saɓi jakarta tana murmushin nasara, sai dai tana murɗa handle ɗin ƙofar taji gam, hakan na nufin an kulleta ta baya kenan. Ai jitai gaba ɗaya ta wani irin gigicewa, bama tasan ta zube a wajen ba ta fashe da kukan takaici, dan ta tabbatar yayanta ne ya rufeta tun fitar jiyan da yayi.......
🤣🥱Ba abun faɗa _________★
Sun fito a jere Maanal na faɗin, “Kai dai ka canja hali ALLAH”. Cikin ƙunƙuni take maganar, amma hakan bai hana AA ɗin jinta ba saboda ƙarfin ji da ALLAH ya bashi. Murmushi yay kawai, sai kuma ƙasa-ƙasa shima yace, “Inba tsoro ba a fito fili a faɗa mana”. Sarai itama Maanal ɗin ta jishi, sai dai bata tanka ba saboda isowarsu wajen motarsa. A dai-dai nan kuma Saheeba ta fito daga sashen Mamy, taje wajenta su Haule suka sanar mata tana sashen Oum. Sai ga Nibras itama ta fito daga sashenta, taci kwalliya abinta sai baza ƙamshi take kamar wadda zata fita. Itama dai sashen Oum zataje, kuma wannan kwalliya duk ta AA ce. A tare duk suka tsaya cak suna binsu da kallo, har Maanal ta shiga mota AA daya buɗe mata ya maida ya rufe sannan ya zaga mazauninsa, sai dai shima kafin ya buɗe da kansa Maanal ta buɗe masa ta ciki kamar yanda suke yi a da. Kallonta yay fuskarsa da murmushi mai sanyi, itama ta masa murmushin tana kauda kanta dan su duka zukatansu suna tariyo musu baya ne. A hankali ya baya mai gadi ya buɗe masa gate suka fice. Daga zuciyar Nibras har ta Saheeba tamkar zata kama da wuta ne. Cikin takaici da wani irin zazzafan kishi Nibras ta ce, “Wannan mayyar yarinyar sai nayi maganinta”. “Haɗa dani nan Nibras dan na tsaneta”. Saheeba ta faɗa itama a zafafe. Da sauri Nibras ta kalleta dan ita bata san nata zancen ya fito fili bane ba. Kai Saheeba ta jinjina mata batare da sanin manufar Nibras ɗin na tsanar Maanal ɗin ba. Ita kuma Nibras tasan dalilin Saheeban bazai wuce taya ƙanwarta kishi ba. Amma saboda takaicin da take ciki sai ta cigaba da faɗin, “To wai ina zasuje a wannan daren? Nine fa?”. Wata ƴar dariyar takaici Saheeba tayi, “Kin san tunda tarewa ta gagareta zatabi duk wata hanya ne yanzu na son ganin taja ra'ayinsa, balle an saba da bin maza a waje”. “Tabbas kumafa hakane. Shegiya mai zuciyar karnuka, mutum yace baya sonki amma ina, inba shashashar amarya ba mara muhimmanci wa ake kawowa a ajiye sashen surukai gana miji”. Nibras ta faɗa zuciyarta na mata raɗaɗi. Dariya sosai Saheeba keyi, ranta fes ta ce, “Ai Abah ne maganin ƴar iska, uwarta na murna bokanta ya iya aiki an mannota gidan da tsiya-tsiya shiko ya harba musu tsiya, Kinga ɗan maganin da aka ɗan cuccusa dan matse can duk ya sane. Ai wlhy sai mun dage munci ubanta a gidan nan ta yanda ko ruwa bazata iya sha ba sai a ɓoye, da ƙafafunta zata gudu ne”. Hannu Nibras ta bama Saheeba suka tafa, dan a ganinta ai gara su haɗa hannu da Saheebar su kori Maanal ɗin ita kuma sai tai yaƙin hana shigowar ƙanwar Saheebar ta bayan fage. Aiko a take ta bada goyon baya ɗari bisa ɗari. Sai da suka gama shirya mugunnyarsu sannan suka nufi sashen Oum ɗin. Acewarsu gara suje su zauna suga dawowarsu...
A hankali AA ke murza steering tamkar baya so, yayinda Maanal tai shiru lafe a cikin kujera. Daga gani kasan duniyar tunani duk suka faɗa. Cikin son kauda yanayin AA yay ɗan gyaran murya. Idannunta dake lumshe ta buɗe ta kallesa, shima ɗan kallon nata yay fisha sai kuma ya maida ga hanya. So yake su dawo kamar da, amma yasan yaƙine babba a gareshi, dan haka maimakon zuwa mata kai tsaye zaibi wasu hanyoyin yin hakan. Muryarsa a tausashe ya furta, “Yaushe kika fara karatun novels? Bayan nasan haushi kike ji idan kikaga inayi ma”. Ɗan jimm Maanal tayi kamar bata jisa ba, har sai da ya ɗan kalleta. Ƙin kallonsa tayi ita, a taƙaice ta ce, “Kawai na tsinta kaina ne a karatun batare da wani dalili ba”. Murmushi ne yaso suɓuce masa, amma sai baiyi ba a bayyane ya tsaya masa iyakar cikin ƙirji. Zamansa ya ɗan muskuta da sake damƙe steering da ƙyau ya tsaya a danja data tsaida su, sai kuma ya koma ya jingina bayansa da kujerar ya juya yana kallonta. “Zuwa yanzu books nawa kika karanta?”. Kaɗan ta ɗan kallesa, cikin yin warrr da idannunta ta ce, “Suna da ɗan yawa fa. Damma Ammie na hanani ne”. “Ammie bata san karatun novels da daɗi bane shiyyasa. Kinga ni akwai wani book da nake nema saboda labarinsa da aka ɗan fara bani amma har yanzu ban samu ba, koda yake busy na ne ya hanani zuwa manyan books store na duba”. Yanzu kam muryar Maanal a sake ta kuma juyo tana kallonsa da ƙyau ta ce, “wanne ne?”. Sai da ya tada motar suka cigaba da tafiya saboda danja ta sake su sannan ya bata amsa. Murmushi tayi mai faɗi sosai har haƙwaranta na bayyana ta ce, “Hum'um kaga nikam na jima da karanta shi, dan tun ina shekarar ƙarshe a makaranta. Ina zaton ma kamar ina da copy ɗinsa yayi daɗi kam ba ƙarya”. “Woow da gaske Besty?”. “ALLAH kuwa bari zan duba maka, sai dai inaga yana cikin kayana da za'a kawo daga Kaduna”. Dai-dai nan yay parking gaban wani baƙin gate madaidaici yana bata amsa, gidan dai daga waje ba wani babba bane, dan kamar gidajen street ɗin ma duk sun fishi girma da ƙyau. Anan wajen gate ɗin ya kashe motar bayan yayi horn, wani ƙyamushashen mutum ya leƙo, alama AA ya masa da hannu na yazo. Bayan ya kunna fitilar cikin motar ta yanda zai ganshi da ƙyau kada ya tsorata. Aiko sai da ya leƙo daga nesa yaga wanene sannan ya ƙaraso yana famar washe baki. Cike da girmamawa ya shiga gaida AA ɗin, amsa masa yay shima da kulawa, kafin yace ya ɗan kira masa yarinyar gidan nan. Nanma da girmamawa mutum ya amsa masa, daga gani dai kasan maigadi ne. Maanal dai na jinsu, dan tunda ta amsa gaisuwar da mutumin yay mata ta ɗauke kanta gefe. Fitilar AA ya kashe, sai kuma ya ɗakko tab.. ɗinsa ya shiga dannawa, miƙama Maanal tab ɗin yay yana faɗin, “Kinga list ɗin novels ɗin da nake nema idan na samu lokaci na karanta su”. Amsar tab ɗin tayi, ta shiga duba list ɗin, cikin manta dawama take tare ta ɗan karkato tana nuna masa wanda ta karanta a ciki da wanda itama take nema ta karanta. Shima karkarowar yayi sosai har jikinsu na haɗuwa, ta shagala a nuna masa da yimasa bayani har ya ɗaura hannunsa a kafaɗarta ya sake kwantota a jikin nasa da ƙyau batare data farga ba, sai ma sake lafewa tayi sosai abinta tana zuba zance, dama can ta fishi magana, yanayine kawai ya maidata miskilar ƙarfi da yaji. Shi ko idan kaga ya saki jiki kamar haka yana magana to lallai tare yake da ita, dan sai kaga ma kamar ba AA Darma sarkin haɗe fuska da jefa magana ɗaɗɗaya ba da ƙyar. Sun shagala a hirarsu dake fita ƙasa-ƙasa dan ko ita Maanal ɗin da maganarta tafi yawa bawani tanayi zuuu bane ba, koda a cikin motar kake ma ba lallai ace ka jisu yanda ya kamata ba. Balle shi dake bata amsa kamar mai raɗa. Glass ɗin motar tinted ne, dan haka Nuratu data fito cikin matsananciyar kwalliya tana zuba wani shegen ƙamshin mayataccen turaren magani da babarta ta zazzage mata kanta tsaye ta nufi gefen mai zaman banzar fiskarta kamar ta yage dan murmushi. Wai itace yau Ya AA yazo wajenta hira, kai ita kam tafi kowa sa'a a duniya yau ɗin nan. Ta tabbata harta mutu bazata manta da wannan rana ba a tarihin rayuwarta. Sai da taja numfashi ta fesar tare da sake dai-daita kanta da ƙyau, dan babarta taja mata kunne matuƙa akan ta nutsu kada taje tana wannan rawan kan tunda tasan halinsa dai sarai. Sai da ta tabbatar ta samu irin nutsuwar da take buƙata kafin ta ɗaura hannunta a handle ɗin motar ta buɗe tana faɗin, “Assalamu aikum Yayan....” sauran maganar ya maƙale a maƙoshinta sakamakon saukar idannunta akan Maanal dake kwance a kafaɗar AA suna kallon abu a tab...........✍️
_😂😂Ni dai Nurry ƙawata ce bani da damar cewa wani abu anan🥱🤣🤣🏃🏃🏃_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣7️⃣
______________
........Nurry tamkar wadda ta suma haka ta kasance, yayinda AA da maaanal suka ɗago idanu a tare suna kallonta kawai. Ta kuma ƙi tashi daga jikinsa sai ma ƙara gyara kanta da tayi. Jitai zuciyarta ta mata wani irin nauyi da ganin Nurry ɗin, dan tabbas da tasan gidan su yarinyar nan zasu zo da bazata biyo shi ba. Amma a zahiri babu ko ɗigon damuwa a fuskar tata, sai ma wani irin murmushi data sakarma Nuratun a karo na farko ta furta, “Hy” a hankali. Sai a lokacin Nuratu ta farfaɗo, a hankali ta zame hannunta dake ɗan rawa daga jikin murfin ta miƙe tsaye gaba ɗaya. Cikin kaushin murya AA ya ce, “K! Baki iya gaisuwa bane?”. Sosai muryar tasa ta ratsa mata zuciya, sanin halinsa na rashin ɗaukar raini ya sakata sake duƙowa dole batare data yarda ta sake kallonsu ba muryarta na ɗan rawa kamar mai shirin fashewa da kuka saboda kishi ta furta, “Kayi hari Yaya ina yini”. Maimakon amsawa sai yaja siririn tsaki kawai. Maanal dai tama maida hankalinta ga tab ɗin gaba ɗaya tamkar bata san mi sukeyi ba. Maanal ɗin ya nuna mata, cikin harara ya ce, “Ita kin gaisheta ne”. Sosai hawayen baƙin ciki suka ciko idanun Nuratu, cikin matuƙar raɗaɗi da jin ƙunar zuciya ta ɗan kalla Maanal ɗin ta ce, “Ina yini”. Tsabar wulaƙanci yatsu biyu Maanal ta ɗaga mata, batare data kalleta ba ta ce, “Kina lafiya?”. Wata shegiyar ashariya Nuratu ta shiga mulmulawa Maanal ɗin a zuciya, a zahiri kam dole ta amsa. AA da bai sake ko kallonta ba juyawa yay sit ɗin baya ya ɗakko ledar da Mamy ta bashi. Ɗan kwantowa yay ta jikin Maanal sosai ya mika mata ledar yana faɗin, “Kiba mamanku inji Mamy”. Sake sumewar takaici Nuratu tayi yanzu ma, har sai da AA ɗin ya mata ƴar tsawa da faɗin, “Wai tunanin uwar mi kike”. Firgigit ta amshi ledar zuciyarta na hautsinawa. Da kansa ya jawo murfin ƙofar kamar a fusace ya rufe. Dole taja da baya da sauri gudun bugeta da murfin. Shi ko ko'a kwalar rigarsa yayma motar key yay reverse batare daya ko sake kallon inda take ba ya bar wajen...