Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul - Chapter 62
Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 62: Ajiya a duhu book 1 & 2 complete by billyn abdul Chapter 62. Gaba ɗaya Nuratu ta zube a wajen…
3,896 words
Gaba ɗaya Nuratu ta zube a wajen ita da ledar, wani irin kukan baƙin ciki irin mai babbake zuciyar nan a lokaci guda ta saki da iya ƙarfinta. Aiko da gudu mai gadinsu dana maƙwaftansu suka fito suna tambayarta lafiya. Amma bata ko kallesu ba. Maigadin maƙwaftansu yace, “Kodai mugu ne yazo wajenta a sanar da securitys ɗin shigowa?”. Kai maigadinsu ya girgiza masa, “A'a nasanshi, ɗan uwansu ne ma sai dai idan wani abunne ya faru. Kaga tsaya min a wajenta bara na sanarma su Hajiya.” baima jira amsar shi ba ya shige gidan. Babu jimawa kuwa suka dawo da Hajiya, basu kowa bane face Maman Nuratun da mariƙiyarta, dan jiya Maman nasu tazo daga Kano batare da ko sanin Mamyn ba. Rufuwa sukai a kanta da tambaya cikin tashin hankali. Ganin bazata basu amsa ba suka kamata zuwa ciki, maigadi ya bisu da ledar (Ramadan basket🤣). Tambayar duniya su Hajiya Turai sunma Nuratu dake kuka kamar wadda ake yankawa amma taƙi basu amsa. Sai da mamanta ta balbaleta da masifa sannan cikin kuka ta sanar musu komai. Suma duk shiru sukayi cikin tsananin ɓacin rai. Musamman ma mamansu. Hajiya Turai ta ce, “Amma dai Kamila bata ƙyauta ba, ni da mukai waya kinga ai tace min zaizo ne wajen Nuratun su ɗan zanta ya kuma bata hasaffin azumi da samari ke ɗan bama ƴammata a yanzu. Shine zasu bari ya taho da wata kuma?”. Ɓacin rai ya hana Maman su Nuratun iya cewa komai. Cikin fushi ta fisga waya da nufin kiran Mamyn Hajiya Turai ta riƙe mata hannu. “Mi zakiyi?”. Rai ɓace ta ce, “Kiranta mana yaya Turai, banda rainin hankali tasan har yanzu bata da power ɗin tanƙwasa ɗanta zata saka mutane yin asara a banza yazo yana wulaƙanta mana yarinya”. “Toke banda abinki keda bata san kina garin ba kuma. Ki barni kawai da ita. Dan ni ba Kamila zanmawa yarinyar zan wulaƙanta. Sai na sakata nadamar dawowa rayuwar ahalin Darma. Shi kansa Ajwaad ɗin zan koya masa hankali, dan banga mai taɓa min Nurry yay barci lafiya ba koda kece da kika haifeta. Dan ni ba yayar uba bace kawai uwa ce”. Sosai zuciyar Maman su Nuratu tai mata sanyi, shiyyasa take matuƙar son Hajiya Turai. Dan akwai mutunci da ƙaunar juna sosai a tsakaninsu tamkar ba yayar mijinta ba. Kai a kaf dangin uban su Saheeban da Hajiya Turai kawai suke ɗasawa, ba kuma komai ya kawo hakan ba sai halinsu ne da yazo ɗaya. Sannan Nuratun tun daga yaye Hajiya Turai ta ɗauketa ta riƙe kasancewar ita har yanzu ALLAH bai bata haihuwa ba, mijin ma ya jima da rasuwa shiyyasa suka baro Lagos inda suke zaune da suka dawo nan Abuja. Sai dai da yake tana bussines koda yaushe ƙafarta na hanyar lagos ɗin da Dubai da Chaina. Shiyyasa Nuratun ke zuba tsiyarta yanda take so a garin na Abuja, dan ƙazamin gata Hajiya Turai ke mata, sannan duk abinda ta nema saita mata shi. Wannan yasa take jinta a babbar yarinya ɗiyar manyan mata masu kuɗin Abuja. Dan ubansu dai bawani kuɗin arziƙi ne da shi ba, hasalima da bazar Hajiya Turai ɗin yake rawa shima.... Hajiya Turai data raka Nuratu ɗaki tace ta kwanta tana fitowa ta tashi, wayarta ta ɗauka tai kiran Sille. Bugu biyu kuwa ya ɗauka. Kamar yanda ya saba cike da yaudara ya shiga yimata kirari da fasa mata kai. “Kaga Sille yanzu ba lokacin kirari bane ba tsaya kaji”. Nuratu ta faɗa muryarta a shaƙe. Ɗan ɓoyayyen murmushi yayi daga can, a zahiri kam murya a dake kamar bai san komai ba ya ce, “Ina jinki uwar ɗakina mike faruwa? Waya taɓa min ke yaga fushin maza dan walle ina iya tada Abuja harda fadar shugaban ƙasa”. Murmushi tayi a karo na farko, shi yasa take matuƙar ji da Sille a rayuwarta, take kuma taɓa duk wanda taso hankalinta kwance dan shine garkuwar ta. Tasha sakashi ya nakasta mata duk wanda ya nuna mata yatsa a garin Abuja wallau namiji ko mace. Numfashi ta fesar mai raɗaɗi, kafin ta shiga faɗin, “Aiki nake so ai min akan jakar yarinyar can da tama AA ɗina asiri ta auresa”. “Angama uwar ɗaki. Ƙafafu za'a cire mata ko hannaye ko fuskar za'aima ɓalli-ɓalli irin wanda kikama Huznah take kowama”. Dariya Nuratu ta kwashe da shi, dan fuskar Huznah ɗin ce ta faɗo mata arai. Ta ce, “Kai Sille kai duniya ne, daɗina dakai baka da mantuwa sam. Ita wannan ai ta wuce ɓalli-ɓallin yarbawa, dan zunubinta mai yawan gaske ne. Zan turo maka abinda nake so ai mata. Kuma a satin bikina bayan salla zaka mata hakan, dan ina son aci shagalin bikina tana asibiti kwance rai a hannun ALLAH dan uban ubanta”. “An gama babbar yarinya, kune Abuja kune kuma masu riƙe da ƙasar gaba ɗaya, dan masu mulkinta a tafin hannunku suke tunda kullum tsaye suke a gabanku haihuwar tsoffinsu”. Sosai Nuratu ta sanya dariya harda kwanciya, cike da jin takaicinta ya ragu ta ce, “Zakaga saƙo a lalitarka Sille”. Daga haka sukai sallama ta yanke kiran.....
Daga can dariya Sille ya kece da ita, sai kuma ya ƙara gudun motarsa mara fasali ya cigaba da bin bayan su AA dake tafiya a hankali kamar wanda baya son isa gida. Tun fitowar su AA daga gida yake biye da su har nan gidan su Nuratu, akan idonsa komai ya faru sai dai baya jinsu kasancewar can nesa yay parking dan kar AA ya lura da shi. Dan tun Mamy na waya da Hajiya Turai cewar ga AA ɗin nan zuwa wajen Nuratu Haule ta tura masa saƙo, shine yazo ƙofa gidan ya tsaya, a zatonsa AA ɗin ne kawai zai fito, amma sai yaga kamar shi da wani ne a motar, shiyyasa ya fasa aikata abinda yay niyya ya shiga binsa a baya har kofar gidan su Nuratun dan yana son ganin shi da wanene. Bai samu ganin ba tunda basu fita a motar ba, sai yanzu da Nuratun ke sanar masa. Dan haka yaji wani kalar karsashin abinda yake shiryama ransa. Yau fa in har bai kashe AA da Maanal ba to sai ya raunata musu wani sashe na jikinsu kuwa....
Tofa munga idi🏃😳.
Sannu a hankali AA ya gangara gefen hanya yay parking, dan tunda suka baro gidan su Nuratu Maanal tai masa ɗif, tama ajiye tab ɗin ta kauda kanta gefe fiskarta a haɗe. Hannunta ɗaya dake ajiye a saman cinyarta ya kamo cikin nashi, ɗayan kuwa ta tallafe haɓarta tana kallon waje. Yanzu ɗin ma batako motsa ba balle ta juyo ta kallesa, hakan ya sake tabbatar masa fushi take yi. Lips ɗinsa ya ɗan ciza kaɗan, sai kuma ya matso kusa da ita gab yana sake rumtse hannun nata cikin hannayensa biyu gaba ɗaya. Da wata irin murya mai taushi da fitar sauti can ƙasan maƙoshi ya furta, “Besty!”. Ƙin amsawa tai yanzu ma, sai ya sake matso jikinta sosai, har buɗaɗɗen ƙirjinsa na kwanciya a kafaɗarta. Hannunsa ɗaya yasa ya kamo furkarta da shi, yana ƙoƙarin juyota inda yake. Amma sai ƙoƙarin hana hakan takeyi ita kuma. Bai barta ba har sai da ya juyo da itan a yanda yake so. Sai ta lumshe idanunta kawai. Guntun murmushin da ya tsaya masa a iya lips ya ɗan saki. Cikin sake sanyaya sauti yace, “Kin gaji?”. Juyar da fiskarta tai ƙoƙarin sake yi, ya riƙe da ƙyau. Tare da sake faɗin, “Barci ne?”. Shiru tayi nan ma. Ya ce, “Ni ne?”. Yanzu ma shiru. Yace “Oh kishi ne?”. Yanzu kam sai ta buɗe idannunta da suka ƙanƙance ta zabga masa harara. Sosai ya saki wani irin sassanyan murmushi daya daki zuciyarta. Babu shiri tai ƙasa da idanun nata tana tura baki. Murmushin ya sake saki, batare daya sake cewa komai ba ya jawota gaba ɗayanta ya rungume a jikinsa. Atare suka sauke ajiyar zuciya mai nauyin gaske, yayinda zukatan ke wani irin bugawa da sauri-sauri a tare. Sake ƙanƙameta yay, yana jin tamkar ya shigar da ita cikin jikin nasa ta narke kawai ta zama jininsa. Ita ɗin ta dabance a rayuwarsa, irin daban ɗin da baki yayi kaɗan a furtawa. Ya rayu da itane a irin rayuwar da baiyi da kowa ba, ya kusantu da ita a irin kusancin da bai samu da kowa ba. Ya shaƙu da ita a irin shaƙuwar da baiyi da kowa ba. Ita ɗin tamkar half ɗinsa ce a rayuwa. Itace abokiyarsa, abotar da bai taɓa yi da ɗan uwansa namiji ba. Dan zai iya cewa sai da suka rabu sannan yasan ya zauna tare da ɗan uwansa namiji har suyi mu'amula irin ta abota. A hakan ma kuma bai taɓa iya sakin jiki da kowa ba koda rabin kwatar yanda suka kasance shi da ita ne. Har garama Rafeeq, shima kuma dan ya kasance ɗan uwansa ne jininsa. Tsitstsinkewar da jinin jikinsa keyi sakamakon jin saukar ɗumin hawayenta a cikin ƙirjinsa ya sashi ɗagota daga jikin nasa, ƙoƙarin hana hakan takeyi, amma sai da yay nasarar ganin hawayen kuwa... “Besty kuka” ya faɗa zuciyarsa na wani kalar hanƙoro, kauda kanta tai yunƙurin yi, da ɗan hanzari ya riƙo fiskarta tata, bai wata-wata ba a karo na farko na rayuwarsa ya manna tausasan lips ɗinsa kan nata............✍️
_Wayyo ana cin amanar Abah. Jama'a kukawo ɗauki daga bashi aro yin rakkiya zai ci amanar Abah a titin gwamnati🤣🤣🤣🥱🏃🏃_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣8️⃣
______________
.......Sosai jinin jikinsa ya shiga wani irin harmutsawa har cikin brain ɗinsa, illahirin ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Domin al'amarin yazo masa da wani irin girma na gaske sakamakon abinda ya ɗauki tsawon shekaru yana dannewa da tsiya-tsiya. Tsaf ya kanainaye Hajiya Maanalu ta yanda bata da damar yin wani yinƙuri koda na motsa kanta ne. Sumbatarta yake cikin rikicewar yanayi da birkicewar tunani, sai dai hakan bai sakashi kasancewa a rashin nutsuwar da ALLAH ya azurtashi da ita ba. Akowane irin yanayi AA nutsatstsen mutum ne mai cike da kamala da dattako, nutsuwa akan komai halittar AA ce, sannan a cikin jinin jikinsa take. Matuƙar nisan kiwo ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa suka tafi ya manta da inda suke, dan kuwa tuni ya fara ƙoƙarin warware mata veil ɗin jikinta da take ta ƙoƙarin ganin ta riƙe ta hanashi hakan, amma yanda ya matseta a cikin kujerar hakan ya gagara, har ALLAH ya bashi nasarar yakicesa ya tura hannunsa a bayanta ya fara kici-kicin sauke zip ɗin bayan rigarta. Zuwa yanzu kam matuƙar ƙololuwar tashin hankali da birkicewar zuciya Maanal ta shiga. Dan tsabar tsoro da firgici zuciyarta neman buɗewa take gida biyu. Abu biyu ne ke maimaita kansu a ƙwaƙwalwarta a wannan gaɓar. Tsoro mai tsananin gaske, da flash back na wasu shekaru da suka shuɗe a rayuwarsu, sai dai tarihin irin wannan gaɓar bazai taɓa gogewa ba har abada dan tabone da ya riga yay tammbari a RAYUWARSU na har abada. A hankali ta saki masa wani irin kuka da kaima bayansa duka dan ta fahimci kamar ya manta itace fa Bestyn sa. Sai dai babu alamar yasan tanayi dan har yayi nasarar sauke zip ɗin yakai ga hook ɗin b ɗinta yana kici-kicin ciresu suma... A dai-dai nan kira ya shigo cikin wayarsa, kiran daya saka komai tsayawa cak harda fitar numfashinsu. Bawai kiran ne yay tasiri ba ga AA, a'a sautin dake tabbatar masa da kiran daga waye ne ya tasirantu a garesa matuƙa. Yafi sakan goma bai iya ya motsa ba balle janye jikinsa kafin ya zare lips ɗinsa akan nata a hankali, sai dai ya kasa raba jikinsa a nata saima sake ƙanƙameta da yay na fin sakan ashirin. A lokacin daya ja jikin nasa baya ya koma a nasa mazaunin jagwab ne ya bama Maanal damar cusa kanta a cikin ƙafafunta ta ƙanƙame jikinta waje guda gaba ɗaya. Jikin nata kuma sai wani kalar rawa yake na tsorata da shiga firgici ga kunya mai tsananin gaske da bata taɓa shiga tsakaninta da shi ba a rayuwarta. Zuciyarta kuwa babu abinda take sai rabewa da komawa ta tsuke kanta da kanta.... Kiran Abah daya sake shigo masa ne ya sashi ɗaukar ruwan dake gefen sa ya ɓalle murfin ya shiga kwankwaɗa duk da uban zafin da yake da shi. Shi kansa ma bai san tun yaushe ruwan yake a motar ba. Sai da yasha kusan rabi ya kife kansa a steering yana maida numfashi, a karo na uku kiran Abahn ya sake shigowa. Sai yanzu ne ya sami damar dai-daita kansa da ƙyar ya ɗaga wayar. “Ajwaad! Kana kallon ƙarfe nawa kuwa? Sai ɗaya tayi zaku dawo?”. Nutsatstsiyar muryar Abah ta daki cikin kunnensa. Idanunsa ya sake lumshewa ya buɗe da ƙyar, cikin ƙoƙarin ganin muryarsa ta kuma samun nutsuwa yay ɗan gyaran maƙoshi kafin ƙasa-ƙasa ya ce, “Gamu nan in sha ALLAHU Abah”. Shiru Abah yay sautin shaƙaƙƙiyar muryar ta AA na dakar masa zuciya. Dan duk wanda ya sanshi ya jisa a yanzu zai fahimci akwai lauje cikin naɗi. Amma kasancewarsa dattijon arziƙi sai cewa yay, “Okay kuyi sauri Oum ɗinku nason kwanciya” daga haka ya yanke kiran. Idanu AA ya sake lumshewa ya buɗe a karo na barkatai, shi kansa ganin ƙarfe nawa sai da yaji zuciyarsa ta girgiza. Harga ALLAH bai san sun jima haka ba, dan sai yake ganin ma kamar basu wuce minti talatin da fitowar ba. A karo na farko ya maida birkitattun idanunsa kan Maanal dake a duƙufe har yanzu. Lallausar fatar bayanta da hasken fitilar titin ta hasko ya zubama idanu, sai farar b ɗin jikinta datai matuƙar dacewa da fatar gata fes babu wani alamar datti a tare da ita. Numfashi ya sake ja a fisge, kafin cike da kasala ya kai hannu kan zip ɗin zai ja mata shi saman. Zaram ta miƙe zaune sosai idanunta share-share da hawaye. Shi dariya ma taso bashi ganin yanda ta wani zazzaro masa idanun alamar gargaɗi. Ƙasan zuciyarsa kuwa sai yaji kamar yana jin nauyinta shima musamman da wani gefe na zuciyar keta maimaita masa kalmar (Bestynka ce fa! Amma ka rufe ido ka aikata mata wannan abin kunyar har kana neman sakin layi) kauda tunanin yay gefe murmushin gefen baki na neman suɓuce masa. Amma sai ya daure a tausashe ya ce, “Yi haƙuri zip ɗin zan rufe miki, idan kuma kina son Abanki ya gane to a barshi a hakan kawai kinga na huta sai yace mu wuce sashen mu kawai ya salllama”. Ai da gudun tsiya ta duƙe alamar ya rufe matan. Yanzu kam saida ya murmusa kaɗan, kafin ya kai hannun yaja zip ɗin, yazo dai-dai jikin b ɗin ta ya dakata, hook ɗin yay ƙoƙarin maida mata dan duk ya ciresu saura ɗaya jal ya rage masa. Rumtse idanu kawai Maanal tayi da ƙarfin tsiya harya kammala ya ƙarasa ja mata zip ɗin. “Oya wanke fuska mu wuce, idan kuma a samu hotel anan kusa muƙarasa to”. A baima gama rufe baki ba ta ɓalle murfin motar, batare data kallesa ba ta warce goran ruwan hannunsa ta juya ta fara wanke fuskanta. Murmushi ya saki, tare da kai hannu ya shafa lallausar sumar kansa dake lashe kuɗaɗe da shima bai san adadi ba. Koda ta gama bata kallesa ba, ta yarda goran a ƙasa ta maida murfin ta rufo, sai kuma ta matsa jikin murfin ta maƙure. Komai baice mata ba, sai handkacheff ɗinsa mai ƙamshi ya miƙa mata kawai. Ɗan kallonsa tayi, suka ko haɗa ido. Da sauri ta janye nata tana fisgar handky ɗin kawai. Nanma murmushi yay yayima motar key suka cigaba da tafiya. Sai dai yanzu gudu yake sosai saɓanin ɗazun. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu a gaban ƙaton gate ɗin gidansu...
Koda suka nufi sashen Oum salaf-salaf Maanal ke tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Gani take kamar tana shiga kowa zai gane abinda ya faru a tsakaninsu. Musamman ma Abah da Oum. Ɗan tsayawa AA yayi, ita kuma kanta a ƙasa tunanin da take yi ya ɗauke dukkan hankalinta har tazo gab da shi bata sani ba. Sai da ta bugu da bayansa sannan ta ɗago da sauri, tayi baya kuma zata faɗi. Saurin juyowa yay tare da riƙota a lokaci guda, cike da kulawa ya jinginata da jikin bango. Muryarsa a sanyaye saboda halin da yake ciki ya riƙe fuskarta, ɗayan hannunta kuma a cikin nashi yana kallon fuskar ya ce, “Tunanin mi kikeyi ne haka?”. Wata irin kunyarsa take ji shima, dan haka tana ɗan ɗago idonta ta kallai ta maida su ta risinar, shiko nashi yawo kawai suke akan ƙyaƙyƙyawar fiskarta. Kanta kawai ta girgiza masa tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa yaƙi bata damar hakan. Hawayen da take riƙewane suka ziraro, ya waro lumsassun nasa sosai. “Ya arrahaman, miye abin kukan kuma?”. Cikin rawar murya ta ce, “Yanzu idan Oum da Abah suka gane fa”. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, a ransa yana faɗin, (Ashefa na manta yarinyar nan ɗanya ce, rinton aji yasata gama makaranta da wuri) a fili kam sai ya shafa fiskarta tare da faɗin, “Sai dai in kece kika so su gane”. Kallonsa ta ɗago tayi sosai a karo na farko, ya jinjina mata kansa yana ɗan laɓe baki da murmushin gefen baki a tare. Sai kuma ya shafa kanta cike da lallashi da tsokana ya rankwafa yana mai kai bakinsa saitin kunnenta da raɗa ya ce, “To ko mu tafi sashen mu kawai ki kwana acan, da asuba na miki alƙawarinkin rakoki da wuri kafin kowa ya tashi”. Tamkar wadda ya zaburar, ta sa hannayenta duka biyu a ƙitjinsa ta tura shi baya. Matsawar yayi yana dariya, ita ko ta kwasa da ɗan gudu cikin sashen Oum. Ko ganin Abah dake bayansu ma batayi ba sam. A falon kuwa akwai Oum, Mamy, Nibras, Saheeba da Fawzan harda babban Yaya a yanzu na zaune suna hira sai kawai ganinta sukai kamar walƙiya ta wuce hanyar upstairs. Da sauri Oum ta ce, “Munga idi Baby waya biyoki haka?”. “Oum fitsari-fitsari” ta faɗa batare data waiwayo ba. Dan tasan wannan dabararce kawai zata rabata da jin kunya. Saboda babu wanda zai kalleta bai fahimci wani abu ba a fuskar ta da lips ɗinta da yasha wahala a hannun wancan mutumin. Dariya Fawzan da Babban Yaya suka saki a lokaci guda, dan abinda Maanal ɗin tayi ya tuna musu da baya ne. Haka take yi idan suka dawo makaranta, sai ta riƙe fitsari tun daga can, mota na tsayawa ta fita a guje zuwa ciki tana faɗin, “Fitsari-fitsari”. Sai da Ammie ta zaneta wataran aka samu lafiya ta daina abin nan. Oum ma dai dariyar tayi, dan itama dai abinda yazo mata a rai kenan. Mamy da su Saheeba kam wani irin takaici ne ya ƙullesu, da kallon abinda Maanal ɗin tayi matsayin wani sabon bariki....
A waje kam, AA na gama dariyarsa dake fita a hankali ya juyo da nufin shigewa shima sukai ido huɗu da Abah daya harɗe hannaye a ƙirji ya tsaresa da idanu. Da sauri AA ya juya yana rumtse idanu da kai hannu ya shafa kansa, haƙoransa damtse da lips ɗinsa. A zuciyarsa faɗi yake (Ajwaad kaga takanka, tsohon nan ba raga maka zai yi ba....) katsewa zancen zucin nasa yay saboda taɓashi da akayi, juyowa yay kansa a ƙasa hannunsa a cikin sumar kansa, sai kuma ya ɗan buɗe ido ɗaya ya ɗan kalla Abahn. Abah da dariya ke cinsa a rai ya gimtse da ƙyar ya wani sake tsatsatsaresa da idanun. Sai AA ɗin cayay, “La Abah kai ne?”. “A'a bani bane aljani ne”. Abah ya bashi amsa cike da gatse. Bayansa AA ya koma ya tungumesa, ya tabbatar hakan shine rufun asirinsa dan wlhy tsaf Abah zai gane halin da yake ciki, musamman idanunsa da suka kaɗe. Cike da shagwaɓa ya kwantar da kansa a kafaɗar Aban yana faɗin, “Kaga ko Abah ALLAH ban lura time ya tafi haka ba. Na tuba! Na tuba! Na tuba!!”. Yanzu kam kasa daurewa Abah yay saida ya murmusa. Amma kasancewar AA na bayansa ba gani yay ba. Fuskar ya maida ya himtse a dake ya ce, “Ai na faɗa maka daman saina ƙara kwanakin suspension idan ka daɗe min da yarinya”. A sanyaye AA ya ce, “Abah holdup ne fa a hanyar”. “Na aljanu ko? Yo in ba na aljanu ba a daren nan wane huldup ne zai taru. Kaji tsoron ALLAH Ajwaad”. Ƙaramar dariya yanzu kam AA ɗin yayi da faɗin, “To Abah kawai abar kaza mana cikin gashinta. Kawai kayi murna mun dawo bamu ɓata ba ma”. Rankwashi Abah ya kai masa bisa kai, da sauri ya sakesa ya shige sashen Oum yana dariya. Shima Aban dariya yake yi da girgiza kansa. Wani irin farin ciki na ratsa masa zuciya. Rabon da yaga Ajwaad a irin wannan yanayin na farin cikin da har zai dinga wasa da dariya kai tsaye an ɗauki shekaru masu yawa. Ko tsokanarsa sukai sai dai yay guntun murmushi kawai yay shiru. Amma yau jiba yanda yake zuba masa surutu da shagwaɓa kai tsaye. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya nufi sashensa yana mai jerama UBANGIJI kirari da godiya.........✍️
_Abah namu, anya! Anya kuwa🥱. Bara dai nayi shiru😂👍_
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣9️⃣
______________
*_LADIES COLLECTION AND MORE_* 08169307477 SHIN MATSALARKI RAMA CE KO KINA SO KI GYARA BREAST DINKI NE? KINA SO KIYI HIPS HAJIYATA KIYI KYAU? KO KUWA KINA SO KI RAGE KIBARKI KO TUMBINKI? KINA SON INGANTATTUN MAGANIN MATA NA GARGANIJIYA? Kinason shape dinki ya fito kamar yanda kowace mace zatai alfaharin ganinki bare ma oga ko saurayinki da kansa, Shin kinason ko koma yar dagwas dinki batareda kashe kudin surgery ba kokuma hana kanki cima da dama da kikeso sbd kinason jikinki yayi daidai?
To matsalarki tazo karshe indai ingantattu sahihan maganin gargajiya ne da muka san inganci da gaskiyarsane,
MAZA KI ZIYARCI LADYS COLLECTION AND MORE ko ta waya ko ta asalin inda take ki tabbatar da Buqatarki tazo inda zata biya insha Allah,
LADY'S COLLECTION AND MORE
ANAN NE ZAKI SAMU DUKKAN ABUBUWAN DA KIKE SO KAMAR HAKA 👇🏻
Zumar kiba Zumar breast Zumar hips Zumar infection Zumar sliming Zumar sabon budurci Back to virgin Abayas Atamfa Less Hijabs Supplements Kitchen items and more Muna maraba da masu siyan Daya ko
08169307477
Address bayan gidan drugs katsina State
Kayan mu masu inganci ne sosae
Muna aika kayanmu a ko Ina ba tare da wata matsala ba🙏🏻🙏🏻 SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA💯
*********** ________________