Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 100

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 100

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 100: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 100. .......Da farko AA baya kulashi kamar…

2,871 words

.......Da farko AA baya kulashi kamar yanda baya kula kowa a makarantar. Yakan dai shiga aji da an gama lecture zai fito yazo wajen ya zauna har sai lokacin wata kuma. Sai yazo yini guda ya fita baiyi magana da kowa ba a school ɗin. Wani lokacin Babban Yaya da RK ke zuwa ɗaukarsa, wani lokcin kuma Abah da kansa kuma su suke kawosa. Kamanin da suke da juna yasa Zhang fahimtar suna da alaƙa ne, ya kuma ji sunan Maanal ne a bakin AA, dan in yana zaune shi kaɗai ɗin nan yakan rufe idanunsa yay shiru a kujerar wajen kamar mai barci amma zakaji sunan Maanal na fita masa a baki ko yace Besty. Tun Zhang na ɗaukar AA nada matsala ta brain shiyyasa yake sambatun kiran abinda bai san miye ma'anarsa ba har daga baya ya gane AA yana cikin depression ne. Dan yayi course na karantar halayyar ɗan adam. AA ya bashi tausayi, dan haka ya fara zama kusa da shi koda bazai kulashi ba, dan wani lokacin ma tashi yake ya bar masa wajen. Shi kuma bai taɓa ce masa komai ba tsawon lokaci har AA ɗin ya daina tashi a waje idan yaga Zhang yazo ya zauna. Yau da gobe sai yake zama suyi gaisuwa kawai har dai shakara taja. Bayan sanin sunan AA abu na biyu da Zhang yaso sani shine miye ma'anar Maanal, sannan waye Besty da yake jin AA yana yawan ambanta. “Maanal suna ne, kuma itace Besty”. Ya bashi amsa a taƙaice. Ya ce, “Mace ne ko namiji?”. Anan ma AA bai kawai komai ba ya ce, “Mace”. Tun daga nan Zhang ya fahimci matsalar AA. Bai sake masa tambaya akan hakan ba kuma har AA ɗin ya fahimci abinda Zhang ya karanta, sai kawai Maanal tazo masa a rai da zane-zanenta. Wannan shine tushe kuma asalin kafa alaƙarsu, kuma shine ya taimaka masa wajen kafa Maawad Company dan da taimakon Professor Zhang. Ya taɓa zuwa Nigeria lokacin buɗe MAWAAD COMPANY. Hakama zanen dake a companyn yasan na Maanal ne dan anan Chaina AA yasa aka zana shi yana siffanta musu ita. Har zuwa yanzu AA bai taɓa bashi any labari akan Maanal ba, iya abinda ya sani kenan, amma da kansa ya fahimci ita budurwarsa ce, amma basa tare. Sanin AA baya kula mata sam ganinsa da mace a yanzu da kuma kamanin da Maanal tai masa da wani hoto daya taɓa gani a wallet ɗin AA passport ne ma yasa shi saurin ganewa duk da bai tabbatar ba ya dai canka ne kawai.... Rungume AA Prof yay cike da tayashi farin cikin jin ga Maanal a matsayin matarsa, cike da tsokana ya ce, “Wannan karon dai tunda Maanal ta dawo ya kamata nasan labarinta”. A mamakinsa murmushi AA yayi, bai kuma musa ba, amma bai ce komai ba dai a bayyane. Maanal AA ta zubama ido, tana son fahimtar mi Prof ke son faɗa, sai dai yaƙi yarda ma su haɗa ido har suka isa wani aji bisa jagorancin Prof ɗin. Sun fara gabatar da lecture ta awa ɗaya. AA na kusa da Maanal dan haka ta dinga masa tambaya akan abinda bata gane ba dan anayi suna rubutawa ne. Bayani yake ɗan mata, wasu kuma yace ta bari su koma masauki dan ta samu damar fahimtar Prof ɗin. Daga school ɗin wani companyn Prof ya wace da su. Su AS suna a motar su kamar yanda suka zo, ita da shi a mota Mr Li na jansu, sai Prof a gefen driver. Hira suke da AA da Chaines, dan haka Maanal ba fahimta take ba. Sai ta ma maida hankalinta a bitar abinda suka koya yanzun nan. Wani katafaran companyn agogo sukazo. Sosai wajen ya birge kowannensu, suka cika da fatan suma wataran suga companyn su a haka. AA da Prof ne suka jagoranci zagayawa dasu, Prof na musu bayanin komai yanda zasu fahimta su kuma ƙaru da ilimi. Suna ko ƙaruwar, dan duk sun nutsu yanda ya kamata. Maanal sai take jin kamar ana wanke mata brain ne, wani sabon karsashi take ƙara ji game da zane-zane bama na agogon kawai ba. Anan sukaci lokaci sosai. Bayan sun fito suka maida Prof makaranta, su kuma suka nufi wani wajen. Isowarsu yasa kowa ya fahimci massallaci ne. Sosai nan ma ya birge su Maanal, musamman ma ita da AA ke mata bayanin komai. Hakan ya fahimtar da ita lallai AA yasan Shanghai sosai, kuma da alama yayi zaman garin ma. A karo na farko ta fara kwaɗayin son jin wani abu game dashi bayan rabuwarsu. Lokacin sallar zuhur ne, ita da CFO Faseelat suka nufi sashen mata, su kuma su AA sashen maza. Itama Faseelat ta taɓa zuwa massallacin dan ita wannan shine karo na biyu da akai irin tafiyar nan da ita a ƙarƙashin kamfani, sannan a karan kanta tazo Chaina har cikin Shanghai yawon buɗe ido da tsohon mijinta. Kuma duk ta ziyarci massalacin dan yanada tarihi mai girma a wajen musulman Chaina. Koda aka idar da salla zamansu sukai, dan AA ɗin yace suna nan har magrib. Alkur'ani Maanal ta ɗauka tai karatu, sai Faseelat ta shagala a kallonta, daga ƙarshe ta ɓingire barci itako Maanal nata karatunta har Asr. Ita ta tada Faseelat ɗin ta fita ta canja alwala, sun gabatar da la'asar sai suka fito domin shan iska kamar yanda Faseelat ɗin ta shawarci Maanal. Bata musa mata ba, dan koba komai matar zata iya haihuwar kamarta idan auren wuri tayi. A mamakinta suna fitowa sai suka hango AA can cikin wata rumfa zaune tare da wani. Kamar ance ya juyo suka haɗa ido. Wani ɗan sassanyan murmushi yay mata itama sai ta samu kanta da maida masa murtani. Da hannu yay mata alamar tazo. Sai ta ɗan juya ya kalla CFO. Gani tai itama hankalinta akan AA ɗin yake, duk da dai tana kallonsa ne cike da basarwa na manyam matan Abuja. Cikin ɗan kwantar da murya na girmamawa Maanal ta ce, “Bara naje yana kira”. Kamar wadda ta daburce CFO ta amsa mata a ɗan daburce. Ita dai Maanal batabi takanta ba tai gaba. A zuciyarta ko faɗi take (Tsohuwar kawai ƙwalelenki wannan kayan sai Maanal) tai gaba abinta. Tan a isowa wajen AA ya kamo hannunta ya zaunar a kusa da shi, kafin cikin girmamawa ya kalla dattijon mutumin da sai yanzu Maanal taga fuskarsa ya nuna masa Maanal ɗin da alamu suka tabbatar ya riga ya masa bayani a kanta. Ita kuma ya juya yana sanar mata cewar shi ɗin malaminsa Āhōng Chen a lokacin da yay zaman Chaina na tsawon shekara biyu. Murmushi Maanal tayi, cikin harshen turanci ta rissina ta gaida shi. Shi ko dattijo ƙyaƙyƙyawa cikakken bacine da hasken addinin Islama ke zageye da kwarjininsa ya amsa mata da kulawa shima da harshen Ingilishi. Ya ɗora da addu'a a garesu. Kan Maanal a ƙasa take amsawa, yayinda AA ke amsawa kai tsaye. Āhōng ya shiga yi musu nasiha da bama Maanal ɗin labarin zamantakewarsa da AA, a labarin Maanal ta fahimci Āhōng ya taimaki AA sosai a rayuwa, dan har lokacin da suka haɗu AA na cikin depression, shine ya ringa masa addu'oi da shawarwari ya jashi a jiki har ya bayyana masa damuwarsa, cikin ikon ALLAH kuma kafin yabar garin sai gashi abubuwa sun dai-daita masa. A cikin labarin yake basu shawarwarin gina ƙyaƙyƙyawar alaƙar rayuwar aure mai tsafta da danƙo. Sosai Maanal ta jinjina ilimin wannan bawa, ashe mu baƙaƙe musamman a Nigeria da muke ɗauka kamar mune kawai musulmai ashe namu wasa ne, dan da yawanmu bama ƙoƙarin neman ilimin addini akwai dai son addinin a tare damu wannan ta shaida kam... Kiran sallar magrib ne ya tashesu a wajen, ita ta koma sashensu na mata su kuma suka nufi na maza. Alwala tayo dan bataga CFO ba. Sai da ta shiga massalacin ta ganta a sahun gabansu, batayi magana ba tasha ruwa da dabinon da aka basu sannan aka gabatar da sallar magrib. Bayan an idar suka fito domin yin buɗa baki anan harabar massallacin da ake shiryawa gwanin birgewa. Ɓangaren mata daban na maza daban. A yanzu sun gaisa da mutane daban-daban dan matan basu da yawa sosai. Daga ita dai CFO ne kuma baƙar fata a wajen, duk da Faseelat farace tas-tas da alamar ma ana ƙarawa da skincare, amma hakan bazai hana a kirata baƙar fata ba. Itako dama baƙar ce, kuma Alhamdullah tana alfahari da fatan ta. Kaɗan ta tsakuri abincin, lokacin isha'i yayi suka koma cikin massallaci. Anyi sallar isha'i akai asham. Sun gaisa da mutane akai sallama kowa ya fito domin kama gabansa. Sosai rayuwa a massalacin taima Maanal daɗi, duk da wani gefe na zuciyarta na missing ƙasarta ta haihuwa da yanda azumi ke kasancewa musamman na farko da ake kaishi cike da ɗoki da buri. Waccan shekarar iyanzu suna a Jos ita da su Zeezah, acan sukai azumin sai da yakai tsakkiya suka dawo Kaduna. Sai ta ƙara jin wani kalar kewar mutanen gida... “Mi matar Ajwaad ke tunani? Bayan gashi a gefenta”. A bazata taji saukar lallausar muryarsa a cikin kunneta, fiskarta da murmushi ta juyo, yana daga bayanta ne ya ɗan duƙo, sai ta samu kanta da kai yatsa ta ɗan dungure masa kai da faɗin, “Miyasa mijin Maanal ya cika sa ido ne?”. Murmushi yayi mai faɗi da ƙyatarwa, ya miƙa sosai tare da kama yatsar nata cikin hannunsa. Sosai abinda ta faɗa ya wani ratsa masa zuciya da cikata da farin ciki. A hankali ya jawota gabansa, batare da tunanin komai ba balle kunyar mutanen dake ɗan kai-kawo ya rungumeta, dan su AS har sun wuce wajen mota. A hankali ta kumshe idanunta, shima haka, suka saki ajiyar zuciya a tare zukatansu na sauka a kankali daga nauyin da su kayi. Cikin ƙaramin sauti mai marmashe zuciya AA ya furta, “Barka da shan ruwa ZUCIYAR AJWAAD”. Wani irin zuuu Manaal taji a jikinta. Sosai kalamansa na ƙarshe suka mata nauyi. Akwai shaƙuwa mai girma tsakanin da AA, irin shaƙuwar da zata iya rantsewa bata taɓa yi da wani ba. Ɗaya baya ƙaunar ganin ɗaya a damuwa, hatta da ciwo sun sha yi a tare. Abubuwa da yawan gaske nasu a tare ne. Amma basu taɓa danganta al'amarinsu da wata kalma ta soyayya ba koda ƙanƙanuwa. Sai dai suji a bakin mutane na ambatawa amma basu da kansu ba. Zata iya cewa wannan itace kalma ta biyu a rayuwarta da taji daga bakinsa da zata iya kamantata da hakan bayan kalaman ɗazun da asubahi, amma sai ta basar, kamar yanda suka saba ta ɗago fuskarta da dariya tana kai masa mintsini.... Da sauri ya ce, “Ouch! Besty wai a ina kika koyo muguntar nan ne?”. Dariya tayi tana ɗan tafiya da baya, girarta a ɗan ɗage ta ce, “Da zafi ne?”. Hararta yay da ɗan haɗe fuska ya ce, “Kina son sani?”. Gira ta ɗaga masa. Ya ce, “Okay bari sai munje makwanci zan banbance miki”.. Duk da gabanta ya faɗi sai ta sanya ƴar dariya, “Besty ai nasan kai bawan ALLAH ne baka faɗa cikin azumi”. Yanzun kam dariya sosai tazo masa amma ya daure baiyi ba ya saki murmushi tare da takawa ya riƙe hannunta daga ƴar tafiyar da take da bayaya. Tafiya suka fara a tare cike da nutsuwa har zuwa wajen motarsu, Mr Li ya buɗe musu suka shiga. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya, sai kuma suka kalla juna. Murmushi sukayi a tare, gira a ɗan ɗage AA ya ce, “Yaya kin gaji ne?”. “Sosai ma, burina kawai nakai kwance yanzu. Gashi kuma ina son duba lecture ɗin yau”. Kafaɗarsa ya ɗan matso mata alamar ta kwanta. Sai da ta kallesa sukama juna murmushi mai sanyi sannan a hankali takai kwance a kafaɗar tana sauke ajiyar zuciya acan cikin ƙirjinta. Sai kuma ta gyara zamanta tana lumshe ido. Baice komai ba illa ɗan kallonta da yay ya ɗauke idonsa. Cikin ƙanƙanin lokaci Maanal tai barci, har bata san sunzo sun tsaya gidan abincin ranar ba Mr Li ya fita yay musu takeaway dan yasan zuwa anjima dole zasu buƙaci abinci........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣2️⃣

______________

........Lokacin da suka iso hotel su AS tuni sun shige, AA ya kalla Maanal dake barci sosai, sai yaji ta bashi tausayi. Ita da ya sani da ragwantar azumi, koda yake yanzu an girma maybe ta daina tunda yaga yau batai raki ba, amma a da duk randa aka kai azumin farko tofa Maanal da kuka take kaishi. Murmushi yayi komai na dawo masa a zuciya kamar film. Baya son takurawa Mr Li, da zasu cigaba da zama a motar ne harta tashi, to yakamata shima a bashi nashi Freedom ɗin yaje ga iyalansa. A hankali AA ya kamata ya kwantar kamar wata ƙwai, kafin ya fita a motar, ta side ɗin da take ya zagaya, ya ɗan duƙo cikin dabara ya kamata tare da juya bayansa ya ɗaurata, a duƙen ya miƙe tana a bayansa har tana gyara kwanci ya miƙe tsaye da ƙyau riƙe da ƙafafunta, ita ko ta sake sarƙe hannayenta a wuyansa ta lafe. Da sauri Mr Li ya tattaro musu kayayyakinsu ya biyosu da shi, a haka ya shiga da ita cikin hotel ɗin, rayuwa ce irin ta ba ruwan wani da wani babu wanda suka zamewa abin kallo, kowa harkar gabansa yake. A haka ya shiga elevator da ita. A bazata ya fito daga elevator ɗin yaci karo da CMO da HOD da alama fita zasuyi, kicin-kicin ya sake yi da fuska, suma duk sai sukai ƙasa da kawuna like bama su ganshi ba. Ko kallonsu baiyi ba balle ya nuna ya ma sansu yay wucewarsa Mr Li biye da shi. Aiko suka juya suna kallonsu cike da mamaki. Eh lallai mace dabance, mace sarauniya ce, mace duniya ce. In ba hakana CEO ne goye da mace, kai lallai babbar magana, al'amarin kamar wani film. Oho AA baima san anai ba, dan yayi gaba kaɗan can ma ya hango CFO tana waya, ɗauke kansa yay dan ta tsaya tsai daga maganar da take kamar wadda ta suma. Shi ko ya saka card ƙofa ta buɗe yay ciki. Mr Li ya saka masa kayan ta ciki yana daga waje ya juya, shi kuma ya saka ƙafa ya rufe ƙofar abinsa sannan ya nufi gadon ya sauke Maanal dake barci bil haƙƙi alamar ta gaji sosai. Takalma ta ya zare mata, ya warware veil ɗin ma ya cire.. Sai ta sauke ajiyar zuciya ta gyara kwanciya. Tsai ya ɗanyi yana kallonta na kusan minti ɗaya, kafin ya sauke ajiyar numfashi ya sake kai hannu ya fara buɗe botiran rigarta, ya ɓalle fin biyar kamar wadda aka ankarar ta farka, wani kalar cafke masa hannu tayi tana buɗe idanu da ƙyau irin na (lafiya kuwa?) shima sai ya zuba mata nasa a wani kalar kasalance, sai kuma ya shiga jansu ƙasa ya sauke akan hannayen nasu, ita kuma sai tai tunanin jikinta yake kallo ta inda ya buɗe botiran, hannun ta saki da sauri ta kama rigar ta cikuykuye a cikin hannunta ta rufe wajen ruf.... Sai kawai ya samu kansa da sakin wani kalar lalataccen murmushi. Baki ta tura irin na jin haushin dan mi zai mata dariya. Fahimtar hakan sai ya sake sakin murmushin tare da matsar da fuskarsa gab da tata suna busama juna numfashi. “Idan abinda kike tsoron zanyi ai idanuna a cikin naki zanyi ba kina barci ba fa, dan haka karki damu kanki saura ƙiris”. Fuskarsa ta ɗan ture ta juya masa baya, sai ya sake yin murmushi ya leƙa fuskar ta bayanta. Cike da son ƙureta ya ce, “Please ki tayani wanka mana na gaji sosai My EverBloom!”. Gaba ɗaya ji Maanal tai tama daburce ta rasa ina zata saka kanta. Yanda tai ɗin ya matuƙar bashi dariya, tsabar son ya sake ƙureta sai ya riƙota yana faɗin, “Okay! Okay shike nan na haƙura har sai randa aka kawo min ke har ɗakin barcina a lulluɓe like kowace sarauniyar amarya, ki kasance cikin shiri dan babu batun ɗaga ƙafa ranar fa, zan zama kurma ne, sannan makaho na haƙiƙa...” Ita dai tuni ta cusa kanta a tsakiyar ƙafafunta ne tana jin kamar gadon ya rabe biyu kawai ta shige ciki ya maida ya rufe da ita. Shima fahimtar ya gama kaita maƙura ya sashi duƙawa ya sumbaci wuyanta ta gefen kunnenta, wani kalar girgiza jikinta yayi dan har tsakiyar kai taji sumbar nan, sai kawai ya miƙewa yana ƴar dariyan shaƙiyanci yabar wajen. Kaya ya fara cirewa dan wanka shi yafi buƙata fiye da komai a yanzu. Ita dai tana rufe a wajen har sai da ya shige sannan ta koma ta buɗe iya fuskarta tabar jikin kawai a rufe, sai dai ta wani ɓata fuska abin dariya.....

___________★

Readers Also Read