Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 99
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 99: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 99. Zamansa a kusa da ita bayan ya kammala…
2,603 words
Zamansa a kusa da ita bayan ya kammala wayar ya sakata ɗagowa ta kallesa, gira ɗaya ya ɗan ɗage mata yana wani ƙanƙance idanu. Idannunta ta kawar, tana ɗan tura baki gaba. Murmushi ya ɗanyi tare da ɗan taɓe baki, sai kuma cikin taushin sauti ya ce, “Kinga Besty zo kiji wata magana”. Shiru kamar bazata tashi ba, sai kuma ta yunƙura a hankali zata zauna. Kamota yay ya kwantar a jikinsa, sai taji tsigar jikinta na tashi, ga wata kunya mai kassara jiki. Agogo ta kalla, gudun karsu shiga lokacin gama sahur. Tsaf ya lura da yanayin nata, sai yay ɗan murmushi a zuciyarsa. A fili ya furta, “Kwantar da hankalinki, awa kusan ɗaya ce damu gaba”. Hannu tasa ta rufe fuskarta kawai. Shi ya san tun Maanal na yarinya ta musamman ce, hakan yasa ɗabi'unta da yawa suke sakashi kallon mata da yawa a basu iya komai ba. Ganin yanda ta rufe ido ya sashi kai yatsarsa manuniya a kansu ya fara sosa mata samansu. Dole ta buɗe idanun a hankali, suna shiga cikin nashi tai ƙoƙarin janye wa amma sai ya hana hakan. Kaɗan yaja mata hanci tare da faɗin, “Yarinyar nan ke da kunyar nan taki ko......” Kauda fuskarta tai tana murmushi. Shima sai ya ɗan murmusa hannunsa riƙe da fuskrta cikin raɗa ya furta, “Na tambayeki wani abu?”. Kanta ta jinjina masa kawai. “Mi doctor yace miki jiya a asibiti?”. Ai da gudu tai ƙoƙarin tashi a jikinsa amma ya riƙeta, magana tai ƙoƙarin yi kamar zatai kuka yace, “Relax! Tunda baƙya son na sani. Amma kin yarda ni na faɗa miki wata magana?”. Shiru kamar bazata amsa shi ba sai kuma ta jinjina kai. Hannunta da take matsewa waje guda ya kamo cikin nashi, cike da lallashi da son kwantarta mata da hankali ya cigaba da magana da sanyin murya da tausasa lafazi. “Besty! Ina son ki kwantar da hankalinki tsakanina dake. Nasan akwai abubuwa da yawa da kike buƙatar ji daga gareni amma ban faɗa ba, nima akwai wanda nake buƙatar son ji daga gareki amma ban tambaya ba. Lokaci nake jira, akwai gaɓar da zamu zo wannan matakin ne in sha ALLAHU. Abu na biyu nasan a baya bamu taɓa kallon kammu a wannan matsayin ba, ko nace daga ɓangarenki, dan ni dai a gareni wannan shine burin rayuwata na farko daya fara ginuwa tun ma ban fahimci wanene ni ba.....” Karo na farko Maanal ta kallesa, wani irin lumshe mata idanu yayi ya sake buɗewa. “Kada kiyi mamaki, kada kuma ki tambaya, kada ki damu da son sani game da jin hakan domin ba yanzu ba. Abinda nake so daga gareki a yanzu kawai haɗin kai, kwantar da hankali, ki kwantar da hankalinki dani, bazan taɓa aikata wani abu a gareki ba bada yardarki ba Maanal! Duk yanda zan tsinta kaina a matsuwa ta buƙatar jiki kota rayuwa ki sani ke kinfi hakan muhimmancin da bazan fifitasu a kanki ba. Domin su na wuccin gadi ne, zasu iya samuwa su wuce sai wani lokaci a buƙace su, ke kuma ta har abada ce, akoda yaushe kece kaɗai Ajwaad, kece kaɗai nake iya buɗema zuciyata, ke ce kaɗai nake iya buɗema damuwa ta, kece ƙawa! Kece ƙanwa! Kece aboki! Kece aminiya! Kece abokiyar dariya! Kece abokiyar magana! Kece abokiyar kuka! Kece abokiyar karatu! Kece abokiyar sirri! Ko duk kin manta? Kin manta haka saboda nisa da ratar da ƙaddara ta bamu ne? Kin mance haka saboda jarabawa da UBANGIJINMU yay mana dan yaga ƙarfin imaninmu? Kin manta saboda a yanzu tunaninki na baki komawarki mace matancin naki ne kawai zan iya buƙata? Noo Manaal! Noooo! Wannan Ajwaad ɗin na nan a naki tun na waccan rayuwar, bakuma zai taɓa canjawa daga hakan ba domin a matsayin da dama na gina kenan tun fil azal. Ki sani tubalin ginin da kayan ginin an samar da su ne daga himmar aiki mai ƙarfafa ƙwanji tun daga ƙarƙashin zuciya da bigire na fitowar TSIRRAI daga HUKUNCIN UBANGIJI. Wallahil azim inda zaki ce Ajwaad bazan taɓa baka kaina ba mu rayu a haka yanda muke ni mai riƙe miki wannan ALƘAWARIN ne dan ba wannan nake kallo ake ɗin ba, ke! Ke! Ɗin nake kallo a matsayin Ke! Kawai Maanal.....”✍️
Hummmmmmm
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣0️⃣
______________
.........Gaba ɗaya sai Maanal taji ta sake rikicewa, hawaye kam gudu suke wasu na bin wasu dan sunanta kai tsaye a bakin Ajwaad babbar magana ce, jikinta na wani irin tsuma zuciyarta na rawa da sake rauni. Bata san sanda ta zabura ba lokacin da AA ya cigaba da faɗin, “Maanal! Har yanzu ke yarinya ce, shekarunki basu kai na fara banbance ƙarfin ikon zuciya dana ƙwaƙwalwa ba. Amma ina son daga yau, daga yanzu kisa a ranki, Ajwaad Aliyu Abubakar zai iya FANSARKI da kansa a kowanne irin TARNAƘI. Sannan zai iya MALLAKA miki kansa da komansa domin biyan buƙatar ki. Zai iya ƙwata daga hannun wani domin FARIN CIKIN KI. Zai iya bayarwa ga wani domin MUTUNCINKI. Zai iya sadaukarwa ga DUNIYA domin ɗaga DARAJAR KI. Koda kuwa kina kallon komansa a matsayin AJIYA A DUHU bazai damu ba Maanal, bazai karaya ba Maanal. Domin rauninki ne kawai ke iya karya lagon Ajwaad a bayyane da raunana shi har ya iya kaiwa ƙasa wanwar. Na rantse miki da ALLAH babu abinda ke iya dukan wannan zuciyar ya sata risina da sallamawa akan komai sai ke Maanal.....” yay maganar yana ɗaura hannunta a dai-dai saitin zuciyarsa, kafin a wani irin ƙaramin sauti ya sake faɗin, “Manaal...” ji tai bazata iya jurewa ba, dan sautin kukanta har ya fara bayyana waje, da sauri takai hannunta ta dafe masa baki jikinta na rawa sosai, idannunta a jikin nashi tana mai girgiza masa kai. Sosai nasa idanun shima sukai wani irin kaɗewa suka koma jaaa matuƙa, ƙyallinsu ya sake zama mai ƙyalli sosai tamkar wanda hawaye suka tararma a ciki. Ji yake tamkar ya tsaga jikinsa ya sakata kawai a ciki duk inda yaje akace ina Maanal yace tana a cikin jikina. Ganin yanda idannunta ke wani tafiya luuu-luuu kamar zata suma sai kawai ya jawota gaba ɗaya a jikin nasa ya rungume tsam-tsam hawayenta na sauka masa a kan ƙirji. Sun fi minti biyar a haka kafin ya kai lips ɗinsa kan kunnenta ya sumbata, ta ƙanƙame jikinta dan har tsakkiyar kai taji al'amarin, cike da raɗa ya furta, “Shagwaɓaɓɓiyar AA minti biyu fa doctor yace ki ringa rungumeni kawai in ba haka ba zan iya BOƘAREWA a tafi step 2 kin san ba mata bane kawai boƙararru”. Ƙaramin ƙulli (dundu) ta masa a baya tana ƙwace jikinta fuskarta da murmushi. Siririyar dariya ya saki shima yana biyota zai sake kamowa ta zille. Ganin ya tsare ko ina cikin shaƙƙaƙiyar muryarta irin ta mai kuka batare data kallesa ba ta ce, “Kasan dai na iya duka a ciki ko”. Yanda tai maganar tana dunƙule hannu kamar zata kawo naushin ya saka shi matsawa baya yana waro idanu. Sai kawai ta wani ƙyaƙyƙyale da dariya tana faɗin, “Matsoraci kawai Oum's boy”. Takai kwance tana masa gwalo. “Kinci bashi”. Ya faɗa yana ɗaukar wayarsa da kira ke shigowa. Ganin Āhōng Chen (Sheikh Chen) ne yasa shi miƙewa a wajen ya koma wajen kujeru. Ita kuma sai kawai ta kwanta ta zuba masa idanu. Wani irin dawo mata kalamansa keyi a zuciya, so take ta fasa komai dalla-dalla amma nauyinsu yay mata yawa. Sai ma wani irin barci mai ɗan karan daɗi daya fara fisgarta. Kafin kace mi ta lula a cikinsa cike da mafarkin AA. Bayan kammala wayar yazo ya tasheta dan lokacin sallar asuba yayi....
_________★
Huznah dai azumi ya gagara kaiwa yamma, dan anayin azhar tiɓis ta zama. Tsoron kar Sageer ya dawo batai komai ba ta miƙe cike da lallaɓawa tai gyaran gidan ita da Khadijah ƙanwarsa da tazo tayata aikin, sannan ta fara hada-hadar ɗaura girki dan ya tabbatar mata yau da ɗan yawa zatai abincin akai gidansu shiyyasa ma ya turo mata Khadijah, dan yana son iyayensa suyi buɗa bakin farko da abincin gidansa, baya son ta kwafsa shiyyasa yace Khadijahn tazo tunda har yanzu hannunta bai wani gama faɗawa da girkin ba. Haka ta lallaɓa sukai komai, abu na ƙarshe data bari yin farfesun kifi da yace yana so duk da bata son ko sunan kifin a kira. Ca tai Khadijah ta ɗaura ita bara taje tai wanka. Khadijah bata kawo komai a ranta ba tace to ganin komai an tanada haɗawane kawai. Abu kamar almara tayo wanka tana shiryawa kifin da Khadijah tasa a wuta ya tafaso sai ga ƙamshinsa har cikin bedroom ɗin da Huznah take. Wani kalar harmutsawa cikinta yayi, kafin kace mi tai bayi a guje sai amai. Kakarin aman nata Khadijah ta jiyo ta shigo a guje. Sosai tsoro ya kamata ganin yanda Huznah ke amai, gashi sai magiya take mata wai taje ta kashe gas ta fita da kifin. Ina ita Khadijah bata fahimta ba, sai da Huznah ta gama birkicewa da galabaita sannan tai hankalin kiran yayanta a waya ta sanar masa. Mamaki ne ya kamashi jin wai Huznah na amai saboda ƙamshin kifi, dama dai shirin tahowa gida yake, dan haka ya taho, ya sameta kwance duk ta saki, ya shiga mata sannu da tambayarta mike damunta. Idannunta cike da hawaye tace, “Dan ALLAH yaya Sageer bana son kifin can kace ta sauke shi”. Kallonta kawai ya tsaya yi, sai kuma ya juya ya fita zuwa kitchen. Ya samu Khadijah na kwashe kifin, sai kawai baice komai ba ya fice. Babu jimawa ya dawo tare da Nurse ɗin yarinyar dake makwaftan su, dan yayarta ce ta duba Huznah ranar first night ɗinsu yanzu kuma yayar na asibiti sai ƙanwar. Tambayoyi ta fara ma Huznah ɗin dake wani yatsine-yatsinen fuska, ita dai yarinyar bata kulata ba dan suna ganin irinsu Huznah har ma wanda suka fisu a iya iskanci. Dama kuma an cika anguwa da labarin Huznah bata da mutunci idan aka shigo gidan taga talakawa ne tata musu yatsine-yatsine. Fitsari ta buƙaci Huznah zuwa tayi, kamar bazata tashi ba sai da Sageer yay mata magana. Koda taje tayo sai ta canja wajan kwanciya. Ita dai yarinya batare komai ba ta bama Sageer tsinken gwajin ciki ta faɗa masa yanda za'ai. Bai wani je ko'ina ba anan gabanta yayi komai. Aiko a farko ma ya nuna akwai ciki. Wani ta ƙara bashi, shima dai haka, ta bashi na uku still shima haka. Ta ce, “Congratuletion Yaya Sageer Auntynmu na da ciki, ya kamata kuje asibiti gobe dan asan kwanakinsa, ga wannan tasha zai taimaka mata daina jin aman. Idan da hali kuma a daina dafa kifin da bata son”. Sosai Sageer da fuskarsa tai matuƙar washewa tun ambatawar Zubaidah cewar Huznah nada ciki murmushinsa ya sake faɗaɗa. Godiya ya shiga yima UBANGIJI, sai kuma ya shiga sanyama Zubaidah albarka itama. Yarinyar nada hankali da nutsuwa gata bata da yawan magana. Sosai ake yabama tarbiyyar yaran gidansu a anguwar, ga girmama na gaba dan duk wanda ya girmesu a Yaya yake ko Aunty a anguwa ko Baba ko Uncle. Koda ya bata kuɗi ƙin amsa tayi... Huznah kam tunda Zubaidah ta ambata kalmar ciki tai sumar kwance, so take brain nata ta banbance mata wake da ciki amma kamar bata wani fahimta da ƙyau saboda ruɗani da shiga gigita na bazata. A haka Sageer ya dawo ya wani rungumeta yana sake jera godiya ga UBANGIJI. Hakama Khadijah da Zubaidah ta sanar mata kamar an jehota ta shigo ɗakin, dole Sageer ya saki Huznah. Farin ciki suke shi da ƙanwarsa, yayinda ita kuma ta shiga halin ɗimuwa da gigita. Ina itace za'ace ma tana da ciki, cikin ma na Sageer ba AA ba. Wannan abune da bazai taɓa yiwuwa ba, dole wannan cikin yabi rariya kuwa. Hakan alwashinta ne dan bazata taɓa yarda ta haihu da Sageer ba koma mizai faru sai dai ya faru.......
Tofa babbar magana, wai ɗan sanda yaga gawar soja🏃🏃🤣
_________★
Tsaf Manaal da AA sukai shirin fita. Duk da Maanal bata so tashi a barcin data koma bayan sallar asuba ba dan ya mata daɗi sosai. Suna fitowa suka ci karo da su AS da rabon su dasu tun randa suka zo. Gaba ɗayansu sun shiga gaishesu da girmamawa ne da tambayar jikin AA dan jiya Mr Li ke sanar musu dalilin fara fita abinda ya kawo su. Da yake anan ba kamar Nigeria ba haka suka haƙura basu je dubashi ba duk da sun so hakan. Maanal nason yima Yaqub magana tana tsoron fushin AA. Sai kuma yanda CFO Faseelat take dama-dama da AA ya ɗan tsayama Maanal a rai. Duk da tun a gida kai tun ma farkon zuwanta MAWAAD ta so fahimtar wani yanayi daga CFO ɗin game da AA. Sai kuma dai ta ƙaryata zuciyarta dan CFO Faseelat A Zakaria ba yarinya bace ba, a ƙalla zatai sa'ar Fawzan koma ta ɗan girmesa kaɗan. A tsakanin Fawzan da AA ma kuwa akwai ƴar tazarar haihuwa kamar yanda Oum take faɗa. Kawai sai Maanal taji ita abun ma ya bata dariya, batare data maida hankali ba ta taɓe baki kawai ta cigaba da istigafarinta a zuciya dan shine mai fishsheta da azuminta a baki. Sun isa *Nicolas G. Hayek Watchmaking school* da zasu samu horaswar. Tarba suka samu ta musamman ga matashin professor Zhang Kuma abokin karatu ga AA. Dan cike da tsokana ya ɗan kalla Maanal dake a sashen AA sannan ya ɗan kalla AA ɗin yana masa wani salon tambaya da ido. Ɗan kallon Maanal ɗin shima AA yay, sai kuma yay murmushi... Prof.... ya ce, “Wow Maanal right?”. Ƙaramar harara AA ya sakar masa, Prof.. ya sanya dariya. Hakama AA ɗin murmushi yake yi. Bayan AA ya gama doguwar jiyyar abinda ta faru da ƙyar su Abah suka samu ya koma makaranta a wancan lokacin, dan likitansa ya tabbatar musu hakan ne zai taimaka ma brain ɗinsa samun daidaito da heart ɗinsa datai breaking. Ga kuma matsanancin depression da yake ciki a lokacin. Haka kuwa akai AA ya zana SSCE ta online abinka da ƴaƴan manya, babu jimawa sakamako ya fita aka shiga nema masa admission, cikin sa'a aka samu kasancewar Abah matsayin ambassador. Sannan takardunsa sunyi ƙyau sosai dan ya samu result mai ƙyau sosai. A jami'ar ya haɗu da Zhang, a lokacin shi yana Masters ɗinsa ne, inda AA ke zuwa ya zauna ya ware kansa nan suka haɗu da Zhang, tun yana tsayawa yayta kallonsa daga nesa dan shi yanayin fatar AA ɗin ke ɗaukar masa hankali har takai ya fara ɗan masa magana.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣1️⃣
______________