Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 102

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 102

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 102: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 102. A yau ɗaukacin musulmai suka kai…

3,199 words

A yau ɗaukacin musulmai suka kai azumi na tara-tara a wasu ƙasashe, wasu kuma na ƙoƙarin ƙarisa kaiwa irinsu Maanal dake a Chaina. Yau gaba ɗaya a busy suke, dan sunata shirin komawa ƙasarsu ta haihuwa. Babu abinda Maanal zatace da UBANGIJI sai godiya a kwanakin nan, domin kuwa ta ƙaru da abubuwa masu yawan gaske. Irin siyayyar da AA yayi mata har tsoro abin ya bata, wai iyaka ma wanda ta gani kenan. Dan bata sani ba ma ya tura wasu kayan Nigeria kusan kwana uku kenan. Duk da daɗi da Chaina tai mata hakan bai hanata jin ɗokin komawarsu gida ba. Dan tayi kewar kowa da Kowa. Duk da zuwa yanzu hatta su Ammie duk tana waya da su...

A ɓangaren AA kuwa a matuƙar takure da azabtuwa yay kwanakin nan. Shi kaɗai yasan ɗunbin yaƙin da yay da kansa wajen kauda ido ga Maanal a tsakanin nan. Sai kuma azumi daya sake taimakawa ya zame masa garkuwa. Rashin walwalarsa a bayyane take, sai dai hakan bai hanashi bama Maanal kulawa mai tsayawa a rai da zuciya ba wadda shi kansa ya fahimci ta sakata ƙara zama mai laushi, shaƙuwarsu kuma nata dawowa kamar da duk da bawai tana sakin jikinta bane kamar da ɗin yanda ya kamata. Dan wataran idan ta miskile masa ma har mamakinta yake. Badan yana kewar iyayensa ba da ita kaɗai zai tura Nigeria shi kam sai bayan salla ya koma dai-dai sanda Abah ɗin ya yarda zai bashi matarsa. Haka dai ya daure yay musu shiri yanda ya kamata. A gajiye sosai suka koma hotel ɗinsu, dan sunje ƙarasa wasu yan abubuwa ne da suka rage. Kasancewar ya tsaya suna magana da CMO a waje ita kaɗai ta shige ɗaki, gudu-gudu ta hau zame kaya da planing ɗin shiga wanka kafin ya shigo. Dan harta fiddo kayan da zata canja a bayin kamar yanda take yi. A bazata kawai ta ɗaga riga zata cire bawan ALLAH ya shigo. Daburcewa tayi gaba ɗaya, ga rigar taƙi fita hasalima ta maƙale mata ɗan kunne dan atamface ga style ɗin ɗinkin wuyan irin ƙaramin nan ne. Faɗin rigar kuma yasa ba'a saka mata zip ba. Cak AA yaja ya tsaya ƙirjinsa na wani dokawa da sauri-sauri. Ji yay kamar ya juya ya koma, sai dai kuma yanda take kicin-kicin yasan zata iya buguwa da wani abun. Gashi ta gagara cire rigar, jikinta kuwa har rawa yake. Kamar wanda aka saluɓewa kuzari ya shiga takawa a slowly, yana zuwa dai-dai gabanta ya tsaya, dai-dai ta ɗan sake duƙewa ta ɗago cikin nasara ta zare kunneta ɗaya daya riƙe, motsawar da zatai kawai tai karo da mutum. Cak ta tsaya zuciyarta na mata gudu a ƙirji, sai taji hawaye ma sun cika mata ido. Dan tasan ya ma riga ya gama kalleta daga ita sai b&p tunda tayi sama da rigar ne gaba ɗaya. A bazata kuwa, matuƙar bazata taji saukar lallausan hannunsa a saman ƙugunta, kafin a hankali ya shiga matsar da shi har zuwa gadon bayanta ya zagayosa ta ɗayan gefen cikinta. Matsota yay ta manne da jikinsa. Ji tai ta ƙara daburcewa, shi kansa zuciyarsa tsitstsinkewa take, dan wannan shine na farko da yake ganinta a haka. Koma yace yake ganin mace a haka a gabansa. Tuni idanun ƴan maza sun juye cikin ƙanƙanin lokaci, sai faman taunar lips yake tamkar zai hudasu da haƙora. Hannunta da take ƙoƙarin turesa ya riƙe, sai ya maida shi baya ya riƙe a hannunsa dake gadon bayanta. Ɗayan kuma ya shiga zare mata rigar jinin jikinsa na narkewa. Rigar na gama fita Maanal tai ƙoƙarin duƙewa, cak ya kamota gaba ɗaya ya tsayar akan ƙafafunta, kafin ya fara tafiya da ita sannu-sannu suka dangane da bango. Bata daina ƙoƙarin turesa ba, ga jikinta na rawa hawaye na gangarowa, sai dai ta kasa magana. Jin ya manneta da bango sai kawai ta kife a jikinsa dan bata da wani zaɓin daya wuce yin hakan. Hawayenta yaji suna sauka a ƙirjinsa duk da akwai riga a tare da shi. Sake rikicewa gangar jikinsa tayi, sai ya dinga jin kamar bazai iya riƙe kansa ba yau. Kamar bazai iya haƙuri da juriyar daya ɗauka ɗammara ba. Kamar bazai iya riƙe alƙawarin Abah ba. Tabbas bazai iya ba, dan kuwa cikin yamutsewar tunani ya kai fuskarsa cikin wuyanta ya fara bata sumba masu zafi da shinshinar wajen yana busa mata numfashinsa. Ƙoƙarin ɗagowa datai a rikice zatai magana ya bashi damar riƙe lips ɗinta cikin nashi. Harga ALLAH Maanal bata taɓa tsorata da shi irin yau ba, dan kuwa a karo na farko hannunsa ya sauka a inda wani mahaluki bai taɓa kaiwa ba koda Ammie ko ƴan uwanta, dan ita ko kaya kunyar sakawa take a gaban Ammie, kai tunda tai hankali wlhy b ɗinta idan ta wanke bata yarda ta shanya inda wani zai ganin mata. Dama su Didi ke siya mata, suma sun san yanda take jin kunya sai su saka mata a cikin kaya bawai su bata hannu da hannu ba, ita kanta kunyar kanta take ji ta yanda koda wasa bata taɓa tsayawa gaban mirror ta kalla jikinta ba. Sosai taji mahaukaciyar gigita mai tarwatsa brain, ga azabar yanda yake mata na ratsata. Cikin sa'a ta ƙwace bakinta saboda yanayin da yake a ciki ƙarfinsa ya fara sanyi, amma inba hakan ba wane ita, ko a fuska ka kalla AA kasan a wajen mazan ma bazai daku ba balle ita ƴar tamatsitsi. Roƙonsa ta shiga yi cikin kuka har tana roƙonsa dan girman ALLAH yayi jaƙuri. Jin yaƙi sakinta ta koma tabbatar masa wlhy in bai bartaba bazata taɓa ta yafe masa ba.... “Kinji nace ki yafe min ne daman?”. Ya faɗa murya a shaƙe yana ɗagata cak zuwa gadon. Ina Maanal fa ta fahimci yau sai ta ALLAH wlhy, aifa jikinta ya shiga rawa ganin yana zame tufafinsa, gashi ya riƙeta da hannu ɗaya kawai amma ta kasa motsi. Sai ta shiga magiya da roƙo da ban haƙuri tana haɗashi da girman ALLAH. Abun yazo mata a bazata ne shiyyasa ta gigice. Gefe kuma zuciyarta na tuna mata wata rana data shuɗe, ranar da bazata taɓa goguwa a brain ɗinta da tarihin rayuwar su ba har abada. Dan ta zame musu tamkar tabo ne mai barin tambari a fuska na har abada. Wani gefe kuma nasihar likita da yace mata ta daina tsorata, tarayya da namiji ba mutuwa bace ba... Cikin shiɗewar kuka da sallamawa idannunta a rumtse ganin ya gama zare kayansa gaba ɗaya bakinta na rawa ga hawaye wasu na bin wasu ta ce, “Shike nan Ajwaad! Shike nan kayi duk yanda kaso, ai dama basan kana ɗaukata ne kamar wata dabba mara daraja, tunda ma ka iya keta min haddi a shekarun da ban wuce sha biyar ba taya zaka jini a yanzu, ta yaya! Ta yaya zaka jini. Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai!!”. Ai cak AA ya tsaya daga yunƙurin sake haɗe lips ɗinsu da yake yi, dan maiba wani ji kalamanta na farko ba balle su masa tasiri, amma kalmar _(Wlhy tsoro nake ji! Tsoro nake ji Yaya Ajwaad ka taimaka min na tuba! Na tuba dan ALLAH kada ka aikata min komai)_ har cikin tsakkiyar kansa suka dinga zirarawa kamar ana buga ƙusa a cikin bango, zuciyarsa ta wani shiga rartabewa gida daban-daban saboda wani tausayinta daya ratsashi, dan jikinta rawa yake sosai. Gaba ɗaya abinda yake ji a jikinsa komai ya tsaya kamar an daka musu tsawa. Jikinsa da ya ɗauka wani kalar ɗumin zazzaɓi lokaci guda ya janye daga nata, sauka yay a gadon gaba ɗaya, gaba ɗaya ji yake ɗakinma na juya masa, kalamanta na sake maimaita kansu a kunnensa cikin amsa kuwwa. Da ƙyar ya iya kai kansa bayi, baima san a yaya ya rufe ƙofar ba kawai ya tsinta kansa ne a ƙarƙashin shower..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣5️⃣

______________

.......Maanal kam tunda ya raba jikinsa da nata taja duvet cikin rawar jiki ta duƙunƙune kanta waje guda, sosai jikin nata ke rawa. Ga hannunsa da take ji har yanzu a jikinta, ga wajen na mata wani irin zugi dan baiyi mata da wasa ba. Kuka take irin wanda ita kanta bata san na minene ba. Sai dai wani gefe na zuciyarta sai maimaita mata kalman roƙon da take masa tana kiran cikakken sunansa yau harda su Yaya. Ita kanta kalaman dariya suke bata yanzu, tare da jin kamar bazata iya sake haɗa ido da shi ba. Amma yaya zatayi? Wannan itace kawai hanyar kuɓuta daga garesa, tabbas taji bata so aurensu ba a randa aka ɗaura, badan komai ba sai dan cika bakin da yay mata a asibiti, amma halin daya tsinta kansa na kusan mutuwa ya lausasa mata zuciya har taji ita wacece da wani zai rasa rayuwarsa a kanta, ai kamar tayima UBANGIJI butulci ne da ni'imomin daya bata kashi-kashi na rayuwa, kamar ta nuna masa bata amshi jarabawarta da hannu biyu ba, tunda tasan ƙulluwar auren ikonsa ne ba wani shiri ba. Na biyu nasihar mahaifiyarta da Daddy da Nene da hujjojin da suka kawo mata akan aurenta da Ajwaad shine rufin asirinta da su kansu musamman yanda zancen ya fara fita a lokacin bikin Ya Yazeed shima ya taka rawar gani wajen haƙura ta amshi auren batare da yin wani bore ba bayan wanda tayi. Sai dai tuna zuwan irin wannan ranar na tayar mata da hankali, na sakata jin tsoro da ɗunbin fargabar da jin anya zata iya yin biyayya ta bashi kanta kuwa. Dan wannan shi kaɗai ne hope ɗin daya rage mata wajen hukunta Ajwaad tsakanin ita da shi kamar yanda su Didi suka tabbatar mata. Dan sun nuna mata suma tabi maganar su Ammie, ta kwantar da hankalinta koda mutunci da darajar Abah da Oum. Itama ta zama jaruma yanda ya share ya nuna kamar komai bai taɓa faruwa ba ta biye masa itama suyi pretending ɗin tare, idan sun kasance a irin wannan gaɓar sai ta hukuntashi dai-dai da laifinsa har sai ya sauke nasa girman kan ya nema gafararta da afuwarta a sigar da ita kanta zataji ta gamsu da hakan sannan ta sallama. Ko a randa ta samu damar faɗama Didi Shahidah abinda taji akan Mamy ta girgiza, ta kuma tabbatar mata to lallai akwai wani abu da ya kamata su sani kenan, a hakan ma dan bata sanar mata wanda taji Mamyn na faɗama Ajwaad ɗin ba fa. Amma kalamansa na ranar sun raunanata, sun karya mata zuciya da duk wani burin horashi yanzu tausayi yake bata kawai... AA ya jima sosai a bayin sannan ya fito, ko inda Maanal take bai kalla ba, dan ya tabbatar in yay hakan duk yanda yake jinsa a dauriya ALLAH sai ya mata fata-fata. Magungunansa da suka rage saura ya ɗauka yasha, daga haka ya koma ya kwanta batare da ya cire bathrobe ɗin jikinsa ba. Duk abinda yake kuma Maanal na jinsa, amma ta daure tai shiru, sai zuwa can ta miƙe dan jin alarm ya sake bugawa alamar lokacin gama sahur na gab da fita. Bayi taje tayo wanka itama, batare daya kalla abin sahur ɗin nasu ba ta ɗauka ruwa kawai tasha, dai-dai nan ya tashi shima daga kwanciyar da yay, sai taji kamar ta zura a guje, amma dai ta dake saboda sanin lokaci ya ceceta. Aiko shi sai baima kalleta ba, bathrobe ɗin ya zare ya ajiye, ya saka jallabiya ya tada salla. Itama sai kawai ta koma daga bayansa ta ɗauka Alkur'ani ta hau karatu. Suna a wajen har lokacin sallar asuba yayi ya jasu salla kamar yanda ya saba, kowannensu yay azkar. Batare daya kallesa ba tace, “Ina kwana”. Fuuuu ya wuceta batare daya amsa ba, itama sai ta taɓe baki. Gadon ya koma ya kwanta, dan tafiyar tasu ma sai 2pm ne. Itama sai tai kwanciyarta a sallayar kawai ta ƙudundune da hijjab ɗinta....

12pm

Ita ta fara farkawa, ta ɗan kalla gadon inda yake a kwance. Rufe yake da duvet har kansa, sai taji gabanta ya faɗi dan kasancewar bedsheet ɗin fari ƙal sai yay like gawa. Da sauri ta ture mummunan tunanin ta wuce bayi, wanka ta farayi ta fito bayan ta saka kaya daga can, ta gyara jikinta sama-sama ta kabbara nafila, tana cikin yi ya farka shima. Alhamdullah yana jinsa da sauƙi babu ƙullewar mara, kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kai, bayi ya shiga, sai kuma gashi ya fito lokacin tana tahiya. Kaf kayansu da suke da datti ya tattare harda underwear ya shiga da su bayin, a washing machine ya zubasu ya haɗa ruwan sabulai dake ajiye a bayin a ciki masu daɗin ƙamshi sannan ya kunna. Yana a tsayen har machine ɗin ya kashe kansa sannan ya shiga fiddosu ɗaya bayan ɗaya yana matsewa, sai da ya kammala tas ya sake ɗaurayewa sannan ya zuba a dryer dake a machine ɗin ta busar. Sannan ya fara wanka....

Maanal na zaune tana addu'a ta idar da salla ya fito da kayan a hannu. Mamaki ya kamata, dan tunda suka zo ita ke wanke musu. Sai dai batace komai ba ya ajiyesu inda akwatinsu yake sannan yay shiri kan Maanal a ƙasa harya saka jallabiya. Salla ya kabbara shima. Kasancewar ita ta idar sai ta miƙe zuwa wajen kayan nasu ta fara shiryawa, suka ɗai suka rage, duk wata siyayyarsu ya riga ya turata gida, tsaf ta kammala shiryawa kayan data ajiye masa dan ya sanya na gefe, ta shiga bayi ta sake duba komai nasu ta tattaro dan kar suyi mantuwa. Shima daya idar da sallar ba zama yay ba, shiryawa ya farayi a kayan data ajiye masa, hakan yasa ta koma gefe kanta a ƙasa harya kammala. Fita yayi daga ɗakin, ta ɗan bisa da kallo ƙasan ido, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tana taɓe baki, daga haka ta maida hankalinta ga kallon tv. Fin mintuna ashirin sai gashi ya dawo, a wani ciki-ciki yace, “Muje” Yana kama hannun trolling bag ɗinsu da handbag ɗinta data ɗaura akai, zai ɗauka bag ɗin laptop ɗinsa ta rigashi ɗauka. A karo na farko suka kalla juna cikin ido, sai kuma kowa ya janye cike da basarwa suka fice....

Sosai Maanal ke jin kewar barin Shanghai, amma kuma tana matuƙar ɗokin komawa ƙasar haihuwarta. Ba wata tafiya mai nisa bace ta kawosu airport, bayan ƴan kunji-kunji na tsarabe-tsaraben tafiya a jirgi suka shige suka bar su Mr Li da kewarsu. Su duka su kowa yayi fresh abinsa, musamman ma mutuniyar taku da angonta. Dan ƴan kwanakin nan a Chaina kwanaki ne masu ɗunbin tarihi da suka taka rawar goge abubuwa masu yawan gaske a zukatansu musamman ga Maanal. Sosai ta ɗan rage jin zafinsa dake ƙasan zuciyarta, ta kuma sake fahimtar halayyen sabon Bestyn ta a yanzu. Shima dai hakan take, ya sake fahimtar abubuwa da yawa game da ita a yanzu. Sannan ya mata uziri akan abubuwa da yawa domin UBANGIJI ne kaɗai masanin gaibu. Kuma ko shine a matsayinta abinda zai yi kenan. Ya tabbata da ace su Maanal nada wani yaya namiji ba lallai ma ya yarda a sake bashi aurenta ba... A wannan karon ma dai ta Qatar suka koma, tafiyar kuma ta ɗauki sabon salo a tsakaninsu ba kamar a zuwa ba. A vip section suke kamar wancan karon, sai dai kowa ya nema wajen zamansa suka ƙi zama da juna. Alkur'ani Maanal ta ɗauka taita karatu ma abinta har suka iso Qatar, dan duk da tanata hamma haka ta jure. Sunyi canjin jirgi yau ma, kuma Alhamdullah kamar a wancan karon ne babu jira. Baccin da yaci ƙarfin Maanal yasa ta kai kwance, sai lokacin shi kuma AA daketa aiki a laptop tunda suka taho ya samu damar zaman nasa karatun Alkur'anin bayan ya lulluɓa mata mayafi. Shima dai zuwa can barcin yaci ƙarfinsa sai ya ajiye Alkur'anin ya kwanta. Su duka basu farka ba sai da aka fara sanar da sauran mintinan da suka rage jirgi ya taɓa ƙasa.....

Alhamdullah sun sauka ƙasarsu ta haihuwa lafiya a cikin birnin Abuja. Kowa ka gani a cikinsu yay laushi, marasa juriya ma tuni sun karya azuminsu a hanya. Wanda basu karya ba irin su Maanal ganin safiya a Nigeria ne sai da suka girgiza, dan ƙarfe 7:30 na safe suka iso. Tab ɗin babbar magana, ga azumin awa kusan 15 a bakinsu. Wannan fa shi ake kira dare biyu. Manaal dake satar kallon AA sai taga ma shi daras yake mutumin nan babu wani rauni a tare da shi, suko duk sunyi yaushi abin tausayi. Cike da girmamawa su AS sukai musu sallama suka nufi motar company da zata kwashesu takai kowa gida. Sun fito suma da shirin hawa taxi sukaci karo da Ya Fawzan, RK, da Najma sunzo ɗaukarsu. Cak AA ya tsaya yana kallon RK, shima dai kallon nasa yake yana haɗiye murmushi da ƙyar, a ransa yana faɗin (Dole ne mu tsaida wannan wasan ɓuyan haka Ajwaad) a zahiri kam sai ya nufoshi dan Yaya Fawzan na waya. Najma ma da gudu ta sheƙo ta ɗane Maanal suna murna, ai take Maanal taji duk wata gajiyarta da kasala ta ware a jikinta, ta ji daɗin ganin Najma a Abuja matuƙa gaya duk da dama sun gaisa kusan sau uku. Sai dai kuma ganin RK ya wani saka gabanta bugawa, amma ta dake abinta tana ambaton sunan ALLAH. Dai-dai nan Ya Fawzan ya iso wajen, RK kuma ya rungume AA. Abinka da maza, shima AA ɗin sai ya basar kawai, har yana ɗan hararar RK dake faɗin, “Ƴan gayu, honeymoon da azumi, abin naka azimun Oum's boy”. Harararsa AA yayi, dai-dai shima Ya Fawzan na nako masa nasa sherin. Shima harararsa yayi, suka kwashe da dariya suna tafawa. Kafin su juya ga Maanal dake gaishesu a tare, dan taƙi yarda ta kalla sashen RK sam. RK bai damu ba, dan yasan dole su kasance a ƴar hakan kafin su saki jiki da juna kuma. Itama tsokanarta Fawzan ya fara, ta shiga ɓoye kanta a jikin Najma dake musu dariya.........✍️

To mun dawo NIGERIA, kowa yazo ya amshi tsarabar sa.💃💃🏃🏃🏃

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣6️⃣

______________

Readers Also Read