Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 103
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 103: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 103. ........Mota suka nufa, RK driver Ya…
3,250 words
........Mota suka nufa, RK driver Ya Fawzan kusa da shi, AA ya shiga baya Maanal a tsakkiya kusa da shi Najma a gefenta. Tafiyar mintoci da bata kai awa ba ta kawosu gida, sun sami ko'ina shiru dan kowa na barci, Oum ce ma kawai tasan da fitarsu tarbo su AA ɗin dan RK ma a gidan ya kwana yau. Ma'aikatan gidan ne kawai dake gyare-gyare ke kai kawo, aiko motar na tsayawa suka iso suna musu barka da zuwa cike da farin ciki, ba'a dangi kawai ba hatta masu musu hidima ALLAH ya saka musu soyayyar AA a zuciya, ba komai kuma ya kawo hakan ba sai kasancewar sa mutum mai alkairi da sauƙaƙawa. Bai da yawan magana, da wahala ka ganshi a sabgar da ba tashi ba, amma mutum ne mai sauƙi gana ƙasa da shi. Ƙyawawan halayyarsa harga wanda ba musulman ba a bayyane take, dan yana iya ƙoƙarin sa wajen kamanta musu iya hurumin da UBANGIJI ya umarce mu yi a garesu. Tuni sun wuce sashen Oum, dan duk inda AA zaije a rayuwa ya dawo sai ya fara dangana da Oum sannan wani ya gansa a gidan, sai dai idan anyi sa'a ya samesu a tare ne. Duk da sashen a cike yake da ƴan hutu ko'ina a tsaftace yake su Inte sun gyara sun saka turaren wuta da air freshener masu sanyin daɗi kamar ba safiya ba. Dan har yanzu bai wuce tara na safe ba. Nan ɗin ma dai shiru dan samarin yaran dake a ƙasan barci suke yi. Su duka sama suka haura, hakan yay dai-dai da fitowar Oum daga bedroom hannunta riƙe da kaskon turare. Ina ai da gudu Maanal ta nufeta ta rungume, AA ma da yaji bazai iya haƙura sai Maanal ta gama nata ba haɗawa yay ita da Oum ɗin ya rungume. Aiko mi su RK zasuyi ba dariya ba. Tuni farin ciki yasa idanun Oum tara hawaye, wlhy ita kanta bata san irin ƙaunar da takema yaran nan ba, Ajwaad da Maanal daban suke a zuciyarta, tana jinsu ƙololuwa a ranta ta yanda ita kanta bata san ta yanda zata musalta irin soyayyar da takema yaran ba. Duk da gidan cike yake da zuri'arta zuciyarta cike take da kewarsu kawai tana daurewa ne. Sun jima a haka kafin ta ɗagosu, tare da kai hannu a tare ta shafa fuskokinsu tana murmushi. A tare suka risina domin gaisheta, sai kuma suka kalla juna dan yanda sukai ɗin abin yazo musu ne a bazata, murmushi sukayi ma juna kamar yanda Oum ke murmushin, su Yaya Fawzan kuwa na dariya. Fawzan harda juyawa ya kalla Najma ya ɗan ɗaga mata gira, ƙasa ta duƙar da kanta tana murmushi. RK godiya yakema ALLAH a zuciyarsa da bai zama sanadin raba wannan ƙauna mai ƙarfi ba, dan tabbas ya ƙara yarda Maanal sai Ajwaad, Ajwaad sai Maanal. Wannan haɗin ALLAH sai dai a bisu da ƙyaƙyƙyawar addu'a kawai. Ƴar hayaniyar ce ta tada yaran suka shiga fitowa a jere. Wayyo zokaga ihun murnar ganin su Yaya AA sun dawo. AA akwai farin jini kam Masha ALLAH. Rungume Maanal suka shigayi kowa na mamakin canjawar ɗan uwansa, kafin su shiga gaishe da AA dake kallon su kawai a dakensa dan ba sabgarsu yake shiga ba, baya sake musu fuska, amma a hakan sonshi suke dan shi mai alkairi ne a garesu, rashin yawan magana kuwa kowa yasan ɗabi'arsa ce shi da babban Yaya da ma wasu a yaran family ɗin da suka gado su. Tuni suma samarin suka shiga haurowa, sukam ai rungume AA ɗin suke, karan farko yay musu murmushi, yana binsu ɗai-ɗai ya shafa kansu. Fahimtar yanda sukai laushi yasa Oum tambayarsu suna azumi. Maanal ce ta amsa da eh, Oum tai mamaki ƙwarai da gaske, tare da jinjina ƙoƙarinsu dan awannin da yawa ai. Jin hakan tace to abarsu suje su watsa ruwa su kwanta su huta. Hakan kuwa akai, AA ya fito zuwa sashensa, yasan dai su Mamy na barci har ma Abah da su Babban Yaya. Maanal kuwa ɗakin Oum ta shige tunda dama anan take. Yaran kuma Oum ta kaɗasu suje suyi wanka lokacin tafiya tafsir yayi.... Su Mamy basu san wainar da ake toyawa a gidan ba. Dan ita bata san yau ne su AA ɗin ma zasu dawo ba. Saboda rabonta da shi tun shekaran jiya data gama zuba masa tujara, dan tunda ALLAH yasa ya kira waya kullum sai ta kirashi ta tisa masa gargaɗi a kan Maanal. Shi dai yakan bata haƙuri kawai yace ta kwantar da hankalinta. Ko a fuska bai taɓa bari Maanal tasan Mamy na kiransa a waya ba. Sai dai abinda bai sani ba Maanal ɗin ta taɓa jinsu har sau biyu, ta ga kuma text message ɗin Mamyn akan wai miyyasa bai cika mata alƙawari na kiran Nuratu ba. Bataga ya bada amsa ba, dan haka tai murmushi kawai tana mamakin al'amarin matar nan. Ƙarfe goma su Oum suka fito, hakama Mamy da Saheeba da Nuratu dan gaba ɗaya suke tafiya tafsir ɗin. Nibras ce kawai babu dan tana zuwa aiki. Kasancewar kuma yau ma juma'a ce sai gata ta fito zata bisu wai bazata fita aiki ba. Sai lokacin su Mamy ke jin dawowar AA da Maanal gidan. Wani abu ne ya tokare maƙoshin Mamy, har fuskarta ta gagara ɓoyewa, amma Oum na kallonta sai tai murmushi. Sai dai Oum ta riga ta ga canjawar fuskar Mamy ɗin, itama a ranta sai taji lallai basu ƙyauta ba, amma harga ALLAH tayi hakane dan tama kowa surprise a gidan, kuma shima AA daya sanar mata yace karta faɗama kowa har su Abah da Babban Yaya. Fawzan ma shine ya gaya masa. RK, ko Fawzan ya fito dan zuwa ɗakkosu yagansa a compound yana waya, shine dalilin tafiyarsu tare. Najma kuwa shine ya kirata yace yazo ta masa rakkiya wani waje, itama sai da akaje airport ɗin ta sani. Fita sukai massalaci, Maanal dai bata bisu ba. Dan tana gama wanka kwanciya tayi, hakama AA yana can ya kwanta. Har suka dawo daga tafsir basu tashi ba, lokacin sha ɗaya da rabi dan yau juma'a an tashi da wuri saboda sallar juma'a. A compound suka iske Babban Yaya da Abah da RK suna shan iska, Fawzan ma barci yake. Cike da tsokana Abah dake kallon Oum ya ce, “Ashe ɗanki ya dawo min da yarinyata, irin wannan bazata haka”. Dariya Oum tayi da faɗin, “Yanzu ai sai hankalinka ya kwanta, ka yarda mu masu cika alƙawari ne”. “Na yarda kam sosai”. Abah ya faɗa murmushi yalwace a fuskarsa su Babban Yaya na taya shi. Babban Yaya yace, “Ai nima Abah na ƙagara su tashi a barcin naga shi da Lillyn wa yafi wani ƙiba yanzu”. Dariya aka sanya, Oum tace, “Oh ni kowa dai ya sama Autana ido a gidan nan. Fadeel ina yabonka salla karka kasa alwala mana”. “To shike nan Oum na bari”. Babban Yaya ya faɗa yana dariya. Wucewa sukai ciki suma, dan Mamy dama tuni takai hanyar sashenta. A mamakin kowa Nibras da Nurry sashen Oum suka nufa suma. Dan tun ɗazu da sukaji wai su AA sun dawo ji sukai kamar ma su fasa zuwa tafsir ɗin, duk hararar da Saheeba ke zabgama Nuratu yitai kamar bata gani ba. ALLAH sarki Oum sai tai murmushi kawai tana nema ma Nibras shiryar UBANGIJI. Dan ita Nuratu idan tayi ai normal ne....
Alarm ɗin da AA ya saita ne ya tadashi saboda sallar juma'a. A lokacin sha biyu. Wanka kawai ya shiga. Yana fitowa ya shirya cikin wani ɗanyen yadi da yaji ɗinkin manyan yara ya kwanta luff-luff. Fuskarsa ya gyara tare da feshe jikinsa da turarensa masu sanyin ƙamshi kala kusan uku. Ya kawo hula data dace da tsarin adon nasa ya kafa. Matuƙar ƙyau kuwa yayi kamar ka sasheshi ka gudu. Kodan bai cika damuwa da saka manyan kayan bane balle hula oho masa. Wayoyinsa daya kashe ya kunna, ya zubasu a aljihu tare da wallet. Sai kuma ya ɗauka atm ɗinsa ya fiddo wallet ɗin ya saka ciki, duk da kuwa akwai wasu atms ɗin a wallet ɗin, da alama dai yana buƙatar wanda ya dauka ɗin ne a kusa, dan a ajiye yake alamar baya amfani da shi sai da dalili. Kai tsaye sashen Abah ya nufa, cike da takunsa na nutsuwa da rashin son hayaniya. Sai da yay knocking tare da sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shigan. Wani irin murmushi Abah dake kallonsa ya saki, sai kuma ya buɗe masa hannayensa alamar yazo garesa. Murmushi shima AA ɗin yayi, tare da ƙarasawa gaban Abah ya zai zauna a ƙasa ya riƙoshi ya zaunar a gefensa, cike da kulawa da soyayya irin ta ɗa da uba ya bashi runguma ta gefe yana faɗin, “Irin wannan yin fresh haka Autan Oum ɗinsa. Har naji na ƙagu naga tawa ƴar yata koma”. Murmushi sosai AA ya sake yi, dan randa Abah kejin nishaɗi daban ne a rayuwa. Ƙasa-ƙasa yace, “Abah tayi fiye da yanda kake tunanin ganinta, dan na kula maka da amanarka yanda ya kamata”. Dai-dai nan Mamy ta fito riƙe da babbar rigar Abah da hula a hannu, karaf kuma a kunnenta zancen AA. Sai kuma akai sa'a suka haɗa ido da shi. Wani kallo kuwa ta zuba masa mai ma'anoni da dama. Shi kuma sai yay ƙasa da kai yana amsa addu'ar da Abah ke masa da sanya albarka. Gaishe da Aban ya fara yi kafin Mamy ɗin data wani basar da farko kamar bata ganshi ba. A mamakinsa sai ta amsa cike da nuna kulawa har tana tambayar yaya Maanal. Wannan hali na Mamy na girgiza zuciyar AA matuƙa. Kodan shi ALLAH yayisa ba mutum mai iya ɓoye abu bane oho, dan in har ka masa abinda yaji bazai iya shanyewa ba sai ya maka magana, sha yanzu magani yanzu yake, shiyyasa irinsu Sen.. Bukar Kaugama manyan ƙasar ke jin haushinsa. Dan sun so jan ra'ayinsa jikinsu ya nuna wannan ba shigarsa bace su sa'annin mahaifinsa ne, suka fito masa a buɗe game da muƙamin da shugaban ƙasa ya bashi na shugaban matasa, nan ma ya nuna musu shifa wannan muƙami baya a gabansa dan office ɗin ma sai ya gadama yake zuwa. Yana dai bibiyar ayyukan waɗanda ke ƙarƙashinsa daki-daki, amma shi ko sisi daya shafi aikin nan bai taɓa yarda ya shigo hannunsa ba hatta da albashi kuwa. Dan shi ya san kasuwanci duniya ne, duk wanda ya saba da neman na kansa babu ta yanda zai iya shagala da wani aiki na gwamnati koda na wucin gadi ne...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖4️⃣7️⃣
______________
.........Tare da Abah suka fito suka bar Mamy na binsa da harara, sashen Oum suka nufa, can suka samu su Babban Yaya cikin shiri suma. AA yaje ya rungume babban Yaya da shima dai yau yake tsokalarsa. RK da Fawzan kuwa na dariya. Zo kaga idanun Nuratu da Nibras kamar zasu faɗi a jikin AA. Gaba ɗaya sun susuce, a kwana goma kawai yay irin wanan sake zama fresh ɗin. Zukatansu suka shiga wassafa musu ba dole yay ƙyau ba yana more angwancinsa. Wani irin ture tunanin sukai rayukansu a ɓace, tun ɗazun suke a sashen amma basu ga Maanal ba. Wai tana ɗakin Oum tana barci. Jin AA na sashensa kuma baisa sun gajiya ba, dan sun tabbatar bazai iya wucewa massalaci bai zo sashen Oum ba. Aiko sai gashi ya shigo duk ya firgitasu da gayunsa. Tsabar sakawa rai masifa su duka biyun ba wanda azuminsa bai raunana ba saboda yanda suke siffanta wa kansu AA ɗin a zukata. Suko sauran ƴammatan da zukatansu fes suke kowama yayi musu ƙyau a yayun nasu bawai AA ɗin kawai ba. Najma da Fawzan kuwa sun wani kashe ma juna ido cike da shauƙi. Sai ko karaf a kan idon AA. (Kai mi Ya Fawzan ke shiryawa haka?) AA ya ambata a zuciyarsa, sai ya ɗan kalla RK daya fahimci shima hankalinsa akansu Ya Fawzan ɗin yake. Wani signal sukama juna da ido, RK yay dariya yana ma bakinsa zip. “Tab ɗin”. AA ya faɗa a ƙasan maƙoshi yana miƙewa abinsa batare da kowa ya fahimci inda tab ɗin ɗin tasa ta dosa ba. Fitowa sukai harabar gidan gaba ɗayansu harda samarin yaran nan duk suka shiga motoci. RK da AA da wasu a yaran suna a mota ɗaya. Babban Yaya, Fawzan da Abah da sauran yaran a mota ɗaya. Acan itama Oum ta kaɗa ƴammatan zuwa kowa yay wanka yay salla a shiga kitchen. Jikin babu ƙwari Nuratu da Nibras suka fito a sashen.....
_________★
A lokacin da su Maanal suka gama hutawa anan airport Yazeed ne da tashi matar ke isowa tasu ƙasar haihuwar bayan kwashe watanni a ƙetare suna hutawa. Masha ALLAH na faɗa, ganin yanda Yazeed ɗin yay wani kalar yin ƙyau da sabuwar nutsuwa ya yi ƙiba irin ta matasan masu kuɗi. Sai dai fuskar kicin-kicin babu fara'a sam a tare da shi abinka da dama bamai yawan fara'ar bane. A gefensa Nazeefa ce cikin matuƙar gayu ta ƙara wani uban haske da ƙiba itama. Kai daka ganta kasan tana jin daɗi da alama kuma ta harbu. Babu wanda yasan da dawowarsu sai Aunty Sabuwa, dan haka ita da kanta ta tafi tarbosu Abujan. Nazeefa na hangota ta wani tafi da gudu ta tungumeta tana ihun murna. Hakan ya jawo musu idanun mutane kuwa. Oho ko'a kwalar rigarsu, dan Aunty Sabuwa ma ɗaga Nazeefa tayi tana juyi da ita abinka da siririyar mace, a hakan ma wai jikin ya murje ne. Ƙarasowar Yazeed da abun nasu ya bashi kunya ya sata sakin Nazeefa, sai kawai ji Yazeed yay an wani rungumesa. Tab ɗin, yau fa ake mutuwar tsaye, dan kuwa ita dai Yazeed ɗin yayi. Yayinda Aunty Sabuwa ke faɗin, “Oyoy my Son”. Yazeed na kama da mahaifiyarsa Hajiya Yaya, Aunty Sabuwa da Hajiya Yaya na kama da juna, shiyyasa mutanen dake kallon ikon ALLAH suka ɗauka ita ta haifesa, duk da dai wasu na ɗan wasiwasi na ganin kamar shekarun Aunty Sabuwa bazai kai ta haifi Yazeed ɗin ba. Nazeefa da abin ya sosa mata zuciya ta riƙo Aunty Sabuwa tana faɗin, “Kai Mom harda runguma kuma?”. “To dan ubanki ba ɗana bane shi, ko a lahira ba ance ɗan ɗan uwa kai yake gani ba. Kinga ko a lahira bazaiga Yaya ba ni zai gani”. Baki sosai Nazeefa ta tura gaba, tana kauda kanta. Oho ko'a jikin Aunty Sabuwa, sai ma amsa gaisuwar Yazeed da take yi. A haka suka rankaya zuwa lafiyayyar motar da aka sakama Nazeefa a lefe. Ba shi kawai ba ita kanta Nazeefar sai da tai mamaki. Ta kalli Aunty Sabuwa cikin waro idanu ta ce, “Mom! Wai motata ce ta koma haka? Hawa akeyi ne?”. Cikin rashin damuwa Aunty Sabuwa ta ce, “Eh mana my baby ina ɗan ɗanawa ne kafin ki dawo. Babanki yace idan aka barta a ajiye ba'a hawa saita samu matsala.” sai kuma ta sake rage murya yanda Yazeed bazai ji ba ta cigaba da faɗin, “Sannan banda ke shashasha ce yanda yaron nan ya moreki da ƙyau a hutawar nan taku ai kinsa zai saya miki wadda ta fita. Dan yanzu kinfi ƙarfin hawa wannan. Agolan gidansu fa tsohuwar budurwarsa motan miliyan 90 aka sako mata a lefe da ta miliyan 20+. Ke sai ki zauna kina hawan wannan ta 20m ƙaramar tata ma tafi taki”. Ai wani irin susucewa Nazeefa taji tayi, a zabure ta ce, “Wai kina nufin Maanal Mom?!”. “To inba itaba wa? Ba itace tsohuwar budurwar mijinki ba”. “Kambu Mom shi ɗan gidan KK kura ɗin ne yay mata wannan lefen?”. “Hummm! Ke dai fa labarin mai tsaho ne, amma ina gaya miki likafa taci gaba, kin san uwarta ta iya tsafi, ai a wajen ɗaurin aure komai ya canja, maimakon ɗan kura sai aka bama ɗan tsohon ambassador Aliyu Darma”. “Kuttun uban can kai, AA Darma fa kenan? Koba shine aka gaya muku ya mata fyaɗe ba tana yarinya”. “Shifa kuwa, kedai shiga mota muje ma ƙarasa a gida mijinki na kallonmu”. Tab ɗin gaba ɗaya jikin Nazeefa ya gama sanyi, ji take farin cikinta ya wani gushe a lokaci guda. Kai ina bazai yiwu ace ta ƙwace Yazeed a hannun Maanal ba, sannan Maanal ta aura wanda yafisa. Yo ba Yazeed ba ai ko Daddynsa kansa AA Darma ya fisa kuɗi kamar yanda taji ana faɗa, balle kuma suma babansu Aliyu Darma ɗin ƙurun kansa ne, hakama sauran brothers ɗinsa suma fa akwai kuɗin. Kai family ɗin Darma ma gaba ɗaya sai dai kawai ace wane yafi wane arziƙi saboda iyayensu sun tara musu. Gashi ba wani uban yawa ne da su ba dan a tarihin data bibiya nasu tushe zuri'ar gana ɗaya shi Harɗo Ishaq Darma ɗin ba ɗan asalin ƙasar Nigeria bane, tushensa da ainahin zuri'arsa na wani yanki na sudan ne. Mahaifiyarsa ce ƴar nan Yola ɗin, bata son Mahaifinsa shiyaysa daga haihuwarsa auren ya lalace ta gudo da shi nan. Shi kuma babansa yay fushi yace bazai biyo ta ba har abada ya bar mata ɗan. Dan haka ainahin dukiyar Harɗo Ishaq ta mahaifiyarsa ce daya gada, iyayenta suka bar mata kuma ita kaɗai, shima ya gada a wajenta.. Nazeefa na wannan tunanin suka iso gidansu. Mamaki sosai ya kama Yazeed ganin gidansu Nazeefa suke, shi a ganinsa ai gidansu ya kamata a tafi, sai dai yaji ya kasa magana sam. Lafiyayyan abinci kuwa suka samu an haɗa musu, dan Nazeefa ta gayama uwarta basa azumi saboda tafiya. Shi dai Yazeed hankalinsa duk a rarrabe, kewar mahaifiyarsa yake shima da ƴan uwansa, so yake ya gansu amma anzo nan an masa ɗaurin goro. Haka dai ya daure ya ci abincin sama-sama. Yayinda Nazeefa da Aunty Sabuwa suka kulle a ɗaki bai san abinda suke tattaunawa ba. Yanda suka barsa shi kaɗai ɗin kuma ya sosa masa rai, amma sai yaji ko'a fuska bazai iya nuna ɓacin rai ba. Sun fi minti talatin kuwa kafin su fito suna ƴar dariya, sai lokacin Nazeefa ta zauna taci abincin itama. Sun kammala Yazeed na shirin cewa su tashi suje gida sai ga Babanta. Wato mijin aunty Sabuwa. Ai da wani irin farin ciki ta daka tsalle ta ɗanesa tana ihu. Sai Yazeed yay kasare kawai yana kallon ikon ALLAH. Bayan sun gama murnar su sanan baban nata ya zauna suka gaisa. Babu kunya sai wani faɗi yake wai amarcin ya amshesu sunyi ƙyau abinsu. Kunya kamar ta kashe Yazeed amma bai iya cewa komai ba. Shima baban jan hannun Nazeefa yay suka haye sama, sunfi minti ashirin sannan ta dawo. Nan ma dai ran Yazeed ya sosu, amma ko fushi bai iya nunawa a fuska ga duk da kasancewar sa mutum mai zafi. Suna fitowa ana kiran magrib, aunty Sabuwa tace ko zasu koma sai anyi salla. Kan Yazeed a ƙasa ya ce, “Aunty ayi haƙuri dai mu tafin”. Ido Nazeefa ta ƙyafta mata, dan haka tai shiru. Yanzun ma Aunty Sabuwa ce ta tuƙasu zuwa gida, duk da kuwa shan ruwa ake kuma tace wai tana azumi....