Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 129

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 129

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 129: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 129. Kamar jiya yau ma Maanal ta hana Oum…

3,207 words

Kamar jiya yau ma Maanal ta hana Oum yin komai, ita tayi girki tsaf su Inte suka shirya a table. Dan yanzu shima Babban Yaya ya dawo nan cin abinci. Suma su Naufal anan suke gun Oum ɗin. Maanal ɗin ce ma taje ta ɗakkosu a school jiya. Yau ma tana ganin biyar tayi ta ɗauka key ɗin motar Oum dan nata sai an kaisu service. Tare da Inte da tace zata rakata suka tafi. Babu jimawa sai gasu sun dawo. Kusan dai-dai lokacin shima AA ya shigo gidan, amma ya rigasu dan Maanal na shigowa da mota ciki shi kuma yana fitowa. Ganin motar Oum ya sashi dakatawa da mamakin ina Oum ɗin taje haka da yamma. Fitowar Anum da gudu ya sashi gane Maanal ce, kai tsaye wajensa yarinyar tayi cike da farin ciki. Shima sai ya ɗauketa ya ɗaga sama yana murmushi da faɗin, “Oh oh Oumna ta dawo school”. Shima Naufal AA ɗin ya nufa ya rungume, dai-dai nan Maanal ta fito itama idonta a kansu. Gira ya ɗan ɗage mata ita kuma tai murmushi. Koda ta iso inda suke tana masa sannu da zuwa sai yay mata nuni da ido tazo. Bata musa ba ta matsa, ya wani matsota ya haɗa ita da yaran ya rungume. Cikin kunneta ya raɗa mata, “In sha ALLAHU nan da 5years haka zan dinga haɗaku ke da yara ina rungumewa”. Murmushi tayi tare da ɗan mintsininsa zata fita a jikinsa ya hana hakan, sai da ya bata wani ɗan sumba a kan wuya yanda yaran bazasu lura ba, da mata raɗa ya ce, “Ina taya kaina murna yau a angona nake”. Harararsa Maanal ta ɗanyi da matsawa yanzu kam dan karma wani ya fito ya gansu. Sai dai bama ta sani ba komai da suke a idon Nibras ne, hakama ma Saheeba dake dakon jiran dawowar Babban Yaya tana a barandar sashen Mamy ita da Nuratu da itama taga komai. Yana ɗauke da Anum ya riƙo hannunta cikin nashi suka nufi sashen Oum. Naufal kuma na ɗauke da ledan tsarabar da AA ɗin yay musu dan kayan sunma Inte yawa ta kwashi school bags nasu da lunch box. Yanda yake murza mata hannu yasa ta kallesa, shima kallon nata yayi cikin lumshe idanu da buɗewa. A saman lips ya furta, “Hannunki yana da sanyi mai nutsar da raina. Ina jin kariya da salama idan kina kusa da ni. Zan so naita riƙe hannunki a haka har abada Besty”. Abinda ta gani kwance cikin idanun nasa yasa ta kauda kanta kawai tana murmushi. Shi ko ya ɗan cije lips da sake lumshe idanu da buɗewa. Suna shigowa main falo ta hanga Oum ta cire hannunta a cikin nasa, bai hanata ba dan duk rashin ta idonsa baiyi a gaban Oum. Barsu dai suyi ɗan faɗansu da tsokanar juna shi da Maanal ɗin shike nan. Oum kam sarai ta gansu amma ta basar, tama maida hankalinta ama su Naufal oyoyo. Suko sun zagayeta, yaran na matuƙar ƙaunar Oum, ana hanasu zuwa inda take ne kawai dan basu da yanda zasuyi. Dan sam ba ƙaunar zama sashen Mamy suke ba. Amma uwarsu ta kafa musu sharaɗin sai can kawai. Shiyyasa yanzu da suka dawo sashen Oum ɗin wani kalar daɗi suke ji ko neman uwar kuwa basayi ma sam...........✍️

Wa yaga tufƙa da warwara Mamy. Kina ƙoƙarin janye wasu, wasu na karuwa, shifa kyakkyawan hali zanen dutse🥰🥰🥰❤️

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣8️⃣

______________

.........Kusa da Oum AA ya zauna, ya saka kansa a kafarta yana faɗin, “Haba Oum ki ƙyale jikokin nan naki kiyi ta ɗanki”. Cike da tsokana Maanal dake wucewa kitchen ɗauka masa ruwa ta ce, “Jealousy”. Harrarta yay yana ɗaukar pillow kamar zai wulla mata ta masa gwalo ta shige kitchen da sauri”. Pillow ɗin ya ajiye yana cije lips alamar zan kamaki, Oum dake murmushi ta shafa kansa. Hannun data shafa masa kan ya kama ya sumbata. Sai kuma cikin ɗan damuwa ya ce, “Oum wai yaushe Abah zai dawo ne? Nifa idan ina gida nafi son naita ganin duk kowa na nan”. Oum da itama take cikin damuwar tafiyar Aban dan cikin fushi suka rabu akan ƙin zuwa duba Mamy asibiti da yay, tambayar duniya kuma yaƙi gaya mata mike faruwa. Amma bata bar su AA ɗin sun san hakan ba, cike da kulawa ta ce, “Maybe cikin satin nan dai, baƙwa waya ne?”. “Munayi, kawai dai na tambaya ne. Dan dana tambayesa jiya cayay min yana da uziri sosai”. Murmushi Oum tayi, kafin tace wani abu Maanal ta ƙaraso da ruwa a tray, a gaban AA ta ajiye, dan haka ya tashi daga kwantar da kansan da yay a kafaɗar Oum ya zauna sosai. Ruwan data zuba masan ya amsa yasha ya miƙa mata kofin yana wani binta da kallon ƙasan ido. Maanal dake basarwa saboda idon Oum ta ce, “Abinci fa?”. Mikewa yay yana faɗin, “No zan fara wanka, sai ma anyi magrib cin abincin gaba ɗaya yafi daɗi. Oum bari naje sai na dawo”. “To Auta a dawo lafiya”. Sai da ya fita da fin mintuna biyar sannan Maanal ta tashi itama. Ruwan da ya sha ta ɗauke ta maida kitchen, ta can tabi ta ƙofar baya ta gudu. Dama jiya haka tayi, aiko mi Oum zatai ba dariya ba. Dan ma ta tabbatar Inte ta kira, koda ta fito cemata tai, “Ina Baby?”. Inte dake ƴar dariya ta ce, “Oum ta fita ta back door”. Itama Oum dariyar tayi, tace “Ja'ira”. Inte dai ta koma ciki tana cigaba da dariyarta. Yanda Maanal ɗin keyi daɗi yakema Oum, dan ta fahimci Autanta zai samu irin kulawar da magidanci ya kamata ya samu ga iyalansa ba irin matan su Fawzan ba. Wannan shine babban dalilinta na ɗora Hajiya Shuwa akan gyara Maanal ɗin dama. Dan bata son Babynta tai rayuwa irin tasu Saheeba sam.....

★Tuni Maanal ta shiga sashensu dan tasan AA na sashen Mamy dubata. Bedroom ta wuce dan haɗa masa ruwan wanka. Ta shagala a haɗa masa turarurrukan ƙamshi a ruwan ya shigo batare da taji motsi ba ma. Sai da ta fito ta ganshi tsaye a closet yana zare jacket ɗin suit ɗinsa. Kallonsa tai ta ɗauke kanta, zata wucesa ya riƙo mata hannu. A slowly ya maidota baya ya jingina da glass ɗin closet ɗin. Shima ya matsa jikinta sosai ya dafa glass ɗin da hannunsa ɗaya. Fuskarsa ya sauke a hankali a gefen wuyanta, yanda yake busa mata numfashi da manna ma wuyan tagwayen kisses ya saka tsigar jikinta tashi, cikin wata irin kasalliyar murya a cikin raɗa ya ce, “I miss you my heart”. Motsawa tai ta shige jikinsa, tare da zagaye duka hannayenta a bayansa kanta na kwance a ƙirjinsa. Shima sai kawai ya rungumetan yana sauke ajiyar zuciya. “Rungumarki tafi laushin katifa, laushin jikinki ni'ima ce mai sauke gajiya da nauyin jikina. Hakan tamkar kwantar da tarnaƙin dake zagaye da ni ne, dan kin saka jikina na min magana fiye da kalmomina. Zan so kiyita kasancewa a cikinsa na har abada, hakan a gare ni gata ne da riritawa”. Itama cikin raɗa ta ce, “I miss You you too My Root-Soul! Nima idan har nayi ko awa ɗaya batare da kai ba duniyata bata da tushe ko kwanciyar hankali. Dauriya kawai nake yi saboda Ina ganinka a kowanne murmushi na, domin kaine ka shuka shi.” A hankali ya wani busa mata iska cikin kunne, tare da raɗa mata, “Zan cigaba da ajiye wannan murmushin kuwa na har abada in sha ALLAHU akan ƙyaƙyawar fuskar nan taki”. Ƙanƙamesa ta sakeyi sosai tana jin kamar ta tsagashi biyu ta shige cikin jikinsa kawai. Shima dai hakan yake ji a ransa. Sun fi minti uku a haka kafin ya cirota daga jikin nasa ya riƙe fuskarta a cikin tafukan hannunsa suna kallon juna. Sosai take karantar ruɗaɗɗen al'amarin dake a cikin ƙwayoyin idanunsa, kamar yanda shi kuma yake karanto tsoro da fargaba mai haɗe da sallamawa a garesa. Lallausan murmushin kwantar da hankali ya sakar mata. Muryarsa na sake komawa cikin maƙoshi ya ce, “Mizan samu?”. Akan lips ta bashi amsa da, “Komai ma”. Ya ɗage gira sama tare da taɓe baki a yanayin murmushi yana jinjina mata kai irin na (kin tabbatar?). Ido ɗaya ta kashe masa alamar (Yes) sai kuma tai ɗiɗɗishe da ƙafafunta kasancewar ya fita tsaho sosai ta zare gilashin idanunsa, hannayenta gaba ɗaya ta zagayo akan wuyansa ta matsar da fuskarta gab da tashi har suna zuƙar numfashin juna. Sai kuma ta lumshe idanunta cike da jin nauyi da kunya. Shi dai kallonta kawai yake kamar ya samu television. Idanun nata a lumshe ta ɗaura lips ɗinta akan nashi ta sumbata. Tana ƙoƙarin janyewa ya hana hakan ta hanyar riƙo kanta kawai ya kamo lips ɗin nata da ƙyau ya tura cikin bakinsa. Da jikin closet ɗin ya mannata, sai kuma ya kamata ya ɗaga cak a jikinsa, tako harɗe ƙafafunta a bayansa kamar yanda ta harɗe hannayenta... A haka ya dinga tafiya da ita har cikin bayin, bai kuma tsaya ba har sai da ya tsaya dasu ƙasan shower, kawai ya sakar musu ruwa mai ɗumi a jiki. A tare suka sauke ajiyar zuciya, ya kuma cigaba da yin yanda yaso da lips ɗinta. Kafin ya saki da ƙyar ya shiga rabasu da kayansu. Daga haka ya sake ɗaukarta ya fito a wajen wankan suka shige jacuzzi. Anan ne fa ya fara tabbatar mata ta tsokalo ƴan samari, dan sai da idannunta suka fara raina fata ganin zai ɗauki wani sabon layin. Ta fara roƙo da magiya da son kuɓutar da kanta. Shi ko ya nuna mata a wannan fannin bai san wasa ba, bai san ɗanɗani haukaci ba. ALLAH dai ya taimaketa akai kiran sallar magrib, amma data gayawa mutanen Giro kam. A gurguje suka ƙarasa wankan suka fito, ta taimaka masa da shafa mai da saka kaya kamar yanda ya buƙata, da ɗan hanzari ya sumbaci goshinta ya fice dan sallar ake ƙoƙarin tayarwa. Yana gama fita ta sauke ajiyar zuciya, sai kuma tai murmushi, dan ita da kanta bama kanta dariya take. Itafa komai ayi tana so, amma tsakani ga ALLAH banda sha ƙundum, dan a tsorace take. Itama kimtsawa tai tayi sallar, tai zaman yin azkar. Tana a wajen har akai sallar isha'i sannan ta miƙe. A gurguje ta gyara jikinta ta canja kaya wanda suka dace dan sashen Oum zasu koma cin abinci.

★Maanal na kammala shiryawa sashen Oum ta wuce. Dan tasan shima ya wuce can tare da su Yaya Fawzan. Ta samesu su duka ukun kuwa a can, Anum na jikin AA yana mata homework. Tana yin sallama da shi suka fara haɗa ido, yanda yake kallonta babu ko kunyar yayunsa yasa ta ɗauke kanta. Cikin girmamawa ta gaida Babban yaya da Yaya Fawzan. Yaya Fawzan sarkin tsokana ya fara tsokanar tata kuwa. Cike da jin kunya tasa hannu ta rufe fuskar tata tana dariya. Dai-dai nan Nuratu da Oum suka shigo, Nuratun najan akwati. Su duka kallonsu suke, banda AA da yay musu kallo ɗaya ta ƙasan ido ya ɗauke idonsa. Yaya Fawzan ne daya kasa haƙuri ya ce, “Lafiya kuwa Oum?”. Sai da Oum ta nunama Nuratu hanyar upstairs tana faɗin, “Jeki kai kayan sama sai kizo kici abinci”. Sannan ta zauna tana bama Fawzan ɗin amsa. “Faɗa suke da Saheeba acan shiyyasa nace ta dawo nan.” Cikin ɗan ɓacin rai Babban Yaya yace, “To ta wuce gida mana dole ne sai ta zauna anan Oum?”. Fuskar Oum da murmushi ta ce, “A'a Fadeel ba ayi haka ba, tunda tana son zama nan ɗin a barta. Kasan Hajiya Turai ba wani zama waje ɗaya take ba. Ga Nuratun ba isashen lafiya ba wazai kula da ita. Su Nana kuma suna nan suma balle ace taje Kano. Kuma muna nan ma ai ba'ace taje Kanon ba koda suna can”. Babban Yaya dai da alama ba son zaman Nuratun yake ba, haka shima Fawzan sai da ya nuna hakan a fuska. Gwaska AA kuwa ma bai nuna yama san mi sukeyi ba balle ya tanka. Maanal kuwa murmushi tayi babu wani damuwa a fuskarta, amma acan ƙasan ranta ita tasan saboda AA Nuratun tace zata dawo nan ɗin da zama ko kuma akwai dai wata a ƙasa. Shekararsu nawa da Saheeba ɗin faɗan baisa tazo nan ɗin ta zauna ba sai yanzu. Amma babu komai zata iya da su, dan a yanzu kam a shirye take tsaf zata buga da kowa akan mijinta, kuma zata basu mamaki. Dan haka ta turama RK saƙo. Ganin duk yanayinsu ya canja Oum tai murmushi, cike da kulawa ta ce, “Bana son ku koyi halin daba naku ba, ku manya ne, sai kun gyara na ƙasa zasuyi koyi. Ko'a fuska bana son wani cikinku ya nunama yarinyar nan wani abu mara daɗi. Fawzan bara na kira matarka a waya, itama kwana biyu naga duk ta tsangwami kanta.” Kafin ma wani yay magana Oum ta fara kiran Nibras a waya. Tana ɗagawa kafin ma tace komai Oum ta ce, “Zo ina nemanki yanzun nan”. Tamkar dama kiran Oum ɗin take jira zambar ta miƙe, cikin ƙanƙanin lokaci sai gata a sashen. Shi Fawzan ma sai abin ya bashi dariya. Amma bai ce komai ba, baima kalla inda take ba tunda ta shigo. Sai ga Nuratu itama ta sakko, wani kallon harara sukaima juna ita da Nibras ɗin kowa ya ɗauke kansa........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖8️⃣9️⃣

______________

........Koda Nibras ta gaida AA kansa kawai ya jinjina mata amma ko kallon inda take baiyi ba itama. Saima ya miƙe ɗauke da Anum datai barci ya haura sama. Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, Naufal dama yay barci shi tun a massallaci, suna shigowa Fawzan ya wuce da shi saman. Koda ya dawo kai tsaye dining ya nufa yana faɗin, “Besty zoki bani abinci barci nake ji”. Amsawa tai tana miƙewa, sai da taje dining ɗin ganin babu plates sai ta wuce kitchen ɗakkowa. Fawzan da Babban yaya ma sai suka miƙe. Sai da suka zauna kamar abin arziƙi Fawzan ya ce, “Babban yaya ina da tambaya”. Babban Yaya da bai san mi za'a tambayesa ba ya ce, “Uhum ina jinka”. Sai da Fawzan ya ɗan kalla AA sannan ya ce, “Dama ango na barci a farkon dare dan ALLAH?”. Kallon AA dake hararar Fawzan Babban Yaya yayi, cikin son riƙe murmushin dake neman kufce masa ya ce, “Nikam ka tambayeni, tambayi Auta maybe shi yana da amsar baka”. Dariya Fawzan ya tuntsure da ita ganin shima dai yau Babban Yaya ya ɗana. Cike da neman son ƙure AA ɗin Fawzan ya ce, “Auta ance na tambaye ka, dama ango na barci a farkon dare?”. Waya AA ya ɗauka yana dannawa batare da ya bashi amsa ba, minti ɗaya ya ajiye wayar yana wani makirin murmushi da kallon Fawzan, sai kuma ya ɗage gira sama ya ce, “Ka duba na tura maka amsar”. Wayar Yaya Fawzan ya ɗauka. Idanu sosai ya waro akan AA, sai kuma yace, “A lallai Auta kaci wake, ni ka turama wannan abun?”. “Naga amsar da kake nema kenan?”. AA ya faɗa ciki-ciki. Babban Yaya dake murmushi Yaya Fawzan ya kalla baki buɗe. Sai kuma ya miƙa masa wayar yana faɗin, “Kalla fa abinda ya rubutan Yaya”. Fitt AA ya ɗauke wayar yana harararsa. “Oh ashe ma kai ƙaramin mara kunya ne, ka bari Babban Yayan ya gani mana”. Fawzan ya faɗa yana dariya. Isowar Oum dining ɗin ya samawa AA lafiya a wajen Yaya Fawzan. Sai ga Maanal ma ta dawo. Suma su Nuratu duk suka zauna. Daga nan tsokana ta ƙare akai zaman cin abinci. Bayan sun kammala sun koma falo su Inte suka gyara wajan. AA dama shi bai zauna ba, sallama yay ma Oum da babban Yaya, ganin Maanal bata da niyyar tashi ya zuba mata ido. Itako ta fiske. Oum na lure da su, sai kawai tai murmushi ta kalla Maanal, babu wasa tace, “Oya Baby tashi kuje sai da safe”. A kunyace Manaal ta miƙe. Fawzan ya ce, “Auwwwwwn! Lillyn Babban Yaya ƴammata”. Ai da sauri ta fice tana murmushi. Oum da Babban Yaya sukai murmushi suma. AA kam hararar Fawzan yayi da faɗin, “Girma dai ya faɗi”. Yaya Fawzan dake dariya ya ce, “Naga kai a jaka ka zuba naka ka ɓoye”. Sarai AA ya fahimci abinda Yaya Fawzan ya ke nufi, sai ma ya rasa abin cewa ya murmusa kawai yana ma Babban Yaya da Oum sai da safe yabi bayanta. Sai da suka fara zuwa sukama su Mamy sallama. Har sun miƙe Mamy tace ya zauna zatai magana da shi. Jin hakan yasa Maanal fitowarta a ɗakin, AA ya bita da kallon ƙasan ido. Mamy dake lure da shi ta sake ɗaure fuska zuciyarta na zafi. Cikin dakewa ta ce, “Gobe ka sayama Aunty ticket zata tafi”. Da mamaki ya kalleta, sai kuma ya daure yace, “Baki gama warkewa ba fa Mamy miyasa zata tafi bayan itace mai ƙoƙarin kula da ke?”. “Ni nace da kai ban gama warkewa ba? Baga Nana nan da Saheeba ba kuma”. Ɗan jimmm yay na sakkani, sai kuma ya ce, “Shike nan ALLAH ya kaimu goben.” A daƙile ta ce, “Ina maganar mu ta tsaya ta documents ɗinka?”. Yanzu kam kasa jurewa yay sai da ya ɗago ya kalleta da ƙyau. Ganin yanda ta zuba masa ido sai ya ɗauke nashi. Baya buƙatar wani abu da zai ɓata masa wannan daren, dan haka ya miƙe yana faɗin, “In sha ALLAHU zan kawo miki ina kan tattarawa.” “Hummm! Ka cigaba da raina min hankali zan baka mamaki. Kuma yarinyar nan bana buƙatar sake ganinta ta shigo dubani”. Murmushi yayi mai ƙuna, cike da girmamawa yace, “In sha ALLAHU bazata sake zuwa ba kiyi haƙuri”. Ya nufi ƙofa abinsa ya fice. Ya yi tunanin Maanal ta wuce, sai ya sameta suna hira da Aunty a falo sunata dariyarsu hankali kwance. Su dukansu basu da wata shaƙuwa da dangin Mamy saboda ba wani shiga sabgarsu suke ba, badan suna talakawa ba ne, kawai dai tun farko Mamyn ba zuwa take dasu sabgohinsu ba, koda yake itama bason shiga take ba sai ta zaɓa, a karo na farko yaji Auntyn ta shiga ransa yau, dan duk wanda yaso Maanal da Oum to shima zai so shi kuwa. Sai da ya gama kallesu sannan ya ƙarasa in da suke. Miƙewa tai sukaima Auntyn sallama suka wuce, ta bisu da kallon sha'awa, a karo na farko taji haɗin nasu ya mata dai-dai kuma ya birgeta....

Readers Also Read