Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 130

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 130

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 130: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 130. Ta riga shi haurawa sama, ya tsaya…

2,990 words

Ta riga shi haurawa sama, ya tsaya kashe wuta da rufe ƙofa, lokacin da yake iskota ɗakin hatta shiga bayi tana yin brush. A haka ya shigo ya sameta. Tsayawa yay ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon ta kawai. Ta cikin mirror ɗin ta zuba masa ido itama. Sai kuma ta ɗage masa gira alamar (kallon fa). Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, ya cigaba da kallonta kawai. Bayan ta kammala ta saka masa makilin ɗin a jikin nasa brush ɗin, ta matso gabansa, hannunsa ta kama ta saka masa brush ɗin sannan tai ɗiɗɗishe ta hure idanun, “Kallon ya isa haka”. Ta faɗa tana zagayesa ta fice. Da kallo ya bita, sai kuma ya saki ɗan murmushi mai sanyi. Ya matsa jikin mirror ɗin kawai ya fara brush ɗin shima. Kafin ya fito harta shirya cikin kayan barci ta ƙarama jikinta turaren Hajiya Shuwa. Sai dai yau kala uku kawai ta sanya dan Hajiya ta gargaɗeta sosai. Sai dai duk da haka bata gane ma'anar turaren ba. Ta gama shiryawa tana gaban mirror tana warware gashinta ya fito. Gaban mirror ɗin yazo shima ya tsaya a gefenta, kamar yanda yay a bayi yanzu ma hannaye ya harɗe ya wani ɗan jingina da katakon mirror ɗin yana kallon yanda take yamutsa fuska, dan a duniya Maanal fa ta tsani abinda zai taɓa mata kan nan koda itace da kanta. Jin idanun nasa sun mata yawa a jiki ta juyo tana kallonsa itama. Sai kuma ta tura baki cike da shagwaɓa da jin zafin taɓa kan da take ta ce, “Wai mi kake kallo?”. Cikin ɗan motsa lips kaɗan ya ce, “Matata mana”. “Tana ina?”. Ta faɗa tana waigawa gefe-da-gefe like tana neman matar tasa. Wani miskilin murmushi ya saki yana kauda kansa gefe da cije lips kaɗan, sai kuma ya sake maido dubansa kanta ya wani bita da kallo tun daga ƙafafunta har zuwa saman fuskarta. Sake ɓata fuska tai tana harararsa, yay murmushi, cike da son sake kunnata ya kai hannu ya shafa gashin nata da faɗin, “Ya kamata ama gashin nan kitso, dan yafi ƙyau”. Rau-rau ta kallesa idanunta cike da hawaye ta ce, “Ni ALLAH bana so. Kai ka cika tada zaune tsaye”. Cikin ɗan waro idanu ya ce, “Yanzu Besty kitson ne tada zaune tsaye? K dan baki san kitso na miki ƙyau bane ba....” “Ni dai bana so”. Shiru bai sake cewa komai ba ya zuba mata ido kawai. Sai kuma taga kamar yay fushi. Juyowa tai riƙe da cumb ɗin tana kallonsa. Sai ya ɗauke kansa gefe. Yatsa tasa tana ɗan takalar hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa har yanzu. Irin ɗan gocewar nan yayi kamar yara na fushi ana son lallashinsu, ta ƙara takalarsa, ya sake gocewa. Sai itama ta haɗe fuskan ta kauda kanta. Fuuu ta yunƙura zata bar wajen ya riƙota da sauri. Fisgewa take ƙoƙarin yi yaƙi barinta. Cikin ƴar shagwaɓa ta ce, “Ni ka sakan, ina maka magana ma kana min wulaƙanci danma kaga ina kulaka zaka wani mun fushi”. Tsayar da ita yay a gabansa yana wani binta da kallon ƙurulla, cikin muryarsa data fara canjawa saboda yanayin daya fara shiga ya ce, “Ni nace ina fushi ne, kawai na tafi wani tunani ne daban.” Yanzu kam nutsuwa ta ɗan yi tana kallonsa ta ce, “Nami to?”. Sai da ya ɗan ja mata hanci sannan ya ce, Naki mana”. Ya ƙare maganar yana binta da ɗan iskan kallon daya bata kunya. Matsawa tai daga kusa da shi tare da faɗin, “Haramm irin wannan kallon baida ƙyau ALLAH”. Haka kawai ya tuna randa ta masa bore a asibiti, murmushi mai haɗe da ƴar dariya ta kufce masa. Sai ta tsaya tana kallonsa tare da sake ɓata fuska. “To miye na min dariyar?”. Cikin son danne dariyar da tsiya-tsiya yay zipping bakinsa da faɗin, “Na bari na bari. Kawai na tuna randa kika min rashin m ne a asibiti. Kai yarinyar nan idan kika birkice kina da wahalar sha'ani dan darunki bala'i ne, ranar kinfa kunna ni fiye da yanda kike zato, tsabar ɓacin rai kwana nai ban barci ba. Rafeeq kuma ya sake tunzurani a washe gari, ai ko kaɗan ya rage na fasa masa baki”. Dariya Maanal ta shigayi, ta ce, “Kai jama'a ban taɓa ganin ɗan daya raina kawunsa ba irin ka, nima ɗin ka kunna nin ai, dan ji na dingayi kamar na faffaleka da maruka, dama ina ciki dakai sosai ta yanda ka ke wani basar da ni like bama ka taɓa sani na ba. Sai kuma kazo ranar kana wani min gadara kai miye-miye, harda wani cewa ba mai shiga gonar da ka shiga, idan na auri wani zaka min fatalwa ne ma ko mi kace... Hummm da gaske fa baka da kirki Besty”. Hannunsa ɗaya ya cire yakai shi saman fuska ya shafo gemunsa. Yana binta da wani kallo mai ƙarfi da laushi, sai kuma ya saki murmushin “Humm bazaki gane ba ne.....” “To ganar da ni”. Tai maganar tana ɗan hararsa. Matsowa yay jikinta sosai ya mannata da mirror ɗin, ya kamo hannunta ya zare cumb ɗin. Sai kuma ya ɗagata cak ya ajiye saman katakon mirrorn ya cigaba da taje mata gashin a hankali. Amma duk da hakan sai da ta riƙe hannunsa tana yamutse fuska kamar zata saki kuka. Daina tazan yay ya tsaya yana kallonta, ta sake cuna masa baki gaba da faɗin, “Besty! Wai mata basa aski?”. Dariya sosai ta bashi amma baiyi ba. Sai ya sumbaci bakin kaɗan yana kallonta gira a ɗan ɗage.........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣0️⃣

______________

.........“Ke yanzu idan akace kiyi aski sai kiyi?”. “ALLAH da gudu ma”. “Ai da yake baki da man kai”. “Eh naji ɗin banda shi, kai baka san zafin kitso bane”. Cikin wani shegen salon iskanci da iya shege ya sake narke idanunsa cikin nata. A yanyin raɗa ya furta, “Duk zafinsa ya kai DAREN AIKAIRI ne”. Wani kunya ne na bala'i ya lulluɓe Maanal. Da sauri tasa tafukan hannunta ta rufe fuskarta. “ALLAH baka da kunya. Nifa ƙanwarka ce”. “Da an shigo cikin ɗaki nake tashi daga Yaya ai, dan haka ni ba yayanki bane yanzu.” Ƙoƙarin tureshi tai zata sauka ya riƙeta yana dariya. Sai kawai ta kife kanta a ƙirjinsa. Murmushi yake mai ƙayatarwa, sai kuma ya samu damar tufke mata gashin nata a hakan. Yana gamawa ya kamata cak ya sauke a ƙasa. Aiko fitt tabar masa wajen. Bai dakatar da ita ba ya fara ƙoƙarin cire kayansa kawai domin canjawa zuwa na barci.. Maanal kam data gudu haye gadon tai ta kwanta, sai kuma ta ɗauka wayarta. WhatsApp ta shiga tana ɗan duba sakwannin, dan shi kaɗai take yi, bayan anan bata da account a kowanne shafi na media sai dai ta shiga ta ɗan yi kallon abu buwa a TikTok da Instagram tunda bata saye bata sayarwa, har YouTube ma takan je. A WhatsApp ɗin ma yawancin groups ne na makaranta, sai sakwanin taya murnar aure da suka tura mata pc, da masu ƙorafin rashin gayyatarsu da batai ba, sai na addini haka da class na abubuwa data ɗan shiga ta koya, mafi yawama girke-girke ne sai harkar zane dan tana son girki, bayan zane-zane. “Yanzu lokacin miji ne”. AA dake hawowa gadon ya faɗa yana zare wayar daga hannunta. Kallonsa tayi a marairaice ta ce, “Hiran group fa kawai nake gani sai sakwannin taya murna”. “Karki damu zan miki hirar ni, na kuma tayaki murnar auren”. Baki ta ɗan tura kaɗan, zatai magana ya hanata. Hasken ɗakin ya kashe gaba ɗaya ya bar musu ta barci datai dummm sosai. Sai kuma ya sake matsota sosai a jikinsa ya rungume. Ajiyar zuciya suka sauke a tare, a cikin kunenta yay mata raɗar data sakata kife fuskarta a ƙirjinsa tana ƴar dariya. Ta ce, “Nidai ba ruwana kai da Abah”. “Shima ya haƙura ya sallama. Alamar jikoki yake so da wuri”. Ƙaramin dundu ta masa a baya. Tare da kai bakinta kan kunensa ta raɗa masa, “ALLAH ka canja hali”. Shima sai ya raɗa mata. “Mudai canja, dan da an ganki da cikin ansan tare mukayi”. Tureshi ta shiga yi tana tirza ƙafa. Wata ƴar ƙanƙanuwar dariya mai tada tsigar jiki ya shiga yi mata yana sake matseta a jikinsa. Yayinda shima kukan shagwaɓar nata ke yamutsa masa garkuwar jikin nasa. Sai kawai ya shiga laluben lips ɗin nata, cike da nutsuwa da tarin ƙauna da shauƙi ya rufesa ruf da nashi. Tun tana ƙoƙarin son ƙwacewa harta nutsu ta sallama tana sake ƙanƙamesa. Ita in dai iya haka ne normal ne zata bada haɗin kai. A zarce nan ɗin ne hankalinta ke tashi. Sai ko daya bari ya shagaltar da ita da salonsa ta miƙa wuya gaba ɗaya sannan ya ɗauki layin da take tsoron. Ai ko a take ta firgice masa. Tana ƙoƙarin masa magiya ya rufe kowacce ƙofar yin hakan. Ta riga ta tsorata da al'amarin tun farko, dan haka yake tayar mata da hankali. A haka yau ma ya bita a sannu saboda ba kamar waccan ranar da shima yake a wani yanayi ba. Amma duk da yanda ya lallaɓata, ya riritata sai da tasha azaba, ta kuma dinga masa kuka hawaye share-share. Addu'a ta dinga yi a ranta ALLAH yasa ma ta suma kamar ranar, amma addu'ar nan bata karɓu ba kuwa, dan sai da ya samu yanda yake so ya barta. Ganin yanda ta galabaita ya sashi jin tausayinta sosai, dan shi da kansa yasan bana wasan yara bane tako wane fanni. Ita kuma dama can yasan tana da tsoro, duk tsiwar Maanal da iya takalar faɗa akwai tsoro, bata ƙaunar abinda zai taɓa jikin nan nata sam-sam. A wajen sit bath ma yasha shagwaɓa da kuka, shi har ma yayi tunanin koya sake ji mata ciwo ne. Bai samu natsuwa ba sai da ya dubata yaga lafiya lau sannan ya sauke ajiyar zuciya. A ransa kuwa yana tunanin lallai akwai daru kenan in dai haka za'a cigaba da kasancewa. Dan Maanal akwai shegen raki. Dama duk mutum mai baki ai sai a hankali ne, zaka samesu akwai ɗan karen rakin tsiya da tsoro. Sai da ya bata magani tasha sannan ta fara sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke ya rungumeta yay musu addu'a sai barci. Gabanin asuba kuwa ya farka cikin wani matsanancin yanayi, jinta a jikinsa kam ya sake tunzura. Cikin barci ta farka a firgice. Kuka ta sanya masa. Bai kuwa ƙyaletan ba dan ya fahimci sai ya mata da gaske zasu dai-daita, saboda ya daɗe da fahimtar yanayinsa. Kuma bashi da sha'awar ajiye mace fiye da ɗaya, kenan dole ya cire tausayi ya horar da ita a irin layin da zata iya ɗaukar lalurar tasa tako wane irin yanayi. Aiko rikicin datai masa yanzu sai da yafi na daren sosai. Sai da ya tabbatar ya samu yanda yake so nan ma sannan ya koma lallashinta. Yanzun ma shine ya gyara mata jiki, ya ɗakkota ya ajiye har kan abin salla dan langyare masa tai bazata iya ba. Shi ko yace yaji ya gani duk zai iya. Yana fita salla ta sama ƙofar key, salla tayi a gurguje tai azkar ta miƙe bama ta ƙarasaba ta haye gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya, anan ta ƙarasa azkar ɗin. Koda ya dawo ya ji ƙofar a rufe dariya ta bashi, amma koba komai ta tsira, dan da ace bata rufe ɗin ba babu abinda zai hanashi sake ziyartarta a safiyar nan. Fuskarsa da murmushi ya koma ɗayan ɗakin dake matsayin nata ya kwanta. Duk da dai yanzu sun raba kayansu biyu kowanne ɗaki akwai na kowa, dan yace babu batun raba ɗaki bai yarda ba. Sai dai duk inda suka so kawai suyi zamansu. Itama tafi gamsuwa da hakan, dan ko shi ya zaɓi su raba ɗin bazata yarda ba....

_________★

GIRO

A guje Sule ya shigo gida. Gwaggo na ƙofar ɗakinta zaune tana gyara ganyen kuka ya tsallaketa ya shige ɗakinta. Tana ƙoƙarin yin magana kawai ƴan sanda suka afko musu. Sosai gidan ya kacame matan dake a tsakar gida suna harkokinsu duk sun tarwatse sun afka ɗakuna sun banko ƙofa. Jikin Gwaggo ya fara rawa, ko ada sanda Babu ke zuwa da kaki ma tsoro take ji ta dinga masa masifa kenan har sai ya ciresu balle yanzu da tsufa ya sake razanata. Cikin tsawa ɗan sanda yace mata ina Sule. Fitsari na zuba mata zuuuu a zane ta nuna ƙofar ɗakinta. Ga hawaye share-share ta shiga rantsuwa da faɗin ita wlhy koma mi Sule yay babu hannunta a ciki. Su nemi uwarsa bata da alaƙa da Sulen. Ko takanta basu biba suka afka ɗakin, babu wani jimawa suka fito da Sulen, handcuffs suka sanya masa. Aiko ya tsaya yayma Gwaggo wani shegen kallo, cike da taurin kai da rashin ji ya ce, “Ke kuma zamu haɗe ne, ki jirayi dawowata na kwanaki ne. Kin san ALLAH garama kikai kanki maƙabarta kafin na fito. Ba dai ni kika tonama asiri ba, kika ce kuma baki da alaƙa da ni ko? Hummmm!!”. Ya cije baki. Tisa ƙeyarsa sudai ƴan sandan sukayi. Aiko matan gida sai leƙe ta windows, ga mazan duk basa nan suna daji ana gyaran gonaki saboda ruwa dake ta haramar sauka. Haka aka tisa ƙeyar Sule aka wuce da shi. Sai da suka tabbatar sun bar kusa da gidana gaba ɗaya sannan aka shiga fitowa kowa baki cike da gulma. Akan daɗe ba'a kama Sule ba saboda yana da shegen wayo, dan ko kame ƴan sanda suka shigo ƙauyen yasan yanda zai gudu. Yau ma dai da alama mamayarsa sukayi gaskiya. Dan in ba haka ba kama Sule ga ƴan sanda ai jidali ne babba. Amma koba komai ai suma sa ɗan huta. Ga Sailu bata gidan tana can yawan biɗiɗinta na tsiya. Hakama Haƙila tun safe ta fita da cin-cin da fara har yanzu ba'a dawo ba, dama tace Suru zataje. Rashin jin motsin Gwaggo yasa aka leƙata, sai gata zube a ƙasa firgici ya sakata sumar wucin gadi. Ruwa aka shafa mata ya farfaɗo, sai kuka wiwiwi tana jama Sule ALLAH ya isa. Kowa dai yasan dan taga baya nan ne ta samu baki. Su dai suka kamata suka shiga da ita ɗaki suka koma cikin gida gutsiri tsoma. A gigice Sailu ta dawo gidan, dan kuwa tun a hanya aka tareta aka sanar mata ƴan sanda sun kama Sule kuma Gwaggo ce ta tona. Tab ɗin, ai tana shigowa gidan Gwaggo ta taƙarƙara ta fito yin alwalar azhar kawai Sailu ta wanke fuskar tsohuwar nan da mari sai da Gwaggo ta zube ƙasa. Jikin Gwaggo na rawa kar-kar ga hawaye ta kalla Sailu ta ce, “Ni kika mara Sailu? Ni dana haifa miki Habibu kika daka?”. “An dake kin munafukan tsohuwa annamimiya, idan kika ƙara magana ma sai na sake wanka miki wanda haƙwaranki zasu zuba a ƙasa. Kuma wlhy ki sani in har wani abu ya sanar min yaro kema ki jira sakamako”. Tana gama faɗa ta fice a gidan. Shiru Gwaggo tai a zaune tama kasa kuka. Babu abinda ke dawo mata a rai sai fuskar Ammie. Ta tuno randa ta hana Babu zuwa inda Asiya take, sai cikin dare ya lallaɓo ya shiga, kawai gabannin asuba ta fito fitsari suka haɗe da Babu ɗin da Ammie sun fito daga bayi alamar wanka sukai tare. A fusace ta wani ɗauke fuskar Ammie da mari, ta sake ɗauketa da na biyu. Amma baiwar ALLAHr nan ƙasa kawai tai da kanta har ta wuce su ta shige bayin. Sai da ta shiga sannan Ammie ta wuce ɗakinta yana sharar hawaye, Babu kuwa tsoron Gwaggon bai barshi ya koma ba haka ya fice... Sharrr hawaye suka sake gangaroma Gwaggo, tabbas ta cuci kanta, ta tsige Asiya jinin Lubabatu da Umar daga jikinta, ta aurowa Habibu wadda ranta ke so, ga shi nan itama tana mata yanda take so ita da ɗan nata. Jikokin kuma da take ƙauna take ganin sunfi ƴaƴan Asiya suma suna tisa karatun uwarsu a a garesu........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖9️⃣1️⃣

______________

........Duk yanda AA yaso Maanal ta fita aiki yau dole ya haƙura. Dan da gaske fa ya jigatata. Haka dole bayan ya tashi ya haɗa mata break fast mai sauƙi da kansa, da ƙyar ya lallasheta tazo ta buɗe masa ƙofar data rufe. Duk da yana ganin zai makara haka ya haƙura ya taimaka mata ya gasa mata jikinta taci abincin ya bata magani sannan yay nasa shirin ya fita. Aiko ko Oum ta waya yay mata sallama. Hakama Mamy ta waya ya kirata yace tai haƙuri ya makara ya wuce. ALLAH sarki Oum ita sai ta fahimta tai murmushi kawai da binsu da addu'a. Mamy kuwa sai ta shaƙa. Amma batai magana ba saboda Aunty dake wajen. Dan yanzu sun haɗema Auntyn kai ita da Maman Saheeba da Saheebar basa zancen komai a gabanta. Shiyyasa ma tace zata wuce yau dan tana son ta tsira da mutuncinta....

Readers Also Read