Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 142

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 142

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 142: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 142. .......An fara gudanar da addu'a ga…

3,348 words

.......An fara gudanar da addu'a ga ma'auratan sannan aka fara abinda ya tara mutane. Biki ne irin na masu aji, babu hayaniya babu tarzoma babu juye kaji da lemuka a jaka. Komai yana tafiya a nutse kuma cike da armashi. Mawaƙa sunyi wasa yanda ya kamata. An kumaci an sha an gode ALLAH. Amare sunsha liƙi suda anguna. Dan Ameer da Yaya Fawzan sunsha rawa, babban Yaya ne dai baima miƙe ba. Amma sai da AA ya bishi har wajen zamansa ya liƙeshi da dollers (😌ato dan mu novel ne sai munyi liƙinmu, karnaji wata tace an hana liƙi a Nigeria mu Ramadhan B Hameed Taura ne shugaban ƙasarmu anan ba Tunbunu ba🤭 kuma yace muyi kayanmu yanda muke so, ko Tunbunu ya zama kuɗi sai mun liƙa shi ehe😜🤫). Ba ƙaramin wasa da kuɗi akai ba a wajen nan. Maanal da AA kamar basu san ciwon dollers ba. Yanda yake zarosu a aljihu haka take zira hannu a aljihunsa itama ta zaro ta farke. Hatta Oum da Ammie haka ta bisu har inda suke tai musu liƙi, AA ya tayata kuwa. Takaici kamar zai kashe su Hajiya Basariyya kuwa, sai dai babu damar magana sai tsaki a zuciya. Dama kuma Maanal dansu tayi hakan ƴar ƙunar baƙin waken🤣. Saƙonta kuma ya isa yanda ya kamata. Kuce min ina Nibras da Saheeba manyan mata. Suna gida abinsu basu zo ba. Duk da Saheeba tayi niyyar zuwa dan ita irin mutanen nan ne dako abu na ƙona musu zuciya sun fi son sugani ƙuryanan-ƙuryanan (Inji Ayshatu ɗan Kano😆 ALLAH ya gafarta mata da iyayenmu baki ɗaya 😭🙏). Sai da Hajiya Turai ta tsawatar mata sannan ta haƙura. Mamy ma dai yau bata zo ba. Dan abubuwan sun fara kwace mata ta tabbatar zata iya tonama kanta asiri a wajen. Maman Saheeba da Nuratu ma dai yau da yake abun su aka taɓa basu zo ba, suna tare da Saheeba sunata ƙullawa da kwancenwa a gida...

Alhamdullahi biki ya ƙayatar yanda ya kamata. Ba'a gajiyar da kowa ba ba'a takura kowa ba. Anguna da amare sun zuba capacity yanda ya kamata. Kafin kace mi wannan shagali ya zama on topic na wannan rana. Tako ina shike kai kawo a yanar gizo. Ƙarfe huɗu aka tashi, mazan ne kuma suka fara fita domin yo salla. Sai da suka dawo aka fara kwasar mutane zuwa gida. Matan ma na zuwa babu zama kowa burinsa ya sauke sallar. Manaal tunda ta idar take gyangyaɗi, amma ta daure dan tace yau ko mima za'ayi bazata kwanta ba sai anyi buɗar kai da ita. Aiko taga buɗar kai dan taci wuya. Ciwon kai har jiri ke kwasarta dan masifa ta dai dage sai da akai buɗar kan nan da ita. Yanda ta sakama Najma da Ameerah kuɗi har sai da ya zama abin magana a dangin Mamy. Al'amarin kam ya girgiza Mamyn matuƙa. Har sai da ta kasa dannewa ta ɗura zagi da faɗin ai Ajwaad ɗin zaizo ya sameta ne dan tasan daga aljihunsa kuɗin ya fito, dama yan uwan nata nata hirar irin ɓarnar kuɗin da AA ɗin sukai shi da Maanal a wajen taron. ALLAH sarki, sai dai abinda Mamy bata sani ba a kuɗin da Maanal tabada na buɗar kan su Ameerah sisin AA babu. Tana da kuɗaɗen ta na kyaututtukan da ta samu a bikinta account shaƙe, a hakama taba Ammie da yawa, dan bayan bikinta sai da ta turama Ammie, ta turama Didi Shahidah da Amaal harda su Waleed. Hatta Nene da ƴaƴanta kowa sai da ta bashi, kai har su Zeezah ƙawayenta bata manta da su ba da Amrah. Wanda suka rage kuma ba wani abu take saya ba, daidai da katin waya wannan da data Babban Yaya, Yaya Fawzan, AA duk saka mata suke. Sai dai kawai taga an turo mata. Hajiya Basariyya kanta sai da taji kamar ta zauna taita kuka. Dan jitai kamar sun rako mata duniya yau sukam, ƴar yarinya ƙarama take irin wannan ƙyautar babu ko gezau. To oho dai, sudai dangin Darma sunji daɗin halin girma da Maanal ɗin ta nuna ƙwarai da gaske. Ana gama buɗar kan su Ameerah aka shiga gidan Hajiya Shuwa akai na Maimoon. Suma sunyi rawar gani dan kowa yasan katsinawa da kara. A wajen gara da baye ba'a magana sun wuce tsara. Darma Family sun shaida hakan kuwa yau, dan gaskiya su Hajiya Shuwa suma sunyi ƙoƙari kamar yanda suma akai musu ƙoƙari akan na Maimoon. To aifa da kama-kama su Amaal suka kai Maanal sashenta dan juwa take gani matuƙa. Hankalin AA ya tashi sai da ya kira RK ya dubata. Oum ma nata faɗa, dan dama gaba ɗaya hankalinta ya rabu biyu wani akan buɗar kan wani akan Maanal dan tasan wannan rashin kwanciyar zata iya zame mata damuwa. Ita kanta Ammie data san yanayin duk inda Maanal ɗin tayi idonta na kanta. Daga baya kuma ta ɓace mata. RK yace su kwantar da hankalinsu da tayi barci zata tashi normal, rashin yin barcin ne ya kawo mata juwar. Dan haka yace AA ya taimaka mata tai salla tai wanka dan inta kwanta da wuya ta tashi a kusa maybe sai asuba. Haka ɗin kuwa akayi, bayan fitowarsu da kansa yay mata wankan, tai sallar daga zaune ya bata fresh milk ɗin tata ta fama tasha sosai. Shi kansa bai ƙara leƙa wajen ba tunda ya dawo daga sallar isha'i. Kajin da yay niyyar fita siyoma su babban Yaya sai order yayi, da'aka kawo ya fita ya amsa ya danƙama RK, dan yace babu shi a ƴan rakkiya. Na su Oum da suma ya saya musu yaje yakai musu ita da Ammie, itama Mamy ya aika mata ya wuce sashensa. Aiki yay zaman yi a kan gadon kusa da Maanal dake barci mai nauyi sosai. Lokaci-lokaci yana kallonta, musamman idan taja numfashi. Dan ƙwaƙwƙwaran motsi dai batayi. Dariyar data dingayi ɗazun ta mugunta ta shiga faɗo masa a rai sai yayta murmushi. Wayarsa ya ɗauka ya rubuta saƙo ya turama Yaya Fawzan yana cizar lips...

_______★

A ɓangaren anguna su Babban Yaya kamar yanda aka saba su Baba Sardauna sun zaunar dasu sun musu nasiha mai girma da nuna musu bambanci auren farko dana yanzu. Da a baya hakkin matan nasu ɗaɗɗaya ne a kansu. A yanzu kam su biyu ne. Nuna rashin adalci ko rinjaye a ɓangare ɗaya babban damuwace a rayuwarsu ta duniya da lahira. Dole ne su zama jarumai wajen tsayawa akan ƙafafunsu matsayin mazan ƙwarai a tsakanin matan nasu. Su zama masu adalci, kuma masu haƙuri da juriya dan ajiye mace fiye da ɗaya bana rago bane. Maza da yawa sukan ɗauka jarumtar ajiye mace fiye da ɗaya a shimfiɗane kawai, sai dai ba haka bane ba, wannan ma idan da hali a kallesa a matsayin matakin ƙarshe shine yafi dacewa a zamantakewar jarumtar. Idan ba haka ba kana nan kana hura hanci kai soja a gado ka tara mata huɗu, uku, ko biyu, amma kanata ginama kanka ƙofar shiga jahannama sakamakon kasa banbance hakkin daya kamata ka sauke da ruɗin duniya. Shi aure ibada ne, komai dake cikinsa kuma shine tubalin gina ibadar. Gwarzon namiji nutsuwa yake ya gina ganuwar adalci a cikin iyalansa da kewayansu, ba yazama shashasha mai tauye wata ya ƙuntatama wata ba. Karka wulakanta matarka ta farko dan ka ƙara aure, kar kuma ka wulaƙanta wadda ka aure daga baya saboda wai uwargida. Kalmar uwargida da amarya kalmace ta al'ada. Addini yana kallonsu ne da sunan matanka ne kawai. Kuma kowacce tana da hakkin a kanka da in ka gagara saukewa tofa ka shirya amsar sakamako a inda ba'a neman yafiya, ba kuma akarɓar tuba dan lokaci ya gama ƙurewa. Daga ƙarshe sukai musu addu'a sosai mai kuma ratsa jiki da ɓargo kafin suka sallamesu. Suna fitowa Babban Yaya ya gudu. Dariya su Uncle Najeeb suka sanya. Dama shi da Uncle Sulaiman Yayan RK ne masu rakkiyar tasa. Yaya Fawzan kawai akama rakkiya, babu kowa a sashen kuwa ta ɓangaren Najma dai, Ammie da kanta ta tattarosu, wasu suka koma sashen Maanal wasu suka zo nan sashen Oum. Itama Nibras ɗin kasancewar duk ƴan gari ne wanda ke tare da ita sun ware. Sai mutum biyu a tare da ita da Mommynta tace su zauna su kwana. Dan ana gama buɗar kai sai Nibras ɗin ta tsinta kanta a wani irin tashin hankali tanata kuka. Zuwa yanzu dai ta tabbatar da bata samu AA ɗin ba, shima Fawzan ɗin ya ƙaro mata wata. Gashi baya ɓoye farin cikin da yake ciki ko kaɗan. Yanzu ma tana jin hayaniyar ƴar rakkiyar Fawzan ɗin jikinta ya kama rawa. Bayi ta afka ta jingina da kofa ta fashe da kuka...

To shi dai ango baima san tana yi ba, sun isoko amarya Najma ne a ɗaki zaune a bakin gado kanta rufe a cikin lafaya.. Kasancewar su daga kawunnai sai yayye aiko tuni kowa ya kame girmansa akai mata nutsatstsiyar nasiha, ita dai tanata hawaye kanta a cikin mayafi bata ganinsu. Sai dai tana jin ƙamshin turaren Yaya Fawzan matuƙa a hancinta dan yana zaune ne a kusa da ita. Basu wani jimaba sukai musu sallama suka fice. Yaya Fawzan bai ma motsa ba balle su saka ran rakkiya. Dai-dai sun gama ficewar saƙon AA ya shigo masa a waya. Fasa maganar da yay niyyar yima Najma yayi ya ɗauka wayar yana dubawa. _(Ka bimin ƙanwa a hankali dan ALLAH Yaya Fawzan, karkace zaka rama abinda naima taka ƙanwar tsautsayi ne. Idan ba hakaba sai dai a rabamu a DSS office gaskiya da safe. A huta gajiya angon Najma)_ Murmushi Yaya Fawzan ya saki mai nauyi, sai kuma ya cije lips yana girgiza kai. Wato tunda Autan nasu fa ya shiga daga ciki bakinsa ya buɗe. Har mamaki yake idan yaji Ajwaad na zaro magana sai yaga kamar bashi ba. Ƴar gyaran murya yay yana ajiye wayar, cike da raɗa ya ce, “Amarsu baza'a buɗen fuskarba?”........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*09032345899*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣2️⃣

______________

.......Shiru Najma tai taƙi motsawa, sai yay murmushi, tare da kama lafayar ya yaye gaba ɗaya. Ganin hawaye share-share a fuskarta ya ce, “Oh oh kukan dai har yanzu bai isa ba ƙanwar Yaya Fawzan”. Sai ya jawota jikinsa kawai ya rungume. Kamar jira take sai ta sake sakar masa kukan. Shiru yay yana shafa bayanta a hankali, a cikin kunenta ya ce, “Kodai nima na tayaki muyi kukan kamar ƙyafi saurin gamawa da wuri”. Ƙwace jikinsata ta shiga ƙoƙarin yi tana ɗan kai masa dukan wasa a ƙirji kaɗan-kaɗan, ya sanya dariya yana ƙoƙarin riƙe hannun, kafin ya kaita kwance ya rufu a kanta yana bin fuskar tata da wani narkakken kallo. Baki ta tura masa. Ya ɗan ja lips ɗin kaɗan da faɗin, “Na tayaki kukan muyi saurin gamawa?”. Kanta ta girgiza masa. Ya ce, “To kema daina in gani”. Hawayen ta shiga sharewa da lafayar, sai da ta goge su tas ya ce, “Inyeee kaga amaryar Fawzan, kinfa daina kukan da gaske dama lallashina ake jira kenan”. Murmushi ya suɓucema Najma. Ta kauda fuskarta gefe tanayi. Shima murmushin yake mai ƙayatarwa, kafin ya maido fuskar tata suna kallon juna. Lips ɗinta ya ɗan sumbata tare da faɗin, “Karna ƙara ganin hawayen nan kinji ko. ALLAH yay miki albarka. Ya bamu zaman lafiya, ALLAH yasa yau mu samo Baby mai kama dake ƴar mutan Zaria”. Hannu tasa ta rufe fuskar ta da faɗin, “Nidai a'a”. “Miyasa?”. “Ba yau ba, yau bana jin daɗi, kuma mai kama da kai nake so dan mutan Darma”. Murmushi yayi da faɗin, “Ko kuma za'a min wayo ba. Dama yayanki ya turon saƙon gargaɗi, danna tabbatar masa sai na rama abinda yayma ma ƙanwata akan ki. Amma maimakon ya jira yaga yanda za'a ƙare har ya nuna karaya kamar ke”. “Ba karaya mukai ba muma, hanyar lafiya a bita da shekara ne kawai”. Dariya yayi mai ƙayatarwa, sai kuma ya tashi itama yana tadata ya ce, “Hakane kuma Love. Bara to na bi a hankali muyi tafiyar kunkuru. Oya muje alwala”. Sunyi alwala da taimakonsa. Bayan sun fito ya sanya musu sallaya suka gabatar da salla. Kazar da AA ya siya musu yace tazo suci. Tace ta ƙoshi. Murmushi yayi da kulawa yace, “Yayanki ne ya saya miki fa bani ba balle kiyi tunanin zance ki biya ni. Oya come and eat ba abinda zai faru”. Babu yanda ta iya dole taci kazar nan sai dai babu sakewa, hasalima bata mata wani daɗi ta riga ta sakama kanta damuwa da tsoro. Ya fahimceta tsaf sai kawai yay murmushi. Fita yay yace tai shirin barci. Shima zaije yayo. Kanta ta jinjina masa, yana fita taita addu'a ALLAH yasa matarsa ta hanashi dawowa. Da wannan addu'ar ta daure tai shirin barcin, ta ƙara shafe lungu da saƙo na jikinta da ƙamshi sannan ta kwanta zuciyarta nata rawa. Waya ta ɗauka ta turama Maanal saƙo, sai dai shiru fin minti biyar babu reply. Ta fahimci tayi barci dan haka ta haƙura ta ajiye wayar tai lamo a kwance....

Fawzan kam na fita sama ya haura ɗakinsa. Babu kowa a falon, amma duk datti bai samu gyaran arziƙi ba kamar yanda aka gyara ƙasan aka saka turare mai daɗi. Kansa kawai ya girgiza ya shige bedroom ɗinsa. Yana cikin zame kaya zai shiga wanka aka turo ƙofar aka shigo. Haka kawai yaji a ransa Nibras ce. Duk da bai tsammanin ganintan ba amma yasan ita kaɗai ce dai zata shigo masa ɗaki haka kai tsaye. Ita ɗin ce kuwa, sanye cikin kayan barci da sukai mata ƙyau. Dan ma ramar da tayi a bayyane take ga mai kallonta. Sannan kallo ɗaya ya fahimci tayi kuka. Bai tanka mata ba ya wuce closet abinsa. Ta bishi da kallo zuciyarta na zafi. Sai kuma ta cije baki tana hararrar inda yabi. Ƙofar ɗakin ta sakama key, ta nufi bayan gado ta ɓoye key ɗin inda bazai taɓa tunanin ta saka ba. Sannan ta koma gadonsa ta haye ta kwanta. Abinma abin dariya, wadda ake kawowa da tsiya-tsiya ce yau ta kawo kanta, lallai Najma kinzo da ƙarhinki😜. Malam ango Yaya Fawzan, tsaff aka gama gyara jiki aka fito ana zuba murmushin yau za'a sha warkajami. Amma mi sai idonsa ya sauka akan Nibras dake kwance a gadonsa ɗai-ɗai. Kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya ciro kayan barci ya saka masu taushi da ƙyau. Sannan ya feshe jikinsa da kalolin turare masu tsada da bala'in ƙamshi. Daga closet ɗin ya fito gaba ɗaya ya nufi wajen mirror kamar bai ganta ba ya gyara sumar kansa da kwantacen gashin fuskarsa sannan yazo ya ɗauka wayarsa a bed side drawer ya nufi ƙofa batare daya dai tankama Nibras ɗin ba. Sai me yana taɓa ƙofa yaji gam. Ya murza handle ɗin ya sake murzawa amma ko motsi alamar tabbacin a kulle take. Juyowa yay ya zubama Nibras ɗin ido, cikin hana kansa hasala ya ce, “Miyasa kika kulle ƙofar nan?”. Shiru ta masa taƙi ko motsi. Ya sake magana nan ma tai shiru. Sai ya tako ya dawo cikin ɗakin ya tsaya a bakin gadon nesa kaɗan da ita ya ce, “Bani key”. Sai yanzu ta kallesa ta watsar, sai kuma ta taɓe baki tace, “Ka bani ajiya ne?”. Shiru yay yana kallonta, ya dai hana kansa yin fushin da take son yayi ya ce, “Amma kin san bana cire key a ƙofa, kuma kece kika shigo bayan ni. Mima ya kawoki ɗakina yau?”. “Oh ka cireni daga matarka ne da har kake tuhumata miya kawoni ɗaki?”. Wani banzan murmushi yayi yana jinjina kansa. Sai kuma cikin taɓe baki yace, “Kema kin san cireki a wannan matsayin babu rana kam, dole ki cigaba da zama a inda baƙya so, ki kuma cigaba da ganin abinda baƙya so, ki kuma dinga hangen abinda kike son a haramun gareki na har abada.” Sosai kamalamsa suka daketa, suka kuma ciji zuciyarta ƙwarai da gaske. Dan har sai da tai ɗan jimm tana kallonsa alamar maimaitasu take a zuciya tana musu fashin baƙi. Barin inda take yayi ya nufi closet duba sauran keys ɗin, sai dai abin mamaki babu ko ɗaya alamar duka ta kwashesu kenan. Baice komai ba ya dawo inda take, camak ya birkiceta yana dubawa a jikinta har cikin b ɗinta dan yasan zata iya sakawa amma babu. Ya duba bed side drawer nan ma haka, ya koma ta mirror nan ma haka. Sosai ransa ya fara ɓaci, cikin tsawa ya ce, “Nibras bani key kafin daga ni har ke rayukanmu su ɓaci yanzun nan”. “Oh oh yo su ɓaci mana. Key ne dai wlhy bazan bayar ba ko zaka kasheni, sai dai mayyar ta kwana ita kaɗai”. Shiru yay yana kallonta. Ƙasan ransa yana mamakin shi kuma take kishi yau, kai lamarin wannan yarinya sai ita. Tunda ya fahimci fitina take son suyi bako zai biye mata ba. Komawa yay wajen sofa ya kwanta, ya ɗauka wayarsa ya shiga kiran Najma. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗaga cikin yanayin barci amma a zahiri pretending ne. Shima ya fahimci hakan sai yay murmushi. Ƙasa-ƙasa yace, “Kina nufin har kinyi barci baki jirani ba Love!?”. Cikin shagwaɓa ta ce, “Ai nasan ka gaji Yaya, kaima zakai kwanciyarka ne ka huta abinka, shiyyasa ma na kwanta harna rufe ɗaki”. “Anya ya dace amarya ta rufema ango ɗaki a daren farko?”. “Yaya ba daren farko bane ai ka manta na uku ne, yau fa kwanana biyu na uku zanyi”. “Uhm haka ne kuma fa. Love mai wayo”. Murmushi Najma tai mai sanyi tana rufe fuskanta kamar tana a gaban shi. Shima sai ya murmusa da sake sauke murya a ƙasa ya ce, “Da gaske kina son na barki ki kwana ke kaɗai?”. A sanyaye tace, “Eh ALLAH kuwa, kaga akwai gajiyar hidima yau ansha zirga-zirga, ga iyayenmu duk basu tafi ba. Please Yaya kayi kwanciyarka, nima na kwanta anan kawai”. Murmushi yayi yana cije lips. Jikinsa gaba ɗaya ya gama saki. Wani irin buƙatar son kasancewa da ita yake ji ƙwarai da gaske. Amma sai ya sauke ajiyar zuciya. Cikin sirkawar murya yace, “Shike nan na barki Love, kiyi barci cikin aminci. Amma ya kamata nazo ko ɗan goodnight kiss a bani ai ko?”. “A'a basai kayi wahalar dawowa ba zan maka daga nan. Muhchhh!!!”. Ta sumbaci wayar tare da yankewa ƙitt. Sosai Fawzan yay sumar kwance, sai kuma ya runtse idanunsa yana mai cije lips tare da karanto addu'a domin samun saisaituwar lamarinsa. Ƙyaleta yay bai sake kira ba. Yay shiru yana tunani sai ya juyo dariyar Nibras cike da ƙularwa. Da ƙyar ya iya danne zuciyarsa yay mata banza. Amma wlhy ji yake kamar ya tashi ya lakaɗa mata dukan ban gishiri. Amma ba komai, baya buƙatar ramawa ta haka. Tunda tace da shi zatai game zata sha mamaki wlhy. Tasowa yayi yazo ya hau gadon ya kwanta, ya kashe fitilar ɗakin yana jinta tana ƴan waƙe-waƙen iskancinta yaba banza ajiyarta. Aiko ya jima kafin barci ya ɗaukesa, ita ko baima san lokacin da tai nata barcin ba........✍️

🤣🤣Ashe Nibras ɗin nan hegiyar kanta ce ina tausayinta

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣3️⃣

______________

Readers Also Read