Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 143
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 143: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 143. .......Anan ko Babban Yaya yana…
3,214 words
.......Anan ko Babban Yaya yana garden abinsa yana aiki, sai da yaga sha ɗaya tayi sannan ya taso. Har lokacin gidan da ƴar hayaniya sai dai bamai yawa ba. Amma ganin fitilu akowane sashe idan ka cire sashen su AA ya fahimci wasu basuyi barci ba kenan. Sashen nasa ya shiga, kai tsaye ya wuce sama ɗakinsa. Yana jiyo ƙus-ƙus a ɗakin Saheeba baibi takai ba. A nan ɗin ma dai kowa yabar sashen ƴan uwan su Ameerah duk sun koma gidan Hajiya Shuwa. Sai Saheeba dake can a ɗakinta tare da uwarta da Nuratu da Hajiya Turai. Kuka take yi suna lallashinta. Sai maimaita masu take ƙirjinta kamar zai fashe. Sudai sunata tausarta ga ruwan rubutu an bata ta sha. Daga haka suka shiga kitsa abubuwansu har Baban yaya ya shigo bama su sani ba. Dan jin ba'ai masa rakkiya ba sunyi tunanin ma bazai kwana a sashen ba yau ma tunda gidan akwai baƙi har yanzu. Wanka Babban yayi ya canja zuwa kayan barci masu laushi da nutsuwa. Ya feshe jikinsa da turare sannan ya fito. Har yanzu yana jin ƙus-ƙus a ɗakin Saheeba. Yay ɗan jimmm sai kuma ya wuce abinsa kawai ya sauka. Bai san minene RK ya bashi ba yace inji Ajwaad, amma dai yana jin ƙamshin nama da zafinsa, sai dai zuwa yanzu ya huce dan haka ya nufi kitchen da ledar. Koda ya buɗe kuwa kaza ce lafiyayya da hadin salad, sai fresh milk. Kazar ya cire ya saka a bowl ya ɗumama. Sannan ya canja mata bowl ya saka a tray da plate ya saka madarar da cups guda biyu ya fito. Taku yake a hankali har ƙofar ɗakin da Ameera take ciki. Yay ɗan jimmm kafin ya murɗa handle ɗin a hankali ya shiga. Ameerah na kwance barci ita yama fara ɗibarta dan tayi tunanin bama zai shigo ba tunda gidan da baƙi, harta gyara jikinta ta canja lafayarta zuwa kayan barci masu ƙyau da laushi sai ƙamshi mai daɗi ke tashi a jikinta da ɗakin. Buɗe ƙofar ta sa ta farka, sai dai da yake fitilar ɗakin na a kashe sai lamp ce kawai a kunne ta gefenta itama ta sa hasken kaɗan sai ta buɗe ido tana kallonsa ta ɗan duhun. Tana ganin zai kunna hasken ɗakin ta maida idanun ta sake lumshe wa. Fitilar ya kunna mara haske sosai, kafin ya cigaba da takowa a hankali har zuwa bakin gadon. Ya ajiye tray ɗin a ƙasa ya kai zaune gefenta jikinsu na gogar na juna. Sai da ya mata kallon fin minti ɗaya kafin yay magana cikin miskilar muryarsa. “Uhmm dama amare na barci a ranar daren farkon su?”. Murmushi tayi amma bata motsa ba. Sai shima ya murmusa. Tare da kai hannunsa a karo na farka ya dafa ta. “My Soha ince kin min alƙawarin yau gaba ɗaya tawa ce ni kaɗai? Mizai sa kuma ki ƙare da pretending?”. Yanzu ma murmushi tayi, ƙasa-ƙasa ta ce, “Ba pretending nake ba barci nake da gaske. Dan na zata kaima ka kwanta”. “Uhm-uhm my Soha, ango yay barci shi kaɗai a daren farko ai babu lafiya kenan, dole a nemo likita ya duba shi”. Kaɗan ta jiyo ta kallesa, zatai magana ganin ita yake kallo shima sai ta kasa tai ƙoƙarin juyawa. Murmushi ya saki a karo na farko, sai kuma ya kamata ya ɗago ya zaunar. Kallonta yake sosai, hannunta na cikin nashi yana murzawa a hankali. Ita dai kanta a ƙasa ta gagara kallonsa. Fin minti ɗaya suna a haka kafin ya ɗaura hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta da ƙyau. Cikin matso da tashi fuskar gab da tata ya ce, “Mi my Soha taci?”. Idannunta a lumshe ta ce, “Sohan ka bata jin yunwa”. “Ban yarda ba, dan bazan yarda ta kwana da yunwa ba gaskiya”. A hankali tai ƙoƙarin buɗe idannunta a kansa, sai kuma ta kauda kai dan bazata iya jurar kallon nasa ba. Shima sai bai matsa ba ya jawota jikinsa a karo na farko ya rungumeta tsam-tsam. Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Cikin kunne ya raɗa mata abinda ya sanyata jin kunya. Tako ɓoye fuskar tata sosai a jikinsa. Murmushi yayi na tsawon lokaci, kafin ya ɗagota tare da miƙewa ya taimaka mata itama ta sakko. Gaban tray ɗin ya zaunar da ita shima ya zauna. Sai kuma ya matsota jikinsa cike da kulawa ya dinga bata naman da kansa. Itama sai ta dinga ɗiba tana bashi a kunyace matuƙa. A mamakin su sunci sosai, da alama duk suna jin yunwa dama. Hakama fresh milk ɗin sun sha, ya tattare komai ya maida gefe sannan ya sake ɗagata yace, “Oya muje ai brush da alwala.” Batai musu ba ta bishi, tana jin tsoron, amma tana gani zai ɗaga mata ƙafa yau kodan baƙi dake gidan. Musamman yanda bai nuna mata komai a kan hakan ba har yanzu. Sunyi brush ɗin tare da alwalar suka dawo. Ya saka musu sallaya sukai sallar. Ya dafa kanta yay addu'a kamar yanda addini ya koyar da mu sannan yay mata nasiha akan yanayin zamansu a yanzu. Ya kuma bata haƙuri akan nanda ɗan lokaci itama za'a gama nata sashen ta koma. Cike da girmamawa tace babu komai. A hakan ma ai normal ne tunda sashen babba ne. A hakan ma sai mutum yaso wani zai san da wani. Dan ko bedrooms ɗin ƙasan an killace su ne a gefe saima ka shigo falon ka gama bulayinka baka san da su ba. Yaji daɗin sauƙin kanta, dan haka ya miƙar da ita yana faɗin, “Saura barci, dan na gaji matuƙa kwana biyun nan babu hutu”. Murmushi kawai tayi batace komai ba. Da taimakonsa ta hau gadon ta kwanta, maimakon shima ya kwanta sai ya zauna yana ɗan duba wayarsa. Sai da ya bata damar nutsuwa a kwancen na kusan mintuna goma sannan ya ajiye wayar ya kashe fitilar ɗakin ya kwanta. A hankali ya nutsata jikinsa, cike da hikima da halin girma ya raɗa mata, “Kinyi barci baki kwaranye ma mjinki kishirwar dake damunsa ba My Soha!”. Gaban Ameerah ya faɗi, amma sai ta daure ciki-ciki ta ce, “Ayi min afuwa na gaji ne kawai, kuma kaima ina son kayi barci ka huta”. Murmushi yayi yana shafa bayanta cike da wayo, kamar bazai amsa ba sai kuma ya ce, “Karki damu zan sauke miki gajiyar gaba ɗayanta tabi iska, na lulluɓeki da ɓargon samun lada mai aminci. Sannan na biki da addu'ar shiga aljanna kusa dani in sha ALLAHU”. Har cikin rai taji kalaman nasa, dan haka ta ɗan sake nutsa jikinta tana sauke numfashi. Batayi magana ba, shima kuma bai bata damar yin ba ya ɗago fuskanta ya manna lips ɗinsa akai. Daga haka wasan ya fara canja salo zuwa na gaskiya. Tun tana tunanin iya takalar faɗan zai tsaya harta fahimci yaƙin za'ai babu ɗaga ƙafa. Abinka da manya da suka gama sanin wacece macen a zahiri da baɗini cikin hikima da tausasawa yake binta. Ita kuma tana nuna dauriya da jarumta duk da a sharar fagen ta bada haɗin kai itama. Sai dai fa a fagen ni sabun shiga ce kuka ta sanya masa da roƙo na yayi haƙuri ya barta. Amma ina Babban Yaya ya kwace da yawa, addu'a ce kawai zata iya tarosa maybe a wannan yanayin. Dan kuwa ya shiga wata sabuwar duniya ce mai abubuwan ban mamaki da al'ajabi. Kafin yau idan akace mata suna suka tara, ko matan nada banbanci sai yay ta mamakin ta ina? Kuma ta yaya? Wani lokacin har ƙaryatawa yake a zuciyarsa. Dan a ganinsa duk mace dai ai sunanta mace kawai. Amma a yanzu kam ya shaida ya kuma fahimci inda aka dosa tsaf sai dai ya zama malamin wasu kuma. Ba Ameerah data fita a hayyacinta ba take shan kuka shi kansa badan kar ace yayi abin kunya ba kukan zai sanya wlhy. Amma dai kada girma ya faɗi bara ai ta kurma kawai. To lallai kuwa ta kurman akai, dan faɗan kurma nacinsa yawa ne da shi har sai ya fanshe yake iya haƙura.....
Anan ɓangaren su Maman Saheeba bayan sun gama tausarta da tsara mata makirci kala-kala suka fito domin tafiya suka barta da Nuratu. Sun fito da tunanin ai Baban yaya bai shigo ba Hajiya Turai tace, “Nikam Nana rakani naga amaryar ma. Dan ina son ma na karanci yanayinta”. Babu musu Maman Saheeba tace, “Muje”. Maimakon suyi hankali ganin fitilar falon a kashe su fahimci kodai mai gidan ya shigo sai da yake kan baya ja basuyi wannan tunanin ba suka tunkari inda bedrooms ɗin suke. Aiko suna isowa gaban na farko babu shiri suka ja uban birki, jiki na rawa Nana ta kama hannun Hajiya Turai suka juya suka fice suna bige juna. Saida suka fito gaba ɗaya sannan Hajiya Turai tace, “Ikon ALLAH dama munafukin mutumin nan ya shigo? Yau kuma jarabawar data sameku na jiyo Ajwaad nima ta ritsa dani.” Gaba ɗaya Maman Saheeba ta kasa magana. Dan gaskiya al'amarin yazo mata a bazata bakamar nasu AA da sukai da gayyaba daman. Sunja tsahon lokaci bata iya cema Hajiya Turai komai ba. Harma ta fidda ran zatai maganar..........✍️
🤣Wanda bai ji bari ba dai. Tsoffin kawai🙄
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣4️⃣
______________
Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍
‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah! MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!
Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:
Gyaran gashi da kitson zamani
Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido
Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai
Kayan gyaran fata na gaske
Lalle mai kyau da salo na zamani
Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi
Shirin amare da na musamman
Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya. Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.
Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.
Tambaya/Booking: WhatsApp: 08062991549 Kira: 09016108092 / 08064532391
Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge. Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge
____________
........Ita ko Saheeba bayan fitarsu bathroom ta shiga, hawaye sun gagara tsaya mata sai kissima abinda zai faru yau tsakanin Babban Yaya da amarya take. Ita ta sani bazai iya kauda kai ba wlhy, musamman da suka jima basa taren nan. Kuka ta sake ɓarkewa da shi tana jerama familyn Darma kaf ALLAH ya isa da tsine musu. Tare da addu'ar in sha ALLAHU suma duk sai amma yaransu kishiya. Tadai gama bore-borenta ta fito. Ta canja kayan barci maimakon ta kwanta abinta dan Nuratu harta fara barci sai shaiɗaniyar zuciyarta ta ingizata wai taje taga ko Babban Yaya ya dawo. Haka kuwa ta fito, ɗakinsa ta nufa, tana buɗewa uban ƙamshin turarensa daya baza ya cika mata hanci. Ta kunna fitilar ɗakin, babu kowa a ciki sai alamun anyi amfani da ɗakin ta gani. (Kenan ya dawo har ya tafi ɗakin shegiyar ita ko sallama bata samu ba) Ta ayyana a zuciyarta. Ɗakin ta rufe ta shiga sakkowa ƙasa, (idan ka saba abu, ko a karan kanka saika aikata shi kake jin daɗi koda zaka cutu) ɗabi'ar laɓe ta riga ta shigi Saheeba ƙwarai da gaske. Duk da duhun falon haka ta dinga tafiya cikin sanda da laluben hanya har bedrooms ɗin Ameerahn a yanzu. Yes tafa ji kukan Ameerah kafim ma ta ƙarasa ga ƙofar amma ta fi yarda da gara dai ta matsa sosai ta tabbatar duk da yanda zuciyarta ke duka da ƙarfi kamar zata buɗe ƙirjinta ta fito. Aiko harda su kanga kunne a jikin ƙofar, tako jiyoma kunnenta abinda yafi wanda take buƙatar jin. Dan har babban gwaska taji nasa kalamin. Kar-kar jikinta ya fara rawa, hawaye suka ɓalle suna rige-rigen zubowa. Ruff idannunta suka mamaye da duhu alamar jininta ya haura sama sosai irin lokaci ɗayan nan na bazata. Da ƙyar ta iya riƙe ƙirjinta dake bugawa kamar zai buɗe ta fara bin bango tana jan numfashi da ƙyar. Kaɗan ya rage itama dai ta maimaita na Mamy a stairscase, ALLAH dai ya taƙaita mata wahala sai tuntuɓe da tayi ta fasa babban yatsar ƙafarta. Tana zuwa stairs na kusan biyar ɗin ƙarshe tafiyar ma ta gaggareta dole ta duƙe ta koma rarrafe. Da haka ta ƙarasa kai kanta cikin bedroom ɗinta sai Nuratu jin nishinta tayi da kakari. A fitgice ta tashi tana kallon ta, sai kuma ta sakko tana faɗin, “Aunty lafiya kuwa?”. Ina Saheeba neman shiɗewa take, dan a rayuwa kunnenta bai taɓa juyo mata mummunan al'amari irin wannan ba. Bata taɓa jin nadamar yin laɓe ba irin yau. Ko lokacin da suka ji na Maanal ita batai ko gezau ba Mamanta ne da Mamy suka ruɗe. Da ƙyar Nuratu ta kamata zuwa kan gado, ta bata ruwa tasha. Kamar jira tana gama shan ruwan ta ɗaɗe da kuka. “Na shiga uku Nuratu, na shiga uku. Shike nan wlhy nasan ma na rasa Daddyn Naufal, na rasashi an aura masa mayya ƴar masu asiri da tsafi azzalumai sun rabani da mijina, sun rabani da shi shike nan na mutu ni Saheeba. Yau ni da kunnena nake ji Daddyn Naufal na jerama wata manyan kalaman da bai taɓa ambata min ba koda wasa duk ƙoƙarin da nake na shan abubuwa dan faranta masa rai. Wlhy ko uhum bayayi idan yana tare da ni. Nuratu surutai fa yake, yana jera mata zantuka masu girma da nuna mutuntawa da jaddada mata ita ta daban ce, tafi sauran mata, bai taɓa sanin mace haka take ba se yau, kenan ma ni ashe baya jina a ransa, na shiga uk......” kuka ya sarƙeta ta kasa ƙarasawa. Cikin takaici Nuratu ta ce, “Kai aunty wai laɓe kikaje kima Yaya? Ina gaya miki gaskiya akan wannan halin amma baƙya yarda, ai gashi nan kin jiyo abinda yafi ƙarfinki. Wannan banzan halin da kuka iya keda Mama haka kuka sakani naje na jiyo a sashen Yaya AA ni da Mamy gashi nan har yanzu na kasa samun zaman lafiya a rayuwata, ina ƴar ƙarama dani hawan jini ya haye min. Sau dubu zanga matarsa yanzu sau dubu abinda ya faru yake faɗo min a zuciya. Hakan kuma na sakani ganin ta min nisa, ta mamaye komai ta yanda koda zan samu sai dai saura, jina nake kamar Maanal ta fini daraja da cika mace. Balle ke dake tare da mijin nan har kije ki musu laɓe a irin wannan ranar, wannan lokacin. Mtsowww! Kin cuci kanki”. Kuka sosai Saheeba keyi, kalaman Nuratu na sake ƙona mata zuciya. Har ji take ƙirjinta na mata wani kalar turiri na hayaƙi. Taci kuka sosai har asubahi bata huta ma kanta ba. Nuratu kam tuni ta juya tai barcinta bayan itama ta gama nata hawayen tunawa da AA maybe shima yana can yana nashi karatun, ta tuna yanda ya wani rungume Maanal a ɗazun da goyatan da yayi. Ita dai ALLAH ya rufa mata asiri barci ya saceta tabar Saheeba a halin ha'ula'i...
______★
Alhamdullahi da asuba garas Maanal ta farka. Gashi ma sun makara salla dan AA yau ya jima bai kwanta ba yanata aiki. Ana yin sallamma a masallaci Maanal na buɗe idanunta. Akansa ta sauke dan yana kwance ne kusa da ita sosai kansu a filo ɗaya. Yanda fuskarsa take a haɗe sai abin ya bata dariya. A zuciyarta tace (a cikin barci ma miskilanci ake Namijin duniya) a zahiri kam yatsarta ta saka akan lips ɗinsa ta shiga zagayawa a hankali. Fin minti ɗaya kafin idanunsa su fara motsawa, sai kuma ya kawo hannu ya riƙe nata da take zagaya masa a lips. Murmushi ta saki, sai kuma cikin raɗa tace, “Baby open your eyes”. Kamar mai controlling nasa da remote a hankali ya buɗe idanun a kanta. Sun kaɗe sun kumburo irin na mai barci. Yanda take kallonsa lips ɗinta a cikin baki tana ɗan murmushi ya sashi yin yanayin kamar ɗan shagwaɓe fuska. Murmushi ta sake sakar masa tana jan hancinsa. Sai kuma ta kama kumatunsa ta ɗan matsa bakin yay kamar na yara na shagwaɓa “ALLAH shagwaɓa na maka ƙyau. Look at your face, just like a baby doll”. “No, I'm not! You're the baby doll, note me”. Ya faɗa a hankali yana tura lips. Murmushi ta sake saki mai faɗi tana shigewa jikinsa sosai. Ta ce, “Nima na girma ba baby bace, kai ne dai baby na tunda kana.......” sai kuma ta matsar da bakinta kusa da kunnensa ta ƙarasa raɗa masa sauran maganar. Murmushi ya saki har haƙoransa na bayyana, yana motsawa ta zille daga jikinsa, kafin ya cafkota harta dire a gadon tana dariya. Binta yay da kallo yana murmushi, sai kuma ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa har lokacin da murmushin dai a fuskarsa. Agogo ya kalla, har shida tayi, ya ɗan waro idanu yana sakkowa da ambaton, “Suhanallahi, haka muka makara yau ”. Bayi ya nufa agurguje, dan a duniya wucewar lokacin salla na ɗagama AA hankali. Yana ƙoƙarin shiga Maanal na ƙoƙarin fitowa, ta bashi hanya ya shiga sannan ta fito. Jiranshi tai ya fito yay musu jam'i. Sai da suka idar ya ɗan samu nutsuwa, amma yanata istigafari da ƙwacewar lokacin sallar. Jikinsa Maanal ta kwanto tana faɗin, “Good morning Bestie”. Sai da ya duƙo ya sumbaci lips ɗinta sannan ya amsa da “Barka da safiya Zuciyar Ajwaad. Yaya jikin?”. Cikin ɗan girgiza kai ta ce, “Ni lafiyata lau, kawai barcin nan dana ɗorama kaina ne dan jiya banyi ba ya nema zame min ƙalli-ƙalalla. Amma zan dage na daina, shiyyasa bana son sabama kaina abu sai kaga ya zamar min jidali idan ina son dainawa”. Murmushin gefen baki ya ɗan sakar mata yana shafa kanta. Muryarsa da sanyi-sanyi ya ce, “Anya zaki iya kuwa Basty, wannan fa nada banbanci da na baya”. Sai da ta ɗan zuba masa idon mamaki sannan ta ce, “Miya banbanta su. Naga dai duk barci sunansa barci”. “Uhmm kumafa haka ne gaskiya. Amma wannan ya shiga jikinki da yawa daina shi da alama sai ansha yaƙi kin san barcin cizon sauro daban ne”. “Uhm-uhm ni ka daina min fatan tsiya. Kuma babu sauron daya cizan”. “Tom na bari”. Ya faɗa yana mikewa da ita zuwa saman gado. Tana buɗe baki zatai magana yace, “Karma kice komai, yau babu wani kitchen da zaki shiga da safen nan. Nima zanci duk abinda aka girka a gidan gaba ɗaya oya sleep”. Baki ta tura masa tana ɓata fuska. Ya ce, “Naji dai”. Ganin zatai magana kawai ya rufe bakin nata da nashi. Tun yanayi kamar wasa har kiɗan ya canja salo, ya ɗaukesu cancak zuwa wata duniyar....
______★