Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 145

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 145

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 145: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 145. Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna…

2,494 words

Anan Abuja ana bidiri, acan Kaduna kam al'amari ne babba ya faru. Ammie da Hajiya Basariyya duk suna nan Abuja wajen biki. Yaran Hajiya Basariyya suna Zaria suma basu koma Kaduna ba. Hakama Daddy tun ranar ɗaurin aure daya taho da Hameed da Waleed basu koma Kaduna ba ya zauna yin wani aiki da da Yaya Yazeed ne keyinsa. Shigowar wannan matsalar tashi kuwa duk ya saki abubuwan ya tare a jikin Nazeera. Sai abinda tace yayi yake yi. Shiyyasa Daddyn ya dakata yin aikin Hameed na taimaka masa duk da yaron sai yanzu ne yake js2 a Secondary. Amma da yake yana da kwazo da fahimtar abubuwa sai Daddyn ke sashi yana taimaka masa da ƙananun abubuwa. Hajiya Yaya ita kaɗai ce a gidan sai ƴaƴanta. Sai Nazeerah da Yaya Yazeed da sai ma ka jima bakaji motsinsu ba. Tunda Daddy yabar gari mijin Sabuwa biye yake da shi, dan haka shima anan yake nasa shiri. Yau kuma daya kammala komai yay kiran Yazeed a waya. Lokacin yana ɗan barcinsa da Nazeerah ta barsa yi da ƙyar, dan jarababbiya ce ta bugawa a jarida. Shi kuma gashi ALLAH bai yosa mai yawan damuwa ba. Indai ya samu ya biya buƙatarsa dan kwana biyu uku ma sai ayi bai nema ba. Amma ita babu fashi babu ɗaga ƙafa. Kuma dole yay mata yanda take so babu abinda ya shalleta da baya ra'ayi. Wayar ta katse aka sake kira, cikin haushi Nazeerah ta ɗauka da nufin kashewa sai taga sunan Babanta. Aiko wani irin duka ta ɗakama Yazeed ya farka a firgice. Harara ta watsa masa tare da jefa masa wayar tana faɗin, “Kaifa wani lokacin wawa ne, to ihu zaka mana da”. A jiyar zuciya ya sauke. A ƙasan ransa yana jin zafin zagin data masa, amma a zahiri sai yace, “Kiyi haƙuri na tsorata ne.” Tsaki taja ta maida kanta ta kwanta, cike da wulaƙanci tace, “Tashi kaje can falo ka amsa bazaka daman ba anan barci zanyi. Shima Daddy ya wani kama kiran mutane a cikin dare suna hutawarsu. Mtsowww ”. taja tsaki. Jallabiya Yazeed ya ɗauka ya sanya, sannan ya fita dai-dai kiran baban Nazeera ɗin na sake shigowa. Cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya shiga gaisheshi harda duƙunnawa kamar yana a gabansa. Daga can baban Nazeera ya amsa cike da isa, kafin cikin bada umarni ya ce, “Yazeed kana jina”..........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣7️⃣

______________

........“Eh Daddy ina ji”. “Yauwa aiki zan saka ka yanzun nan. Kaje sashen Babanka ka buɗe wardrobe ɗinsa ka bincika min ko ina na cikinta ka tattaro min takardun duk wata kaddara da dukiyarsa. Ka ɗaga har ƙasan gado. Na baka daga nan zuwa asuba zan kiraka ka fito waje ka kawo min”. Ɗan jimm Yazeed ɗin yayi, baban Nazeera ya daka masa tsawa. A firgice ya ce, “To Daddy an gama an gama kayi haƙuri idan ranka ya ɓaci, nama san duk inda yake ajiyewa ai”. Har tuntuɓe yake ya fice zuwa sashen Daddy. Ya taɓa ƙofar a kulle sai ya shiga laluba jikinsa. Jin babu key ya juya ya koma sashensu. Ɗakinsa ya wuce ya ɗakko key ɗin sashen Daddy da yake da shi kamar wanda ake controlling da remote jikinsa har rawa yake yi. Haka ya buɗe ya shiga. Duk da ba shiga ɗakin barcin Daddy yake ba sai inta kama kai tsaye yasan inda duk Daddy ke ajiye abubuwansa mai muhimmaci. Aiko ko cikin minti talatin ma ya tattara komai a cikin akwati ya fito, Baban Nazeera ya kira, ya sanar masa gasu. Abun sai ya bashi mamaki, jin an samu wannan da sauki sai yace, “Kaima jeka tattaro min naka. Ka kuma shiga sashen matan Babanka dana uwarka duk gwalagwalansu da nasu takardun ka tattaro min”. “To Daddy an gama” Yazeed ya faɗa yana nufar sashensu. Kaf abubuwansa hatta atm bai bari ba sai da ya tattaro. Harda su system ɗinsa ta aiki duk ya tattara ya haɗe dana Daddy sannan ya fito. Sashen Hajiya Basariyya yaje, ya taɓa ƙofa a rufe nan ma, sai ya zagaya ta kitchen, bawan ALLAH sai zufa yake, cikin sa'a nan a buɗe yake. Aiko ya shiga, kai tsaye bedroom ɗinta ya shiga. Ita kam bai san inda take ajiye abubuwanta ba sai da yasha wahala sosai kafin ya gano, aiko kaf ya tattaro harda sarƙoƙin ƙanensa na gwal da nata, da takardun kaddaririnta da take tunƙaho da su. Dana yaranta dan Daddy duka yayansa babu wanda bai mallakawa takardar fili ba da anan gaba zai amfana da shi. Sai da yay mata kat sannan ya shiga ɗakin ƙanensa nan ma yay kaca-kaca da shi sai dai bai samo komai ba sai takardunsu na makaranta, dan Hajiya Basariyya bata barin komai a hannunsu. Daga nan sashen Ammie ya nufa, can dai tako ina a kulle dan Sakina sai da ta rufe ko ina saboda tsoron halin Nazeerah sannan ta wuce. Harta window ya gwada shiga amma bai samu dama ba dole ya haƙura ya siɗaɗa sashen Hajiya Yaya. Kai tsaye ɗakinta ya nufa, tana barci motsinsa ya sakata farkawa. Da farko firgita tayi, sai da ta kunna fitila taga shine sai mamaki ya kamata. Ta shiga yimasa magana cikin faɗa, kawai yazo yasa abu ya ɗaure mata baki, itama ya ɗaureta a jikin gado. Yanda hankalin Hajiya Yaya ya tashi ALLAH dai ya kiyaye zuciyarta bata bugaba. Dan ita kam a gaban idonta ya tattare komai da komai nata dana ƴaƴanta kasancewar yasan inda suke kuma itama bata barin yara da su anan take adanawa yay ficewarsa ya barta a ɗaure. Cikin matuƙar takaici ya hararari sashen Ammie da bai samu nasara ba. Sai kuma ya nufi sashen su Hameed. Tsaf ya hargitse komai amma bai samu ko atm ba kam ya fito cikin takaici. Babban Nazeerah ya kira yace gasu duk ya haɗa, sai dai Ammie ta kulle sashenta nata ne kawai babu. Duk da Babban Nazeerah yaji takaici sai yace ba komai fito ka kawo min ina waje. Haka Yazeed ya buɗe gate ya fita. Babban Nazeerah kam yana nan a mota yana jiran nashi, yayi mamakin samuwar komai cikin sauki dan bai san haka aikin zai zamo ba ai da tuni ya saka Yazeed ɗin yayi an wuce wajen. Koda ya amsa kayan sai ya amshe har wayar Yazeed. Sannan ya kallesa cikin gargaɗi. “Kaga idan za'a kasheka kace nine na sakaka ka kawo min abubuwan nan sai na wulakanta rayuwarka. Ka ɗauka bama ka taɓa sanina a rayuwarka ba har abada. Kaje zan nemeka bayan na gama dubasu na tantance masu muhimmanci, zan saka kai min signing a Wanda kake da damar haka dan nasan kaine next of king na ubanka. Wanda kuma bakai bane ɗaya bayan ɗaya zan sace ku kuyi min signing. Na gama da ubanka kuma sai next, gidan Darma bye”. Yazeed kamar robot haka yayma Babban Nazeerah godiya ya juya cikin gida.......

Tirƙashi🤔 nama rasa abin faɗa🥺

________★

Dangin Mamy sune suka fara shirin wucewa. Koda sukazo yima Oum sallama kamar yanda ta saba ta haɗa musu alkairi mai yawan gaske. Cikin su Ajwaad babu wanda ta gani tasan kowa na barcin gajiya. Balle ma Babban Yaya da Fawzan bai yiwuwa a kirasu, ya kamata a basu damarsu. AA ne ma mai ɗan dama-dama yau dan haka ta shiga kiran tashi wayar.... Da ƙyar AA dake rungume da Maanal ya iya buɗe idanunsa ya ɗauka wayar. Badan ringtone ɗin Oum bane ma bazai ɗaga ba. Shiyyasa ma shi yafi yarda da saka waya a vibration koma a silent gaba ɗaya saboda bai ƙaunar damuwa. Wannan wayar ce kawai yake bari a buɗe da ɗan ring ƙasa. Jin yanda yay sallama murya a shaƙe Oum ta ce, “Oh sorry Auta baka tashi ba ne kaima”. “Oum an gaji ne shiyyasa, amma yanzu na tashi ina kwana”. “Lafiya lau, ya Baby”. “Lafiya lau Oum ta tashi normal kamar yanda Uncle ya faɗa”. “To Alhamdullahi ALLAH ya kiyaye gaba. Dama baƙine zasu wuce ya kamata a nema musu mota mai ƙyau, nima banyi zaton tafiyar wuri zasuyi haka ba”. “Okay Oum suyi haƙuri su jirani bara na ɗanyi wanka.” “Okay tom sai ka fito”. Ta faɗa tana yanke kiran. Tana yimusu hakane dan su san muhimmancin dangin Mamyn a wajensu. Kuma Alhamdullah hakan yana yin tasiri sosai. Dan ita dai Mamyn ba damuwa tai ta sakasu suyi masu alkairin ba. Sai Maman Saheeba kawai da Aunty, Maman Saheeba ɗin ma tafi ci. Suko wannan itama ɗan bata da yanda zata yi ne take yarda ana nuna su a ƴan uwanta saboda talakawa ne. Idan ma sun yi musu alkairin idan ta amsa sai ta gadama take basu, gara ma ɗan rabon azumi tana basu abinda ya samu sauran ta rabama wanda take so...

Tunda ya fara wayar Maanal ta farka. Yana ajiyewa ta buɗe idannunta. Dama barcin dole aka sakata bayan ya gama yamutsata, amma ita barci safe a yanzu dai sam bayinsa take ba. A hankali ya hure idanun data zuba masan. Sai ta lumshesu ta sake buɗewa. Da muryarta ta barci ta ce, “Waye ya kira?”. Cikin raɗa yace, “Oum. Wai baƙi zasu tafi, nasan ƴan jigawa ne ƴan uwan Mamy”. Wai ƴan uwan Mamy, ita dariya ma ya bata. Amma sai batayi ba itama cikin raɗan tace, “Kai banda kai?”. Kumatunta ya ɗan matsa, bakinta tada cuna masa ya ƙara dan tsukewa waje ɗaya kamar yara na shagwaɓa. Yay murmushi da sumbatar bakin ya ce, “Sarkin fassara zance ni bance ba”. Idanunta ta ɗan juya zuzu sai kuma ta murmusa tana janye hannunsa dake matse mata kumatu, sai ta kai yatsarsa cikin bakinta ta ciza kaɗan”. “Ouch! Besty wace mugunta ce haka?”. Ƴar dariya tayi kaɗan. “Sorry, ALLAH kawai jinai ina sha'awar in cijeka. In gani wajen yayi jini”. Ƙin bata ta gani yayi sai ma ya ɓoyeshi yana ɓata fuska. Ita kuma ta hau dariyar ƙeta tana ƙoƙarin kamawa da tsiya. A haka suka rikice da ƴar kokawa, ta dage sai ta gani shi kuma yaƙi. Ta koma saman jikinsa. Sai kawai ya shiga yimata cakulkule tana dariya sosai shima yanayi. Sai da suka gajiyar da kansu kowa idonsa ya ware daga barcin sannan ya ɗauketa suka wuce bayi suna dariyar ƙasa-ƙasa. Sun ɗan jima kafin suka fito, dan a bayin ma ba'ai wankan kai tsaye ba. Da taimakon juna suka shirya. Sunyi ƙyau kamar ka sacesu ka gudu. Ga wani sirrikan ƙamshi mai ratsa zukata. Shi ya fara fita ita kuma ta gyara ɗakin sannan tabi bayansa.... Ta sami su Umma a falo suna breakfast harda Ammienta da su Hajiya Basariyya, sai AA zaune a dining yana waya RK a kusa da shi yana shan abu a kofi shima. Oum na daga tsaye. Zuwa Maanal tai ta fara gaishe da su Umma sannan ta je ta rungume Oum. Cike da shagwaɓa tace, “Oum yunwa cikina kamar anmin sata”. Cike da kulawa Oum ta shafa kanta tana murmushi, yayinda RK ke mata dariya. AA kam kallonta yake kawai yana wayarsa. Oum da kanta ta haɗa mata abinci, ta zauna tana ci AA ya kammala wayar yana kallonta yanda take cin abincin da sauri-sauri, sai kuma ya ɗauke kansa ya maida ga Oum. “Oum su shirya gashi nan zuwa. Gashi babu kash a jikina na kuɗi dole zan fita na samo”. RK yace masa nawa kake so? Faɗa masa yayi. Shi kuma ya jefa masa key yana faɗin, “Za'a samu a motata ka duba”. “Yauwa thanks you Uncle”. “Munafuki, ka dai nema Uncle ɗinka bani ba”. Murmushi AA yay yana tashi ya fice. Maanal da Oum kuma na musu dariya.........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣8️⃣

______________

......Koda AA ya ɗiba kuɗin a motar RK sashen Mamy ya nufa. Ya samu duk sun kammala shiri jira kawai suke. Ya gaishesu da girmamawa, tare da godiyar ƙoƙarin su sannan ya basu haƙuri na jinkirin daya sakasu. Yace ga wanda zai kaisu nan zuwa. Aunty ya bama kuɗin yace ta basu. Aiko sunata godiya da sanya albarka. Tare da addu'ar zaman lafiya su da iyalansu. AA da addu'ar tasu tai masa daɗi ya amsa da Amin yana miƙewa da tambayar ina Mamy. Dan bata a falon. Shine aunty Babba tace masa tana ɗakinta. Ɗan jim yay na mamaki, sai kuma baice komai ba ya haura saman. A falo ya samu Maman su Saheeba da Nuratu suna magana. Suna ganin shi sukai shiru. Shima kallo ɗaya yay musu ya wuce abinsa ko gaida Nana baiyi ba. Cike da takaici ta bishi da kallo, dan ta fahimci ɗan iskan yaron nan fa ya daina gaisheta yanzu. Nuratu kam tamkar mayya haka take kallonsa zuru, wani irin sonshi na ratsa mata zuciya da ɓargon jiki, jitake kamar taje ta rungumeshi wlhy.... Knocking ƙofar ɗakin Mamyn ya ɗanyi, ta zabura daga tagumin data zuba abin duniya ya isheta. Musamman maganar Sille dake tsaye a ranta. Tana son taƙi bashi kuɗin tana jin tsoron yazo ya mata tonon silili gida cike da mutane. Ko bai ce komai ba wani ya ganshi ya shigo mata ai sai ma ai mata wani zargin daban, balle gashi da suffar tantirai. Jin an ƙwanƙwasa ƙofar sai da gabanta ya faɗi, sai ta dinga tunanin ko Sille ɗinne ma. Yana ƙara kwanƙwasawa ta dirgo a gadon jikinta har rawa yake ta buɗe kofar. Sai sukai ido biyu da Ajwaad. Wata irin ajiyar zuciya mai nauyi data bashi mamaki ta sauke. Sai kuma ta juya ta koma ciki. Bin bayanta yay ajiyar zuciyar tata na tsaya masa a rai. Koda ya zauna a cikin sofa sai da ya sake kallonta. Sai ramarta ta fito masa sosai yau a idanun. Gaisheta yay cike da kulawa, ta amsa masa sama-sama. Ya ce, “Mamy baki da lafiya ne wai?”. Shiru tai masa, kusan minti ɗaya sannan tace, “Ƙalau nake miya kawoka?”. Shiru ya ɗanyi jimm. Sai kuma ya girgiza kai da faɗin, “Babu komai, kawai nazo gaisheki ne na kumayi sallama da baƙi da sukace zasu wuce”.....

Readers Also Read