Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 146
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 146: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 146. ★★ A nan sashen Oum kam bayan ficewar…
3,130 words
★★ A nan sashen Oum kam bayan ficewar AA a bisa tsautsayi Nuwaira ta ɗakko naman kai da taima RK farfesu dan yana sonshi, kawai tana gamawa sai ta ɗakko tukunyar gaba ɗaya ta fito da ita ta ajiye a dining ɗin tana faɗin, “Yauwa to Yaya naman kanka yayi”. Maanal ta tsaya cak da cin abinci, Ammie dake daga falo ma tana jin furucin Nuwaira sai da ta ɗan juyo ta kallesu, dan tabbas tasan in dai hasashensu gaskiya ne, kuma irin ɗaukar cikinta Maanal tayi to akwai matsala dan bata shiri da naman kai da soyayyan ƙwai. Aiko tunanin nata bai kai ƙarshe ba Nuwaira na buɗe tukunyar ƙamshin naman ya wani bigi kan Maanal dan anyi rashin sa'a ta inda take iskar ke kaɗawa, ai da wani kalar sauri ta miƙe tana mai sakin spoon ɗin hannunta jikinta har rawa yake nason barin wajen. Duk kallonta sukai, Oum tai ƙoƙarin riƙota tana faɗin, “Subahannallahi Baby lafiya? Kuwa”. Kai Maanal ke girgiza mata, idanunta sun wani kaɗe sunyi jazur lokaci guda. Tana buɗe baki zatai magana kawai sai amai. “Ya ARRAHIM”. Oum ta faɗa tana riƙota dan neman zubewa take ƙasa. Duk mikewa su Mah-mah sukai suma suna nufo dining ɗin, Ammie kam ta fuske kamar bata san mike faruwa ba. Sai dai zuciyar nakan Maanal, dan tasan yau kam zata ɗan ɗana kuɗarta, dan in ba sa'a akaci ba sai tai kwanaki tana jin ƙyanƙyamin abinci. Dan zatai ta tuna wannan ƙamshin naman ne. A farkon ciki da wahala ka gane mata dan bata wani laulayi ko ciwo da sauransu, sai yawan barci da shagwaɓa da neman rigima da buƙatar miji a kusa da ita matuƙa, kamar dai yanayin Maanal. Amai ko wani zubar da yawu duk batayi. Sai dai duk randa taji ƙamshin naman kai ko soyayyan ƙwai babu zaman lafiya. Sai tai kwanaki tana fama. Sai ciki ya shiga irin wata bakwai ɗin nan take fara ɗanɗana kuɗarta. Bazata sake lafiya ba sai kuma ALLAH ya rabasu. Yanda Maanal ke amai kamar zata zubo da kayan cikinta waje sai da tabama kowa tausayi, ga kuka tanayi da faɗin, “Wayyo Oum zan mutu” sai wani ya sake yunƙurowa sai ta rirriƙe Oum ɗin. Gaba ɗaya hankalin Oum ya tashi jitake kamar tai mata kuka. Shi kansa RK duk ya daburce kamar ba likita ba. Ƙamshin naman dake shiga mata hanci yana hawar mata kai yasa aman yaƙi tsayawa, su kuma kowa bai fahimci ƙamshin naman ne bata so ba. Kamar ya tsaya Oum ta kamata ta miƙar sai ya ƙara bugarta, ai da sauri ta koma ta sake duƙewa. Sai lokacin ne Ammie dake daga falo har yanzu bata taso ba tace ma Aunty Sharifah matar Uncle Modibbo. “Wannan naman ne ke sata aman, idan ta daina jin ƙamshin zata bari”. Aiko cikin haushi Gwaggo Khadijah da taji Ammien ta fara mata faɗa. Murmushi kawai Ammie tai ta ce, “Ayi haƙuri Gwaggo”. “Ƙyace fa haka, dan rashin tausayi yarinya na wahala kin san miye matsalar sai kiyi shiru saboda ALLAH Asiya. Sai kace wata ƴar fari. Auta ce fa. Kawaicinki yayi yawa ALLAH sai kace wata bafulatana”. Ammie dai murmushi kawai tai bata sake cewa komai ba. Ana kuwa ɗauke naman Maanal ta daina jin kanshi ta daina yunƙurin aman. Sai dai tayi laushi gaba ɗaya ta zube a jikin Oum tana sauke wahallen numfashi ga hawaye sunƙi su tsaya. Dai-dai nan AA ya shigo, dangin Mamy biye da shi zasuma Oum sallama. Ganinsu sun tattaru waje ɗaya yace, “Lafiya?”. Meeno datai kwale-kwale kamar zatai kuka tace, “Yaya Auntyna ce keta amai”. Yasan Maanal take cema auntynta. Gabansa ya faɗi ya bi ta gefe ya shigo inda Oum take riƙe da ita tana hawaye da riƙe ciki. Gaba ɗaya idanun AA ya rufe, ita ɗin kawai yake gani cike da tashin hankalin halin daya ganta a ciki. Gabansu yazo ya tsugunna ita da Oum ɗin, fuskarsa na bayyana matsananciyar damuwa. Inte na gyara wajen da Maanal ɗin ta ɓata. Ƙamshinsa kawai taji, sai ta ɗago daga jikin Oum dake shafa mata baya kamar yanda RK yace a mata ta kallesa. Sai ta sake fashewa da kuka ta ce, “Besty cikina.” Gaba ɗaya shima idonsa ya kaɗe, ya riƙo mata hannu sai kawai ta shige jikinsa ta ƙanƙamesa tana sakin sabon kuka. Ina shi wlhy yama manta da wani batun iyaye a wajen, ya ƙanƙameta idanunsa na sake juyewa. Yanda take kukan cikinta-cikinta yasa RK faɗin, “Ajwaad ɗauketa muje ciki ina zuwa”. Ya fita da sauri. AA ɗin kuma ya miƙe ya ɗagata cak. Sama ya nufa da ita bedroom ɗin Oum. Kukan da take na kekketa masa zuciya. Ammie ta girgiza kai kawai a zuciyarta tana ayyana (Indai haka za'ai renon cikin kowama zaiji jiki a gidan naku kenan). Hajiya Basariyya ta kalla Maman Yaseerah, Maman Yaseerah ta kalleta, gulma fal cikinsu da hassada. Ƙasa-ƙasa Maman Yaseerah tace, “Tab ɗin, wannan fa daga gani ciki ne”. Sosai gaban Hajiya Basariyya ya faɗi, har taji ta gagara iya cema Maman Yaseerah komai. Bayi ya wuce da ita, da taimakon Oum suka ɗauraye mata fuska da baki dan bata ɓata jikinta ba. Kafin ya sake ɗakkota suka dawo ɗakin ya sata a gado, yanda taƙi yarda tabar jikinsa dole ya zauna a gadon shima tana a jikin nashi. A haka RK ya shigo, allura ya haɗa ya bama AA yay mata. Sai kuma ya haɗa wani ɗan madaidaicin drip da wasu alluran. Da yake ba tsoron allura take ba lafiya lau akayi, shima ruwan AA ɗin ya saka mata a hannu bayan ya ɗiba jinin da RK ɗin ya buƙata duk tana lafe a jikin nasa. A hankali ciwon cikin ya fara raguwa sai kuma jikinta ya fara saki sai barci. AA dai na faman riƙon hannunta dan karta tunɓuke ruwan. RK kuma ya miƙe yana faɗin zaije asibiti ya dawo dan a gwado jinin. ALLAH sarki ana gayoma su Abah suka taso suka fito, a karo na farko na tarihi yau Baba Sardauna da Abbu, da Baba har bedroom ɗin Oum sun shigo a dalilin Maanal. Sai yanzu ne AA yaji ɗan nauyi dan gaba ɗaya Maanal ɗin a jikinsa take kwance. Oho su Baba Sardauna babu ruwansu, cike da kulawa da nuna damuwa suke mata addu'a. Mamy ma dai dole ta fito jin gasu Baba Sardauna can a sashen Oum ɗin. Tsoron kar Abah yay mata wata ƙullatar dole ta fito tazo dubantan itama. Kamar an saita sai ga RK ya dawo abinka da masu abu yana zuwa asibitin abinda ya dace yayi. Yanda yake wani makirin murmushi yasa Uncle Mahmud yin magana. Sai kawai RK ya miƙa masa takardar hannunsa yana kashema AA dake kallonsa shima ido ɗaya. “Woww!! Alhamdullahi! Alhamdullahi! ALLAH to ya bada lafiya ya kuma inganta mana.” Uncle Mahmud ya faɗa bakinsa na washewa da fara'a, kowa yasan son haihuwa a jinin Darma Family take. Ya miƙama Baba Sardauna dake kusa da shi result ɗin yana faɗin, “Baba ƙaruwa ce muka samu ai, ALLAH ya bata lafiyar raino ya kuma raba kafiya”.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣1️⃣9️⃣
______________
.......Lokaci ɗaya bakin kowa ya washe a ɗakin, duk da Oum tana hasashen hakan daman a hankali takai duƙe tai sujidar shukur, hakama Abah daya kasa haƙuri. AA kam ƙasa yay da kansa idanunsa cike da ƙwalla. Ya zuba ma Maanal ido yana jin wani abu mai nauyi na mamaye masa zuciya da jinin jiki. Shima sujidar shukur ɗin ya kamata yayi, sai dai tana jikinsa dole ne yay haƙuri. Su Umma ma sai ambaton Alhamdullah suke cike da farin ciki. Yayinda wani irin jiri ke ɗibar Mamy sai da ta lafe a jikin bango... Hajiya Basariyya kam jitai gaba ɗaya duniyar ta mata nauyi, karo na farko tayi dana sanin zuwanta Abuja. Dan da tasan wannan mummunan labarin zataji a kunnenta a safiyar yau da tun jiya ta kama hanyar Kaduna. Takaicin data ƙumsa na kwana biyun nan ma sun wadatar. Yanda kowa ke nuna farin ciki kam ya matuƙar tsaya mata a ƙirji, tana ƙara jinjina al'amarin Ammie. Uncle Hussain yace, “Lallai da ace yaran nan basu auri juna ba rabo zai kashe mutane da yawa a wannan gaɓar. ALLAH yay maka albarka Rafeeq. ALLAH mun gode maka”. A take kowa ya shiga jinjina kai, dan tabbas wannan zance na Uncle Hussain haka yake. Ashe rabo ne mai zafi a tare da yaran wannan karon shiyyasa ma AA ɗin ya kusan aunawa barzahu. Ga shi nan adadin kwanakin cikin dai-dai da kwanakin tarewarsu ba ragi babu ƙari a rubuce. ALLAH sarki Oum AA ɗin da Maanal ɗin ta haɗa duka ta rungume. AA ya sa hannu ya sharema Oum hawaye yana mai girgiza mata kai.... Yiiiifffff!! Ƙarar faɗuwar Mamy ta saka kowa juyawa inda take a firgice. RK da tun ɗazun yana sane da halin da Mamyn ke ciki ya saki wani ɓoyayyan murmushi. Sai kuma ya zabura kanta yana faɗin, “Subahanalillahi Aunty Kamila”. Oum ma miƙewa tai da sauri tai inda Mamyn take. Ai kowa mamakin duniya ya isheshi da wannan faɗuwa. Sai dai babu wanda yace komai su RK ɗin suka kamata aka ɗora a saman gadon Oum. Cikin sauri RK ya fara dubata. Sai kuma ya ɗauki wata allura a kit ɗinsa ya haɗa da sauri-sauri yay mata yana faɗin, “Jininta ne ya hau sama sosai. A saka towel a ruwan sanyi ku bani da sauri jikinta ma akwai zafi mai tsanani”. Cikin sauri kuwa aka kawo towel ɗin, Oum ta rufa mata a jiki na kusan minti biyar, RK yace a sake bashi ƙarami, aka janye wannan da har yay wani zafi. Wanda aka kawo ɗin aka saka mata a goshi sai gashi tana sakin ajiyar zuciya a jajjere. Baba Sardauna da abin ya girmesu sukace dama bata da lafiya ne. ALLAH sarki ɗan uwa dai ɗan uwa ne. Aunty Babba domin kare ƴar uwarta tai saurin bama Baba Sardauna amsa da Mamyn bata da lafiya, dama da ƙyar ta iya fitowa tace mata gana ganin jiri. Ba dai dan kowa yaji ya gamsu ba akai shiru, duk da ramar da Mamyn tai a bayyane take, dan saima yanzu da take a kwance kowa ya ƙara tabbatar da hakan. Nan dai aka shiga jajanta al'amarin ana mata addu'ar samun lafiya mai ɗorewa. AA dai yayi shiru kawai yana kallon Mamyn, zuciyarsa cike da nauyin abu biyu, farin cikin samun ƙaruwa dana halin da Mamyn ke ciki. Dan ɗazun da masifa ta koroshi daga sashen nata bayan ta gama zazzaga masa masifar da bai san laifin da yayi ba... An sake musu addu'ar samun lafiya ita da Maanal ɗin kowa ya fice. A mamakin kowa kuma Abah bai ko taɓa Mamyn ba. Yadai jajanta kamar kowa. Da zasu fita kuma ya busu suka fice. Sai Oum, RK, AA aka bari a ɗakin, dan RK yace Mamy ɗin na bauƙatar iska....
_________★
A Kaduna kam yaran Hajiya Yaya basu san mike faruwa ba sai da asuba koma muce gari ya waye. Sun saba ita ke tashinsu sallar asuba. Amma yau sai sune suka tashi da kansu. Hankalin Amrah yaƙi kwanciya, tana idar da salla ta ce, “Aunty ko lafiya yau Mamma bata tada mu salla ba.” Nusaiba dake kusa da ita ta ce, “Yanzu nake son yin magana Amrah, amma jeki leƙata ko itama makarar tayi jiki da jini. Balle Kinga kwana biyun nan ba wani isasshen barci take ba”. Kai Amrah ta jinina tana miƙewa, mintuna kaɗan sai gata da gudu har maganarta bata fita sai nuna hanyar waje take. A zabure duk sauran ƴan uwan nata suka miƙe suka bita. Wani irin shock da tashin hankali suma suka shiga da ganin Hajiya Yaya a ɗaure. Ga ɗakin yay kaca-kaca alamar ansha bincike a cikinsa. Atare kuwa sukai kanta suna kiranta kowa na fashewa da kuka. Sai dai koda suka cire abinda ya ɗaure bakinta ma bata numfashi, kuka suke na tashin hankali. Siyama dake babba a cikinsu ce tai hankalin kiran layin Daddy. Yana ɗagawa ta sanya masa kuka da faɗin, “Daddy wlhy ɓarayi sun shigo mana gida jiya da dare. Sun ɗaure Mamma gashi nan ma bata numfashi”. Matuƙar bugawa ƙirjin Daddy yayi, dama yau yake shirin su koma gida Ammie dai sai gobe idan ALLAH ya kaimu dama sukai da ita. Cikin ruɗewa Daddy yace, “Ina Yazeed, ku kirashi, nima in sha ALLAHU gani nan tahowa”. “Daddy kasan ko mun kira Yaya ba zuwa zai yi ba. Daddy mun shiga uku idan Mamma ta rasu ya zamuyi”. Kuka ya sarƙeta. Tausayin yaransa ne sosai ya ratsa shi. Cikin kwantar da murya ya ce, “Siyama bazata rasu ba in sha ALLAHU. Ku kwantar da hankalinku bara na turo muku Doctor. In sha ALLAHU nan da awa biyu nima zan iso, idan kuma mun samu train shike nan ma, kumata addu'a kudai, kinga kace babba sai kin nutsu suma sauran zasu nutsu okay”. Kai ta jinjina kamar tana a gaban Daddyn ta share hawaye. Gaba ɗaya Daddy ma shi ya rasa ina zai kama. Sai kawai yay kiran layin Ammie. Amma ba'a ɗaga ba. Doctor ɗinsu ya kira ya sanar masa yaje gidansa Please da gaggawa ana buƙatarsa. Yana yankewa ya kira dpo ɗin dake station ɗin kusa da anguwarsu. Da ga haka ya sake gwada kiran Ammie amma ba'a daga ba. Dole ya ajiye wayar ya tada su Waleed da suka koma barci yace su shirya. A gurguje duk sukai shiri, cikin sa'a ya kira train station ya samu ticket. Gidan su AA suka nufo yana cigaba da gwada kiran Ammie. Amma har suka iso bata ɗaga ba... Ammie wayarta na'a silent ne, anata kuma wannan kai-kawo na Maanal sai ga na Mamy, shiyyasa sam bama tasan Daddy na kiranta ba. Sai yanzu da kowa ke fita ta ɗauka wayar dan kiran su Shahidah taci karo da miss calls din Daddy da yawa. Sai da gabanta ya faɗi, tai ƙoƙarin kiransa back. Aiko kasancewar ita ɗin shima yake son kira dama ko ringing batayi ba ya ɗaga. Cikin tashin hankali Ammie ta ce, “Daddyn Hameed lafiya dai kuwa. Tarin miss call ɗinka sun tada min hankali”. Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya sanar mata ai gashi ma a gidan Darma ɗin. Yana tare da Babban Yaya yanzu haka. Dan cikin sa'a motar Daddy na shigowa Babban Yaya na fitowa daga sashensa shar da shi. Sashen Oum yake shirin wucewa ya hango Waleed na fitowa a mota shine ya nufosu. Koda Ammie ta fito ta samu har su Abah ma sun fito dan Daddy yace bazai shiga ba. Train ɗinsu na gab da wucewa. Koda Daddy ya gaya mata ta shiryo su wuce hankalinta sake tashi yayi. Abah ne yace ta kwantar da hankalinta ga abinda ke faruwa ne. Aifa Ammie da saurinta ta juya ciki tana sanar masa Hajiya Basariyya na nan tare da su ai. Daddy yace ya korata. Shi kuma ya fara ƙoƙarin saya mata ticket ɗin da farko ya manta ne ma gaba ɗaya tana nan itama. Babu abinda Ammie ta ɗauka sai wayarta da handbag, acewarta Amaal ta taho mata da sauran kayan. Kowa nata jajanta al'amarin. AA nason tashi babu dama, haka ya haƙura yabi Ammie da addu'a, amma yasa a ransa in sha ALLAHU ko yau bai bi bayansu Kaduna ba zuwa gobe zaije. Sai da su Ammie suka wuce sassan su Oum suka dawo ciki ana ƙara jajantawa. Sai lokacin kuma Babban Yaya kejin Lilly da Mamy babu lafiya. Sai ga Yaya Fawzan shima kamar an saita. Farin ciki matuƙa suka nuna da jin labarin cikin jikin Lilly, suka jajanta na Mamy dake kwance tana jin kowa amma tai lambo. Shi dai RK yasan ba barci take ba, amma yay shiru kawai.... Cike da tsokana Yaya Fawzan dake kallon AA bayan ya gama duba result ɗin gwajin Maanal da RK ya bashi dan neman magana. Kasancewar yana zaune ne a bed side drawer kusa da AA ƙasa-ƙasa ya ce, “Uhm-uhm wato yaron nan kai bala'i ne, afa ranar daka tafka tsiyarka a ranar komai ya kankama...” Baki buɗe AA ya kalla Yaya Fawzan, sai kuma ya kalli inda Babban Yaya ke tsaye jikin mirror yana danna waya. Ganin hankalinsa ba'a kansu yake ba ya dawo da kallonsa kan Yaya Fawzan dake dariya shi da RK. Caraf RK yace, “Kai ko babban sauro ne fa, kaima kasan sau ɗaya yake shan jini a kwanta. Bugun ƴan ball ake gaya maka Son”. Ai dariya suka sake kwashewa da shi, har Babban Yaya na ɗagowa ya kallesu. Ya ce, “Kuna lafiya kuwa?”. AA daya watsa musu harara ya ce, “Inafa sukaga lafiya Yaya. Ai sai kun haɗa da addu'a”. “Tare dakai za'a haɗa ai mana addu'ar ai. Ka gama tafka tsiya a ɗaki ka fito kana mana wani sanyi-sanyi kai na ALLAH”. RK ne mai maganar yana hararar AA. Kai AA ya girgiza kawai. Babban Yaya yayi murmushi da faɗin, “Ku biyun nan dai kun saka min Auta a gaba. Bayan kuma da naku tambarin a goshi.” Yaya Fawzan ya ce, “To ai mu Yaya bamuyi musu ba. Shi ko fa, yayta wani ciccin magani yana dakewa. Kai yau ba gashi fuskarka murmushi yaƙi barinta ba alamar godiyar UBANGIJI ”. Da gudu Babban Yaya ya waro idanunsa akan Yaya Fawzan. “Oh iya shegen naku ya bar kan Auta ya dawo kaina kuma kenan?”. Yay maganar yana wurgoma Fawzan gwangwanin turare. Mi RK da Fawzan zasuyi in ba dariya ba. Shi kansa AA ƙasa yay da kai yana murmushi, dariyar kuwa ya danneta da ƙyar. Dan harga ALLAH shima fa tunda Babban Yaya ya shigo gulmarsa yake a zuciya. Fuskarsa a sake, ga wani ƙyallin angwanci da cikar kamala a tare da shi. Ƙamshinsa kam gaba ɗaya ya gauraye da wanda ba nashi ba...........✍️
Ehem-ehem 🤣🤣😂🏃🏃🏃
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣0️⃣
______________