Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 147
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 147: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 147. .........“Oh jama'a, yaran nan jiyya…
3,358 words
.........“Oh jama'a, yaran nan jiyya kukeyi ko shargallenku?”. Oum data leƙo ta faɗa tana kallonsu. Muƙuy AA ya haɗiye murmushinsa yana nuna RK da Fawzan. “Oum kin san in dai waɗan nan biyun na a waje to sai addu'a. Sun addabemu ki korasu waje dan ALLAH”. Oum dake satar kallon Babban Yaya ganin yanda fuskarsa ke ta annuri ga murmushi yaƙi barinta ta ce, “Ai za'a kai ga hakan Auta. Kunsa marasa lafiya gaba dan iya shege sai dariya kuke?”. RK yace, “Aunty ai barci suke. Kuma dariyarmu nutsuwa ma zata basu su duka kedai jeki cigaba da hidimar bikinki Maman anguna”. Kai Oum ta girgiza kawai da faɗin, “ALLAH to ya shiryeku” ta juya ta fita. Kusa da Babban Yaya RK ya koma ya tsaya. Da sauri Babban Yaya yace, “Kana cewa tak zan ajiye kawun gefe nima nayi ta auta yau. Tunda na fahimci kai da Fawzan kun zama ƴan iska yanzu”. Ai yanzu kam AA sai da ya dara. ALLAH sarki babban Yaya yana tsoron yan iskan biyu su tasashi gaba. RK da Fawzan kam dariya ba'a magana. RK ya ce, “Haba Son yada tsarguwa haka? Nifa tambaya kawai zanyi amma kana neman fassarani da wani abu kuma”. Babban Yaya ya hararesa da faɗin, “Bar tambayarka na yafe. Shiyyasa auta ya raina ku wlhy, manyan banza ne anan kawai. Kudai tuna ga Lilly nan kwance zata iya farkawa ta jiku. Ga kuma Mamy”. Cike da mugunta RK yace, “Ai Mamy barci take bil haƙƙi, Lilly kam tashinta ba yanzu ba.” A hankali hawaye suka silalo ta gefen fuskar Mamy, kasancewar tacan take kwance ta juya musu baya ba gani suke ba. Tsinuwa take jerama RK a zuciyarta tari-tari. Dan yau tsanar da take ji tana masa tafi ta kullum shi da kowa ma dake a Darma Family. Wani irin sukar zuciyarta da ƙonata dukkan hirar da sukeyi take mata. Zuwa yanzu ji take tazo gaɓar da bazata iya haƙuri ba, dan in har tai hakan lallai Fateema na shirin cinta wasa ne. Kuma wannan cikin tayi alwashin ko zata tafi tsirara sai ta zubar dashi wlhy. Manaal bazata taɓa haihuwarsa ba...
Ehem-ehem. Ashe watan samun matsalar AA da Mamy ya tsaya kuwa🤭, dan wannan cikin duk wanda yay gigin taɓashi to bara dai nai shiru, ɗan soyayya ne fa, komu ai sai inda ƙarfinmu ya ƙare ko ya kukace mutane na?😆😜
_______★
Anan Mamy na a birkice da batun ciki can ma ɓangaren Nibras da Saheeba da su Nuratu da uwarsu cike zukatansu suke da baƙin ciki bayyananne kai kace sun haɗa miji ne da Maanal ɗin su duka, dan kishinta suke ji na gaske a zukatansu bayan kishiyoyin nasu. Karan farko Nibras taji wani abu mai kama da tashin hankali a ƙasan zuciyarta game da haihuwa. A sati huɗu kacal cikin na biyar Maanal nada cikin masoyinta AA, itama Najma fa nanda wata sati biyar ɗin za'a iya cewa tana da cikin mijinta kuma. Hakama Ameerah zata iya samu. Ga Saheeba ance ciki ne da ita itama. To itafa?. Zuciyarta tai wani kalar motsawa. Ai babu shiri ta ɗauka waya ta kira mamanta ta labarta mata komai. Itama dai Maman tata hankalinta ne ya tashi, dan sak irin tunanin Nibras ɗin ne yazo mata. A sanyaye Mom dinta ta ce, “Nibras kodai kinsha wani abun hana ɗaukar ciki ne a farkon aurenku? Shekara biyar ana shirin kulle ta shida ba wasa ba. Kin fa samu Saheeba da tsohon ciki a gidan nan, ta haihu kina nan, ta raina ta yaye ta sake samun wani ta haifa ta raina ta yaye, badan ma jinkiri data samu ba da yanzu maybe tayi wani wannan cikin da akace ta samu zai zama na huɗu ne. Ga kuma wadda aka auro jiya-jiya itama harta samu. Suma wannan da suka shigo karki raba ɗayan biyu nan da sabon wata su fara nasu amaye-amayen tunda ɗaukar cikin yanzu ba wuyane da shi ba. Shi ke nan kin zama ƴar kallo mu da dukiyar Darma sai hasashe daga nesa muna ji muna gani wasu naci. Lallai muna cikin babbar jarabawa, dan ba haukan kishi ya kamata na tayaki ba Nibras rashin samun cikin ki ya kamata ya dameni ma a wannan gaɓar. Nibras kinsha wani abu ne? Ki gaya min dan ALLAH nasan ina zan kama ina zan samo mafita”. Shiru Nibras tayi kalaman mahaifiyarta na mata luguden daka a zuciya da ƙwaƙwalwa. Mahaifiyar tata ta daka mata tsawa daga can. “Nibras! Magana nake dake fa kika min shiru! Ki faɗa min kinsha wani abun hana ɗaukar ciki ne dan ubanki?!!!”. Tsabar yanda tsawar ta ratsata sai da ta zabura jikinta na ɗan rawa. Sai kuma hawaye sharrr suka shiga ziraro mata kamar an buɗe fanfo. Tasan halin mahaifiyarsu sarai, da abinda zata iya, ta musu raino na gata musamman ma ita da take mace, amma idan tana son abu bakai mata ba ka banu, sarai zata iya ɗaukarta takai asibiti a bincikata. Dan haka gara ta faɗa mata gaskiya kawai. Murya na rawa ta ce, “Wlhy Mom allura ce kawai nayi kuma lokacin ma da sukace zata daina aiki tuni yayi, kuma wlhy daga nan ban sake zuwa nayi ba, ban kuma sake shan komai ba shekara kusan huɗu kenan”. “Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Amma ban taɓa sanin ke wawuya ce ba mai dusa a cikin kai irin yau. Ashe ni wahalar banza ma nake. Nibras dama ke muguwar yarinya ce ban sani ba. Wlhy dana san abinda zakiyi kenan da ni na auri Aliyu Darma ɗin ma kawai bayan mutuwar ubanku, kuma wlhy babu abinda zai hana na haihu masa a shekarun nan nawa. Ai shike nan sai ki fara shirin dawowa gida mu cigaba da goga jigida dan amarya dai kam ta gama samun gida. Dama gata ƴar uwarsa, ke da kanki yanzu kike faɗin irin murnar da sukeyi akan cikin facalarku, shiyyasa dama gaki nan ko kwarjini baki da shi a gidan, to kin kasa sama musu abinda suke so mara hankali wawuya kawai......” Ƙitt ta yanke kiran. Wani irin fashewa da kuka Nibras tayi dan kamar uwarta ta mata wata allura ne mai ƙarfin gaske a yanzu.....
★★
A ɓangaren su Saheeba kam, ko leƙowa duba Mamy basuyi ba kuma sunji sarai ance ta faɗi, balle Maanal ta samu itama, suna can suna ƙulla hanyar salwantar da cikin Maanal ɗin kamar yanda Mamy tai alwashi. Maman Saheeba ta rantse ta ƙara rantsewa Saheeba ce kawai zata haihu a gidan sai Nuratu idan ta shigo itama. Amma har Najma da Ameerah da Nibras basu isa ba, dukiyar Aliyu Darma ta ƴayanta ce kawai a gidan. Har Mamy data haifi ƴaƴan zero zata tashi. Balle Oum datai wahalar banza. Saheeba dai da akema ƙarin ruwa hawaye kawai take yi, hakama Nuratu kuka take rurus jikin Hajiya Turai data zo da likitar data duba Saheeba. Dan da wani mugun zazzaɓi ta tashi tanata sambatu dole Nuratu ta kira Nana ta sanar mata. Shine Babban Yaya na fita suka shigo bayan hanyar bedroom ɗin Ameerah tasha harara. Hajiya Shuwa kanta yau tasha zagi gwargwadon iko bama Oum kaɗai da Babban Yayan kansa ba. Suna gama ƙulle-ƙullensu Hajiya Turai data fito tai kiran Sille ta labarta masa komai. Dariyar mugunta yayi da faɗin, “Ai na daɗe da gane shegiyar matar ƙanin nan naki mayyar kuɗi ce. Shashasha kafin ƴaƴan nata su gama haihuwa mazan nasu su mutu ni na gama tatikesu tas. Dan sai na ƙarar da abinda kamila ta tara kaf ta koma amso na ƴaƴan nata tana tura min, ƙarshe ta fara satar na mijinta shima dan ubana ma nada haƙƙi a ciki ai....” sai kuma ya wani kwashe da dariya cike da mugunta. Hajiya Turai na tayashi. Dama Haule ta kira shi ta gaya masa komai na zancen ciki da faɗuwar Mamy yanzu babu jimawa....
_______★
Barci Babban Yaya ya bar Ameerah nayi, dan haka bata san wainar da ake toyawa ba sai kusan sha ɗaya ta farka. Wani irin zazzaɓi take ji a jikinta, ga ciwo da ko'ina ke mata. Tunda taga babu Babban Yaya a ɗakin tasan ya fita ne. Sai dai akwai wayarsa ɗaya ajiye bed side drawer. Cikin dauriya ta ɗan kintsa ɗakin ta shiga bayi tai wanka ta sake gasa jikinta yanda taga yayi mata ɗazun. Sai kuma cikin ikon ALLAH taga maganin da Mommy ta dinga dafama Maanal tana sit bath. Tunanin itama tayi amfani da shi ne yazo mata. Dan haka koda ta fito a wankan sai ta zura dogon hijjab ta ɗauka ɗauri ɗaya ta fito cike da dauriya domin dafawa a kitchen. Gida cike da mutane ai bataso a shigo a ganta tana wannan tafiyar gwale-gwalen ba. Sannan ai ya kamata ta fita ta gaida su Oum amma take a haka ai da kunya. Dan duk wanda ya ganta ALLAH sai ya gane abinda ya faru. Ga idanu a kumbure tasha kuka. A bisa tsautsayi ta fito ɗin ne tana shiga kitchen taji wayar da Hajiya Turai keyi, kuma tas taji abinda ta maimaita ma wanda suke wayar da Nana ta faɗa. Mamakin duniya ya zagaye zuciyar Ameerah. Gabanta ko sai faɗuwa yake. Da sauri ta baro kitchen ɗin ta koma ɗakinta zuciyarta na kai-kawo da fasa maganganun dalla-dalla. Tofa babbar magana, shin Maman kishiyar tata ba uwa ɗaya uba ɗaya suke da Mamy bane? Kamar dai haka ta sani tun tuni. To kenan akwai wata a tsakaninsu kokuma AJIYA A DUHU Maman Saheeban keyi batare da sanin Mamy ba. Wato su bazasu haihu ba sai ƴaƴanta kawai. Turƙashi. Eh lallai tasan yau ta shigo family house aure kam. To lallai akwai tsallen baɗake kenan. ALLAH sarki Maanal ashe ciki gareta, ta tayata murna sosai ita da Yaya AA, kuma sai inda ƙarfinta ya ƙare wajen kare cikin nan. Za kuma ta sanya ido akan su Saheeba ƙwarai d gaske..........✍️
Tofa, sabon wasa kenan tsakanin su Saheeba da Ameerah 🥱😂
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣1️⃣
______________
.........Turo ƙofar da akai ya katse mata tunaninta. Ta ɗago tana kallonsa. Shima dai kallonta yake cike da wani yanayi mai sanyi. Sai kuma ya cigaba da takowa a hankali zuwa inda take. Zama yay kusa da ita ya sanyata a jikinsa cike da kulawa ya ce, “Kin tashi?”. Kanta ta jinjina masa kawai, dan bata jin ma yin magana sam. Zafin da yaji a jikinta ya sashi faɗin, “Ya salam zazzaɓi ne jikinki haka? Aiko bara na kira Uncle Rafeeq ya duba ki”. Ganin duk yanda ya rikice ta riƙo hannunsa tana ɗan girgiza masa kai. Cike da shagwaɓa da disa-sashshiyar muryar ta ta ce, “Bafa sosai bane zan warke baga maganin daka bani ba ɗazun zan ƙara sha Yaya”. “Bazai yiwu ba Ameerah”. Babban Yaya ya faɗa yana ɗaukar wayarsa. Layin RK ya kira. Lokacin suna fitowa shi da Fawzan daga sashen Oum saboda dangin Mamy da sai yanzu ne zasu wuce. RK ya ɗaga, babu wasa a muryar babban Yaya yace ya tura masa likita zata suba Ameerah bata da lafiya. Jimm RK yayi, sai kuma ya danne dariyarsa da ƙyar yace, “Okay bara na bincika wake asibiti a yanzu cikin matan, ALLAH ya bata lafiya”. Da Amin babban Yaya ya amsa. Yana katse wayar suka kalli juna shi da Yaya Fawzan. “Babban ɗa fa yayi aika-aika da alama”. “A haba dai?”. Cewar Yaya Fawzan. RK ya ce, “Gashi ya kira a nemi likita amarya babu lafiya, sai dakewa yake bai san na harbosa ba. Wai kai dan ƙaniyarka ma mika zauna jira ne ana hayya-hayya kai kana nan gulma a cikin gida”. Fawzan da dariyar Babban Yaya ke cinsa ya ce, “Oh mudai munga takanmu ALLAH ya bamu kawun banza. Haba shiyyasa naga Babban Yaya ya kasa zama hankalinsa duk yana can ashe yasan yabi dare kai jama'a girma yayi tangal-tangal” Dariya shima RK ɗin yake yi, ya ce, “Kaima fa a ne wlhy Son. Amma ba komai zuwa zan na haɗe kai da Ajwaad kaima mu maka tas gobe. Sai muga yaya naka girman zai yi tangal-tangal ɗin kaima”. “Karen hauka ya cizan kusan nayi, ai nasan Auta ma wannan shiru-shirun da yake jirace yake dani munafukin, shiyyasa ɗaukarta zan mubar gidan, gara muje honeymoon ma dawo muku da result”. Kiran wayar da akai ta hana RK bashi amsa ya danne dariyarsa da ƙyar ya daga kiran ya fara magana. Dai-dai nan kuma Najma ke fitowa daga sashensu ita da su Lailah zasu rakata gaida su Oum daga nan ta duba Maanal dan har an baza mata labari. Gaba ɗaya hankalinsa ya koma kanta. Tayi wani shegen ƙyau daka ganta kaga amarya. Ya zubama lips ɗin daya gama morewa ɗazun da safe idanu. Haɗa ido da sukai da Najma ya sata duƙar da kai cike da kunyar abinda yay mata da safen itama, sai take jin kamar kowa idan ya kalleta zai gane ne. Kanta a ƙasa ta ƙaraso inda suke ta gaida RK cike da girmamawa. Kamar ba shi ba ya wani dake yana amsawa da kulawa. Ta ɗan kalli Fawzan ƙasa-ƙasa tace “Sannu Yaya”. Shima ƙasa-ƙasan ya ce, “Yauwa sannu ƙanwa”. Kallonsa RK yayi baki buɗe. Fawzan ya hararesa. Sai kuma ya maida kallonsa ga Najma, “Je ki dubasu wajen akwai zafin rana”. Kanta ta jinjina a kunyace ta wuce. RK yace, “Eh lallai yau naga bariki, bafa Ajwaad bane kawai ƙwallo a gidan nan kowa kwar-kwar ɗin kansa ne na lura”. “Ai karatunku muke bi kaida Yayunka su Abah. Idan bamu zama kwar-kwar ɗin ba zamu ƙara muku yawa ne. Ka jimin sa ido, kai mafa ko ɗaga ƙafa babu mukaga Aunty Nuwaira na amaye-amaye ga ƙaninmu nan na shiga wata na shida a ciki”. “Oh, nima iskancin zaka min to nayi nan”. Dariya Fawzan ya sanya. Cikin ɗan ɗaga murya yace, “Ai yau kaima sai kaji a jikinka bari dai Auta ya gama jiyyar ya fito”. RK dake shigewa sashen Abah ya ce, “Idan kun ganni kenan”. Ya ƙarasa shigewa....
________★
Su Ammie sun iso Kaduna lafiya. Sadda suke isowa gida sun sami ƴan sanda na jiransu. Hajiya Yaya kuma ta farfaɗo an sakata barci dan jininta daya haura ya sauka. Sai da suka fara zuwa suka dubata yaran sukai musu bayanin iya abinda suka sani suma ganin ɗakin Hajiya Yayan kaca-kaca yasa babban ɗan sandan faɗin suma ya kamata su duba sashensu duka ko za'a samu wani abu. Dan maigadi ma dai an bugar da shi ne har yanzu barci yake. Likita kuma daya dubashi ya tabbatar musu tun kusan takwas na dare aka bugar da shi ɗin. Al'amarin ya sake bama Daddy da su Ammie mamaki. Badai suce komai ba kowa ya nufi sashensa dan dubawa. Hajiya Basariyya ce ta fara fitowa a haukace tana kuka da ihun ta shiga uku an yashe mata komai. Babu abinda aka bar mata kaddararta sai sutura. Sai ga Daddy ma ya fito a rikice. Yace ai shima komai an yashe, takardunsa da duk wani abu mai muhimmanci babu shi. Dama su Amrah sun faɗa musu na sashensu duk an tattare suma. Fitowar Ammie tace ita gaskiya ba'a ma shiga ba dan komai yana a yanda yake yasa Hajiya Basariyya dake kuka riris sake fasa ihun tashin hankali. Yanda take kuka da ihu sai da abin ya bama kowa mamaki, can kuma sai gata ta zube a ƙasa babu numfashi babu alamarsa. Babbar magana, babu shiri su Ammie sukai kanta, yara suka kawo ruwa aka zuba mata ta kawo numfashi, sai ta hau sambatu kamar wadda kan ya taɓu. Faɗi take shike nan an talauta su, ita babu Daddy babu, miyasa ita Ammie ba'a ɗiba nata ba. Ƙilama itace ta saka aka kwashe musu..... Wata gigitacciyar tsawa Daddy ya daka mata. Cikin matuƙar faɗa ya ce, “Halan kin haukace ne Basariyya? Matar tawa kike jifa da wannan mummunan aiki. To ki iya bakinki idan ba hakaba wlhy zakiyi kuka biyu shashasha kawai da bata da girma sai na jiki”. Yanda yake faɗan sai da kowa ya nutsu, sai Ammien ce ke lallashinsa ma da ido. Amma yaƙi kulata itama dan harga ALLAH yaji matuƙar haushin kalaman Hajiya Basariyya. Ko ina ƴan sanda saida suka shiga, suka ga komai daya faru sukai hotuna da aune-aune dan a bincika ko za'a samu hoton yatsu. Duk wannan bidiri da akeyi babu Nazeerah babu Yaya Yazeed. Suna sashensu kamar ma basa gidan. Hajiya Basariyya dake a birkice dan sai kika take ta ce, “Wlhy bazan yarda ba, a binciki matar Yazeed, mudai itace baƙuwa a gidan nan, yaranmu duk mun san halinsu”. Kallonta Ammie da Daddy sukayi, sai kuma suka kalli hanyar sashen Yazeed ɗin. Salima ta ce, “ALLAH Ummi nima nayi wanan tunanin, kuma fa tun ɗazun duk ihun kukan da muke ko leƙe bata fito ba, dama shi Yaya sai ta bashi umarni zai yarda ya fito”. Ta share hawayenta. Da yake yaran suma babu wadda suka tsana yanzu a duniya irin Nazeerah ɗin duk sai suka goyi bayan zancen Hajiya Basariyya. Ɗan sanda yace, “Waye Yazeed ɗin wacece Nazeerah?”. Daddy ya gyara tsaiwarsa da faɗin, “Yarona dai daka sani, ita kuma matarsa ce”. “A to ya kamata su fito, munata kai-kawo tun ɗazun sunyi shiru, ni nama zata yaran nan ne kawai a gidan ai Alhaji. Kai kofur Hamza yi musu knocking”. Wanda aka kira da kofur Hamza ya amsa da faɗin, “Yea sir”. Yana nufar sashen Yaya Yazeed. Knocking yayi har sau fin biyar sannan aka buɗe a fusace. Nazeerah zata fara bala'i taci karo da kofur Hamza. Dama fuskar marasa mutunci ce da shi ai da gudu ta haɗiye abinda tai niyyar faɗa. Sai dai cikin ƙarfin hali tace, “Lafiya”. “Lafiyar ce ta kawo haka, ku fito ke da mijinki ana nemanku”. Ɗan jimmm tayi, sai kuma ta saki ƙofar tana faɗin, “Yana ciki bari na kirashi”. “Basai kin koma ba kirashi daga nan inda kike”. Rasa yanda zata yi tai, gashi sai mazurai yake mata. Dole ta ɗaga murya daga nan ta ƙwalama Yaya Yazeed kira. Sai ko gashi ya fito da saurinsa daga kitchen, da alama girki yake mata. Mamaki ya kusa halaka kofur Hamza, ganin har ɗan duƙawa Yazeed yay yace mata “Gani”. Batayi magana ba ta fito, sai shima kofur Hamza ɗin yace masa ya fito. Amma Yazeed yay tsaye yana kallon Nazeerah. Dan in batace ya fito ba bazai fito ba. Kofur Hamza ya sake jinjina kai yana gaskata maganar yaran can, kai wannan koba ita ta aikata ba itace ta saka aka aikata dole. Tsawa yay mata, tai tsalle gefe tana tura baki gaba ga ciki tirtsi-tirtsi. Ta kalla Yaya Yazeed tana kumbura baki ta ce, “Malam ka fito fa akace”. Ai a zabure ya fito kuwa. Sai Kofur Hamza ya sake mutuwa a tsaye a ransa yana ayyana (Kaga mata ƴan wuta ƙuru-ƙuru tun a duniya. Yo wannan ta mutu a haka ai tasan makoma itama). Haka dai ya tasasu a gaba har inda su Daddy suke. Babu wanda Yazeed ya gaida yana tsaye a gefen Nazeerah. Itama kuma bata gaida kowa ba. Daddy ya girgiza kansa zuciyarsa na masa zafi sosai. Ammie kam ƙwalla ne suka cika mata ido ranta fal tausayin Yazeed da Hajiya Yaya.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣2️⃣2️⃣
______________