Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 171
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 171: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 171. ........Tunda Babana yayma Junaid…
3,372 words
........Tunda Babana yayma Junaid managar sake turo iyayensa a tsaida rana sai ya daina zuwa gidan mu, ya turo abokinsa gidanmu wai yayi tafiya tare da babansa zuwa ƙasar waje. Ni kuma nasan ƙarya yake yi, kawai dai na lura yanzu bai cika zaman garin Kano bane amma ban san inda yake zuwa ba. Tarayyata da su Fateema yasa nasan ainahin Junaid, anan kuma na fahimci mutanen daya tura gidanmu akan batun aure na ƙarya ne ba iyayensa bane ba, hasalima babu wanda yasan labarina a gidansu, shi a matsayin baida ko budurwa yake, tafiye-tafiye da yake yi yanzu harkar kasuwanci babansa ya saka shi farawa daga Kano zuwa Lagos. Wannan magana tai matuƙar tsaya min a zuciya, kwatsam wata rana sai gashi, banyi nauyin baki ba na jero masa dukkan abinda naji a kansa, sai ya hau borin kunya da zagina, wai bincikensa naje inayi saboda ya sakani a jikin su Fateema, to wlhy nayi kaɗan, sai ya wulaƙanta ni shi ba ruwansa, kuma daga ranar ya rabani da Fateema tunda dama shine ya haɗamu. Niko nace bai isa ba yayi kaɗan alaƙa da fateema yanzu ne ma na fara, sai dai tawa da tashi ta yanke. Na gaggaya masa maganganu masu zafin gaske nima muka rabu baran-baran. Tun daga wannan lokacin ban sake ganinsa ba har muka shiga aji biyu na makaranta, inata dai neman hanyar da zan iya samun Aliyu duk da a zahiri bazaka taɓa cewa da wani abu a raina ba sam. Kwatsam sai ga batun an cirema Fateema mahaifa ya ɓullo, wato idan nace muku banyi farin ciki ba a lokacin nayi ƙarya wlhy, dan ina ganin kamar hakan wata hanyar da zanci nasarar shiga gidan Aliyu ce, sai dai ta ina? Ban sani ba. Ina tsaka da neman mafita Fateema tazo min da labari mafi daɗi da ba'a taɓa sanar min ba a duniyata, wato tana son na auri Aliyu. Ya suhanallah, a wannan rana har ruwa na zuba a ƙasa na sha, amma na dake da farko na ɗan nuna turjewa, tanata lallashina Ita kuwa. A ɗan tsakanin ne kwatsam sai ga Junaid, bayan kuma tsahon kusan shekara guda rabona da shi, har ma na fara mantawa da shi a babin rayuwata. Da farko naji tashin hankali da ganinsa, amma na dake masa nace miya kawoshi. Murmushi yay min kawai da faɗin Hummm Kamila kenan, ni kike tunanin zakici amana? To bari na gaya miki idan har kina son rayuwarki kada ki sake ki amince da buƙatar Fateema, dan nasan dama wannan shine burin ki, wannan gargaɗin kawai nazo nai miki, idan kunne yaji, jiki ya tsira, na barki lafiya. Daga haka ya juya yay tafiyarsa batare da ya bani damar cewa komai ba. Hankalina yayi ƙololuwar tashi, dan na fahimci komai Junaid zai iya aikata wa, ni kuma har abada banga kurarin da zai hanani auren Aliyu Darma ba a wannan gaɓar, hakan na nufin dole na nemawa kaina mafita da kariya kenan, sai dai ta ina ban sani ba. Haka dole na matsawa kaina da ƙwaƙwalwa ta a ɗan tsakanin, na dinga kai gwauro ina kai mari. Daga ƙarshe dai na yanke shawarar da zuciyata tafi aminta da ita. Akwai wasu ƴan daba a bayan layinmu saboda tsoronsu ko ta inda suke ba'a bi, nasan ɗaya a cikinsu a dalilin ƙawata ɗin nan data rasu, dan da kamar saurayinta yake ma, dan haka cikin kasada na sameshi da batun ina son suyi min aiki. Kamar bazai amsa ba sai yace na faɗa masa aiki, ƙarya da gaskiya na haɗa na faɗi masa na kuma tabbatar masa ko nawa ne zan biya. Kun san dai ɗan daba da fusata akan wanda ya sani, cikin ɓacin rai yace karna damu basai na biya ko sisi ba, kodan ƙawata zasu min aikin. Naji daɗi sosai, amma dan na faranta musu rai na kawo dubu uku na basu a lokacin dan kaf kuɗaɗena ne na haɗa, sannan dubu uku nada daraja matuƙa gaya a lokacin. Baƙaramin farin ciki kuɗin nan kuwa suka saka shi ba, sai ma ya miƙe yana faɗin karna damu a gobe-gobe Junaid ya shigo garin Kano ko gidansu bazai je ba zasu min ram da shi, dan shima yasan shi ya taɓa masa wani rashin mutunci. Daɗi sosai naji, haka na wuce gida nai zaman jiransu. Ai ko kamar yanda ya faɗa washe gari gab da magriba akai sallama ƙofar gidanmu, koda na leƙa sai naga wani yaro yace naje baya Ɗan-taure na kira na. Ko gida ban koma ba na wuce, yana hangoni yay gaba na cigaba da binsa a baya kamar ba tafiyarmu ɗaya ba. Da yake duhun magriba yayi babu ma wanda ya maida hankali a kammu har bayan primary cikin wani kangon aji da rufinsa ya yaye. Mizan gani, Junaid ɗaure a window yaci duka yay lilis ko iya buɗe idanu bayayi da ƙyau. Abin ya min suga na shiga kwasar dariya ina tafi, ya buɗe idanunsa da ƙyar yana kallona, sai kuma yay murmushi yace Kamila dama kece kika sa akai min haka?. A gadarance nace eh, namaka hakanne dan ka tabbatar niba kanwar lasa bace. Ba kace zakayi maganina ba ka kasheni, to kafin hakan ni a yau zanyi naka a yanzu ma. Murmushi ya sake yi yana runtse idonsa da jini ke ɗiga ta sama, yace Kamila kenan, har yanzu baki gama sanin ni wanene ba, ba kuma ki gama sanin nafi ƙarfin ƙaramin kanki ba. Idan har zan iya ɗaukar fansa akan Aliyu Darma akan abinda bai taka kara ya karya da yay min ba ke mi kike tunani zanyi a kanki. Yawu na tofa masa a fuska da faɗin, babu abinda ka isa kayi, ko a wancan ƙaramin wasan naka da kake tunanin ka turani jikin Fateema kawai kake ɗaukar kanka wani shege ne kai. To daga turani jikin nata sai me ka iyayi kuma?. Nan ma yar dariya yayi, yace Kamila kenan iya abinda kika sani kuma kika gani kenan, karki yaudari kanki da ɗan guntun rainon da nai miki na shekaru huɗu kacal. Idan kuma har kina fata da son tsira da rayuwarki to lallai karki bari mutanen nan su barni da raina. Idan ba haka ba kika bari har na rayu wlhy sai na baki mamaki ƙwarai da gaske.” “Ko'a jikina kalamansa basu wani daman ba, sai ma taɓe baki da nayi cike da rashin damuwa nace, can ta matse maka kuma wannan. Mi kuma kake ci na baka na zuba, ai dama ni ban maka alƙawarin barinka a raye ba, dan babu abinda zamu yi da annoba a cikin al'umma. Na kalla Ɗan-taure nace yayana ina son ku ɗauki wannan sakaran muje yanzu nan mu jefa shi a ruwan can na ƙasan mu, dan ko gawarsa zanji baƙin ciki idan aka sallata aka saka masa likafani. Ɗan-taure yace an gama ƙanwata, haka nake son naga mace a dake malam ba farar kura ba. Kai ku ɗaure masa baki tamau yanda ko nishi bazai iya ba muje. Dariya irin ta ainahin boss Junaid yayi, dariyar data ratsa har cikin kwakwalwar kaina ta kuma tsoratani, amma sai na dake ina kallonsa. Idonsa a kaina yace. Lallai kinyi kuskure Kamila, babban kuskure ma kuwa na cin amanata. Amma ki sani kuma ki shirya ɓadda Junaid a wannan duniyar tamkar kin KASHE MACIJI NE BAKI SARE KANSA BA. Domin akwai AJIYA A DUHUn ki a hannuna dake a karan kanki bazaki taɓa iya hasaso minene ba har sai a lokacin dake zaki koma cikin duhun. Maza jeki, jeki da iya gudun da zaki iya ki taka irin taki rawar yanda kike so, ni kuma ZAN DAWO a gaɓar da ƙafafunki da gangar jikinki har ma da zuciyarki da ƙwaƙwalwa suka gaji. Dan kinfi kowa sanin JUNAID baya barin BASHIN GABA. Koni na ɓuya ina da madadin da zai ɗauka min fansa a kanki.” “Duk da maganganunsa sun min dukan guduma a saman kai sai na taɓe baki, cikin halin ko'in kula nace kai ka sani kuma wannan. Sai ka bari har sai ka rayu kafin kai tunanin bibiyar bashin gabar. Yayana na gaji da jin muryarsa a cikin kunena Please ku ɗaukesa muje dare nayi. A gabana suka daure masa baki suka saka a buhu suka ɗaukeshi, ni kaɗai mace a cikinsu amma ko ɗar banji ba na bisu har bakin ruwan. Haka suka jefa shi a cikin ruwan nan ina kallo, banji ko tausayinsa ba na juyo na tafi gida suma suka koma wajen zamansu. Da farko abin ya dameni dan a ranar harda mafarki na, amma zuwa kwana biyu da Fateema ta sake zuwa min da batun Darma sai na manta da wani al'amarin Junaid gaba ɗaya, ga dawowar mahaifiyata da ƴan uwana a lokacin, sai daɗin yay min yawa matuƙa. Haka aka sha bikina da Aliyu Darma duk da na fahimci ba sona yake ba sam. Oho karya sonin ai ni wanda nake masa ya wadatar. Tabbas ban wani samu tarbar arziƙi daga Aliyu ba a gidansa, hasalima randa aka kaini ko ganin idonsa banyi ba, bamma fahimci a gida ɗaya muka kwana ba sai da safe. Al'amarin ya cizar min zuciya amma na dake na kuma daure. Nayi zaton abin zai tsaya a iya kwanakin farko-farko ne sai naga fa da gaske yake bana gabansa, matarsa ce ta tirsasashi aurena sai na kasa danne zuciyata, shiko ya tabbatar min akan matarsa fa zai iya komai, kodai na nutsu ko kuma na kama hanyar gidanmu. Dan wlhy bazai taɓa rayuwa a inuwa ɗaya da maƙiyin Fateema ba in har ya sanshi. Bayan ya gama gasa min magana yace naje gida. Tofa babbar magana. Hankalina ya sake tashi, kofa wata ban cika ba, hasalima ko kwanciyar aure bai taɓa yi da ni ba.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣4️⃣
______________
........Bayan an maido ni sai na canja takuna akan Fateema da shi kansa. Na boye komai a zuciya har Aliyu ya yarda dani, ya kai gareni kuma a shimfiɗa. Atsorace nake da sakamakon jina ba cikakkiyar mace ba da nasan zaiyi, amma sai naji baice komai ba, naga dai canji a tare da shi na wannan yinin harma sati guda, amma cikanki baice dani ba, tun ina a tsorace da hakan harna saki jikina, cikin ikon ALLAH ma sai ga ciki, farin cikin samunsa kuma nake tunanin ya goge komai a ran Aliyu game da ni mara ƙyau, nima kuma sai na sake nemawa kaina fada ta hanyar bata ya'yan da duk na haifa ɗin. Na kuma kauda mata ido a kansu kamar ban damu da su ba....”
Zuwa yanzu jami'an tsaron sun zagaye gidan tako ina, harma suna bada sanarwar su Mabera su miƙa wuya kawai. Amma da yake zuciyar a bushe take sai Sille ya bama yaransu umarnin harba bindugunsu sama duka a lokaci guda. Hakan kuwa sukayi, yanda sukai ɗin kuma ya isar ma jami'an tsaron saƙon waɗan nan a shirye suke. Dama saboda tabbatar da hakan yasa Sillen saka su yin harbin. Matuƙar tashi hankalin su Baba Sardauna da su RK yayi, dan harda su aka shigo jejin, duk da jami'an tsaron basu so hakan ba, amma sukace bazasu iya zama ba, dan RK ma harda likitoci ya shirya da Ambulance har biyar saboda shirin kota kwana. Sai dai Ambulance ɗin da sauran jami'an da suka biyo mota basu kai da isowa ba...
A karo na farko Abah ya jefama Mabera tambaya idonsa akan Sille dake ta zuƙar sigari kamar ALLAH ya aikoshi, kai da ka kallesa kasan hankalin maza a tashe yake. “Da gaske shi ɗin wanda ta haifa ta yadda ne?”. Murmushi Mabera yay da faɗin, “Tabbas shine, domin kuwa abinda bata sani ba nasan tana da ciki, sai dai a ƙurarren lokaci nasan hakan nima. A ranar da mukaje da abokina wajenta yin sulhu, da yake yana karatun lafiya muna baro wajen ya tambayen nasan kuwa Kamila nada ciki?. Nace masa ciki kamar ya? Yace min ciki dai na haihuwar ɗa, dan shi kallo ɗaya yay mata ya fahimci hakan a gare ta. Da farko na shiga tashin hankali, dan tabbas nasan cikin nan nawa ne, saboda nasan bata mu'amula da kowa sai ni. Ni ɗin ma sau uku ne kacal, sai dai ta zama sanadin da ina neman wasu matan kuma a yanzu. Ganin yanda na rikice sai ya shiga kwantar min da hankali, shine ya bani shawarar yanda muka ɗiba jininta batare data fahimci dalilin hakan ba. Koda muka kai akai gwajin aka tabbatar mana da cikin rikicewa na sake yi, nace ma abokin nawa wlhy dole na biya ko nawa ne a zubar da shi. Amma sai ya ƙwaɓeni, yace Junaid kada ka aikata hakan, dan cikin nan ya wuce batun zubarwa cikin sauƙi, da aje yarinyar nan ta rasa ranta ka saka kanka a matsala gara ka barta da cikin, kawai dai dole mu sanyama duk motsinta ido dan bamu san manufarta na ɓoyeshi ba har a gareka. Da farko dai badan na gamsu da shawararsa ba na ƙyale, sai dai nima dana nutsu nayi nazari sai na ajiye batun zubda ciki, muka sakama duk wani motsinta ido batare da itama ta sani ba. A yanayin da muka ganta da rana a randa zata haihu abokina ya tabbatar min da naƙuda take a tsaitsaye, kuma tabbas zata iya haihuwa daga ranar zuwa kowane lokaci, dama kuma gwajin da yay mata yasa a lissafe muke da watannin cikin. Har taje asibiti ta kaima su kakarta abincin dare ta dawo a biye nake da ita, ganin ta shiga gida ga hadari sai na haƙura na yanke shawarar tafiya gida tunda babu wani labari, amma zuciyata taƙi yarda min da hakan, haka na cigaba da zama a ɓoye cikin layinsu har ruwan nan ya sakko, na gama sarewa akan na tafi kawai sai gata ta fito daga gida tana tafiya da ƙyar tana kuma waige-waige, ko tsoron duhun dare dana ruwan sama da akeyi bataji da alama, sosai taurin zuciyarta ya sake bani mamaki, dan tabbas da ace namiji ce yarinyar nan ba ƙaramar tantiri za'ayi ba. Haka na dinga bin bayanta harta shiga cikin kangon nan, harga ALLAH a lokacin da take naƙudar ni tausayi ma ta bani, sai na dinga jin kamar na fito ma na taimaketa. Amma dai zuciyata na ƙwaɓata, ga ƙaunar yaron data bari yashe a ƙasa ruwa na dukansa ta shigeni, jikina har rawa yake akan naje na ɗaukesa. Na dai daure da ƙyar harta gama hutunta ta tashi ta naɗe yaron a zani ta saka mabiya a leda ta fita a kangon. Cikin sauri nabi bayanta, duk tunanina gida zata koma sai naga ta ɗauki wata hanyar daban babu tsoron komai a tare da ita. Mamaki ya kamani, amma ina dai biye da itan harta isa ga bolar data ajiye yaron ta zuba masa bola tabar wajen. Karo na farko da naji tsanarta mafi muni a zuciyata, tsana irin wadda ban taɓa ma wani mahaluki ba a rayuwata, ina hawaye da komai naje na ɗaga yaron daga bolar har lokacin bai kuka ba, amma kuma alamu sun nuna yana da rai, dan zuciyarsa na bugawa. Haka na rungumeshi nabar wajen da shi har mabiyyar data yarda dan bazan iya barinta a wajen ba, na koma kangon data haihu na kwashe duk wani abinda ta bari da zai iya zama shaida. Haka na ɗauki hanyar gidan su abokina a ƙafa ga yaron a ƙirjina na naɗesa a cikin leda ta baya, da ƙyar na samu acaɓa ya ƙarasa da ni. Hankalin abokina ya tashi sosai, yayi kuma mamaki da jinjina taurin zuciyar Kamila, haka ya shiga bama yaron taimakon gaggawa da ƙyar muka samu yay kuka. Ni da kaina nai masa wanka muka saka shi cikin babbar rigar abokina muka naɗeshi ya samu ɗumi, asubar fari muka fita zuwa kaishi wani asibitin kuɗi da abokina ya sani kuma yake da alaƙa da su. Anan akai treating yaron na tsawon kwanaki goma, har sai da lafiya ta dawo jikinsa sosai sannan aka salleme mu, ranar ban kwana garin Kano ba na biya kuɗin jirgi na wuce Lagos. Saboda shi na kama ɗaki a anguwar da ba'a sanni ba cikin ƙabilu kuma dan babu bahaushe ko ɗaya ta wajen. Haka na cigaba da rainonsa ni kaɗai, har lokacin daya kamata na sayi kaya na koma gida yayi, sai na rasa yanda zan yi dan bana son mahaifina yaga na saɓa lokacin dana saba komawa, hakan ne ya zama dalilin fara neman mai raino, kasancewar nafi son bahaushiya yasa na sha wahala sosai, sai da ƙyar na samu wata anan anguwar da muke sai dai mai aiki ce a wani gida nan kusa damu, gidan da ban taɓa sanin hausawa bane a ciki sai ranar, duk da dai matar ce bahaushiya, mijin kuma ƙabila ne. Da wannan damar na dinga zuwa kai kaya Kano sai dai bana daɗewa kamar da nake dawowa Lagos, dana dawo rainon yarona ke dawowa hannuna, nine uwa nine ubansa, har ALLAH ya sa yakai shekara biyu da haihuwa. Yayi wayo sosai, kamanina da nashi na ƙara fitowa. Ƙaunarsa na sake tasiri a raina, ina jin kamar bani da kowa a duniya sai shi kaɗai. Shine farin cikina, bani da wani buri sai na naga ya girma. Ban taɓa bama kowa labarin uwarsa ba, idan ma aka tambayeni sai nace ta rasu wajen haihuwarsa. Hatta da mai rainonsa da uwar ɗakinta haka na gaya musu kawai. Ya fara tafiya ina tsaka da wannan farin cikin na taho Kano kawo kaya, na sauka airport na shiga taxi zai kaini gida yaran data saka su kasheni suka taremu a hanya. Bayan sun min abinda ta sakasu harda jefani a ruwa, amma kamar yanda na faɗa mata zan dawo gashi na dawo ɗin. Dan kuwa suna barin wajen cikin yaran data saka suka jefanin ɗaya ya dawo ya fiddani, duk da dai nasha ruwa sosai zuwa lokacin haka ya ɗaukeni ya kaini nesa da anguwar tasu, a wani kango ya bani taimako, kwana uku da yini guda yana tare dani har na dawo hayyacina. Alkairi nai masa mai tsoka. Sai ya bani shawarar nayi nesa da garin Kano, dan tabbas Ɗan-taure hatsabibi ne baya juyama wanda ya bashi aiki baya, sannan yanda ya fahimta Kamila hatsabibiyar yarinya ce komai zaki iya sake aikatawa idan ta tabbatar ban mutu ba. Na gamsu da bayaninsa dan haka na buƙaci yazo muje Legos, dan inada wajen zama acan. Baiyi musu ba muka tafi. Sai dai muna isa ciwo ya kwantar da ni sosai, shine yay jiyyata tsahon watanni bakwai, yarona dana sakama Junaid matar nan da uwar ɗakinta da basu taɓa haihuwa ba ita da mijinta ba na kula min da shi, har ALLAH yasa na warke sarai na dawo normal, dawowar data sakani turo yaron nan yay min bincike akan Kamila da gidanmu. Sai ya samu ALLAH yayima mahaifina rasuwa, sannan ni kuma anyi nema na har an gaji an haƙura da tunanin na rasu, ɓatan nawa ne ma ya saka mahaifinmu a damuwa ya kwanta ciwo har ya rasu, har ma yayuna sunzo sun tattare dukiyar Abbanmu da nake juyawa anan Lagos ɗin sunje sun raba gado iya su kaɗai banda ni. Hasalima zuwa lokacin basa ƙasar, ita kuma mahaifiyarmu wai ta auri ƙanin mahaifinmu sun bar nan Kano suna Bauchi da yake can ne asali mu. Kamila kuwa ta auri Aliyu Darma, har ma tana da ciki a lokacin...........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*