Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 172

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 172

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 172: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 172. Read My Book "AJIYA A DUHU" on…

3,419 words

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣5️⃣

______________

........Wannan abu yamin ciwo ƙwarai da gaske, dan labarine mafi muni da bazan taɓa mantawa da shi a rayuwata ba. Gaba ɗaya naji na tsani ahalina, dan tabbas basu min adalci ba, musamman ma mahaifiyarmu naji ciwon auren ƙanin babbanmu da tayi, dan baya shiri da babanmu sam sanda yake raye. Amma ta aure shi bayan rasuwarsa ko shekara ba'a rufaba, a lissafi ma tana gama takaba akai auren. Wannan al'amarin shine sanadin canja min tunani, naga babu wani amfanin cigaba da zama na mutumin kirki, na fara rainon zuciyar Junaid da ɗaukar fansa akan mahaifiyarsa, ni kuma na huɗe shafin iskanci ba kama hannun yaro. Na kuma fara shaye-shaye saboda ɓacin rai. Mai rainon Junaid ce taita ƙoƙarin dawo dani kan hanya, tare da nuna min ita zata aureni kodan junaid, amma sai naji bazan iya ba, kamar itama tazo min ne da irin fuskar Kamila. Sai na fara hantararta, amma sai batai fushi ba ta cigaba da bibiyata harna amince da ƙyar da takurawar Junaid a lokacin yana da shekara kusan biyar. An ɗaura mana aure da ita, sai nace mata bana son sake haihuwa. Iya Junaid ya isheni rayuwa. Ta amince da hakan kuma tana bama Junaid dukkan kulawar data dace, idan ma ba'a faɗa maka ba sai ka ɗauka itace ta haifeshi. Kwatsam Junaid nada shekara tara sai gata da ciki, aiko na shiga yi mata rashin mutunci, amma sai Junaid ya nuna bata kariya da son cikin, dole na bari nima na koma bata kulawa tunda dai mai afkuwa ta riga ta afku, sannan akan Junaid komai zan iya amsa na kumayi haƙuri da shi. Tasha wahala a rainon cikin har ALLAH yasa yakai ga haihuwa, ta haifi ɗa namiji, sai dai ko ganin fuskarsa batayi ba ALLAH yayi mata rasuwa. Munci kuka ni da Junaid sosai, sai uwar ɗakinta ce ke lallashinmu da mijinta daya kasance ba wani mazauni sosai ba. Haka shima wannan jaririn na shiga rainonsa tare da Junaid, bana zuwa ko ina kullum ina gida, a hankali yaro da muka sakama suna Ra'iz na girma zuciyata na ƙara mutuwa daga barin neman na kaina, sai dai na daina shaye-shaye dana fara, sai danfarar mutane kuɗi. A hankali hakan ya fara min daɗi, sai ya zama itace sana'ata mafi shahara. A haka Ra'iz da kusan Junaid ne ke rainonsa shima ya fara girma, sai uwar ɗakin mahaifiyarsa da itama take taka rawar gani a kammu dan mafi yawancin lokaci suna a gidanta ne koda yaushe idan suka taso makaranta, kawai sai tsautsayi ya gitta min a tsakanin, na damfari wani mutumi aka kamani, bayan shari'a ta kwana ɗaya kacal aka turani prison. Wannan shine dalilin yin nesa da yarana guda biyu, kulawarsu ta koma hannun uwar ɗakin matata, ba kowa bace kuma face wannan shegiyar matar Hajiya Turai.....” Babu wanda bai kalli Hajiya Turai ba, ita ko ta duƙar da kai kamar ta ALLAH. Cikin jin zafi sosai Mabera ya cigaba da faɗin, “Tunda aka sakayani a prison karatunsu Junaid ya tsaya, matar nan ta dinga shagwaɓasu sai abinda suke so take musu. Junaid ya fara bin abokan banza, gashi dama na karantar da shi wacece ainahin mahaifiyarsa wannan al'amarin ya zauna daram a zuciyarsa. Tun bai gama balaga ba ta dinga bashi magani ya fara amfani da ita saboda ita tsinanniya ce azzaluma ta biyu. Har takai idan mijinta baya nan Junaid ya zame mata kamar shine mijinta. Taso fara lallata Ra'iz ɗin shima amma Junaid ɗin ya taka mata burki, da yake ya fara zama gawurtaccen mara ji sai ta fara tsoransa... A lokacin ne na fito a prison, gatan da naga Turai na bama su Junaid ya sakani cikin farin ciki da jin daɗi mara misali batare dana san ainahin alaƙarta da Junaid ɗin ba, ban zauna ba ganin yarana na samun kulawa duk da tarbiyyarsu ta canja na baro Lagos dan na fito prison ne da dabarun yaƙi kala-kala, nazo kano cikin shigar ɓurtu, nai binciken komai daya shafi Kamila a yanzu, ban zauna ba dan yanzu kam arziƙi na fito nema kodan ƴayana na kuma maida murtani ga ahalina, dan hatta su sai da na bibiyi al'amarin kowannensu nasan halin da yake ciki da abinda yake yi yanzu. Mahaifiyata ta rabu da ƙanin babbanmu bayan ya cinye duk abinda ta gada, tana aure a kaduna yanzu. Wannan shine dalilina na zuwa Kaduna na jinginu da Alhaji Bello dake aminin mijin data aura,(Baban su Hajiya Yaya). Sai da na fara karantar halayensa tsaff sannan naje gareshi da siffar neman taimako, yako taimakeni ɗin ya haɗani da babban yaronsa Alhaji Usman Chalawa. Da farko naso kwantar da kai a jikin Chalawa, amma lissafin ya canja ganin ya sanya min ido yana faman kaffa-kaffa da dukiyarsa, kawai sai na fara masa ɓarna, amma yakai ƙarata ga Alhaji Bello ya tsawatar min, sai na bari na zama mutumin kirki adalilin ƙyalla idanuna akan ƴarsa a ranar, yarinyar bata da kunya, da ganinta kuma idonta a buɗe yake, na koma ta bayan gida domin nemanta ta nuna min ita ba ƴar iska bace, sai na wayance nace mata nima da aure nazo ai. A mamakina sai ta amsheni hannu biyu, ba kuma tai jiran komai ba taje ta sanarma mahaifinta, shiko babu wani ja'in ja ko jin ra'ayina ya bani aurenta, wannan shine dalilin aurena da Sabuwa, a kuma nan ne naga mahaifiyata, itama ta ganni sai dai naƙi saurarenta, na kuma tabbatar mata idan ta nuna tana da alaƙa dani sai na tona asirinta ga mijin aurenta nace itace ta kashe babana ita da ƴan uwana da ƙaninsa nima suka kasheni dan naƙi basu haɗin kai. Wannan barazanar da nai mata ce ta sakata shiga hankalinta, akasha biki aka bani wajen zama nace kano zan zauna. Haka Alhaji ya kama mana haya muka koma Kano, ba wani zama nake sosai ba, dan inata kai-kawon harhaɗe kuɗaɗen mutane, sannan ina shiga cikin ƴan siyasa. Ina kuma zuwa Lagos akai akai duba yarana dake hannun Hajiya Turai da mijinta. Ban gayama kowa a cikinsu na ƙara aure ba har na saki Sabuwa, a lokacin kuma ta haihu yarinya mace. Sai dai ashe da wani cikin ma a tare da ita. Kawai a wata waiwayowa da nayi Kaduna saboda mutuwar mahaifiyarmu na samu Sabuwa ta ƙara haifa min yarinya mace harma an yaye ta, wannan shine dalilin maida aurenmu da ita dan na fahimci zata min amfani a tafiyata, a kuma lokacin ne naje Lagos na samu Turai zataje Kano da su Junaid. Naso hanawa, sai dai rokon da yaran sukaita min yasa na barsu. Ashe zuwan zai yi amfani, dan kuwa a wannan zuwa da tayi Kano dasu na gano akwai alaƙa tsakanin Turai da Kamila, ƙanwar Kamila Nana na auren ƙanin Turai uwa ɗaya uba ɗaya harda haihuwa a tsakaninsu, hasalima ƴar yarinyar da Turai ke riƙo ɗiyar Nana ce, nayi farin ciki sosai, dan haka na samu Turai na ƙara bincike sosai akan Kamila naji harma abinda ban sani ba game da zamanta a gidan Aliyu, burinta na son ƙwace ƴaƴanta a hannun Fateema data bata na har abada. Burin son kai Fateema a ƙasa ta mallaki Aliyu ita kaɗai sai ƴayanta. Dan ana ma shirin yima yaran nata aure babu jimawa da wasu yaran maƙwaftansu. Amma ita Kamila bata so hanyar da zata dakatar da hakan take nema, ta fison babban ɗanta ya auri babbar ƴar Nana. Ta ce a lokacin ma suna ta ƙulla abubuwane amma ita Nana ɗin ce ke gaya mata komai, dan bata da wata alaƙa da Kamila sai ta gaisuwa da zumincin dake tsakaninta da Nana. Naje inata nazarin yanda zan ɓulloma wannan al'amari sai ga Turai ta kirani a waya tana sanar min Nana fa ta sameta da batun shirinsu. Har sun bata damar samo musu wai wanda zaima wata yarinya fyaɗe a ƙannen yaran da za'a aurama ƴaƴan Kamila. Dariya abin ya bani sosai, na kuma tabbatar da Kamila tayi nisa bata jin kira, ba kuma zata taɓa sauyawa ba kwarai da gaske. Amma zan mata kamun kifi a wannan gaɓar, wato na jefa mata ƙaramin kifi dake jikin fatsa, idan ta kama domin ci sai ni kuma na kamata. Kai tsaye nacema Turai mu zamu amshi aikin, kuma Ra'iz shine zaiyi, dan haka ta kaishi gidan a matsayin ɗan ƙanin mijinta, su kuma tace musu bata da alaƙa da shi. Da yake yaran nawa duk sun juye da suffar ƙabila hausar ma tasu a gurɓace take tana kai Ra'iz suka aminta, har ma aka zube masa kuɗin aikinsa dama ƙari a sama. Ke dan ubanki Turai koba haka akai ba?”. Jikin Hajiya Turai na rawa kanta a ƙasa ta ce, “Hakane, duk abinda ka faɗa gaskiya ne. Kuma wlhy ni babu ruwana, sai da suka gama ƙulla shirinsu su biyu Nana da Kamilar sannan na sani. Kai kuma da nazo na gaya maka ka tsara yanda za'ayi, na kai Ra'iz wajensu matsayin ɗan ƙanin mijina, koda aka haɗashi da Ajwaad sai Ajwaad ɗin bai kulashi ba, shine akace ya zauna wajen Fauzan. Shima da farko Fawzan ɗin yaƙi sai da Kamilar tai masa faɗa sannan. An shirya komai zai faru a ranar ɗaurin aure, su Kamilar suka aiko da zoɓo da aka dafa a gidan makwafciyarsu da sunan ta kawo gudummawa ma Fateema, sai dai anyi hakanne kawai saboda ita yarinyar da za'ama fyaɗen wai tana son zoɓo, abinda aka zuba a zoɓon da sunanta kawai akayi dan haka ita kaɗai aikin zaici. Danni lokacin ma ganin abun naitayi kamar bazai yiwu ba, amma sai Nana tace min na jira na gani, ai wanda yay aikin ya iya aiki sosai. Ko ba haka akai ba Kamila! Nana gaku dai da ran ALLAH ba ƙarya na muku ba.....” Nana ta share hawaye tana kallon Abah, ta ce, “Wlhy Aban Fadeel bamu kaɗai muka shirya hakan ba, kai hasalima ni da farko ba dani aka shirya ba Aunty ce da kakar yarinyar da matar ubanta.....” “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un wai Gwaggo da Sailuba?”. Oum data kasa haƙuri ta tambaya hawaye na ziraro mata tun ɗazun. Nana tace, “Tabbas su Hajiya Fateema. Kuma ga Aunty Kamila ɗin nan ta rantse batare suka shirya abinsu ba, sai daga baya aka nemoni a ciki saboda Saheeba ta auri Fadeel.” Idanu sosai Abah ya zubama Mamy, hakama AA da su Yaya Fawzan da Babban Yaya kallonta kawai sukeyi, Sille ya shuri Kamila da ƙarfi har sai da tayi ƙara, ya ce, “Dan ubanki bazaiyi magana ba shaiɗaniya. Annoba”.........✍️

*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*

*+234 805 568 7449*

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣6️⃣

______________

.........Wasu wahallun hawaye suka zubowa Mamy, da ƙyar yanzu kam ma take iya maganar. Ta jinina kai da faɗin, “Wlhy nima bani nace ayi asiri ba, dan tunda nake ban taɓa zuwa wajen malami ko boka ba. Gwaggo da Sailuba ne suka kawo maganin. Amma nice na fara zuwa musu da zancen son hana auren yarana da ƴayan Asiya, saboda nasan Gwaggo bata son Asiya dan tasha kawo min gulmarta akan alaƙarsu da Fateema. Ni kuma dama irin yanda Gwaggon kema Asiya namin daɗi, sai na yarda na haɗe kai da su musamman ma Sailuba, sai ya zama ma nice mai gayama Sailuba duk wani sirrin Asiya, takai duk wani asiri da Sailuba taima Asiya anan gidanmu ake shirya komai a bata taci ta hanyar Maanal batare da sun gane ba, shiyyasa bata gane abinda Sailuban ke mata sai wulaƙancin Baban su Maanal ɗin kawai da take fuskanta. Hatta batun bada zoɓon Gwaggo ce ta shirya komai, sai kuma aka samu matsala ita Maanal tasha zoɓon tare da Ajwaad, duk da ance a jikinta kawai zai yi tasiri abin mamaki sai yayi tasirin har a jikin Ajwaad ɗin ma. Dan lokacin da Ra'iz ya sanar mana Ajwaad yasha zoɓon tare da Maanal bamu damu ba, mukace ya koma wajensu, ya tafi ya haɗu da Maanal zata shiga ɗakin su Ajwaad tana riƙe ciki, shine ya dawo yana gaya mana, ya tabbatar mana Ajwaad na a ɗakin shima. Hankalina ya tashi nace yaje ya kira min Ajwaad ɗin, nan ma ya koma kiransa sai yaci karo da shi ya fito neman Fateema, da wannan damar Ra'iz ya shiga wajen Maanal, ni kuma na tare Ajwaad na tambayesa mike faruwa? Yana faman riƙe ciki shima ya gaya min halin da Maanal ke ciki shine nai masa wayo nace yaje ɗakina ya ɗakko min magani na bata, ya bar Fateema tana cikin taro kada ya tada mata hankali. Yana shiga bedroom ɗina na kulleshi ta baya, ashe nabar wajen ina sauri ban cire key ɗin ba wani kuma yazo ya buɗe shi, wannan shine dalilin komawarsa ɗakinsu ya samu Ra'iz akan Maanal. Daga nan bamu san miya faru ba kawai al'amarin ya juye kan Ajwaad cewar yayma Maanal fyaɗe. Hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, ga Ra'iz mun nema a gidan mun rasa tako ina. Gida kuma ya rikice akan abinda ya faru. Cikin ɓacin rai muna ɗaki inama Gwaggo da Sailuba masifa akan yaya akai haka, bayan sunce maganin Maanal ɗin kawai zaici gashi ya haɗa da Ajwaad, maimakon yaron da muka kawo fyaɗe ya koma kan Ajwaad. Suna cikin min rantse-rantse kawai juyawar da zan yi naga Ajwaad a bayanmu, kuma tabbas yaji komai da muke faɗa. Ƙoƙarin juyawa yake zai fita na damƙoshi, wannan ya bama su Gwaggo damar fita a ɗakin, kuka Ajwaad kemin akan miyasa zanyi hakan? Miyasa zan aikata, takaici ya sakani buge masa baki. Cikin ɓacin rai nace masa nayi ɗin, kuma idan ya sanarma wani ina da alaƙa ko hannu a cikin abinda ya faru ɗin wlhy sai na kashe Fateema da Maanal ɗin, shi kuma sai na tsine masa. Ko tuhumarsa akayi ya faɗi cewar Ra'iz ne ya aikata komai, shi yazo ceton Manaal ɗin ne, kuma daga ranar na haramta masa huɗɗa da Maanal na har abada. Idan kuma ya sake yarda ko zama waje ɗaya sukayi ALLAH ya isa ban yafe masa ba, ko mutuwa nayi idan ya aure Maanal nan ma ban yafe masa ba. Kai yana ma ƙara haɗa alaƙa da zuri'ar Asiya da Habibu koda ta magana ce ALLAH sai na kashe Maanal da Fateema har lahira. Ina gama yimasa wannan barazanar na fito na baroshi a ɗakin, na samu gida ya ƙara rikicewa Fateema ta faɗi, ita kuma Maanal ɗin an wuce da ita gidansu ana kuma neman Ajwaad dan maza sun shigo. Ban san ya akai ba, ban san miya faru ba kawai an tsare Ajwaad da tambaya bayan likita ya tabbatar da amma yarinyar fyaɗe yaron nan ya amsa cewar wai shine yay fyaɗen. Raina ya ɓaci, sai dai ta wani ɓangaren naji sanyi da akace za'a aura masa ita yace baya so, ta haka na fahimci kurarin danai masa akan kashe Maanal da Fateema yayi tasiri kenan. Oho ko'a hakama naci riba ai, tunda aure dai ya fasu, duk da amsar zancen fyaɗen nan da yaron nan yayi har yanzu yana min ciwo a rai, muka zo kuma muka shiga tashin hankalin ciwon daya tsinta kansa a ciki dan ni na Fateema bai wani dameni ba....” “Toke dama kin damu da damuwar wani ne inba taki ba Kamila”. Mabera ya faɗa yana murmushin takaici, sai kuma ya kalla ƙofa da jami'an tsaro keta faman ɓaɓatu amma sunƙi tankawa. Baki ya taɓe ya dawo da kallonsa kan Abah dake ta kallon Kamila ko ƙyaftawa babu. Ƴar dariya yayi da faɗin, “My Darma indai wannan matar ce kaɗan daga abinda zata iya kaji, dan mun yanke maku abubuwa da yawa a kanta ma saboda bamu da time sosai , dan lokacin fara aiki ya kusa cika. Bana son mu wuce 2 a jejin nan. Gashi har 12 ta wuce yanzu. Amma a gurguje zan ƙarasa muku abinda ya rage kodan kasan halin da kake ciki a yanzu kai kanka game da ƙullinta” Sille dake ƴar dariya ya ce, “Gara dai ka faɗa masa kam Baa! Ko dan wannan tsageran ɗan nasa da yayta ɓoye ainahin halin uwarsu da abinda ta dinga aikatawa saboda bata kariya yasan ita ɗin kara da kiyashi ce ɗaukar mara sani, ɓoye hallayarta bazai amfane shi da komai ba. Dan bana son mu rabu basu san komai akan wannan azzalumar matar ba”. Ya ƙare maganar yana shurin ƙafar Mamy har sai da ta saki marainiyar ƙara. Ko'a kwalar rigarsa. Cikin rashin damuwa Mabera ya cigaba da faɗin, “Bayan Ra'iz yabar gidan a wahale ya koma wajen Junaid, ransa ya ɓaci da bayanin da yay masa akan abinda ya faru yace sai ya ɗauki fansa. Nine na hanashi, na kuma sanar masa ai lokaci baiyi ba da saura dan wanan wasan ya ɓaci kuma, dan bai kamata Kamila ta faɗi ba a wannan gaɓar da sauƙi tunda al'amarin ya juye haka. Dan haka na tattara su suka koma Lagos. Sun koma da sati ɗaya Turai ma ta koma nima haka, itace ta bamu labarin dukkan cakwakiyar data ƙarasa faruwa har barinku ƙasar. Anyi haka da kusan wata guda na tafi saudia yin wani aiki, watana kusan uku na dawo, na tarar da wani tashin hankali na asalin halin da Turai ta jefa ƴaƴana a ciki, wato maida Junaid tamkar mijin aurenta. Hankalina ya tashi matuƙa, dan abune da ban taɓa kawoma raina ba. Naci mata mutunci matuƙa, na bayyanawa mijinta ainahin wacece ita, na kuma ce sai mun shiga kotu da ita tunda ta lalata min yara. Da ƙyar mijinta ya lallasheni ya bani maƙudan kuɗaɗe, ya tabbatar min idan wannan maganar ta fito shine zai faɗi a ƙasa, dan dama danginsa basa son aurensu shine ya dage. Kuɗin daya bani ne ya kashe wannan rikici, na canjama yarana anguwa dan hayar gida guda na kama musu, wannan shine sanadin rabuwarmu da Turai, su kuma suka baro Lagos suka dawo Abuja da zama, sai dai ko shekara basuyi ba mijinta ya rasu. A lokacin nima ina tsakanin Kaduna da Abujar amma ko gaisuwa ban mata ba, kai inda take ma ban taɓa nema ba. A wannan gaɓar ne kuma Ajwaad yazo Nigeria, bamu san ta yanda akai ya gano inda Ra'iz yake ba, kawai sai kirana akai wai nazo Lagos ga Ra'iz a hannun jami'an tsaro an kaishi asibiti wani ya masa dukan mutuwa, ya ragargaza masa ƙafafu ya illatashi a gabansa. Hankali tashe naje, zuwa lokacin an kaishi asibiti, hankalina ya tashi da ganin halin da yaron yake ciki, wlhy saika ɗauka haɗarin mota yayi ba duka bane, dukan ma wai na yaro kusan sa'arsa, dan Ra'iz da Ajwaad sa'anni ne ai. Junaid ya shirya ɗaukar fansa a lokacin amma nine na hanashi, muka maida hankali a kan jiyyar Ra'iz, dan bincike ma ya tabbatar min Ajwaad ya sake barin ƙasar dama yazo neman su yarinyar da akaima fyaɗen ne. Sai dai baima sameta ba, Darma yazo ya sake maida shi ƙasar da suken. A ƙarshe dai bayan gama jiyyar Ra'iz ya zama gurgu, sannan an tabbatar mana shi da mace sai dai kallo dan Ajwaad ya masa babbar illa a mazantakarsa. Wannan al'amari ya min ciwo, ya yima Junaid ma. A tsakanin kuma kuka dawo Nigeria cikin Abuja, sai dai bamu samu labari ba sai daga baya sakamakon mu duka munyi nisan kiwo, wannan shine sanadin dawowar Junaid cikin Abuja shima, muka kuma cigaba da bibiyar al'amarinku. Kwatsam kuma sai na ganku a Kaduna bikin ɗan Chalawa, sai dai ban yarda ku kun ganni ba, na taƙaice muku labari dai nine na fallasa batun yima Maanal fyaɗe da ɗanka yayi a wajen bikin nan dan kawai na ƙuntata Kamila da itama bata ganni ba. Daga nan kuma Junaid ɗan Junaid ya bayyana mata ainahin kansa. Abu na ƙarshe da nake son ka sani shine Kamila ta tanadi guba domin kasheka kaima, sai dai ban sani ba ko ta baka gubar ko bata baka ba.....” A wani irin hankali tashe su AA da kowa ma suke kallon Mamy, Babban Yaya ya ce, “Guba?”..........✍️

Readers Also Read