Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 174
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 174: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 174. Tunda Doctor ta tafi tabar Hajiya…
2,528 words
Tunda Doctor ta tafi tabar Hajiya Basariyya a ƙofar gidanta taji ta kasa motsa ƙafarta. Haka ta cigaba da tsaiwa ita ba gunki ba ba kuma mutum mai rai ba. Sai da taji hajijiyar dake jujjuyawa da ita na neman zubar da ita a ƙasa sannan ta daddafa ta shiga mota, kanta ta kife a steering tai shiru tsahon lokaci. Kafin ta tada motar, da farko rasa ma inda zata dosa tayi, sai da ta samu waje ta tsaya tai kiran maman Yaseerah. Harta tsinke bata ɗaga ba, dan hakan ta ɗauki hanyar Zarian. Tunda ta shigo maman Yaseerah ta miƙe tana kallonta, dan suna zaune ne a falo ita da yara suna cin abinci hankali kwance duk da kuwa sunji halin da ƙasar ke ciki akan zuri'ar Darma. Amma tunda ahalin kishiya ne sai abin bai wani taɓata ba ita kam balle damunta. Duk da kuwa akwai Najma da ko ba komai ƴa ce ga mijinta. Yaran kuwa duk da sun shanye a ransu suna cikin damuwa akan ƴar uwarsu. Ai jini ba ƙarya bane ba, duk da uwarsu na rabasu da ƴan uwan nasu shi tuwo dai tuwo ne ba'a sake masa suna. Najma dai jininsu ce dole suji rashin daɗi idan wani mugun abu ya sameta. “Lafiya kuwa na ganki haka? Badai wannan abun dake ta yawo bane ya birkitaki?”. Maman Yaseerah ce ta faɗa tana kallon Hajiya Basariyya bayan sun shiga bedroom saboda yara. Sai da Hajiya Basariyya ta kai zaune a bakin gado hannayenta duka biyu a saman fuskarta ta furzar da zazzafan iska a bakinta... Maman Yaseerah ta sake faɗin, “Ke ko Basariyya ki rufama kanki a siri, har miye tsakaninki da wasu zuri'ar Darma da kikabi kika birkita kanki haka. Dama Huznah ta auri jininsun ne ma sai ace. Kada ki manta Yaseerah da ƴar uwar mijinta ke ciki wlhy banji komai ba tunda ba sonta suke ba balle ke......” “Haba wai mi kike faɗa haka ne? Ki ƙyaleni da abinda ya dameni dan ALLAH. Kin dameni da wani maganar zuri'ar Darma zuri'ar Darma ni ban san miya faru da su ba, tawa ta isheni ma.....” Kallonta kawai Maman Yaseerah take yi a firgice, ganin hawaye share-share a fuskar Hajiya Basariyyan, “Basariyya kuka fa kikeyi? Wai mike faruwa ne?”. “Miye ma bai faru ba, na kai Huznah anyi allurar nan amma ban san yaya akayi ba ta ɓoyo waya ta kira Daddynta ta sanar masa inda muke.....” “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ke ko ya akai kikayi wannan gangancin haka? Yanzu ina Huznar?”. “Sun ɗauke ta shi da Yazeed, na tabbatar asibiti suka tafi kaita”. “Yazeed!? Shi Yazeed ɗin dama ya samu lafiya ne?”. Kasa bata amsa Hajiya Basariyya tayi, dan hankalinta baya anan gaba ɗaya. Shiru itama maman Yaseerah tai tana tunani, zuwa can ta furzar da iska tare da faɗin, “Ihmm nace ba, Hajiya Basariyya bai kamata ace nan kika tahoba ai gaskiya. Dan kinga shi Alhaji Usman zai iya tunanin dani aka haɗa wannan al'amarin, alhalin kuma ban san komai ba gaskiya. Ya kamata ki tashi kije dan nikam ban shirya rasa aurena da ƴayana ba. Nima matsalolin gabana sun isheni. Dan yanzu haka su Yaseerah na hanyar tahowa Zaria”. Sosai Hajiya Basariyya kema maman Yaseerah kallon mamaki, amma sai ta daure ta ce, “Yanzu ni kike kora Hajiya Jummai?”. “A'a nifa ba korarki nake ba Basariyya kada ki canja min magana. Amma dai kin san halin mazan nan namu ba sai na zauna miki bayani ba. Kidai je ɗin idan na samu lokaci zan shigo sai mu tattauna. Dan wlhy bana ma son Abban Yaseerah ya shigo ya sameki a gidan nan akwai babbar matsala. Sannan maganar kuɗina dan ALLAH kiyi ƙoƙarin a cikin satin nan na samesu akwai uzirin daya taso min nima gashi duka abinda ke hannun nawa na tarkata na baki”. Ai kaɗan ya hana zuciyar Basariyya fitowa waje. Maman Yaseerah ta miƙe ta fita a ɗakin, dole Hajiya Basariyya ta miƙe kamar wadda ƙwai ta fashewa ta bita a baya..........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣6️⃣9️⃣
______________
.........Anyi hannun karɓa hannun bayarwa tsakanin Mabera da jami'an tsaron akan Abah da Sille. Duk da dai bai yarda ya bada Abah ba sai da ya shiga mota shi da ɗansa. Kafin ya shigan ya kalla jami'an tsaron da su Baba Sardauna fuska da murmushi ya ce, “Ku kwantar da hankalinku bazan taɓa kashe Aliyu ba duk da shi a baya yayi iƙirarin kashe ni akan laifin da ban aikata ba. Ba buƙatar haka dan shi kam babu abinda ya rage masa sai jiran mutuwar tasa in har ya tabbata matarsa Kamila ta bashi gubar data saya da kuɗinta domin sa. Na yafe masa a yanzu, sai dai ku sani zan dawo ɗaukar fansar ƴayana akan ɗansa Ajwaad....” ya hankaɗa Abah ya wani irin ja motar da masifar gudu. Da gudu wasu a cikin jami'an sukayo kan Abah, wasu kuma suka shiga motoci akabi bayan su Mabera..... Matuƙar tashin hankali su Baba Sardauna sunji akan batun wannan guba. Hakama su AA da suka zo da gudu suka kama Abah. Suna tada shi tsaye akan ƙafafunsa Abbu ya da zancen guba yafi tsayama a rai ya matso ya buɗe idanun Abah, ya kuma ɗaga ƙasan harshensa ya duba. A rikice ya ce, “Mutumin nan fa da gaske yake akwai guba a jikin Aliyu harta fara nuna kanta. Oya ba ɓata lokaci maza muje”. Lallai tashin hankali ba'a saka maka rana, ahalin Darma sun shaida wannan salla. Ana murna an rabu da bukar ashe an haifi habu. Kafin wani dogon lokaci an wuce da su Aba gaba ɗaya cikin jirgi mai saukar angulu. Sauran jama'an da aka bari a jejin kuma suna tattare komai da aka samu. Ga yan jarida har sun ƙaraso sunata ɗaukar komai. Dole kafin isowar jirgin aka tsaida motoci a kan titin asibitin KK domin samawa jirgin wajen sauka. Su Maanal da dukkan ahalin Darma sun fito suma wajen asibitin sunata kuka harma da mutane masu majiyyata. Dan labarin akwai guba a jikin tsohon ambassador Aliyu Darma harta fara yawo. Yanda al'amura suka gudana da batun gubar nan ya tsayama Abah a zuciya, dama ga waɗanda ya jima yana tarama zuciyarsa akan Mamy tsahon lokaci. Zancen lalata mahaifar Oum da kashe masa yaro da Mabera yayi duk sai suka taru suka tsaya masa a ƙahon zuciya. Dan da nan jininsa yay wata irin hayewa ta tashin hankali. Lokacin da ake fiddoshi a jirgin ai komai ya rikice. Da gudu ma'aikatan asibitin suka fita da gadon ɗaukar mara lafiya, yanda ƙirjin Abah ke wani irin ɗagawa da sauka tamkar numfashin nasa zai bar gangar jikinsa dole ne hankalin duk wani mai imani ya tashi. ALLAH sarki Oum sai a lokacin ta yanke jiki ta faɗi. Dama tunda aka baro jejin da su bata furta ko a ba na magana. A take hankalin kowa ya ƙara tashi, itama aka kwasheta zuwa ciki. ALLAH sarki AA tafiya kawai yake, ko gane abinda ke gabansa ma bayayi, Yaya Fawzan kam sarkin karaya jikin Baba kawai ya kife kansa ya fashe da kuka. Babban Yaya dashi aka shiga da Oum ciki. Nibras da tun ɗazun itama sun iso da Mamanta asibitin da Yayunta tunda ita ALLAH ya ƙaddara bata da rabon wahala, dan daga idi ta wuce gidansu duk hidimar da akai babu ita, sai dai itama tasha tashin hankali matuƙa..
Su Abbu kam suna kan Abah, dan ana kaishi ɗakin daya dace sai almakashi aka saka aka yanka rigar shaddar jikinsa ma. Dan danna aka saka masa oxygen. Kwararrun likitoci da suka san aikinsu da Abbu suka fara abinda ya dace. Dai-dai nan kuma saƙon rasa Anum ya isa ga ahalin Darma. Duk da kasancewarta yarinya ƙarama mutuwar tata ta dakesu ƙwarai da gaske. To itama dai Nana sai abinda ALLAH yayi, ita da Mamy dai har yanzu su akwai doctors a tare da su......
_________★ KADUNA
Gab da kiran magriba ALLAH yay ma Nazeerah rasuwa. A dai-dai lokacin da Sabuwa ke farfaɗowa daga sumar wahala. Tashin hankali ya sakata fasa gigitacciyar ƙarar ihun kuka. To ya za'ayi, ta ALLAH ta riga ta tabbata sai kuma haƙuri. (Irin wannan wa'azin mutuwar ake jiye mana shiyyasa akowane motsi na rayuwarmu ake so mu dinga tunawa da hakan. Babu ruwan mutuwa da shekaru, ba ruwanta da gata, bata jinkirtawa kowa, bata rage maka ko sakanni domin tuba ga UBANGIJI ko ga mutanen daka tauyewa hakkokinsu ko zaluntarsu. Ga dai Nazeefa, iyayenta sun cuta mata matuƙar cutarwa, ALLAH yayi mata gata ya bata mijin aure, maimakon ta nutsu ta nema aljannar sai ta shagala, suma suka saka hannu a wajen shagaltar da ita, da taimaka mata cutar da mijinta da zaluntarsa. Ɗan dazai mata addu'a babu, tabar miji da ɓacin rai da takaicin sakashi a masifar rayuwa. Uwa sai a hankali, uba nacan yana ta tashi rayuwar. Ƴan uwa mu daina tunanin dan munada ƙarancin shekaru rayuwa zata cigaba da bamu damar yin abinda muke so har zuwa gaɓar tuba ko tsufa, shi UBANGIJI ba abokin wasan kowa bane ba. Wlhy mu dawo hankalinmu, ki dinga sakawa a ranki idan gari ya waye da wuya kikai dare, idan dare yayi da wahala kikai safiya, mu yawaita istigafari, mu rage ma kammu ɗaukar nauyin mutane koda na kallon banza ne. ALLAH ya gafarta mana ya gafartama iyayenmu 🙏 😭). Ba sabuwa kawai ba hatta su Ammie da su Hajiya Yaya wannan mutuwa ta dakesu ƙwarai da gaske. Ƴar samun nutsuwar dawowar su Maanal duk da ance Abah da matarsa ɗaya da ƙanwar matar tasa na cikin wani hali ya ɗan kawo nutsuwa a zukata kaɗan. Ammie da Nene dake shirin wucewa Abuja jirgin bakwai sai suka fasa saboda wannan rasuwar. Haka shima Daddy da Yazeed dole suka haƙura. Gida suka wuce aka bar gawar Nazeefa da Jaririnta mai tsannanin kama da ita anan asibitin sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai mata sutura a miƙata gidanta na gaskiya. Huznah ma na asibitin aka barta da Salima tunda itace babba..
Tun kafin magriba Hajiya Basariyya ta dawo gidan, sai dai tunda ta shige sashenta ta zauna a falo tai tagumi bata iya ta motsa ba har ƴan asibitin suka shigo kusan takwas na dare. Motsin dawowar mutanen gidan ya saka zuciyarta dukan ɗari-ɗari, sai dai tun tana tsumayen shigowar wani a cikin yaƴanta ko Daddy harta sallama. Dan ko autarta bata gani ba. Kasa haƙuri tayi ta tashi tana leƙawa ta window. ALLAH sai da taji zuciyarta kamar zata zubo dan tashin tashin hankalin hango Sageer, Yazeed, Daddy, Baban Sageer, Yayanta, da Baban su Hajiya Yaya da tayi a tsakar gidan. Da sauri ta nufi bedroom ɗinta kamar zata faɗi. “Na shiga uku ni Basariyya badai na rasa Huznah ba?”. Babu mai bata amsa, ta kai zaune bakin gado, sai kuma ta sake mikewa zaram tayo waje. Sai tayi kamar zata buɗe ƙofar falo ta fita sai kuma ta koma da baya tana girgiza kai. Hawaye kam da tarawa ake da yanzu an cika wani abu ai. Waya ta ɗauka tai kiran Madeena ƴarta ta biyu, amma bata ɗaga ba. Sai ta ƙara ruɗewa tai kiran Maman Yaseerah. Itama dai bata ɗauka ba. Tun tana leƙa window tan hango su Daddy harta leƙa taga su Ƴaƴanta sun shiga mota, sai karaf taji makwafcinsa na faɗin, “Alhaji Usman ALLAH ya ƙara haƙuri, ALLAH ya jiƙanta ya gafarta mata. Bari muje sai da safen an haɗu wajen jana'iza”. Yaraf kake jin Hajiya Basariyya a ƙasa. Ta daddage ta fashe da ihun kuka da faɗin, “Na shiga uku ni Basariyya na bani, shike nan na kashe ƴata da kaina. Wayyo Huznah wayyo ALLAH na. Ba ƙaramin tayar da hankalin kowa wannan kuka yayi ba. Kowane sashe suka shiga fitowa a guje. Amma duk sai Daddy yace su koma. Haka duk suka koma suna jiyo ihun Hajiya Basariyya da kururuwa tana ƙwala kiran sunan Huznah. Tun tanayi da buɗaɗɗiyar murya har muryar tata ta dishe. Daddy kuma ya hana kowa zuwa inda take har ƴayanta. Kuka taci na innalillahi. Daga ƙarshe ta zube anan falon tana nishi ƙarfinta ya ƙare sai hawaye, tayi wujiga-wujiga da irin kukan mutuwar da ba'ason ma musulmi yayi ma mamaci koda ace mutuwar ce.
Washe gari ana idar da sallar asuba dangin su Hajiya Yaya suka fara isowa gidan, musamman mahaifiyarta da ƴan uwanta. Dan da farko ance tunda babu aure tsakanin Nazeefar da Yazeed aje can gidan su Sabuwar ai jana'izar tata sai shi Baban su Hajiya Yaya ya roƙi alfarmar yi anan ɗin, tunda koba komai a wajen haihuwar jinin gidan ALLAH yay mata rasuwar. Ba kuma kowa ma yasan da batun sakin ba sai isu isu. Babu wanda ya nema Hajiya Basariyya balle tuna halin da take ciki har aka iso da gawar Nazeefa cikin gidan dana yaron misalin takwas da rabi. Kukan tashin hankalin da Sabuwa keyi ne ya farkar da Hajiya Basariyya daga barcin wahalar daya figeta da asuba. Ko salla batayi ba. Zane kawai ta yayuba ta ɗaura, ko ɗankwali babu a kanta ta fito daga sashenta tana tangaɗi. Hakan yayi dai-dai da fito da gawar Nazeefa a mota za'a kaita sashenta. Hajiya Basariyya taje da gudu tana kuka ta riƙe gawa ko lura da Sabuwa batayi ba da itama ta riƙe ɗin. Kuka take iya iyawa da kiran ta shiga uku Huznah ta yafe mata. Nan dai ta shiga tonama kanta da kanta asiri akan abinda babu wanda yasan ya akayi daga Daddy sai Yazeed, sai Sageer da Huznah ta turama massege.. Mutane anyi cirko-cirko ana kallonta, sai Ammie ce tai ƙarfin halin zuwa ta kamasu ita da sabuwar, amma babu wanda ya saurareta. Abin ya bama yayan Hajiya Basariyya haushi kawai yazo ya ɗauketa da maruka har biyu. Anan ne fa dole ta saki gawar, taruwa akai ana bashi haƙuri, ita kuma aka kamata aka maidata sashenta. Sai lokacin ake sanar mata bafa Huznah bace ta rasu Nazeefa ce. Huznah na asibiti ita. Wannan shine ya kawo ma zuciyar Basariyya salama. Asiri dai kuma ta riga ta tonama kanta shi ai, dan yanzu dai kowa yasan mike faruwa sai ALLAH wadai ake da halinta........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
*_BOOK 2_* 🅿️➖1️⃣7️⃣0️⃣
______________