Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 175
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 175: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 175. ........Anan Abuja har dare babu wani…
3,319 words
........Anan Abuja har dare babu wani bayani akan Abah da Oum. Dole su Umma suka tattara kowa aka wuce gida musamman ma su Maanal dake buƙatar wanka da abinci tunda an dubasu babu wata matsala. Itace ma dai abinka da mai ciki sai da suka ɗan saka mata drip. Anan aka bar su AA. Gawar Anum ma sai zuwa safiya zasu amsa. Haka suka kwana su da suke gidan, da su da suke a asibitin babu wani kwanciyar hankali.. Washe gari anayin sallar asuba suka koma asibitin. Isarsu babu jimawa kuma ta ALLAH ta kasance akan Nana itama ALLAH ya ɗauke kayarsa. Gigicewa su Nuratu sukayi matuƙar gigita ma kuwa. Musamman Saheeba da sai lokacin ta farko daga nata barcin wahalar. Dan itama dai ta maku matuƙar makuwa. Ga ciki ya fita gaba ɗaya mahaifarta kuma ta samu babbar matsalar da har abada bazata sake haihuwa ba. ALLAH sarki Aunty kuka take tana ƙari ƴan uwa duk suna neman kuɓuce mata. Dan itama dai Mamy ɗin sai a hankali. Ga abin kunyar data tafka na ciyar da Abah guba, wai uban ƴayanka kai jama'a, wannan wane irin rashin imani ne da bushewar zuciya. A yanzu haka tana kwancen amma hannunta ɗaya da handcuffs. Dan ita ƙarƙashin ma jami'an tsaro take. Mahaifin su Nuratu ma da ƴan uwansu duk sun iso Abujar. Haka suka ɗauki gawar Nana suma aka nufi gidan Hajiya Turai da ita. Ita kuma Anum gidan Darma. Saheeba kam ma babu damar barin asibiti, haka ta dinga kuka sai da akai mata allurar barci mai ƙarfi. Umma ce tama Anum wanka, aka sallaci yarinyar aka binneta anan cikin gidan ta garden tunda yarinya ce sosai. Amma rasuwarta ta daki yan gidan, dam itace suka fara rasawa a gidan yarinya mai wayo. Sauran na baya da suka rasu duk ƙannanu ne basa wuce 2years. Itako har ta kusa 5 ma. Da yake su AA duk da su aka sallaceta suna gida. Suna ƙoƙarin komawa asibiti Baba Sardauna ya hanasu yace suje suyi wanka su kwanta su huta, zuwa anjima sai suje suyi gaisuwar Nana itama dan su su Baban sunje dasu akayi jana'iza ma. Sune dai basu je ba. Badan sun so ba suka zauna ɗin. Maanal na falo tare da su Shahidah sun gama yima su Ammie gaisuwar Nazeefa da itama har an kaita makwancinta AA ya shigo. Har zai wuce sama ganin su Shahidah yasa ya dawo ya zauna suka gaisa. Sun masa ta'azziyar Anum da Nana, da yima su Abah addu'ar samun lafiya. Sannan suka sanar masa saƙon Ammie. Sai yanzu yake jin rasuwar Nazeefa shima. Sosai abin ya dakesa matuƙa, ya dinga ambaton innalillahi wa-inna ilaihiraji'un dan gaskiya yaji mutuwar yarinyar itama. Kai jama'a duniya-duniya, duniya budurwar wawa kenan. Ashe duk abinda yarinyar nan ke aikatawa rayuwa tazo mata gangara, kai kai kai iyayenta sun cuceta wlhy. Da wannan sambatun a zuciya ya tashi ya haura sama. Sai lokacin Maanal tai ƙarfin halin miƙewa zata bishi. Harta fara tafiya Shahidah tai kiranta. Dawowa tayi ta zauna. Shahidah tace, “Ki samu wani abu mai ɗan ruwa-ruwa ki haɗa masa Maanal ya samu ya ɗan ci, sannan ki daina wannan kukan kodan ki ƙarfafashi, amma a haka ai karyar masa da zuciya zaki sake yi, bayan yanzu mai ƙarfafashi yake buƙata”. Kanta ta jinjina mata, tasa bakin hijjab ɗin jikinta ta share fuskarta. Da kanta taje kitchen ta haɗa masa tea tana son soya masa ƙwai bazata iya ba dan bata son ƙamshinsa yanzu. Sai kawai ta haɗa masa sandwich tai toasting ɗinsa tunda tasan yana so, ta ɗaura a ƙaramin tray da ruwa ta nufi saman. Kai tsaye bedroom ta nufa ganin babu shi a falon, dama tasan da wahala ya zauna. Maybe ma wanka yake dan yau kwana kusan uku rabonsa da wanka daga shi har su Yaya Fawzan. Sosai gabanta ya faɗi ganin duhu a ɗakin ya kashe fitila, cikin ƙarfin hali ta kunna mara haske saita hangoshi can a zaune a ƙasa kan carpet ɗin gaban gadon kansa a duƙe ya riƙeshi da hannayensa duk biyu. Cike da sassarfa ta ƙarasa ta ajiye tray ɗin a table ɗin gaban sofa ta nufi inda yake. Duƙe ta kai a gaban nasa, tare da kama hannayen ta janye. Karo na farko ya ɗago idanunsa da gaba ɗaya sunƙi ko sassauta jan da suke ciki tun a randa su Mabera suka tafi da su sai ma ƙara rinewa da sukeyi ya zuba mata. Ita sai tama ji kamar jikinta na kaɗuwar tsoro. Amma sai ta daure ta dake itama tana kallon cikin idanun nasa. Hawayen dake neman zubo mata yasata matsawa ta shige jikinsa kawai ta ƙanƙamesa. Shiru yayi tsahon lokaci bai motsa ba, bai kuma rungumeta kamar yanda ya saba ba shi. Tsahon mintuna biyu suna a haka shiru kafin a hankali yay mata zobe da duka hannayen nasa ya ɗaura haɓarsa a saman kanta ya lumshe idanunsa a karo na farko sai ga hawaye a fuskar maza yau ma. Maanal bata san kuka yake yi ba sai da suka ɗiga mata a saman goshi ta ɗago da sauri tana kallon fuskarsa. A firgice tai yunƙurin tashi amma sai ya hanata, sai ma kife fuskarsa da yayi a saman cikinta hawayen suka cigaba da sauka. Itama an kai gaɓar da bazata iya riƙe nata ba, sai kawai ta ƙanƙame kansa dake a cikinta ta fara nata. Dole su baka tausayi, sun tsara abubuwa masu yawan gaske a wannan bikin sallar da yawace-yawace daban-daban amma komai ya juye, juyewa mai ban mamaki da tashin hankali. Sunsha kukansu har suka gode ALLAH, batare da kowa yacema ɗan uwansa komai ba akan hakan Maanal ta tashi ta cire hijjab ɗin jikinta ta ɗakko tray ɗin data shigo da shi ta dawo gabansa. A yanzu ya kwantar da bayansa ne jikin gadon kansa na a saman gadon yana kallon sama, fuskar Mamy kawai take masa kai-kawo a cikin idanunsa sanda take zayyane musu ainahinta. Hannunsa ta kamo, hakan ya sashi ɗagowa yana kallonta. Murmushi tai masa, muryarta a dasashe tace, “Tashi kaci abinci sai kayi wanka”. Kai ya girgiza mata alamar a'a. Shiru tayi tana kallonsa, idanunta na cika da sabuwar ƙwalla. A hankali ya sake girgiza mata kai alamar kada tai kuka. Sai kuma ga hawayen, muryarta na rawa ta ce, “In dai baka son nayi ka tashi kaci abinci dan ALLAH. Besty rayuwa bazata yiwu da yinwa ba. Abinda ya faru ya riga ya faru, ƙaddararmu ce kuma tun ran gini tun ran zane. Yanda bamu hanata faruwa ba, bamu isa gogeta a jikinmu ko zukatanmu ko kundin tarihinmu ba a yanzu. Amma zamu iya tawakkali da haƙuri da juriya sai komai yazo ya wuce tamkar ba'ayi ba koma bai faru ba. An jarabci ANNABAWAN ALLAH, an jarabci Sahabbai, dammu UBANGIJI ya jarabcemu sai kuma mu kasa haƙuri da godiya a gareshi bisa sauran ni'imomin da yay mana a rayuwa kashi-kashi. Bayan kuma ta hanyar haƙurin da juriyar ne kawai zamu nuna godiyar tamu a gareshi. Dan ALLAH kaci abinci, kayi wanka ko yaya zakaji nauyin zuciyarka ya ragu, zaka samu ƙarfi kaima da sasautawar abubuwa. Kalla kaga Babynka shima kuka yake yi fa tun jiya” Cikin nata data dafa ya zubama idanu, sai kuma a hankali ya saki ɗan guntun murmushi da kai hannunsa kan cikin shima yana shafawa. Yanda take masa magana cikin lallashi da karaya ya sake saka zuciyarsa raunana. Maanal da Oum kaɗai ke saka zuciyarsa irin wannan laushin da karayar a lokaci ɗaya. “Zakaci ko?”. Ta faɗa a hankali. Kansa ya jinjina mata shima a hankalin, sai ta lumshe idanu tana sakin murmushi, tare da matsawa ta sumbaci lips ɗinsa da suka ɗan bushe suka tattare waje ɗaya. Sannan ta matsar da bakinta cikin kunensa ta raɗa masa, “I love you my Root-Soul”. Siririyar ajiyar zuciya ya sauke, ya shafa kanta kaɗan. Itama sai ta gyara zamanta kawai ta fara bashi abincin. Fuska a yatsine yake amsa, kai daga gani kasan baya masa wani daɗi. Amma duk yanda yaso dojewa Maanal bata yarda ba, sai da ta tabbatar yaci sosai sannan ta barshi. Ta maida tray ɗin gafe ta tashi. Bayi taje ta haɗa ruwa masu ɗan ɗumi tasa kayan ƙamshi a jacuzzi sannan ta fito, yana zaune inda ta barsa idanunsa a lumshe batace komai ba ta durƙusa gabansa ta fara cire botiran gaban rigar, sannan ta zare agogon hannunsa ta taimaka masa suka cire rigar. Duk fa yafi ƙarfinta ta shiga kiciniyar kamashi wai ya tashi, shi sai ma taso bashi dariya. Amma sai ya biye mata, ganin ta fara ƴar zufa ya ɗanyi murmushin gefen baki ya miƙa da kansa. Kayan ta taimaka masa suka ƙarasa cirewa sannan suka nufi bayin, ta juyo zata fita ya riƙota, zatai magana yay mata alamar zipping a baki, tare da ɗaukarta cak suka shige cikin ruwan a tare. Lokaci guda suka saki ajiyar zuciya, ɗumin ruwan da ƙamshinsa na ratsa musu jiki. Da taimakonta wankan ya gudana, daga baya kuma salon ya canja saboda yanda ta dinga jan ra'ayinsa. Al'amarin kamar zai tsaya a wasan sai aka ɗauki wata hanyar daban, dole dai bayan anyi wanka an fito sai da aka sake komawa yin wani. ALLAH sarki AA sai sauke ajiyar zuciya yake, ko yaya kulawar da Maanal ta bashi ta rage masa nauyin ƙirjinsa sosai. Dan cikin ikon ALLAH suna kwantawa barci yay gaba da shi, itama tun tana kallon sa har barcin ya kwashe ta. Basu tashi farkawa ba sai 2 da wasu mintina. Hakan na nufin sun makara salla. Wanka suka sake yi sannan sukai sallar azhar, suna idarwa Maanal ta fita nema musu abinci.........✍️
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*+234 805 568 7449*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
171
.........Su Shahidah sun gudu, sai abinci data samu jere a dining. Murmushi tayi cikin jin daɗi da ƙaunar ƴan uwanta, ta haɗa komai ta koma sama. Yanzun ma haka taita hillatarsa da lallashi da magana mai daɗi ya ɗanci, itama yana bata kamar yanda take bashi har sukaci sosai. Ta sakko kawo kwanikan ƙasa ta samu Najma ta shigo sashen nasu. Sai da suka gaisa dan rabinsu da juna tun safe, Najma tace, “Ya jiki-jiki?”. “Lafiya ta lau, ni daina min sharri”. “Ai bance komai ba daman, Yaya AA fa?”. “Yana sama, yanzu na samu ya ɗan ci abinci da ƙyar. Jikinsa zafi rau da zazzaɓi amma ya gaddame min wai lafiya Lau yake shi”. Sai da Najma ta sauke ajiyar zuciya. Ta ce, “Nima matsalar da nazo da ita kenan. Tun ɗazun nake fama da Yaya Fawzan amma yaƙi ma cin komai shi. Wlhy yanzu harda kuka na amma ina fita kiran Babban Yaya saina samu ha kulle kansa a ɗakin ma. Ga babban Yaya ya fita abokansa sunzo masa gaisuwa”. Gaba ɗaya hankalin Maanal ya tashi, ta ce, “Ina zuwa bari na kira shi”. Kai kawai Najma ta jinjina mata. Sai kuma takai zaune a hannun kujera tana jiran fitowarsu. Bata wani jima da shiga ba sai gasu a jere sun sakko. Najma ta gaida AA, ya amsa mata da kulawa yana tambayar miya faru. Bayani ta kora masa kamar yanda ta sanar ma Maanal. Ya ɗan lumshe idanu ya buɗe tare da faɗin, “Muje na ganshi”. A tare suka tafi har Maanal, suna gab da shiga sashen sai kuma ga babban Yaya daya shigo ya hangosu, tsayawa sukai har ya ƙaraso, AA yay masa bayani. Cikin damuwa ya ce, “Kasan Fawzan da saka damuwa a rai, kaima ai daga gani ba lafiyar ce da kai ba”. “Yaya lafiyata ƙalau”. “Haka ne”. Cewar babban Yaya yana kama hannunsa suka shige cikin sashen su Najma ɗin. Dai-dai nan Nibras ke sakkowa daga sama zatama ƙawarta da tazo musu gaisuwa da jaje rakkiya. A tare suka tsaya cak. Ƙasa-ƙasa ƙawar tata tace, “Friend ku kam dai ALLAH yay muku arziƙin ƙyawawa a gidan nan. Shi kuma wannan dake tare da mutuminki fa?”. “Humm shine babban yayansu gaba ɗaya. Ƴarshi ce ai aka kashe”. “Wayyo, ALLAH ya gafarta mata. Amma ina zasu haka?”. “Oho, maybe wajen ɗan uwansu, dan naga matar nata buga ƙofa wai ya rufe kansa sanda nake ɗakko miki ruwa. Kinga muje na rakaki ni kam wanka nake son shiga”. Sun sakko gaba ɗaya suka samu su AA na knocking ƙofa da kiran sunan Fawzan, hakan ya sasu fahimtar babu lafiyar dai da gaske. Suma sai suka tsaya. Fin mintuna biyar har su Maanal suna kiran sunansa suma sannan ya buɗe ƙofar, zai juya ya koma Babban yaya ya riƙo hannunsa ya fito da shi. Sai kawai Fawzan ɗin ya rungumesu su duka yana hawaye. Ganin haka Maanal ta kalla Najma, sai kuma ta kalli su Nibras data ƙurama AA ido kamar wata mayya, cike da takaici ta ce, “Kamar mu basu waje zai fi”. Daga Nibras har ƙawarta abin ya basu haushi, amma basu ce komai ba suka haɗu su huɗun suka fice. Kukan Fawzan ya karya musu zuciya su duka, cikin kujeru suka koma suka zauna. Babban Yaya yace, “Haba Yaya F ɗin Lilly, yanzu kana kuka Auta da Lilly kuma suyi me su da suke ƙannenka. Najma, Nibras idan sunyi su yaya zaka lallashesu. Abinda ya faru ai ya riga ya faru ko......” “Amma bazai taɓa ya gogu a zukatanmu ba Yaya. Ace mahaifiyarmu tai yunƙurin kashe mana mahaifi da guba, duk abubuwan data aikata a baya basu isheta ba kenan, ta hanamu auren waɗan da muke so, duk hallacin da Oum tai mata ta maida wannan alkairin da sharri. Haba wannan wace iriyar zuciya ce, wane irin tunani ne? Inama ace Oum ce ta haife mu ba ita ba, wlhy ji nake kamar na kashe kaina nama huta kawai”. Babban Yaya ya riƙo hannunsa tare da ɗora kansa a kafarɗarsa, shima AA ɗin haka ya kamo hannunsa ya ɗaura kansa a ɗayar kafaɗarsa. A hankali ya haɗiye nannauyan abinda ya riƙe masa maƙoshi, sai kuma yay murmushi mai ciwo hannayensu a cikin na juna. “Kuyi haƙuri ƴan uwana kuyi haƙuri. Ita rayuwar kanta gaba ɗayanta ma jarabawa ce. Ni kaina tsakanin shekaran jiya zuwa yau ji nake inama Oum ce mahaifiyar mu ba matar nan ba. Amma haka UBANGIJI ya tsara, ya fimu sanin dalilin yin hakan kuma. Sannan ai koba komai ya mana rahama da gatan zama a ƙarƙashin tarbiyyar Oum da rainonta. Idan muka nutsu zamu fahimci akwai wani ilimi da darasi a cikin hakan. Sheɗanin saurayinta da taso harta iya sallamawa rayuwarta dan karya kuɓuce mata ya cutar mana da Oum ɗin mu da Abah ta hanyar lalata mata mahaifa da kashe mana ɗan uwanmu. Sai ya jarabceta da auren mahaifinmu tazo ta haife mu, ta ɗauka da hannunta ta mallakama Oum domin ƙuntata mata ta mallake mata mijin da ita batayi ƙyashin ɗauka ta bata ba. Amma sai ALLAH ya saka ma Oum kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ya kwaranye mata dukkan damuwarta. Ta rainemu babu mugunta babu cutarwa, babu mahalukin da zai iya tunanin ba itace ta ɗauki cikinmu da shayar da mu ba sai in an faɗa. Wani ma in za'a kwana ana faɗa masa zai kwana gardama ne. ALLAH kuma ya dasa mana soyayyarta da ƙaunarta muma, ta yanda koda wasa baku taɓa jinta a matsayin da bana uwa ba. Ita ko ta ƙare tsahon rayuwarta wajen ganin ta ruguza wannan kyauta, ta ƙuntata mana Oum. Ta nisanta kanta da mu, ALLAH ya hanata kowacce irin damar samun shaƙuwa da mu. Mu ɗin rainon Oum ne, tarbiyyar Oum ne, mallakin Oum ne mizai sa mu damu kammu, mizai sa bazamu cigaba da godema UBANGIJI ba. Bazamu wulaƙantata ko tozartata ba darajar haihuwa da wahalar ɗaukar cikinmu da tayi, amma in har mahaifinmu ya rasa rayuwarsa akan abinda muke da yaƙinin itace ta aikata bazamu ƙyaketa ba. Bazamu yafe mata ba. Bana son sake ganin hawaye a idanunku, mu duƙufa yima iyayenmu addu'ar samun lafiya mai amfani da ɗorewa, sannan mu ƙarfafa kammu ta yanda suma zasuji ƙarfin amsar komai cikin sauƙi.” Cike da fahimta da gamsuwa suke jinjina masa kai. Ya ajiye hannunsa cike da kulawa da lallashi ya ce, “Promise bazan ƙara ganin kuka ko damuwa daga idanun Mazajen Oum da Abah ba”. Suma hannayen nasu suka ɗora akan nashi sukace, “Promise”. Murmushi yayi musu, yaja hancin Fawzan, ya juya yaja na AA shima. Sai suka sanya ƴar dariya dan sun tuna baya. Abincin da su Maanal suka ajiye ita da Najma a falon Babban Yaya yace su sauka ƙasa suci. Duk da AA yaci abinci bai musa ba, haka suka sauka kan lallausan carpet ɗin dake ta tashin ƙamshi suka zauna, AA ya zuba musu a plate ɗaya, ɗiba babban Yaya yayi ya bama Yaya Fawzan a baki, ya sake ɗibowa ya bama AA shima a baki. Sai shima Yaya Fawzan ya ɗibo ya bama Babban Yayan sannan ya bama AA, shima AA haka ya ɗibo duk ya basu. Haka suka dinga bama juna abincin su Maanal na leƙensu ta window suna murmushi da share hawaye har suka kammala. Babban Yaya ya ɗauka box ɗin magani da Najma ta ajiye ya duba musu na zazzaɓi ya basu suka sha. Yaya Fawzan daba son magani yake ba sosai sai yamutsa fuska yake, sai abin ya basu dariya suka hau tsokanarsa. Bayin ALLAH a haka suka ɗan saki jikinsu har akai kiran la'asar suka fita salla. Daga can ne Baba Sardauna ya ce su wuce suyi gaisuwa gidan Hajiya Turai. Badan sun so hakan ba suka shiga mota ɗaya suka tafi, babu wanda ya bisu dan Baba Sardauna yace a basu damarsu kwana biyu kodan su dinga tattauna abinda mahaifiyarsu ta aikata, hakan zai rage musu damuwa da nauyin zukata.....
________★
Ƙiri-ƙiri dai an gagara kama su Mabera a jejin nan. Domin kuwa lokacin da jami'an tsaro suka bisu bayan ya saki Abah abin mamaki motar aka samu a hanya kawai babu su babu dalilinsu. Babu ɓata lokaci jami'an suka fita a motocin suma suka watsu a cikin jejin, amma tako ina babu su babu alamunsu. Hakan ya tabbatar musu sun san jejin matuƙar sani, amma suna da tabbacin lallai basu bar jejin ba suna a ciki. Dan haka tsahon kwanaki biyu jam'an nan na dajin sai ma wasu da aka ƙara musu tako ina aka zagayeshi.....
Ilai kuwa su Mabera na dajin, abinda jami'an suka kasa fahimta a dai-dai inda motar tasu ta tsaya daga ƙasa rami ne, waɗan nan ramuka akwaisu da yawa a cikin dajin sun kuma yisu ne dama domin yin mafaka idan irin haka ta faru. Shiyyasa ba ramukan kawai ba hatta motocin su nada irin tsarin da in har suka tsayar da su a dai-dai inda ramin yake zasu shige daga cikin motar batare da an gane komai ba. A kowane rami akwai abinci, akwai ƙofofin da iska ke fita tamkar tagogi sai dai an musu tsari da sai mai matuƙar lura ne zai fahimta, dan bututai ne aka fidda ta nesa da ƙofar samin. Hankalin Jami'an tsaro na akan kawai sun ajiye motar sun fita ne, dan haka suka maida hankali a ta nema kawai motar kuma aka rufeta kawai. Ko motsa ta a wajen ba'ayi ba. A cikin rami duk wani taimako Mabera ya bama idanun Sille amma ya kasa buɗe su, abin tashin hankalin ma fuskar Sille wata irin kumbura tayi dam kamar wanda aka daka. Ko yaya ya tauna abu kuwa har cikin ƙwalwar kansa. Dan jijiyar ido nada alaƙa da matauna sosai. Shi kansa Maneran wani irin ciwon kai mai azaba ne ke neman tarwatsa masa brain. Cikin kwana biyu sunyi wujiga-wujiga dan wannan dai maɓoya banbancinta da kabari ai ƙalilan ne. Tun fa suna jin zasu iya daurewa zaman koda sati guda ne idan jami'an suka gaji zasu bar wajen har suka fahimci abin fa ba wasan yara bane. Sille ya fara kuka rurus akan gaskiya bazai iya ba asan mafita.......✍️
😆Babbar magana ance da MAƘASAU BAWA🏃🏼♀️😂🤯.172