Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 176
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 176: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 176. ..........A ƙofar gida su AA sukaima…
3,261 words
..........A ƙofar gida su AA sukaima baban su Nuratu gaisuwa. Basuyi niyyar shiga cikin gida ba sam dan kaf ahalin Mamy a yanzu ko ganinsu basa son yi. Amma sai baban su Nuratun ya basu tausayi da yi musu kwar jini, dan kuwa shi ɗin dai mutumin kirki ne. ALLAH yayi masa jarabawa ne kawai da auren Nana. Shine yay musu jagora har cikin gidan. Babu wani mutane sosai, dangin shi baban nasu ne kawai ba kowa ba, sai Aunty, sai ita Hajiya Turai da Nuratu. Dangin su Mamy ɗin ma sai gobe ne zasu taho jibi ai addu'a da su kamar yanda sukace. ALLAH sarki Aunty baiwar ALLAH, tana ganinsu kawai ta fashe da kuka. Sai suma zukatansu suka karaya. Cikin ƙarfin hali Babban Yaya ya dinga bata haƙuri da mata nasiha. Nuratu ma kallonsu take tana kuka mai taɓa zuciya. Musamman AA jitake a yanzu bata da kowa sai shi, amma tasan ta rasa shi, rasawa ta har abada. Hajiya Turai kam kunya ce ta isheta, dama gaba ɗaya bata da wata sakewar amsar gaisuwar, tama fi zama a ɗaki sai in zafi ya isheta ne take fitowa. Amma al'amarin ta da Sille daya fito yasa gaba ɗaya kunyar mutane da nauyinsu ya hanata sukuni. Ga tashin hankali da tsoron kada a kama su Sille su tona mata asiri akan mutuwar mijinta. Shiyyasa cikin addu'a take a dukkan motsinta na ALLAH yasa kada a samu su Mabera. Ta sansu tasan halinsu akan indai ta kife to sunfi son a hau tsanin kowa ma ya rasa dan bakunansu ba masu suffar yin shiru bane ba sam. Kuɗi masu yawa su AA suka ajiye ma Aunty sukace gashi nan ayi duk abinda ya dace, dan su hankalinsu ya rabu kashi-kashi ga asibiti ga suma da mutane a gidansu ga kuma nan ɗin. Sosai Aunty ta fahimcesu, ta kuma yi musu addu'a da godiya da sanya musu albarka. Da zasu tafi ta biyosu har harabar gidan. Muryarta na rawar kuka ta ce, “Dan ALLAH Fadeel kuyi haƙuri kunji, bamu da abinda zamu baku ko lallashin zukatanku a yanzu sai haƙurin kawai. Ku ɗauki dukkan abinda ya faru a matsayin ƙaddararku kuma jarabawarku. UBANGIJI yay muku ni'imomi da yawan gaske, ku gode masa ta hanyar haƙuri akan wannan ƙalubalen zaku cigaba da zama a masu nasara. ALLAH ya bama Fateema da Mahaifinku lafiya, ya tashi kafaɗunsu. Dan ALLAH kada wannan al'amarin ya saka ku gujemu ko ku gujeta, ALLAH shine mai hukunci akan kowa ku kuyi biyayya da haƙuri matsayinku na ƴaƴa sai ku ribantu da tagomashi mai yawa”. A kan laɓɓa duk suka furta Amin. Babban Yaya yace, “Ba komai Aunty in sha ALLAHU zamu kasance fiye da yanda kike fata. Bazamu manta da ku ba, ba kuma zamu yadda ku ba dan bakuyi mana laifin komai ba. Musamman ke, wadda ma zamu ce ta mana kaifin ALLAH ya amshi kayarsa, sai muyi haƙuri tunda itama bata aikata dan kanta ba sanyata akeyi. ALLAH ya gafarta mata ya yafe mata kura-kuran ta”. Aunty tace Amin tana share hawayenta. Sai kuma ta miƙa musu waya tana faɗin, “Akwai video recording da marigayiyya tasa nai mata a daren shekaranjiya tace na baku. Dan ALLAH ku daure ku gani da saurara yana da amfani”. Babu musu Babban Yaya ya amsa, daga haka sukai mata sallama suka tafi dan kukanta ɗaga musu hankali yake sosai. Suna son matar da ganin kimarta da mutunci sosai......
_________★
A Kaduna ma dai gidan Chalawa cike yake da ahalin su Hajiya Yaya da na Alhaji Usman kansa. Dan mafi yawa ana zuwa gaisuwar ne domin mahaifin Hajiya Yaya da Daddy da Yazeed. Amma danta Sabuwa wake ma ta tata. Yau bayan la'asar sai ga tawagar ƙawayen Sabuwa. Da farko kowa ya ɗauka gaisuwa sukazo yi, amma sai me ƴan sanda ne biye da su. Ba tausayi ko shakka matar Bakori farkar Mabera ta nuna Sabuwa tace, “Ita zaku kama. Duk inda mijinta yake ta sani, dan haka ku kamata ta faɗa maza a kamo shi ya dawo min da dukkan dukiyata. Idan ba haka ba wlhy sai dai ai gwanjon gidansu da duk abinda ya mallaka a maida min kuɗaɗena”. Wata shegiyar dariya ƙawayen suka sanya harda tafawa kamar ba gidan mutuwa ba. Rawa jikin sabuwa ya fara yi, muryarta na rawa alamun tahowar kuka ta ce, “Zahedah Baki san mutuwa akai min ba? Ba ki san na rasa Nazeefa ba ne?”. Sai da ta watsa mata kallon sama da ƙasa sannan ta ce, “Ke ma bakiji bakinki miya faɗa ba ne, ban san an miki mutuwa ba? (An miki!) Kinga kenan ke ta shafa ko. Na gaji da wannan ka-ce-na-ce ɗin, jami'ai bismillah.” Ba ƙaramin mamaki al'amarin ya bama mutane ba, su Daddy ma dake ƙofar gida duk sun shigo. Ganin da gaske yan sandan sakama Sabuwa handcuffs zasuyi Daddy yay magana. Sai suka dakata suna kallonsa. Shima kallonsa ya maida ga Hajiya Zahedah, ya ce, “Hajiya kince mijinta ya ci miki kuɗi, to ita minene nata da zaki zo kisa ƴan sanda su kamata a randa aka cika kwana biyu kacal da kai ɗiyarta kabari. A lokacin da ya amshi kuɗin ki ta sani? Ko itace ta zama shaidar amsar miki kuɗi?”. “Babu ɗaya Alhaji Usman, amma ai matarsa ce, komai nashi ta sani. Duk abinda ya wawuro ɗin bada ita suke ci ba, duk kuma tsiyatakun da yake aikatawa ai ta sani”. “Koma dai minene wannan ai mijinta ne. Dan haka nan gida nane, babu wanda ya isa kama Sabuwa ya fita da ita sai dai idan ta fito wannan duk abinda kukai mata ya rage tsakaninku ku da ita. Amma a yanzu dai baku da wannan hurumin. Dan haka kafin na ɗauki matakin shigo min gida ma da kukayi kuna neman tayarma iyalina hankali ku kama gabanku ku da ƴan sandan, idan ba haka ba suma zan ɗauki mataki a kansu. Ai ban san lalacewata a garin Kaduna takai har hakan ba. Amma bari na kira cp naji koda yardarsa ku jami'an nasu kuka shigo min gida ina tsaka da zaman makokin ƴata”. Sosai hankalin ƴan sandan ya tashi, dan sun san Daddy yanada ƙarfin faɗa ajin da ko gwamna yace zai kira zai iya hakan, nan fa suka shiga bama Daddy haƙuri da tabbatar masa su wlhy basu san haka al'amarin yake ba, da taje station ba abinda ta gaya musu kenan ba shiyyasa suka zo. Da ƙyar da kyar aka samu Daddy yabar batun kira. Ƙawayen Sabuwa suka fita suma suna jaddada mata zata fito a gidan Chalawa ɗin ai suna nan suna jiranta. Ba ƙaramin mamaki wannan al'amari ya bama kowa ba, mahaifiyar su Hajiya Yaya ta fashe da kuka. Ita kanta Sabuwar kuka take yi sosai ga ƙafa tana fama ga hannu da ɗaurin karaya, ga raɗaɗin zafin mutuwa gana abin kunyar da miji ya jawo mata, wasu ma suna zuwa gaosuwar ne da biyu badan ALLAH ba....
★★
Duk wannan abun dake faruwa Hajiya Basariyya na sashenta ita kaɗai, dan tunda aka fara zaman gaisuwar nan babu wanda ya taɓa shiga inda take, har ƴaƴanta gaba ɗaya sun tare a sashen Ammie da Hajiya Yaya. Tana son ta fito amma ta kasa saboda tsoron gamuwa da Daddy ko ƴaƴanta. A jiya da taji ƴan Zaria sunzo tanata baza ido taga Hajiya Jummai ta shigo mata amma shiru. Ƙarshe ma tana leƙensu ta window ta hangosu suna shiga mota suka wuce ko kallon sashen ta Maman Yaseerah batai ba. Al'amarin ya girgizata matuƙa, ta ɗauki waya tai kiranta taƙi ta ɗaga. Sai da ta dameta sannan ta ɗauka a daƙile tace mata lafiya. Zuciyarta na rawa tace, “Aminiya kona miki laifi ne, kece wai har zaki shigo gidanmu ki fita baki ko kalla sashena ba”. Babu ko ɗar Maman Yaseerah ta ce, “To kinga laifina ne Basariyya, ko so kike nazo inda kike mijinki da nawa mijin su ɗauka da saka hannuna a cikin taɓargazarki na zubar da cikin yarinya gata can rai a hannun ALLAH a asibiti. To lalala wlhy ni yanzu nasan ciwon kaina. Ke ni bama wannan ba, nace miki ina buƙatar kuɗina amma najiki shiru babu wani bayani. To gaskiya kiyi ƙoƙarin daga nan zuwa kwana biyu dan zanyi amfani da su ne. Sannan ki ɗan rage min irin wannan kiran a waya bana son mijina ko yaƴana ma wani ga gani, abinda ya daman nima ya daman ji da taki damuwar”. Ƙit ta yanke kiranta. Tun daga wannan yanke kira har yanzu Hajiya Basariyya ta gagara dawowa dai-dai. Mamaki da ruɗani sun saka rayuwarta a gaba..
Washe gari akai addu'ar uku. Dan haka kowa ya fara shirin tattarawa domin wucewa. Har ita Sabuwar duk da bataso haka ba Baba yace ta tattara ta koma gidanta tai jiyya. Suma dangin su kaf kowa ya kama gabansa, sai iya su ƴan gida kawai suka rage. Bayan sallar azhar sai ga ƴan sanda sun doka sallama. A lokacin Daddy da Yazeed sun tafi Abuja domin yoma ahalin Darma jaje. Da yake so suke suje su dawo a ranar shiyyasa ana yin addu'a suka tafi harda Baban su Hajiya Yaya. Su Ammie kuma sai gobe idan ALLAH ya kaimu zasu tafi dan su Shahidah ma suna anan Kadunar da su akayi addu'an uku. Kowa na sashensa sai ihun kuka da kururuwar Hajiya Basariyya suka dinga jiyowa. Babu shiri suka shiga fitowa, mi zasu gani wai ƴan sanda sunzo kama Hajiya Basariyya. A kammi? Idan sunzo office zata ji. Iya ƙoƙari su Ammie sunyi amma basu sauraresu ba. Haka aka wuce da Hajiya Basariyya tana kuka. Hajiya Yaya ta ɗaga waya tai kiran Daddy, amma sai cayay miye nashi shi kuma. Ta daina ma kiransa akan wata Basariyya shi yana cikin mutane. Suma in zasu kwantar da hankalinsu suyi sabgar gabansu su kwantar. Amma har wanda ya sake kiranshi. Daga haka ya yanke wayarsa bai sake neman kowa ba kuma, suma kuma suna tsoron sake kiransa, sai suka zauna jigun-jigun kamar an sake sabuwar mutuwa a gidan.......✍️
Hummm ALLAH yasa muyi ƙyaƙyƙyawan ƙarshe 😭🙏173
.........Da ga gidan Hajiya Turai asibiti su AA suka wuce. Sun sami su Daddy da Yazeed sai Baban Sageer da Baban Hajiya Yaya. Sun gaisa tare da yima juna gaisuwar waɗan da aka rasa. Suka kuma jajanta musu abinda ya faru. Daddy yace, “Ai daga can gidan naku muke ance kunje gaisuwa, shine mukace bari mu duba su Alhaji sai mu koma sannan kun dawo. ALLAH ya kiyaye gaba. Yay mana maganin wannan azzalumin mutumi. Gashi har yanzu jami'an tsaro basu kamashi ba. ” Babban Yaya ya ce, “Basu so kamashin ba dai. Tunda sun tabbatar yana cikin jejin bai fita ba har kamashi zai zama abin wahala. Wannan ƙasar tamu kawai sai Alhamdullah, tsatsa tama mutanenmu yawa a zukata ne, ba nasaman ba, ba naƙasan ba, kowa da tashi illar”. “Wannan haka yake Fadeel, ALLAH dai yay mana maganin waɗan nan abubuwa.” Suna amsawa da Amin dai-dai Doctor na fitowa daga ɗakin da Oum take. Fuskarsa cike da murmushi yana kallon su AA ya ce, “Alhamdullah Hajiya ta farka”. A tare suka kalla ƙofar, sai kuma suka zabura zuwa ɗakin gaba ɗaya. Abbu dake ɗan nesa da su basu ma ganshi ba hawaye suka cika masa idanu. Sosai yake jinjina ƙarfin ikon ALLAH da yardarsa akan wannan soyayya dake tsakanin Fatemansa da yaran nan. Soyayya ce ziryan irin ta uwa da ƴayanta. Itama tana farkawa su ta fara ambata tun ɗazun, sai kuma ta sake komawa barci sai yanzu kuma ta ƙara farkawa...
A cikin ɗaki gaba ɗaya su AA sun zagaye Oum. Har rige-rigen tambayarta suke mike mata ciwo yanzu? Ya take jin jikinta? Su kira mata Doctor?. A hankali Oum ta haɗiye hawayen da suka cika mata idanu, tare da sakin murmushin ƙarfin hali ta kamo hannun Yaya Fawzan dake kusa da ita, ta miƙawa Babban Yaya hannu shima sannan ta riƙo na AA daya zuba mata ido kawai yana kallon ta. Kallonsu take dukkansu fuskarta da murmushin ƙarfin hali, sai kuma ta motsa lips da ƙyar ta furta, “Alhamdullah! Everything is going to be fine, my children” tai maganar tana yunƙurawa zata tashi, kamata sukai a tare suka zaunar da ita, suka daga gadon tare da sanya mata pillow a baya ta jingina. Ƙara binsu tai da kallo sai kuma takai ɗayan hannunta duk ta shafa fuskokinsu, AA ne ƙarshe, ta ƙureshi da ido ganin yanda idanunsa suka canja launi sai taja masa hanci kaɗan tana faɗin, “Waya taɓa min Auta dan anga bana kusa?”. Kauda kai gefe AA yay yana mai ɗauke hawayen da suka taru masa a gefen ido, sai kuma ya zame a hankali yasa kansa a kafaɗar Oum ɗin ya lumshe idanunsa. Harararsa Yaya Fawzan ya ɗanyi da faɗin, “Kaifa ji kake kamar kai ɗaya keda Oum, yaƴanka suyi shagwaɓa kai kayi an girma ba'asan an girma ba naga dai Lilly ce Autar gidan”. Idanu AA ya buɗe shima ya rama hararar da faɗin, “Kai kuma kana kishi dani, to nan gani nan bari ɗumamen mayya kai da Lillyn taka babu yanda kuka iya dani”. “Oh haka kace? Nasan maganinka bari Abah ya tashi shima nasan maganinka, yaji zan saka Lilly tayi sai kazo ka duƙa ka gaisheni kayi biko matsayina na surukinka”. “Oum kin ganshi ko”. AA ya faɗa yana kallon Oum kamar zai yi kuka. Dariya Sosai Babban Yaya ya fashe da ita, itama Oum sai ta shiga taya shi tana riƙo hannun AA. Ta ce, “Auta ƙyaleshi kaji, idan yasa ƙanwarsa tayi yaji kaima basai ka saka taka ƙanwar tayo yaji ba har sai yazo ya maka biyayya sannan ka bashi”. “Yeass! Oum haka ne ma”. AA ya faɗa yana ma Yaya Fawzan gwalo. Rankwashi ya kai masa a kai, Oum ta kare tana faɗin, “Haba Yaya Fawzan ko mutuwa ai tana kunyar idon mahaifi, a gaban uwarsa”. “Oum ki daina tausayin yaron nan, jiya da yake baƙya kusa biyayya ya dinga min, amma yanzu kinga rashin kunya ta gashi.” Kafin Oum ta bama Yaya Fawzan amsa babban Yaya ya zauna yana faɗin, “To ya isa abar min mama ta huta haka, ku ajiye rigimarku idan Abah ya tashi kwa ƙarasa masa. Oum yi brush sai a haɗa tea.” Abin sha'awa da birgewa a tare suka taimaka mata tai brush ɗin, Yaya Fawzan na tausa mata ƙafafunta Babban Yaya na bata Tea ɗin da AA ya haɗo. A haka Nurse da RK suka shigo. Fuskarsa da murmushi yana danne hawayen da suka cika masa ido yace, “A'a kaga ƴar gatan yaranta. Wato kunzo kun zagayeta irin ko ƙuda ɗin nan karya taɓa muku ita ko? To kuzo nan nima ku nema tabarrakina”. A tare suka hararesa yau har babban Yaya, sai abin kuma ya basu dariya suka shigayi a tare. Nurse ɗin kam sai kallonsu take cike da sha'awa da birgewa. A haka RK ya ɗan yiyyima Oum tambayoyi suna wasa da dariya. Bayan Oum taci abinci an bata magani su Daddy dake shirin wucewa suka shigo suka dubata. Tace ma Daddy ina ƙanwarta. Haƙuri Daddy ya bata akan in sha ALLAHU gobe zata ganta itama. Oum tai murmushi tace ba komai. Sun ɗan jima a ɗakin harda Abbu sai kuma gasu Maanal sun iso da abinci ita da Ameerah da Najma. Yaya Fawzan yace ina Nibras, dan su kaɗai akace su zo anjima su Umma sai suzo. Ganin yanda ya tsare Najma da ido alamar ita yake jira ta bashi amsa ta ce, “Zata zo tayi baƙi ne ƙawayenta sunzo gaisuwa?”. “Bakinta sunfi mahaifiyata dake kwance a asibiti kenan?”. Ganin yanda ya fusata Oum tai gyaran murya, sai ta basar da zancen ta hanyar fara tsokanar su Maanal wai wane abin daɗi suka kawo mata. Da wannan suka saki jikinsu suka zagayeta suma. Gaba ɗaya sai farin ciki ya mamaye Oum taji dukkan damuwarta ma babu ita. Da su Daddy zasu wuce Maanal ta fita sukai sallama, har wajen mota ta rakasu tare da su AA bayan sun sake leƙawa sun duba Abah da har yanzu ba'a barin kowa shiga inda yake. Hakama Mamy, sai dai su AA sun doje a ƙofar ɗaki sunƙi shiga inda Mamyn take. Abun sai ya tsayama Maanal a zuciya amma dai batace komai ba suka shiga itama Saheeba suka dubata suka mata gaisuwa. Sai aikin hawaye take kawai ita da Nuratu dake tare da ita......
_________★
Koda su Daddy suka koma gida ƙiri da muzu yaƙi maida hankali akan batun Hajiya Basariyya. Ammie ce da shi yau ɗin, ta tasashi da naci da magiya amma yay mata shiru. Da yaga zata takura masa sai yace taje sashenta bai buƙatar taya kwanan. Ƙin tafiya tai, ta koma gefe ta ɓata fuska, shima yana gama shan tea ɗin daya saka ta kawo masa yaje bayi yayi brush yazo ya haye gado ya kwanta. Haushi ya sake kama Ammie. Cikin rawar murya zatai masa kuka ta ce, “Amma Daddyn Hamee.....” “Asia! ALLAH ranki zai ɓaci. Nace ki ƙyakeni! Ki ƙyaleni mana. Ko dolene sai na shiga abinda bai shafeni ba. Matar nan bata da wani haƙƙi a kaina yanzu ko dole sai kin tilasta min ne”. Sosai gaban Ammie ya faɗi, ta ce, “Wane irin magana ce wannan Daddyn Hameed. Taya zakace matarka bata da hakki a kanka?”. Harara Daddy ya zuba mata, cike da takaici yace, “Tunda so kike kiji bara na gaya miki na saketa, saki uku kuma. Karki sake min maganarta, idan ba haka ba kuma wlhy zaki bar ɗakin nan shirme kawai!”. Ba ƙaramin suman zaune Ammie tayi ba, sai kawai hawaye suka shiga rige-rigen zubo mata. Tabbas mutuwar aure kota maƙiyinka ce bata da daɗi wlhy. Tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta miƙe ta fita tabar masa ɗakin. Karan farko da taji kamar ta kama Daddy da duka. Wane irin yanke ɗanyen hukunci ne haka. Koba komai Basariyya ai uwar ƴayansa ce, ƴaƴan ma mata da suke zaune tare da su babu aure. A tunaninsa hakan masalaha ce ko shuka sabuwar cakwakiya a gidansa. Dan duk yanda yake tunanin zasu iya riƙema Basariyya ƴaƴa wlhy bazai yiyu ba tinda yaran dai rainonta ne, komai mugun halin mahaifiyarsu kuma bazasu so su sama da son da suke mata ba...
Washe gari itama Hajiya Yaya ta sameshi da zancen Hajiya Basariyya saboda ganin yanda damuwa ta fara bayyana a fuskokin ƴaƴanta. Ta saka Yazeed yaje ya bincika station har ya gano inda Hajiya Basariyya take. Koda yay ƙoƙarin yin belin ta sukace bazasu bada ita ba. Dan ana zargin ta ne da yunƙurin kashe rai. Hankalin Yazeed a tashe yazo ya sanar ma Hajiya Yaya, itama ta kira Ammie. Sosai al'amarin ya girgizasu. Yazeed yace shifa yana zargin Sageer ne yasa aka kama Hajiya Basariyya kuma da haɗin kan Daddy. Nan ma zancen sai ya ƙara basu mamaki, Hajiya Yaya tace bara ta samu Daddy ɗin to taji ta bakinsa. Shine tazo itama ta samu kalar tujarar da yayma Ammie a daren jiya. Haka ta fita ta barshi. Jin abinda yace shima Yazeed yace bari to ya sameshi shi. Yana shigowa Daddy ya dakatar da shi. Dan a harzuƙe ya ce masa, “Dakata anan, idan kaima iyayen naka ne suka turoka akan batun Basariyya ALLAH tak kace da ni sai ranka yafi nasu ɓaci. Dan haka ka rufama kanka asiri ka koma inda ka fito tun muna mutunta juna”. Jiki a sanyaye Yazeed ya fita, koda ya koma inda su Hajiya Yaya suke duk abinda ya faru ya sanar musu. Hajiya Yaya ta dafe kai da faɗin, “Matsalata da Alhaji kenan Ammien yara, shi idan yay fushi babu mai iya tankwarashi. Ya kamata ya duba kodan yaran nan ai”. Kafin Ammie tace wani abu Yazeed ya ce,.........✍️174