Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 184

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 184

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 184: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 184. .......A Giro tamkar jira ake su…

3,244 words

.......A Giro tamkar jira ake su Maanal su baro garin wanda suka san matsalar su Gwaggo suka fasa ƙwai. Hadda batun fyaɗe da cutar dake tare da su. Amma sai basu faɗi na Babu ba. Dan haka kawai sukaji bazasu iya tozarta mahaifin waɗanda sukai musu rana ba. Amma Talle dama kowa nada cikinta, hakama Sailuba kodan wahalar da su Sule ke basu bazasu raga mata ba. Abinka da ƙaramin ƙauye cikin abinda bai wuce awa biyar ba labari ya zagaye kowanne gida. Dan danan gutsiri tsoma ta tashi, tun anayin ƙus-ƙus har zance ya fito fili aka tabbatar ma su Gwaggo ansan komai fa daya faru dasu. Ruɗewa kuwa sukayi, zasu fara rantse-rantse mijin Gwaggo ya ce, “Karma ku rantse, dan nima an min bayanin komai akan dolene fa na sakeki idan ba haka ba zaki goga min. Dan haka saki uku”. Sosai Gwaggo ta rushe da kuka, amma ko tausayinta babu wanda yaji. Abinka da ƙauye kowa ya fara gudunsu, dan ance musu ko taɓasu sukayi shike nan sun kamu. Kai ko abu suka taɓa ka taɓa shike nan ka kamu. Harda masu cewa ko magana kayi da su. Kai hatta da Sule gudunsu yake yi, ba ruwanshi da lamarin Gwaggo da Sailu. Babu kawai yake taimakawa shima dan su Maanal su gani su ɗaukeshi su maida gidansu. Dan kullum dukansu sai sun kira video call an haɗasu da Babu. Wani lokacin ma haɗuwa suke a tare kowa ya kira sai suyita hira da shi Sule na nane da shi yana musu soki burutsunsa. Rayuwa tama su Gwaggo zafi matuƙa. Tsangwama da tsana da ƙyama da hantara tasa sai rama suke a tsaye. Kullum cikin kuka suke da dana sani. Dan kuwa kai tsaye kowa ke gaya musu alhakin su Maanal ne. Ashe sune ƴan iska masu karuwanci amma sukace Maanal ce. Gwaggo kuka take tana ƙari da rantsuwar bata taɓa iskanci ba, wanan ma daya faru tsautsayi ne. Amma babu wanda ya kulata. Nan kuma ƴan tsubbun da Sailu ke bi suna iskanci da ita da wasu a mazan gari dama na wasu ƙauyikan ne hankalinsu ya tashi. Kafin kace mi ƙwai ya fara fasuwa. Gaskiya ta fara fitowa. Dan danan kuma sabon zance ya tashi, ana cikin wannan cece kuce sai ga Haƙila ta dawo daga nata yawon tambaɗar da ciki. Ai kaɗan ya rage Sailu bata haukace ba. Abin bai tsaya a kanta ba aka haɗa harda Gwaggo. ALLAH sarki Babu al'amarin ya ɗaga masa hankali sosai. Amma haka su Maanal suka dinga lallashinsa da magana masu daɗi har ya samu nutsuwa. Kai ko kallon Haƙila baya son yi, yarinya ƙarama da cikin shege a gaba. Iyaye sun taru aka tsare Haƙila a gidan maigari, ganin za'a bata kashi ga babu goyon bayan Sule a yanzu, Sailu tayi sanyi bata da tacewa itama Haƙila tayi bayani. Ciki dai na Temo ne mai shago, ashe shine ya ɗauketa ya tafi da ita, dan sanda abin nan ya faru shi da ita suna rufe a shago suna iskancinsu sai da sojoji suka wuce da daddare ya lallaɓa da ita suka gudu. Daga baya akazo aka kwashe masa kayansa da ƴan sanda. Can ya wuce da ita wani ƙauye a garinsu can yankin kudanci. Yace ma ƴan uwansa matarsa ce, haka tana ji tana gani yake ɗaukarta suje coci, ya shiga maida mata ɗabi'u irin nasu. Da farko abin ya fara mata daɗi saboda ƙuruciya, kwatsam ranar ta jiyoma kanta abinda ya tashi hankalinta, dan kuwa Temo da abokinsa taji suna zanta za'a kaita gidan wani boka zai musu tsafi da ita suyi kuɗi, wai dama bokan yafi son mai ciki. Dan haka abokin yace masa ya shirya ya fara kaisa wajen bokan tukunna. Wannan tafiya ta bata damar gudowa, akwai wani bahaushe a garin yana harkokinsa taje ta sanar masa komai da daddare. Hankalinsa ya tashi dan bai taɓa sanin ita ɗin bahaushiya bace musulma ƴar arewa sai ranar. Bawan ALLAH duk da yasan zai iya shiga cikin matsala amma ya taimaketa ya fito da ita daga ƙauyen ya kawota bakin titi inda yasan manyan motocin na wucewa kuma hausawa ne drivers ɗin. Da ƙyar suka samu wani ya tsaya, a gurguje ya sanar masa komai, shima an dace mutumin kirki ne ya ɗakkota shi kuma wancan ya koma. Wannan shine sanadin dawowar ta gida. Dan direban ya kaita kano daga can ya sakata a motar Kebbi.. Wannan labari na Haƙila ya girgiza kowa, Sailu tace zata zubar da ciki maigari yace kull, idan kuma taje ta kashe ta wajen zubar da cikin fa. Ai dole haka zasu amshi ƙaddara ta haihu. Idan kuma wani abu ya samu ciki to sai sun kai ƙararta Suru wajen hakimi, a hakan ma maigari ya tabbatar da sai ya gayawa hakimi komai gudun abinda zai iya zuwa ya dawo koda nan gaba. Wannan fa takunkumi da akaima Sailu ne ya hana a zubar da cikin Haƙilah. Dole ta cigaba da rainon sa zuciyarta babu daɗi ta uwarta babu daɗi. Ga halin da suke ciki akan hiv. Dan itama Haƙilar na jin haka ta janye jikinta daga Gwaggo da Sailu. Tace bazasu goga mata jaraba ba.....

__________★

A yau su Maanal suka wuce ƙasar Saudia. Ita da Ameerah, Najma, babban Yaya, sai Yaya Fawzan da AA. Dan har yanzu Nibras na gidansu suna neman mafita ita da uwarta. Sai zaryar asibiti sukeyi daga ƙarshe suka samu Yaya Fawzan wai zasu kaita Egypt ganin likita kwararre. Bai hanasu ba yace ALLAH ya kiyaye hanya. Shi ko Babban Yaya babu ma wata kwana-kwana ko neman dalili ya gaya ma Saheeba ga inda zasuje, zata ɗaga masa hankali yaja mata gargaɗi da tuna mata halin da take ciki na jiyya da shan magani. Dan har yanzu ko turaka bata koma ba, duk da taso yin hakan likita ne ya kafa mata sharaɗin sai ta kammala shan maganinta. To a yanzu dai tana gab da kammalawar, sai kuma ga batun wannan tafiya da take ganin Babban Yayan ya samu na makalewa. Taso zuwa takai ƙara ma Aunty, Nuratu ta kwaɓeta. Tace ta barsu suje mana kwana nawa sun dawo. Tace ita tana son zuwa taga Naufal ne. Nuratu tace, “Idan suka dawo basai muje ba”. “Da wane kuɗin? Bayan kin san komai bamu da shi yanzu?”. “Shi Yayan zai biya mana ai. Muma sai muce zamuje duba Aban, shi yaƙi ai ɗan zamba ne ko”. Da wannan karatun Nuratu ta kwantar mata da hankali. Sai dai ita Nuratu tana da nata shirin ne shiyyasa bata damu da tafiyar mutanen gidan ba. Hasalima daɗi taji dan hakan zai bata damar yin komai yanda ya kamata. Haka kuwa suka wuce suka barsu gidan shiru. Aunty duk sai taji zaman babu daɗi, gidan ya musu girma. Haka ma su Saheeban. Ashe mutane rahama ne. Aunty na basu shawarar dawowa sashen Mamy caraf Nuratu tace to. Kallonta Saheeba ta tsaya yi, dan ita kam ta kasa fahimta da gane mi Nuratun ke nufi a kwanakin nan take son maida alaƙarsu da sashen Mamy. Koda ta nema ba'asi sai Nuratun tace babu komai. Kawai dai ita tana jin tsoro ne gaskiya. Badan Saheeba ta gamsu ba ta amince. Haka suka tattara suka koma can. Mamy zatai magana Aunty ta hanata. Dole tai shiru amma dawowar su Saheeban sashenta ya sosa mata zuciya. Abinka da mugu shi yasan makwantar mugu sai ta kasa aminta da su. Dan haka ta saka sabuwar mai aikin da su AA ɗin suka kawo tana taimaka musu da abinci da gyare-gyaren sashen saboda kar abubuwan suma Aunty yawa ta saka musu ido. Sai dai kuma an samu matsala, dan kuwa a yanzu Mamy bata da ko sisin bama mai aiki tai mata aikin da take so koda na mugunta ne kamar su Haule, ita wannan ɗauka ma take taimakon su Mamy ɗin akai aka kawosu gidan dan daga ƙauye aka kawota bata san abinda ya faru ba. Sai dai irin ƙwarƙwararrun matan nan ne da komai zasu iya aikatawa akan kuɗi. Tsaff kuma Nuratu ta fahimci hakan dan haka ta fara janta a jiki, sannan ta dinga yima Mamy hidima har Aunty ta ji ta gamsu da Nuratu ta canja ne. Sai kawai tace bara ta ɗan je kano taga yara ta dawo. Dan duk da sun girma suna karatunsu kuma babansu na kula da su da abokiyar zamanta, sun kuma zo har sau uku sunga Mamyn itama ya dace taje ta gansu. Mamy zata nuna mata isa wai bazataje ba Aunty tace “A dalilin mi. Ba gori ba Kamila idan bani ɗin ba wazai zauna dake? Ko kinga a cikin dangin nan namu wani ya kiraki ko a waya ya miki jajen abinda ya faru balle jin yaya kike? Wata kusan huɗu ai kyamin adalci da kanki ma kice naje naga nawa iyalan, ko kin manta miji ne dani nima”. Shiru Mamy tayi dan kalaman sun mata zafi kuma. Itako Aunty ta watsar da ita tai shirinta ta wuce ta barta da su Nuratu......

________★

Oum da Abah da kansu sukaje taro zaratan mazajen ƴaƴansu da matansu har jidda. Cike da farin ciki su AA suka rungume Oum, kafin su koma kan Abah, su Maanal suma suka rungume Oum, sunyi kewarta matuƙa irin yanda baki ma bazai iya muslatawa ba. Haka itama tayi kewarsu, ga farin cikin ƙaruwar da aka samu ƴaƴayen nata duka uku da cikunnansu. Shi kansa Abah wani irin farin ciki yake ji, dan ya tabbatar da zuwa yanzu yaransa sun sami irin farin cikin auren daya jima yana musu addu'a da fatan samu. Sun sami irin matan da yake fatan ganin su a ƙarƙashin ikon su. Fatansa ALLAH ya saukesu lafiya daga alkairin da suka ɗauka. A tare suka duƙa suna gaishesa. Da sauri yace, “Haba yaran albarka ku tashi ku tashi abinku, muje mota kun gaji ayi gaisuwar a gida. Babu musu suka shiga haɗaɗɗiyar motar da akazo ɗaukarsu suka ɗauki hanyar Madina inda su Aban suke..........✍️189

......Sosai gidan da su Oum suke yayi ƙyau, ba wani babba bane ba kuma mai hayaniya ba. Ga abinci kala-kala Oum ta shirya musu. Dama duk yunwar suke ji, dan haka babu ɓata lokaci kowa ya baje sukaci suka ƙoshi musamman Maanal da yanzu sam bata wasa da cikinta. Suko su Najma ma abincin sai da suka zaɓa, musamman Ameerah cikinta nada tsurfa, ba komai take iya ci ba. Su Maanal ne suka tattare komai zuwa kitchen, duk da akwai mai aiki suka taimaka mata aka wanke komai aka maidashi inda yake. Sai lokacin aka gaisa sosai aka ɗaura da hira. Abah babu ruwansa, shi kallon ƴaƴa yake musu ba surukai ba, dan haka jansu yake sosai a jikinsa da labari masu ma'ana. Sanin sun gaji Oum tace suzo suje masauki ayi hirar bayan sun huta. Basu musa ba dan tabbas sun gajin, musamman ma matan da kowa ke fama da kanta...

Masaukin da inda su Oum suke ba wani nisa sosai, dan a ƙafa ma sukai musu rakkiya har Abah. Sun ji daɗin hakan duk da shi Babban Yaya yasan wajen dan shine ma ya kama masauki, hakama gidan da su Oum ɗin ke zaune mallakinsa ne. Daga gate su Abah suka juya, su kuma suka ƙarasa shiga ciki. Ai yanda kowa yay tiɓis suna amsar keys ɗin ɗakunan kowa yaja matarsa suka shige. Basu sake jin juna ba sai washe gari, dama Oum ta riga ta cika musu ciki miya rage kuma. Barci kawai. Aiko barcin suka sha sosai, sai washe gari zasu tafi gidan su Oum yin breakfast suka haɗu da juna. Rayuwar saudia tama su Maanal daɗi, dan wata irin rayuwa ce mai saka farin ciki da shaƙuwar zuminci. Sai suka ji kamar ace inama iya su kaɗai ne kawai. Sun gabatar da umrah, sunyi yawo kuma sosai sunyi farin ciki. Dan ma Maanal bata jin daɗi sosai dauriya ce kawai, har ma su Ameeran kowace laulayi ya sakata a gaba amma suna daurewa dan ji suke kamar kar a koma Nigeria anan kusa, dan tattali da soyayya kawai suke samu daga zaratan Oum. To ashe ma mazan nasu sun shirya musu ma shiri na musamman ne. Dan satinsu uku a Saudia suka ɗauke Aban da Oum suka wuce wata ƙasar. Abah harda musu faɗan ai da sun san yawo suka fito da sun taho da Nibras da Saheeba suma. Su dai suka lallaɓashi kawai aka tafi. Abin kamar wasa sai gashi sun zagaye ƙasashe sosai. Dan kuwa watanninsu biyar ciff Maanal har ta shiga watan haihuwarta. Ameerah da Najma nasu cikin duk sun fito ana gani masha ALLAH. Da yake tuni su Oum sun sake komawa Saudia dan ƙasa uku kawai sukaje sukace sun gaji sukam suka koma saudia suko sukai gaba. Suma saudia ɗin suka sake dawowa. Hankalin Oum ya tashi ganin yanda Maanal tai nauyi sosai. Faɗa ta fara musu akan yanzu haka Maanal ɗin ta koma amma suka zauna. Yanzu ina zasu ɗauketa haka zuwa Nigeria, ai dole su bari ta haihu anan kawai sannan su tafi. Su duka sun gamsu da hakan, sai suka sake miƙe ƙafafun hutawa a Saudia abinsu.....

_________★

A Nigeria kam tunda su Babban Yaya suka wuce Aunty ma ta tafi Kano Mamy da su Saheeba babu zaman lafiya. Basa taimaka mata da komai koda ɗorata a weelchiar ne dan yanzu dole a kanta take saboda ƙafarta data samu matsala bata iya takata sam. Ba kuma harbin ne yaja matsalar ba ainahin karayar data taɓa yi ce lokacin bikin su Maanal take neman zame mata damuwa a yanzu. Babu kunya idan ta zagi su Saheeba suke ramawa. A randa Aunty ke cika kwana uku da tafiya sai Saheeba ta saka mai aiki ta dafa mata nama zata ci, ta fita zuwa sashenta ɗakko abu sai ga Mamy ta fito a ɗaki dan yanzu itama a downstairs take saboda babu ƙafafu. Ta gunguro kekenta ta ƙwalama mai aikin kira. Koda ta fito tana kallonta da idonta ɗaya duk da akwai gilashi dan dole take sakawa saboda rufe munin ido ɗayan da Sille ya fasa mata duk da ya warke sun masa dabara an rufe shi amma babu ƙyawun gani kuma bata gani da shi kwata-kwata sai ake sirrintashi da gilashin. “Mi kikeyi a kitchen tun ɗazun Ina kiranki kizo ki saukeni a gado?”. Mai aiki na ɗan tuttura baki da yamutse fuska dan ko shakkar Mamy bataji, hasalima har rashin kunya take mata, tana zaune ne kawai dan kuɗi gata dama ba yarinya ba ta ce, “Ayya Hajiya Saheeba ce ta sakani dafa mata nama, kema ya kamata kina ɗaga murya, kuma kina ƙoƙarin kanki bawai komai kice sai an miki ba kina zaune turus”. Sagale Mamy tayi tana kallonta, sai kuma cikin ɓacin rai da gadarar data zame mata a jini ta ce, “Iye ni kike gayama haka kina ƙasƙantacciya ƴar aiki na da nake biya. Ko baki san nan gidan mijina da ƴaƴana bane ba...” “Ake dai biya na, kuma kece ƙasƙantacciya wlhy, dan koba komai ni halak ɗina nazo nema ba son kashe miji da kishiyar da tai min hallacin bani mijinta na aura danna handame dukiya ba. Ƴaƴa kuma na mai su dai Hajiya Fateema matar ƙwarai ba naki ba, dan in za'ai yaƙin duniya na uku zamu tsaya mata ƴaƴa nata ne kekam ga naki can barbaɗaɗɗe Sille yake ko mi. Ke bari kiji nifa badan kuɗin da ake biyana ba babu abinda zan zauna yi a nan, ke har kina tunanin kina da wani sauran capacity ne a yanzu, dibeki fa kamar wata almajira, yo banda ma kishiyar taki data matsa ki dawo gidan harta ɗaukeni matsayin mai aiki na miki hidima da yanzu kina bakin gada kina bara wlhy, dan wannan ƴaƴan da kike tunanin kin haifa ko ƙaunar ganinki basa son yi yanzu banzar mata kawai. Ko ca kike ban san komai a kanki bane yanzu, to na sani wawuya”. Ta juya zata koma ciki, sai kawai baƙin ciki da zuciya suka kwashi Mamy ta fisgo matar mutane, keda kike zaune kina fama da ƙafa ɗaya ga babu ido ina ke ina faɗa da mace maiji da ƙarfin jiki gata rainon ƙauye jikinta ya ginu da ingantaccen tuwon dawa dana masara ga aiki. Ai ko tana juyowa ta falle fuskar Mamy da lafiyayyen mari, ta kuma shiga jibgarta. Ihun Mamy ya fargar da su Saheeba, suka shigo da gudu, tsabar mugunta Saheeba ta kulle ƙofa da windows tana faɗin, “Wlhy ci ubanta uwangale karki raga mata. Ki mata lilis, kiyi komai ba komai abinki muna bayanki.” Wannan zuga ta Saheeba ta sake tunzura Uwangale, ta cigaba da jibgar Mamy da ƙyau, Nuratu kam wata dama hakan ya bata, da sauri ta nufi ɗakin da suke ta ɗakko syringe, haka ta ɗiba jinin jikinta tana matse baki ta fito da shi a ɓoye. Har lokacin Uwangale nakan Mamy tana suburbuɗa, sai kawai tai kamar zata taimaki Mamy a hannun Uwangale ta samu ta danna mata allurar wannan jini a jiki. Ta ɓoye syringe a jikinta sannan ta kwaci Mamyn data gama yin lilis sai kuka take yi. Nunata Uwangale dake hakki tayi, ta ce, “Shegiya munafuka karuwa maima maza fyaɗe. Gobe dan ALLAH ki sake kawo min wargi ki gani. Ke bama ni ba ko wani a ma'aikatan gidan nan kika sake ma koda kallon banza sai na miki abinda yafi haka. Bakince ke muguwa bace mai baƙin hali, to kin sami mai horaki kuwa a gidan nan dan nice zan koya miki tarbiyyar da kika gagara samu tun daga ƙuruciya. Kuma idan ƙaiƙayin bakinki ya jaki kika gayama wani ko Hajiya Shuwa da Maimoon idan sun shigo ko Hajiya Asiya idan tazo zaki sha mamaki wlhy suna fita zan sake zaneki”. Sosai ALLAH ya tasirantar da tsoron Uwangale a zuciyar Mamy, su Saheeba kam suka dinga kwasar dariya. Sai gashi koda Hajiya Shuwa ta shigo Mamyn kasa gaya mata tayi, sai tace wai faɗuwa tayi lokacin su Saheeba basa kusa Uwangale kuma na kitchen haɗa mata abinci. Hajiya Shuwa harda yima su Saheeba faɗa akan su daina nesa da Mamyn, su kuma kamar na ALLAH sukace in sha ALLAHU zasu kiyaye. Hakama da Ammie tazo suka tsarata. Dan Hajiya Shuwa da Ammie suna iya ƙoƙarin su na zuwa duba Mamy, Ammie idan tazo yau sai gobe ta huta jibi tazo, wani lokacin harda Hajiya Yaya da yara suke zuwa. Hajiya Shuwa kuwa safe da yamma ita da Maimoon suke shigowa. Damma ita Maimoon ɗin na fama da kanta ne dan laulayin ta mai wahala ne sosai. Shi kansa Ameer duk bayan kwana biyu yana zuwa yaji mi suke buƙata duk da kuwa komai sai da su AA suka ajiye, ga RK kullum yana cikin musu hidima dan gidan yake kwana ma saboda Nuwaira na Kano. Oum tace kuma bai kamata abar su Mamyn su kaɗai ba duk da akwai masu aiki da securitys da aka ƙara a anguwar dama ƙofar gidan nasu saboda guduwar Sille daga gidan mahaukata, ba'a san ko abin shiri bane watarana yace zai dawo ya cutar da su. Sai dai duk wannan hidimar da su Ammie, Hajiya Shuwa, RK keyi akan Mamy ba birgeta suke ba, kullum cikin zaginsu take a zuciya da tsine musu, kawai dai ALLAH ya ragema aya zaƙinta ne bata da damar yin wata muguntar gata a tauye babu ƙafa babu idanu bata kuma samu haɗin kan mai aiki da zatai mata abinda take so ba sai ta haƙura. To yanzu ma sai ga Uwangale tazo da sabon salon daya karantar da Mamyn cikin sauƙi..........✍️

🤣🤣Yanzu ne fa Mamy ta shiga ainahin hannun ƴan tuwo-tuwo. Uwangale maganin kukanmu😆😆😆😆🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️🏃🏼‍♀️ 190

Readers Also Read