Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 185
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 185: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 185. .......A ɗan tsakani nan wani irin…
2,701 words
.......A ɗan tsakani nan wani irin tsoron Uwangale ALLAH ya dasama Mamy mai girma a zuciya, magana kaɗan Mamy zatayi koda bamai zafi ba Uwangale ta mareta, bata isa sakata komai ba a gidan, sai yazam Mamyn ce ta koma yima kanta komai da kanta. Dan su Saheeba babu abinda ya shallesu sai dai su zauna ma suna dariya da kallon drama ɗin. Karo na farko da Mamy ke addu'ar Aunty ta dawo a gidan kosu AA. Amma shiru kake ji, ko kiran waya Aunty tayi sune suke ɗauka su kanainaye su hanata magana, idan kuma sun bata Uwangale na tsaye a kanta da bulala idan ta faɗi abinda bai musu ba tana ajiye wayar ta zaneta. Haka ma idan Oum ta kira suke mata.. Kai da abu yakai kukan kure tsakanin Mamy da su Uwangale sune suka koma sakata aiki a gidan. Haka zata dinga gungura kekenta tana musu hatta girki. Mopping da shara ana idar da sallar asuba suke tasota, haka takeyi tana kukan zuci dan babu damar yin na fili Uwangale da bulala. Sam RK bai san wainar da ake toyawa ba. Dan barci kawai ke kawoshi gidan. Gari na wayewa yake shiri ya wuce asibiti sai kuma wani daren. Idan ya shiga duba Mamy kuma da safe tsaff yake samunta dan suna dai-daita lokacin shigowarsa ne su killafata waje guda, wani lokacin ma su haɗa kayan daɗi a gabanta Nuratu na mata tausa Uwangale na kai-kawo, Saheeba na bata abinci a baki. Yana fita Saheeba da Nuratu sai sun bata maruka suce ta sauka tai musu abinda sukai mata. Haka zata sakko jiki na rawa tayi dan in ba haka ba taci duka a hannun Uwangale. Tashin hankali yasa jininta kullum a sama yake, ga zuciya ta kumbura sosai har sai da dole RK yasa aka maidata asibiti. Ya zauna yay mata nasiha dan shi a tunaninsa har yanzu tana nan da mugun ƙudirinta ne a rai bai san ƙaniyarta take ci wajen su Saheeba yan boko haram ba🤣😆. Satinta uku a asibitin dan dole Aunty ta dawo ta zauna da ita. Ji Mamy ta dinga yi kamar kar a sallameta, gashi ta kasa gayama Aunty abinda ke faruwa saboda tsoron Uwangale da su Saheeba. Suna komawa gida kuma kwannan Aunty biyar kawai su Saheeba suka zugeta akan taje abinta zasu cigaba da kula da Mamyn, kuka Mamy ta sanya bata son Aunty ta tafi, sai abin ma ya bama Aunty mamaki sosai. Wai yau Kamila ce da kuka bata son ta tafi, lallai mata sun fara laushi ashe. To ita dai Aunty lallashinta tayi akan tayi haƙuri zatai ƙoƙarin dinga zuwa akai-akai, haka ta tafi tabar Mamy na kuka. Kamar jira su Nuratu suke Aunty na wucewa suka kama Mamy suka lakaɗa mata duka wai tana son tona musu asiri wajen Aunty. Haka taita rantsuwa da basu haƙuri. Bayan sun ja mata dogon gargaɗi suka barta da jiyyar ciwon jiki. To wannan irin azabobi fa Mamy ke fuskanta tunda su AA suka tafi, idan kaga ta samu sassauci sai Aunty tazo kwana biyu. Tana tafiya ake ɗorawa daga inda aka tsaya. Da ace wani zai duba jikinta sawun bulalaine kaca-kaca dan sun zame mata tabo. Yau tunda sukai waya da Oum tace mata sun kusa dawowa ji Mamy tayi kamar tai ihu dan murna. Har yanzu zuciyarta bata ƙaunar Oum, amma tasan dawowarsu gidan zai zame mata rahama ta wani fannin, dan zata samu sauƙi daga cin ubanta da take a hannun su Uwangale da Saheeba da Nuratu.....
😂😂😂🤣🤣🤣😆😆😆Hajiya Kamila tamu, waya gaya miki barno gabas take🥱😜🤏
__________★
Ba Mamy bace kawai ke amsar sakamakon abinda ta shuka, anan ƙauyen su Kawu Manu ma Hajiya Basariyya na amsar nata sakamakon ne. Bana duka ko zagi ko hantara ba, wannan karon ko aiki ma babu mai sakata a gidan su Kawu Manu sun kawo ido sun zuba mata. Azabar canjin abinci dana canjin waje kawai ke ƙona zuciyarta da rayuwarta. Tana gama iddarta kuma kawai wani mutumi dake mutunci da Kawu Manu a can ƙauyen gaba da su yazo wai yana son aurenta. Mutumin shine mai anguwar ƙauyensu, yana da shanaye da gonakin noma. Dan haka a yankin ƙauyukan yana cikin masu kuɗin da ake lissafi da shi. Suna huɗɗa sosai da Kawu Manu dan abokinsa ne na amana sosai. Matansa uku da yara kusan ashirin da takwas. Yaje makka dan Alhaji Balala ake kiransa ma. Karku ɗauka dukiyar tasa yana da wani haɗaɗɗen gida ne. A'a sam ba haka bane, gida ne dai irin na ƙauye jar laka. Sai dai ƙaton gaske ne dan duk yaransa maza idan sunyi aure anan suke yankar waje suyi ɗaki su kewaye. Hakan yasa ma gidan albarka sosai ya zama family house, dan aƙalla yaransa maza bakwai nada iyalai. Ɗakunan matansa a jere suke reras guda uku falle ɗai-ɗai sai doguwar baranda. Abinda ya ɗan ɗara gidan Alhaji Balala dana sauran ƙauyen filastar da yay ma ɗakunan matansa da wannan doguwar baranda aka kuma shefe gaban ɗakunan nasu suma da simintin. Sai kuma na tsakar gida dake iyakar tsahon barandar da faɗinta. Ba'a abincin safe a gidan Alhaji Balala balle na rana. Tuwo ne ake yi ƙatuwar tukunya duk bayan kwana biyu a raba kowacce ta ɗauki nata dana ƴaƴanta ta adana taita ɗumamensa. Da yake tuwon anayin wadatacce kam sai kwana biyun ma ya cika wata bata gama cinyewa ba, abinda ya rage ɗin saita shanya ya bushe ta adana kayanta, randa suke jin kwaɗari ta dafa da barkono da manja da ɗan magi kamar shinkafa dan sai an dakashi sannan. Shine mutanen ƙauye muke kira da (Dabuwa. Ku wlhy akwai daɗi😂). To wai a hakan mutane ke ganin gidan Alhaji Balala wadace yake da abinci, dan sauran gidaje wasu ma sai suyi sati basu ɗaura tukunyar ba musamman idan damina ta gabato an cinye amfanin gona. Lokacin da Iya ke sanarma Hajiya Basariyya batun Alhaji Balala hankalinta tashi yayi, ta shiga wassafo Alhaji Balala data san yana zuwa wajen Kawu Manu duk bayan kwana biyu a cikin idanunta. Kawu Manu ya fishi shekaru, amma shi ƙato ne da ƙibarsa ga tsayi masha ALLAH. Kullum zaka ganshi cikin manyan kaya na yadi mara fasali shi adole ga Alhaji. Amma wuyan rigar kawai ka kalla da hularsa dauɗar dake jikinsu sai ta sakaka amai. Bakinnan ba'a magana dan yana cin goro. Ga uban gashi ya tara a fuska babu gyara duk ya ƙududune yay ƙuda-ƙuda sai kace dole sai ya ajiye sajen a fuska. Ƙafarsa ko faso ba'a magana sai kai ajiyar ƙwandala a wani ramin ta zauna abinta tana hutawa. Yana da arziƙin kudin ƙauye sai dai fa ba'a ci sai iya cikinsa, dan kuwa kullum yana ƙauyen su Kawu Manu wajen mai shayi da tsire dan su babu a nasu ƙauyen. Shiyyasa ƙaton cikinsa ba'a magana, idan yana tafiya har nishi yake kamar mai shirin haihuwa. Ji Hajiya Basariyya tai amai na shirin taho mata, ta fashe da kuka tana faɗin, “Haba Iya, nice wannan kucakin mutumin zai ce yana so har azo ana gaya min, wlhy ALLAH ya kiyaye, ai ko a ɗan aikin gidana ba zan iya ɗaukarsa ba”. Dariya ma abin yaba iya, ta ce, “Lallai samun wuri, ina ma laifi da kika samu Alhaji Balala ɗin? Mutumin kirki abinci baya yankewa a gidansa. Ke har mafarkin samun wata daular rayuwa da tafi wannan kike yi? To ai saiki matsa kiyita jira”. Da harara Hajiya Basariyya ta raka bayan iya tana ƙunƙuni. Kamar magana ta wuce kawai bayan kwana biyu Kawu Manu yace mara taje soro su gaisa da baƙo. A tunaninta Daddy ne ko wani dai daga birni, kawai taci karo da Alhaji Balala shirim a zaune cikin wata daddauɗar shaddarsa datai uban squeezing, ga wata shegiyar hularsa a karkace shi a dole yazo zawarci. Jitai amai na neman taso mata, ta kauda kai tana zubar da yawu. Shi ko sai faman washe mata baki yake haƙora jazur da goro. Ganin taƙi yin magana ya ce, “Hajiyata an fito? Ina fatan kina cikin ƙoshin lafiya?”. Maimakon amsa masa gaisuwar sai cewa tai “Miya kawoka wajena?”. “Haba Hajiya Basari, (Basari🤣 Alhaji Balala ya iya saka suna fa) duk namijin da kika gani yazo gun mace kamarki ai alkairi ne ya kawoshi, alkairin ma na aure. Mu ba yara bane dan haka babu wani batun kwana-kwana aure ya kawoni, kawunki ya sanni, ya kuma san wanene ni. Kai duk kewayen ƙauyukan nan kikace Alhaji Balala ko yaron goye in dai yana magana zai ce miki ya sanni. Dan haka babu wasa a lamarina, zan riƙeki amana kuma zan hidimta miki gwargwadon iko......” “Mtsowww!! Kai nifa ka isheni da magana. Karma ka wahalar da kanka ni bana sonka, jibeka, kai banda ƙaddara ko a hanya ka ganni ka isa min magana ma. Dan maigadin gidana ma ya fika komai wallahi wawa baƙauyen banz......” Bata ƙarasa ba taji saukar lafiyayyen mari a kumatunta. Juyowar da zatayi taci karo da Kawu Manu. Fuskarsa na nuna matsanancin ɓacin rai da fushi ya ce, “Yanzu Alhaji Balala ɗin kike zagi Basariyya? Saboda ki nunama duniya ke mara tarbiyya ce. Da shekarunki da komai amma sam baki da isashen hankali. To bara kiji auren Alhaji Balala babu fashi, dan nima na gaji da zama min da kike a gida wawuya kawai. Alhaji kaje ka shirya nan da kwana uku kacal ka turo magabatanka”.. Kuka sosai Hajiya Basariyya ta fasa da faɗin, “Wlhy dana auresa na gwammaci na gudu kuwa”. Tai cikin gida fuuu. Ƙwafa Kawu Manu yayi da faɗin, “Shike nan Alhaji in dai da sadaki a tare da kai muje masallaci yanzun nan, dole ne na nunama yarinyar nan bata isa ba kuwa. Duk da itace da damar zaɓar mijin aure bata da cikakken hankali ni zan zaɓa mata dan bazan sake bari ta koma birni ta sake fanɗarewa ba.” Bakin Alhaji Balala a washe ya miƙe yana faɗin, “Ai ko babu yanzu zan aika gida a ɗakko Malam, ALLAH ya saka da alkairi ya bada kadan zuminci”...........✍️
Kambu Hajiya Basariyya an shiga gidan ɗan kande, wayaga ɗaurin goro 🤣😆.
191
.......Aure dai kam ya ɗauru tsakanin Hajiya Basariyya da Alhaji Balala. Dan ana idar da sallar la'asar ya biya sadaki aka ɗaura. Sai ga Kawu Manu ya shigo da goro da sweet, sai kuɗi dubu hamsin ƴan ɗari biyar-biyar. Wani irin kukan tashin hankali Hajiya Basariyya ta saki lokacin da Kawu ke musu bayani ita da iya. Ko kallo bata ishesa ba, sai ma miƙewa yay yana faɗa mata ta shirya gobe zuwa jibi zata tare ta bar masa gida, dan bazai iya zama da mai taurin kai da bijirarriyar zuciya irin tata ba. A gobe ma Alhaji Balala zai turo a fara kwashe kayanta zuwa can, dan haka iya ta nema wanda ta yarda dasu suje yin jere. Suma ne kawai Hajiya Basariyya batayi ba a ranar tsabar yanda ta dinga zuba musu bori. Da daddare ta gama shirya kayanta tsaff da shirin guduwa sai dai ta makaro, dan kar Kawu Manu ke kallonta. Tana fitowa ma taci karo da shi zaune a ƙofar gida. Turus ta tsaya tana kallon sa kamar yanda yake kallonta. Sai kuma yay murmushi mai ciwo da faɗin, “Oh guduwa kike shirin yi da aure wani a kanki? To kada ki fasa dan ALLAH ga hanya nan”. Yay maganar yana tashi ya shige gida abinsa. Ga dai ƙofa a buɗe ga kuma dama an bata amma ta kasa yin komai, sai ma rushewa da kuka tayi a wajen tare da zamewa ta zauna dirshan. Haka ta ƙara cin kukanta babu mai lallashi ta taso ta dawo cikin gidan....
__________★
KANO
Zaune take tana shayar da bebinta, yaro ƙyaƙyƙyawa yay ɓul-ɓul gwanin sha'awa. Sosai yake kama da babansa, haske kuwa nata ne. A zahiri yaron take kallo, amma tunaninta baya tare da shi. Sageer daya shigo kusan mintuna goma ya fahimci hakan, dan ko shigowarsa da alama bata sani ba. Numfashi ya ɗan furzar ya wuce kitchen ya ajiye kayan hannunsa ya fito. Sai da ga kai zaune har ya taɓa sannan firgigit ta dawo tunaninta. Kallonsa tayi, shima ita yake kallon, sai ta sauke kanta ƙasa kawai. “Har yanzu jikin ne?”. Kanta ta girgiza alamar a'a. “To mike damunki?”. Cike da son danne abinda ke ranta tace, “Babu komai fa, kawai dai na tafi tunani ne. Sannu da dawowa”. Amsa mata kawai yayi badan ya gamsu da abinda ta faɗa ba. Itama sai ta miƙe tana miƙa masa fodio ta nufi kitchen. Babu jimawa ta dawo da ruwa ta ajiye masa. Ta ɗan kallesa yanda yakema fodio wasa kamar yana yi da babba mai wayo. “Kawoshi kasha ruwan”. “No barci, ɗan samin dai ruwan wanka na watsa ruwan nan yasa garin yin sanyi”. Kitchen ɗin ta wuce, ta ɗauka kettle ta fita zubo ruwa a rigiya, koda tazo ta jona a wuta sai tai tsaye, sai kuma ta ɗauki wayarta, tana dannawa screen ɗin ya kawo haske hoton AA ya bayyana. Yayi matuƙar ƙyau cikin ƙananun kaya sai coat data kai masa har gwiwa fara sol mai gashi. Ya saki ƙatuwar hular rigar bayansa ta kwanta. Akwai alamun kyakkyawan hannun mace dake a kafaɗarsa alamar tana a bayansa ne, kodai zooming hoton akayi, ko kuma yanke macen akayi. Yanda AA ɗin yay wani shegen murmushi idanunsa a lumshe gashinsu sun kwanta gazar-gazar ga murmushi akan ƙyaƙyawar fuskar tashi kaɗan yaɗan turo lips gaba yay masifar yin ƙyau. Gashi ya fito tar-tar kamar kai magana ya amsa. Ajiyar zuciya Huznah ta sauke mai ƙarfi, sai kuma hawayen da suka taru mata a cikin ido suka zubo sharr. Hannu tasa ta sharesu... Sageer da yaji shiru ya biyo bayanta kasancewar ta juya masa baya tsaff yaga abinda take kallon. Da farko sai da zuciyarsa ta buga, wani irin kishi mai zafin gaske ya turniƙesa. Har ya buɗe baki zai yi magana sai kuma yay shiru ya koma da baya-baya. Kasancewar hankalinta ba'a wajen yake ba ko motsinsa bata ji ba. Koda ya koma falon ma da ƙyar ya iya nutsuwa yay controlling fushinsa. Bayan ruwan yayi ta ɗakko ta fito, da kallo ya bita har ta shiga ɗakin barcinsu. Bata wani jima ba ta fito tace masa ga ruwan can. Shima komai baice da ita ba ya miƙa mata Fodio ya wuce. Duk yanda yaso shiga wankan kasawa yayi, ya zauna bakin gado ya ciro wayarsa ya buɗe data. Karo na farko ya shiga google ya fara searching sunan AA Darma da accounts nashi na media. A X kawai ya samu, sai facebook. Na facebook ɗin ya fara shiga, sai dai babu wani abun kirki a ciki ma, dan posting ɗin abubuwan da akai basufi goma ba, duk ma agogo ne. Amma kuma yana da followers sosai. Daya shiga ainahin profile ɗin account ɗin ma sai ya fahimci kamar ba ainahin AA ɗin bane. Fitowa yay ya shiga X, anan ne yafi gaskata AA ɗin ne da kansa, sai dai nan ɗin ma babu wani posting ɗin hotonsa ko guda ɗaya balle matarsa ko wani family member na Darma kaf. Hotunan agoguna ne manyan kai na manyan masu hannu da shuni kawai. Koda ya shiga comments na posting ɗin farko yaga kusan duk manyan mutane ne ke masa comments ɗin ma. Fitowa yay zuciyarsa na tunanin a ina to ta samu wancan hoton? Sai zuciyarsa ta ayyana masa brothers ɗinsa mana. Nan take ya koma neman account ɗin su Babban Yaya. Sai dai babban Yaya irin AA ne, shima twitter ɗin ce kawai yake da account kuma babu komai akai sai harkar business. Yaya Fawzan ne keda a Instagram da X ɗin, anan ne ya samu hotunan Babban Yaya, da AA ɗin har ma dana Abah. Mafi yawanci kuma hotunan salla ne, dana juma'a sai na ɗaurin aurarraki. Akwai wasu hotunan da dama na zuri'ar Darma, sai dai shima babu hoton mace ko ɗaya, kuma babu irin wancan hoton da yaga Huznah na kallo. Ajiye wayar kawai yayi ya shiga wankan, abubuwa da yawa zuciyarsa ke ayyana masa, ciki harda Huznah na charting da AA Darma ne ya tura mata hotunan da kansa. Sai dai zuciyarsa na ƙaryatawa ta wani gefen, dan yasan labarin wanene AA Darma da halinsa akan mata. Kai har yanda Huznah ta dinga bibiyarsa da ƙin kulata duk sai da ya binciko...