Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 186
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 186: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 186. Har washe gari yana son ture abin a…
3,085 words
😂😂Manyan Mata an shiga halin ni ƴasu🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🏃🏼♀️🤭193
........Tsaf AA ya haɗama Maanal dafaffen ƙwan daya cire bayan da miyan attaruhun yasa mata albasa sosai suka haɗe jikinsu sannan ya juye plate. Daga shi har su Yaya Fawzan sun iya girki, yanzu ne dai kawai basu damu dayi ba sai sun so. Coffee ya ɗan haɗama kansa shima sannan yasa a tray yay sama. Dai-dai lokacin da ciwon ke ɗan lafa mata, sai dai kallo ɗaya yay mata ya fahimci bata cikin ƙoshin lafiya. Tray ɗin ya ajiye idanunsa a kanta ya ce, “Babie what happened?”. Maanal ta sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya tana danne ɗan sauran abinda take ji idanunta da suka kaɗe akan tray ɗin daya ajiye ta ce, “Ba komai. Ka bani naci”. Zama yay kusa da ita, dan gaba ɗaya bai yarda da abinda ta gaya masa ba, sai kallonta yake yi da lallaleƙa jikinta. Ta tura baki gaba da katseshi ta hanyar faɗin, “Besty yunwa fa nake ji”. Ajiyar zuciya yayi kaɗan, “Okay tashi muje kiyi brush”. Batai musu ba ya taimaka mata suka muƙe tare, haka ya rakata tai brush ɗin sai kuma tace kawai ya mata wanka da ruwa masu ɗumi. A tunaninta in akai wankan zataji sauƙin abinda take ji a jikinta. Haka yay mata wankan suka fito, ya duba mata simple doguwar riga irin na Egypt ɗin nan masu babban mayafi dan su take sakawa yanzun. A maimakon mayafin ya saka mata hula sannan ta zauna cin kwan. Shi kuma yana shan coffee ɗinsa amma idanunsa ƙyam a kanta. Ko yaya ta yamutsa fuska sai yace minene?. Sai ta girgiza masa kai ta cigaba da cin kwan cikin dauriya. Taci ya kai shida tafa kasa daurewa saboda exactly irin ciwon ɗazu dake taso mata. Plate ɗin ta miƙa masa jikinta na rawa, zata kai kwance sai kuma ta kasa dan bayan ta ya riƙe. Ai baima san ya wancakalar da plate ɗin ƙwan da kofin coffee ɗin hannunsa yayo kanta ba da kiran sunanta. Dai-dai nan Oum data iso ƙofar har ta kai hannu zatai knocking taji yanda AA ɗin ke kiran sunan Maanal ita kuma ta saka masa kuka tana kiran “Besty bayana, ƙafata, marana ya riƙe”. Ai kawai shigowa Oum tayi, cikin tashin hankali ta iso inda suke, kallo ɗaya ta fahimci haihuwa ce. “Auta ɗagata muje maza-maza haihuwa ce wannan”. Ko musu baiyi ba ya ɗaga Maanal gaba ɗaya suka fito, Abah na falo ya miƙe da sauri yana tambayar lafiya? AA bai iya ya amsa masa ba sai Oum dake biye da su da kayan haihuwa tace, “Gadanga haihuwa ce”. “Suhanallahi”. Abah ya faɗa yana binsu a baya shima. Sai waya a hannunsa yana ƙoƙarin kiran asibiti. Dole a falon ƙasa AA ya ajiye Maanal, sai dai tana jikinsa tana kuka. 20min kawai sai ga Ambulance tazo ɗaukarsu.......
________★
Kamar yanda Kawu Manu ya faɗa hakan ce ta faru, washe gari maƙota da abokan arziƙin iya suka nufi ƙauyen su Alhaji Balala yin jere. Dan tunda sassafe ya aiko akori kurarsa ta ɗiba kayan. Sun wuce babu jimawa Yayan Hajiya Basariyya ya iso garin, tare yake da wani kawunsu shima ta ɓangaren mahaifiyarsu. Shima dai ba mutum bane mai wasa, amma a zuciyarsa yaji tausayin Basariyya. Dan rayuwa a ƙauye bayan ba'anan aka haifeta ba, sannan ta auri mai kuɗi irin Chalawa har ta haifi yara duk sun zama manya zuwa yanzu da shekarunta ace tazo wannan ƙauyen tai aure da gidaje basufi goma sha ba abune bamai sauƙi ba gaskiya. To amma hakan shine kawai punishment ɗin da zasuma Basariyya ta dawo cikin hankalinta ta kuma fahimci micece ainahin rayuwar kanta. Tunda da yarinyarta datai yunƙurin zubarma ciki ta rasa ranta ai daba wannan maganar akeyi ba kuma yanzu ko. Gwara ta ɗanɗana idan da rabo gaba sai ta koma gidan ƴaƴanta tunda saki uku ne dama. Bayan sun gaisa dasu iya ansha hirar bayan rabuwa tsakanin Kawu Manu da Uncle Faruk akai kiran Hajiya Basariyya. Kallo ɗaya yayanta yaji zuciyarsa tayi rauni, sai dai dole ya dake abinsa dan Basariyya bata buƙatar a nuna mata tausayawa. Tana da busashiyar zuciya kamar ba mace ba. A yanzun ma da tazo da farko ƙin gaishesu tayi, sai da Uncle Faruk yay mata tsawa sannan. Yayanta kuma ya shiga zaginta, dan yanda take musu raini sosai a ciki. Tuni suka ajiye batun tausayinta a gefe suka mata tatas, tare da sharruɗa masu ƙaifi akan wannan auren. Ta inda suke shiga bata nan suke fita ba. Sai da suka tabbatar sun razanata sannan suka sallameta, sun kuma sanar mata anan zasu kwana su da kansu zasu kaita ɗakin mijin ma kawai, dan sun fahimci bazata taɓa tanƙwaruwa ba..
Chapter notes and social links
Har washe gari yana son ture abin a ransa amma zuciyarsa taƙi nutsuwa. Ƙarshe dai ya ɗauki wayar tata ya fita da ita bata sani ba. Da yake tsakanin jiya zuwa yau ya saka mata ido sosai ya fahimci password ɗin data canja yana gwada sakawa wayar ta buɗe. Haka ya shiga ya fara mata bincike daki-daki. Tun daga kan massages, bai samu komai ba ya koma WhatsApp, nan ma normal sai sisters ɗinta kawai take charting da su dan canja mata layi da yayi dama duk babu ƙawaye yanzu. Ya koma facebook, bata buɗe account tabi dokar daya kafa mata kenan, sai ya shiga Instagram. Sai ko kai tsaye ga hoton jiya tana akan shafin da hoton yake ma bata fito ba. Koda ya duba mai account ɗin sai yaga sunan Saleem Mahmud Darma. Ya shiga profile ya duba yaron tabbas da ganinsa kaga jinin Darma ɗin, koda ya shiga account ɗin sosai hotuna ne kala-kala na zuri'ar Darma. Akwai kuma na AA ɗin sosai a wajen, dan wanda ma Huznah ɗin ke kallo kwana biyu da ɗorashi, yanzu kam sosai hoton ya buɗe alamar zooming ɗinsa ita tayi, bayansa black beauty mace ce, kai tsaye ya gane Maanal ce tunda ya santa a gidan su Huznah ɗin, tana sanye da doguwar riga ta ɗora ƙatuwar jacket a kai alamar ba'a Nigeria suke ba. Kwance take a bayansa hannayenta duk biyu a kafaɗarsa ta kamo kunnensa ɗaya da baki like tana cizonsa ne. Hannunsa ɗaya ya tallafo kan nata shi kuma. Fitowa kawai Sageer yayi daga account ɗin, ya blocking ya fito gaba ɗaya yay deleting account ɗin nata na Instagram ɗin ma gaba ɗaya. Koda ya dawo gidan bai ce mata komai ba, amma kai tsaye ya bata wayarta. Sai da ta nuna mamaki, dan bata san ya ɗauki wayar ba sam. A ɗan daburce tace, “Dama wayata na hannunka?”. “Uhhhm”. Kawai yace mata ya wuce ciki. Sai tasha jinin jikinta. Zaune ta kai jagwab fodio na bayanta, zuciyarta sai bugawa take da sauri-sauri. App na Instagram ta fara nema dan ta goge, saboda bai san ta buɗe sabon account ba kasancewar ya hanata. Sai me babu app ɗin ma babu dalilinsa. Hakan na nufin ya gani shi kuma ya goge. Gaba ɗaya sai taji ta sake ruɗewa, ALLAH tsoron Sageer take har ranta, duk da kuwa yana iyakar ƙoƙarin sa wajen janta a jiki ta yanda zata sake da shi. Amma ta kasa ƙarfafa kanta sam al'amarin kamar wani asiri. Ko kuwa hakkin wulƙantashi data dingayi ne lokacin yana gidansu oho. Dan babu irin zagi da cin kashin da batai masa ba ita da ƴan uwanta. Musamman ma ita ɗin daya nuna yana so. A yanzu kuma sai ALLAH ya saka mata ganin girmansa da kwarjini ƙwarai da gaske. Balle ma a tsakanin nan da wannan al'amarin ya faru tsakaninta da mahaifiyarta. Dan koda suka dawo Kano bai taɓa tayar mata da maganar ba ko tambayarta yanda akayi, ya dai sake ninka kulawar da yake bata fiye da da. Tana jin farin cikin yanda yake mata, duk da tana jin tsoronsa, gefe soyayyar AA na nan daram a zuciyarta, babu abinda ya canja.. (In son mai karatu ya fahimci kuskuren Huznah anan. Eh zuciyarta na son AA mun yarda da haka, amma ƙyautatawar mijinta da ƙoƙarinsa na taka rawar gani shima a zuciyar tata. Sai dai bata taɓa nutsuwa miƙama UBANGIJI kukanta akan ya cire mata zuciyar wanin mijinta ba ya bata nutsuwar zama da shi ya saka mata soyayyarsa tunda ta fahimci anzo gaɓar da tafa rasa AA ɗin dole kuma ta zauna da shi Sageer. Yan uwa duk yanda muke tunanin al'amari mai ƙyau ko mara ƙyau ya tsananta a tunaninmu da zuciyar mu mu nutsu wajen maida al'amuranmu ga UBANGIJI da kai kukanmu, in sha ALLAHU zamu samu sauƙi da sassauci dan wani lokacin shaiɗan da son zukatanmu na jan zaren matsalolinmu ne kai tsaye. Idan bamu haɗa da roƙon ALLAH ba sai komai ya rikice mana mu rasa wanda muka samu, wanda yay mana nisan ya sake mana nisa. Kamar dai nan wane tunani kuke yi akan matakin da Sageer zai ɗauka a kanta yanzu?).........✍️192
.......A nan Saudia AA ne a kitchen a gidan da su Oum suke yana dafama Maanal ƙwai da tace tana so. Yanzu kullum anan gidan suke yini sai dare su wuce masauki, jiya da Oum ta fahimci yanayin Maanal ɗin na canjawa sai tace AA ɗin ya barta anan ta kwana. Ba ƙaramin tashi hankalinsa yayi ba, ya marairaice ma Oum ya shagwaɓe murya wai ai Maanal ɗin na tayashi aikin office miye-miye. Sai da ta gama jinshi Abah dai da Babban Yaya na murmushi, Yaya Fawzan kam ya saki baki da hanci yana kallonsa kamar wani robbot. Sai da ya gama tsara Oum tsaff sannan tace, “Koma dai miye bazata bika ba Auta, shi aikin office ɗin ba'a bama masu tsohon ciki hutu. Kai baka ganin yanda gaba ɗaya yanayinta ya canja”. Kallon Maanal AA yayi, duk da kullum tana a manne da shi. Amma sai ya dinga binta da kallo daki-daki. Ta ƙara ƙiba sosai dan cikin ya kumburata, duk da shi cikin ba wani yayi mahaukacin girma bane abinka dana farko. Fatanta ya wani sake komawa luf-luf kamar kalar ruwan sahara. Gaba ɗaya hankalinta ba'a kansu yake ba, suna hirarsu ne su uku Ameerah na sakama Najma lalli jaa a yatsu. Idanunsa ya ɗauke, sai kuma cike da sake marairaicewa ya ce, “My Sweetheart Oumna ALLAH na miki alƙawarin zan ninka kulawar idan ma yayi kaɗan”. “Ikon ALLAH, yau ni Fawzana naga cingum boy, to kai malam Ajwaad ance maka kulawar da kake batan ce batai ba. Kawai ka barmin ƙanwa ta dawo gaban mamant.....” Cike da jin haushi AA ya ɗauki pillow ya tilla masa, mi Abah da Babban Yaya zasuyi ba dariya ba. Sai AA ya sake tunzura. Fuuuu ya tashi ya fice abinsa. Oum ma dai ta kasa daurewa dariyar ta sanya. Suma hankalin su Maanal sai ya dawo wajen. Kowa ya ɗauka fushin na AA na ɗan lokaci ne waje ya fita ya huce zai dawo sai suka ji tsitt har lokacin tafiyarsu masauki yayi. Koda Fawzan ya leƙa babu shi babu alamarsa, ya dawo yana dariya da faɗin, “Oum autanki fa da gaske fushi yayi?”. Oum dake murumushi ta ce, “Zai ma sakko ne, amma bazan bashi ita ba”. Cike da mugunta Fawzan ke dariya. Babban Yaya ya ce “Kadai yi a hankali dan randa yazo kanka Auta ba raga maka zai yi ba. Duk bakai ka kunnashi har yayi fushin ba ma”. Dariya suka sake sanyawa dan yanda AA ya fita a fusace ya kasa barin ransu. Haka dai Oum ta korasu suma. Su a tunaninsu AA yayi fushi ya tafi masauki ne. Maanal dai batace komai ba, ko'a fuska kuma bata nuna damuwarta ba. Duk da zuciyarta na cike da damuwar yanda Bestyn ta ya tafi babu ko sallama. Kama hannunta Oum tayi ta haura da ita sama, ɗakin dake kusa da wanda suke ta shiga da ita. Ɗaki ne babba, komai akwai na buƙata, hatta kayan haihuwarta na'a ɗakin. Dama daga shi sai wanda su Oum suke ciki a gidan, Naufal ke kwana anan su Oum na ɗayan ɗakin. Yanzun ma yana a gadon kwance yana barcinsa. Cike da lallashi Oum ke kallon Maanal, dan tasan raba Besty da Besty ba abune mai sauƙi ba. “Babyna kada ki sanya wata damuwa a ranki kinji, zaman na kwana kaɗan ne kawai zaki koma wajen mijinki. Fatan mu dai ALLAH ya saukeki lafiya. Ki ajiye waya a kusa da ke da kinji wani canji tare dake ki kirani, nima kuma zan dinga leƙoki akai-akai kinji ko?”. Kanta ta jinjina ma Oum tana haɗiye hawayenta. Sarai Oum ta karance, amma sai ta basar, a ranta kam fal mamaki ne na irin wannan soyayya da ƙaunar juna da ALLAH ya haɗa tsakanin Ajwaad da Maanal. Koda yake itama gata nan da Abah, koda rayuwa ta gangara musu da shekaru ji suke kamar yanzu suka fara son juna. Tabbas soyayya gaskiya ce, kowa kuma da irin yanda zuciyarsa ke ɗaukarta. Oum ta sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Tashi kije ki kimtsa ki kwanta, komai da kike buƙata na ajiye miki a wadrob, kinyi shafa'i da wutri ko?”. Kanta ta jinjina ma Oum. Oum tai mata addu'a da sallama ta wuce. Sai lokacin ta saki hawayen da take riƙewa. Sai kuma ta ɗauki wayarta ta shiga WhatsApp, voice call tai masa har sau uku bai ɗaga ba. Ta koma video call, nan ma shiru, tai massage nan ma shiru. Sai ta sake rushewa da kuka. Kamar wata almara sai ga AA ya buɗe ƙofar toilet ya fito, ita Maanal ma razana tayi. Ta zabura zatai ihu a tunaninta aljani ne ke neman buɗe mata ido yay saurin ɗaura yatsarsa a kan baki yana mata alamar tai shiru. Dole ta saka hannunta ta rufe bakinta. Shi kuma ya rage hasken fitilar ɗakin ya ƙaraso inda take tsaye kawai ya rungumeta. A tare suka saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske, sai kuma a hankali ya saukar da kansa a dokin wuyanta ya shiga kissing nata step-by-step. A haka yay sama zuwa fuskarta ya cafke lips ɗinta. Babu musu ta bashi haɗin kai suna sauke ajiyar zuciya, kai kace shekara sukai basuga juna ba. Hannayensu ɗai-ɗai akan cikinta, kai da kaga yanda suka dafeshi kasan wannan abinda ke a ciki akwai ɗumbin soyayyarsa a zuciyar iyayen nasa. Sai da ya tabbatar yayi irin lallashin daya dace kafin ya janye lips ɗin sa ya sake rungumeta, sai kuma ya kamata suka zauna a ƙasan tattausan carpet dake a gaban gadon yana shafa bayanta, ita ko ta kwanta lamo a ƙirjinsa. “Besty baka tsoron Oum ta dawo ta ganka?”. “Komai zan iya ɗauka a kanki Maanal”. “Dama fushin ƙarya kayi kenan?”. “Na gaskiya ne mana, harna koma masauki kawai naji bazan iya daurewa ba kawai na dawo.” Ƙaramin murmushi ta saki, sai kuma ya ɗaga kai tana kallonsa, shima kallonta yake yi cike da kulawa da soyayya mai karfin gaske. Fin mintuna biyu sunama kansu kallo mai rugurguza garkuwar jiki kafin ta motsa lips ɗinta cike da raɗa, “Ka zama aljani ko? To ta ina ka biyo?”. Sai da ya kashe mata ido ɗaya sannan yay mata nuni da window. “Are you serious?”. “Akan besty da unborn ɗina zan iya komai, idan nace komai ina nufin komai fa ina har bazan saɓama UBANGIJI da sakawa da hanin MANZON ALLAH ba. Tambayoyin nan ya isa haka tashi muyi wanka mu kwanta nasan kina jin barci, jiba yanda idanunki suka koma ƙananu”. “Ni dai na gaji sai dai kayi min”. Lips ɗinta ya sumbata ƙasa-ƙasa da yanayin maganar nan tashi kamar an masa dole yace, “An gama my Everbloom”. “Thanks you my bestie”. Tare sukai wankan, ita tana da kayan barci shiko babu, sai kawai yay canja da wata bathrobe bayan ya cire wadda ya fito wanka da ita gudun mura. Ƙofar suka sakama key, ya ɗauka Naufal dake barcinsa ƙaƙas ya maida kan sofa bayan ya sake buɗe masa ita kamar gado, ya lulkuɓa masa blanket su kuma suka haye gado. Can cikin barci Oum tazo dan ta duba Maanal amma tana taɓa ƙofar yaji a rufe. Mamaki ya kamata, amma sai ta shiga kiranta a hankali. Cikin barci AA ya jita, amma Maanal tayi nisa a barci, sai kawai yay murmushi, a ransa yace Oum dama kin kwantar da hankalinki tana tare da GARKUWA TA. A zahiri kam luf yayi har Oum data fahimci barci Maanal take mai nauyi ta juya ta koma. Ana kiran sallar farko AA ya tashi, cike da lallaɓawa ya raba jikinsa dana Maanal. Bayi ya shiga ya watsa ruwa yay alwala ya fito ya maida kayansa, cike da sanɗa ya fita a ɗakin da gidan ma gaba ɗaya. Koda Maanal ta farka da asuba taga bashi nan mamaki ya kamata, amma ganin agogon sa ya sakata sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ga Oum ta shigo tashinta, ganin Naufal a sofa ya bama Oum mamaki, dan tasan Maanal bazata iya maidoshi nan ɗin ba. Sai kuma yanda alamu suka nuna gadon kamar mutum biyu suka kwanta. Can idonta ya sauka akan agogon AA. Sai kawai ta shiga tunanin yaya akai haka? Amma dai batace komai ba ta juya ta fita. Koda ta koma nasu ɗakin bayan Abah ya dawo daga sallar asuba sai tai magana. Murmushi yayi da faɗin, “Oh dama kina tunanin Ajwaad zai tafin ne da gaske. Ai ni tunda na hawo saman nan ma naji ƙamshin turarensa nasan bai bar gidan ba”. Dariya ma abin ya bama Oum ita kam. Sai kawai ta girgiza kai. Can wajen takwas sai ga AA kamar bashi ba yazo gidan shi a dole lokacin ne yazo. Bayan sun gaisa da Oum da Abah da suma suka basar kamar basu san a gidan ya kwana ba sukace zasu fita ɗan motsa jiki. Suna ficewa ya haura sama. Ya samu Maanal kawai na barci Naufal ya wuce makaranta. Zama yay a kusa da ita yana murmushi, sai kuma ya ranƙwafo a kanta ya sumbaci lips da idannunta. A hankali ta buɗe idanun tana kallon sa, suka sakarma juna murmushi. Cike da raɗa ya ce, “Ƙyaƙyƙyawata yunwa fa?”. Baki ta ɗan tura masa ƙasa-ƙasa ta ce, “Bana ji”. “Kin tabbatar?”. Kanta ta jinjina masa, sai kuma can tace, “Da dai zan samu dafaffen ƙwai naci da yaji ko miyan attarugu”. “An gama Bestyn Besty. Bani 30mint kawai in sha ALLAHU yanzu zakiga kwai ke da my unborn”. Yay maganar yana sumbatarta ya miƙe ya fita. Ta bishi da kallo tana lumshe idanunta. Kamar wasa barci mai shegen daɗi ya sake fara figarta, sai kuma kamar wadda aka tsikara ta farka a firgice sakamakon wani irin juyawa da ɗan cikinta yayi, sai kuma bayanta ya riƙe gam, hakama mararta ta ƙulle. Sai kawai jikinta ya hau rawa..........✍️