Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 187

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 187

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 187: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 187. A can kuwa ƴan jere basu sami tarbar…

2,942 words

A can kuwa ƴan jere basu sami tarbar mutuntawa ba a wajen matan Alhaji Balala. Tun jiya ya sanar musu ya ƙara aure, ya kuma tabbatar musu duk wadda ta kawo masa hauka zai saita mata layi ta tafi gidansu ya cike gurbinta da wata matar. Shi dama haka yake, indai zai ƙara aure babu batun tausasawa a tsatinsa. Saboda yanda yake jin alfaharin yana da kuɗi matan bazasu iya barinsa ba. Hakan ne kuwa, dan suma bazasu iya tafiya ko'ina ba. Dan kaf ƙauyen sune matan mai kuɗi masu ci su ƙoshi kullum duk da kuwa ɗumamen tuwo ne abincin. Sutura kuwa sai shekara-shakara kuma roba-roba atamfa ce da takalmin roba na danƙo shima. Da salla kuma za'a yanka musu akuya ko tunkiya matsayin naman salla. Suyi tuwo miyar taushe. Idan kuma ALLAH ya jarabci dabbobinsa da ciwo baya sayarwa zai yanka a ci a gida. Shiyyasa wani lokacin da biyu yaran ke buge dabbarsa dan a yanka musu. Sai dai kuma idan ya ganoka ka shiga ukunka. Tunda sassafe ya saka yaransa gaba suka gyara ɗakin da Hajiya Basariyya zata zauna suka hau shafen farar ƙasa, harta ƙofar ɗaki ma aka yayyarfa mata kamar dai yanda akema ɗakin amarya a ƙauye. Lokacin da ƴan jere ke isowa har sun kammala. Dan haka babu ɓata lokaci suka fara aikinsu. Sai dai gadonta na gidan Daddy ne kawai ya shiga da wadrobe sai mirror. Amma ko bedside drawers basu samu waje ba ɗakin yayi kaɗan. Dole haka aka tattara sauran kayan aka jibge mata a ƙofar ɗakin, sai kuma ga kishiyoyin nata na leƙen ɗaki daga nesa. Dan basu gaɓa ganin irin wannan kayan ɗaki ba haka. Su dai ƴan jere bayan sun gama suka zauna sukaci taliya da mai da yajin da kanwar Alhaji Balala ta dafa musu Karime. Harda kazarsu guda sukutum. Sai da sukaci sukai nak sannan suka kullo ɗaki suka taho sai kuma gobe tarewa......

_________★ SAUDIA

Karɓar gaggawa akama su Maanal a asibiti, abinka da babu wasa komai ana bashi haƙƙinsa yanda ya dace babu ɓata lokaci aka hau yi mata abinda ya dace. Sai dai ga haihuwa gadan-gadan amma ta kasa yi da kanta. Dole likitar ta shiga binciken minene matsalar. Babu wani jimawa ta fahimci yarinyar bazata iya haihuwa da kanta bane ba dalilin yanayin jikinta ƙugu yayi jaɗan, bayan kuma ga komai matsa ALLAH a zahiri. Dole suyi mata aiki da gaggawa. Babu wani ɓata lokaci ta fito tanama su Abah bayani. Dan zuwa lokacin suma su Babban Yaya sun iso asibitin duka dasu Najma. Sun gamsu da bayanin duk da akai musun, dan haka babu ɓata lokacin AA ya saka hannu ga dukkan abinda ake buƙata. Su kuma suka shiga da ita cs na gaggawa, dan tana a matakin buƙatar taimakon gaggawar.

A Nigeria babu wanda yasan halin da ake ciki, dan basu kira kowa ba sai suketa faman kai-kawo da addu'oi, dole Babban Yaya yaja AA a jikinsa ya rungume. Dan kallo ɗaya zakai masa ka fahimci yana cikin wani matsannacin yanayi. Jarumtarsa da iya kame damuwa ce kawai ta ɓoye komai. Kasancewar safiya ce babu wani uziri daya saka ɗayansu barin ƙofar ɗakin. Haka suka kasance zaune idanunsu a ƙofa tsahon awanni. Zuwa can sai ga wata baƙar fata Nurse daga ganinta kaga ƴar Nigeria kodan fetalin dake fuskarta ta fito daga ɗakin. A tare duk suka miƙe suna tambayarta yaya ake ciki. Murmushin kwantar musu da hankali tayi cikin yaren hausarta daya fara canja salo ta ce, “Alhamdullahi, komai lafiya, everything is fine, an ciro baby lafiya, yanzu muna buƙatar jini ne, idan kun amince a ɗauka na asibiti....” Da sauri AA yace, “No! Ba buƙata. Muje a ɗiba nawa”. Murmushi Nurse ɗin tayi tana kallon AA ɗin ƙasa-ƙasa. Gaskiya zaratan mazajen uku sun tafi da imaninta. Musamman wannan mai duhun fatar da kallo ɗaya zai tabbatar maka da ingarman namiji ne a tsayensa. Duk da dai suma sauran masha ALLAH babu rago. Itace ta jagorancesu zuwa wajen ɗibar jinin. Dan Babban Yaya da Yaya Fawzan basu bar AA ya tafi shi kaɗai ba. Kusan mintuna talatin da wucewar tasu wata macen baturiya ta fito da jariri a hannu cikin kyakkyawan fari ƙar ɗin showal da kallo guda idan kai masa kasan zai yi bala'in laushi. A tare su Oum suka miƙe har Abah, sai kuma ga wata ta fito itama, sai dai ita ɗin balarabiya ce. Itama ɗauke da jariri nannaɗe a sky blue na exactly irin wancan farin. Gaba ɗaya sai aka koma kallon kallo tsakanin su Abah da su Ameerah. Su kalla juna su kalla matan da suka jeru suna kallonsu da murmushi. Oum ce tai ƙarfin halin ƙarasowa gabansu, ta leƙa na farko sannan ta leƙa na biyu. Jarirai ne kuwa guda biyu masu tsannanin kammani da juna, kama kuma irin tata da yaranta da Abah, a taƙaice dai suma gida suka kwaso, wato kamanni Darma Family. Ai da sauri Oum ta juya tana kallon Abah, ta ce, “Wlhy Gadanga da gaske ƴan biyu”. Da wani irin sauri su Najma suka ƙaraso, hakama Abah. Ma'aikatan asibitin dake ɗauke da yaran suna dariya sukace, “Congratulations an ciro twin's duk maza. Suna cikin ƙoshin lafiya kuma, hakama mamansu Alhmdllh babu wata damuwa a tare da ita sai cs da akai mata, in sha ALLAHU nan da kwanaki kaɗan kuma zata koma normal”. Farin ciki ya saka Abah da Oum summa kasa magana, sai Oum dake hawaye, Abah kuma ya koma gefe yay sujidar shukur kamar yanda yayi a lokacin da akai masa albishir da samuwar cikin. Yau dai alƙawarin ALLAH ya cika ga jinin Ajwaad ɗinsa gauraye dana Maanal ɗinsa waje guda kamar yanda ya daɗe yana fata da addu'a a rayuwarsa........✍️194

.......Sageer na fitowa a wanka shiri yayi ya barma Huznah gidan batare da ko kallonta yayi ba. Dan wlhy gaba ɗaya ransa a jagule yake, zuciyarsa a ƙuntace take. Yana buƙatar bama gidan iska ya samu ya huce idan ba haka ba komai zai iya faruwa, ji yake kamar ya mammari Huznah koma ya daketa, sai dai zuciyarsa na hanashi. Ace matarka ta aure da har rabo ya ratsa na haihuwa tana rayuwa da kai amma zuciyarta na akan wani can da baima san tana yi ba. Duk wani ƙoƙari yayi domin ganin ya karkato da hankalin Huznah a kansa sun taru sun rufawa juna asiri ashe a banza ne. To abanza mana tunda ta kasa ajiye abinda ya zama kabari a rayuwarta. Idan yace ma ya zargi AA Darma ko yaji zafinsa shi minene laifinsa tunda ko'a baya baice yana sonta ba, zuwa yanzu ma yana da tabbacin ya manta da wata Huznah a duniyarsa. Hakafa lokacin da akai kidnapping su AA ɗin nan tunda ya ɗakkota daga Kaduna suka dawo Kano ta saka kanta a wani hali, shi duk zatonsa abinda mahaifiyarta ta aikata mata ne akan yunƙurin zubar da ciki ya sakata shiga yanayin, ashe-ashe damuwarta akan AA ne. Abinda yasa ma har ya tuna haka a yanzu yanda ta dinga maimaita masa zancen da tambayarsa yaya ake ciki? An saki su Maanal? Suna cikin ƙoshin lafiya kuwa?. Duk da ya ɗan yi mamakin yanda ta damu da al'amarin Maanal ɗin tunda yasan ba sonta take ba sai yay tunanin ai yanzu Huznahr ta canja ne, ga yanda Ammie ta dinga kai-kawo akan nata al'amarin maybe shiyyasa itama yanzu ta damu da halin da Maanal ta shiga. Ashe-ashe nata tunanin ita daban ne. Kofa motar daya saya bata nuna farin ciki ba kamar yanda ta nuna damuwa akan kidnapping ɗin nan..... “Sageer wai kana lafiya kuwa?”. Abokinsa da tun ɗazun yake magana amma babu alamar ya jisa saboda yanda yay zurfi a tunani ya faɗa yana zungurarsa. Firgigit Sageer ya dawo hayyacinsa, sai kuma ya sauke kakkauran numfashi tare da furzar da shi ya juya yana kallon abokin nashi. Shi da shi amanar juna ne, basa ɓoyema junansu komai na rayuwarsu sai abinda shari'a ta hanesu da bayyanarwa wato sirrin aurensu. In ma zasu bama juna shawara ta wannan ɓangaren sai dai cikin hikima da iya lafazi bawai kai tsaye ba. Dan ko akan zamantakewar sa da Huznah ɗin ya taka rawar gani sosai a kai da shawarwari. Sageer ya sake furzar da huci sannan ya ce, “Toufeeq akwai matsala ne wlhy?”. “Matsala tami kuma?”. “A gidana”. “Gidanka kuma? Ai na zata mun wuce wannan matsayin komai ya wuce kuma itama Huznah ta kwantar da hankalinta yanzu tunda kayi wining game ɗin har ga Usman Fodio”. “Humm Toufeeq kenan, a zahiri ne nai wannan nasarar. Amma a zuciyar Huznah har yanzu bana ciki. Dan kuwa jiya da rana sanda nake cemaka zanje gida nakai mata naman nan karya lalace kawai na sameta cikin zurfin tunani.......” tsaff ya kwashe komai ya sanar masa. Mamaki sosai ya kama Toufeeq. “Kai amma Huznah bata ƙyauta ba, wannan ai rashin wayo ne kamar batai islamiyya ba dai. Koda yake wannan itace irin masifar dake yawo a gidajen aurenmu tsakanin mata a wannan zamanin. Ƙiri-ƙiri yarinya da igiyar auren wani a kanta harma da ƴaƴa tsakani sai kaga ta mutu a son wani dake waje. Imma tsohon saurayinta, in ma haɗuwar media bayan aure. Idan sun samu sakarkarun samarin mazan nasu sai kaga anata yaɗa fasadi ta hanyar waya da charting kai miji kana nan wasarere da baki kana ciyar da ƙatuwar banza kullum kana rana. Tun abun na tsayawa a wayar sai kaga sheɗan ya tunzurasu haɗuwa zina kuma ta shiga da aure. Shiyyasa wani lokacin wlhy bana ganin laifin mazan dake hana matansu yin harkar social media ɗin nan musamman masu rawar kai da son ƙarya. Dan wata acan take haɗuwa da lalatattun ƙawaye su sakata a group dake da maza sai mazan suna biyosu, idan wata bata kula ba wata fa daga nan ake haɗa alaƙa. Watama ba mazan bane da mata ƴan uwanta take lalacewar, innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, mun ɗauki shaiɗanci abu mai sauƙi. Amma kam tabbas a yanzu wayoyinmu sune kawalanmu batare da mun fahimta ba. Amma Alhamdullah hakan ba yana nufin an taru an zama ɗaya bane. Dan wata mace wlhy ka ganta a media kamila, mumina ko ɗar baka ji idan ka ganta da waya koda tsakkiyar dare ne. Saboda abinda zai amfaneta kawai take yi sai nishaɗin yau da kullum. Wannan kam babban ƙalubale ne a gareka Sageer, dolene kuma ka tashi tsaye domin yin yaƙi da shi tun kafin al'amarin ya cigaba da nisa...” “Shiyyasa na sameka Toufeeq, dan a wannan gaɓar jinake kamar na haƙura na rabu da Huznah. Bazan iya rayuwa da macen da ba ni ne a zuciyarta ba. Gagangar jikinta kawai kenan na aura komi? Idan hakan ta kasance minene amfanin auren to? Gangar jiki wata rana tsufa zai risinar da ita ya tauyeta, itako zuciya da soyayya ta gaskiya har abada bata tsufa a zuciyar ma'aurata koda ɓacin rai ya danneta lokaci-lokaci sai ka samu tana motsawa.” “Hakane maganarka tana kan gaskiya. Amma bazan baka shawarar rabuwa da iyalinka ba. Kaima nasan kishi ne kawai ke cin zuciyarka. Dan haka kada kayi gaggawa. Amma kayi haƙuri ka ɗauki hakan matsayin ƙalubale da jarabawa. Sannan ka shirya fito mata ƙuru-ƙuru kawai tare da nasiha da lallashi da nusar da ita illar abinda take yi bayan ka nuna mata fushinka. Idan ta fahimta shike nan. Idan bata fahimta ba kaga sai muyi tunanin mataki na gaba ko”. Kai Sageer ya jinjina masa. Sai kuma zuwa can ya ce, “Shike nan na gode Toufeeq, zan gwada kuma na gani, in sha ALLAHU komi kenan zakaji”. “ALLAH ya kawo komai da sauƙi. Amma ka dage da addu'a dan ALLAH, komai yay tsanani maganin sa ALLAH”. Kai kawai Sageer ya jinjina masa.....

___________★

Anan Abuja kam Nibras da aka gama treating da magunguna iri-iri da aka amsa a wajen likitoci daban-daban a Nigeria da ƙetare ce ke shirin komawa gidan Darma. Duk da kuwa tunda Fawzan ya wuce basu taɓa waya ba. Maimakon ma ta damu ita hankalinta nakan AA, dan kuwa uwarta na nan na damuwa da tsalle-tsallen ganin ta samu lafiyar mahaifa ita tana nan tana shirya matakan takawa zuwa ga cimma AA. Dan a watan jiya ta cire tsoro ta fara tura masa saƙwannin soyayya ta WhatsApp da sabuwar number ɗinta. Sai dai tafi sati uku tana turawa kullum babu gajiyawa amma bai taɓa ko buɗe saƙon ba ma balle yasan tanayi. Sai ranar tana tura saƙon barka da juma'a taga an buɗe ko second biyu ba'ai ba. Kai tsaye ta fahimci a mistake ya taɓa irin saƙo ya shigo makan nan ka taɓa kawai. Tata jiran wani motsi ko zai duba amma bata sake jinsa ba, data cigaba da turawa kuma ba'a sake buɗewa ba. Ta tabbatar idan ta kira shi sai ya gane itace, dan haka ta koma turawa ta text message nan ma cike da roƙo da magiyar dan ALLAH ya saurareta. Amma har zuwa yau shiru kake ji. Ga wasu irin mahaukatan magungunan mata Mom ɗinta nata ɗura mata. Tun basa damunta har sun fara cizonta. Dan haka a karo na farko tace ita kawai a ƙarasa shirya mata komai ta koma tunda Yayanta yayi waya da Fawzan yace a satin nan suke saka ran dawowa matar Autansu kawai suke jira ta haihu. Wannan yasa shirye-shiryen komawar tata ya kammala tsaff dan so suke ana gobe zai dawo ta koma in sha ALLAHU. Kwance take yanzu ma a ɗaki ita kaɗai tunanin AA da sha'awar kasancewa da shi ta gama zagaye gurɓatacciyar zuciyarta, wayarta dake saman cikinta ta ɗauke ta shiga lalubo layin sa. Kawai sai zagayen cycle ɗin nan na dp ya nuna mata green alamar AA ya saka status. Mamaki ya kamata dan abinda bata taɓa gani yayi ba. Ko dp ɗinsa hoton agogone kawai a jiki, kuma tunda ta sanshi bataga ya taɓa canjawa ba. Da gudu ta danna, sai ko kai tsaye ya kaita status ɗin nashi, hoton jarirai guda biyu a cikin white showal da sky blue. Masha ALLAH yaran ƙyawawa masu matuƙar kamanni da juna, sai dai ƴan ƙananu da su dan basu da wani gurma. Gabanta ya faɗi wani ras. A take wata irin zufa ta shiga karyo mata, rawa jininta ya fara. Da gudu ta fito ta koma account ɗin Yaya Fawzan. Nan ma sai ga hoton jinjiraye ya rubuta Alhamdullah my boys sun iso. Tashin hankali, ai cike da rawar jiki ta dinga bin status na duk numbers ɗin ahalin Darma da take da number ɗin shi. Al'amarin kamar wani wutar jeji ko'ina ta shiga hotunan yaran ne ana musu addu'oi da su da mamansu. Ai bama tasan ta cillar da wayarta gefe ta fashe da kuka ba. Kuka sosai take yi jikinta har yana girgiza wa. Yanzu shike nan dai Maanal da gaske ta mata nisa tunda gashi har ta haihu da Ajwaad ɗinta. Haihuwar ma yara har biyu a lokaci ɗaya, ai ko wlhy bazata ƙyaleta ba, bazata barta ba, yanda tai mata wannan babban raunin a zuciya itama sai ta bar mata tabo a tata zuciyar. Dan duk abinda zatayi dan rabata da Ajwaad sai tayi.........✍️ 195

........Sai da ta gama haukarta da duƙe-duƙen alƙawarinta sannan ta tashi ta shiga bayi tai wanka, fitowa tai ta gyara jikinta tare da ƙarasa haɗa kayayyakinta sannan ta ɗauki wayarta, sai yanzu kuma wani tunani yake zuwa mata a rai, shin miyasa taga status ɗin AA? Hakan na nufin yayi saving number ɗinta kenan?. Sai kawai taji wani irin sanyi mai daɗi ya ratsa mata zuciya, murmushi ya kufce mata. Kaso ashirin cikin ɗari na nauyin da zuciyarta yay mata ya sauka. Haka ta shiga gunguro akwatina ta fito. Mom ɗinta na falo zaune sai Yayanta ɗaya da yazo gidan duk suka ɗago suna kallonta ita da akwatinan. “Ke lafiyarki kuwa? Ina zuwa da akwatina haka da yammar nan?”. “Mom gidana zan koma. Gara na koma yau Maanal ta haihu, Kinga kuwa daga yau zuwa koyaushe zasu iya dawowa ƙasar nan ko”. “To kuma shine dan rashin hankali babu bayani babu komai sai ki kama kinkimo akwatina zaki yafi? Ke wai yaushe zakiyi hankali ne dan ALLAH Nibras? Ke dai kullum kina girma amma gaki nan shashasha, sakara-sakara, gaula-gaula.” Baki ta cika da iska jin baƙaƙen maganar da Yayan nata ke jera mata. Idanunta cike da ƙwalla tace, “To amma Yaya Ma'aruff ya kake so nayi, kufa kuka matsa saina koma ɗin nan, naƙi kanata min faɗa kai da Yaya Asad, yanzu kuma na yarda zanyi abinda ya dace kana zagina. Suma can nazo ban koma ba ace ina baƙin cikin ta haihu har ƴan biyu”. “What! Yan biyu fa Nibras?”. Cewar Mom kafin Yayan nata yace wani abu. Idanun Nibras cike da hawaye ta ce, “Wlhy Mom ƴan biyu duk maza”. “Tab ɗi! Aiki ga mai ƙare ka. Lallai ita wannan da shirinta tazo...” “Shiri kuma kamar ya Mom, dan kawai ta haihu ƴan biyu shine kuma shiri? Ba ALLAH ne ya bata ba.” “Uhmm! Ku maza shashashai ne ba gane komai kuke ba. Ke ajiye akwatinan nan ki jirani zuwa anjima zan rakaki da kaina amma not now”. Sosai al'amarin ya girmi kan Ma'aruff. Sai yaji ma ya kasa yin magana ya miƙe kawai yay ma Mom ɗin tasu sallama dan ya fahimci yanzu hankalinta bama a kansa yake ba.. Yana wucewa Nibras ta dasa sabon kuka, ita manufar kukanta daban, abinda Mom ɗinta ke fassarawa daban. Haka ta zauna ta lalace a lallashinta da tsara mata abubuwa babu kunya yanda zata dage wai itama ta samo cikin, idan kuma ya gagara nanda watanni uku dashen da Doctor ya basu shawarar yi shi zasu koma ai mata. Haka ta ƙara ɗiɗɗirka mata maganin mata da abubuwa iri-iri ta tattara mata sauran kayanta anayin sallar magrib suka tafi gidan Darma....

__________★ SAUDIA

Readers Also Read