Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 188
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 188: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 188. Ba'a basu damar ganin Maanal ba a…
3,150 words
Ba'a basu damar ganin Maanal ba a lokacin, dan sunce sai an gama ƙara mata jinin da aka ɗiba jikin AA. Shima kansa AA ɗin basu barshi ya tashi ba sai bayan awa ɗaya ya samu natsuwa, haka suka dawo inda su Oum suke suka samesu cikin matsanancin farin ciki. Kafin ma su tambayi mike faruwa Oum ta fara basu labari, Ameerah ta nuna musu hotunan babys data ɗauka. A karo na farko kawai AA yaji jikinsa na tsuma koda wasan wasa basu taɓa kawoma ransu twin's ne a cikin Maanal ba. Dan basu ma taɓa yarda an duba musu mace ne ko namiji ba. Saboda duk abinda ALLAH ya basu suna farin ciki, hasalima sunfi ƙulafucin samun macen kodan basu da ita a gidan, dama Anum ce dan haka suka so yarinyar kamar ransu, yanzu kuma ta kufce ta barsu. A hankali AA ya zame yay sujidar shukur, kafin ya miƙe ya fita massallaci. Ai babu ɓata lokaci su Babban Yaya suka bishi, dan Abah ma yana can. Dukansu sai da sukai sallar godiya ga UBANGIJI tare da addu'oi, kasancewar azhar tayi suka gabatar sannan suka dawo. Zuwa lokacin an sake fito da yaran zuwa ɗakin da za'a maida mamansu dan dama sunje da su ne ana sake duba lafiyarsu da duk abinda ya dace. Babban Yaya ya fara amsarsu duka, ya rungumesu a ƙirjinsa yana mai jin ƙaunarsu tamkar Naufal. Yay musu addu'a sosai sannan Yaya Fawzan ya ɗauka. Shi kam ai sai da yaji hawaye na cika masa ido, yana masifar son yara a rayuwarsa kodan bai samu nashi da sauri bane. Amma haka yake ma su Naufal gata dama kamar kamar mi. Shima bayan ya gama rurrugumesu da musu addu'a mai gayya da aiki ya amsa. Shi kam da farko idanu ya zuba musu, zuciyarsa na wani irin rawa a cikin ƙirjinsa, shi Ajwaad Aliyu Abubakar Darma ne da ƴaƴa har biyu mallakinsa, ƴaƴan ma daga jikin Maanal Habib Giro Bestynsa. Yarinyar nan dai daya rayu da ita tun ƙuruciya, yay mata wanka yay mata wanki da abubuwa daban-daban, yarinyar da yake jinta tamkar jini da tsokar jikinsa, dan bai taɓa jin ƙaunar wata halitta bayan MANZON ALLAH da iyayyensa da ƴan uwansa irin Maanal ba. Da ace ana buɗe zuciya aga yanda asalin soyayya take da idan aka buɗe tashi sai masoya da kansu sun girgiza. A hankali hawayen da suka cika masa idanun suka ɗigo akan yaran, sai kawai ya rungumesu a cikin ƙirjinsa ya ɗauke hawayen batare daya bari kowa ya lura ba. Addu'oi sosai yay ma yaransa. Bai iya ya sake bama kowa ba sai da akazo aka amshesu dan ba'a son ana yawan daƙunasu. Daga nan ne fa suka fara kiran ƴan uwa nan Nigeria ana sanar musu tare da tura musu hotunan babys. Kafin wani dogon lokaci ahalin Darma ya ɗauki farin cikin ƙaruwa da suka samu. A kusa-kusa an haifa musu yara huɗu kenan. Ga ta RK, ga na Uncle Najeeb dan shima matarsa ta haihu namiji kusan wata uku kenan, tsakaninta da Nuwaira babu nisa. Ga kuma na AA har biyu. Saura Najma da Ameerah kuma da Maimoon, duk da dai na Maimoon basu da ƙarfi a kansa suna son kayansu..
A ɓangaren Ammie ma da yaran gidansu tunda Oum ta kirata ta sanar suka kaure da farin ciki. Ammie harda hawayenta. Itama batayi ƙasa a gwiwa ba tai kiran Nene a waya ta sanar mata. Suma su Shahidah Aunty Sakeena ta kirasu ta gumtsa musu. Sai kuma ga hotuna AA ya turama Ammie da kansa. Suma nan suka fara yawo a tsakaninsu. ALLAH sarki Yaya Yazeed sai da yaji hawaye na neman cika masa ido, lallai ya yarda wani baya haihuwar ɗan wani. Yau ga ƴaƴan Ajwaad da Maanal dai a duniya. Hajiya Yaya kam kunya taji ta mamayeta, sai hawaye kuma suka shiga biyo baya. Ta zuba ma Yazeed idanu cike da tausayi da rauni ta ce, “Ka yafe min Yazeed, nasan na cutar da kai, na rabaka da Maanal bayan nasan kana sonta. Duk da dai wani baya haihuwar ɗan wani, haka wani baya auran matar wani. Amma nima nayi abinda bai kamata uwa tayi ba kodan ƙyawawan hakayyarka na ɗa nagari. Duk cikin ƴaƴana babu mai min irin biyayyar da kake min da hidima. Amma son zuciyata da zugar sabuwa ya kaini ya baroni na ƙuntata yarinya saliha irin Maanal....” “Dan ALLAH Mamma ki daina cewa haka, duk abinda ya faru yana cikin ƙaddara tane ai, tun farko kuma dama Maanal ba matata bace ba. Harga ALLAH kuma na haƙura dan ta dace da Ajwaad, shine ya cancanci dama aurenta kodan soyayyar dake tsakaninsu mai ƙarfi tun ƙuruciya. Nima in sha ALLAHU ALLAH zai bani tawa”. Ammie da zuciyarta ta ƙara raunana da tausayinsu tace, “In sha ALLAHU Yazeed ALLAH bazai taɓa taɓar da kai ba. Kuma ALLAH da zaka yarda mizai hana ayi ƴar gida kai da Khadijahn Kano, yarinyar nan nada nutsuwa da hankali. Gata da iliminta na addini dan Kawunku Sani baya wasa da ilimin addinin yaransa. Amma fa idan har kaji ta maka dan babu mai sake tirsasaka auren wanda baka so kaji”. Murmushi Yazeed yayi yana wani sinnar da kai, ƙasa-ƙasa yace, “Ammie in dai tana sona mizai hana na amince”. Yanda yay ɗin sai ya bama Daddy da Ammie da Hajiya Yaya dariya dan duk suna a falon Daddy ɗinne. A karo na farko Daddy ya ce, “Wannan kuma aikinka ne Son, kai zaka sameta ka koya mata soyayyar ka. Mu namu addu'a ne da farin ciki, dan suma ƙannan nan naka na gaji da zamansu haka, zan basu gargaɗi na ƙarshe idan son samu ne zuwa ƙarshen shekarar nan kaga sai a haɗa duka na aurar daku nima na huta, sai nasan hidimar ƙannenku ne kawai ya rage min”. “Karka damu Daddy in sha ALLAHU zamuyi ƙoƙari, yaran nan kuma ka barni dasu kawai yanzu lokacin da zaka fara hutawa ne”. Sosai Daddy yaji daɗin bayanin Yazeed, hakama su Ammie da Hajiya Yaya....
★★
Kamar yanda doctors suka faɗa basu sami ganin Maanal ba sai dare, kusan 8 ta farka daga barcin da suka sakata sannan aka barsu shiga ɗakin da take ita da babys ɗin. Tunda suka shigo ta zuba musu idanunta da suka shanye suka ɗan kumburo. Suma kallonta suke kowanne fuska da murmushi, Oum ta zauna kusa da ita tana mai kamo hannunta cikin nata, Abah kuma ya zauna a kujerar kusa da gadon, sai AA ya zagaya can ɗayan gefen shi da su babban Yaya. Ameerah da Najma na zaune suma a bakin gadon ta gefen da mazansu suke.........✍️
196
........A hankali ta motsa lips ɗinta ta ce, “Oumna? Abanah!”. Cike da so da ƙauna suka amsa mata a tare, sai kuma ta kalla Ameerah da Najma suma ta kira sunansu. Amsa mata sukai suma cike da farin ciki. Ta sake juya kanta a hankali ta kalla Babban Yaya da Fawzan suma tace, “Yayana, Yaya F.” Suma da kulawa suka amsa mata fuskokinsu da murmushi har babban Yaya da kakan daɗe baka yana yi ba. AA ta tsare da kallo na sakanni, shima kallon nata yake ƙasa-ƙasa, yana jira a kira sunansa yaji tsitt. Sai kawai catai “Yaya F. Wanene wannan?”. Mi zasuyi inba dariya ba, musamman Yaya Fawzan. Ya ce, “Lilly baki ganesa ba ko?”. Kai ta jinjina alamar e. Aiko aka sake sanya dariya. Babban Yaya shima dai yau ya ɗana. Ya ce, “Lilly wani ɗan riƙo ne da aka kawo mana kin manta da shi, miskili, rigimamme ga dukan yaran mutane saboda Bestynsa. Ga kishi da duk wanda ya kula masa ita. Idan kaga yana dariya sai da besty, idan kaga yana surutu sai da Besty”. A hankali tana murmushi ta ce, “Lah Yaya na tunashi. Yaushe yazo?”. AA dake kallonta yana murmushi ya duƙo yana dungure mata kai kaɗan, cike da raɗa yanda ita kaɗai ta jisa duk da suna a kusa da su ya ce, “Randa na baki cikin my twins baby's nazo.” Sosai maganar ta bata kunya, tasa hannu ta ture masa fuska. Su dai su Abah murmushi suke cike da jin daɗi da farin ciki. Irin wannan yanayin yake fatan dinga ganin iyalansa a ciki akoda yaushe, yana son farin cikin iyalansa matuƙa. Dan haka yake jin daɗin ɗan zaman nan nasu na saudia kamar su kasance a haka dindindin. Amma ba komai, ko Nigeria suka koma ya shirya tsaff da sabon shirin gyara zamantakewar gidansa fiye da ta baya in sha ALLAHU...
_________★
Amarya Hajiya Basariyya dai ta tare gidan Alhaji Balala. Bayan yayanta da Uncle Faruk da Kawu Manu sun mata faɗa sosai da nasiha. Maƙwafta da abokan arziƙin iya sukai mata rakkiya a motar Yayanta driver ya kaisu. Dan duk da Alhaji Balala ya turo mashina dan ya burge Yayanta ya hanasu hawa. Hajiya Basariyya zata iya rantsewa bata taɓa shiga baƙin cikin rayuwa irin na yau ba. Ji take kamar zata mutu, babu abinda ke dawo mata a zuciya da ruhi sai fuskar Daddy. Ƙyaƙyƙyawan mutum ɗan gaye ga son ƙamshi da tsafta. Iya magana ga ilimin addini dana zamani. Kuɗin idan ka ƙwanƙwasa kuma akwaisu masha ALLAH. Iya ƙoƙari yanayi akansu su iyalanshi. Ga jarumta dan duk da shekaru sunja su duka ukun Daddy yana iyawa da su har ke da kika kwana da shi sai kinji a jikinki. Hakan kuma baya hana washe garin kwananki ya sake jigataki, girkin wata ya shiga washe gari itama ta samu makamancin farin cikin da kika samu. Duk da wannan ƙyaƙyƙyawar rayuwar data rayu a cikin kusan shekaru ashirin da tara yanzu ta ƙare a auren ƙauye, ƙazamin mutum irin Alhaji Balala. Haba jama'a miyasa zatai irin wannan mummunan ƙarshe haka mara fasali da daɗin ji koda a labari?. Rashin mai bata amsa yasa ta sake rushewa da kuka. Su dai ƴan rakkiyar amarya har abin nata ya fara gundurarsu. Haka suka iso ƙauyen su Alhaji Balala da bai da nisa da nasu. Duk da dare ne sai ga mata da yara na fitowa kallon mota. Alhaji Balala kam nata washe baki ransa fes amarya ƴar gayu an kuma kawota a mota an ƙara mutuntashi. Sai rawar uwawu yake kai kace shine zai shiga da ita gidan. Haka yay musu jagora har ɗakinta yana haska musu hanya da dalleliyar tochlight ɗinsa da taji sabon zubin battery. Matan nashi ma dai duk suna tsakar gida ransu a ɓace, sai ƴan uwansa mata da matan ƴan uwansa maza cike da gidan sun saka mp wai ana bikin tarewar amarya. Sai kuma surukansa duk su sun kasa sakin jiki da ƙyau saboda iyayen mazansu kar suce suna murnar an musu kishiya. Anyi faten tsaki tun da yamma shi suketa kwasa. Haka aka kai Hajiya Basariyya ɗakinta, aka kawo ma ƴan kawota tuwo miyar taushe na tarba sai kaji har uku akai dan su kaɗai ma akaima tuwon aka ɓoye. Ganin dare yayi basu zauna ba sukace zasu wuce da tuwon gida kawai. Haka aka kwasa aka kai musu mota sukai sallama suka tafi. Sabon kuka Hajiya Basariyya ta saki musamman data gama bin ɗakin da kallo, gadai kayanta ne na gidan Daddy amma ko ɗakin maigadinsu yafi wannan ɗakin ƙyau da tsaruwa. Wannan abu ya sake tayar mata da hankali. Da girmanta da shekarun ta anfi ƙarfinta an mata auren dole. Tun tana jin hayaniyar gidan har ya koma tsitt. Abinka da ƙauye goma zuwa sha ɗaya ko'ina kake ji yayi shiru. Tana nan zaune abin duniya ya isheta abubuwa da yawa take saƙawa ranta iri daban-daban Alhaji Balala yay sallama ya shigo. Wani irin bugun hancinta da turarensa yayi mara daɗin shaƙa sai da hanjin cikinta suka wantsala. Ga wani irin ƙarni-ƙarni komi ma zata kira abun oho na fitowa daga ledar hannunsa wai kazar amarya. Haushi, takaici, baƙin ciki kamar zata mutu. Kasa masa magana tayi har yanzo kusa da ita ya zauna shirim bayan ya danna ma ƙofa sakata. Da sauri tai ƙoƙarin matsawa, ya damƙota ya riƙe yana faɗin, “Haba amaryata Basari. Yada gudun miji kuma. Ni kin ganni nan wlhy banda haƙuri”. Ya ALLAHU. Bakin Alhaji Balala ai duniya ne a wajen wuri, anya mutumin nan ya taɓa brush ko asuwaki a rayuwarsa. Kawai sai Hajiya Basariyya taji tana neman sumewa. Shi ko ango Alhaji Balala ko'a kwalar rigarsa, da yake ma bashi da man kai yana fassara yanayin nata ne da kunya. Bawan ALLAHn nan ya bari ko ƴar kazar aci ayi hirar baƙinta ina kawai ya mamuƙeta jiki na ɓari shi kawai angwanci zai yi. A wannan gaɓar roƙon ALLAH Hajiya Basariyya keyi da magiyar ya ɗauki ranta ta huta. Duk da tana da jiki itama amma ko rabin Alhaji Balala batai ba. Dan kuwa dai yafi ƙarfinta, haka kuma yayi amfani da ƙarfin ya turmushe uwar mutane, ƙanwar mutane kuma ƴar Kawu Manu. Nauyin da ƙirjin Hajiya Basariyya yayi yasa yanzu ma ta kasa yin kuka, har yay bidirinsa ya gama ya sauka a gadon bakinsa har kunne. Sai kuma yaja gyalenta ya ɗaure ƙugu yana tulewa a ƙasa yaja ledar namansa ya hau ci yana faɗin, “Kai kai kai Basari ALLAH yay miki albarka. Ai irinku ku ake kira da hurulanin duniya. Kinga taso kici naman nan karya huce amarya taso na samu na kammala abinda ya dace kafin alfijir waɗan nan jarabbbun matan da ƴaƴansu su hanani rawar gaban hantsi. Ai banyi ƙyan kai ba gaskiya, da nasan haka ne dana ajiye ki a ɓangarenki daban na saka ƙyaure yanda dan uban mutum dole su barni na shaƙata. Amma bari kiga gari na wayewa yanda kika san kajin bashi haka zasu ishemu da kaya-kaya gida da sai kace ana bikin suna mtsowww. Yoni ace tun farkon aurena irinki na samu banga abinda zai sa na ƙara aure ba. Wannan al'amari haka cakwai malam. Ai babu abin faɗa ga wannan miji naki sai ALLAH ya shi mishi albarka...” duk fa wannan surutu yana yi ne yana danna nama a baki. Kafin ya kai ƙarshen labaran nasa na rashin kangado yakai ƙarshen kajin biyu tas sai kasusuwa. Sai kuma ya hau salati da faɗin, “Oh ni Balala, kinga dai Basari na cinye miki kajin sayen bakin yo dama yunwa nake ji, matan nan najin haushi na yau babu wadda ta bani tuwo. Kinga taso ki suɗe ko ƙashin ne na miki alƙawarin gobe zan kawo wasu. Idan ma tsiren Hashibu kike so sai na haura gobe na sayo miki a Ingawa.” Ko motsi Hajiya Basariyya batayi ba, haka ya daddafa ya tashi da ƙyar yana tura ciki gaba ga hakki da nishi ya sake ɗare gado inda take. “Haba basariri na wai fushi kike na cinye kazar? Kwantar da hankalinki kinji ai nace zan sayo wata”. Yana maganar ne fa yana ƙoƙarin sake haike mata. Itako abinda ya tokare mata ƙirji ya hanata ko motsi. Haka ya sake bidirinsa babu batun yin wanka ko yin alwala ma balle addu'ar kasancewa da iyali. Dama ɗazun baiyi ba. Kafin wayewar gari Hajiya Basariyya ta sake tabbatar da Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane. Daddy kawai take tunowa tana rusar kuka dayin dana sanin wautarta, bata taɓa sanin rabuwa da Daddy zai zame mata masifa da bala'in rayuwa ba irin yau. Sai yanzu nasihar Kawu Manu ta wancan karon ke dawo mata a rai da zuciya. Ashe gaskiya suke gaya mata ta dawo a hayyacinta kafin lokaci ya ƙure mata. Gashi ko ya ƙure matan, Daddy ya mata saki uku wani ƙaton banza ƙaton ƙauye ya aureta. Haka tasha kuka da rashin barci, ana kiran sallar farko ya tattara kayansa ya ɗauki butar ta ya fita. Daga haka bata sake jin ɗuriyarsa ba. Itama dai haka taje tayo wankan ranta duk tsantsamin banɗakin dana Alhaji Balala data kwana a ciki. Sai ko da tayi amai taji daɗi. Ai gidan Kawu Manu gidan ƴan gayu ne sosai, dan ko ina shafe yake da siminti sai wajen dabbobinsa kawai. Sannan banɗakinsu tsaff yake dan iya akwai tsafta. Balle ma basu da yaran da zasu ɓata musu. Bayan ta idar da salla barci ɓarawo ya ɗan saceta a wajen. Kawai zuwa can gari yayi shaaa sai taji kawai an faɗo mata ɗaki. Firgigit ta buɗe ido tana tashi. Wata busashiyar mata ce a kanta kayan jikinta idan wankewa za'ai saci omo jakka biyu. Tana wani yamutse-yamutse ta ce, “Sunana Deluwa, uwargidan Alhaji Balala. Munji shiru ne baki fito kin ɗora ɗumamen tuwo ba ga yaranmu sun fara kukan yunwa”.........✍️
To gafa Hajiya Deluwa uwargida ran gida ta iso jama'a 😂🤌. 197
........Mamaki ne ya nema kashe Hajiya Basariyya, yo gari fa bai gama wayewa ba ma. To wai ma ita da aka kawo jiya ake jiran ta fita ta saka ɗumamen tuwo ne komi ma. Maimakon tai magana sai ta zubawa matar ido kawai tana kallon ta, ALLAH tsabar ramarta tasan idan kamata zatai sai ta karyata. Yo ai tayi biyar ɗinta. Takaici ya hanata bata amsa ta maida kanta kawai ta sake kwanciya. Cike da rashin hankali matar ta ce, “Ikon ALLAH, yoke haka keyi ki shige da miji ɗakin tun farkon dare har ketowar alfijir amma ace ki fito kisa ma mutane abinci a wuta kiyi banza. Ke mu fa nan babu ruwanmu da wata ƴar masu kuɗi ko hajiyanci daka mace zamuyi wlhy. Idan Kinga bazaki iya ba ce ya sakeki kiyi gaba mu tafi nono fari a wajenmu. Aikin ɓur inji tusa. Kina son nuna birnancin naki miya hanaki zama gidan mijinki lafiya da kishiyoyi, su can sun rabu da alaƙaƙai munan kuma an kwaso an kawo mana. To wlhy mu basu bane ba bazamu ɗauka ba ehe. Garama ki shirya ki ɗaura ɗamarar zama gidan Alhaji Balele sai jaruman mata”. Ta wani buga labule ta fice abinta. Eh lallai yau kam Hajiya Basariyya taga mata, ashe Hajiya Yaya Sayyada ce, Asiya ko ai sai dai a kirata waliyya. Tofa, wai yanzu akan wannan kucakin mijin ake wannan tada jijiyar wuyan? To ita wlhy bataga mata ba anan. To jama'a shifa ƙauyen ma nada ƙauye, wannan ai sune asalin ƴan ƙauyen ga jahilci ga rashin sanin ciwon kai. Yo idan ƴan ƙauyen su Kawu Manu na kiran nan ƙauye sai taita mamaki, ashe-ashe sunada hujja. Babbar bala'i ALLAH ya jiƙan Hajiya Yaya da Asiya badan sun mutu ba. Tana a cikin wannan jimami sai ga Alhaji Balala da wani tsohon kofin silba da leda. A gabanta ya ajiye yana washe baki da faɗin, “Tashi amar sugun-sugun tashi na sayo miki shayi da burodi ne da ƙosai, har fa garin kawunki naje yanzu da safen nan nine ɗibar farko a tukunyar shayin nan. Sabi'u nasa ya kaini a mashin ai nasan kin kwana da yunwa bakici komai ba”. Gaba ɗaya maganarsa hawa mata kai yake yi, dan haka tace, “Nagode”. Daga haka taja bakinta tai shiru.....
😂🤌Gaskiya Basari kina cikin ƙaulani, nace dole na baku First night na Alhaji Balala da Basari bazanci amanarku ba😂 sai ku tabbatar kun min godiya da sanya albarka, dan bana son harkar shiru anan tom🤣😜.
__________★