Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 189

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 189

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 189: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 189. Canjawar Sageer a gidan ta saka…

3,051 words

Canjawar Sageer a gidan ta saka Huznah a matuƙar tashin hankali. Gaba ɗaya sai taji duniyar da komai basa mata daɗi. Babban tsoronta kada ya gayama Daddy abinda ke faruwa ma. Tana son yi masa magana amma tana jin tsoro dan yaƙi bata fuskar yin hakan. Zaman gidan ma kwana biyu ya rage yi, baya dawowa sai dare sosai, baya cin abincinta. Komai zai sayo ya ajiye kamar yanda ya saba amma ya barta da su. Daga sallar asuba idan ya fita baya dawowa sai sha ɗayan dare. Daga sannu idan tai masa ya amsa ciki-ciki baya ƙara kulata. Sai ta shiga wata irin rama. Idanunta kullum a kumbure alamar kuka. Ta tattara wayarta ma ta kai ɗankinsa ta ajiye duk dan ya gane ta haƙura da komai amma yaƙi kulatan dai. Hatta ɗansa da yake ƙulafuci da bama kulawa kwana biyun nan ko ɗaukarsa baya yi. Bata taɓa tunanin hakan zata kasance da ita akan Sageer ba. Rayuwa kenan, wannan shine ashe magabata ke cewa kayi hankali kafin duniya ya koya maka karatunta. To ita dai ta koya daga duniya a tsakanin nan kam. Karo na farko ta yanke shawarar tunkarar ƙanwarta Madeena da matsalarta. Bayan ta kammala gyara gidan dan yanzu kam zagewa take tayi ta shiga ɗakinsa, inda ta ajiye wayarta tana nan a wajen har yanzu bai taɓa ba tabbacin fushin yake da ita sosai. Ajiyar zuciya kawai ta sauke. Ta ɗakko wayar ta fito. Fodio na a falo kwance a ƴar katifarsa yana barci itama ta zauna a ƙasan. Wayar ta kunna, ta sayi kati a account ɗinta harna dubu biyu yanda zai isheta sannan tai kiran Madeena. Sai da ta kusa tsinkewa ta ɗaga, cikin muryar barci tace, “Aunty Huznah”. Murmushi Huznah tayi tausayin ƙannen nata na ƙara kamata, dubesu a gidan mahaifinsu babu cas babu as na wahala sai dai suci suyi barci a binsu, su suna ganin gata ne sai an kaika gidan wani ka gane ALLAH ɗaya ne. Cikin sauke ajiyar zuciya ta katse tunanin nata da faɗin, “Madeena har yanzu baki ma tashi ba?”. Miƙa Madeena tayi tana tashi zaune da ɗan jan tsaki, ta ce, “Wlhy jiya ban kwanta da wuri bane ba. Fatan dai lafiya kema kira da safen nan ina Daddyn mu?”. “Gashi yana barci, magana na kira muyi Madeena. Dan haka ina son ya kasance ke kaɗai ce a wajen”. “Babu damuwa ni kaɗaice a ɗaki na kuma kulle ina jinki.” Komai Huznah bata ɓoyema ƙanwar tata ba saboda akwai shaƙuwa sosai a tsakaninsu. Babu abinda Madeena ke nanatawa sai kalmar innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Kafin tace, “Amma wlhy ban san har yanzu baki da wayo ba Aunty Huznah. Yanzu dan ALLAH dama baki cire tunanin bawan ALLAHn nan a zuciyarki ba har yanzu. Haba aunty Huznah haba dai kamar wadda bata da ilimin addini. Ki daina biyema Ummi fa wlhy kina dai ganin yanda ta kasance mata. Jiya Uncle ke gaya min wai tayi aure a ƙauyen gaba da su Kawu Manu.....” “Aure kuma?”. “Eh wlhy, yo in ba ƙauyen ba wazai yarda ya auri Ummi da wannan halin nata. Ai taima mutun nasiha da nuna masa gaskiya amma ya dinga rufe ido yaƙi fahimta. To wlhy ki dawo hayyacinki kar ki zama mai irin wannan halin. Aunty Huznah ALLAH ya miki gata, ya baki miji mai sonki da kula dake, kalla yanda yake rawar jikin kiyaye dukkan haƙƙokinki, wlhy ɗan zaman da mukayi haihuwar fodio bakiji yanda zamanku ya birgeni ba, sai naji ina addu'a ALLAH ya bani miji ko bai kai Yaya Sageer ba. Dan ba auren mai dukiya bane ke nuna ka more aure, masu auren masu kuɗin nawa ne a cikin bala'i da masifar rayuwa, mazan ma basu da lokacin su kullum suna yawon ƙasashe, kuma bazasu iya tsare rayuwarsu ba sai sunbi wasu matan. Wanda kuma ke ma yawo a iya Nigeria ko Africa shima zaki samu ƙalilan ne masu iya riƙe kan nasu. Gamu nan an ce mu fito da mazan aure munma samarin magana duk sun tarwatse kamar anyi ruwa an ɗauke, ka rasa ubami ke kawosu gunka da idan ba auren ba. Amma ke kin samu mai tattalin rayuwarki mai sonki kina wasa da damarki kuma akan haramun ma son wani a gidan aurenki. Haba aunty Huznah ni wlhy duk sai ma kika bani kunya, nazata ai a wuce wajen zuwa yanzu. Ni dai shawarar dazan baki ki koma ga ALLAH, ki koma gayama UBANGIJI kukanki ki shirya tsarkake zuciyarki da rayuwar aurenki ALLAH zai dafa miki ya cire miki Yaya AA a zuciyarki, ya kuma saka miki son mijinki. Shi yana can yana farin ciki da matarsa, Maanal gashi har ta haihu jiya twin's ke kina nan kina ɓata ƙyaƙyƙyawar rayuwar da ALLAH ya baki. Kiyi ƙoƙari ki bama Yaya Sageer haƙuri ki nema yafiyarsa, dan wlhy ko Yaya Yazeed kika bari ya gayawa sai ya ɓata miki rai balle Daddy. Ki cire ZUCIYARKI daga wannan AJIYA A DUHUN ki maidata cikin haske ALLAHU zai haskaka ki ya haskaka rayuwar aurenki ya haskaka jikinki da zuri'ar da kuka fara tarawa...” Sosai Huznah ta sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi, “Nagode sosai Madeena, Nagode da tunarwarki, wlhy wani lokacin rashin mai gayawa mutum gaskiya shike sake dulmiye tunainsa a wahalar rayuwa. Na jima da son jin ina son na cire soyayyar AA Darma a raina amma na rasa tayaya zanyi hakan, ta ina ma zan fara. Amma yanzu kam kin haska min hanya, kin cireni daga duhun dana shiga nakai zuciyata AJIYA A DUHU. In sha ALLAHU zan dage da addu'a, dan wlhy nima nasan na fara son Yaya Sageer, amma wancan ke danne zuciyata. Amma ina sha ALLAHU zan canja, zan canja daga waccan Huznah fandararriyar zuwa Huznah nagartacciya jinin Usman Chalawa.” “ALLAH ya tabbatar Aunty Huznah ki daina kuka. Nima zan tayaki da addu'a kuma zan saka a islamiyya a tayaki a kuma yi miki saukar Alkur'ani. Amma kema ki dage da addu'a jarabawace in sha ALLAHU zaki cinyeta. Nima zan kira Yaya Sageer na bashi haƙuri ”. “Nagode Madeena idan kikai min hakan kin taimakeni ƴar uwa ta. Ngd sosai. In ce dai baku da wata matsala?”. “Wlhy Alhmdllh babu matsalar komai, Mamma da Ammie na iya ƙoƙarin su a kammu, hakama Yaya Yazeed. Shima Daddy, Dan yanzu haka ma ni na dawo sashen Ammie ne”. “ALLAH sarki ALLAH ya saka musu da alkairi. Amma da Ummi tasa muyita zaginsu da kallonsu mugaye, gashi yanzu bata kusa kuma sun riƙeku da zuciya ɗaya. ALLAH yasa wannan auren ya zame mata izina itama ta canja”. “To amin”. Sun jima suna hira da tattauna abubuwa akan mahaifiyarsu kafin sukai sallama. Sai Huznah taji nauyin zuciyarta ya ragu sosai sai sauke ajiyar zuciya take yi.......

_______★

Anan gidan Darma kuwa tunda labarin haihuwar Maanal yazo musu tsakanin Saheeba, Nuratu, Mamy babu wanda baiji tashin hankali, baƙin ciki da hassada ba. Dan Mamy batayi kwanan gida ba a daren jiya sai asibiti. Sosai abu ya birkita mata zuciya sai aman jini. Haka aka kwasheta dan ALLAH ma yaso Aunty tazo Abujan ne jiya da safe, kamar yanda ta saba zatai kwana biyu ya koma. Sai kuma ga wannan al'amari dan AA da kansa yay kiran aunty ya sanar mata. Da yake kuma tana da babbar waya ya tura mata hoton yaran. Anan ne fa take nunama Mamy, su kuma su Saheeba a media suka gani. Kawai Mamy na ganin hoton yara ta fara jan numfashi da ƙyar, abu kamar wasa tari ya sarƙeta sai ga aman jini. Ba Aunty kawai ba shi kansa RK da aunty taima bayanin komai mamakin baƙin zuciyar matar nan yake yi. Ya tabbata wlhy itace zata kashe kanta da kanta. Yanzu idan dukkan abinda ya faru bai zame mata izna ta koma ga ALLAH tana neman tuba da roƙon gafarar duk wanda ta zalunta ba mi kuma take buƙata? To lallai kuwa aiki ya ganta. An tsayar da aman jinin nata da ƙyar kuma sai ga sabuwar magana a gwajin da akai mata na jini dan doctor dake dubata yace a gwada ko akwai maleria a tare da ita. Sai kuma sakamako ya nuna akwai ciwon HIV...........✍️

Tirƙashi, wasu na murnar haihuwa. Wasu na kukan kabari ya tunkarosu. Wannan fa itace ainahin duniyar mutane na😩😩.198

........Ba ƙaramin tashin hankalin RK yayi ba da bayanin likitan, cikin rashin yarda ya ce, “Dr. Hamaad, how could you say that? She's my family. I can't believe this! This can't be true. Ta ina zata samo wani HIV?”. “I'm sorry Sir, shiyasa na fara samunka da maganar dan nima abin ya taɓani sosai.” “No, I think it's the machines namu na lab na buƙatar canjawa. Amma kaga muje zan duba da kaina”. Ba musu Dr Hamaad ya miƙe suka fita tare, dan shi dai bashi da haufi aikinsa nakan dai-dai gaskiya. RK da kansa ya sake ɗibar jininta ya wuce lab ɗin. Anan ɗin ma komai da kansa yayi. Abin mamaki result ɗin ne dai irin na ɗazun yanzu ma ya fita. A rikice ya sake komawa ɗakin da Mamy take tare da Nurse, yawunta suka ɗiba, duk da a yanzu basa amfani da fitsari wajen gwajin HIV dan ya zama tsohon yayi haka yasa tayo fitsari. Nan ma aka sake gwajin yawu da fitsarin. HIV dai ta ƙara bayyana. Ya subahannallah mike shirin faruwa haka. Idan matar nan nada wannan ciwon a ina ta samu? Yayansa da Auntynsa kuma fa?. Karo na farko da a cikin aikinsa na likitanci ya ji abu mai girma da nauyi ya cushe nasa zuciya. A duk bibiyar Mamy da yake na tsawon shekaru da aƙalla yanzu akai huɗu bai taɓa kamata da sabga ta bin maza ba, wanda tayi kafin aurenta daban. A wannan gaɓar zai shedeta, bata bin malamai, bata bin maza. Tsantsar mugunta ce kawai a ranta da busashiyar zuciya. To a ina aka faɗi a ragaya kenan?. Kasa bayyana ma kowa wannan magana RK yayi, dan washe gari ma su Umma suka iso Abuja daga Kano ita da Gwaggo Khadijah. Sai ƴammatan family ɗin su biyar da masu aiki. Gidan Darma aka shiga gyarawa lungu da saƙo. Da yake Nibras na nan Umma tace ta gyaro ɗakin Yaya Fawzan, su Lailah kuma suka gyarama Najma nata. Itama Saheeba ta gyara na babban Yaya, nan ma su Lailah suka gyara na Ameerah. Sashen su Maanal babu kowa, aka gyara falon sama sai ƙasa zuwa bedrooms na ƙasa da kitchen. Sai bedroom ɗin dake sama babu kowa ciki aka fidda kayan ciki tas aka gyarashi ma yara, komai na ciki bibbiyu aka saka ɗakin yay masifar ƙyau, kai daka gani kasan kuɗi yayi aikinsa. Sashen Abah ma ko'ina an gyara banda bedroom ɗinsa. Oum kuwa ko'ina an gyara mata fes itama. An ma flowers ɗin gidan gyara zuwa garden sannan aka zuba decorating na tarbar baƙin duniya. Kai daka ga gidan kasan yasha gyara. Motoci kaf bola sai da ya gama wankesu aka maida kowacce muhallinta tunda masu ita zasu dawo. Duk wannan bidirin gyara da akeyi su Umma ne kawai ke abinsu. Amma karka tona zuciyar Saheeba, Nuratu, Nibras kaga yanda suke a ƙuntace. Kai dukansu babu wanda baiyi addu'a a zuciyarsa ALLAH yasa jirgin da zasu shigo yay haɗari ba tsabagen baƙar zuciyarsu. Oho su suka san sunayi, family na Darma basu san sunayi ba kam...

Kwanan su Umma uku a gidan aka sallamo Mamy, zuwa lokacin komai ya gama dai-daita a gidan. Sam bata so aka sallamota ba muguntar RK ce kawai, dan yace wlhy sai tazo ta zauna a gidan komai na shagalin suna so yake ayi akan idonta. Dan haka ma yasa aka sallameta akan doctor zai cigaba da zuwa gida dubata. Batun result na HIV kam bai gayama kowa ba ya adana ya ajiye har sai su Oum sun dawo suma ya musu gwaji. Kwana biyu da sallamo Mamy ahalin Darma suka fara isowa daga Kano, dan kuwa zuwa jibi ake saka ran saukar ƴan saudia suma. Babu kuma wanda ya leƙa Mamy a cikinsu har su Umma data samu a gidan. Washe gari Amaal ta iso itama, dole Shahidah da Aunty Sakeena, sai Salimar Hajiya Yaya suka dawo nan suma sashen Maanal, dan zuwa yamma ƴan Giro zasu iso suna hanya Daddy ya aika musu da mota ta ɗakkosu tunda basu halarci bikin ba ayi bikin suna da su. Harda Babu za'a taho dan zasu ƙara ganin likita shi da su Gwaggo dan haka har da su. Kai Harda Sule da Haƙila dake fama da ciki ta dage sai tazo itama. Da yake babu mai iya saka su ko hanasu dole aka barsu. Dole Amaal ce ta buɗe bedrooms ɗin su Maanal ta gyaro tsaff, babu wanda ya hau musu upstairs duk suna a ƙasa. Ƴan Giro dama gida Daddy ya bayar can za'a saukesu. Washe gari aka tashi da shirye-shiryen suna dana tarbar masu jego duk da dai ba gobe ne sunan ba....

_________★

Gaba ɗaya al'ummar Giro ruɗewa sukai da ganinsu a garin Abuja. Yo wannan al'amari haka kamar ba'a duniya ba. Basu ƙarasa zarewa ba sai da aka iso dasu masaukinsu. Gida ne dake da komai a ciki Daddy ya bayar aka saukesu. Ɓangaren mata da ban na mazan daban duk da mazan basu da yawa sosai duk yayun su Maanal ɗin ne ma sai wanda ke matsayin kawun nan su biyu. Sai Babu da Sule. Dukansu dai mazan su goma ne. Matan ne dai fa suna da yawa damma an hana zuwa da yara. Masu goyo ma in dai ba ƙaramin ɗane da kai sosai ba ance su barsu gida, tafiyar kwana uku dai ALLAH na tuba. Kuma dama dai masu tsara tafiyar sai da suka zaɓi waɗanda suka dace gudun zuwa a zubar da mutunci. Ammie da Hajiya Yaya da Nene suka tarbesu a gidan sun tarbesu da lafiyayyen abinci, dan girki akai musu sosai na gani na faɗa. Aifa ba wasa sukaci sukai nak, daga haka akai zaman gaishe-gaishe da barkar samun ƙaruwa. Duk da Sule yabi jama'a ya nuna musu hoton yara a waya da su Amaal suka tura masa haka Hajiya Yaya ta sake nuna musu. Aka kuma sanar musu sai gobe in sha ALLAHU mai jego zasu iso daga saudia. Jinjina kawuna suka dinga yi, kowa a ranta tana sake yarda Asiya da ƴaƴanta sun sami duniya. Yanzu haihuwar ma baza'ayi ba sai a wata ƙasa. Duk da dai dama sun san Maanal ɗin bata ƙasar tun dawowar su Giro. Hajiya Yaya ce kawai ta koma gida, amma Nene da Ammie anan zasu kwana tare da su. Sailu da Gwaggo abin duniya ya ishesu, duk sun tsangwami kansu, to dama babu mai shiga sabgarsu. Koda suka taho zuwa Abuja nan ma kowa ƙin zama yay a kusa da su doke sai a gaban mota aka haɗosu su biyu. Kai daka ga yanda suka rame suka bushe sunyi baƙi kasan babu lafiya. Garama ita Sailu an ɗorata a magani daman, Gwaggo ko sai yanzu za'ayi mata gwaji a tabbatar da HIV ɗin ko babu.. Haka suka dinga kukan zuci suna bin Ammie da kallo. Sun dai tabbatar da yanzun kam WITSIYAR RAƘUMI tayi nesa da ƙasa. Ammie ta zame musu RAINA KAMA KAGA GAYYA musamman ma Gwaggo. Yau babu Lubabatu da Umar data tsana a duniya ga ƴar Lubabatu da Umar ta zame mata ɗan hakkin daka raina......

_________★

A nan Saudia kam Maanal da twin's na samun dukkan kulawar data dace ta ɓangaren lafiya da na family, dole Oum da su Ameerah suka wuce Dubai a washe garin cs ɗin, dan lissafin ya canja, dukkan sayayyar da akai a baya ta yaro ɗaya ce. Yanzu kam dole a ƙara tunda ALLAH yay musu ƙyautar biyu. Anan kuma su Yaya Fawzan sunata haɗa abinda ya dace suma sun tura komai Nigeria, sai Abah da AA ne ke tare da Maanal da Babies duk da bama wani barinsu ake koda yaushe suna ganinsu ba sau ɗaya ne a rana. An bama Maanal isashen lokacin hutu ita da yaranta. Aiko tana shan barci sosai bana wasa ba, dan yunwa kawai ke tashinta hakama yaran da ake ba nn da ƙyar tana mita da shagwaɓar zafi-zafi. Wani lokacin dole Doctors ɗin ke neman taimakon AA idan za'a basu abincinsu. Sai ya zauna yana lallashinta da bata baki take haƙuri su sha yanda ya kamata. Gashi kuma Alhamdullah suna wadatuwa da abincinsu. Duk da ma AA ɗin tausayin Maanal yasa kai tsaye ya nema shawarar likitar akan haɗa musu da madara tace hakan yayi. Dan haka yaje ya kwaso irin wadda ta dace ana haɗa musu da ita. Da rana kawai suke shan nn, da dare kuma madara dan ta samu tayi barci ta huta itama. Aiko tsarin yayi, da alama hakan kuma zai tafiyar da tarbiyyar yaran akan cin abincin dare dake jikin mahaifiyarsu. Maanal nada jiki mai ƙyau, a kwana shida kacal abubuwa suka fara daidaita mata sai dai abinda ba'a rasa ba dan cs ba'a rabashi da tsarabe-tsarabe a jikin wanda akaimawa. Kawai dai wanda basu gane bane suke ɗauka cs yafi haihuwa sauƙi. A kwana na tara suka bata sallama, a kuma ranar su Oum suka dawo saudia, dukan sayayyarsu sun turata gida Nigeria. Babu zama suka fara shirin wucewa suma washe gari dan dangi sun ƙosa su koma. Suma dai a ƙage suke da komawa ƙasar haihuwarsu haka nan musamman Abah da Oum dake neman watanni bakwai. Alhamdullahi a yau da Maanal ke cika kwanaki goma ciff da ciro mata kyawawan yaranta jinin Darma da kallo ɗaya zaka shaida haka babu tambaya suka iso gida Nigeria. A mamakinsu sun sami zuri'ar Darma dana Chalawa cike da airport sun zo tarbarsu. Babies na hannun Babban Yaya da Yaya Fawzan, AA angon ƙarni na riƙe da Bestynsa. Yayi ƙyau cikin ƙananan kayansa na fama, itako tana sanye da Abaya ƙirar Egypt kalar oxblood datai mata masifar ƙyau, dan jegon ya sakata zama wata shar da ita. Kumburin nan da tayi duk ya saɓe sai wani uban haske da glowing fatanta keyi like wata laɓuɓuwa can. Bata wankan jego ba wani shan kunu da su miye-miye namu na gargajiya tsabar kulawar data samu a asibitin ce da abincin da suka tsara mata tana ci ne da nutsuwa waje ɗaya, ga isashen barci babu wata hayaniyar ƴan barka ta sakata komawa hakan. Ƙanshi kam da Oum ke dafata da shi ya zauna ɗaram kamar ba maijego ba ya subahannallah........✍️

199

Readers Also Read