Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 26
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 26: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 26. Wanka yake son shiga yayi, sai dai haka…
3,343 words
Wanka yake son shiga yayi, sai dai haka kawai ya samu kansa da tsayawa jikin window ɗin falonsa ya zubama harabar gidan ido ko nace flat ɗin Oum. Shi kansa bai san ma'anar tsaiwar tashi ba, amma ya cigaba da tsayawar. Hannunsa ɗaya a aljihu ɗayan kuma yana faman ɗagosa ya kalla agogo alamar duba mintuna. Mintuna ashirin ya ɗauka cif a wajen kafin abinda zuciyarsa ke jiran gani duk da yana faman ƙaryata hakan su fito. RK ne gaba Maanal a bayansa, sai dai suna gama fitowa RK ɗin ya dai-daita tafiyar tasu kafaɗa da kafaɗa, tare da ɗan ranƙwafowa gefen Maanal yana magana fuskarsa da wadataccen murmushi hannayensa duk biyu goye a bayansa. Gani yay Maanal ɗin ta tsaya cak, tare da hararar RK ɗin, amma shi sai hararar ta juye masa zuwa kallon soyayya ne, musamman daya ga yanda RK ɗin yay wata irin dariya cike da nishaɗi yana kuma maganar da shi sam baya iya jiyowa daga nan. Da ƙarfi ya rumtse idanunsa tare da datse laɓɓansa da haƙori tamkar zai hudashi. Haka yake idan har abu zai ɓata masa rai ko zaiyi magana yanada ɗabi'ar rufe idanu. Kamar wanda aka zabura ya wani irin buɗe idanun tare da fara takawa cike da nitsuwa da ƙasaitarsa yayo waje. Kai tsaye sashen gaban Oum ya nufa tamkar wanda ake ingizawa, dai-dai nan motar RK ta gama ficewa a gidan, yayinda Maanal dake tsaye har yanzu ta yunƙura zata koma sashen Oum ɗin tana sauke ajiyar zuciya. Haka kawai yau kuma sai abubuwan RK ɗin ke mata tasiri a zuciya. Duk da dai tasan a tsakanin nan tabbas bata jin zafinsa kamar sanda suna a Jos. Da sauri taja da baya tare da tsayawa cak ganin mutum a gabanta gingirin. Sai a lokacin ni'imtaccen ƙamshin turarensa ya wani bulala mata cikin hanci saboda yanda iska ta kaɗo mata shi sosai. Ɗan lumshe idanunta dake a cikin gilashi tayi sai kuma ta buɗe a lokaci guda tana ƙoƙarin daidaita kanta. A dakenta, a kuma nutsenta ta ɗago manyan idanuntan ta sauke akan ƙyaƙyƙyawar fuskarsa dake a tsuke, sai dai tsukewar tata bai hana kwarjininsa da mutumtaka da gizagonsa bayyana ba. Shima idanun nasa dake cikin fari tas ɗin eyeglasses ɗinsa dake matuƙar sake ƙawata fuskarsa da gwarzantashi akanta suke. Hakan yasa suka zubama juna ido, kallo irin na tsakkiyar idanun nan. Sai dai sam Maanal bazata iya jurewa ba, dan haka ta janye nata a hankali tare da rissinar da kanta. Cikin sabon yanayinta dake baƙanta masa zuciya da ƙona masa ita ta furta, “Kayi haƙuri sir, ban san kataho bane”. Tai maganar ƙasa-ƙasa da ƴar muryarta mai zurfi tana sake jan jikinta baya, tare da raɓawa ta gefensa zata zagayesa ta wuce.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖3️⃣7️⃣
______________
https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871
__________
........Babu shiri taja ta tsaya cak, sakamakon jin an cafke tsintsiyar hannunta. Idanunta ta lumshe da ƙarfi sosai, zuciyarta na wani irin mahaukacin bugawa tamkar zata faso ƙirjinta ta fito. Sai dai me wannan Maanal ɗin ba Little Maanal bace ta shekarun baya. Wannan Maanal ce, Maanal cikakkiya ɗiyar Ammien ta. Wadda taga jiya taga yau take kuma fata da ganin gobe. Maanal ɗin data iya ɗauka da shanye abubuwa masu nauyin gaske da ko namiji sai jarumine zai iya zama irinta. Tuni ta saita kanta cikin dakiya da jarumta. Batare da ta juyo ko yin magana ba tai ƙoƙarin fisgar hannun nata. Sai dai me wannan rikon bana rago bane, ba kuma na sakaran namiji bane. Dan riƙone akai mata irin na manyan sadaukai. Ta fahimci hakan ta yanda koda ta fisgi hannun nata duk da da ƙarfi tayi shima bai ko motsa daga yanda yake ba, bai kuma juyo ya kalleta ba balle yin magana. Sosai zuciyarta ta fara hasala, hasala irin wadda har take jin ɗacinta a maƙoshi. Cikin bayyanar ɗacin a harshenta ta furta, “Minene ma'anar hakan da kake yi?”. Idan ginin gidan ya tanka shima zai tanka kenan, maimakon yin maganar ma sai fisgarta yay da ƙarfi yay sashensa da ita. Tana ƙoƙarin tirjewa amma hakan bamai yiwuwa bane gareta. A haka ya bugi ƙofar sashen nasa da ƙafa tare da tura kai ciki. Da wani kalar salo ya jefa Maanal saman lallausar kujerar falon, kafin tai wani yunƙuri ya rufu a kanta ta hanyar ɗaura ƙafarsa ɗaya a kujerar ya dogare, ɗayar na a ƙasa. Wani irin matsewa da matuƙar takura Maanal taji da tsaiwar tasa a haka, tuni jarumtar tata ke neman suɓucewa, dan yanayin neman tuno mata da babban al'amarin daya shuɗe yake a rayuwarsu ta baya amma tana fisgo dakiyarta da tsiya-tsiya. Komai ta haɗiye daga fuskarta da harshenta idanunta a rissine dan bazata iya kallonsa ba ta furta, “Sir minene kake yi haka ne?......” “Oh you're still pretending?”. Ya faɗa cikin wani irin kaushi da ɗacin murya mai razanarwa. Dan ita kanta Maanal ɗin sai da taji kayan cikinta sun kaɗa. Amma da yake itama yanzu gwanarce. Ta karantu daga kowanne irin salo da taku sai ta zuba masa idanunta, wani shegen murmushi mai saka yin kamar zaka lumshe idanu ta sakar masa. A nutsenta tana mai sake tsatstsaresa da idanu ta ce, “Pretending?! Dan mi zanyi pretending? Akan me kuma? Yallaɓai”. Wani kalar taune laɓɓansa yay da rufe idanu yana dunƙule hannunsa. Kamar zai kai mata duka sai kuma miya tuna ya fasa. A maimakon hakan sai ya nunata da yatsansa manuniya. “Na fiki zafin kai”. Yanda yay furucin yana wani wara mata manyan oily fararen ayes ɗinsa masu girma da cikar gashi dake cikin gilashi sai ta sake jin tsoro na mamayeta. Amma dai tai ƙoƙarin sake dakewa yanzu ma ta taɓe bakinta ta dauke kanta kawai. Cikin ƙunƙuni ta ce, “Ina ruwana to da zafin kan naka”. Hannu ya kai zai cafko fuskar tata, a zabure ta matsar da jikinta tayi ta gefen daya ajiye ƙafarsa, dan gaba ɗaya ji take kamar an sakata a wani kurkuku dama. Hatta da iska bata shaƙa yanda ya kamata saboda kusancin nasu. Haka ta miƙe ta nufi hanyar fita cikin sassarfa. Wani irin juyowa yay tare da sanya mata ƙafa sai gata a saman kujerar ta sake zubewa. Hannayensa duka ya zuba a cikin aljihun wandonsa yay wani irin tsaya mata bisa kai ya zuba mata idanun sa tamkar zai haɗiyeta da su. “Ni kike ma ƙunƙuni?”. Baki ta ɗan tura gaba, sai kuma ta kauda kai gefe, “Ni yaushe na maka ƙunƙuni?”. Ƙwafa yayi cike da sake ƙuluwa, cikin kakkausan lafazin da bata san ya iya ba ya furta, “Na baki nan da kwanaki uku kacal ki fito ki faɗama Rafeeq gaskiya. Idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki”. A karo na farko ta zuba masa wani irin kallo tana miƙewa akan ƙafafunta, a gabansa ta tsaya sunama juna kallon ido cikin ido, cikin kausasa masa harshen itama ta ce, “Oh mamaki? Ai ba yau na fara shan mamaki daga gareka ba daman. Gaskiya kuma bismillah ai ban hanaka sanar masaba kai, maza sanar masa kafin iska ta rigaka. Ina dai iyaka yace ya janye daga aurena ko, sai me? Nace sai me idan yayi hakan? Ko hakan sabon abu ne daga cikin rayuwata balle ya daman. Ba shi kaɗai ne namiji ba, dubu bayansa biye suke dani kuma in har na basu dama tamkar ƙyaftawar ido zasu amsa da rawar jiki har suna shelantama duniya samuna cike da murna da farin ciki. Balle nayi imanin ko ƴaƴa goma na haifa a duniya Rafeeq zai amsheni ni da su da hannu biyu ya godema ALLAH saboda soyayyar da yake min ta dabance, SO na yake, tsananin SO da wani mahaluki baitaɓa min kwatankwancinsa ba a wannan duniyar.....” “Ƙarya kike yi!!! I said you are lying!!!!!”. Ya faɗa cikin wani irin ƙaraji idanunsa da suka kaɗa jazur na firfitowa tamkar zai mareta. Matuƙar tsorata tayi, dan ta gama yarda marin nata zai yi kawai, sai da taji shiru sannan ta buɗe idanunta data rumtse. Suma sun kaɗa sunyi jazur kamar nashi. Cikin dakiya da sake tsatstsaresa da idanun ta ce, “Kai ka ɗauka ƙaryar ne, amma ni da yake nunama soyayyar zan bada labari. Zan kuma tabbatar maka da hakan nan da ƙanƙanin lokaci. Wata ɗaya kacal zuwa biyu zan zama MATARSA, MALLAKINSA ta har ABADA in sha ALLAHU”. Ta raɓashi tai wucewarta fuuuu. Baiyi wani yunƙurin dakatar da ita ba a yanzu, dan bai ma motsa daga yanda yake tsayen ba harta gama ficewa. Sai lokacin yay wani irin kai hannu ya hankaɗar da flower base ɗin dake ata bayan kujerar mai tsananin ƙyau da ƙayatarwa. Jikake tatsatsa ya tarwatse a ƙasa komai ya zama pieces. “I will teach you lesson”. Ya faɗa da tsananin kaushin murya dake bayyana dukkan fushinsa. Daga haka ya juya zuwa cikin bedroom ɗinsa. Kayan jikinsa ya fara zarewa kawai yana wulli da su, kafin ya wuce cikin closet ɗinsa ya ratsa ya shige bathroom. Ƙaton gaske ne shima. An kuma tsarashi da kayayyakin toilet masu ƙawa tamkar ba banɗaki ba. Ƙarƙashin shower yaje kawai ya buɗe duka ukun ruwa suka fara saukar masa a jiki shaaaaa!! Tamkar irin ruwan samar nan mai zuwa babu zato. Hannayensa kawai ya dafe a jikin glass ɗin da aka zagaye wajen wankan da shi ruwan na cigaba da saukar masa. Yafi mintuna talatin a haka dan har numfashinsa ya fara fisga alamar ruwan ya masa yawa sannan ya kashe, a haka ya cigaba da tsaiwar ruwan daya saukar masa na kwararewa musamman na cikin sumarsa dake lashe kuɗaɗe da shi kansa bai san adadi ba. Ada shi ba ma'abocin tara suma bane, amma wasu dalilai suka sakashi fara tarawar harta zama ɗabi'arsa. Ba tara sumar kawai ba, abubuwa da yawa ya ɗabi'antu da su ne daga baya bisa wasu dalilai. Kuma a yanzu sun zama halittarsa kuma jinin jikinsa da shi kansa bai taɓa tunanin raba kansa da su ɗin ba... Ya jima a hakan, dan sai da zuciyarsa ta koma ta kwanta cikin ƙirjinsa luf kafin yayi wanka kamar yanda ya saba da brush ya fito, idanun nan sunyi matuƙar juyewa da komawa jajaye. Gaban mirror ya tsaya yana goge jikinsa, kafin ya shafa mansa mara hayaniya ya feshe jikinsa da sprys ɗinsa masu ƙamshin tsiya da saka zuciya nutsuwa. Ya kuma gyara kansa da kwantaccen gashin dake lafe a kumatunsa, ya sama bakinsa ƙamshi. Tausasan kayan barci farare tas ya sanya, ya sake feshe jikinsa da turarurrukansa na barci tamkar ba kwanciya zaiyi ba sannan ya nufi katafaren bed ɗinsa dake a wani kalar dunƙule waje guda tamkar zero. Zama yay ya jingina da gadon tare da kai hannu ya rage fitulun ɗakin ya maida mai duhun haske sai bed side lamp kawai dake kunne itama ta gefensa. Sai da yaja lallausan duvet ɗinsa ya rufe ƙafafunsa zuwa ƙugu sannan ya ɗauki eyeglasses ɗinsa dake ajiye kusa da novel ɗinsa dake a bed side drawer ɗin ya saka, novel ɗin shima ya ɗauka. Alamar daya saka a inda ya tsaya ya sashi buɗewa kai tsaye ya fara karatu cike da son kauda komai dake cinkushe da zuciyarsa.....
___________★
Kamar yanda ta saba damunsa a kowanne dare da sakwanni yau ma tsaf ta kammala shirin barcinta ta faɗa saman gado. Jinta take wani free yau ita kaɗai a ɗaki babu Maanal. Sai hakan ke sakata nishaɗi tun ɗazun. Yayinda tuni ta kaima uwarta gulmar fitar Maanal ɗin da saurayi da rashin dawowar tata. Nan sukasha gulmarsu da aibanta Maanal ɗin wai tana can an kaita hotel yawon fasiƙanci dai aka fake fa dubiya. Bayan sun kammala wayar ne tai abubuwan da malam ya bata tai shirin barci shine ta ɗauki waya. Kai tsaye data ɗin ta ta buɗe. First WhatsApp ta fara shiga, duk da ta fahimci kamar bai cika damuwa da WhatsApp ɗin ba sam. Amma tanan take saurin gane idan yana online. Koda yake da wahala ma kaga ya kashe data shi kam. Yanzun ma dai kamar yanda tai fata yana online ɗin, cike da farin ciki ta tura masa sallama da gaisuwa kamar yanda ta wajabtama kanta a yanzu. Ganin fin minti biyar babu amsa ta shiga masa WhatsApp call. Amma har ya kashe ba'a amsata ba. Fita tai ta koma ta tura masa ainahin massege, nan ma mintuna biyar shiru. Sai tai direct call kawai tana fatan ya ɗauka koda bazai ce mata komai ɗin ba kamar yanda ya yi mata. Dan data taki sa'a ya ɗauka har sau kusan uku data kira shi, sai dai daga sallama da amsa mata gaisuwa a cinkushe baya sake cewa komai zai barta taita surutunta harna tsahon mintinan data fahimci batasu yake daga haka a takaice yace goodnight ya yanke wayarsa. Kota sake kira kuma bazai amsa ba. Sau biyu yana mata haka, sakamakon roƙon wannan alfarmar datai a garesa jiya data bisa office, a lokacin bai tanka mata ba, amma data kira ɗin bayan ya gama bata wahala sai ya amsata a jiyan, hakama yau da safe. Shine ta samu hope ɗin sake kiransa yanzu ma da fatan ya ɗaga ɗin dan tanada yaƙinin aikin malam ya fara karɓuwa. A wajen bikin Yaseerah ko kallo bata ishesaba fa, amma a wannan karon gashi ya kulata har a office data samesa ya kuma bada mota aka maidata gida, ai dole tace aikin malam yayi. A kasalance ta ajiye wayar ganin kira har uku babu amsa, amma sai zuciyarta sam bata gajiyaba, har yanzu tana jin zalama da fatan ya amsa ɗin. Sake tura masa text massage tayi har uku na roƙon ya ɗaga kiran, ta watsap ɗin ma ta tura masa, sannan ta sake kira. Sai dai yanzun ma babu alamar zai ɗaga mata. Idanunta na zubar da hawaye ta tura masa tsararren sabon saƙo masu kalamai masu armashi da kashe zuciya sannan ta kwanta badan taso hakan ba. Ta jima batai barci ba hawaye na bin fuskarta. Ita kanta bata san irin son da takema bawan ALLAHn nan ba. Amma tabbas mai zafi ne. Matuƙar zafin da ta tattabar idan bata mallakesa a matsayin miji ba akwai ƙura......
___________★
Maanal bata koma sashen Oum ba sai da ta tabbatar ta daidaita kanta da nutsuwarta a waje. Dan sai da tasha kukanta sannan ta share hawayenta tsaf ta koma sashen Oum ɗin. A falo ta sameta mai aikinta na kwashe su Barrah da sukai barci za'a kaisu ɗaki ai musu shirin barci kamar yanda taji Oum ɗin na bada umarni. Komai batace ba, sai zama tai tana murmushi da faɗin, “Oum duk munzo mun sakaki wahala”. Harararta Oum tayi cikin sigar wasa. “Oh haka kike ɗauka shiyyasa kika kasa sakin jiki dani. Gaba ɗaya kamar ba Lillyn babban yaya ba, kamar ba Autar Oum ba, kamar ba Bestien Auta ba. Maanal kin canja min, matuƙar canjawa da mamakin hakan ya kasa barina”. Kai kawai Maanal ta duƙar tana murmushinta mai sanyi, sai kuma ta furta, “Nama manta banga Babban Yaya da matarsa da Mamy da Abbah ba?”. “Uhm sai yanzu kika tuna da su? To suna nan abinsu. Mamy tana tare da Abbanku ne a ƙasar Oman, Amma ina ƙyautata zaton nan da kwana biyu suna hanya insha ALLAHU. Babban yaya kuma da matarsa da matar Fawzan da yara suna Kano ana bikin ƴar ƙanwar Mamy ɗin ne kin san kuma itama Saheeba kamar ƙanwa ce a wajenta. Shine matar Fawzan ta mata rakkiya shima yau Babban yaya ya wuce da yammar nan dan yana fita kuna shigowa. Ɗaurin auren safe ne shiyyasa yaje ya kwana sai ya dawo goben idan ALLAH ya kaimu. Su kuma sai biki ya tashi, Fawzan da Auta aiki ya hanasu zuwa, ni kuma jikin nawa ne sai a hankali” Cikin gamsuwa Maanal ta jinjina mata kai batare data sake cewa komai ba, sai dai tayi mata addu'ar lafiya mai dorewa. Daga haka itama Oum ɗin ta zuba mata ido kawai. Sai kuma zuwa can ta katse shirun nasu da faɗin, “Rafeeq ɗin ya wuce kenan?”. Batare data ɗago ba ta ce, “Eh wai ana jiransa a asibiti ne”. “Uhm ai ya riga da ya ɗaurama kansa irin aikin Papa. Gashi nan gaba ɗaya nauyin ya koma kansa yanzu, dan ma Papan na ƙoƙarin rage masa wasu abubuwanne. Mu kuma so muke shi ya huta saboda tsufa, dan ma ALLAH ya bashi jiki mai ƙyau ne da kuma zuciyar taimakon al'ummar. Tun yaushe kuke tare da Rafeeq Maanal?”. Matuƙar dukan zuciyarta tambayar tai, dan har sai da ta motsa mata a cikin ƙirji, maƙoshinta ya ɗan bushe saida ta haɗiyi yawu da ƙyar. Yanzun ma bata ɗago ba kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta bama Oum ɗin amsa cikin Muryar tan nan ƙasa-ƙasa. “Shekara ɗaya kenan Oum, a Jos inda nayi sarvese”. “Oh iko ALLAH, dama kece yaketa bani labarin ya samu a Jos ashe. ALLAH mai girma kenan. Ya jima yana faɗa mana ni da Majdiya, sai dai bamu maida hankali ba saboda sanin halinsa sarai. An jima ana fama da shi akan aure yana botsarewa da faɗin shi baiga wadda tai masa ba. Har Papa ya fusata zai haɗashi da wata yarinyar abokinsa sai gashi da zancen ki. Amma sai babu wanda ya ɗauka serious ne. Ko kwanciyar asibitin nan naƙi zuwa ne saboda ban wani yarda da gasken yake ba duk da Majdiya ta sake tabbatar min. Ashe nayi sake da tuni naga ɗiyata da ƴar uwata. Nayi kewar Asiya matuƙa Maanal. Haka ke da su Amaal, idan na tunaku a raina har hawaye nake wani lokacin. Bana fatan ALLAH ya sake maimaita min abinda ya faru a baya”. Hawayen da suka cika idonta suka gangaro. Hannu tasa ta sharesu da sauri tana murmushi mai ciwo. Sai kuma ta miƙe tana faɗin, “Kinga tashi muje kiyi shirin barci ki kwanta. Dan Rafeeq ya jaddada min ki kwanta da wuri”. Ta ƙare maganar tana ƴar dariya da kama hannun Maanal ɗin da jikinta yay wani kalar sanyi ƙalau.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖3️⃣8️⃣
______________