Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 27

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 27

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 27: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 27.…

3,149 words

_________

........A haɗaɗɗen bayin Oum Maanal tayi wanka. Ita dai sai bin ko'ina take da kallo. Tun can baya tasan su Oum nada kuɗi, amma komai nasu ya sake canjawa daga sanin datai masan. Ita kanta Oum ɗin ta sake gogewa ko tsufa batayi. Da waɗan nan tune-tunen ta fito a wankan. Rigar wanka ce dan haka bata ɗan ji takura ba sosai, koda yake Oum bata cikin mutanen daya kamata acema tana jin kunya, to mi zata ɓoye mata, matar da tun bata san kanta ba take mata wanka harda goyo. Tasha kwana a gadon Oum daga ita sai pant. Oum da Bestyn ta ne suka fara sanin jinin haila yazo mata. Kalmar (Besty) ta sake maimaita kanta a cikin zuciyarta, sai kawai taji zuciyar tata ta mata nauyi. Ture tunanin tayi da ƙarfi ta maida hankalinta ga bin ɗakin da kallo. Oum ta fita, sai kaya da aka ajiye a saman gado. Kayan ta matsa ta ɗaga. Wando da riga ne na barci, sunada yalwar da bazasu matseta ba ko kaɗan. Bata wani ɓata lokaci ba ta sanya, tana gama sanyawa Oum ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da wani ɗan basket mai ƙyau golden. A gefen Maanal ta ajiye, Maanal ta kalleta tana mata sannu sannan ta kalla kayan. Mayukane da zasuyi dai-dai da fatarta, ba daidai da fatarta kawai ba ta jima da saninsu, dan dasu take amfani ada, bayan ita kuma mutum ɗaya tasan yana amfani da su a gidan.... Kamar Oum tasan mi take tunanin ta katseta da faɗin, “Nasan nawa bazasu ma skin ɗinki ba. Shiyyasa na kira Auta ya kawo miki nasa dan nasan fatanku yana ɗaukar mai iri ɗaya ne, sai kuma akai sa'a irin wanda ma kike amfani da su ne. Maza ki shafa kada jikinki ya bushe bara nima nai wankan”. Daga haka Oum ɗin ta miƙe batare da ta jira cewarta ba. Maanal ta jima bata motsa ba idanunta akan kayan shafar, wani abu ne mai nauyi ke tsikarar mata zuciya. Yayinda tunaninta ke kai kawo da tambayar kanta miyyasa ya cigaba da amfani da irin manta? Miyyasa wasu abubuwa nashi har yanzu suna a yanda ta sansu, waɗansu kuma a baya suke yawan faɗa akan tana so yayi su yaƙi yi. Amma a yanzu duk sai taga yana yin su..... Knocking ƙofar da akayi ya sata ture tunaninta gefe ta kalla ƙofar, jin an ƙara na biyu yasa ta miƙewa ta ɗan gyarama su Barrah bargo sannan ta nufi ƙofar, duk zatonta cikin masu aikin Oum ne. Sai dai tana buɗewa taci karo da abinda bashi tai zato ba. Muƙut ta maida abinda tai niyyar faɗa ta haɗiye abinta tare da janye idanunta daga kansa taja jikinta baya ta koma tai zamanta a inda ta taso. Sai lokacin ya ƙarasa shigowa ɗakin hannayensa duka biyu zube cikin farin wandon kayan barcin sa. Tafiya yake cike da ƙasaita, ga mayataccen ƙamshinsa duk ya rikita ɗakin. Baiko kalleta ba ya wuce closet ɗin Oum kansa tsaye kuma hankalinsa kwance. Ƙasa-ƙasa Maanal ta bisa da kallo, tana mamakin mi kuma ya kawo shi yanzu. Bata da mai bata amsa, sai ma kira daya shigo wayarta a dai-dai lokacin. Wayar dake acan saman mirror ta ɗan zubama ido, sai ta tsinta kanta da jin nauyin jiki har kiran ya tsinke. Wani kiran ne ya sake shigowa, sai hakan yay dai-dai kuma da fitowar AA hannunsa ɗauke da wata bag ƙarama. Har ya wuce batare daya kalleta ba itama ta miƙe da nufin ɗaukar wayar sai ta hangesa agaban mirror ɗin kamar mai neman wani abu. Komawa tai ta zauna, sai kawai jin ƙarar wayarta tai a ƙasa. Da sauri ta ɗago, wayar tata ce kuwa, yayinda shi kuma yake duƙe yana duba abu a drawer ɗin jikin mirror ɗin tamkar ma baiga abinda ya faru ba. Oum dake fitowa ta ce, “Subahannahi kako yaddoma Auta waya Auta”. Tsabar rainin hankali irin na AA sai ya juyo irin as bai lura ɗin nan ba ya ɗauki wayar yana jujjuyawa, ƙarasowa itama Oum ɗin tai inda yake ta amshi wayar ta duba. Gaba ɗaya tayi tatsa-tatsa. Screen ɗin yay wani irin zuuuuu alamar ya tashi aiki shima. Babbar waya ce, dan SS ce babba Daddy ya saya mata ita gift ɗin kammala karatun ta. “Auta kayi ɓarna”. Oum ta faɗa tana sake jujjuya wayar. Fuskarsa dake a tsuke ya yamutsa babu alamar damuwa a tattare da shi ya ce, “Oum ban lura bane. Kawo zanba Ahmad da safe ya gyaro”. Yay maganar yana miƙama Oum hannu. Kanta kawai ta girgiza da ɗora masa wayar a hannunsa. Shi kuma batare daya ce komai ba ya ɗauka bag ɗinsa ya fice. Ajiyar zuciya Oum ta sauke tare da juyawa ta dubi Maanal. “Karki damu kinji Auta, nasan in sha ALLAHU zai bada a gyara kafin wucewar mu goben”. Murmushin yaƙe kawai Maanal taima Oum. “Babu komai Oum”. Itama Oum ɗin sai tai murmushi tana jinjina mata kanta. Haka sukai shirin barci suka kwanta. Dan har Oum ɗin kwanciyarta tai a gadon tana faɗin, “ALLAH ya yarda yau zan sake kwanciya gado ɗaya da Babyna”. Siririyar dariya Maanal ta saki, yayinda Oum ke tayata itama zuciyarta cike da nishaɗin yanayin.....

__________★

Washe gari da safe bayan sunyi wanka suna dining da shirin karyawa harda Ya Fawzan AA ya shigo. Da mamaki Oum daya fara gaidawa take kallonsa. Dan a shirye yake tsaf cikin baƙaƙen suit da suka sake fiddo ainahin cikar haibarsa da madarar ƙyau. “Yau ba Saturday ba na ganka da shirin office?”. Oum ta faɗa cikin kasa haƙuri. Hannu ya miƙama Yaya Fawzan yana bata amsa da, “Oum project ɗin nan da nake gaya miki yau zamu fara aikinsa da Engineers ɗinmu”. “Okay aina ma shafa'a, ALLAH yasa ayi cikin nasara ya kuma ɗaga darajarsa. Maza to zauna ka karya dan bazaka fita da yunwa ba”. Agogon hannunsa mai matuƙar nauyin kuɗi da zama designer daba ako ina zakaje ka samesa ba sai ga wanda ya isa ya kalla. Cikin ɗan ɓata fuska ya ce, “Oum Please zansha coffee a office”. “Ban yarda ba kuwa. Zauna in ba hakaba nasa Fawzan ya riƙe min kai na maka ɗura”. Dariya sosai Fawzan yake yi, ya ce, “Tsaf kuwa zan danne miki shi Oum dan wannan girman jikin nasa da ƙarfuna suka bubbuɗe ba tsoro zai bani ba.” Harararsa AA yayi, dan dole yakai hannu yaja kofin gaban Maanal da tunda ya shigo tai masa kallo ɗaya ta maida kanta bata sake ba, daga tsayen da yake ya kai shayin bakinsa, dai-dai Maanal ɗin tana ɗagowa ta kallesa da mamaki, hakama Fawzan da Oum duk kallonsa sukayi. Amma ya wani basar kamar bai gani ba. Sai Oum ce tai masa nuni da kujera. “Maza zauna tunda kadai san babu ƙyau shan abu daga tsaye”. Baice komai ba ya zauna ɗin, sai faman kallon agogonsa yake yi alamar dai a ƙagare yake. Barrah da Haneeff ne suka fito daga kitchen tare da mai aiki. Dan sunce su noodles zasu ci shine taje dafa musu suka bita. Ganin AA ya sasu nufosa, cikin haɗa baki da ɗokin ganinsa sukace, “Uncle good morning”. A mamakin kowa sai ya saki murmushin nan nasa na rowa tare da shafa kawunansu ya na amsawa. “Good morning Handsome & Oum na. Fatan kun tashi lafiya?”. “Uncle Alhamdullah”. Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ya sake sakar musu da cewa, “Masha ALLAH”. Daga haka ya miƙe yana ajiye kofin da sauran shayi a inda ya ɗauka. Sai Maanal ta samu kanta da tsurama kofin ido kawai har yay sallama dasu Oum ya fita kafin ta farga. Yaya Fawzan ne ya katseta. Kayan shayin ya tura gabanta yana faɗin, “Haɗa wani shayin tunda ya shanye miki kinji Lilly”. Ɗan murmushin yaƙe Maanal tayi, cikin muryar nan tata mai sanyi ta ce, “Yaya akwai a ciki ya isheni”. “Kin tabbatar?”. Kanta ta jinjina masa. Oum dai Murmushin ta take irin na manya batace komai ba. Sun kammala breakfast ɗin babu jimawa sai ga RK. Da gudu su Haneeff suka maƙalƙalesa suna murna. Hakan yasa Oum sake fahimtar akwai shaƙuwa sosai tsakaninsa da yaran. Fawzan ma har yanzu yana a sashen Oum ɗin suna hira, sai kawai RK ɗin ya baje aka dora da shi bayan mai aiki ta haɗo masa breakfast dan yace bai karya ba. Anan falon ya karya suna hirar, idonsa akan Maanal dake kwance kanta a cinyar Oum tana karatun novel ɗin nata na fama. Sai ƙara jinjina shaƙuwar Oum ɗin yake da Maanal ɗin, dan kuwa yanda Maanal ɗin ta saki jiki ya ishesa shaida. Musamman idan yay dubi da miskilancin tsiya irin na Maanal ɗin....

____________

Da mamaki Shahidah ke sauraren Linda dake mata bayanin fitar Huznah tun 8. Ranta ne ya fara ɓaci da iskancin Huznah ɗin. Yaya tana a gidanta amma bata da mutuncin da zata dinga gaya mata zata fita. Kai ko gaisuwa tunda Huznah tazo gidan nan bata jin ta mata. Shi kansa Abbansu Barrah duk kawaicinsa yau da safe sai da yay magana. Shine ma dalilin da yasa yanzu da zasuyi zaman breakfast taima Linda magana akan ta tado Huznah ɗin su karya. Amma sai take sanar mata wai ta fita tun 8. Da alama kuma anguwa ta tafi dan taci gayu. Komai batace da Linda ɗin ba ta juya tabar dining ɗin. Bedroom ɗin ta ta shiga ta ɗau waya tayi kiran Ammie. A lokacin Ammie na tare da Daddy dan yau itace da shi. Bata ɗaga kiran ba har ya tsinke. Cikin hikima tacema Daddy tana zuwa dan wayar tata dama a silent take. Sashenta ta koma sannan tai kiran Shahidah ɗin. Bayan ta amsa gaisuwar da Shahidahn ke mata ta ce, “Mike faruwa da safen nan kira Shahidah?”. Cikin matuƙar ɗacin murya Shahidah ta ce, “Ammie akan yarinyar nan ne Huznah. Nifa gaskiya ina jin tsoro. Tunda tazo fa ba zama take ba, da mun fita aiki take shiryawa itama ta fice gidan nan wani lokacin ma sai mu rigata dawowa. Yau kuma da take weekend ma kinji tun 8 tabar gidan nan. Ammie ina jin tsoron kar wani abu ya faru ace a zamanta nan ne ban saka ido a kanta ba fa”. Numfashi mai nauyi Ammie ta sauke. Cike da nazarin maganganun Shahidah ɗin ta ce, “Kenan akwai dai abinda tazo yi Abujan, saboda uban ya barta suka jinginata da zuwa gidanki ta zauna. Ki kwantar da hankalinki in sha ALLAHU babu abinda zai faru. Zuwa anjima zan kira Yazeed nai masa bayani ya sanya ido a kanta tunda yana Abujar.” Ajiyar zuciya Shahidah ta sauke cike da gamsuwa tace, “Yauwa Ammie hakan dai yafi kam gaskiya. Dan shi kaɗai ne maganinta nikam bajin maganata zatai ba tana ganin shekarunmu ɗaya. Yasu Hameed da Aunty Sakina”. “Lafiyarsu ƙalau gaba ɗaya. Ya batun dubiyar da su Auta sukaje jiyan?”. Gaban Shahidah ne ya faɗi, amma sai cikin wayancewa ta ce, “Lafiya lau Ammie babu wata damuwa. Dan yanzu haka ma barci takeyi”. “To Alhamdullah, dan inata tunanin kar taje gidan mutane ta nuna bata son yaronsu. Ni kuma harga ALLAH yaron ya shiga raina saboda nutsuwarsa da sanin darajar mutane. Tunda al'amarin Yazeed ya koma wani iri gara ta haƙura da Rafeeq ɗin ayi a wuce wajen zaman nan nata damuna yake yi”. “Ammie adai cigaba da addu'a, in sha ALLAHU komai zai dai-daita, nawa ma Maanal ɗin take, rigimarta ce ta sata gama karatu da da wuri amma da yanzu ne fa ma ya kamata ta shiga jami'a. Rafeeq kam baida matsala mutumin kirki ne. Ya cancanta ai masa komai, kuma sun dace da Maanal ɗin. Sai dai nasan akwai rikici Ammie.....” “Rikicin mi kuma? Wani abu ya faru ne?”. “A'a babu abinda ya faru Ammie. Kawai nasan janyewar Yazeed akan Maanal bazai kasance mai sauƙi ba. Dan yana matuƙar sonta, auren nan dan baida yanda zai yi ne kawai uwarsa tafi ƙarfinsa ne. Yanzu haka kullum cikin roƙon Maanal yake akan ta bari a haɗa bikin ayi gaba ɗaya zaifi samun kwanciyar hankali. Ni wlhy duk sai ma tausayinsa ya fara damuna”. “Nima ina jin tausayin nasa Shahidah. Sai dai su haƙura da junan sai yafi alkairi fiye da yin, dan nasan wacece Hajiya Sadiyya. Komai zata iya yi kamar yanda ta faɗa. ALLAH dai ya kawo mafita cikin sauƙi. Bari anjima mayi wayar na bar babanku shi kaɗai ina wajensa kika kira”. “To Ammie ba damuwa sai anjima”...........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖3️⃣9️⃣

______________

.........A ɓangaren Huznah tana can gidan Yaseerah. Dan dama sunyi da ita yau da wuri zataje gidan kasancewar tunda tazo sai dai tayi zuwan fisha. Ta samu ko barci basu tashi ba. Saboda weekend ne mijinta na gida. Sai kawai ta shige ɗayan bedroom ɗin Yaseerah ta kwanta itama ta ɗora barcin da bata samu yi ba a daren jiya isashe. Sai wajen sha ɗaya Yaseerah da mijinta suka fito. Suna a d/table zasu fara breakfast mai aikinta ke sanar mata zuwan Huznah ɗin. Mijin nata ta kalla tana ɗan murmushi. “Baby Uncle ɗinka fa ya rikita min ƙawata. Munata binsa kuma yaƙi bamu muhimmanci. Yakamata ka shiga lamarin nan haka nan”. Murmushi yay shima dakai kofin tea bakinsa. “Ai dama na faɗa mata tun farko, shi bana wasan yara bane. Dama Uncle Fawzan ne da sauƙi, amma Uncle AA tab ɗin, ina tausaya mata ALLAH. Da zata ji shawarata da ta jima da manta ta taɓama saninsa kawai.” “Bazan iya haka ba Abdul-hakeem. Dan a yanzu bani da wani burin daya wuce mallakar Uncle ɗinka.” Muryar Huznah da basu san da zuwanta wajen ba ta ratsa kunnunwansu. Gaba ɗayansu juyawa sukai suna kallonta, ganin yanda hawaye ke sauka mata da gudu a saman ƙyaƙyƙyawar fuskar ta ya sasu miƙewa. Hannunta Yaseerah ta kamo ta zaunar a kujerar kusa da ita, itama takai zaune tana riƙe hannunta alamar lallashi. Shima zama yay mijin Yaseerah ɗin, wani irin tausayin Huznah na ratsa shi. Tabbas yasan ta ɗaukarma kanta abinda yafi ƙarfinta, amma ko ya cigaba da gaya mata gaskiya yasan ba lallai ta fahimcesa ba. Gyaran murya yay a hankali, hakan ya sasu ɗagowa su duka suka kallesa.. “In sha ALLAHU zan taimakeki. Sai dai ki sani wlhy Uncle AA nada wahalar sha'ani. Amma akwai mafita ɗaya da nake miki hasashen idan kin gwada maybe ki dace....” Jikin Huznah har rawa yake ta ce, “Wace irin mafita ce. Komai wahalarta ALLAH zan gwada, komai ƙalubalenta kuma zan jure”. Kansa ya jinjina mata, sai kuma ya sauke numfashi. “Batun yanzu ba nasan Grandma suna fama da Uncle AA yay aure. Kuma a yanzu haka ma suna gab da masa auren ne amma bani da tabbacin sun sama masa matar ko basu sama masa ba, duk da dai akwai wata sister ɗin mu dake sonsa matuƙa kuma naga duk dangi nason a gaɗasu aure, shine dai bai maida hankali ba. To ina ganin mafita ɗaya ce na baki number ɗin grandma, ko kuma ki shirya na kaiku ke da Yaseerah kamar zaku gaisheta sai muce ai ke budurwar Uncle AA ɗin ce. Idan ALLAH ya taimaka aka dace sai kiga ya amsheki dole bisa umarninsu. Hakan yayi miki?”. Cike da zumuɗi ta amsa masa, tana share hawayenta ga dariya. Shima murmushi yayi hakama Yaseerah. Ya ce, “Sai ki zama cikin shiri dan sai nan da kwana uku”. “Miyasa ba yau ba?”. Ta faɗa cikin damuwa. “Bata nan ne shiyyasa, amma ina saran dawowarta gobe ko jibi in sha ALLAHU”. Ajiyar zuciya Huznah ta sauke. Badan taso hakan ba tace ALLAH ya kaimu. Dai-dai nan kira ya shigo wayarta. Koda ta duba sai taci karo da Yaya Yazeed. Mamaki ta kamata, dan hakan kan jima bai faru ba ganin kiran yayan nasu. Haka dai ta daure ta ɗaga dan tasan in har wayar ta tsinke bata ɗaya ba sai taci ubanta a hannunsa. Ko amsa sallamarta baiyi ba cikin kaushin murya ya ce, “Kina ina nazo gidan Shahidah baƙya nan?”. Rawa jikinta ya fara, cikin karkarwar harshe tace, “Yaya wlhy bawani wajefa naje ba ina gidan Yaseerah ne nazo gaisheta”. “Na baki mintuna ashirin kawai ki dawo gida. Idan ba haka ba hummmm!”. Ya yanke kiran. Kanta tai wani irin dafewa dan takaici, batama san ta fara antayama Yazeed ɗin zagi ba Yaseerah na tayata. Babu dai yanda zatai dole ta kimtsa mijin Yaseerah ɗin ya ɗauketa domin maidata da kansa. Dan hakan kawai zatai ta kuɓuta daga bala'in Yaya Yazeed. Dabarar tata kuwa ta taimaketa, dan ganin Abdul-hakeem ɗin ya sassauta tanadin da Yazeed ɗin yay mata. Sai dai duk da haka taci zagi da faɗa akan fitar sassafe babu kuma sanarwa. Ya kuma ja mata dogon gargaɗi akan in har ta kara fita a gidan wlhy sai ya mata dukan mutuwa. Yana tafiya ta koma ɗaki tai kiran uwarta ta gaya mata tana kuka. Zage-zage itama Hajiya Basariyyar ta dinga yi da tsinar Yazeed ɗin. Sai da sukai san ransu ta koma lallashin Huznah da kwantar mata da hankali akan zatama Yazeed ɗin magana da kanta. Daga haka sukai sallama. Bata ko ƙara fita a ɗakin ba duk ɓuruntun da su Shahidahn keyi akan shirin tarbar baƙi su Oum. Sai ma nacin son samun AA take a waya amma hakan ya gagara. Da alama ma yayi blocking ɗin ta ne ita bata gane ba. Ai ko saita zauna tanata kuka. Sai da tayi mai isarta barci yay awon gaba da ita.....

___________★

Chapter notes and social links

https://chat.whatsapp.com/KU8Mqd2Mo530Pc14hc7QOG *ROYAL JELLY* *(MAIDA TSOHUWA YARINYA)* 🔥💃💃 Wani kayan sai amale wannan supplement shi akecema maida tsohuwa yarinya ita Kuma yarinya ta koma jaririya😂💃 Ina kuke Mata masu aji waanda sukeso suga suna walwali kamar tauraro toh gafa dama tasamu kiyi washar washar abinki.....🔥⭐⭐👑 Royal jelly nasa jikin mace yayi glowing mace jikinta yayi Kamar tangaram😍😍 ⭐👑 Royal jelly natsoro da gashin mace yayi kyau ⭐👑 Royal jelly na gyara mace ciki da wajenta ⭐👑royal jelly na fidda shape din mace...💃💃⭐👑 Royal jelly na Hana fatar mace tamukewa , yasa tayi looking fresh ⭐👑 Yanasa mace yayi looking under age dinta💃💃💃kiji ana wacce ke kullun kamar wata budurwa🔥🔥 ⭐👑 Royal jelly nakara hasken Ido yakuma gyara gashin ido 🔥⭐👑 Royal jelly na tsirar da farce da kwarinshi... Idan kinji ana maganar glowing to kici birki a royal jelly 🔥🔥⭐👑💃🏼💃🏼 Haseer supplements ta kawo muku supplement kaloli sai wanda ranki keso hajiya a cikin farashi mai sauqi Phone: 08038796871

Readers Also Read