Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 28

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 28

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 28: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 28. Ƙarfe huɗu da kusan rabi danƙareriyar…

3,045 words

Ƙarfe huɗu da kusan rabi danƙareriyar motar Fawzan ta iso gidan. Yana gama parking Barrah da Haneeff suka fice zuwa cikin gida aguje suna ƙwala kiran mamansu. Dariya Fawzan ya dingayi, dan shi ALLAH ya ɗaura masa son yara matuƙa. Kodan har yanzu ALLAH bai bashi bane. Dan matarsa bata taɓa ko ɓatan wata ba shekara shida kenan. Oum ma dariya take ma yaran. Maanal dai komai batace ba, sai ma jagorantar su Oum tayi zuwa cikin gidan. Sun sami Shahidah na ƙoƙarin fitowa tarbar su Oum, dan haka sukaci karo a ƙofa. Cike da wani irin farin ciki Shahidah da Oum suka rungume juna. Sai kawai Shahidahn ta saki kuka. Harga ALLAH tana matuƙar son Oum, dan mace ce ƴar halak da bazasu taɓa mantawaba a tarihinsu. Ta matuƙar taka rawar gani a garesu da Ammien su ta yanda baki yayi kaɗan ya bada labari. Itama Oum ɗin hawaye take da murmushi duk a lokaci ɗaya, ta ɗago Shahidah tana mai share mata hawaye. “Uhm-uhm kefa yanzu kin girma Sheedan Oum, ke uwa ce babbar yaya kuma”. Dariya Shahidah ta shigayi, hakama Fawzan dan tuno wani abu daya shuɗe. Maanal ma dai murmushi ne mai faɗi akan fuskarta. Abinda a yanzu yake da matuƙar tsada da wahala a gareta. Sai da Shahidah ta saki Oum sannan ta lura da Fawzan, cike da mamaki ta riƙe haɓa da faɗin, “Oh ni ALLAH wanake gani haka ya zama dattijo?”. “A'a tsoho na zama ba dattijo ba”. Fawzan ya bata amsa yana hararta. Dariya duk suka sanya masa. Shahidah ta ce, “ALLAH kuwa ka yarda ka zama dattijo yanzu Yaya Fawzan”. “Kema kin zama dattijuwar ai”. Ya faɗa dai-dai suna kaiwa zaune a ƙayataccen falon nata. Dai-dai nan mijinta ya fito. Cike da mamaki idonsa akan Fawzan ya ce, “Kai kai wanake gani haka kamar Darma a gidana”. “Ya arrahaman Busam!”. Shima Fawzan ya ambaci sunansa yana miƙewa. A tare suka cafke alamar lallai sun san junan kuwa sani bana wasaba. Ai sai su Oum suka koma ƴan kallo. Sai da ƙyar Shahidah ta iya faɗin, “Nifa ban gane ba, wai dama kun san juna ne?”. “Farin sani ma kuwa. Darma tare mukai degree master namu ai a Germany, sannan a yanzu haka akwai alaƙar aiki a tskaninmu. Kawai dai baya son zumuncine shiyyasa baki taɓa ganinsa a gidan nan ba.....” “Wulaƙanci ai kai zumuncin kake so?”. “Nadai fika tunda ni naje gidanka har sau biyu”. Cewar Abban su Barrah. Dariya Fawzan yay da faɗin, “Gori kenan. To yanzu ai gashi ALLAH ya kawoni, ashema ni ƙanwata kake aure kai wannan abin kunya da yawa yake”. “Ato kaima dai ka faɗa”. Cike da girmamawa Abban Barrah ya gaida Oum. Itama ta amsa masa da kulawa cike da farin ciki. Nan fa aka ɓalle taɗi tsakanin Oum da Shahidah, Fawzan da Abban Barrah. Yayinda Linda tuni ta cika musu gabansu da kayan ciye-ciye Maanal na tayata. Duk wannan bidiri da ake Huznah na ɗaki tana shaƙar barci abinta. Sai da Maanal ta taje ɗakin ajiye kaya ta ganta baje a gado. Komai bataceba ta ajiye ta dawo wajen su Oum. Sai ga RK da dama yay musu alkawarin samunsu a gidan. Nan fa hirar ta ƙara armashi dan tuni Abban Barrah ya janyesu sun koma falon baƙi dan Oum ta sake itama suyi tasu hirar. Hakan yama Oum ɗin daɗi sosai, dan ta samu tattauna abubuwa da yawa da Shahidah wanda Maanal ta kasa sanar mata komai saboda zurfin ciki da miskilanci. Sai da akai magriba sun dawo Huznah ta fito. A ɗan yatsine ta gaishe su, sai dai saukar idanunta akan Fawzan yaso birkita mata lissafi. Sai da ta nutsu ta fahimci ashe ba AA ɗinta bane kammanni ne kawai. Dan suna kama sosai da AA ɗin, sai dai wasu abubuwa da suka ɗan babbanta su. Hakama kuma suna kamanni da Oum matuƙa. Hankalin Huznah ne ya tashi, dan haka kawai take ji a ranta wannan mutumin na kama da AA ɗin ta hakama matar, sai dai yanda ta gaishesu yasa daga amsa gaisuwar kowa ya watsar da ita musamman RK da kamar basu ƙaunar juna ita da shi. Su Oum na gidan nan har tara, dan har sai da Autan ta ya kirata yana damunta shi dai ta dawo ya koma gida tun ɗazun duk basa nan gida babu daɗi kuma yana jin yunwa. Dariya Oum take masa da tsokanarsa akan wannan hali nasa na ɗafa, ya girma amma bai san ya girma ba koda yaushe yana laƙafe da ita. Idan tai masa aure yaya kenan. Shi dai roƙonta ya cigaba da yi akan su taho kawai. Tace shi bazai zo ya samesu anan ba yace ya gaji. Ƙyalesa tai tace gasu nan tahowa. Amma wayar Maanal fa ba'a gyara bane?. Sai cemata yay eh wai mai gyaran yace sai Monday ma. “ALLAH ya kaimu” ta bashi amsa tare da sanar masa gasu nan dawowa. Sosai Shahidah ta haɗama Oum shata ta arziƙi, duk da tasan tafi ƙarfin duk abinda ta batan. Saboda suma su Maanal haka Oum ɗin ta haɗo musu abubuwa iri-iri na tsaraba. Da suka fito kuma sai da suka shiga super market ma aka ƙara wasu sayayyar. Huznah dai duk jikinta yayi sanyi da ganin waɗan nan ƴan gayun mutane gogaggu wayyayun ƴan boko da hutu da jin dadi ya gama ratsawa. Sai kuma gefe ɗaya na zuciyarta ya kasa samun nitsuwa akan kamannin Fawzan da AA ɗinta da kuma Oum. Jiki a sanyaye ta biyo su Maanal rakkiyar su Oum har mota. Maanal na manne da Oum ɗin sai shagwaɓa take mata cikin maganar nan tata ƙasa-ƙasa dake sake narkar da RK tana baƙanta ran Huznah da ganin tsantsar iskanci ne kawai da bariki kesa Maanal ɗin maida muryarta haka. Gefe kuma Fwazan na tsokanarta wai sun saka musu Oum ɗin su tsakkiya da shagwaɓar tsiya, ita tayi Auta yayi. Dariya kawai Oum tayi da faɗin, “Babu ruwanka barni da kayana, suyi abinsu san ransu ko Auta?”. Cike da jin kunaya Maanal ta ɓoye fuskarta a jikin Shahidah. Dariya suka sanya mata. Daga haka sukai sallama Oum na sanar mata wayarta zata taso mata ƙeyar AA ya kawo mata idan an gyara. Kai kawai ta iya ɗagama Oum tana ɗan murmushi, amma a ranta tasan bamai yiwuwa bane ya kawo da kansan. Shima kansa Fawzan murmushi yayi yaja mota suka fice. Sai RK dake tsaye jikin tasa. Ciki su Shahidah suka koma da yaran aka bar Maanal a wajensa zasuyi sallama, kamar zata sharesa. Sai dai ganin yanda Huznah ke wani binsu da kallon ƙwaf ya sata nufarsa.... “Humm dama haka kika iya shagwaɓa my queen?”. RK ya faɗa yana binta da kallo ƙasa-ƙasa. Murmushi kawai tai masa mai sanyi kanta a ƙasa. Batare da tace komai ba. Shima sai ya saki murmushin da sake maida hannunsa ya harɗe a ƙirjinsa. “Koda yake ma ni fushi fa nake dake”. Ɗan ɗagowa tai ta kallesa da faɗin, “Akan mi?”. “Humm akan komai ma. Yanzu ace akwai alaƙa mai ƙarfi irin haka a tsakaninki da AA amma ban taɓa sani ba Maanal, ko'a fuska baki nuna min ba shima haka kuka wani rufeni a duhu. Zaman amana kenan?”. Sosai gaban Maanal ya faɗi, ta zuba masa ido, ganin shima ya zuba mata nasa idanun tai saurin janye natan zuciyarta na duka. A ranta kuwa tunani take wace alaƙar a ciki yake magana kenan? Badai yaji komai ba? Badai yasan komai ba? Shi AA ɗin ne ya sanar masa kenan kamar yanda yace zai yi ko kuwa? Dan tanada yaƙinin Oum bazata faɗa masa ba duk da kasancewarsa jininta ƙani uwa ɗaya uba ɗaya. Cikin wani irin sanyi ta ce, “Mi kaji a kaina?”..........✍️

😨😨😨😨😨🚶‍♀️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖4️⃣0️⃣

______________

.......Da mamaki ya ce, “Abubuwa da yawan gaske”. Harbawa zuciyarta ta sake yi, ta ce, “Wanne da wanne?”. Sai da yay wani ɗan murmushi da gyara tsaiwarsa ya bata amsa da, “Ai bazasu ƙididdigu ba. Ashe ke ƴar gaban goshin Aunty Babba ce”. “Bazaka faɗa min alaƙar da kaji ba kenan? Bayan kuma kai ne ka ɗakko maganar”. “Miyasa kika damu da sai kin ji? Ko akwai wani abu da kike tsoron kada ace naji ne?”. Harararsa ta ɗan yi, cikin rashin sakewarta da miskilanci ta ce, “Nikam mizan so ace kar kaji? Kawai dai naga ka ɗakko maganar ne da zurfi”. Ƙaramar dariya yayi da faɗin, “My queen rikici. To kwantar da hankalinki banji komai ba bayan wanda kika san naji a gabanki. Amma dai zan koma Aunty ta bani labarin ƙuruciyarki kaf, idan ma da hotuna duk a haɗa min nasha kallo.” “Kaji da shi dai”. Ta faɗa tana ɗan yin murmushin da yake matuƙar son gani akan fuskarta. Sai dai bata yi masa sai idan taso. Sai da ya wani ɗan lumshe idanu da buɗewa sannan a kanta, ya ce, “Miya samu wayar taki ne wai? Inata kira ba'a ɗagaba daga baya kuma naji switch off. Na tambayeki ɗazun baki ce komai ba yanzu kuma naji Aunty na faɗin AA zai kawo idan an gyara”. “Uhm faɗuwa tayi ne a jiyan lokacin da kake kira. Shine Oum ta bashi ya gyaro”. “Ayya ALLAH ya kiyaye to, da gyaran nan ai da wata aka saya kawai. Ga wannan ki riƙe kafin asan abinyi dan zama ba waya babu daɗi”. Yay maganar yana miƙo mata iPhone 15 ɗinsa. Kanta ta girgiza tana kallon wayar, sai kuma ta ɗan kallesa. “Kabar wayar ka ai yace zuwa gobe za'a kammala gyaran”. “Ni kuma gashi bazan iya cigaba da haƙurin rashin jinki ba. Please kar muyi jayayya”. Komai bata sake cewa da shi ba ta amsa wayar. Daga haka tace masa sai da safe. Tsareta kawai yay da idanunsa bai amsa ba. Ta ɗan ƙibta masa nata, alamar yaya dai? Sai ya saki murmushi da ɗan ɗage mata gira shima. Harara kawai ta sakar masa da juyawa tana faɗin, “ALLAH ya kaika gida lafiya”. Tai gaba abinta. Har ta shige ciki yana binta da kallo. Sai da ta ɓace masa ya sauke ajiyar zuciya yana wani lumshe idanu ya buɗe. Sai kawai ganin Huznah yay a gabansa. Tsaf ya shanye murmushin dake saman fuskarsa kamar bashi ba. Yay kicin-kicin da fuska batare daya nuna yasan da ita ba ya buɗe motarsa zai shiga amma sai ta riƙe murfin caraf. A ɗan fusace ya ce, “Lafiya?”. Dan shi tun randa ya fara ganin Huznah sam bata masa ba. Fuska ta ɗan marairaice kamar ba ita ba ta ce, “Kayi haƙuri dan ALLAH ina da tambaya ne”. Kamar bazai tanka mata ba sai dai ya daure ya ce, “Tami?”. “Wanda naji kana kira da Uncle Fawzan, da wannan matar. Dan ALLAH suma ƴan family ɗin Darma ne?”. Wani kallon sama da ƙas ya mata a wulaƙance ya ce, “Kina da bussines da sune ko Darma Family ɗin?”. Murmushi ta saki mai sanyi da ɗan duƙar da kai kamar mai jin kunya. Sai kuma ta ce, “Kusan hakan, ni ce wadda AA Darma zai aura”. Gaba ɗaya RK ya wani wantsalo mata idanu waje da mamaki ya ce, “What AA fa?”. “Yes”. Ta bashi amsa cike da jin alfahari da kwarin gwiwa. Sai ya rasama abin faɗa dan aljabi. Shi dai yasan idan bai faɗama wani halin AA ba wani bazai kuwa bashi labari ba. To amma masu iya magana kance baka shaidar mutum akan mace. Sai dai sanin da yayma AA kai da kamar wahala. Mutumin da aketa fama da shi tsayin shekaru yay aure yaƙi. Tabbas Huznah mace ce ƙyaƙyƙyawa da duk inda kake son mace mai ƙyale-ƙyale za'a nunata. Amma miya ja AA nan wajen da babu kamun kai babu aji da akasan cikakkiyar mace data amsa mace da shi. Kai shifa zai iya rantsuwa yanda Maanal ke jansa a ƙasane ke ƙara masa soyayyarta. Dan yana son mace mai suna mace data san kimarta. Rasa abin faɗa ya sashi cewa, “Sai da safe nikam zan wuce”. “A'a yayana ai baka gama amsa min tambayata ba Please”. Sake juyowa yay daga haka kansa yunƙurin shiga mota da yake ya kalleta da mamaki, wai yau shi take kura Yaya, bayan duk ganinta da yake a gidan kusan kwana nawa baya jin tama taɓa ko gaidashi. Amma sai ya shanye mamakinsa ya furta, “Mi kike son ji kuma?”. “Alaƙar matar nan da suka zo da Fawzan ɗin da kuma AA?”. “Wannan ai shi AA ɗin ya kamata ki tambaya nake ga ko? Ko kuma su masu nan gidan tunda naga suma suna da alaƙa da su mai ƙarfi ma kuwa”. Sosai gaban Huznah ya faɗi da jin kalaman RK. Sai dai kafin ta samu damar sake furta komai ya shige motarsa yay mata key. A gabanta ya fice a gidan aka maida gate da aka wangale aka zugesa. Rasama wane tunani Huznah zatai tayi, amma tai ƙoƙarin hana kanta kiran mahaifiyarta har sai ta bincika ainahin gaskiya sannan dai. Da wannan tunanin ta koma ciki itama......

___________★

Washe gari lahadi Maanal ta tashi da burin fita gyaran jiki. Sai ga Yazeed yazo gidan. Jin inda take shirin zuwa yace tazo ya sauketa kawai. Haka badan taso ba suka wuce ita da Barrah da Huznah data maƙale akan zataje. Kasancewar Huznah a motar yasa Yazeed kama kansa. Dan shi fa agaban Maanal ne kawai dama zakaji muryarsa ko sauƙin kansa. Amma ƙannesa da sauran mutane shi mai matuƙar kamun kai ne da tsare gida. Ya dai tambayeta wayarta da yake kira baya samu ta sanar masa accident ɗin data samu, yayi addu'ar ALLAH ya kiyaye gaba daga haka ya kaisu wajen gyaran jikin. Yau ma kamar waccan ranar atm ɗinsa ya bata, ya kuma ce idan sun kammala ta kiranshi. Bataƙi amsa ba tai godiya kawai kodan idon Huznah ƴar saka ido. Haka suka shiga wajen gyaran jikin. Sun sami mutane ba masu yawa ba, kasancewar sun fito da wuri sannan mai wajen ƙawar Shahidah ce. Ana tsaka da musu gyaran ita Maanal ana wanke mata kai, Huznah kuma wankin ƙafa da gyaran farce wata ƙyaƙyƙyawar mata ko budurwa za'a kirata ko bazawra ne ma oho ta shigo wajen ita da ƙawarta. A fuska dai kam akwai ruwan ƙyau, sai dai a jiki haka take slim babu gaba babu baya. Duk rashin jiki irin na Maanal sai ta ganta da ƙyan fasali akan matar. Dan Maanal rashin jikin ne dai kawai bata da, amma tanada cikar halittar jiki gwargwado duk da suma bawani na manyan mataba can. Amma dai duk inda mace zata kira kanta mace kam itama zata buɗe baki. Yanda yarinyar ke yamutse-yamuste da shan ƙamshi ne yaja hankalin mafi yawan mutanen dake a wajen kanta. Tuni wasu suka ɗan fara mata magana tana amsawa da gyar, banda Maanal da ko kallon inda take batai ba. Ana gama ma wanke mata kai ta ɗauka novel ɗinta ta cigaba da karatu, yayinda Barrah da akema kitso ke gefenta tana game da wayar wajen RK. Ashe yarinyar nan hankalinta nakan Maanal data watsar da ƙurarsu. Sai hakan yay mata zafi ta shiga habaici da yaɓa magana ƙawarta na tayata da mata kirari da dariyar iskanci. A hakan ma Maanal bata ma nuna tasan bayan ita da wasu ma a shagon ba. Cikin masu aikin wajen ce ta ce, “Oh ni, yau dai da alama da fitina kika fito gida Nurry, irin wannan takale-takale shin na miye? Dawa kike anan?”. Sai da ta watsawa mai aikin harara sannan ta tauna chewing gum ɗin bakinta ya bada wani ƙas-ƙas ta ce, “Da ƙananun karuwan Abuja mana. Masu baro gidan ubale suzo nan su kama hotel suna girman kai da ɗaukar kansu wata tsiya. Ƴan iska ɗaya bayan ɗaya sai mun saitasu gidan iyayensu da ake cin masara sun bar mana garin mu shegu ƴaƴan talakawa”. Dariya ƙawarta ta ƙyal-ƙyale da shi tana zuba mata wani kirari. “Sai dake tawajena, sa gabanki inda kike so. Kuɗi ya haifeki, cikinsu kika girma gidan su zaki zama matar aure. Kaga amarya a gidan tauraron matasan ƙasar nan kaf mai kiran kuɗi koda kwance suzo su masa bargo a gado. Yi yanda kike so kune Abuja dama ƙasar gaba ɗaya ai ko anƙi ko an so dai da ku”. Wani yyyuuuuu Nurry ɗin tai da idanunta manya dake a juye kamar ƴar shaye-shaye. Cike da jin alfaharin Kirarin ƙawar tata ta wani watsama Maanal kallon banza. Hakan datai ya saka kowa fahimtar da Maanal ɗin take. Wani shegen murmushi Huznah ta saki na jin daɗi, sai kawai ta dubi Nurry ɗin fuska da murmushi ta ce, “Hy Mss”. Da farko Nurry kallonta tai zata watsar, sai kuma dai taga itama Huznah ɗin ba daga baya ba. Jiki da suttura duk sun nuna ƴar wani ce. A ɗan yangance ta amsa da “Hy” itama tana watsama Huznah yatsu biyu. Tsam Huznah ta miƙe kasancewar an gama mata ta koma kusa da Nurry ɗin. Sai lokacin Maanal ta ɗan kallesu, kanta ta ɗan girgiza kawai ta miƙe tabar musu wajen ma gaba ɗaya ta koma sashen ƙunshi dan tana son a mata ɗan jan lalli a yatsunta da ɗan baƙi kaɗan a hannun kawai. Ai hakan kamar yama Huznah daɗi ne. Tuni ta baje a tsakkiyar su Nurry aka ɗora hira harda musayar numbers. Haka dai akai musu gyaran jikin nan har bayan la'asar sannan suka fito domin komawa gida. Kasancewar Maanal bata kira Yazeed ba duk da yace ta kirashin sai ta tare taxi dan su tafi, sai kawai Huznah catai suje ita su Nurry zasu sauketa. Dan kusan tare suka fito da su Maanal ɗin suma. Ko ci kanki Maanal batace mata ba suka shige taxi ita da Barrah suka wuce abinsu. Ita kuma ta shiga jibgegiyar motar Nurry da take driving da kanta suka tafi.....

_________★

Readers Also Read