Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 42

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 42

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 42: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 42. .........Babu bai sake bi takan bikin…

2,152 words

.........Babu bai sake bi takan bikin su Maanal ba, yama maida hankali a shirya musu tafiya gida. Yayinda Ammie taketa ƙarfin halin yin nata shirye-shiryen itama batare da su yaran sun san mi ake ba. A haka ranar juma'a akai partyn da Oum ta shiryama Maanal da Ajwaad. Abin kamar wasa sai gashi ya ƙayatar. Anci ansha yara sun sha bidirinsu musamman Maanal da ko zama ta huta batayi. Shi kansa AA duk ta takurama rayuwarsa. Haka dai aka tashi gab da magriba, tsabar gajiyar da Maanal tayi a inda tai sallar magrib anan ta ɓingire barci. Kallonta kawai Oum tai tana murmushi, dan a tare sukai sallar a ɗakinta. Ɗaukarta tai cak ta maida saman gadonta ta kwanar, ita kuma ta cigaba da lazimin ta. Bayan idar da sallar isha'i su Ajwaad suka shigo harda Aban su. Kai tsaye ɗakin Oum Abah ya shigo. Yakai zaune bakin gado fuskarsa da murmushi yana kallon Maanal ya ce, “A'a anan surukar taki tai barci?”. Dariya Oum tayi tare da faɗin, “Kaji Aban su da wata magana suruka kuma?”. Murmushin sa ya sake faɗaɗawa shima da faɗin, “Eh mana. Ai abunne na Maanal da autanki akwai ban mamaki. Zan so wannan abotar tasu ƙarshenta ya kasance hakan”. “To ALLAH ya zaɓa abinda yafi alkairi. Idan hakan ta kasance zanfi kowa farin ciki Gandanga. Dan har cikin raina nake jin matuƙar ƙaunar yarinyar nan wlhy”. “Nima haka yarinyar ta shiga raina sosai. Badan kar ace ma na cika zumuɗi ba nifa da a yanzu zan ɗaura musu aure kawai”. Dariya sosai Oum keyi. Shima Aba na tayata. Sai da sukai mai isarsu Oum tace, “Ayi haƙuri dai a barsu sukai hankalin kansu. Kar a tauyesu musamman ita da take mace. Gara shi namiji ne yana da damar auren fiye da ita”. “Hakane kuma kema kinyi magana. Kinga nama shafa'a ɗazun Baban nasu ke sanar min zasuje gida hutun nan ma, dan mahaifiyarsa tana kewarsa sosai.” “Kai masha ALLAH, ai ni har ƙoƙarin su nake gani ma. Musamman Ammien Shahidah. Garama shi tace yaje kusan sau uku. Amma ita tunda suka dawo Kano bataje ba hakama yara”. “Abin ne sai a hankali ai. Kin san idan iyali sukai nauyi tafiya ma wahala take yi. Balle wannan aikin nasu na ƴan sanda sai a hankali. Kwanaki ma kamar zasu masa transfer ALLAH dai ya taimakesa aka samu canji. Hankalinsa ya tashi sosai dan yace baya son yawon da yake da yaran musamman a yanzu da suka fara girma”. “Yana da gaskiya. Ita kanta takance ALLAH yasa ko ya samu canjin wajen aiki ya barsu su anan Kano dan tana jin daɗin zaman garin......” Sallamar Ajwaad ta katse Oum. A tare suka amsa masa da bashi izinin shigowa. “Lafiya Autana?”. Oum ta faɗa tana kallonsa. Fuska ya ɗan yamutse kamar zai saki kuka ya ce, “Oum kaina ke ciwo. Kuma ina jin yunwa”. “Ya rabba. Autana badai duk kai kawon nan baka ci abinci ba?”. Kansa ya ɗaga mata alamar “eh”. Da sauri ta kama hannunsa suka fice tana jan salati. Aba ya mike yana musu dariya....

___________★

Sosai su Ammie suka shirya wannan tafiya. Yayinda su Shahidah keta zumuɗi banda Maanal da tace idan fa bada Ajwaad ba babu inda zataje ita kam. Babu wanda ya tanka mata dai akan batun. Su dai sun cigaba da shirinsu kawai. A ɓangaren Ajwaad ɗin ma tunda yaji batun tafiya jikinsa yay sanyi. Da farko shima ya nuna son binsu. Har ya samu Oum da maganar tace ita dai babu ruwanta ya sanarma Aba. Bai Musa ba ya samu Aban da batun. Amma sai ya kwaɓesa akan maganar. Kai tsaye ya sanar masa bazai iyu ba. Suma zasuyi tasu tafiyar zuwa Adamawa suga gida... Tafiya ta tabbata, amma ansha fama da badaƙala kafin Maanal ta yarda. Sun tafi tana kuka kashirɓan kamar zata shiɗe. Shima uban gayyar da taurin kansa yasa baiyi kukan ba da farko yana ganin sun wuce ya shige ɗaki ya kwanta a gadonsa sai ga hawaye. Daga ƙarshe da zazzaɓi ya yini ranar. Har washe gari sai da aka sanya masa ƙarin ruwa. A ɓangaren Maanal ma kuka taci sosai har sai da Babu ya mata buyagi, itama ƙarshe zazzaɓi ya rufeta. Taita kwara musu amai a mota. Haka suka isa Kebbi tayi ligiff a wahale. Anan suka ɗan tsaya aka dubata. Washe gari suka ɗauki hanyar Suru da shima keda ɗan nisa daga nan cikin birnin Kebbi ɗin. Dan a ranar ɗin ma basu isa ba sai da zuhur.. Gari ne tsaka tsaki a komai. ba ƙato bane can sosai. Ba kuma ƙarami bane ba. Suna da wutar lantarki sannan akwai titi har a cikin garin. Kusan zaka iya samun duk abinda kake so naci ana saidawa musamman wanda ake mu'amala da shi ako ina kamar su kayan sanyi, kayan marmari, nama, da ire-iren hakan. Mutanen garin na neman ilimi gwargwadon iko, dan suna da manyan mutane sosai a ƙasar da ake damawa da su a gwamnatin jahar dana tarayya. Daga Suru hanyar Giro suka ɗauka, nan kam basu isa ba sai yamma sosai. Giro dai ƙaramin garine, amma ƙauyene mai ƙyau da ƙayatarwa. Tun kafin motar Babu ta isa labari ya iso gidansu. Lokacin da motarsa ta tsaya tuni yara sun zagayeta cike da zumuɗi musamman ganin harda baƙin fuska da basu sani ba. Dan duk sanda aka haifesu wasu kuma sukai wayo Ammi bata garin. Tun daga waje zaka san gidan ƙaton gaske ne. Dan ƙofa ce wangamemiya ƙwarai da gaske. Sai ƙatuwar bishiyar ceɗiya da kufan wutar makarantar allo irin ta tsangaya an zagayeta da dutsuna. Gefenta kaɗan massalaci ne da ɗakuna a jere kusan guda goma ko muce shaguna da jikin bangonsu duk alluna ne. Jiki a sanyaye Ammie ta fito fuskar ta ɗauke da murmushin ƙarfin hali. Yayinda su Shahidah keta kalle-kalle suna son tuno abinda suka manta musamman ma ita da aka tafi da ita da ɗan wayonta. Tuni yaran sun fara kwasar kayayyakin suna shiga dasu, yayinda su kuma suka bisu a baya Babu biye da su. Ɗakuna ne guda biyu masu kallon juna a farkon shiga. Ana hannun dama ke buɗe wani dattijo mai farin gashi fatt zaune kan buzu yanata rubutu a wani ƙatoton allo. A hanli Ammi ta cire takalman ƙafarta zuciyarta na mata ɗan sanyi, ganin haka yasa suma su Shahidah cirewa, yayinda Maanal ta dogara tana kallonsu... “Barka da hutawa Baffah”. Ammie ta faɗa a hankali kanta a duƙe dai-dai tana shiga cikin ɗakin. Sai lokacin tsohon ya ɗago ya ɗan kallesu fuskarsa da murmushi. Cikin kamala da tausa harshe ya furta, “Lale da mutanen garin dabo”. Murmushi Ammie ta sake yi hakama Babu da ya shigo riƙe da hannun Maanal data dogare a ƙofa. Sai da suka kai zaune tsohon ya sake faɗin, “Ashe zaka cika alƙawari Habibu ka kawo min iyalanka na sake gani kafin na koma ga ALLAH?”. Sosai Babu ya sake sunkiyar da kansa cike da girmamawa ya furta, “Ai min afuwa Baba, ai min afuwa”. Murmushi tsohon yay mai faɗin gaske. Sai kuma ya miƙama Maanal dake ta faman kallonsa cikin zare ido hannu alamar tazo gareshi. Da sauri ta matsa jikin babanta tana maƙe kafaɗa alamar bazata je ba. Turata Babu yay yana mai daka mata tsawa. Cikin harshen turanci ya ce, “Wuce kije mana ban son raini”. Duk da tsohon bajin abinda Babu ya faɗa yay ba sai yay murmushi. Dan ya fahimta ganin yanda Maanal ta zabura jiki na karkarwa ta matso inda yake sai dai duk a ɗarare. Bai ƙiba ya kama hannunta ya zaunar a gabansa. Cikin tausasa harshe ya furta, “Wannan shi ake gudu dama ai Habibu. Shiyyasa muke kwaɗayin ku ringa matso da iyalan naku gab damu koda lokaci-lokaci ne”. “ALLAH ya huci zuciyarku Baba”. Babu ya sake faɗa da sauri. Cikin sanyin murya itama Ammie ta nema afuwa. Kafin ta ɗora da gaishesa cikin girmamawa. Ya amsa mata da kulawa tare da tambayarta bayan rabuwa. Hakama su Shahidah duk suka shiga gaishesa. Hannu duka ya miƙa musu alamar suzo garesa. Babu musu duk suka matsa. Sai da duk ya taɓa kawunansu sannan ya tambaye su sun ganesa?. Kai tsaye Shahidah tace ta ganesa. Amma Amaal na ɗan inda-inda. Ta dai san ta sanshi sama-sama. Sai dai a wancan lokacin bai kai haka tsufa ba. Gashinsa kuma bai furace kamar yanzu ba. Murmushi yay da akazo kan Maanal da yana tambayarta kawai ta fashe da kuka. Itafa harga ALLAH tsoronsa take ji. Musamman wannan farin gashin nashi dogo sosai daya zagaye ƴar ramammiyar fuskarsa. Ga farin rawani ya naɗa akan nashi. Lallashinta ya shigayi tare da bata farar alewa dake cike da wata ƙwarya a gefensa. Badai ta sha ba amma ta daina kukan..... Sun jima a wajensa dan har duhu na neman rufawa kafin su shiga cikin gidan. Lallai ƙaton gaske ne da sassa daban-daban. Tarin manyan turamen daka dake a ƙarƙashin bishiyar dalbejiya a farkon shigowa gidan zai tabbatar maka da hakan. Sai runbuna da ake ajiye abinci da aƙalla sun kai kusan ashirin. Yara ne sosai a haka ma dan mangariba ta rufa ne wasu basa gida. Sai mata da akalla sun kai goma sha biyar dake tsaitsaye wasu ma daga su sai karin ƙirji. A hakan kuma ƙalilanne a matan gidan, waɗan nan wanda bazasu iya haƙuri bane saboda zumuɗin son ganin Ammie da yaranta. Itama Ammien ganinsu yasa tuni ta manta da fargabarta. Fuskarta da murmushi ta nufesu. To suma dai bakunan nasu a washen suke. Duk da dai wasu fara'ar tasu bata kai ciki ba. Su dai su Maanal na raɓe jikin Babu da matan nan keta faman yima sannu da zuwa. Garama Shahidah da Amaal na ƙoƙarin gaishesu da kalmar “Ina yini”. Lallai shekara shida ba kwana shida bace. Suma sai kallon yaran suke da mamakin canjawarsu. Sun yi girma kuma sosai musamman ma Maanal da aka tafi da ita daga garin tana ƴar shekara biyu. Yanzu ko gashi tana ƴar budurwa shekara takwas ai ba wasaba su a wajensu. Dan yara sun ma fara kula samari. Kamar Shahidah kuwa masu sha biyar ai sun haihu ta biyu kota farko dana biyu a ciki. Kamar Amaal mai sha uku sune amaren wannan shekarar.. Har sashen gwaggo akai musu rakkiya. Inda anan ne ɗakin da Ammie tai rayuwa a ciki yake. Wajene aka dan katange da ɗakuna guda uku. Ɗaya na Gwaggo mahaifiyar Babu ɗaya nata. Sai ɗayan na kishiyarta da bata wuce wata biyar a gidan ba ta fita. Fitar tata ce kuma ya ƙara mata baƙin jini a gidan da ma wajen surukar tata da bata samu sassauci ba sai da suka bar garin da zama. Gwaggon na saman wani ɗan dutse daga ƙofarta tana alwala. Sau ɗaya ta ɗago ta kallesu ta maida kanta. Amma haka Babu ya nufeta fuskarsa da fara'a yana faɗin, “Barkanki da wannan lokaci Gwaggona”. Ganin haka itama Ammi da sauri ta matsa ta tsugunna tana faɗin, “Sannu Gwaggo! Mun sameku lafiya?”. Maimakon ta amsa su su duka a daƙile ta jefama Ammie wani kallo ta maida idanunta akan su Shahidah dake tsaye suna kallonsu sannan ta maida ga Babu ta sakar masa murmushi. “Babana kasha hanya”. Murmushin ƙarfin hali yayi dan abinda taima Ammin ya ɗan sokesa. Sai dai bai nuna ba ya danne abinsa ya maida mata da murmushin yana faɗin, “Aiko dai Gwaggo. Bara na je salla gashi har za'a shiga damma ina da alwala”. Kanta kawai ta jinjina masa. Ya miƙe yana kallon su Shahidah dake rakuɓe suna kallon Ammie dake duƙe kanta a ƙasa har yanzu. “Ku kuma kukai tsaye anan. Ku shigo mana”. Jikinsu a sanyaye suka ɗaga kawuna. Shi kuma ya fice batare daya waiwayesu ba zuciyarsa duk babu daɗi. Yasan dole sai haƙuri, dan hutun nan sam bazai zame musu na farin ciki ba sai abinda suka gani. Tsakaninsa da mahaifiyarsa babu wata damuwa. Amma yanda takema matarsa da yaransa abun na damunsa matuƙa. A ganinsa matarsa bata cancanci hakanba kodan hallacin iyayenta a garesa ya kamata Gwaggo ta rangwanta mata. Amma ina, ya rasa wace irin ƙiyayyace wannan mai zafi........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖5️⃣9️⃣

______________

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/F7aIYP99bGn9mIqLhjUWKR GOLDEN COLLECTIONS TA TANADAR MUKU KAYAN ADO N FITA KUNYA KAMAR SU ATAMFA,LACES ABAYA SHOES AND BAGS DA KAYAN DECORATIONS D FURNITURES A FARASHI ME SAUKI

__________

Readers Also Read