Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 43
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 43: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 43. .........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji…
2,184 words
.........*_SU WAYE SU AMMIE?:-_* Alhaji Umar da mutane sukafi sani da Alhaji Umar Giro ɗan asalin jihar Kebbi ne a garin Giro dake ƙarƙashin Suru LG. An haifesa a babban gida da yay suna matuƙa a cikin garin Giro saboda kasancewarsu manyan mutane masu ƙarfin ilimin addini. Su kusan ashirin da bakwai mahaifinsu ya haifa, maza sunfi yawa, dan mata huɗu ne kawai a cikinsu, sauran su ashirin da uku duk maza ne. Malam Ibrahim shine mahaifinsu, sai iyayensu mata su uku. Ta tsakkiyar itace mahaifiyar Alhaji Umar, shi kaɗai kuma ta haifa a duniya, sauran ƴaƴa ashirin da shida duk na matan biyu ne. Dan matarsa ta farko haihuwarta goma sha ɗaya amma ƴaƴa goma sha shida duk nata ne. Sai amarya nada goma cif duk da itama dai wasu sun rasu a ciki. Kishi sosai ake zubawa a gidan Malam Ibrahim, hakan yasa ƴaƴansa suka tashi da zafin ƴan ubanci. Kowa ɗan ɗakinsu kawai yake so. Wannan aƙidar tafi wahalar da Umar, dan shi kaɗai shi mahaifiyarsa ta haifa shiyyasa sam baya wani jin daɗin zaman. Yasha wahala ƙwarai da gaske a hannun ƴan uwansa, har takai karatun ma baya fuskanta dan anan cikin gidansu suke ɗaukar karatu wajen mahaifinsu, ƴan uwansa manya kuma sune gardawa a yanzu. Ganin yanda Umar ɗin ke cikin tsangwama da ƙyara yasa mahaifinsu ɗaukarsa ya bama wani amininsa shima malami ne amma a can cikin birni, yanada tarin almajirai kuma Alhamdullah ana karatu. Mahaifiyarsa tasha kuka, amma hakan yafi mata kwanciyar hankali akan zamansa a gidan. Umar ya koma cikin birnin kebbi, kuma Alhamdullah yana samun ilimi, ya kuma kwantar da hankalinsa sosai dan Malam Khamisu ya saka shi cikin ƴaƴansa babu banbanci. Ƴaƴan malam Khamisu su suna karatun boko, hakan yasa shima Umar aka saka shi a boko. Zamu iya cewa Umar ya fara karatunsa cikin nasara, kasancewarsa yaro mai basira cikin ƙanƙanin lokaci yay zarra. Ga kuma ilimin addini shima alhmdllh. Umar na zuwa Giro akai-akai saboda mahaifiyarsa, dan haka canjin da rayuwarsa ta samu a bayyane yake ga kowa. Cigabansa na saka ƴan uwansa sake jin tsanarsa da hassadarsa su da iyayensu, sai dai babu yanda zasuyi. A haka ya gama secondary school ya fara jami'a, yana level 2 ALLAH yay ma mahaifiyarsa rasuwa. Ya shiga tashin hankali matuƙa daga shi har mahaifinsu, sai dai babu yanda aka iya da hukuncin UBANGIJI. Bayan rasuwar mahaifiyarsa ya sama ransa dangana ya maida hankalinsa ga karatunsa, har ALLAH yasa ya kammala jami'a. A kuma wannan lokacin ALLAH yay ma uban riƙonsa Malam Khamisu rasuwa shima. Umar ya sake shiga ruɗani, dan komai ya fice masa a rai. Dan haka ya tafi yin sarvese ɗinsa nesa da Kebbi. A jihar Niger cikin garin Minna Umar ya fara Sarvese, inda anan kuma ALLAH ya haɗashi da matar aure. Lubabatu yarinya ƙyaƙyƙyawa mai ilimin addini da nutsuwa. Gata da haƙuri da tarbiyya. Cikin ƙanƙanin lokaci soyayya ta ƙullu tsakaninta da Umar da hidimar ƙasa ta kawosa garin Minna. Lubabatu su biyu ne a wajen mahaifinsu, daga ita dai ƙanwarta Shamsiyya. Suma ALLAH yayma mahaifiyarsu rasuwa matar uba ke riƙonsu, suna matuƙar shan wahala a hannunta. Hakan yasa Umar na nuna yana son Lubabatu mahaifinta ya bashi. Cikin ƙanƙanin lokaci aka gama komai, dan kafin ya gama sarvese har ranar aure an saka musu. Yana kammalawa akasha biki. Nan Giro aka kawo amarya family house ɗinsu, dan ba auren nasu kaɗai akai ba harda wasu a cikin ƴan uwansa da suma akayi duk a ranar. Sai da aka gama shan biki, bikin da aka nuna matuƙar banbanci dan sam Umar baida wani gata a cikinsu, gashi itama Lubabatun duk sai a hankali tunda basu da wani gata suma sakamakon rashin uwa. Haka dai akayi biki aka gama, amare suka tare da mazajensu. Umar baya son zama a Giro, amma saboda kunyar mahaifinsa ya kasa magana. Ga aiki ya samu a Kebbi, sai ya zam dole ya koma Kebbin sai weekend yake zuwa. Sam Lubabatu bata jin daɗin zama a cikin waɗan nan ahali, dan kishi da ƴan ubancin da ƴan uwansa ke nuna masa duk sai ya tattaru ya koma kanta a yanzu. Ga matan ƴan uwansa suma sun sakata a gaba, facalanci mai muni ake zubawa a tsakaninsu. Musamman ma da Matar yayansu na biyar wanda Umar ke bimawa a wajen mahaifinsu mai suna Talle. Talle irin matan nan ne masu mugun hali da hassada da ƙyashi, duk wani cigaba tafi son ace itace da shi. Yaranta biyu a gidan, Habibu da mace, sai ƙaramin ciki da take laulayi. Tayi matuƙar tsanar Lubabatu a gidan, dan tafisu wayewa da cigaba. Ita tayi karatun boko har zuwa secondary kuma gana addini dan tayi sauka. Suko mafi yawansu musamman ma Talle kota allon bata nutsu tayi ba sai talla. Sosai matsi yayma Lubabatu yawa, dan matan ƴan uwan mijin nata sun haɗe mata kai bisa jagorancin Talle. Koda yaushe tana a ɗaki babu sakewa, idan kaga farin cikinta sai idan Umar na gidan. Ba kuma wai zaman nasa na hana ai mata abu bane, a'a farin cikin da yake bata a gidan ne kawai ke sauƙaƙa mata baƙin cikinsu. Ana haka ta samu ciki, haka taita rainonsa har lokacin haihuwa, sai dai ALLAH baiyi mai rayuwa bane wajen haihuwa ya rasu. Itama tasha wahala, wahalar data saka Umar roƙon mahaifinsu ɗaukarta su koma cikin Kebbi, dan kuwa tana naƙuda matan gidan babu wanda ya kulata wai ai bata gaya musu ba. Wannan yaja tasha wahala har ɗan ma ya rasu. Sai da Malam ya shigo gidan ne yake ji a wajen yara ransa ya ɓaci yasa aka kira wata unguwar zoma dake anan kusa da su. Ɗari bisa ɗari Malam Ibrahim ya basa goyon baya. Aiko ya tattara matarsa suka wucewarsu. Wannan abu ya baƙantama mutanen gidan rai sosai musamman irin su Gambo, sai dai basu da yanda zasuyi sai haƙuri. Komawa Kebbi tama Lubabatu daɗi matuƙa, dan hayar gida madaidaici Umar ya kama musu. Ya kuma nema mata admission ta koma makaranta. Alhamdullah komai Lubabatu na samu yanzu, bata da wata damuwa. Ga Umar abubuwa nata zama masa. Dan ya shiga harkar kasuwanci tako ina kuɗi ke shigo masa. Sosai yake ƙoƙarin taimakama mahaifinsa dama ƴan uwansa duk da basu taɓa nuna jin daɗin abinda yake musu ba, sai dai Haruna mijin Talle shi da yake dama tun can yana son Umar, kasancewar sun tashi ne a tare. Matarsa ce da mahaifiyarsu da ƴan uwansa kan canja masa tunani wasu lokutan. Amma a yanzu sai yake ƙin biye musu suka ƙulle da Umar ɗin har ya fara jan ra'ayinsa ya fara kasuwanci shima anan dai Giro ɗin. Abinda Haruna ɗin yayi ya ƙona ran matarsa da ƴan uwansa, amma ya nuna musu shifa babu abinda Umar yay masa dan haka babu ruwansa da ɗaukar ma kansa hakkin ƙuntata masa. Wannan abu da Harunan yayi yasaka mahaifinsu farin ciki, ya dinga saka masa albarka kuwa. Shaƙuwar Haruna da Umar tasa Umar ɗin cewa Haruna ya bashi Habibu ya saka shi a makaranta, babu musu kuwa Haruna ya bashi yana faman godiya. Sai dai rigima ta ɓarke dan Talle tace bata yarda ɗanta ya koma hannun maƙiyinta ba. Shi ko yace bata isa ba dan ya bashi kuma babu yanda zatai. Rigima tai rigima har Haruna yama Talle saki ɗaya, ya kuma ɗauki Habibu ya bama Umar. Sai da akaita roƙonsa Talle ta ma kusa gama idda sannan ya maidota. Rayuwar Habibu ta inganta, dan Lubabatu da zuciya ɗaya ta riƙe Habibu kamar ba uwarsa ce ba ta gallaza mata. Habibu ya fara boko da islamiyya, kuma Alhmdllh yana fahimtar komai Dan yaro ne mai ƙwazo. Yana son Lubabatu da Umar, dan yanda suke tattalin rayuwarsa har ji yake sunfi masa iyayensa, saboda Talle masifaffiyace har su ƴaƴan nata ba daɗi suke ji ba. Sai da Habibu ya kammala primary sannan ya fara zuwa Giro, dan malam ne ya saka wannan dokar saboda sanin halin uwarsa. Duk da cigaban da Habibu ya samo bai hana Talle nuna tashin hankali da son ganin ɗanta ya dawo gareta ba. Sai dai kuma babu yanda ta iya, dan Haruna ya tabbatar mata idan tai masa hauka sauran matan huɗu ma da take dasu zai kwashe ya bama su Umar ita kuma ya saketa. Wannan furuci ya tada mata da hankali dole tai shiru, amma ta koma yima Lubabatu habaici da gorin haihuwa dan ita tun wancan haihuwar bata sake ba har yanzu. Yanda take mata gorin haihuwa haka sauran matan gidan suma suka fara, sai ya zam sam kwanakin da sukai a Giro bai mata daɗi ba, bama su gama cika kwanakin ba tace ita dai zata koma. Haƙuri malam Ibrahim ya dinga bata kamar ba surukarsa ba. Ita kuma tace ba komai baba. Haka dai suka dawo Giro harda Habibu. Ashe ALLAH mai rahama mai jinƙai tana maƙale da ciki harna wata biyu. Ta raini cikinta cikin aminci da yarjewar UBANGIJI, babu kuma wanda yasan da shi sai da ya shiga wata takwas Baba Haruna yazo Kebbi ya ganta da shi. Ya taya ɗan uwansa murna matuƙa, yana dawowa Giro kuwa ya fasa zance. Ashe shi Baba yasan da cikin, dan Umar ya sanar masa amma yay shiru dan ya fahimci yanda Umar yake rayuwa a cikin yan uwansa da matansa, da yanda itama matarsa ke fuskantar ƙyara da hantara wajen surukansa. Aiko wannan batun ciki sai da ya ɗaga musu hankali, musamman Talle, dan da farko ma saida ta jefa cikin da mummunar kalmar data saka Haruna marinta. To babu dai yanda suka iya, haka ALLAH ya sauki Lubabatu lafiya, ta haifo ƴarta mace. Habib yafi kowa farin ciki dan ya samu ƙanwa. Giro baba yace su dawo ai suna, haka kuwa akayi duk da Lubabatu bata so ba, amma darajar baba zata iya yin komai. Shagalin suna akai na garari na faɗa aji, dan Umar ya kashe kuɗi batuƙa, ta yanda a lokacin kowama ya fahimci lallai ya kama ƙasa, dan lokacin tabbas kuɗi na shigo masa Alhamdullah. Sosai mahassada su kuma suka zuba hassadarsu, dan su Talle dai habaici suke. Wai ai ta banza, idan ana son nuna musu anyi kuɗin miyyasa bata haifi namiji Magaji ba. Babu wanda ya kulasu, dan sune jahilai. Bayan suna da sati ɗaya suka shirya komawa Sokoto saboda makarantar Lubabatu data Habib, amma sai Talle tai tsalle ta dire Habib bazai koma ba. Nan ma ubansa Haruna yace bata isa ba tayi kaɗan. Haka tana ji tana gani suka tattara suka wuce suka barsu da ƙunar zuciya...
Bayan haihuwar Asiya Lubabatu bata sake ko samun ciki ba, dan haka ta maida hankalinta akan yaranta biyu, wato Habib da Asiya. Gata suke musu matuƙa daga ita har Umar ɗin. Ga tarbiyya suna samu mai inganci. Sosai Habib ke son Asiya, dan ita yake kallo a matsayin ƙanwarsa uwa ɗaya uba ɗaya ba ƙannansa na Giro ba. Yakan je Giro ɗin, wani lokacin ma harda Asiya. Amma sam babu mai nunama Asiya soyayya sai baba kawai da Baba Haruna. Sai ko shi Habib ɗin dake zama yayta kaffa-kaffa da ita duk da kuwa hakan baya hana Talle dukanta da hantararta. Dan gaba ɗaya ƙiyayyar da takema Lubabatu da Umar ta koma kan Asiya yanzu. A haka Umar ya kammala karatunsa. Ya nuna yana sha'awar aikin ƴan sanda. Aiko babu musu Baba Umar ya sama masa. Ya fara aikin babu jimawa Asiya ta kammala secondary ta fara jami'a itama. Sai kawai Baba Umar ya yanke shawarar haɗasu aure, koda ya tuntuɓi Lubabatu murna tayi sosai, dan acewarta wa suke da shi bayan Habib ɗin dazai riƙe musu yarinya, Habib tarbiyyarsu ne hakama Asiya, suna ƙyautata musu zaton alkairi. Wannan magana tata ta ƙara masa ƙwarin gwiwa ya nufi Giro da batun. Anan ma Baba yayi matuƙar murna da sanya masa albarka, hakama baba Haruna. Amma sai Baba yace suyi shiru da zancen kawai sai ranar ɗaurin aure. To dama akwai bikin jikokin gidan da za'ayi har su bakwai, saboda yawan family ɗin da wahala kaga an tashi auren yara an aurar da ɗaya ko biyu. Hakan kuwa akayi, aka fara taron biki batare da kowa yasan dana Habib da Asiya ba. Har ita Asiya da Habib ɗin kuma. To dama yanzu indai za'a aurar da yara a gidan Baba Umar shike yin komai na hidimar batare da gajiyawa ba, duk da ƴan uwansa basu taɓa gode masa ba sai ma zaginsa akan kullum baya musu. Baba Haruna ne kawai mahaifin Habib ke ganin ƙyautatawarsa.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣0️⃣
______________