Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 44

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 44

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 44: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 44. ........Ba ƙaramin tashi hankalin kowa…

2,806 words

........Ba ƙaramin tashi hankalin kowa yayi ba lokacin da akaji a ɗaure-ɗauren aure harda Asiya da Habib, tab ɗin jan inji mata. Ai a ranar kowa yaga ainahin Talle a wannan gida. Tayi tujara ta fitar hankali, tai tsalle ta dire akan bata yarda ba kuwa. Aiko Baba Haruna yace idan bata yardaba kuwa sai dai itama ta koma gidansu da zama. Ansha rikici kam bana wasa ba, harma wanda basu san ainahin matsalar gidan ba da takurar da Umar ke fuskanta da iyalansa kowa ya sani yanzu. Baba ne dai yasa Baba Umar da Lubabatu da tsirarun danginta da sukazo biki, dan ƙanwartace ma kawai Shamsiyya da itama yanzu tayi aure a Kaduna harda yaranta biyu. Sai dai mijinta yana tafiya da ita Lagos shiyyasa sukan daɗe basu haɗu ba. Dama dai an tsara ma amarya da ango gidan zamansu anan Kebbi, dan haka can suka tare su. Sudai suna musu addu'a da fatan zaman lafiya da zuri'a mai albarka. Alhamdullah Habib na nunama Asiya kulawa, duk da kuwa a yanayin nasu kamar dai babu wanda ke son ɗan uwansa da kalmar soyayya sai dai ƴan uwantaka, kawai iyayensu sun musu shigar sauri ne tunda basu tambayesu ba. Amma kuma bazasu taɓa iya musu da su ba dan haka suka haƙura suka amshi juna kamar babu komai. A farkon zaman tarbiyya da ilimi ne kawai ke jagorantar zaman auren, amma a hankali sai Asiya ta fara son Habib, so kuwa mai tsananin gaske, tun bai fahimci ƙanwarsa ta faɗa soyayyarsa ba har ya fahimta. Dan haka ya sake ninka kulawar da yake bata. Bawai shima Habib baya son Asiya bane ba, yana sonta shima sosai, sai dai shi Talle mahaifiyarsa itace matsalarsa. Dan yana samun matsi a gurinta a duk sanda yaje Giro akan sai ya saki Asiya komai daren daɗewa. Irin wannan abubuwan yasa yake jin bai son zuwa Giro ɗin ma, Asiya kuwa tunda sukai aure bai yarda taje ba. Sai ya fake da karatun da take yi. Baba ne kakansu idan ya samu lokaci yana shigowa Kebbi, shima Baba Haruna haka, dama ko zasuso zuwa sai dai domin su. Itama dai Asiya ta mayi mahaifiyarta Lubabatu, dan sai da tai shekara biyar harta kammala karatunta ma da service sannan ALLAH ya bata ciki, babu irin tujarar da Talle batayi ba akan wannan rashin haihuwa amma kowa yay uwar watsi da ita har shi ɗan nata Habib. Dan yanzu ma ba'a Kebbi suke ba an maida shi aiki Zamfara can suke da Asiya. Sosai Baba Umar da Mama Lubabatu sukai farin ciki da samuwar cikin ƴar tasu, hakama kakansu Baba Ibrahim da Baba Haruna mahaifin Habib. Gambo kuwa sai taita aibanta cikin har sai da Baba ya tsawar mata. Ciki ya girma suka dawo Kebbi haihuwa, inda ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta haifo ƴarta mace mai kama da ita da kakarta Lubabatu. Babu ta inda yarinya ke kama da Habib gaskiya. Oho hakan bai damu Habib ba, farin ciki yake shima ya samu ɗiya jininsa. Hakama Lubabatu da Baba Umar da Baba Haruna suna farin ciki da samun jika. Giro aka koma akai suna saboda Baba, sunan daya haɗa hargitsi da farin ciki duk a lokaci ɗaya, dan kuwa Talle ana kai mata ƴa ko taɓawa batai ba sai cewa tai ba ƴar Habib bace, dan babu ta inda tai kamanni da shi. Wannan magana ta tada ƙura matuƙa, ƙura irin wadda a karo na farko Baba Umar ya zuba tsiya irin wadda ba'ayi zaton ya iya ba. Dan sai da Talle ta raina kanta kuwa. Murmushi Baba yay tayi dan shi kansa daya haifi Baba Umar bai san ya iya faɗa haka ba, saboda bayayi, shi mutum ne mai sanyi da nutsuwa. Wannan tujara da Baba Umar yayi tasa aka samu sassaucin ƙarasa taron gagarumin sunan lafiya. Ana kammala taron suna suka tattara suka koma, Habib ya wuce Zamfara yabar Asiya anan tana wankan jego ita da jinjirarta mai suna *_Shahidah_*, sai ya koma zuwa musu weekend har suka kammala wankan ta koma can Zamfarar wajensa. Bayan komawar tata ne ALLAH yay ma mahaifin mama Lubabatu rasuwa. Hankali tashe suka wuce Minna ita da Baba Umar. Wannan tafiya itace ta canja komai daga rayuwar Asiya Umar Ibrahim Giro (Ammie) itace ta canjata daga sarauniya ƴar gata zuwa baiwa da ƙaddarorin rayuwa suka zagaye, dan kuwa a hanya Baba Umar da Mama Lubabatu suma sukai haɗari, babu kuma wanda ya shura a cikinsu tun a wajen dan gawawwakinsu aka kawo Giro. Kamanta irin tashin hankalin da Baba da Baba Haruna da Habib da Asiya suka shiga ma ɓata lokaci ne. Dan Asiya komawa tai kamar ta zare ma. Sauran jama'ar gidan kuwa bazaka iya cewa ga abinda ke cikin zukatansu ba akan wannan rashi. Bayan rasuwar su Baba Umar da sati biyu shima Baba ALLAH yay masa rasuwa. Dan tun da yaga gawar Baba Umar da Lubabatu a kwance jikinsa ya rikice, abinka da dama ga tsufa. Asiya tayi kuka har ta rasa hawayen zubarwa. Dan tasan ta rasa dukkan gatanta a family ɗin su sai Baba Haruna kawai ya rage mata sai kuma Habib da ƴar ɗiyarta. Haka dai aka sha alhini komai ya lafa. Habib ya ɗauka Asiya dan su koma Talle tace bai isa ba, ai kuma Asiya ta dawo Giro da zama kenan. Hankalinsa yay matuƙar tashi hakama na Asiya. Gashi ta kafa matsa tsaurara dokoki ciki harda in Baba Haruna ya tambaya yace shine yace zai barta ta ɗan huta. Idan ba hakaba ALLAH sai ta tsine masa. Wannan kalma ta girgiza Asiya Ammie tace zata zauna kawai. Ta dinga lallashin mijin nata. Haka badan yaso ba ya shirya ya koma Zamfara ya barta a Giro. Rayuwa a Giro ga Ammie rayuwace mai tsanani da takura da damuwa. Tasha wahala matuƙa a hannun Talle da suke kira Gwaggo. Gaba ɗaya Ammie ta fita a hanyyacinta kamar bata taɓa shiga ajin makaranta ba. Ga Baba Haruna baya iya magana a yanzu saboda Talle ta danne masa kai a gidan teacher. Habib na zuwa weekend, amma bai isa sauka ɗakin Asiya ba. Ko da dare idan ya shiga domin kwanciya babu kunya Gwaggo ke zuwa ta buga musu tace ya taso ya koma ɗakin soro ya kwanta, inda ɗakin Baba kakansu yake. Haka babu yanda zai yi zai fito. Tom dai kuma UBANGIJI ya nuna mata ita bata isa hana abinda ya hukunta ba. Dan kuwa sai ga Asiya Ammie da ciki, gashi bata yaye Shahidah ba. Ta shiga tashin hankali, dan mutanen gidan ƴaƴa da iyaye sun tasata a gaba da zagi da habaici wai mayyar miji jarababbiya tayi gwanne. Abin kuma tsoro da firgici Gwaggo tace ai ciki bana Habib bane tunda ba kwana yake a ɗakin ba, dama ai Shahidah ma ba ƴarsa bace. Magana kamar wasa ta nema zama babba. Dan har gari ya ɗauki wannan zance. ALLAH gafurin rahimun sai ga Baba Haruna ya dawo hankalinsa a lokacin, dan kuwa asirin Gwaggo ya sakesa. Shine ya bama Asiya kariya har ya sake yina Gwaggo saki ɗaya. Ya rage saura igiya ɗaya a tsakaninsu kenan. Wannan saki shine fa ya sake haddasa wutar ƙiyayya tsakanin Gwaggo da Ammie. Da ƙyar dai Mahaifiyar Baba Haruna tasa ya dawo da Gwaggon dan ƴar ƙanwarta ce dama auren zumunci akai musu. Gwaggo ta dawo amma ta ƙara ninka ƙiyayyarta ga Ammie, sai dai a yanzu Baba Haruna na tsaye akan al'amarin Asiyar, dan ya ma fara shirin Asiya tabar giro tabi mijinta. Amma sai ta haihu kodan yanayin samun cikin. Haka Asiya taita rainon ciki cikin matsi da takurar surukarta. Ga Shahidah dake ta fama da ciwo. Babu mai taimaka mata a gidan har tsoffin gidan saboda Gwaggo ta zama boss ga kowa. ALLAH ya sauki Asiya lafiya ta sake samun mace mai kama da ita itama kamar Shahidah. Aiko Gwaggo ma ta sake aibanta jinjira tace ba ɗiyar Habib bace. Sai da Baba Haruna yay mata tas. Baba Haruna shine ya tsaya akan komai akai suna yarinya taci suna Lubabatu, amma sai suke kiranta Amaal koma ace Asiya da Habib ke kiranta. Dan su dai ƴan gidan Lubabatu suke cewa. Zuwa lokacin an ma Habib transfer zuwa Maiduguri. Dan haka ana gama bikin suna ya sake shirya komawa. Sai Baba Haruna yace ya ɗauki matarsa su tafi. Hankalin Gwaggo ya tashi akan hakan amma Baba Haruna yace bata isa ba kuwa Habib kamar ya tafi da iyalinsa ya gama. Hakan yama Habib daɗi, ya ɗauka Asiya da yaransa biyu suka wuce abinsu, suka bar Gwaggo na tujara. Wannan tafiya ita ce ta samawa Ammie sauƙi, suka koma Maiduguri da zama ta samu damar rainon yaranta cikin aminci, anan ta koya gyaran jiki da haɗin turarruka. Shekararsu biyu a Maiduguri aka sake masa transfer zuwa jihar Nasarawa. Nan ma ya kwashesu suka koma. Anan ɗin ma shekararsu uku aka sake maida shi Sokoto, zuwa lokacin kuma bata sake haihuwa ba. Yaransu Shahidah da Amaal sunyi ƙyau abinsu yara kamar ka lashe, dan Ammie ma ƙyaƙyƙyawa ce kamar mahaifiyarta. Dole kaga yaran nan sai ka tanka, dan kamar wasu ɗiyan hamshaƙin mai kuɗi bana ɗan sanda mai ƙaramin muƙami ba. Shima Habib yana son yaransa, sai dai irin mutanen nan ne shi da bai cika jan yaro a jiki ba, komai dai na buƙatar rayuwa yana tsaye a kansu. Dan ko ita Ammie bazata ce ga wata soyayya a bayyane da yake nuna mata ba. Baya dai takura rayuwarta ko hanata duk abinda take so, ba kuma ya nuna mata tsantsar soyayya a zahirance. Ga wanda ma bai sansu da ƙyau ba idan yaga rayuwar zamansu sai ya ɗauka tana a cikin matsin rayuwa ne. Sun tattaro sun dawo Sokoto, a lokacin Shahida nada shekara bakwai, Amaal nada shekara biyar da wasu watanni dan tsiransu da Shahidah kaɗanne. Saida sukai sati biyu a Sokoto sannan suka je Giro. Babu wanda bai firgita da canjawar Asiya da yaranta ba. Dan ta koma ƴar gayunta kamar batai rayuwar Giro ba. Tuni kishinta da hassada ya shiga zukatan jama'ar gidan kamar yanda suka dingama mahaifiyarta Lubabatu. A ɓangaren Gwaggo ma babu abinda ya canja, dan ƙiyayyar Asiya sai wacce tai gaba. Haka su Shahidah ko kallo basu isheta ba dan tace ita ba jikokinta bane ba uwarsu dai tasan inda ta samo su. Hakan na ma Habib ciwo amma baya cewa komai. A wannan zuwa kuma Gwaggo ta tsira sai Habib ya ƙara aure, dan a haifa masa namiji. Kai tsaye ya nuna mata bashi da wannan ƙarfin, dan shi dai bamai kuɗi bane, dukiyar da yake juyawa kuwa kowa yasan ta Asiya ce da iyayenta suka bar mata duk da ma dangin nasu sun kusa cinye rabi da kwata. Aiko ta tujaresa da masifa da bala'in daya sashi tattara matarsa da ƴaƴansa suka koma abinsu. Sai kuma suna komawar sai ga Asiya da ciki. Yayi farin ciki matuƙa, ya kuma shiga addu'a da fatan ALLAH yasa Asiya ta haifa namiji dan shima fa yana son a haifa masa namijin, ga maganar mahaifiyarsa ta sake kwaɗaita masa abun a rai. Kawai dan bashi da ƙarfin aure ne. Amma tabbas a ransa yana son ƙara auren ma. Dan yana ɗan neman mata batare da Asiya ta sani ba, tun kafin yay aure yake yi, bayan aurensu ya rage sosai sai dai kuma ita dama zina masifa ce. Faratane mara wuya, amma indai ka fara sai ALLAH ya soka da rahama kake dainawa. Ammie tayi rainon cikinta cikin aminci da kulawa, har ALLAH ya kai cikin watan haihuwa ta haihu lafiya. Ta samu ƴa mace ma a wannan karon. Sai da Habib yaji wani iri a ransa, sai dai kuma yana ɗaura idonsa akan yarinya yaji ƙaunarta ta shigesa. Dan ita kam tayo kamannin mahaifiyarta da ƴan uwansa, ta kuma yo kammaninsa ta bangarori da dama da suke a bayyane........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣1️⃣

______________

.........Wannan karon ma dai Giro suka koma suna, sai dai babu wanda ya nuna murna da wannan haihuwa kamar ta Amaal daga Baba Haruna sai uban jegon sai kuma su Shahidah dake murna an haifa musu ƙanwa. Wannan karon dai Gwaggo babu damar aibanta yarinya tunda tana kama da ubanta a abubuwa da dama. Amma hakan bai hana sako batun haihuwar ɗa namiji ba data fahimci yana tasiri a zuciyar ɗan nata. Haka dai akai bikin sunan babu wani armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin ta sauya ne. Dan yanzu ta ɗan rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ƴar sauran igiyar ɗaya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta ƙasa, dan Habib ta koma takuramawa akan sai ya ƙara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice. Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ƙara aure, dan ya samu damar sheƙe ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka haɗu anan Sokoto ɗin kwanan nan. Zama kamar wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk ƙarshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi ƴaƴanta. Cikin ƙanƙanin lokaci akasha biki kuwa, yarinya ƙarama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib ɗin ya dinga kiyaye duk wani abu da zai taɓa mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka ɗoro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a wajensa a ɗaki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki. Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har ɗaki ta sameta ta mata wankin babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya kuma murje idonsa ya sauka ɗakin Ammie, itako tanata roƙonsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga Gwaggo har ɗaki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa ɗanta gaba har ɗakin amarya Sailu. Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya, Habib kuwa irin mazan nan ne da basa ɗaukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a wajensa, Ammie ce kaɗai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu lokutan. To ataƙaice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan fa gari ta ɗauka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren amarya da mijinta, ƴan gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara ɗaya da rabi sannan akaima Habib transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin daɗinsa ne kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da kuɗin Ammie na gado, shine dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara ɗaya da wasu watanni da kaɗan ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san ƴan Giro ba....

________★★★

Readers Also Read