Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 46

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 46

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 46: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 46. ✨ZAFAFAN DAI ✨

3,243 words

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣3️⃣

______________

.........Sai da Aba yasha furar da Ammie ta kawo masa sannan suka zauna tattaunawa. Gently Ajwaad ya miƙe idonsa akan Maanal dake tama Aba surutun Giro har yanzu. Nuni ya mata data tashi, ta maƙe masa kafaɗa bakinta a sama. “A'a ni ban gama ba Aba labari ba. Ka zauna na ƙarasa masa sai muje na nuna maka su Hanne dake dukana ɗaya bayan ɗaya ka musu duka har ɗakunan uwayensu”. Harararta Ajwaad yayi, sai kuma ya sake tsuke fuska. “Idan baki taso ba ALLAH nan zan barki mu wuce ni da Aba”. Ai baima gama rufe baki ba ta miƙe zaram, sai kuma ta kalla Aba kamar zatai kuka. “Aba ai dai dani zaku tafi ko?”. Da ƙyar Aba ya gumtse dariyarsa da faɗin, “Sosai kuwa. Ai ƙafar bestynki ƙafarki har Kano. Oum ɗinku ma tace karna sake na baroki”. Sosai ta shiga dirga tsallen farin ciki, sai kuma ta nufi Ajwaad ta kama hannunsa. “Besty muje kafin Aba ya gama kama yaran can su Hanne jina-jina. Dan bazan tafi ban bar fuskokinsu da tabon da zasu dinga tunawa da ni ba, dole kuma asan Bestyna mai ƙarfin ILIYA ƊAN MAI ƘARFI YAZO”. Komai bai ce ba ya riƙe hannun nata shima suka fice. Kai kawai Baabu ya girgiza, yayinda Abah ya fashe da dariya. Ammie ma murmusawa kawai tai da jerama Maanal ɗin addu'ar shiriya a zuciyarta. Bayan sun tsagaita da zancen su Maanal Aba ya gyara zama yana fuskantar Ammie. “Ammien Amal ki kwantar da hankalinki, dan mun tattauna da su kuma ga shi Habib ya fahimta. Duk da dai an kai ruwa rana akan batun su Shahidahn gaskiya. Dan sai da nai katoɓarar nuna musu ai su Shahidahn nada mazaje a hannu, ba kuma su kowa bane sai yarana Fadeel da Fawzan sannan suka amince, amma da sharaɗin nan da wata shekarar za'ayi biki”. Cikin matuƙar mamaki da ruɗani Ammie ke kallon Aba da Baabu. Muryarta har harɗewa take wajen faɗin, “Amma Yaya sufa su Fadeel ba'asan ra'ayinsu ba”. “Ai basu ya dace asan ra'ayinsu ba Ammien Amaal. Su su Shahidah sune ya dace asan nasu ra'ayin saboda sune mata sune zasu zauna da su. Suko maza ne ai, sannan ni nasan daga Fadeel har Fawzan basu da bakin ƙin yarana zuƙa-zuƙa masha ALLAH, sai ma godiya ya kamata suma ALLAH da samun su a cikin sauƙi dan Shahidah da Amaal duk matan manya ne”. Ya ƙare maganar cike da barkwanci. Ammie zata sake magana Aba ya katseta. “Aifa magana ta ƙare Ammien Amaal, fatanmu ki saka albarka kawai dan ALLAH. Sai kuma batun shi Habib, ina son ki kwantar da hankalinki kiyi hakuri kiyi koyi da ƴar uwarki Fateema, zai ƙara aure bawai yana nufin ya bar sonki bane ba. Mu maza ALLAH ya saka mana son ku ku mata kuma fiye da ɗaya a zukatanmu. Wani lokacin ba gazawarku bace ba, daɗin zama da kune ke kawo hakan. Kiyi haƙuri kinji, in sha ALLAHU sai kinci ribar haƙurinki kuma na tabbatar miki bazan taɓa bari Habib ya wulaƙantaki ba. Shima kuma nasan bazai ko kwatanta hakan ba koda da wasa ma.” Ajiyar zuciya Ammie ta sauke a hankali, dan ta fahimci dai shi nashi auren na nan daram. Fuskarta da murmushi ta ce, “Wlhy babu komai yaya. Ni dama ba nashi bane damuwata. Karatun yaran nan ne da kuma banbanci wannan rayuwar da basu tashi a ciki ba. ALLAH ya sanya albarka ya bamu zaman lafiya baki ɗaya. Baga Aunty ba ita da Mamy ai kosu ababen koyine a gareni idan ma ban tashi naga mhaifiyata da abokiyar zama ba. Dan haka ku daina tausata ma dan bashine dalilin son kuzo ɗin ba”. “Na sani Asiya, ko shi Habib ya yabi ƙyawawan halayenki yanzu a gaban iyayenku, in sha ALLAHU kuma zakiyi nasara a rayuwarki”. Murmushi Ammie tayi, hakama Baabu. Sai kuma Aba ya haɗasu ya cigaba da musu nasiha su duka biyun. Daga ƙarshe yace shi zai wuce dan zasu kwana a Sokoto da safe su kama hanyar Kano in sha ALLAHU. Idan kuma sun sami jirgi a daren nan ma zasu wuce. Sai dai kuma da Maanal fa zasu koma bazai bar Auta a cigaba da dukar musu ita ba. Dariya sosai Ammie da Baabu suka sanya. Baabu ya ce, “Humm kaima kasan rigimar ƴar taka ai, ALLAH ta addabi kowa a gidan nan. Hatta da Gwaggo bata bari ba. Dan bata tsoron kurarin Gwaggo sam, shiyyasa kullum sai sunyi faɗa.” Sosai Abba ke dariya. Yana mai sake jinjina rashin jin Maanal. Dan shi dai a ƴar fahimtar da yayma Gwaggon a iya yau kawai yaga kamar tana da zafi sosai. Sannan rashin ƙaunar da takema Ammie da yaran nasu a bayyane suke. Dan da ƙyar fa aka tankwarata akan batun su Shahidah ɗin nan. Shiko batun auren Baabu cewa tai idan yace zai bijire sai ta tsine masa wlhy. Dan haka da sauri Abban yace ai bama za'ayi hakan ba wannan kam sun karɓa. Shi yana ɗauki alƙawarin yin komai. Shine fa aka rabu lafiya, koda yake ko yanzu da suka shigo sashen nan yana kallonta tana harararsa, dan suna yin sallama ta shige ɗaki abinta kamar bata gansu ba. Amma a hakan Aban yace zai shiga ya sake gaisheta. Badan Baabu yaso ba ya masa rakkiya har cikin ɗakin, anan ɗin ma sama-sama ta amsa musu duk da kuwa Aban na janta da hira tana basar da shi.....

★★

Maanal da Ajwaad kam koda suka fito haka ta dinga nuna masa yara abokan faɗanta, har cikin ransa yaso rama matan amma baba Haruna da ALLAH yakai idonsa ya janyesu su duka biyun zuwa ɗakinsa. Shi yayta jansu da labari bayan ya basu zuma da magani a cikin a wani ɗan ƙoƙo yace su sha duk da su basu fahimta ba sun ɗauka zumarce kawai. Daga Maanal har Ajwaad na matuƙar son zuma, dan wajen shi ma za'ace Maanal ta koya. Aiko hankali kwance suka hau sha, ko nace Ajwaad na sha yana bama Maanal Baba Haruna na musu labari. A haka Aba da Babu suka fito suka samesu. Maanal na jin zasu tafi ta fara kuka itafa sai tabi Besty. Babu kalar lallashin da Baba Haruna bai mata ba tace ina itafa sai Kano. Haka dole suka sake komawa cikin gidan aka shiryata tai sallama da mutanen gidan hannunta maƙale a cikin na Ajwaad. Dan ko shirin ma shine yay mata da kansa, su Amal ma dai da basu san yanda aka canja komai ba yanzu idanunsu duk sunyi ƙwal-ƙwal, ji suke kamar suyi ta Maanal ɗin amma babu dama. Zuma da dabino da mazarkwaila mai yawa Baba Haruna ya haɗama Ajwaad da Maanal na tsaraba. Haka aka musu rakkiya har cikin mota. Ko'a kwalar rigar Maanal bata damu da barin su Ammie da Babu da sauran ƴan uwanta ba, tana baya a tsakkiyar Aba da Ajwaad suka wuce tanata ɗagama ƙawayen faɗanta hannu dan tace sun shirya ta yafe musu😆..

__________★

Bayan wucewar su Maanal sabuwar tujara Gwaggo ta kafa a gidan, dan sai da taima Ammie zagin ƙare dangi na fitar hankali. Daga ƙarshe tace an sake matso da bikin Baabu nan da kwana huɗu juma'a kenan. Duk da abin na dukan Ammie haka ta dinga dannewa. Sai ta shiga ɗaki tai kuka. Dan ma yaranta na tausarta da lallashi dan Baabu kam ma dai takan yini bata sakashi a ido ba. Ba'a nan yake kwana ba. Tunda sukazo Giro bai kwana tare da ita ba. Ita da yaranta suke kwana, sai dai ya ɗan shigo musu a tsaitsaye saboda tsoron Gwaggo ma baya jimawa yake ficewa. Sai dai in suna buƙatar abu tai kiransa a waya. Idan kuma ya sayo sai dai a shigo da shi a ɓoye kosu Shahidah suje su amso su ɓoyo a hijjab. Maanal ce kawai ba'a ƴar haka da ita. Dan itafa bata tsoron Gwaggo. Idan tai mata tsawa ta murguɗa baki da ƙugu tai gaba abinta, haka Gwaggo zataita rantsuwar sai ta dake ta, sai ta sumar da ita. Duk kuma yanda zatai lambon kamata bata yarda, dan tsaf take cajama Gwaggo kai. Duk da taji haushin tafiya da akai da ita taji daɗi ta wani fannin, dan ta hutama da fitsararta...

Yau ɗin ma dai kuka sosai Ammie taci kafin ta dake zuciyarta, dan Babu tun daga rakkiyar su Aba har yau bai dawo gidan ba. Da alama ma Sokoto ɗin zai kwana....

_________★

Alhamdullah su Aba sun iso Kano lafiya. Duk da a lokacin anata shirin shiga sallar isha'i ne. Dan basu baro Sokoto ba sai da akai magrib. ALLAH ne ya taimake su suka samu jirgi mai zuwa Kano a daidai lokacin. Tuni Maanal tayi barci a jirgi, dole Ajwaad ya goyota suka fito tana a bayansa, sai Aba riƙe da ledar tsarabarsu dan ma sunƙi ɗakko kayan da yawa. Dan dama jirgi suka bi da zasu je. A sokoton ne abokinsa kuma ɗan uwansa ƙanin Oum amma cousin da suka fara sauka a gidansa ya bada mota driver ya kaisu Giro dan shi anan Sokoto yake zaune da iyalinsa. Aiki ne ya cillarosa nan kuma. Alhamdullah nan ma sun samu babban yaya (Fadeel) da drivern dake kaisu school na jiransu a airport ɗin. Yana hangosu yay saurin nufosu, shima baida yawan fara'a, dan halinsu kusan ɗaya da Ajwaad. A fuska ma sunfi kamanni, duk da dai su duka ukun suna tsananin kamanni da Abba da Oum, kasancewar su ɗin iyayen nasu aurene na zuminci, zumuncin ma na kusa kusa sosai, shiyyasa suke kamanni ɗaya, dan duk family ɗinsu haka suke da wannan kamannin. Su har alfahari suke indai ɗa na tsatsonsu ne koda an auro uwarsa bare baya ɗakko kamanninta sai nasu saboda ƙarfin jininsu. Koda Babban yaya ya gaishe da Aba ya maida hankalinsa akan Ajwaad da son taimaka masa ya amshi Maanal ɗin dake bayansa kansa ya girgiza alamar ya barta. Hakan ya saka Babban yaya da Aban yin murmushi kawai. A haka suka ɗinguma zuwa ga mota. Driver ya gaida Abba cike da girmamawa sannan suka shiga, Abba da Ajwaad da Maanal dake barci a kusan jikinsu su biyun na baya. Shi kuma babban Yaya ya shiga gaba kusa da driver. Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso gida, inda suka samu tarba daga Oum da Mamy da Fawzan. Sai dai Oum tayi mamakin ganin harda Maanal, dan batai tunanin zasu bari a taho da itan ba kamar yanda Ajwaad ke faɗin da ita zai dawo gida. Mamy dai bata tanka ba, dama kuma babu wanda yay tunanin tankawar tata dan dama haka take ita shiru-shiru. Ba komai ne zakaji bakinta a gidan ba. Garama idan suna hira da Oum ko Aba zaka jita cike da nishaɗi kamar ba ita ba. Amma akan yaran babu ruwanta da sabgarsu. Sosai take nuna kawaici da kara bama zaka taɓa tunanin tana da wata alaƙa da su ba... Ɗakin Oum Ajwaad ya kai Maanal, Oum ta taimaka masa ya kwantar da ita bisa gado. Kwanciya ta gyara mata da rufa mata duvet dan ɗakin akwai ac. Batare daya zauna ba ya ce, “Oum naje wanka, jikina duk babu daɗi”. Murmushi Oum ta masa, dan kowa yasan Ajwaad da tsaftar tsiya dama a gidan. Idan yana wani ƙalƙalin saika rantse ba yaro bane ƙarami ɗan shekara sha... Komai nashi zaka samesa kwaf-kwaf da kulawa kamar wani babban saurayi maji ƙarfi. Idan Ajwaad yay ado dole ka tsaya kallonsa. Sam bai damu da manyan kaya irin namu na malam bahaushe ba. Dan duk juma'a ma sai ankai ruwa rana da shi yake yarda ya saka. Garama idan Maanal ta saka masa rigima ta ɗakko da kanta tace ya saka sai ya saka. Dan duk da baya so Aba bai taɓa tsamesa a ɗinkin manyan kaya ba. Yanda akema su Fawzan da Babban yaya haka shima ake masa su, shiyyasa ya tarasu tab wadrobe yana ado dasu. Yana shiga ɗakin nasu Fawzan Sarkin tsokala ya fara tsokanarsa da dariya. “Ah-ah kaga baban soyayya, kaga Auta na Auta, Besty kuma na Besty. Wai yanzu nan dan ALLAH ko kunya baka ji ba Auta kaje gidan surukai ka ɗakko Lilly? Oh kai wannan wane kalar abin kunya ne haka?”. Harara ya ballama Fawzan ɗin yana wucewarsa bayi batare da ya tanka masa ba. Aiko Fawzan ya shiga kwasar dariya har sai da Babban yaya ya shigo ya tsagaita. Koda ya maimaita na Babban yaya dalilin dariyar daya tambaya murmushi kawai yayi shima, dan shi kansa soyayyar autan nasu da Bestynsa na ƙayatar da shi, da. Haka yana musu fata da addu'ar ɗorewa a haka har girma su kuma kasance ma'aurata kamar yanda kowa ke tofa albarkacin bakinsa akan dangantakar tasu.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣4️⃣

______________

.........Duk suna a d/table suna dinner Maanal ta fito tana faman murzar ido alamar yanzu ta tashi. Fawzan ne ya fara ganinta. Dan haka cike da shaƙiyanci ya furta, “Oyoyo Bestyn Auta, bada kanki a sare kije gida kice ya faɗi. Kaga surukar Oum da Abah”. Daina susan idon Maanal tayi ta tsaya tana kallon sa da farko kamar mai mamakin ganin kanta a nan ɗin. Yayinda suma duk suka zubo mata ido suna kallonta musamman Ajwaad. Oum kuwa da Abah murmushi suke yi, hakama babban yaya. Mamy kuwa kamar bata a wajen abincinta kawai take famar ci. Hannu Oum ɗin ta miƙo mata alamar tazo gareta. Da gudu kuwa ta iso ta shige jikin Oum ɗin, sai kuma ta saki kukan shagwaɓa. Shi ko Fawzan ya wani tuntsure da dariya yana faɗin, “Oh oh yau naga ikon rabbu surukar Oum shagwaɓaɓɓiya kenan, an dawo zakuma a ɗaura daga inda aka tsaya ko”. Rankwashi Oum ta kai masa sakamakon ɗagowar da Maanal tayi cike da taɓara da tsiwa ta ce, “Oum kinga Yaya F ko, kice ya daina ni Babynki ce ya bar cewa suruka bana son sunan”. Yanda tayi ɗin sai da ya bama kowa dariya. Dan shi kansa Bestien nata wani guntun murmushi ya saki kawai ya cigaba da kallonta. Ita ko ta cika tayi fam dan duk zatonta ma surukar wani mugun sunane da ake gudu. Gwalo Fawzan ya mata da faɗin, “Anƙi a daina ɗin, da wani bakinta kamar na tsuntsu”. Kuka sosai ta buɗe baki zata sanya, Abah ya saka hannu ya ɗauketa cak yana hararar Fawzan. “Kinga ƙyalesa kinji babyn Oum ɗinta. Kin san dama shi bashi da aiki sai neman faɗa da mutane in dai Fawzan ne. Shiyyasa ma bazanje da shi saudia ba sai ke da bestyn ki kawai”. Cike da farin ciki Maanal taima Fawzan gwalo da harara. Sai kuma ta hau murna za'aje dasu saudia ita da Bestyn ta. Da wannan lallashin Abah ya kashe rigimar, ya saka mata spoon a abincinsa sukaci tare...

Bayan sun kammala cin abincin ta gama tsiyaya musu surutunta Oum tajata zuwa ɗakinta tai mata wanka. Kaya gareta fal a gidan, anan ɗakin Oum da ɗakin su AA a cikin kayansa. Tana cikin shiryata Ajwaad ɗin ya shigo hannunsa riƙe da kayan tsifa. Tana ko kallon hannunsa ta ɓata rai dan bata ƙaunar kitso sam. Fuska a marairaice kamar zatai kuka ta ce, “Besty kaina na ciwo”. Harararta ya ɗan yi yana kaiwa zaune a bakin gadon Oum da faɗin, “Idan an gama zaki sha magani”. Sosai ta tura baki gaba, sai kuma ta kalla Oum dake gumtse dariya. “Oum dan ALLAH kaina bada zafi ba? Taɓa kiji ma”. Dariya sosai Oum ta fashe da shi tana taɓa kan, “Gaskiya Babyn Oum babu wani zafi, kanki yayi datti ki daure a tsefe kinji, jibi ƙasa a cikinsa tule. Ko baki son kuje Saudian da Abah yace?”. Jiki a sanyaye ta ce, “Ina so Oum”. “Yauwa ton daure kinji ƴar albarka. Ai Auta bazai miki da zafi ba kin sani ko? Gama chocolates bari na baki kije anayi kina ci baza kiji ma anayi ba har a gama”. Da wannan lallashin ta yarda badan taso ba. Haka suka fito hannunta ɗauke da ɗan bowl da Oum ta haɗa mata kayan kwaɗayi, ɗayan kuma Ajwaad ya riƙe mata. Tsakar gida suka fito tacan baya inda garden ɗin gidan yake, wajen akwai ni'ima sosai dan an gyara shi yanda ya kamata. Ga kujeru an shirya domin hutawa harda na yara, sai lilo da dai kayan wasan yara. Koda suka zauna sai da ya ɓare mata chocolate ɗin ya bata wayarsa sannan ya fara mata tsifar. A hakan ma yana farawa ta ɓata fuska zatai masa kuka. Sai da shima ya ɓata fuskar da faɗin, “Oh nacema Abah ɗin mu wuce mu barki?”. Da sauri ta girgiza masa kai. Ya ce, “To oya malama nutsu”. Baki ta tura gaba da faɗin, “Niba sunana malama ba”. Murmushi yay a karo na farko, tare da jan hancinta ya ce, “To Bestyn bestyn ta ko?”. Cike da jin daɗi ta ce, “Yes”. Ƙaramar dariya yayi, sai kuma ya buɗe baki alamar ta bashi chocolate ɗin. Cirowa kuwa tai ta saka masa a bakinsa, ganin ya ɗan ɓata mata yatsun yasa shi kama hannun nata ya lashe wadda ta maƙale. Murmushi tai da faɗin, “Kwaɗayi”. “Ai ke kika koya min”. Ya bata amsa yana murmushin shima. Sannan ya fara mata tsifan. Tana kallon cartoon ɗin daya sanya mata tana masa surutu da juyowa ta bashi chocolate ɗin da sauran kayan ciye-ciyen. Shi ko yana biye mata. Dama in kaga Ajwaad na zuba surutu da murmushi to lallai Maanal na a wajen kuwa tabbas. Baya wasa da al'amarinta ko kaɗan. Idan ka gansu dole su birgeka kamar ba yara ba. Haka dai aka gama tsifan, wajen taja kuma aka hau faɗa, sai da ya riƙeta da ƙyau sannan ya iya taje mata, ita ko tana kuka da faɗin babu ruwanta da shi kada ya sake kulata. Dariya ya dinga yi shi dai bai kulata ba sai da ya gama ya ɗaure mata da ribbon duk da yayi datti. Dan cikinsa uban ƙasa ne na faɗan data dinga kwasa a Giro, a hakan ma wai kusan kitso na fin biyar ne akan nata a zuwansu. Koda suka dawo cikin gidan fushi ta dinga masa, sai ta koma kula Fawzan shiko Ajwaad ɗin ya sharesu. Hakan da yake yi idan tana tare da wani a cikinsu yake sa suke faɗin suma yana kishi da su akanta..

_____________★

Readers Also Read