Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 47
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 47: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 47. Washe gari suna gama breakfast Ajwaad…
3,365 words
Washe gari suna gama breakfast Ajwaad ya tasa Maanal gaba zuwa wajen kitso. Ita ko tana faman kuka da faɗin bafa zataje ba. Sai da ƙyar Oum ta lallaɓata ta yarda bayan ta mata alƙawura. Koda suka fito tsakar gida inda ɗan kekensa yake sai da ya hau itama ta hau daga gabansa tanata cika baki da iska. Shi dai bai kulata ba yaja keken suka fito. Ai tun daga gida har zuwa shagon Aunty Saloon duk inda suka gitta sai an musu magana. Dan Maanal fa cele ce a anguwar tasu saboda tsabar fitinarta da neman faɗa. Yara ɗai-ɗai ne batai rigimar da taja Ajwaad ya jibgesu ba. Da farin ciki Aunty Saloon ta tarbesu tanama Maanal oyoyo da dawowa. Itako ta ɓata fuska taje jikin Ajwaad ta maƙure idanunta cike da ƙwalla. Dariya Auntyn ta fara yi da faɗin, “Maanal ke baki girma da ƙin kitso? Haba ƴar gatan Ajwaad Bestyn ta. Shi gashi yana son yaga ana gyara masa ke da kitso ke kuma baƙya so”. Baki Maanal ta sake turawa gaba da kallon Ajwaad, shima kallon nata yake yi. Sai ta sake ɓata fuska zatai kuka. A hankali ya kai durƙushe gabanta ya dai-dai tsahonsu hannayensa duka akan kafaɗarta cike da lallashi ya ce, “Ba kin min alƙawari bazakiyi kuka ba? Ko kina son yaran anguwar nan su ganki su samu abin raina ki da tsokana”. Kanta ta girgiza masa hawayen dake cike a idonta na gangarowa. Hannu yasa ya share mata, “To kada na ƙara ganin hawayen nan. Inba hakaba kuma na fasa shiga secondary ɗin tare dake”. Da sauri ta haɗiye kukan, cikin rawar murya ta ce, “To bana bari ba”. “Yauwa my sweet Besty. Faɗa min mi kike so naje na saya miki? Ko awaran can?”. Ya nuna mata waje can tsallaken titi da mai awara ke ta soyawa. Kanta ta jinjiina masa. Shima sai ya miƙe tare da kama hannunta ya kaita saman kujerar wanke kan ya zaunar, fita yayi tana kallonsa daga nan. Bai wani jima ba ya dawo da awaran a leda. Lokacin har Auntyn Saloon tayi shirinta na fara wankema Maanal ɗin kai. Dan duk ta fito da kayan shampoo ɗinta da suka zo dasu a cikin ƴar bag. Haka komai na Maanal a tattale yake ga Ajwaad. Sam bai yarda a mata amfani da kayan wankin kan wajen saloon ɗin ba, duk abinda yasan ana buƙata idan sukaje shopping da Abah ke kaisu duk ƙarshen wata zai ɗakkosa. Dan shi dama ko a wajen shopping ɗin zakaga duk abubuwan da yake ɗakkowa na Maanal ne. Ƙalilan zaka samu nashi. Kujera ya jawo gabanta sosai ya zauna, dan yasan bazata yarda ba sai anyi darun. Bai bata awaran ba ya ajiye gefe yacema auntyn Saloon ta fara. Kuka Maanal ta fara ƙoƙarin farawa ya girgiza mata kansa, sai tai shiru. Haka dai aka wanke kan yana riƙe da hannunta da lallashi kamar wata ƴar mitsilar yariya can ba ƴar shekara kusan takwas ba. Koda aka gama shi da kansa ya goge mata kan da towel ɗin da sukazo da shi ya ɗaure mata shi, sannan ya dinga bata awaran a baki ana busar da kan. Da aka zo kitso kam daru aka sha na haƙiƙa, dan dole sai da ya riƙeta, amma a hakan yasha cizo a hannu da bibbigewa. Kitson ma ba wani mai yawa ba dan shikku ne. Sosai ya mata ƙyau aka saka mata bet. Maanal akwai gashi Masha ALLAH, dan sun biyo Ammie ne cikar gashi da tsaho kamar ba nasu ba. Sai faman sauke ajiyar zuciya take idanu sun yi jazur saboda kuka ta kama hannunsa tana dubawa, dan duk sayin ƙananun haƙwaranta. Sake fashewa tai da kuka tana shafa cizon da kallonsa, shima idon nasa duk ya kaɗa saboda kukan nata. A hankali ya ce, “Minene kuma? Ba'an gama ba?”. Hannunta na bin wajen cizon ta ce, “Da zafi ko? Muje na amshi magani wajen Oum na baka”. Murmushi yay mata da girgiza kansa, sai kuma ya shafa kitson nata da yay ƙyau sosai ya ce, “Babu zafi fa. Jiba yanda kanki yay ƙyau. Ya kamata ki daina kukan kitso Besty kin girma.” “To ai Oum ta ce idan na girma zan daina ”. “Wane girma kuma ya rage Besty. Secondary fa zamu shiga ai kin girma ko. Ba kiga ni idan kika rakani wajen aski bana kuka ba”. A sanyaye ta ce, “Zan bari. Besty muje gida zanyi barci”. Kansa ya jinjina mata tare da miƙewa. Cikin girmamawa ya kalla Auntyn Saloon dake kallonsu cike da sha'awa da mamakin irin wannan al'amari tamkar ba yara ƙanana ba. Godiya ya mata ya ɗauka bag ɗin sannan ya duƙa Maanal dake faman lumshe ido ta hau bayansa. Kekensa ya kalla sai kuma ya kalla Auntyn Saloon ɗin. “Aunty zanje na kaita sai na dawo na ɗauka”. “To babu damuwa Ajwaad sai ka dawo. Ka gaishe da Hajiya. Maanal daru sai kuma next”. Maanal dai bata kulata ba, sai ma sake lafewa da tai a bayansa dan barci take ji sosai. Tana fita wanda ke a cikin shagon suka fara gulma. Aunty Saloon dai dariya take yi da sake basu labarin wannan shaƙuwa ta Maanal da Ajwaad dake birge kowa a layin tamkar ba yara ba...
Kafin su iso gida har tayi barcin. Oum da Mamy na falo suka shigo. Muskar Oum da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Ai na sani dama da barci zaku dawo gidan nan. An sha darun ma yau kenan?”. Fuskar Ajwaad da murmushi shima ya ce, “Tab Oum miza'a fasa. Duk na sha cizo”. Dariya Oum ɗin tayi da faɗin, “In ba Bestien taka ba wazai cijeka a zauna lafiya Auta. Maza jeka ka kwantar da ita to”. Ɗakin Oum ya kaita ya kwantar, sai da ya rage acn ɗakin ya cire mata ɗab hijjabinta sannan ya fito. Oum na tambayarsa ina kuma zaije yace zai ɗakko kekensa ne. Daga haka ya fice. Mamy dai bata saka musu baki ba. Yana kuma fita suka ɗora da hirarsu da suke yi ita da Mamyn hankali kwance cike da farin ciki kuma kamar ba kishiyoyi ba. A haka Ajwaad ya sake dawowa ya samesu. Ɗakinsu ya wuce yana tambayar ina su Fawzan. Oum tace sunje aikan datai musu ne. Daga nan zasu duba malaminsu na islamiyya suji yaushe zasu koma. Dan tun wancan satin ya kamata su koma matar ya sayyadin ta haihu, haihuwar kuma tazo da matsala shine ya ƙara hutun, sai dai bai sanar da ranar komawar ba taka maimai. Ciki ya shige suma su Oum ɗin suka miƙe dan lokacin salla yayi.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣5️⃣
______________
.......Abah bai samu zama da su Oum ba sai daren yau akan batun daya faru a Giro. Komai bai ɓoye musu ba daya faru A to Z har hukuncin daya yanke akan Fadeel da Fawzan. Sosai tausayin Ammie ya sake baibaye Oum. Dan tamkar ƙanwa uwa ɗaya take jin Ammie a ranta ba maƙwafciya kawai ba. Ɗari bisa ɗari kuma ta bada goyon baya ga hukuncin mijin nasu. Ta kuma yabama dattakonsa. Itama dai Mamy ta jimanta al'amarin ƙwarai da gaske. Akan batun yara kuwa ta nuna kawaici kamar yanda ta saba. Daga ƙarshe ma miƙewa tai tana faɗin, “Wannan maganarku ce Oum, mu ƴan ALLAH ya sanya alkairi ne”. Daga haka ta fice tabar falon. Da kallo duk suka bita. Kowanne na sake jin ƙaunarta a cikin ransa daga Oum ɗin har Abah. Mamy abar alfahari ce a garesu, dan suna matuƙar alfaharin shigo da ita cikinsu. Tana da wasu irin nagartattun halaye masu matuƙar ƙayatarwa a zahiri. Oum da Abah sun cigaba da tattaunawa, kafin suma su miƙe bayan sun gama yanke yanda zasu fahimtar da yaran nasu batare da sunga an ƙasƙantar da su Shahidah a idanunsu ba.
A ɓagaren Mamy kuwa koda ta shiga ɗakinta kasa tsaye da zaune tayi. Ta jima a haka kafin ta ɗauka waya tayi kira. Ba'a wani jimaba kuwa aka ɗaga. Sallama tayi tana kaiwa zaune. Sai kuma ta ɗora da gaisuwa. “Yaya mutanen nan ban san mi suke so dani ba. Shike nan ni bani da wani ƙarfin iko akan ƴaƴana ma. Daga mijin har matar kamar tare suka auro ni? Nifa na fara kaiwa gaɓar da zan nuna ma matar nan ina buƙatar ƴaƴana nima. Sai dai ya sakan ko itama tayi zuciya ta haifi nata.......” kuka ya sarƙeta. Numfashi aka sauke mai nauyi daga can, kafin cikin isa a furta, “Kamila! Dama wannan shine abinda aka dinga guje miki tun farko. Amma kika kasa fahimta soyayyar mutumin nan ta rufe miki idanu. Daga baya aka sake nusar dake illar sakar mata yaran nan tun suna zanin goyo nan ma kika kasa fahimta ke wai neman soyayyar miji. Ai gashi nan, ƴaƴan da mijin duk suna a hannunta ke baki amfanu da komai ba sai baƙin ciki da damuwa. Kin san wacece Hajiya Fateema kuwa akan mijin nan nata? Dukkan fa bincike sai da nayi a kansu. Akwai matsananciyar soyayya da shaƙuwa a tsakaninsu tun ta ƙuruciya. Tun fa tana ƴar shekara goma sha a duniya aka aura masa ita. Shi ya raineta, gida ɗaya suka tashi, shi ya koya mata komai taya dama kike tunanin zaki shiga wannan gidan ki samu farin ciki? Haihuwa da kike ganin bazatayi ba? Humm irin su Alhaji Aliyu Darma da kike gani ba wannan bane a gabansu....” “Yaya ni dai naji. Koma minene dai ya riga ya faru ai. Kawai yanzu ina buƙatar dawo da yarana hannuna kota ƙarfin tsiya. Musamman Ajwaad. Wlhy yaron nan yi yake tamkar ma bai san muna da alaƙa ba. Har tayata kishi yake fa. Dan ALLAH ki taimkeni”. “Hummm ai wannan yaron taƙadari ne daga gani. Kuma ba kowa ya busar masa da zuciya ba sai ita. Ga shegiyar yarinyar nan da suke ƙalatar juna ƴar maƙwaftanku, kai na tsani yarinyar nan da uwarta wlhy saboda aminiyar Fateema ce”. “Wlhy Yaya na fiki tsanar Asiya. Dan haka koma mi za'ayi sai dai ayin wannan haɗin auren bazai yiyu ba. Sai kace ma ita na haifamin ƴaƴan kenan”. “A da'alama kam ita ɗin kika haifamawa. Ba kuma makircin kowa bane sai na Hajiya Fateeman. Kinga idan yaran sun auri ƴaƴan Asiyar ai itace zata cigaba da juyasu ko. Ke wannan fa ƙulline babba wlhy. Amma karki damu zamuyi maganinsu. Kizo ki sameni gobe”. “Aunty sai dai weekend. Dan yanzu ina cemasa zan fita zai iya zargin wani abu kin dai sanshi da kaifin tunani. Amma weekend zan tambayesa zuwa kitso sai na zo”. “To hakan ma yayi ALLAH ya kaimu. Kidai kwantar da hankalinki”. “Humm Yaya kenan, amma in sha ALLAHU zan yi ƙoƙari sai anjima”....
___________★
SU WAYE SU OUM?.
Abah da Oum jini ɗaya ne. Makusanta sosai dan kuwa da mahaifiyarta da mahaifinsa uwa ɗaya uba ɗaya suke. Kunga kenan su cousins ne. Asalinsu ƴan jihar Adamawa ne, a wata ruga da ake kira RIGAR DARMA. Baffa Ishaq Darma da Gwaggo Halima sune tushen zuri'ar. ALLAH yayma Baffah Ishaq Darma arziƙin kiwo da noma matuƙa gaya. Dan yana da shanaye, tumaki, awaki, raƙuma, harma da dokuna da shi kansa bai san adadinsu ba. Sannan yana noma da ake kira noma ba wasan yara ba tun duniya na kwance. Yaransu huɗu. Mata biyu maza biyu. Abubakar shine babba, suna kiransa da suna Sardauna. Sai Umar, sai Maryam, sai auta Khadijah. Baffah Ishaq baiyi karatun boko ba daga shi har matarsa. Amma hakan bai saka ya tauye yaransa ba daga yi. Su duka sunyi karatun boko mai zurfi har matan. Kafin Sardauna ya fara aure bayan kammala degree ɗinsa na farko. Ya auri ƴar aminin Baffa Ishaq da yakema kallon tamkar ɗan uwa. Ansha shagali matuƙa irin na nunama tsara a wancan lokacin, amarya da ango suka tare acan cikin garin Adamawa. Bayan auren Sardauna da kusan shekara huɗu sannan Umar shima yayi tare da Maryam a rana ɗaya. Shima Umar ya auro ne daga ɗiyar dangi anan cikin Rigar Darma, ita kuma Maryam aka aura mata wani ɗan Alhaji da suke huɗɗa da baffah tsahon shekaru. Yana zuwa ya sayi dabbobi masu yawan gaske a duk ƙarshen shekara, a hankali zuminci ya ƙulle tsakaninsa da Baffan har suna kallon kansu tamkar ƴan uwa (mutanen da kenan masu girmama alkairi). Shi wannan Alhaji dai yana zuwa daga jihar Kano ne, asalinsa kuma ɗan garin Kura ne. Ɗansa ɗaya tal a duniya mai suna Kasheem. Yana karatu a turai. Yazo wani hutu gida Nigeria ya biyo babansa nan Adamawa shine ya ga Maryam itama a lokacin tazo hutun makaranta daga Yola. Aifa yace yaga mata, Baffa kuma yace ya bashi halak malak. Ansha biki nan ma na nunama tsara, Umar ya tare da matarsa anan Rigar Darma, ita kuma Maryam aka wuto da ita Kano. UBANGIJI mai hikima shakara ɗaya tak ALLAH ya sauki matar Umar lafiya, har kuma lokacin yayan su Sardauna ALLAH bai bashi haihuwa ba shi. Dan matarsa ko ɓatan wata ma bata taɓa yi ba. Kaf family sunyi murna, sun kumayi farin ciki, an sha shagalin suna shanaye sun sha wuƙa da ƙananun dabbobi yaro yaci suna Aliyu (Abah kenan😂👍). UBANGIJI mai rahama matar Abubakar bata yaye Aliyu ba sai ga wani cikin. Dole aka cire Aliyu daga nn, sai kawai matar Sardauna ta amshesa ta yaye. Daga wannan yaye ne kuma bai sake dawowa wajen iyayensa ba su Baba Sardauna suka cigaba da riƙo tunda su har lokacin ALLAH bai kawo iyaka ba. Matar Umar ta sake haihuwar namiji yaci sunan Hamza, shima bata yaye ba ta kuma samun wani cikin. A taƙaice dai sai da ta jera yara huɗu duk maza sannan itama Maryam ALLAH ya kawo ciki. A kusan tare kuma suka sake haihuwa da matar Umar da tai mace a wannan karon. Itama dai Maryam ɗiya mace ta haifa da taci suna Fateema (Oum kenan😂👍). Itama Maryam matar Babban Yaya wato Sardauna suka kawoma yayen Fateema. Bakuma su sake waigawa ba dan a lokacin ne ma suka bar ƙasar. Hakan da sukai na nufin suma sun barma Sardauna Fateema har abadan. Wannan abu ya saka Sardauna da matarsa kukan farin ciki da sake jin ƙauna da soyayyar ƴan uwansu. Basu haihu ba amma gashi suma sun mallaki ƴaƴa. Bayan nan itama Auta Khadijah tayi aure anan cikin garin Adamawa. Itama kuma babu jimawa ta fara haihuwar. Itama kuma ɗanta na fari haka ta mallakama Sardauna shi kamar yanda sauran ƴan uwanta biyu sukayi. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH fin shekara goma sha sai ga matar Sardauna da ciki. Zamu iya cewa wannan zuri'a basu taɓa tsintar kansu a irin farin cikin da suka samu kansu ba na wannan tsakanin. Dan tuni Maryam ta baro ƙasar waje tazo gida Nigeria. A lokacin yaranta biyu da Kasheem Kura bayan Fateema da sukai ƙyauta. Majdiya, Sulaiman. Itama Khadijah nada biyu bayan Sa'eed da sukai ƙauta ma Sardauna. Sai matar Umar nada biyar bayan Aliyu da sukaima Sardauna ƙyauta suma. Ansha matuƙar shagali da bidiri na wannan ciki har ALLAH ya kaishi haihuwa aka haifo ƴan biyu duk maza. Kwantata muku irin shagalin da akai ai bashi misaltawa. Musamman Aliyu da Fateema da Sa'eed da akai ƙanne. Zuwa yanzu Aliyu ya fara zama saurayi, dan yana da shekara kusan goma sha bakwai a duniya. Yayinda Fateema keda goma sha ɗaya cif. Akwai wata irin shaƙuwa da ƙaunar juna a tsakanin Fateema da Aliyu mai ban mamaki. Sun tashi tamkar wasu tagwaye duk da Aliyu ya bata shekaru sosai. Soyayyar ce mai ƙarfi irin wadda zaman rubutata ma jan lokaci ne. Gashi suna matsanancin kamanni dan ita Fateema ta ɗebo dangin mahaifiyarta ne gaba ɗaya. Sauran yaran Maryam kuwa sun biyo mahaifinsu Kasheem Kura sosai. Hakama yaran Umar ƙannen Aliyu kaf ɗinsu sun ɗebo gida ne, babu wanda ya biyo mahaifiyarsu, suma yaran Khadijah duk suna kamanni da danginta. Sai su ƴan biyu. Wannan yasa suke jin alfahari akan su jininsu nada ƙarfin da suke ɗebo kamannin gida ne. Yanda su iyaye ke kamanni da juna haka suma ƴaƴan duk suka ɗebo. Hatta da yaran Maryam dake kamanni da mahaifinsu sun ɗebo wasu abubuwan nasu, ita dama Fateema gaba ɗayanta sune. Soyayya da shaƙuwar Aliyu da Fateema yasa Baffah Ishaq bama ƴaƴansa shawarar haɗe yaran aure saboda gudun shaiɗan a tsakaninsu, dan shaƙuwar tayi yawa matuƙa komai zai iya faruwa. Babu kuwa wanda yayi musu akayi hakan. Fateema nada shekara goma sha biyu da wasu watanni, Aliyu nada goma sha tara da wasu watanni aka ɗaura musu aure. Akai kuma shagalin biki irin na gata sai dai sun tare anan gidan Baba Sardauna ɗin dan yace yaransa bazasuyi nesa da shi ba. Balle kuma gasu yara ƙanana basu kai ƙwarin da za'a barsu su kaɗai ba tukkuna. Soyayya ta ƙara ƙarfi a tsakanin Fateema da Aliyu, yayinda a gefe suke ta karatunsu ga kuma kulawar iyaye. Aurensu nada shekara uku ALLAH yayma gwaggo Halima rasuwa. Kaf wannan zuri'a ta Darma sunji wannan mutuwa matuƙa, sunyi kuka har sun rasa hawaye musamman ma Baffa Ishaq Darma daya rasa mata ƴar uwa uwar ƴaƴansa. Bayan rasuwar tata kuma shima duk sai lafiya tai masa ƙaranci. Shekara biyu tsakaninsu shima yace ga garinku nan. Matuƙar ruɗani wannan family sun sake shiga, har takai Baba Sardauna da Baba Umar sun kasa jin daɗin zaman garin Adamawa sukayo hijira zuwa Kano. A lokacin shekarun auren su Aliyu biyar cif a duniya. Fateema nada sha shida, Aliyu nada ashirin da uku. Ya kammala karatunsa na jami'a, ita kuma zata shiga ss a sakandire. Shekarar da Fateema ta kammala sakandare a shekarar ALLAH ya bata ciki. Murna da farin ciki ba'a magana. Dan wannan zuri'a na matuƙar son haihuwa. Sosai cikin ke bata wahala, kullum tana nane da Ummanta. (Matar Sardauna) Dan soyayya take musu ta haƙiƙa da sam bama su san ainahin ba itace mahaifiyarsu ba sai lokacin da akai musu aure. Hakan kuma bai sa sun canja daga soyayya da ƙaunar da suke mata ba. Itama kuma haihuwar da tai baisa ta sassauta soyayyar da take musu ba a matsayin ƴaƴa har gobe. Haka dai akai wannan rainon ciki Fateema kullum na sashen iyayensu. Har abun na damun Aliyu dan idan yana son ya kasance da ita sai yayi mata wayo da ƙyar tazo nasu sashen da aka ware musu a gidan. A haka ALLAH ya kai wannan ciki lokacin haihuwa. Sai dai yazo da doguwar naƙuda. Tun ana hasashen haihuwa a kusa har al'amarin ya fara bama kowa tsoro aka yanke shawarar yimata theater. A wancan lokacin matuƙar tsoron theater akeyi dan kodai a rasa ɗa ko a rasa uwa. Dole da wahala cikin biyun nan ɗaya bai kasance ba sai idan duk suna da tsohon kwanan ne uwar da ɗan. Aliyu kuka ya sanya akan bai amince ba, sai da likita yayta lallashinsa da su Baba Sardauna sannan da ƙyar ya amince aka shiga theater da Fateema.......✍️
_(Ina fatan dai kuna gane kan labarin😆. Fateema itace OUM a yanzu, Aliyu ne ABAH a yanzu😂👍)._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000
0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣6️⃣
______________