Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 48

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 48

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 48: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 48. .........Alhamdullah bayan dogon zaman…

2,818 words

.........Alhamdullah bayan dogon zaman jira da fargaba da kasancewa a tashin hankali an samu nasarar ciro yara ƴan biyu a jikin Fateema duk maza. Sai dai ɗaya bashi da rai, rabin jikinsa ma har ya ɗan fara ruɓewa. Wannan yanayi ya saka farin ciki da alhini a wannan zuri'a duk a lokaci guda. Sai babbar damuwarsu sanin halin da Fateema ke a ciki kuma. Dan Doctors ɗin dai since su basu lokaci. Haka suka sake koma a yanayin damuwa da taraddadi musamman ga Aliyu har zuwa washe garin safiyar ranar. Dan wajen ƙarshe sha biyu aka samu nasarar farfaɗowar Fateema. Dama wannan shine tsaikon da likitocin suka samu na zahiri. Zuwa yanzu kam kowa ya warware, farin cikin kowa ya fito a bayyane, anatama juna barga da addu'a ga jaririn da ya rage, wanda ma bai zo da ran ba ana masa addu'a.....

Watan Fateema ɗaya cif a asibiti aka sallesu, jikinta da sauƙi sosai, sai dai yanayin cs na wancan lokacin ba dai-dai yake dana yanzu na zamani ba. Sai ya kasance wasu tsarabe-tsarabe kan biyo baya da har mutum kan iya ɗaukar dogon lokaci yana mafa da jiyya sama-sama har komai ya zama normal. Zuwa lokacin tuni an raɗa sunan jariri da aka barsa da sunansa wato Hussain. Dan Hassan ɗinne baizo da rai ba kasancewar shi aka fara cirowa. Raɗin suna kawai akai, sai bayan sallama aka shirya taron suna. Ansha shagalin kam mai birgewa da nunama tsara, sai dai maijego na dauriyane kawai dan sam bata jinta cikin isashiyar lafiya har lokacin. Sai dai bata son ɗagama mijinta da ƴan uwanta da iyayenta hankali, shiyyasa ta cigaba da daurewa har taro ya tashi lafiya ta cigaba da wankan jegon da Umma ke mata da kanta. Wato matar baba Sardauna. Sun gama wankan jego lafiya, dan kusan ma arba'in biyu sukayi, ta ɗan zaga dangi harda Saudiya ita da Aliyu sukayo sati uku sannan suka dawo. Abin ƙaddara satinsu biyu da dawowa Hussain ya fara wata mura mai ban tausayi, murar fa ko numfashinsa da ƙyar yake fisga. Hankali tashe suka wuce asibiti da yaron, sai dai UBANGIJI shi mai hikima ne, a daren shima yabi ɗan uwansa. Kuka rurus Aliyu ya dinga yi, amma a mamakin kowa Fateema ko ɗigon hawaye, sai ma ta koma itace ke lallashin mijin nata kuma ɗan uwanta. Bayan rasuwar Hussain da kusan wata biyar sai ga Fateema ta fara laulayin sabon ciki. Murna a wajen Aliyu ba'a magana ko kwatantawa. Hakama sauran ahalinsu kowa na fatan alkairi da addu'ar ALLAH ya inganta. Sosai wannan ciki yazo ma Fateema da tsanani fiye dana ƴan biyu, dan bata sati guda a gida sai a asibiti, ƙarshe dai suka riƙeta a asibitin domin samun bedrest. Dan haka kawai saita dinga bleeding, doctors sunyi iya ƙoƙarin ganin sun shawo kan matsalar amma al'amarin ya gagara, har takai mahaifin ta dake matsayin babban likita a saudia wato Kasheem Kura ya nufo Nigeria da kansa. Shine ya tsaya akan matsalar, inda ya fahimci ƴar tasa tana fuskantar babbar ƙaddarane mai girma. Ya shiga tashin hankali amma haka ya daure ya jure ya fito fili yama uban riƙonta da uwar riƙon ta da mijinta bayani akan dole ne fa a raba Fateema da wannan ciki, dan sam mahaifarta bazata iya riƙeshi ba. Hasalima sai an rabata da mahaifar kanta sakamakon ciwo mai haɗari data kamu dashi, in ba hakaba kuma ciwon zai fara girma wataran a wayi gari ya harbi dukkan illahirin jikinta. Amma idan sunyi ƙoƙarin cirewa yanzu in sha ALLAHU an rabu kenan. Wannan al'amari ya matuƙar ɗagama kowa hankali, musamman ma Aliyu. Amma lafiyar matarsa tafi masa duniya da abinda ke cikinta. Dan haka babu wani ja'inja ya amsama Abbu cewar kawai a cire ɗin. Haka kuwa akayi, aka cirema Fateema cikin da dama bai wani zauna da ƙyau ba, aka kuma cire mata mahaifa. Wannan shine ya kawo mata sanadin yin doguwar jinya ta kusan watanni takwas, kafin ALLAH ya bata lafiya komai ya daidaita tamkar ma ba'a taɓa yi ba. Har kuma lokacin bata taɓa sanin an cire mata mahaifa ba. Bayan samun lafiyarta abu na farko shine nema mata gurbin shiga jami'a da Baba Sardauna yayi ana BUK. Dan danan kuwa ta fara karatunta. Dan Fateema yarinya ce mai hazaƙa matuƙa da son karatu. A randa ta fara shiga makarantar ɗaukar darasi a ranar suka fara haɗuwa da matashiyar budurwa da bazata wuce sa'arta ba, in ma ta girmeta baifi da shekaru uku zuwa huɗu ba. Kamila Shu'aibu ƙyaƙyƙyawar yarinya, baƙace amma baƙinta mai ƙyau ne. Tana da matuƙar sanyin hali da rashin son yawan magana. Wajen zama ya fara haɗa su da Fateema a ranar farko, Fateeman ce kuma ta samu Kalima. Bayan ta mata sallama fuskarta da murmushi tai nuni da kusa da ita tana faɗin, “Sis... Kozan iya zama?”. Murmushi mai sanyi Kamila tai mata itama, tare da nuna mata wajen ta ce, “Bismillah mana ki zauna”. Murmushi Fateeman ta sake mata sannan takai zaune da faɗin, “Thanks you”. Daga haka babu wanda ya sake shiga sabgar ɗan uwansa suka maida hankalinsu ga malamin. Tun daga wannan ranar sai ya zam duk wanda ya riga wani zuwa a cikinsu sai ya tanadarma ɗan uwansa waje a kusa da shi. Tun abin na musu kamar wasa har shaƙuwa ta fara tasiri a tsakaninsu. Sai dai babu wanda yasan komai daga rayuwar ɗan uwansa, karatun kawai suke yi har tsawon watanni. A hutun farko da suka farayi har aka dawo akaci kusan sati biyu babu Kamila, hankalin Fateema ya fara tashi ta fara bincike a wajen ƴan ajinsu, sai dai kowa kance shi bai san inda Kamila take ba ba tare ake ganinsu ba. Kamar wasa Kamila ta shafe watanni har biyu bata dawo school ba. Har Aliyu ya fahimci matsalar Fateema ya tambaye ta. Bata ɓoye masa komai ba ta sanar masa, shiko dama yasan labarin Kamila a wajenta tun farko. Haka domin farin cikinta yazo har makarantar ya tayata bincike har ALLAH yasa suka samu wanda yasan gidan su Kamila ɗin. Shine yay musu rakkiya. Sosai Kamila ta shiga matuƙar mamaki tare da jin ƙaunar Fateema a ranta. Suka rungume juna suna kuka. Aliyu ne ya shiga basu baki, inda sai a lokacin Kamila ta ganshi. Mutuwar tsaye tayi dan lallai bawan ALLAHn ya haɗu, ya kuma daki zuciyarta da nashi tsarin, amma sai ta danne. Da farko tayi zaton yayan Fateema ne kawai saboda tsananin kamanni da sukayi, dan haka ta gaisheshi da girmamawa da kiransa da sunan Yaya. Shima ya amsa mata kadaran kadahan dan babu wata mace dake birge Aliyu sai Fateemansa. Hatta sauran yara matan family ɗinsu sam baya sakar musu fuska. Anan soro aka masa shimfiɗa, su kuma suka shiga daga ciki. Su Kamila talakawane sosai, sannan tana rayuwane a hannun kakarta Iyale. Ashe ciwone ya kwantar da Iyalen ita kuma Kamilar ke jiyyarta shiyyasa bata koma makaranta ba. Ta wani gefen kuma babu kuɗin da zataje tai buƙatun makarantar ma. Dan mahaifinsu kaɗai Iyale ta haifa, su uku kuma suka haifa duk mata. Mahaifiyarsu ta rabu da babansu tuni saboda tsananin rayuwar talauci da suke a ciki. Yayi yunƙurin ƙwacesu a hannunta amma sai ALLAH ya bata nasarar guduwa da yayarta da ƙanwarta. Ita kuma a lokacin tana hannun Iyale dan tun yaye dama take anan. To a yanzu hakan dai ance Maman nasu na Saudia tana tukari, suma ƴan uwanta biyu na'a tare da ita. Babansu na son karatu shiyyasa ya tsaya mata cewar zatayi, dan baya son nan gaba ƴan uwanta dake a wajen mahaifiyarta su fita cigaban rayuwa. To da ƙyar da ya ALLAHU aka haɗa kuɗin makarantar ta fara saboda takardunta sunyi ƙyau, sai kuma gashi tunkan aje ko'ina karatun na neman fara tangal-tangal, dama Sakandire ɗin ma dayaya aka gama, mahaifiyarta ce ke turo kuɗi. Ɗan tsakanin nan kuma ta ɗauke musu wuta saboda roƙon da Iyale ke mata akan ta dawo garesu kodan ƴaƴan dake tsakani. Zuwan Fateema da Aliyu gidan shine ya zamewa Kamila rahama da tarin alkairi, dan kaɗan daga tarihinta da Fateema taji ya ɗaga mata hankali, suna dawowa gida ta sanarma Aliyu komai tare da roƙonsa ya taimakawa Kamila ta koma makaranta. Baiyi musu ba kuwa ya taimaka da iya nasa ƙarfi Baba Sardauna ya ƙarasa sauran shi kuma. Hakan ya zama sanadin komawar Kamila makaranta, aka kai Iyale asibiti, aka kuma bama mahaifinta jari ya fara sana'a tare da tsaya masa ya ƙara aure. Wannan hidima mai ban mamaki daga ahalin Fateema shine ya sake dunƙule Fateema da Kamila waje ɗaya, wadda zuwa yanzu ta fahimci Aliyu mijin Fateema ne Kuma yan uwane na jini. Tayi kuka sosai dan harga ALLAH Aliyu ya shiga ranta sosai, amma ta dannema zuciyarta tare da ƙoƙarin ciresa a ranta duk da tasan abu ne mai matuƙar wahala. Haka wannan abota ta cigaba da tafiya, shaƙuwa da zumunta mai ƙarfi na ƙara tasiri a tsakanin Kamila da Fateema. Har takai Kamila kanzo gidan Sardauna tai kwanaki a wajen Fateema. Babu wanda ya taɓa ƙyamatarta ko ƙyararta balle kallon banza. Ƙyautata mata suke da iya iyawarsu har ma da iyayenta. Suna da shekara biyu sun shiga farkon ta uku a jami'a hankalin Fateema ya fara tashi da ganin bata sake samun ciki ba. Ta fara takurama Aliyu suje asibiti amma sai yay biris da ita. Ta cigaba da masa naci daga ƙarshe yace babu inda zaije. Haihuwa ta ALLAH ce kuma lokaci ce. Idan sukai hakuri lokaci yayi zai basu. Shi ba haihuwar yake so ba ita yake so. Sam kalamansa basu gamsar da ita ba, dan haka ta samu Kamila da ƙorafin. Amma itama Kamilar kasancewar bata san komai ba sai ta lallasheta da bata shawarar ta bisa a hankali ta kuma cigaba da yin addu'a. Hakan kuwa akayi, Fateema ta sake yin haƙuri, sai dai kuma ta kasa daurewa dan sosai take son haihuwa. Musamman daya kasance ta ɗanɗana haihuwar da daɗin ɗa a hannu taji. A wata ranar juma'a ta zagaye taje asibiti batare da sanin Aliyu ba. Acan ne fa ta jiyo abinda ya sakata yanke jiki ta faɗi dan tashin hankali, dan sai nemo ahalinta akai suka sameta a nan. Hankalin Aliyu da Baba Sardauna da Umma ya tashi jin abinda Fateema tazo ta binciko, dan haka suka rufeta da faɗa musamman ma Aliyu, yayinda ita kuma take kuka mai ban tashin hankali da tsuma zuciya. Dole suka koma lallashinta kuma. Kwananta biyar a asibitin aka sallameta, ta koma gida da sabuwar jiyyar zuciya. Sai dai mijinta da iyayenta na tsaye a kanta da lallashi daban baki da nasiha. Dan har malami sukutum Aliyu ya ɗakko mata yay mata doguwar nasihar yarda da ƙaddara ga bawa. Alhamdullah hakan yayi tasiri zamuce, dan ta rage damuwa sosai. Gefe kuma ga Kamila itama tana sake tausar zuciyarta. Yin haka babu jimawa mutanen Saudia sukazo hutu gida, a lokacin kuma aiki ya maida Dr Kasheem Kura Paris dan haka sukazo hutu gida daga nan kuma can zasu wuce. A wannan ɗan zama ne Maryam (Mahaifiyar Fateema kenan ta asali) ta nutsu wajen yima ƴarta Fateema nasiha da nusar da ita karta sake saboda ƙaddaratta ta tauye ɗan uwanta kuma mijinta daga samun ƴaƴa daga wata matar, ta barshi ya ƙara aure duk wadda ta zo ta haifa kamar nasu ne su duka. Tun wannan nasiha na tada hankalin Fateema saboda dunbin soyayyar da takema mijinta harta fara tasiri saboda tausayi da ƙaunar da take masa ta haƙiƙa ce. Bayan tasha fama da yaƙi da kanta da tsananta addu'a bayan wucewar iyayenta da ƙannenta biyu ta tunkari Aliyu da batun ƙara aure. Wayyo ai ranar Fateema taga ainahin abinda ake kira tujara. Dan rufe ido Aliyu yay ƴamata tas, ya kuma tabbatar mata idan ta sake tunkararsa da wani batun ƙara aure sai ya ɓata mata rai fiye da haka. Shi yace mata yanada sha'awar zama da mace fiye da ɗaya ne. Koya sanar mata rashin haihuwarta matsala ce ga rayuwarsa. Ita yake so ai, zai kuma cigaba da rayuwa da ita a haka har ƙarshen rayuwa........✍️

_🥲Tofa rikitata_

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee) 2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo) 3 DUNIYAR MU (Huguma) 4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500 Book 2:-1000 Book 3:-1500 Book 4:-2000

0022419171 Access bank Maryam Sani Gumi Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF 89825722 Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖6️⃣7️⃣

______________

.........Bayan yin hakan kamar Fateema ta haƙura tabar Aliyu, zuwa wani lokaci kuma saita dawo da zancen. A wannan gaɓar ma sunyi rikici sosai da har ya kaisa ga kai ƙararta ga Baba Sardauna da Ummu. Dole sukai zama dasu domin sasanta rikicin. Sai dai a wannan sasanci ma bawai Fateema tabar wannan rikici bane, dan ko'a gaban su Baba Sardauna tace tana akan bakanta. Shima yace yana akan bakansa. Fateema ta cigaba da naci da takurama Aliyu akan batun aure da yaƙin son fahimtar da su Baba Sardauna dalilinta. Tun kowa bai fahimceta ba har aka fara goya mata baya. Musamman da taga su Baba Sardauna kamar basa so sai ta shirya tai tafiyarta gidan Kakanninta wato Alhaji Lawan mahaifin Kasheem Kura. Sai da ta bari hankalin Aliyu yay masifar tashi sannan ta bayyana kanta bisa tasota gaba da Baba Lawan ɗin yay suka zo gidan Baba Sardauna. A wannan zamane suka tattauna sosai Baba Lawan ya nuna musu Fateema ta fisu gaskiya, ya kuma kawo hujjoji da dole suka amsa kodan kasancewarsa Uba ga harsu su Baba Sardauna ɗin. Duk da haka har a lokacin shifa Aliyu bai gamsu ba. Amma baice komai ba. Sanin halinsa yasa anan Fateema tace ayita ta ƙare dan karma yace ya fasa. Ya zaɓa a ƴaƴan dangi duk wadda tai masa in ma a gefe ne ma duk taji ta gani. Ai ko a fusace Aliyu ya balbaleta da cewar shi bai son kowa. Ita da tace taji ta gani sai ta kawo matar tunda ita zai aurowa dan ita ta damu. Dariya kawai su Baba Sardauna sukayi, dan sun tabbatar fa Aliyu bai ƙaunar batun ƙara auren nan sam. Aiko Fateema bata gusa ba tace to ga ƙawarta aminiyarta Kamila, tasan halinta tasan tushenta ta kuma yarda da tarbiyyarta. Wani mugun kallo Aliyu ya watsa mata kuwa. Itama ta murguɗa masa baki ta ɗauke kanta dan zuciyata ta gama rufewa ita dai kawai Aliyu yay aure su samu yara ace nasu ne. Anan ma Aliyu yaso tirjewa. Amma sai su Baba Sardauna sukaita lallashinsa da ƙarfafashi. Badan yaso ba ya amsa kawai. Ammafa suna komawa sashensu ya balbale Fateema da faɗa itako ta masa banza. Ita dai tunda burinta ya cika yaje yayta yi. Anyi haka da sati ɗaya Fateema ta shirya taje har gida ta tunkari Kamila da zancen. Ruɗewa Kamilar tayi. “Haba Fateema wace irin maganace wannan. Shin kina zargin ina son MIJINKI ne komi?.....” Hannu Fateema tai saurin ɗaga mata. “Kinga Kamila kada ki sauya min magana. Ni ban taɓa zarginki da koda kwatankwacin hakan ba. Hakama mijina nasan wanene shi, dalilin ƙara auren ne kawai ya taso masa. Kamila da'aje a auro wadda ban san halinta ba tazo ta rabani da shi ba gwara wadda na sani nasan halinta tasan nawa ba. Ina sonshi Kamila so mai tsanani, bazan so wadda zata zo ta cutar damu ba, domin maganar aure fa ake ba hutu ko zaman wucin gadi ba. A gaba ɗaya na hanga na hango kece kawai halayenki sukai min dai-dai da rayuwar mijina. Na kuma tabbatar miki zai soki kamar yanda yake sona in sha ALLAHU in har kin cigaba da zama akan ƙyawawan halayenki. Ba tallarki nai masa ba, haka kema ba tallarsa nake miki ba. Cancantar kasancewar mu a inuwa guda mu uku kawai na hango. Ki taimaken Kamila kada kice a'a, dan cewar a'a ɗinki na nufin wata da ban sani ba zata shigo min gida. Bai zama lallai ta kasance mai ƙyawun zuciya irinki ba. Maybe ta rabani da shi, maybe ta maidani gefe maimakon farina ya koma ganin baƙina da kasawata. Amma ke fa. A tsahon shekaru uku da muke tare ina jinki tamkar jinina, tamkar wata twin sister ɗina da muka tashi tare muka girma tare. Dan ALLAH ki tausaya min, ki auresa kizo ki haifa mana yara mu haɗu mu rungumesu tare. Mu rainesu tare, mu basu tarbiyya tare, su tashi a tskaninmu tare. Ba'a auro wadda kota haifi ƴaƴan zasufi ƙarfina ba, su ringa min kallon matar uba ba uwa ba. Please na roƙeki”. Kuka ya sarƙe Fateema. Itama Kamila kukan takeyi, sun jima a haka kafin Fateema ta miƙe ta tafi, tare da bata damar yanke hukunci....

Readers Also Read