Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 63
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 63: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 63. “Kamila Kano kuma? Wace irin tafiya ce…
3,232 words
“Kamila Kano kuma? Wace irin tafiya ce haka ta ujila kin san fa gobe juma'a, kuma na sanar muku Saturday zaku rakani Kaduna ko?”. “Hakane Abahn su, nima tafiyar ta dole ce. Kuma ai a goben zanje na dawo in sha ALLAHU. Sai nabi jirgin safe na dawo da yamma. Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni, ALLAH idan banje a goben ba da wahala na samu lokaci”. “Humm to wai mizaki je yi ne?”. “Nafa gaya maka Yaya Raliya ce bata jin daɗi, tunda aka gama hayaniyar bikin nan sai a hankali. Jiya su gambo sukaje, shiyyasa nace nima bari naje gobe ai kaga dai baza'ace ba'aga mutum ba. Da harda Oum ɗin yara ma zamu je, to bana son takura mata tunda jikin bawani yayi tsanani bane ba”. Ɗan iska kaɗan Abah ya furzar daga bakinsa tare da lumshe idanunsa ya buɗe kamar yanda AA keyi idan zai yi magana. “Shike nan ALLAH ya kaimu. Aiko sai ki daure ki ƙarasa gidan Baba dan kwana biyu yayi mura shima. Ya hana na faɗa muku ne dan kar Fateema ta tada hankalinta”. “ALLAH ya bashi lafiya. In sha ALLAHU can ma zan fara zuwa, har Baban Yola ma saina leƙa su dan kwana biyu bamu je ba. Da bikin nan naso zuwa sai kuma tafiyar nan tamu ta ratsa”. Kai kawai Abah ya jinjina mata ya cigaba da aikinsa. Ita kuma ta miƙe cike da farin cikin samun nasara tace masa tana zuwa. Nan ma hannu ya ɗaga mata kawai.....
_________★
Bugun shigar kiran na bugawa ne da bugun zuciyar Maanal. Sai da wayar tana gab da tsinkewa sannan aka ɗaga. Sosai ta rumtse idannunta ta kasa cewa komai, daga can shima kuma baice komai ba har na tsawon sakanni. Sai zuwa can ƙasa-ƙasa ya furta. “Ina massallaci, idan na fito zan kira”. Daga haka ya yanke. Da masifar ƙarfi ta saki numfashinta data riƙe, tare da buɗe idanunta. Kai anya zata iya kuwa? Kodai ta barshi kawai. Kai ina bazata iya ba, maganar videos ɗin nan sune tashin hankalinta. Kada mutumin nan yaje ya aikata abinda zai zama sanadin bugawar zuciyarta. Ganin lokacin sallah zai ƙure ya sata haƙura da tunanin ta tashi ta hau cire kaya duk da ba sallar zatayi ba, tana dai son yin azkar ɗinta a irin lokacin kamar yanda ta saba. Jiki a sanyaye ta wuce bathroom yin wanka. Har akai sallar isha'i bai kira ba. Ita kuma ta kasa fita dan gudun kada ta fita ya kira. Bata son zuwa da wayar falo kuma ya kirata a gaban Didi da Uncle Sadeeq. Koda Linda ta shigo ta sanar mata abinci ya zama ready catai ta kawo mata ɗaki yau ta gaji ne. Ta kuma ce tana gaida Didi. Da girmamawa Linda ta amsa mata ta fita, ita kuma ta hau shirin barci. A haka Linda ta sake dawowa ɗauke da abincinta. Kasa taɓa abincin tayi, ta zauna a bakin gado ta ɗauka novel ta hau karatun dole wai duk dan cinye lokaci. Sai dai sam ba wani fahimta take ba sam. Sai ƙarfe tara da wani abu kiransa ya shigo. Zabura tayi daga kwancen da take tana duba wayar, ganin shine ke kiranta video call ma sai da zuciyarta ta girgiza. Ji take kamar taƙi ɗagawa, amma zuciyarta na ingizata. Haka ta tashi zaune ta warware ƙaramin veil ɗin data naɗa a kanta ta rufe jikinta sannan ta ɗaga dai-dai gab zata tsinke. Ai wani irin faɗuwa gabanta yayi lokacin daya bayyana mata a screen ɗin wayar tar. Jikinta har rawa yake ta kife wayar da sauri tana ambaton sunan ALLAH numfashinta na wani sam da ƙasa da sauri-sauri.....
Daga can shima AA ɗin kife wayar yayi da sauri yana ambaton sunan ALLAH, harga ALLAH shi duk zatonsa Rafeeq ne fa, ko video call ɗin yayisa ne dan tabbatar da Rafeeq ɗin yana a Kanon ne kamar yanda yace zai je. Dan gaba ɗaya ya manta ne da maganar kiranshi da yace zai yi ɗazun sai yanzu yana cikin wanka abin yazo masa a rai, shine yana fitowa batare da tunanin komai ba ya shiga masa video call daga shi sai guntun towel daya saka iya ƙugu zuwa gwiwa. Gashi ya ajiye wayar a saman mirror ne ta yanda ta hasko jikin nashi sosai. Ya jima tsaye hannayensa duk biyu dafe da mirror ɗin yana ambaton sunayen ALLAH kafin ya samu ya ɗan dai-daita. Wayar ya ɗauka, har yanzu tana online sai dai baya ganin komai sai duhu. Zama yay da ƙyau ya katse kiran, maƙoshinsa sai yawo yake cikin wuyansa da sauri-sauri. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zai yi akan wayar Rafeeq a hannunta. Sai duk yaji zuciyarsa ma na masa zafi. Ɗayar number RK ya shiga kira, sai dai harta katse ba'a ɗaga ba. Cike da takaici ya sake ajiye wayar, sai da ya bada wasu sakanni zuciyarsa ta ɗan sauka sannan ya sake ɗaukar wayar yay mata normal call.........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣8️⃣
______________
.........Harta yanke ba'a ɗaga ba. Haka ya sake kira. Kira fin biyar bata ɗaga masa ba. Ya cije lips, dan duk duniya Oum kawai yakema kira fiye da ɗaya sai ko Abah. Amma daga basu ba in har ya maka kira ɗaya baka ɗaga ba shike nan, sai in ka kirashi back, bai kuma zama lallai ya ɗaga maka ba sai yaso koda shike da buƙatar wani abu kuwa. Samun kansa yay da sake kiran, yanzu ma har ya fidda rai sai kuma yaji an ɗaga. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke acan ƙasan maƙoshi, tare da kai hannu ya shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake jiƙe da damshin ruwan wanka. Kamar ɗazun yanzu ma shiru tai masa, amma sai ya danne yay sallama. Amsa masa tai murya ƙasa-ƙasa, kai daga ji kasan a cikin kunya take. “Am sorry nazata Rafeeq ne, shiyyasa na kira a wannan yanayin”. “Uhm”. Kawai ta faɗa a can ƙasan maƙoshi, alamar matsanancin nauyinsa take ji har ma bata son maganar. Shina ya fahimci hakan, dan haka ya saki batun kawai. Cikin son kauda wancan yanayin ya katse shirun da sukayi da faɗin. “Kina son ganina ne?”. Da sauri ta ce, “A'a, dama.......” Sai kuma tai shiru. Numfashi ya ɗan sake fesarwa, kafin a ƙagare ya furta, “Daman mi?....” Sosai tsigar jikinta ke tashi saboda yanda yake magana can ƙasan maƙoshi. Ga wani amo dake ratsa mata zuciya na fita daga cikin silent voice ɗin nashi. Daƙyar ta iya danne kanta, da ɗaɗɗaya ta ce, “D..a man akan Abideen ne”. Lips ɗinsa ya ciza da ƙarfi, kamar wanda yake a gabanta idanunsa suka ɗan kaɗa. Muryarsa na ɗan canjawa da ƙara kauri ya furta, “Miye damuwarki da shi ɗin wai?”. “Yazo gidanmu ne”. “Gidan ku?”. “Eh har ya sanar min komai daya faru. Wlhy hankalina a tashe yake da maganar videos ɗin nan. Kada mutumin nan ya cutar dani kamar yanda ka faɗa, kuma wlhy ko saninsa banyi ba, bamma taɓa ganinsa ba.” “Amma yake iƙirarin an bashi aurenki?”. Yay maganar cike da zafi. “Ni wlhy ban sanshi ba ƙarya yake min. Ni dan ALLAH ka bani number ɗinshi zanyi magana da shi”. A taƙaice ya ce, “Banda”. Shiru ta ɗanyi na wasu sakanni dan jin yanda yay maganar a Zafafa. A tunzure, kuma cike da shagwaɓa itama ta ce, “Toni ya kake so nayi?”. Shiru ya mata, har sai da ta cire wayar a kunne ta kalla. Ganin yana online ya sata sake jin haushi. Cike da tsiwa ta ce, “Ni zaka wulaƙanta dan na nema taimakonka?”. Nan ma shiru. Ai a fusace ta yanke kiran, tare da dangwarar da wayar. Shima a nasa ɓangaren wayar ya ajiye kawai ya miƙe. Zuciyarsa sai kumbura take a cikin ƙarji. A haka yay shirin barci ya haye gadonsa. Yana ƙoƙarin ɗaukar Alkur'ani dan yin karatu wayarsa ta motsa. Ɗauka yay da tunanin itace ta sake kira. Amma sai yaga number yarinyar nan ce dake damunsa, yayi blocking numbers ɗinta fin huɗu, amma yanzu saita koma kiransa da sabbin lauyuka. Kasancewar kusan irin wannan lokaci take kiransa a kullum yasa ya gane. Maida wayar yay ya ajiye batare daya ɗaga ba ya cigaba da buɗe Alkur'anin. Dan yanda yake jin zuciyarsa karatun kawai zai yi yaji sanyi......
_________
WASHE GARI.
Yau juma'a, koda Maanal taje office signing kawai tayi ta fito. Dama tama tsayar da mai taxi ɗin daya kawo ta. Tana ƙoƙarin shiga taxi ɗin motar AA ya shigo. Kallo ɗaya taima motar ta ɗauke kanta ta shige abinta. Sai dai tana ƙoƙarin rufe murfin taxi ɗin idannunta suka sauka akansa. Shima kallona yake cike da wani yanayi na tuhuma-tuhuma, mamaki, da kuma kewa. Fuska ta yamutsa tare da ɗauke idanunta a kansa tace ma mai taxi ɗin, “Muje”. Mai taxi da bai san mike faruwa ba yaja motarsa yay gaba... Daga Mawaad Company wajen gyaran jiki aka sauketa. Dan Didi nacan tare da Barrah. Itama gyaran jikin aka shiga yi mata, dan Manaal ƴar gaye ce. Aka mata ƙunshi dai-dai misali baƙi da ja kaɗan da yay mata ƙyau kamar itace ma amaryar. Dan Didi sai tsokanarta take yi. Ita dai murmushi kawai take yi batare da tace komai ba. Basu baro wajen ba sai la'asar. A gajiye suka shigo gida. Nan ma kuma basu zauna ba suka ƙarasa shirinsu. Biyar da rabi a train station tai musu. Sun iso Kaduna ana magriba. Amal ce da su Munaya suka zo ɗaukarsu. Ai fa Munaya ta maƙalƙale Maanal dan ALLAH ya haɗa wannan ƙauna. Gashi kuma Munaya na kama da Maanal ɗin sosai. Sun iso gidan cike da mutane, dan yau za'ai mothers event. Ɗazun akayi Sister & brothers event da ƙannen Yazeed suka shirya ma amarya. Kusan ma duk danginsu ne a wajen sai ƙawayen amarya. An kuwa rankwashe an ƙwalle dan ango kansa dole ya halarci wajen bisa tirsasawar Hajiya Yaya. Kasancewar su Maanal na wajen gyaran jiki basu maida hankali a gani ba. Koda yake ita bama tana bibiyar komai bane, Didi ce idan ta gano da Amaal ke bata labari. Koda suka fito a mota da yawan mutane sukai musu caa da idanu. Wasu ma har suna ɗan ƙus-ƙus. Cikin ikon ALLAH kuma Maanal na fitowa akan Yazeed ta fara sauke idanunta. Ya fito daga sashen Daddy abokansa kusan shida da duk ta sansu zagaye da shi. Yayi masifar ƙyau cikin shadda ɗinkin tazarce, ga hula ya murza fuskarsa na fidda wani annurin gyaran fuskar da yasha. Sosai ya zama wani sakwakwa saboda ganin Maanal. Har takai suma abokan nasa duk suna zuboma inda sukaga yana kallo idanu. Suma dai kamar sun ɗan shiga shock da gannin Maanal ɗin, sai sukai duru-duru. Ɗauke kai Maanal tai tare da jan hannun Munaya da Barrah tai wucewarta sashen Ammie. Haka kawai ta ɗan ji ɗaci a ranta. Sai faɗi take, (yace bai son aure amma gashi yana faman zuba kwalliya da washe baki kamar tsohon gwauro) a fili kam miskilar fuskarta ta shanye komai. Suna shiga ta saki su Barrah ta ɗane Ammie. “La'ila yarinyar nan wai karyani zakiyi ne dan ALLAH”. Ammie ta faɗa tana kai mata mintsini. Dariya Maanal ta sanya da sake mamaye Ammien sosai. Sai kuma ta mata kiss a gefen fuska tana faɗin, “I miss you sweetie na”. Dariya ƴan falon suka sanya. Dan dangin Daddy ne da suka sauka anan sashen Ammie ɗin. Sai yanzu Maanal ta farga da mutane. Sai kuma taji kunya ta shiga ɓoye fuskarta a jikin Ammie. Nan ma dariya kowa ke mata har dasu Amaal da suka shigo. Sai kawai ta janye jikinta ta nufi bedroom ɗinta da gudu. Dan tasan duk rintsi Ammie tasan zasu zo bazata bari kowa ya shiga ɗakin ba tunda ma akwai na baƙi ai. Aiko babu kowa ɗin, an dai gyarshi tsaf yanata ƙamshi.....
Bayan sun huta Ammie ta sakasu shiryawa domin zuwa wajen event ɗin. Maanal taso ta turje. Amma Ammie taita lallashinta. Dan bata son Manaal ɗin ta zauna a gida a fassara zaman nata da wani abu daban. Haka badan taso ba ta shirya tsaf cikin wani swiss lass fitted gown datai masifar zauna mata a jiki. Ta zauna tai kwalliya dan a ɓangaren kwalliya ma Maanal artist ce sosai. Ta koya kuma ta iya saboda sonta da ado, dan ma yanzu kura tayi lafiya. Su Amaal ma har Ammie duk itace ta musu kwalliyar, tai ɗauri daya saka kitsonta fitowa ɗas kamar ka lashe. Koda suka fito babu wanda bai yaba ba a falon. Wasu a dangin Daddy ɗin har suna faɗin, “Kai jama'a yarinyar nan ma ai tafi amaryar ƙyau da komai ga nutsuwa wlhy. Amma uwarsa na neman cuta masa. Ga yarinya mace har mace Masha ALLAH”. Ita dai Maanal da su Ammie babu wanda yace komai. Haka suka fito compound. Kusan duk an wuce. Sai ɗai-ɗaikun mutane a gidan da suka rage. Dan ana kai wasu ne ana dawowa. Dole Maanal taja mota ɗaya, Amaal taja ɗaya Shahidah ma haka. Dan mota uku sukai, a hakan ma a ɗan matse suke dan Ammie tace bazatai driving ɗin dare bane dan Daddy ya hana.....
___________★
Gida ne katafaren gaske daya amsa suna gida. Komai a cikinsa tsari ne irin na gogaggun ƴan boko da sukaci suka yada kai aka kuma tashi a cikin rayuwa irin ta turawa. A nutse farar bafulatanar dattijuwar ke sakkowa daga staircase ɗin dake tsaye ƙam a tsakiyar katafaren falon tamkar an zana. Sosai ta manyanta, sai dai tsufane irin na masu jin daɗi da babu wahala. Ga ƙaramin jikin Fulani ALLAH ya bata. Cike da girmamawa masu aikin dake ta ƙoƙarin shirya abinci a ƙaton dining table suke mata sannu da fitowa. Amsa musu tai da kulawa. Kafin ta furta, “Babu wanda ya fito ne har yanzu?”. “Eh Mah-mah, amma Alhaji ƙarami da Yaya Rafeeq yanzu suka dawo suna a sashen Yaya Rafeeq”. Kanta ta jinjina kawai. Sai kuma ta sake juyawa upstairs ɗin tana faɗin, “Ku ƙarasa wani yay kiransu. Bara nama Doctor magana”. Daga haka ta sake hayewa saman. Fin mintuna goma sai gasu sun fara firfitowa. Kamilallen tsoho da akaga jiya akaga yau Dr Kasheem Kura ne ya fara fitowa matarsa Hajiya Maryam Ishaq Darma biye da shi. Sai ga kuma wata matashiyar mata da bazata wuce shekaru talatin ba da ɗoriya itama. Sosai take kamanni da Mah-mah da su Oum. Hakan na nufin itama ta fito daga tsatson Baffa Ishaq Darma ne. Yara biyu biye da ita ƙyawawa da shekarunsu zasu iya kaiwa biyar da bakwai. Da gudu suka barta suka nufi tsoffin kakanninsu. (Rufaidah kenan, itace Autar su Abah, dan Baba Umar Ishaq Darma mahaifin Abah ne ya haifeta. Itace kuma ke auren Sulaiman ƙanin Oum dake bima Hajiya Majdiya, RK kuma ke bi masa. Yaransu uku duk maza, babban mai shekara tara bai kai ga fitowa ba. Suna zama a dining ɗin RK da Sulaiman da suke kira Alhaji Ƙarami suma suka sakko. Hira suke suna dariya kamar wasu abokai, duk da Alhaji Ƙarami ya girmi RK nesa ba kusa ba akwai shaƙuwa mai yawa a tsakaninsu. Rayuwar Turai sun tashi sune abokan juna, sune ƴan uwan juna. Suma duk kujera suka ja suka zauna, bayan RK ya gama ɗaga yaran sama suna dariya. “Barka da dare Abbu, Mah-mah barkan ki”. Murmushi Hajiya Maryam da Dr Kasheem sukayi a lokaci guda idanunsu akan RK da yay gaisuwar. Cike da kulawa Mah-mah ta ce, “Auta anya tuzurancin nan bai isa ba haka nan? Na fara gajiya da baka abinci fa a gidan nan”. Kai RK ya shafa yana murmushi, sai kuma ya kalla Abbu. “Abbu ai kai baka gaji da kawowa naci ba ko?”. “Nima kamar na kusa fara ƙorafi irin Mah-mahn ku”. Dariya suka sanya gaba ɗaya. Alhaji ƙarami ya ce, “Abbu kaima bazaka bashi kariyaba yau?”. “A'a ina zan bari aima Autana tawaye Alhaji ƙarami. Kawai dai nima ina son yayi auren ne na gaji da ganinsa haka nan.” “Ai ni nama daina cewa komai Doctor. Amma gab nake da dubawa cikin ƴaƴan dangi na aurama Rafeeq da Ajwaad da Najeeb. Su ukun nan tuzurancin su ya ishi kowa a family ɗin nan. Garama su yanzu suna a ƙasar tasu, shiko Najeeb yaje ya tare a ƙasar turawa da anyi magana yace bussines”. Fuska da murmushi Abbu ya ce, “Insha ALLAH zasuyi kwanan nan. Dan autanki dai gobe zamu tattauna akan nashi batun. To Inaga Ajwaad ɗin da Najeeb ɗin ma duk za'ayita ta ƙare, dan ta bakin Kamila sai an biyo musu ta bayan gida.” “To ALLAH ya tabbatar da alkairi”. A tare duk suka amsa da Amin, kafin kowa ya fara ƙoƙarin zuba abinda yake buƙata a plate ɗin da ya ɗauka. Dining ɗin RK ya ɗan kalla sai kuma ya duba Rufaidah. “Ƙanwa! Wai ina spider man ne?”. Baki ta ɗan taɓe da faɗin, “Yana ɗaki Yaya Rafeeq, fushi yake har yanzun. Daga ni har Mah-mah ya daina kulamu a gidan yau. Tunda kuka fita ma bana tunanin mun gansa, shi a dole sai yabi Mamy Abuja bayan kuma ga makaranta ba hutu akayi ba”. Dariya Abbu yayi, cike da manyantaka ya ce, “Ai laifinku ne. Daga ke har Maman taki kun cika faɗa ne. Shi kuma ku lura yaro ne da bai son yawan hayaniya, komansa irin na iyayensa ne Ajwaad da Fadeel, shiyyasa ma yake ƙulafucinsu, dama kun barshi yabi Kamila ɗin sai a maidoshi ranar lahadi”. “Tab Abbu murɗa-murɗa kenan. Garama Fadeel ɗin da ɗan sauƙi. Amma wannan Autan na Aunty Babba sai ita wlhy. Ai sai mu tattara idan yayi aure mu maida masa can su ƙarata. Dama ai duk duniya ba wanda Abdull ke ƙauna sama da Ajwaad”. “To ai hali yazo ɗaya ne”. Cewar Alhaji ƙarami. Dariya duk sukayi, sai kuma RK ya miƙe yana faɗin, “Ina zuwa bari na fito da shi.” abincin su sudai suka cigaba da ci. Kusan mintuna biyar kuwa sai gashi ya fito goye da matashin yaron a bayansa. Sosai yake kamanni da Alhaji ƙarami. Kai da ka gani kasan shi ya haifi abinsa. A kujerar kusa da shi ya saukesa, shiko yaron sai wani ciccin magani yake. Yaki ƙallon kowa. Dariya sosai Abbu yake gumtsewa, dan ganin Mah-mah da Rufaidah da yaran ke kira Ummy na hararrar yaron. Shi kuma sai wani ƙara tsare gida yake yi. “Ni mutum ma idan ya sake shiga sabgata a gidan nan ba sai nayi kuli-kulin rakiya da shi ba”. Cewar Mah-mah. Aiko Abdull sai ya sake tura baki gaba yaƙi kallonta. Kasa haƙuri Abbu da RK da Baba Ƙarami sukai suka sanya dariya... Haka sukaci abincin nasu cike da raha. Dan akwai shaƙuwa mai ƙarfi a tsakanin wannan zuri'a. Musamman daya kasance mahaifinsu mutum ne mai sauƙi da sanyin hali. Dan kaf halayen Rafeeq irin nashi ne. Mah-mah ce ma mai ɗan zafin yanayi............✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖8️⃣9️⃣
______________