Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 64
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 64: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 64. ........Shigowar su Maanal cikin hall…
3,258 words
........Shigowar su Maanal cikin hall ɗin ya matuƙar ɗaukar hankali. Dan a dai-dai lokacin da ake addu'a ne. Wajen ya kasance tsit. Suko yanda aka zubo musu idanun bai damesu ba. Sai ma wajen zama da suka samu aka ƙarasa addu'ar da su. Kafin a fara abinda ya shafi mutane. Duk motsin Maanal a idon Yazeed ne, ita ko taƙi yarda ma ta kalla inda suke shi da amaryar tasa da tasha ƙyau. Itama amaryar hankalinta duk yana akan Maanal ɗin, sosai take jin tsanarta, amma tsoron nunawa take a gaban Yazeed. Dan ranar data nuna ɗin ya tabbatar mata zai iya fasa aurenta akan Maanal. Dan haka ta kiyaye idan tana son kasancewa da shi. Dole ta kama kan nata take kuma yin taka tsantsan. Amma a ranta wata irin wutar ƙiyayyar Maanal ce mai ci da zafi da ƙarfi ke sukarta. Hakama mahaifiyarta Aunty Sabuwa. Dan ko yanzu taso yin abinda zai wulaƙanta su Ammie a wajen mai bima Hajiya Yaya ita kuma Sabuwar yayarta ce ta ƙwaɓeta. Dan ita tana da hankali da sanin yakamata matuƙa..
Taro ya tashi lafiya. Ammie ce kawai taje taima amarya da ango liƙi. Amma su Amal duk ƙi sukayi, balle Manaal da dama ko motsawa batai ba. Hasalima charting suke ita da RK hankali kwance. Ana tashi sune ƴan gaba-gaba a masu wucewa gida. Yanayin gajiyar tafiya da rashin samun isashen hutu suna shigowa gidan kowa makwanci ya nema. Washe gari safiyar asabar aka tashi da shirin ɗaurin aure. Sai yinin biki da Hajiya Yaya zatayi. Zuwa dare ayi dinner sannan a kawo amarya. Sai washe gari walima da buɗan kai baki ya tashi. Duk da nan gidan anguna ne bana su amarya ba cike yake...
Sosai abin duniya ya dami Yazeed. So yake yaga Maanal amma hakan ta gagara. Dan jiya daga wajen mothers event ɗin nan dole hotel ɗin da abokansa suka sauka yaje ya kwana. Ya kira wayarta kuma a kashe. Yanda ya kwana da ita a rai ya sashi zuwa gidan yau da wuri. Dama anan sashen Ammie aka haɗama abokansa breakfast, sai ya samu damar fakewa da hakan kuwa. Bayan ya gaishe da dangin Daddy dake nan sai ya zauna suka cigaba da hira. Dan yaga kowa tsakanin Shahidah da Amaal dake shirya abincin abokan nasa da Aunty Sakina amma babu Maanal. Cikin raɗa-raɗa yake tambayar Munaya da tazo gaisheshi. “Uncle sun fita ita da Aunty Amrah.” Sai da ya kalla agogon hannunsa da mamaki ya furta, “Fita kuma da safen nan? Ina suka je to?”. “Nima ban sani ba”. Shiru kawai yayi ransa na ƙara jagulewa da tunani. Sai kuma ya miƙe ya fita. Can waje ya koma ya tsaya a ƙofar gida. Duk ma inda suke ai dole in sun dawo tannan zasu shiga gidan. Yana a wajen kusan minti talatin yana dakon jiransu sai ko ga napep ta tsaya a ƙofar gate ɗin. Amrah ta fara fitowa tana dariya, sai Maanal fuskarta da murmushi, da alama dai wata maganar suke data basu dariyan. Su duka hannayensu da kaya. Amrah ce ta fara lura da yayan nasu, ganin yanda ya tsume fuska ya sata haɗiye dariyarta. Ita dama Maanal tuni ta daina murmushin duk da bata gansa ba, sai da ta juyo zasu nufi hanyar shiga idonta ya sauka a kansa. Ɗan turus tayi tana kallonsa, sai kuma tai ƙoƙarin janye dubanta a kansa a taƙaice ya ce, “Good morning ” ta raɓa zata wuce. “Zonan”. Ya kirata a dake. Cak ta tsaya, jitake kamar tace bazata zo ba. Amma dai ta dake ta dawo da baya, yayinda Amrah ta amshi kayan hannun nata. Dan daga gidan Amaal suke, ɗinkunan su ne da tela bai samu gamawa ba sai jiya, shi kuma mijinta ya amso jiya da dare shine yau Maanal ɗin suka je ɗakkowa a gidan... “Fushi ake dani ko?”. Ya faɗa cikin kwantar da murya, kamar ba shike tsume fuska ba. Batare data kallesa ba ta ce, “Mi kamun da zanyi fushi da kai Yaya. Kawai dai yanayi ne”. Murmushi ya saki mai armashi. Sai kuma ya sake matsowa kusa da ita sosai. Cike da lallashi ya ce, “To nidai ina roƙon afuwa dan ALLAH. Har yanzu kuma baki maida wayarki ba ne?”. Kallon wayar tata dake hannunta tayi, batare data kallesa ba. “Kwana biyu da suka gabata na maida.” “Shine kuma koma a taɓani. Naso sauka Abujan sai aka samu matsala. Dan bammayi zaton ganinki a kd ɗin ba”. Yanzu kam murmushi ta saki, murmushin daba cika gani yay a fuskarta ba. Sai dai batace komai ba. Kafin shima yace wani abu wasu ƴan uwan Hajiya Yaya suka iso. Wani shegen kallon banza suke zuba mata, dan labarinta duk ya gama karaɗen danginsu daga jiya. Yayinda shi kuma Yazeed hankalinsa ke a kansu yana musu sannu da zuwa. Da wannan damar Maanal ta zame jikinta ta gudu. Sai waigawa yay yaga wayam bata a wajen. Yaso bin bayanta, sai baƙin suka sake janye hankalinsa dole ya haƙura......
_________★
Da mamaki Oum ke kallon AA dake shaƙar barci a gadonta. Da alama ma ya manta da yau zasuyi tafiya. Tunda suka kammala breakfast yau a ɓangarenta su duka gidan aka cigaba da hira shi kuma ya tashi ya shige bedroom ɗinta basu sake jin ɗuriyarsa ba. Umarnin zuwa kowa ya shirya da Abah ya basu ya saka kowa tashi ya nufi shiryawa. Ita dama cikin shirinta take dan haka ta shigo domin ganin mi AA ɗin keyi a ɗaki, kawai saita ci karo dashi a bargo ma ga ac ya ƙure. Ac'n ta kashe, kafin ta ƙarasa gaban gadon tana kiran sunansa, dan tasan bashi da nauyin barci. Idanu kuwa ya buɗe a hankali ya sauke a kanta. “Kowa nacan ya shirya kai kana nan kana barci Auta?”. “Oum ALLAH ni barci nake ji, weekend ɗin nan nefa mutum ke ɗan samu ya huta. Wai inama za'aje ne?”. “Koma inane idan munje zaku gani. Kuma ka tashi kafin Abah ya shigo ya samu baka shirya ba”. Fuska sosai ya ɓata. Sai kuma ya yaye duvet ɗin ya tashi tare da sakkowa. Oum dai na tsaye tana kallonsa. Gadon ya fara ƙoƙarin gyarawa. Oum ɗin ta dakatar da shi. “Kaga barshi jeka shirya zan gyara”. Kafaɗa ya maƙe mata ya cigaba da gyarawa, sai da ya gama tsaf sannan. Wannan ba komai bane a garesu su duka. Dan Oum ta riga ta horesu da aiki har girki babu wanda bazai iya yi ba su duka ukun. Yana fita tayi murmushi, dan tasan a cike yake fam. Itama ɗan shishshirya abinda take buƙata ta shiga yi...
Kusan sha ɗaya duk sun fito cikin shiri, AA ne ƙarshen fitowa cikin ƙananun kaya. Aiko Abah ya korashi canjawa. Oum ya kalla a shagwaɓe, ta masa alamar ba ruwanta. Sai ya tura baki ya koma. Aiko Fawzan ya shiga dariya da tsokanarsa. Babban yaya yayi murmushi su Nibras na taya shi dan sun san su dai babu damar yi a zahiri. Abah ma murmushin yayi, yayinda Mamy tai kamar bata san anyi ba. Bai wani jima ba sai gashi ya fito cikin wani arnen yadi omo blue daya ji ajiyayyen ɗinki. Ya kawo hula ya murza. Kusan su duka sai da suka ambaci masha ALLAH a zukatansu. Dan manyan kaya nama AA masifar ƙyau shi kuma baya son sakawa. Nibras kam ji take kamar ta haɗiyesa ta huta. Fawzan da bakinsa baya iya shiru ya shiga yimasa hoto da faɗin, “Kai wankan nan gaskiya bai kamata ya tafi a banza ba tuzurun gidan mu. Dolene na poster ka a media ko zamu samu wata tace tana so mu haɗa mata da cin hanci.” Dariya su Abah suka sanya. Oum ta ce, “Yarona yafi ƙarfin sai an haɗashi da cin hanci sannan ya auru. Fawzan ka kiyaye mu”. “Oum kada fa ku cika baki, yanzu yayin yara ake masu jini a jika shi kuma ya zama tuzuru”. AA dai bai kulashi ba. Sai ma kama hannun Anum yay suka shige mota. Aiko zaram Nibras ma taje jikin motar ta tsaya. Babu wanda ya damu da hakan, sai ma Abah da Oum da Mamy suka shiga tasu motar tare, Babban yaya ma ya shiga Saheeba ta shiga kusa da shi. Sai Naufal ya shiga baya. Can kuma AA a mazaunin driver Fawzan ya shiga kusa da shi Nibras da Anum suka shiga baya. Fawzan yasan AA ba ƙaunar tuƙi yake ba a rayuwarsa, dan haka ya kallesa da faɗin, “Zaka iya kaimu har Kaduna babu wata damuwa”. Kallonsa shima AA ɗin yay da faɗin, “Wai dama Kaduna zamuje? To yin me?”. “Nima ban sani ba, amma biki Abah yace ai kamar”. “Yanzu saboda zuwa biki aka hanani barci na. Kuma dan ALLAH ba sai a tafi a train ba”. “To ya muka iya, kasan Abah da Oum akan son dangi. Ni kaina yau inada wani ɗaurin aure a cikin Abujan nan, yanzu dai bani driving ɗin kawai”. “No barshi muje, idan na gaji sai ka amsa”. Cewar AA yana yin horn. Shi ya fara fita, Babban Yaya biye da shi sai drivern Abah a ƙarshe. Haka suka ɗauki hanya a jere gwanin sha'awa. Babu damar yin gudu dan in ana tafiya tare da Abah dama babu zancen gudu yaci ƙaniyar mutum. Sai dai abinka da lafiyayyun motoci cikin amincin UBANGIJI sha biyu da kusan arba'in a Kaduna tayi musu. Babban Yaya da Abah suka koma motar AA. Nibras suka haɗe da Saheeba data amshi tuƙin Babban yaya, oum da Mamy suna tare da driver. Su gidan Ammie aka nufa da su. Su kuma su Abah suka wuce masallaci domin yin sallar juma'a da ɗaurin aure. Invitation card ɗin Abah ta miƙama AA. Bayan ya gama dubawa ya juyo yana kallon Abah ɗin, dan suna baya shi da Babban Yaya. “Abah kasan nifa ba wani sanin Kaduna ɗin nan nayi ba.” “Eh mu samu mai napep ai zai kaimu in sha ALLAH”. Haka kuwa akayi, dan da mai napep duka samu ya jagorancesu har zuwa masallacin da aka rubuta a jikin katin. Sun kuwa samesa cike da jama'a, da alama akwai wasu ɗaurin auren bayan wanda suka zo.....
____★
Su Oum ma sun isa gidan Alhaji Usman Chalawa. Tun fa a kallon anguwar jikin Mamy ya fara ɗan sanyaya, dan tayi zaton har yanzu su Ammie a irin waccan rayuwar ta baya suke. Ko dataga gaban ƙaton gate ɗin da sukai parking sai tai ɗif. Godiya driver yay ma mai napep ɗin daya jagorancesu suma, Oum ta masa alheri sannan suka samu waje sukai parking a nan gefen gidan. Akwai ƴan biki dake ta shigi da fita dan haka suma suka shige. Tabass gida ne babba kuma sashe-sashe. Duk da nasu yafi ƙawa da girma sun san anan ɗin ma babu raini gidan masu akwai ne. Basu san inda zasu nufa ba dan haka Oum tai ƙoƙarin kiran layin Shahidah. Bugu biyu kuwa ta ɗaga, cikin girmamawa tai sallama da fara gaishe da Oum ɗin. Murmushi Oum tai tana amsa mata, kafin ta ɗora da faɗin, “Gamu a harabar gidan ku bamu san ina kuke ba”. Cikin mamaki da kuma rashin fahimta Shahidah ta ce, “Oum gidan mu? Wai nan Abuja?”. “A'a Kaduna, inda ake biki”. Ai ji Shahidah tai tana neman rikicewa. Hakama Amal ta saki soson shafa hodan hannunta tana kallon Shahidah. Suna a ɗakin Maanal ne suna shiryawa dama. Dan sai yanzu suka samu dama saboda aiki. Cikin sauri Shahidah ta yanke kiran, ta ja mayafi Amal biye da ita suka fito. Su Ammie na falo da su Hajiya Majdiya da suka kwana anan suma. Tambayarsu Ammie take lafiya? Ina zasu haka?. Batare da sun tsaya ba sukace suna zuwa. Cike da farin ciki Oum ta kama Amaal da Shahidah ta rungume a jikinta. Musamman ma Amaal da sai yau ne ita suka gaɗu. Itama dai Mamy murmushin yaƙe ta shiga yi, yayinda Saheeba keta wani faman taɓe baki. Nibras dai ƴar kallo ce, dan ita dama nata baƙin halin akan AA ne kawai. Sashen Ammie su Amaal suka musu jagora, inda shigowar tasu tayi dai-dai da miƙewar Ammie da Hajiya Majdiya dan zataje ɗakin Ammien tai salla. Cak Ammie ta tsaya kamar wadda ta suma. Itako Hajiya Majdiya ta shiga ƴar dariya tana kallon yanda Oum da Ammie ɗin suka tsaya suna kallon juna kamar kaji. Kai daka kalla Ammie kasan a ruɗe take, dan jin take kamar irin mafarkin data saba yi ne akan Oum ɗin. Ɗan jujjuyawa tayi ta kalla kowa a falon, ƙarshe ta sauke idonta akan Amaal da Shahidah da duk suka koma yanayin tsoro. Dan su fargabarsu basu san yanda su Oum suke a zuciyar Ammien tasu ba a yanzu. Saboda tunda aka rabu bata sake yin maganar waninsu ba..........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣0️⃣
______________
........Sai kuma a mamakinsu sukaga a hankali Oum ta nufi Ammie. Ai tuni itama Ammie ta zaburo kansu suka rungume juna. Hakan ba komai bane, dan duk wanda yasan tarayyar Ammie da Oum yasan alaƙace mai ƙarfin gaske irin ta yaya da ƙanwa ciki ɗaya. Ciki ɗayan ma irin wadda akafi shaƙuwa ɗin nan. Su duka hawaye suke yi, hawayen kewa da begen juna da farin cikin sake haɗuwa a gaɓar da babu zato babu tsammani musamman ga ita Ammie. Ɗayan ƙaramin falon Ammie dake a rufe dan kar mutane su ɓata Amaal tazo ta buɗe. Sai da su Oum suka gaggaisa da mutane anan falon sannan suka shiga. Gaba ɗaya Ammie ita tama rikice, ta rasa ina zata kama ina zata saka su Oum. Yayinda su Oum keta sake mamakin ganin yanda ta canja, duk wanda yasan Ammie a shekarun baya ya ganta a yanzu za'a iya kwana ana gaddama da shi akan ba ita bace ba. Gaba ɗaya ta zama matar manya. Tayi ƙiba ta ƙara haske da cikar kamala. Dan ita kanta Mamy a wannan gaɓar jitai ta raina kanta. Saboda ko suturar dake a jikin Ammien ka kalla kasan lallai nagaba yayi gaba yanzu kam, na baya sai labari. Gefe kuma ga ganin Hajiya Majdiya a tare da Ammie ɗin ya sake tabbatar ma Mamy lallai dama Oum na tare da su Ammie kenan take munafuntar ta (kun san idan mutum nada halin banza kullum gani yake haka kowa yake ma😏)....
Salla suka fara gabatarwa saboda gudun fitar lokacinta. Kafin a cika musu gaba da abinci kala-kala. Kan Ammie dai a matuƙar ɗaure yake da ganin sanayya tsakanin Hajiya Majdiya da su Oum. Daga ƙarshe dai ta kasa haƙuri ta magantu. Dariya Hajiya Majdiya tayi, kafin ta warwarema Ammie komai. Matuƙar mamaki da al'ajab ne ya nema kashe Ammie, ta dinga raba ido tsakanin Hajiya Majdiya da Oum. A lallai tabbas bata san ƙannen Oum ba a fuska a tarayyarsu har suka rabu, saboda lokacin su suna ƙasar waje, amma tasan labarinsu, tana jin kuma tana ambatar ƙanwarta datai aure amma tana acan kasar wajen mijin kuma na nan Nigeria saboda yanada mata biyu a Zaria amma yana zuwa can wajenta dan yana kasuwanci a ƙasashen ƙetare. Cikin kasa daurewa Ammie ta ce, “Aunty! Dama Maman Najma ce kike yawan bani labari da mijinta ke Zaria amma ita tana can Paris”. “Tabbas itace Asiya. Shekara shida kenan da dawowarta Nigeria har ma da su Abbu. Dan yanzu haka su suna Kano ne”. “Ikon ALLAH kenan, shekaru biyar kenan muna tare amma bamu san akwai muhimmiyar alaƙar data taɓa haɗa ƙaddararmu ba. A lokuta da dama wasu al'amura na Maman Najma kan so sakani a ruɗani wlhy. Dan sai kita dawo min cikin idanu duk da bakwa kama ko kaɗan a fuska.” “Gaskiya ne bama kama da Majdiya da Rafeeq sam. Garama Sulaiman shi kam da kin gansa zaki san akwai alaƙa. Mu kamar mun kwaso Mah-mah ne. Itako Majdiya da Rafeeq Abbu. Wai ni naga kowa banda Baby na fa, ko bata zo bikin bane?”. Murmushi Ammie tayi. “Tazo, suna tare da su Najma Nene ta aikesu.....” Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammie. Ganin Daddy ya sata ɗauka batare data ƙarasa maganar ba. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar tana kallon Oum. “Aunty dama harda su Yaya kuke tare?”. “Ai mu duka gidan ne ba'a bar kowa ba. Halan har an ɗaura auren?”. “Eh an ɗaura harma sun shigo. Amma inaga su basu ƙarasa wajen walima bane ba. Dan yace gasu nan a hanya a shirya musu abinci a sashensa.” “Oh oh ji son bama mutane wahala. Maimakon su ci acan kamar kowa”. Mamy ce mai maganar. Dariya Ammie tayi, da faɗin, “Babu wata wahala Mamy, hakan ai shine dai-dai suzo na gansu shekara nawa”. Daga haka Ammie ta fice. Da wani shegen hararar ƙasan ido Mamy ta bita, sai ko karaf a idon Hajiya Majdiya. Mamaki sosai ya kama Hajiya Majdiya dan abu ne da basu taɓa gani ga Mamy ba. To kodai sunada matsala ne da Hajiya Asiyan? Kai to amma a dukkan labarin da Oum ta bata na alaƙa da tarayyarsu babu wani saɓani ai, hasalima Mamy bata da yawan shiga sabgar mutane. To kodai idonta ne ya gane mata ba daidai ba? Kai to gaskiya hakanne. Da wannan tunanin ta saki zancen a ranta suka cigaba da hirarsu.....
★ Har cikin gida motar su AA ta shigo dan suna biye da Daddy ne. Yanzu kam Fawzan ne ke driving ɗin. AA na gefensa Abah da Babban yaya na baya. A kusan tare duk sukai ƙoƙarin fitowa. Hakan yayi daidai da fitowar su Huznah daga sashensu. Cak taja wani kalar wawan birki. Itama dai cikin kwalliya take, sai dai ɗan kwalinta a hannu ta yana siririn veil a kanta. Tare take da wasu ƴammata guda biyu. Sai wata dake biye da su da makeup box a hannunta, da alama dai kwalliya zatayima Huznah ɗin. Dan su sauran biyun da kwaliyarsu raɗam a fuska. Bakinta har harɗewa yake wajen ambaton “AA Darma! A gidanmu?”. Duk kallonta ƙawayen nata sukai, wadda ke'a gefen haggunta ta ce, “AA Darma naki da kuka haɗu a Abuja lokacin bikin Yaseerah?”. Bata iya ta bama ƙawar tata amsa ba. Jiki na rawa ta juya sashensu da sassarfa. Wani iri zallo zuciyarta keyi kamar zata fasa mata ƙirji ta fito. Hajiya Basariyya na falo tsakkiyar ƙawayenta su Maman Yaseerah Huznah ta faɗo musu. Tama manta a cikin taron mutane suke. Yanda take ƙwala kiran “Ummy! Ummy!” yasa Hajiya Basariyya miƙewa zaram. Tareta tayi tare da girgizata tana faɗin, “K Huznah lafiyarki kuwa? Wane irin kirane wannan? Jibafa yanda kike shigowa kamar wadda aka biyo.” “Ummy AA Darma fa na gani a gidan nan”. Rasama inda Hajiya Basariyya zata kamo AA Darma tayi. Ta ce, “Waye kuma AA Darma?.” “Ummy AA Darma ɗin ne baki sani ba? Mijin da zan aura na Abuja”. Ai sosai Hajiya Basariyya ta waro idanu waje, hakama Maman Yaseerah zaram ta taso inda suke. Hannun Huznah ɗin ta kama sukai cikin bedroom, Hajiya Basariyya ta take musu baya. “K Huznah nutsu, da gaske kike kuwa”. “Wlhy da gaske nake Mamah.” “Tab ɗin jan, eh lallai malam yayi gaskiya. Hakan na nufin aiki yayi kenan”. Maman Yaseerah ta faɗa tana kallon Hajiya Basariyya.......
_In dai da gaske aikin nan yaci nima ai arakani wajen malamin nan zai min aiki akan makaranta AJIYA A DUHU musamman ƴan Discussion House da ƴan AREWABOOKS ina son a musu ASIRI su fara son Uncle RK🥱🥱🥱🤪🏃🏃🤣👍_
__________★