Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 71
Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 71: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 71. Su Ammie sun samu ƴan tahowa a mota sun…
2,820 words
Su Ammie sun samu ƴan tahowa a mota sun iso. Dama da abincinsu nacan Kaduna duk suka taho, dan haka sai aka samu sauƙi babu wata damuwar abinci ko ruwa balle lemuka. Sai a wannan lokacin Daddy ya samu zama da su Nene da Ammie, dan suma su Yaya Nuhu sun iso, dama suna a Kanon su ai tun daurin aure tunda Daddy ne kawai da Yaya Sani suka wuce ɗazun. Dalla-dalla Daddy yay musu bayani da tabbatar musu dama can tun kawo kuɗin aure da akayi bada sunan RK akai ba, da sunan AA su Abbu suka kai kuɗi Kaduna. Kuma sun tabbatar masa RK ne da kansa ya sakasu yin hakan, amma sun roƙesa akan dan ALLAH kada kowa yasan hakan har sai ran ɗaurin aure. Suka kuma bashi haƙuri akan al'amarin AA da Huznah bamai yiwuwa bane, dan da'a haɗa auren shi AA ɗin ya cutar da ita gara a aura masa Maanal ɗin kawai kamar yanda kowa yasan hankalinsa akanta yake. Dalilin ƙin bijirewarsa ne kawai basu sani ba kuma sun gagara ganowa. Da kuma suka binciki miyyasa shi RK ya haƙura ya sadaukar masa, sai yace musu wataran zai faɗa, yanzu dai shi buƙatarsa duk rintsi AA ya samu auren Maanal ne kawai. Shi kuma ya basu zaɓin koma wacece zai amsa da hannu biyu kuma zai riƙe amana in sha ALLAHU. Wannan zance shine ya girgiza Daddy, yaji zuciyarsa ta karaya sosai game da son haɗa Yazeed da Maanal daya dage a baya. Bayan wucewarsu kuma washe gari ya zaunar da Yazeed yay masa nasiha sosai sannan ya gaya masa gaskiya akan yabama AA Maanal dan shine yafi cancanta. Abinda ya shiga tsakaninsu a barshi kawai a matsayin ƙaddara da babu makawa sai ta faru su basu isa hanawa ba. Yazeed mai biyayya ne a garesa, dan haka ko jayayya baiyi masa ba. Daga ƙarshe ya bama Ammie da Nene akan ɓoye musu da sukayi tun farko shi da yaran Nenen. Murmushi kawai Ammie tayi, sai Nene ce keta faman sanya albarka da tabbatarma Daddy cewar baiyi laifin komai ba. Hakan ma da yay shine dai-dai. Dan ɓoye aure alkairi ne kodan gudun maƙiya da mahassada. Yanzu ba gashi anyi komai cikin kwanciyar hankali ba babu wani tsugunne-tsugunne. Amma da ace an bayyana ai ba'asan irin ƙurar da zata tashi ba sam. Hakan kuwa hankalin kowa kwance. Shi kuma Ajwaad ALLAH ya bashi lafiya da ita kanta ma Maanal ɗin. Itama Huznah suka sanya ma nata auren albarka sosai tare da roƙar Daddyn a lallaɓata dan ALLAH harta haƙura. Dan an mata laifi sosai. Murmushi kawai Daddy yayi. Ya kuma basu labarin yanda ya ƙulla shima auren na Huznah bayan wucewar ƴan Kano da yay nazari. Ya kuma shawarci Yazeed suka yanke hukuncin hakan dan a samu masalaha, itama a taimaketa da zaman gidan tana kara tsofewa.....
WASHE GARI
Zuwa washe gari duka ɓangarorin uku sai muce Alhamdullah. Idan ka cire AA dake kwance a gadon asibiti har yanzu bai farka ba. Amma dai ana saran daidaituwar al'amura da yawa a tare da shi. Maanal ma ta tashi jikinta da sauƙi, sai rashin ƙarfi da rashin walwalar fuska. Dan ko abinci sai da Nene ta zaunar da ita ta bata da kanta a baki cike da kulawa, tana kuma mata nasiha cikin hikima. Zuwa tashin hantsi Daddy da Ammie da manyan gaba ɗaya suka je asibiti suka duba jikin AA, har yanzu dai ba'a bari a shiga inda yake. Dan sun tarar da su Oum duk a waje, suma kuma basu jima da zuwa ba, tare kuma suka baro asibitin da su, saboda manyan family ɗin na Darma sun yanke a cigaba da bikin kawai, dinner ce da aka shirya gaba ɗaya sai walima, sai suka soke dinner ɗin za'ai walima kawai. A jiya ya kamata a kawo amare ayi dinner da daddare da safe ai walima da buɗar kai kowa ya ɗauki matarsa. Da kuma abin ya juye sai ya zam yau za'a kawo amaren ayi walimar zuwa gobe kowa ya kama gabansa. Wannan yasa shi kansa AA ɗin farkawarsa kawai ake jira dan za'a wuce da shi can KK HOSPITAL na Abuja ne. Idan kuma an samu yanda ake so ma falillahil hamdu.....
________★
A ɓangaren su Hajiya Basariyya kam dole ta sauka a gidan ƴan uwarta, su kuma can dangi suna gidan amarya wasu kuma a gidan iyayen angon musamman dangin su Daddyn, ita kuma dangin Hajiya Basariyya ɗin aka barsu a gidan Huznah amarya da har safiyar yau kuka ya gagara tsaya mata. A hakan ma dan Maman Yaseerah na tsaye a kanta da tabbatar mata ta kwantar da hankalinta auren nan sai sun kashesa ta auri AA ta fidda Maanal. Dan haka ita da wata ƙanwar Hajiya Basariyyan itama hatsabibiyar kanta sune zagaye da Huznah ɗin suna ta ɗorata akan mugayen abubuwa da zata dinga tafkawa mijin dama iyayensa duk da kuwa ƙanin ubantane uban nasa uwa ɗaya uba ɗaya. Itako tsaf take ɗauke komai harma tana ƙara nata a cikin zuciya. Oho sudai dangin Daddy ko'a kwalar rigarsu, shahalin bikinsu sukeyi cike da farin ciki, Hajiya Yaya kuwa ta shige cikinsu tayi kane-kane danta ƙona ran Hajiya Basariyya, dan su basu san su Ammie suma suna nan Kanon ba sam, tunda sai da suka taho sannan Daddy ya taho da su Ammie, kuma sunji ance ango babu lafiya a tunaninsu ai biki ya tsaya tunda anata kai waketa kaya, shiyyasa taga gwara ta maida hankali tayi maganin Hajiya Basariyyar kafin ta koma kan Ammie, duk da ma dai case ɗinta da Ammien yanzu kaɗanne ALLAH ya raba ɗanta da ƙarfen kafa, sai dai hassadar wanda yarinyar ta samu a matsayin miji ne ya kasa wuce musu a ƙahon zuciya daga ita har ƙanwarta Sabuwa... Duk abinda Hajiya yayan keyi yana komawa kunnen Hajiya Basariyya, tayi niyyar shiryawa kuma itama ta koma can cikin dangin mijin nasu da ƙyar ƴan uwanta suka dinga tausarta akan tabar komai a gama bikin lafiya idan suka koma gida ayita. Amma yanzu kam ta shanye kodan su san ta yanda zasu raba wannan aure na Huznah.....
________★
Hajiya Mamy kam duk mai hankali yay mata kallo ɗaya zai san a harmutse take, sai dai da yake za'a iya danganta yanayin nata da halin da AA ke a ciki kai tsaye, tunda an san duk kawaicin da zata nuna dole hankalinta ya tashi. Amma a ɓangaren Hajiya Majdiya wata kalmar data fita daga bakin Mamy karaf ta shige a kunnenta batare da su sun farga da ita ba, sai dai kafin Mamy ta cigaba da surutunta yan uwanta na tausarta Maman Saheeba ta lura da Hajiya Majdiya ɗin, shine tai saurin ƙwaɓar Mamy da fargar da sauran kasancewar Hajiya Majdiya ɗin a wajen ta hanyar ambaton sunanta. Ita dai Hajiya Majdiya ta fita tana juya kalmar Mamy ɗin da tace, _“Nifa bana jin zan iya cigaba da wannan kauda kan, gara ayita kawai ta ƙare tunda basu da wuta basu da aljanna”._ Hajiya Majdiya ta wuni da waɗan nan kalamai na Mamy, sai kuma abinda ya faru a Kaduna na hararar da Mamy tai ma Ammie ya shiga dawo mata. Ta auna da yanda Rafeeq ya tsara kasancewar auren batare da ko su kansa dake ƴan uwansa ciki ɗaya sun san manufarsa ba. Kai hatta Mah-mah bata san da wannan shirin ba. Daga shi sai baba Sardauna sai Abbu da Alhaji ƙarami da Baban Yola. Kai itafa magana ta ALLAH zuciyarta ta fara mata rawa akan Mamy. Daga ƙarshe ta kasa haƙuri tai kiran RK a waya tace tana son magana da shi, dan ita irin mutanen nan ne mara iya riƙe abu a rai yayta damunsu, tafi son sha yanzu magani yanzu dan ma karta shiga haƙƙin mutum. Babu wani jimawa kuwa RK ɗin yazo tunda dama suna a kusa da gidan ne. Gefe suka koma yana tsokanarta da faɗin, “Aunty wai ko kuɗin zaki ƙara min ne, dan dama a talauce nake wlhy babu daɗi ango ya kasance babu kuɗi a jikinsa”. Dariya tayi da faɗin, “Kai dai son kuɗinka yayi yawa Rafeeq. Sai kace kayi wata tsiya a bikin ne kuda akaima auren gata. Ni yanzu ma da zaka saka min ƴar miliyan biyu zan so hakan ina son shiga kasuwa kafin na bar kanon”. “Ni da ke ba'a san wanda yafi wani son kuɗi ba ai, ina ma laifin kice dubu ɗari biyar”. “Ko ita na samu ɗin na gode”. “To wannan kam zaki samu ɗin”. “Aiko na gode ALLAH ya saka da alkairi angon Nuwaira”. Murmushi yayi da ɗan taɓe baki, itama sai ta murmusa ɗin kawai. Sai kuma ta kallesa da ƙyau. “Wai nikan Rafeeq na tambayeka mana”. “Ina jinki Aunty miya faru?”. “Ya akai al'amarin aurarrakin nan ya canja haka wai, tun jiya kowa abu ke cinsa a rai halin da Ajwaad ke ciki ya danne komai.” “Kai aunty dan ALLAH ku bar wannan zancen kawai, mu ɗauka haka ALLAH ya tsara dama tun farko, ni banga wani abun kace nace ba....” “Ba kace nace bane ba Rafeeq, wani abu ne ya ban mamaki yanzu, Aunty Babba da Umma sun sakani kira musu Aunty Kamila zasuyi magana sai na samesu cikin wani yanayi ita da ƴan uwanta, yayinda wani furuci nata ya daki zuwciyata, _wai ita bata jin zata iya cigaba da wannan kauda kan, gara ayita kawai ta ƙare tunda basu da wuta basu da aljanna._ To su waye? Kauda kan mi kuma ta daɗe tanayi har take jin bazata jureba a yanzu? Dan inda zaka gane maganar nada muhimmanci Maman Saheeba na ganina tai saurin fargar da su kasancewata, sannan a jiya sai bayan mun wuce asibiti da fin awa guda sannan ta zo ita da ƴan uwanta. Bazan ɓoye maka ba ranar bikin Yazeed a Kaduna da suka je wlhy wani mugun kallo naga tanama Hajiya Asiya, sai dai ban yarda hakan bane ba tunda ni dai ban san akwai wata matsala tsakaninsu ba a labarin rayuwar zamansu da naji ta baya, naso ɗan tuntuɓar Aunty Babba to amma kasan halinta akan Aunty Kamila”. Sosai RK ke kallon Hajiya Majdiya har takai ƙarshen zancenta, kafin ya ɗan yi jimm na wani lokaci. “Tab ɗin inji mata, to ai nima dai bayanan naki sun sakani a ruɗani, mizai saka Aunty Kamila tai wancan furucin? Kuma miya haɗata da Ammien su Maanal da zata mata kallon banza?”. “Ai shine, nima dai abin da ban wani ɗaukesa da muhimmanci ba, sai dai furucin nata na yau ya girgizani tare da dawo min abinda ya shuɗe. Shiyyasa nace bari na tuntuɓeka kodai akwai abinda kake ɓoye mana dan kowa yana mamakin haƙurewarka akan sadaukarma Ajwaad yarinyar nan, musamman ma ni dana san kana sonta sosai”. Fuskarsa da ɗan murmushi ya ce,............✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣0️⃣0️⃣
______________
.......“Aunty wannan maganar sai mun zauna kawai zan fahimtar dake komai. Amma maganar Aunty Kamila kamar ya kamata muɗan saka mata ido mu nazarceta dan karmu yanke hukunci kai tsaye akan abinda ba haka yake ba. Amma bazan ɓoye miki ba nima zuwanta Kano akwanaki game da auren Ajwaad ya tsaya min a rai na kuma jima abin bai bar zuciyata ba gaskiya, musamman dana san yaran data kawo akan ya aura shi hankalinsa baya akansu, sannan basu da nagartar da zaka zaɓesu a matan aure nagartattu ma ɗan daka haifa. Dan haka harna kasa haƙuri na tambayi Mah-mah akan Fadeel da Fawzan sune suka zaɓi matansu na aure ne? Bayan rikicin daya hana wancan auren na farko? Amma sai ta bani amsa da cewar ta manta gaskiya, amma kamar Aunty Kamila ce ta bada shawarar shi Fadeel ya aura ita Saheeba ɗiyar ƴar uwarta a lokacin, Fawzan kuma shine ya kawo matarsa da kansa, daga baya suka fahimci akwai alaƙa tsakanin Maman yarinyar da Aunty Kamila, amma hakan ai ba komai bane tunda Fawzan ɗin ne da kansa yace yana so”. “Tofa, kaji wata kuma sabuwa.” Shi dai RK baki kawai ya ɗan taɓe da faɗin, “To koma dai miye su suka sani. Yanzu yaya ake ciki? Yau za'a kawo amaren ne?”. Harararsa Hajiya Majdiya tayi, shi kuma ya sanya dariya yana susar kai...
Tattaunawar da Hajiya Majdiya tayi da Rafeeq ta sake sakata aune-aunen abubuwa, amma dai sai ta ajiye komai kamar yanda suka ajiye magana akan zasu nutsu su sake tattaunawa bayan biki...
________★
Ana yin sallar la'asar iyaye suka sanya Maanal a tsakkiya, nasiha akai mata mai ratsa jiki tana kwasar kuka. Ji take ita da zasu tausaya mata da sun barta. Dan tunda taji ana faɗar yau za'a kaita hankalinta ya sake tashi ta ƙara langarewa ita a dole bata da lafiya. Amma su Nene sun nuna idan taje can ta warware gara ta matsa tai jiyyar mijinta dake cikin halin ciwo. Duk da tun a jiya taji AA ɗin baida lafiya sai taji zuciyarta na ƙara shiga tashin hankali a yanzu. Amma dai ta danne. Kafin magrib an gama shiryata tsaf cikin lafaya ƴar ubansu mai ƙyau da tsadar gaske da Ammie ta tanada domin wannan ranar kawai ga autar ta, dan lokacin su Amal ma haka tayi. Aka kuma kawo alƙyabba data amsa sunanta alƙyabba aka ɗora mata akan lafayar, sannan aka baɗeta da ƙamshi na musamman. Ana idar da sallar Magrib jerarrun motoci daga zuri'ar Darma suka iso domin ɗaukar amaryar su. Anan fa ne sabon kuka ya tashi. Maanal ta ƙanƙame Ammie da su Shahidah tace babu inda zataje. Babu wanda kukanta bai bama tausayi ba, dan ita kanta Ammie kukan take sosai balle su Amaal, duk da tasan inda Maanal ɗin zataje baida maraba da gabanta, zama ta iya samun kulawar da ƙila bazata samu a gabanta ba, dan Oum ba akan Manaal ba ita kanta uwace a gareta kuma babbar Yaya da kake jin alfahari da samunta a gareka. To a haka dai da ƙyar aka raba Maanal da su Ammie. Yaya Fawzan da kansa zai ɗauki amarya, wannan alƙawarine da yay ma kansa dama shine zai kaima Auta Maanal a duk randa aka ɗaura musu aure. To Alhamdullah alƙawarin ALLAH kuwa ya cika. Kasancewar ba wani yawa ne da su ba ƴan kai amaryar tunda dangin Ammie ne kawai sai wasu a dangin Daddy da yay musu magana tun ɗazu suka baro can gidan bikin Huznah suka dawo nan a wadace suka shiga motocin, a kuma nutse babu hayaniya babu hargowa. Su Aneesa ƙawayen amarya na tare da ita. Sauran amare biyu dama sun iso suma tun ɗazun daga gidan Baban Yola, dan jiya da suka iso daga Yola a gidan baban Yola suka sauke turuga ba'a ƙaraso da su nan gidan Baba Sardauna ba da za'a amshi amaren gaba ɗaya sai yau. To su tun bayan sallar la'asar aka ɗakkosu, dan haka yanzu hankalin kowa ya koma kan isowar amaryar AA ɗin wato Maanal. Lokacin da suka iso bayan Oum ta gabatar da sujudar shukur ta fita da kanta har harabar gidan inda motar amarya kawai ta shigo ta fiddo Maanal da kanta daga mota. Aiko Maanal najin maganar Oum sai ta sake ƙanƙameta ta fashe mata da kuka. Itama Oum ɗin sai kawai ta fara hawaye da murmushi a lokaci guda. Nan ko wayoyi suka fara aikinsu na hotuna da video, a gefe dama Yaya Fawzan ya tanadi mai ɗauka dama na musamman da zai ɗauki komai na bikin nan dan AA idan ya samu lafiya yaga komai yanda ya kasance. Tunda ALLAH ya ƙaddara za'ai bikin yana a halin ciwo. An shiga da amarya Maanal har ɗakin Umma inda sauran amaren biyu suke, su Nene kuma aka basu masauki mai ƙyau dan Hajiya Majdiya ce tsaye akan komai. To da yake ma basu zo da shirin daɗewa ba sai suka wuce da wuri akan zuwa gobe zasu zo wajen walima in sha ALLAHU. Sai dai su ƙawayen amarya na tare da ita. Aiko sun haɗe da ƙawayen sauran amaren nan ko suka dunƙule anata kwasar hira. Maanal dai bata kula kowa ba, hasalima a kwance take zazzaɓi yay mata rijif. Suko sauran amaren Nuwaira da Raihana nata dama-dama da ita. Suma dai ƙyawawa kuma yarane kamar dai Maanal ɗin, garama Raihana ta girme musu dan itace yayar Nuwaira. Daka gansu suma kaga jinin Darma Family, dan kamaninsu da su Oum a bayyane suke sosai. Sun san Maanal a zamanin ƙuruciya, musamman Nuwaira da Maanal ɗin tasha jibgarta idan suka zo Kano a wancan lokacin. Sai wancan lokacin yayta dawo musu a rai suka amshi Maanal ɗin hannu bibbiyu, to dama dai baka gayama jinin Darma wulaƙanci, dattakonsu da mutuntawarsu ga kowa a bayyane take yaransu da manya. Sai dai su kuma basa ɗaukar wulaƙanci da raini ga kowa....
_________★