Kenza eBookz

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 72

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul - Chapter 72

Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 72: Ajiya a duhu book 1&2 complete by billynabdul Chapter 72. Zuwa washe gari hankalin su RK ya fara…

3,424 words

Zuwa washe gari hankalin su RK ya fara tashi akan rashin farkowar AA. Dole suka fara kaikawo a kansa da gwada dabaru. Amma dai babu alamar hakan, cigaban kawai da aka samu shine daidaituwar bugun zuciyarsa. Normal zuciyarsa ta koma dai-dai tana aiki, sai dai bayan ita babu wani ɓangare na jikinsa dake motsawa balle akai ga batun numfashi. Gashi dai nan kwance samɓal abinsa zagaye da na'urorin a ƙirjinsa da hancinsa har ma da baki. RK ne da yay wani tunani ya bama su Abbu shawarar ko a kawo Maanal asibitin ta gwada kira musu sunansa a cikin kunne. Babu wani ja inja su Abbu suka amince da hakan, dan irin wannan abubuwan duk dabarune na likitoci. Babu ɓata lokaci kuwa RK yay kiran Oum ya mata bayani. Dama shirin zuwa asibitin suke yi sai kawai aka saka Maanal ta shirya itama. Dama dai tayi wankanta kamar sauran amaren tun safe. Tana sanye da atamfa data mata ƙyau sosai. Sai farin mayafi daya sake ƙawata ƙyawunta da ɗaurin da Najma ta mata akan dole harda ƴar kwalliya. Sam fuskarta babu walwala sosai, dan kanta ciwo yake mata har yanzu. Ga kukan data sha a kwana biyun nan idanunta duk a kumbure. Koda suka taho ma tana kwance a jikin Oum ne. Bata wani yi mamakin ganinsu a asibiti ba tunda an sanar mata dama AA na asibiti, sai dai wani abu daya ɗan zunguri zuciyarta bayan sun fito a mota suma su Mamy dake a cikin wata motar sun fito, risinawa tai ga gaishesu, kanta a ƙasa shiyyasa bata banbance wanda ya amsa mata da wanda bai amsa ba. Sai da ta ɗago saboda kama hannunta da Oum tai zasu shiga cikin asibitin sai idonta ya sauka akan Mamy, wani mugun kallo ta samu idon Mamyn na mata akai-akaice, harga ALLAH sai da gabanta ya faɗi, amma kuma Mamyn tai saurin janye idonta dan dama a yanda take mata kallon bai zama lallai kowa ya lura ba gaskiya, da alama itama ta kamata ne a bazata. Sai dai kuma komai ya faru ne a idon Hajiya Majdiya, dan haka itama zuciyar tata sai da ta girgiza... Sun dai shiga ciki, inda suka samu su Babban yaya da su Abah su Baba Sardauna, Baban Yola da su Abbu duk acan, kusan ma duk mazan family ɗin na'a asibitin ne. Hakan ya ƙara saka Manaal a cikin matsanancin kunya, ta ƙara jan mayafinta ya rufe mata rabin fuska kanta kuma a ƙasa. Cike da girmamawa taje har gaban su Baba Sardauna ta durƙusa tana gaishesu kasancewar su iyayen duk suna a waje ɗaya ne zaune. Dukansu babu wanda fuskarsa bata kasance a cikin fara'a ba. Suka shiga amsa mata da kulawa da sanya albarka shi Baba Sardauna ma harda tsokanarta irin wasa na jika da kaka. Ita dai kanta a ƙasa fuskarta a rufe babu wanda zaice ga'a yanda take. Hakan sai ya ƙara saka musu ƙaunarta da jin gamsuwa da ita, dama kuma a binciken da sukai basu samu wani aibu a tare da ita ba kamar yanda suka sami akan Huznah, balle ma sun san ƙuruciyarta kaf ɗinsu musamman ma shi Baba Sardauna da Baban Yola da Abah. Abbu ne kawai sai tsintsa-tsinta saboda lokacin ba'a ƙasar suke ba. RK ne ya jagoranceta zuwa ɗakin da AA yake, karon farko kuma kenan da wani zai shiga ya ganshi idan ka cire likitoci da kullum ke kai-kawo a kansa. Wani bala'in girgiza zuciyar Maanal tayi da ganin yanda AA ɗin yake zagaye da na'urori tun kan su shiga, sai jikinta ya fara rawa. RK ya riga yasan tata matsalar itama, dan haka da sauri kuma cike da lallashi ya ce, “Please Maanal relax, ba wata babbar matsala Ajwaad yake a ciki ba, numfashinsa ne yay nisa da tun a daren jiya muke saka ran dawowarsa amma shiru, amma in sha ALLAHU idan yanzu kikai juriya ringa kiran sunansa a cikin kunne muna fatan nasarar dawowar tasa dan bugun zuciyarsa ya dawo normal. Dan haka ki kwantar da hankalinki nutsuwarki muke buƙata. Sannan zaki kira shi da sunan Besty ne ba sunansa ba.....” Da sauri Maanal ta kalla RK a karo na farko. Kansa ya jinjina mata. “Hakan shine mafita Maanal, dan wannan halin da yake ciki yana da alaƙa da tsoron rasaki da ya shiga, idan kuma ya jiki a kusa da shi a yanzu in sha ALLAHU muna fatan nasara.” Sosai ta zubama RK ɗin idanu saboda kalamansa, da alama jin cewar a kanta ya shiga halin ya girgizata. Shima RK ɗin ya fahimci hakan, dan haka yay murmushi da faɗin, “Maanal wasu abubuwan ba kai tsaye muke fahimtarsu a rayuwa ba sai dalili ya ratsa. Shiyyasa barin wasu al'amuran a dunƙule yafi alkairi sama da buɗesu ma duniya ko mu mu sansu. Yanzu dai kece hope ɗinmu na ƙarshe akan Ajwaad, dan haka bismillah”. Gaba ɗaya jikin Maanal ya gama mutuwa, hawayen da take ta faman riƙewa suka shiga zubowa, dole ta saka gefen mayafinta ta share sannan suka ƙarasa shiga cikin ɗakin. Sun sami likitoci biyu sai Abbu a tare da AA ɗin, dan haka kai tsaye gaban gadon da AA ɗin yake kwance aka kaita, tare da nuna mata kujerar dake gab da gadon ajiye. Sai da ta zauna sannan ɗaya daga cikin likitocin ya matso ta ɗayan ɓangaren AA ɗin hannunsa riƙe da file, umarnin riƙe hannun AA ɗin ya bata, dan haka tai diri-diri na jin kunya tana satar kallon inda Abbu yake. Murmushi Abbu yay a karo na farko, tare da ƙarasowa gaban gadon cike da lallashi ya ce, “My dear karki damu kinji, ki saka a ranki ceton rai zakiyi dan Ajwaad na a gaɓar rayuwa ko mutuwa ne a yanzu, in har zuciyarsa ta tsaya daga aiki to shike nan dan itace kawai ke nuna mana yana a raye a halin yanzun. Ke kuma mun tabbatar kina a cikin wannan zuciyar tasa, wannan abun da zakiyi shine zai motsata da ƙarfin ikon ALLAH ƙarfin bugunta ya gauraye raunin gaggangar jikinsa dukkan hanyoyin numfashinsa su buɗe”. Kanta dake a ƙasa ta jinjinama Abbu, kafin a hankali ta kai hannunta dake zane da baƙin lalle da ja saman nashi dake ajiye a kan shafaffen cikinsa. Jitai wani irin shock ya shigeta, ta ɗan ja hannun baya tana rumtse idanu, fin sakan biyu kafin ta sake kaiwa saboda maganar da Doctor ya sake mata. Gently ta sarƙe tafukan hannunsu cikin juna, sai ta samu kanta da matsesu, wata rarrauniyar ajiyar zuciya na suɓuce mata. Sanyin tafin hannun nasa ratsata yake har cikin ƙwaƙwalwa, yayinda nata dake da ɗumi na tasiri a daskararriyar gangar jikinsa. Sai da ta sake matsar da kujerar sosai gaban gadon kafin ta samu damar rankwafar da fuskantar a saitin kunnensa nunfashinta dake fita a sarƙe na sauka a ciki. Bugun zuciyar ta na ƙaruwa saboda yanda tasirin ƙamshinsa da ya gama kama masa jiki ke shiga cikin ƙofifin hancinta. Idannunta a lumshe, lips ɗinta na rawa, muryarta da wani irin rauni da sanyi kamar mai raɗa ta furta, “Besty! Besty! Besty ka tashi gani a tare da kai, Maanal ɗinka ce, Bestyn ka, ƙanwarka daka raina da hannayenka, ka buɗe idonka dan ALLAH ka ganni kaji Besty, muci abinci tare, muyi wanki tare, muyi hira tare, ka kaini kitso ina maka kuka kana lallashina. Na takalo faɗa ka tare min koda su Didi ne.” sai hawaye sharrr suka shiga sakko mata daga idanu suna sauka akan jikinsa. Sosai kuka ya sarƙeta harta kife fuskarta a jikinsa ta sake shi mai ƙarfin gaske a cikin kunnen nasa..........✍️

09032345899

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_* _Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖1️⃣0️⃣1️⃣

______________

........Babu wanda ya dakatar da ita a cikin likitocin, saboda hakan su ya musu dai-dai ne, dan RK ma gefe ya maida kansa yana murmushi. Hakama Abbu tausayin yaran ne ya wani sake mamayesa. Al'amarin kamar wani film sai ga yatsan ƙafarsa babbar ya motsa. Ai wata irin zaburar farin ciki likitocin da dama idanunsu tsaye suke kyam akan duka gaɓɓan AA ɗin sukai. Ita dai Maanal da gaske kuka yaci ƙarfinta ta yanda tama manta da ba ita kaɗai mace ba a ɗakin. Sai da hannun AA dake cikin nata yay wani irin nasifar matse nata, shi kuma yay wata irin yunƙurawar zabura har sai da gadon yay girgiza wasu a cikin igiyiyin na'urorin dake jikinsa suka fincike kansu da kansu. Da wani kalar sauri ta ɗago itama, yayinda su RK suka zagayeshi suna ambaton Alhamdullahi a tare. Sosai riƙon da AA yayma hannun Maanal ke azabtar da ita, dan riƙo ne na mazan gaske, amma ta daure dan anyi-anyi a raba hannun nasu hakan ya ta gagara, sai Abbu yace a barshi kawai a hankan. Haka yana riƙe da hannunta a gaban idonta suketa ƙoƙarin dai-daita numfashinsa da zaburar da yake yi. Fin mintuna talatin kafin komai ya daidaita ya koma dan kansa ya nutsu, yayinda numfashin nasa ke fita a hankali a hankali... Ƙasa-ƙasa Abbu dake kallon Maanal ya ce, “Sake kiransa”. Kanta ta jinjina, a hankali ta sake ɗan matsawa gab da gadon ta ce, “Besty!!”. Hannunsa dake riƙe da nata ya ɗan motsa, sai kuma ya ɗan ƙara damƙe natan ta yanda har sai da ta ɗan yamutsa fuska dan zafi. A hakan ta cigaba da kiran sunan nasa. A yanzu kam idanunsa dake rufe ya ɗan fara motsawa, sannu a hankali dogayen eyelashes ɗinsa dake baƙaƙe siɗik kwance suka fara rawa suma, sai kuma ya fara ɗaga su kaɗan-kaɗan tsagar idanunsa suka sake bayyana. Nuni Abbu yake mata da hannu alamar ta cigaba da kiransa dai. Ita kuma tanata maimaitawar batare da gajiyawa ba, har ALLAH ya bama AA damar buɗe gaba ɗaya juyayyun idanunsa dake a kumbure kuma jazur. Lumshesu ya sake ƙoƙrin yi irin luuuu ɗin nan, sai dai kafin su gama rufewa ya sake ɗagasu suka buɗe saboda tasirin da muryar Maanal ke cigaba da yi masa a cikin kunne. A buɗewa ta biyun kam sosai ya buɗesu, ya kuma tsaidasu a kanta, yanda ya zuba mata su cikin tsakkiyar nata idanun kamar ɗan maye yasa tsigar jikinta tashi. Dole bakinta ya kasa cigaba da motsawa ta daina kiransa, haka su Abbu ma sunyi tsittt kamar ruwa ya cinyesu a ɗakin. Fin minti biyu yana mata wannan kallon kafin ya sake ƙoƙarin jan idanun zai rufe Abbu ya kira sunansa shima.. “Ajwaad!!”. Luuuu ya sake ƙoƙarin buɗe idanun ya saukesu akan Abbu. Murmushi yay masa, sai kuma ya nuna masa Maanal. “Kasan wannan?”. Idanun nasa ya juya a hankali ya sake maida su kan Maanal da Abbu ya nuna. Ɗan sake kafeta yay da kallon kafin ya maido idanun kan Abbu ya jinjina masa kansa alamar ya santa. Murmushi Abbu yay da jinjina kansa ya ce, “Alhamdullahi minene sunanta?”. Idanunsa ya ɗan rufe kamar yanda ɗabi'arsa take musamman a lokacin da bai son yin magana, kafin ya buɗe a karo na farko ya motsa pink lips ɗinsa da suka tattare waje ɗaya suka bushe kaɗan ya furta, “Besty”. Babu wanda yaji sautin muryar amma sun fahimci abinda ya faɗa daga motsin laɓɓansa. Cike da gamsuwa fuskar Abbu da murmushi ya nuna kansa shima ya ce, “Nifa?”. Nan ma lips ɗin ya motsa kawai ya ce, “Abbu!”. Nan ma Abbu ya jinjina kai ya juya ya nuna masa RK ya ce, “Wannan fa?”. A mamakinsu sai ya kauda kai yaƙi magana. Abbu ya sake maimaita masa, batare da ya juya ya kalla RK ɗin ba ya ɗan jujjuya kansa alamar bai sanshi ba. Kasa haƙuri RK yay ya fashe da dariya. Abbu ma dai murmushi yake sosai. Su dai sauran likitocin basu fahimci abinda ke faruwa ba sukam, amma sunyi mamaki da yace bai sanshi ba. Maanal da abin ya bama mamaki itama ta ce, “Rafeeq ɗin ne baka sani ba?”. Idanunsa ya ɗaga a hankali ya zuba mata, itama kallonsa take fuskanta da mamaki har yanzu. Cikin dariya RK yace, “Barsa daughter, zan fasa tariyar taki ne har sai randa ya fara ganeni ɗan rainin hankali”. Barin wajen Abbu yay yana dariya da girgiza kai, yayinda AA ya ɗan juya ido alamar don hararar RK yake son yi amma idanun sun masa nauyi, sai ya sake jimƙe hannun Maanal da ƙarfi har sai da ta saki ɗan ƙara dan dama a takure take dama, hannun ya mata tsami sosai. Karo na farko AA ɗin ya kalli abinda ke cikin hannun nashi, da mamaki ya zubama hannun nata mai zane da lalle raɗam idanunsa kumburarru. Fuskarsa na nuna mamaki ya juya ya kalleta, fuska ta ɓata sosai da tura baki gaba. Idanunsa kawai ya rufe, dan a karo na farko sai ya fara jin kamar mafarkin daya saba ne. (Wai ya akai ma ta kasance a kusa da shi, hannunta kuma cikin nashi? Ya rabba) Ya ayyana a zuciyarsa yana sake buɗe idon dai a kan hannayen nasu dan ya yarda kawai mafarki ne. Cike da shaƙiyanci RK ya duƙo saitin kunnensa ya raɗa masa, _“Kada ka wani firgita kanka yanzu kam HALAL ce. Besty ta zama mallakin Besty yarona”. Da sauri AA ya juya yana kallonsa. RK ya kashe masa ido ɗaya”. Harga ALLAH daburcewa AA yayi, sai numfashinsa ya nema fara wani irin fisga. Dai-dai nan Abbu da yaje yayma su Oum albishir ɗin farfaɗowar AA ɗin ya sake shigowa. Da sauri ya ƙaraso gaban gadon yana faɗin, “Subahannallahi mi kuma ya faru?”. Kallon da sauran doctors ɗin kema RK yasa Abbu kallonsa shima. “Miya faru Rafeeq?”. “Relax Abbu babu komai fa. Kawai na masa albishir ne”. Baki buɗe Abbu ya ce, “Amma kasan zaka iya maida shi cikin suma wane irin likita ne kai?”. Dariya RK yay. Ya ce, “Ai karka wani damu Abbu koya suma sai ya sake farfaɗowa. Ɗan rainin wayon bani yace bai sani ba”. Da sauri Abbu ya jawo abu alamar zai daki RK, aiko ya fita da gudu yana dariya.....

_____________★

Sai muce Alhamdullah, zuwa bayan sallar la'asar AA da aka saka barcin awoyi dan brain ɗinsa da zuciyarsa su zama fresh ya sake farkawa. Zuwa yanzu dai kam anata shiga duba shi, dan har an canja masa ɗaki ma. Maanal dai tun da ya fara barci suka wuce gida ran Oum fes, dan anayin azhar aka fara gudanar da walima. Bayan an idar da la'asar akai buɗar kai, a kuma lokacin ne AA ya farka acan asibiti su Abah zagaye da shi. Dan duk mazan ne dai yanzu matan duk suna gida wajen walima. Duk da dai hankalin Oum da Maanal duk yana asibitin amma suna daurewa ne kawai na dole. Hakama Mamy da gaba ɗaya take a jagule dan ko wajan walimar bata zauna ba, sai ma ƙirƙirar barin gidan da sukayi ana fara walimar zuwa can gidan babbar yayarsu. Acan suka samu damar baje zantukan bakinsu yanda ya kamata. Da tsare-tsaren yanda zasu cimma Maanal da Oum, dan yanzu kam dai yaƙin ya zame musu biyu. Sai batun Nuratu da suke tunanin Darma Family ɗin da zasu iya cewa bazai yiwu a wannan satin ba saboda halin da AA ɗin ke ciki. Dan haka hankalinsu a tashe yake tannan ɓangaren shiyyasa suketa faman tausar Mamyn akan son birkicewar da take neman yi.... Shida na yamma aka kammala komai da komai, aka shirya amare domin musu rakkiya. Nuwaira gidan Abbu za'a kaita ɓangaren RK daya sha gyara, sai daga baya zai ɗauka abarsa su wuce Abuja tunda can rayuwarsa take shi. Sai Raihana haɗaɗɗen gidan Uncle Najeeb dake kusa dana Baban Yola shima dai, hakama su Modibbo duk kusa da kusa suke. Wannan kusan aƙidar Darma family ce, da wahala kaga yaransu sunyi nesa da su.. Maanal dai tana nan gidan Baba Sardauna su sai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce Abuja. Danginta dai da ƙawayenta da suka zo wajen walima duk a ranar suka tattare a can gidan da suka sauka. Suma dai zuwa gobe in sha ALLAHU zasu wuce Kaduna. Su Didi wayo sukaima Maanal akan zasu dawo gobe suka gudu, dan haka ta sakankance da hakan. Ga kuma Najma na ɗebe mata kewa ga Oum. Dan yanzu tana a ɗakin Oum ɗinne. Zuwa bayan isha'i gidan Baba Sardauna ya rage mutane sosai, dan wasu zasu kwana a gidan Baban Yola da gidan Abbu ne da sauran gidajen ƴan uwa. Zuwa safiya kowa ya kama gabansa, dama dai danginsu ne na Yola sukafi yawa. Sai dangin mahaifin su Nuwaira da ƴan kura dangin Abbu. Kusan takwas da rabi Oum ta saka Maanal shiryawa dan zasuje asibiti sake duba AA, duk da Fawzan ya kira Oum yana sanar mata Autan nata ya saka bore shi sai an sallamesa sai da Abah yay masa jan ido da Abbu sannan. Amma yace shi gobe babu wani asibiti da zai wuce gida zaije, tunda an sanar masa gobe zasu wuce Abuja. Ji Maanal tai kamar ta langare tace bata da lafiya. Dan dama ɗazun allurar da akai masa ce ga ceceta suka gudo. Amma babu yanda ta iya dole ta shirya ɗin suka wuce. Sauƙin ma basu kaɗai bane. Harda Umma, Hajiya Majdiya, Mamy, da wasu sauran dangi da suka rage manya. Sai ita sai Najma a yara da su Saheeba. Sun iso asibitin abin mamaki suka sami ƴan uwan Mamy harda Nuratu da basu san sanda ta zo Kanon ba. Dan tunda aka fara bikin nan babu ita. Tunda Mamy taga Nuratu take ta faman murmushi, yayinda Nuratun babu kunya ta wani rungume Mamy. Su Mamanta kuma suna gaisuwa da su Oum. Sai da aka gama gaishe-gaishen sannan suka shiga, dan suma su Nuratun isowarsu kenan ashe. Oum dake riƙe da hannun Maanal ce a gaba, sai Umma sannan Mamy da Hajiya Majdiya dake a jere. Bayansu su Nuratun ne da su Shaheeda. Zaune yake kam yanzu an ɗan ɗago gadon ta saitin kansa sosai sama sai ya zam ya jingina. RK na tsaye a gefensa yana cire masa drip, babban yaya a kujera, Fawzan a gadon kusa da ƙafafunsa da kofi a hannu, sai Uncle Mahmud da Uncle Hussain nata ɗayan gefen zaune a kujeru suma. Yanda fuskokinsu ke wasai zai baka tabbacin hira suke cike da nishaɗi. Yayinda AA ke ɓata fuska yana kallon kofin shayin hannun Yaya Fawzan da alamu suka nuna shi zai ba mawa. Sannu da zuwa gwarazen mazajen kema iyayen nasu, suka kuma shiga tashi domin basu kujerun. Yayinda AA ya zubama Maanal idanunsa shanyayyu har yanzu. Ita ko tunda dai masa kallo ɗaya ta janye abinta kanta ma a ƙasa take gaida su babban Yaya. Cike da neman magana Ya Fawzan ya ce, “Kai Alhmdllh gara ma dai da kuka zo. Lilly zo kiji da mijinki dama daru yake ma mutane yaƙi cin abinci”. Ji Maanal tayi kamar ƙasa ta tsage ta shige. Ta sake riƙe hannun Oum sosai cikin nata tana matsawa jikinta. Murmushi Oum tayi da faɗin, “Kace kana nan kana takura min shi da takurarka”. “Oh Oum hakama zakice. Shikenan wlhy Lilly zauna ku ƙarata tunda babarsa ma maimakon ta gode min kinji mitake faɗa.” “Eh anji ɗin”. Cewar Oum tana zaunar da Maanal a inda Fawzan ɗin ya tashi kusa da AA kenan a gadon jiyyarsa. Ta kuma amshi tea ɗin ta miƙa mata. Kuka kawai ya rage Maanal ta saki dan kunya. Dan yanda ta kalla Oum kamar zata fasa ihu. Amma sai Oum ɗin tayi kamar bata gani ba ta damƙa mata kofin a hannu. Dariya su Umma daketa tsokanar Maanal irin wasan kaka da jika tun jiya take musu. Ta zauna a kujerar da Babban yaya ya tashi yana gyara mata tana faɗin, “Ɗan nema, ni zaka kalla ba ita ba ai, kasan dai da tsohuwar zuma ake magani”. Dariya su Oum sukayi, AA daya shagala a kallon Maanal tun ɗazun ya janye idanunsa a hankali yana ɗan murmushi saboda zancen Umma. Dama shi bai iya maida wasa sai Fawzan da Babban Yaya. Kosu kakanni sukai masa iyakarsa murmushi ne. Umma ta riga ta san hali dan haka bata damu ba ta maida kallonta akan Maanal da tunda Oum ta damƙa mata kofin shayi ta kasa motsi. “Maanal matsa ki bashi kada ya huce kinji, idan ma dan nice bazanyi kishi ba, zan daure na haɗiye ko iya na yau ne tunda amarya kike. Amarya kuma ance kota buzuzu ce daɗin suna ne da ita”. Dariya su Fawzan suka sanya. Hakama su Oum.........✍️

Readers Also Read