ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 10
ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 10: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 10. Da dare yayi Ya Almu ya kara bani maganin na sha nayi barci sai na samu sauƙin ciwon kan,…
4,322 words
Da dare yayi Ya Almu ya kara bani maganin na sha nayi barci sai na samu sauƙin ciwon kan, sannan na samu barci a hankali tunanin da nake yawan yi ya ragu, sai tsoron yadda zan isa gida, ya zamu kare da Iyayenmu? Sai tsoro ya kara kamani. Haka kwanakin suka tafi har zuwa ranar da zasu mai da ni, da wuri muka bar Kaduna, domin ya ce yana son ya dawo ranar ne, haka yasa muka fita da wuri da yake maganina ya saba da jinina ba wani barci, sai dai nayi kaɗan kafin muka iso saminaka. Ya Almu ya sayi tsaraba muka cigaba da tafiya har zuwa rahama rishi, tunda muka iso nabardo na ji tsoro ya kara mamaye ni, kafin karfe biyu na rana mun iso garin Bauchi. Sai a lokacin na rude kamar zan shiɗe, har muka iso kofar gidan aka bude get din gidanmu ya shigar da motar, kasa fitowa nayi bayan yayi parking. "Darling sister shiga gani nan zuwa!" "Tow!" Na fada ina jin wani irin tsoro yana cika ni, ina saka kafana a waje naji kamar an kwashe min karfina haka na cigaba da tafiya har cikin gidan a dan barandar da zata kai ni cikin gidan anan na hango Ya Hafiz tsaye, wani irin bugawa zuciyata tayi naji kamar na juya da gudu. Kanshi a sunkuye da alamu waya yake cikin farin ciki da nutsuwa, kamar ance ya d'ago kai sai a kaina. Ji nayi kamar zan takowa yayi nima na fara yin baya ji nayi an janyo ni baya. Sai da na sake wata irin ajiyar zuciya da naji kamar numfashina zai bar jikina. Baya Ya Almu ya dawo da ni. "Wani irin hauka ne haka?" "Ba ruwanka Malam matata ce!" Ya fada yana kokarin kai hannu ya riko ni, kunsan a binka da soja ba sai Ya Almu ya sake ledar tsarabar ya kai mishi wata mahaukaciyar naushi ba, sai da ya fasa mishi baki, sai da ya zube a kasa yana mai d'ago kai yana faɗin. "Ni ka nausa?" Ya fada yana kallona murmushi yayi sannan ya mike tare da nufar cikin gidan, haka na rike rigar Ya Almu. "Yaya ina jin tsoro." Shigar Ya Hafiz shi ya sanar da yan gidan mun iso, Ya Ado ya fara fitowa. Ganin yadda nake rike hannun Ya Almu na tirji na ki shiga gidan, isowa yayi ya riko hannuna yana faɗin. "Princess welcome back!" A hankali na kalle shi. "Abba yayi fushi ko?" Girgiza kai yayi ya riko hannuna muka shiga cikin gidan, wanda yayi daidai da fitowa Hajiya tana faɗin. "Aure sai kace na jaraba dole ne sai ka zauna da Kanwarsu? Ace kamar Almu ya d'aga hannu ya zabga maka naushi akan Kanwarsu aka fara samun matsalar aure ne!" Lokacin da muka isa parlourn ina rike da Ya Ado, har muka zauna jikina bai daina rawa ba, ba zato ba tsammani Mama ta rufe ni da duka, Ya Ado yayi maza ya kare ni, Ya Tahir shima ya taso suka kare ni, haushi ya kama Mama ta dauki takalmi tayi ta dukan mu da shi haka Yayuna maza da matan nan da ake zaune dasu a dakin suka rufe ni, kallonsu na tsaya ina yi, madadin na ga damuwa sai naga suna murmushi. A hankali na daura kaina a kirjin ya Ado na rufe idanuna har Mama ta daina dukarsu ta fashe da kuka, hannu Ya Almu ya saka ya toshe min kunnena. Bude idanun nayi ina kallonshi, murmushi yayi min hawaye na zuba daga idanunsa, ban san me Mama take fada ba, amma yadda suke kuka ya sani zare hannunsa a kunnena. "Kin zame min ƙaddara ko numfashi bana iya ja mai kyau kin lalata min suna a ko ina kowa gani yake ina daure miki kugu ki yi yadda kike so, da wanda ya kai ya gaya min magana da wanda bai kai ba mai na miki na cancanci haka Lubnah wannan shine kyautar da zaki min na haihuwarki." "Idan na isa da ita, ta bi mijinta bana son jin wata kalma su kuma duk wnada ya sake shiga rayuwar auren Lubabatu Allah ya isa ban yafe masa ba." A wannan zuwan Baban Jama'are bai zo ba su Goggo ma basu zo ba. Haka Yayuna suna ji suna gani na bi Ya Hafiz da Hajiya Baba Malam yana faɗin. "Allah ya maka albarka dole ka ga alkhairi a rayuwarka dole kayi gba ba zaka tab'a ganin baya ba." Wannan addu'ar da Uba yake yiwa dansa duk saboda yabi son zuciyarshi ne.
Haka na cigaba da bin su Ya Almu ya biyo ni da wata karamin akwatin da kayana da maganina yake ciki sai wayata da Aunty Hindatu ta bashi ya bani, sai da ya bani ya juya ya kwashe ya Hafiz ya buga shi da kasa tare da take wuyarshi. "Wannan kashedi na maka, abinda zai faru yana zuwa idan na samu labarin ka mata wani abu sai na maka dukar da ba zaka moru ba." "Amma dai baka da mutunci!" Inji Hajiya. "Ga mara mutunci nan a kasa ya nuna mata Ya Hafiz, tashi yayi ina kallonshi yayi murmushi ya ce mishi. " Yadda kuka min Allah yana gani kome dai wuce! " Daga haka ya budewa Hajiya gaban mata ta zauna sai ni na bude baya na shiga. Tunda muka fita a gidan suka shiga zagina. Dakyar ya iya danne kanshi. "Ina shiga dakina ya biyo ni."
Ban san yadda zan fada ba, amma a ranar Ya Hafiz ya cika min raina da wani irin tsoro he tell me kaf duniya babu wnada ya isa kashe mishi aure, sannan babu wanda ya isa ya kara takowa ko ni na fita, gidansa shine kurkukuna har na mutu be with keep me saboda ya nunawa Yan uwana babu wanda suka isa su mishi. Kun san abinda ake kira tsoro? Anya kusan ma'anar tsoro, to kada Allah ya jarabce ku da tsoro domin tsoro mugun abu ne me kashe rayuwa da kome, sai da ta kai Ya Hafiz ya birkita min ƙwaƙwalwa, ko karar kwano naji sai na ji kamar na mutu, domin ko yaya naji kara zan dawo daki da gudu nayi ta kokarin rufe kofar, domin yadda yake dukana yana min barazanar zai kashe ni, kuma Hajiya tana gani tana ji. Bata hana shi ba.
Wata daya zuwa biyu na manta da wani zancen magani tow ya kwashe yana kawo min wnada yayi mishi, ko ban sha ba zai matse ni sai na sha, ganin yadda nake kin sha sai ya shiga jika maganin a gora ya daura min sai na shanye, duk saboda me yasa? Saboda yadda aurenmu zai yi survive haka abinda ya aikata zai rufe har abada, da bakinsa ya ce min. "Idan na sake ki, zan kara gaya miki ba zaki tab'a samun wanda zai zauna da ke, ki rufawa kanki asiri ki dawo dakinki, domin ni dai bani da matsala. Zan zauna da ke kamar yadda wancan tsohon da Malam Babba suke son na zauna da ke. " Yana murmushin keta, tun daga lokacin duk maganar da zata fito daga bakinsa iya abinda yake aikatawa yake gaya min. " Ba zan tab'a sake ki ba haka zaki mutu a dakin nan gawarki kawai za a sallata! " Ire-iren waɗannan maganar kawai suka kashe ni, haka kawai zasu turo min Yara suta ihu a dakina, duk yadda naso na fahimci kome ya dagule min, ganin yadda nake kokarin rasa lafiyata ya kara dawo min da maganin ba batun ganin likita ma, sai da na fata shan maganin ya ga da gaske na fara dawowa dai-dai sai ya sake daukewa, ko sati ba ayi ba ciwon ya kara dawowa.
*** Aunty Innah. Kuka take tana faɗin. " Don Allah ki saka baki muje my duba ta, sau biyu ina mafarkin tana niman taimako, don Allah ki yi wani abu Lubnah tana niman agaji!" Ta fada tana kuka. "Idan baso kike ki kashe min aure ba ai ya kamata ki bar gidan nan kada ya dawo ya same ku, ai kune kuka dagula kome! " " Mama bamu bane, kune Mama kune kuka hana ta magana, Allah kaɗai yasan ciwon da take ji, Allah kaɗai yasan yadda zuciyarta take cike da rauni." " Ai haka ne? Tow ni ba zaki kashe min aure ba, fita ki bani wurin mun gode da muka saka Lubnah a cikin wannan halin!" Kukan Innah yayi yawa wanda ya janyo hankalin Ya Sani da yake dakin Yadiko, fitowa yayi ya nufi dakin, yana shigowa ya same Innah tana rokon Mama, juyawa yayi ya fita, bai tsaya ba sai gidan wani abokinsa wanda ake kiranshi da Sadiq Bhai, saboda yadda yayi kaurin suna a aikin daba, ya gaya mishi inda zai raka shi. Shiru yayi sannan ya ce mishi.......... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
*Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641
Posting Arewapen da Telegram
SHA HUƊU
"Bari na kira maka abokina a zangon ni yanzu na tafi zango al'amarin zai girma fiye da haka." Haka ya kira abokin ya gaya mishi, shi kuwa ya ce Sani yaje, lokacin da ya isa zango suka rufa mishi baya, har kofar gidan da aka rufe ta ciki, buga kofar Sani yayi Karimah ta amsa da cewa. "Waye ne?" "Sani ne!" "Ok ka kira shi ya ce kada na budewa kowa ya shiga!" Wani Ash'ar da ya danna tare da yin baya ya daki kofar sai da ta ɓalle, daga jikin bangon suka take kofar suka shiga yadda yan sara suka suka cika gidan yasa ta yin shiru.
Ina kwance kamar a mafarki na ji muryan Ya Sani, bude ido nayi ina kallonshi kafin na lumshe, lekowa yayi ya ce musu. "Don Allah ku nima mana Napep." Ya fada yana dauko min hijab ya saka min tare da d'aga ni, ya fitar da ni waje aka saka ni a Napep. Ya koma dakin ya rufe ya tawo da key, tun a hanya ya kira Aunty Hindatu ya ce mata. "Maza mu hadu a asibiti gata nan ina ganin mutuwa zata yi!" "Waye?" "Lulu!" Ya fada da karfi, yana tallafo ni, kafin mu isa asibitin kowa ya hallara haka aka wuce da ni emergency, ni dai ban kara sanin me ya faru ba.
Sai after few days, na farka shima din bana magana, domin idan na kalle su sai naga suna komawa Ya Hafiz haka yasa ko na buɗe idanun zan rufe da sauri. Maganar da Ya Umar yake na fahimci an kama Ya Sani, wanda shi kaɗai aka kama kuma maganar da ake wai Abba ya zare shi cikin Yaransa, ya kara da cewa ko mutuwa nake ina dawowa na koma dakina idan kuwa Hafiz yace ban koma ba tow kuwa wannan karon sai dai Mama da Yadiko su bar mishi gidansa. Wani irin tsoro ya kama ni, sai da na samu sati biyu me kyau aka sallame ni, anan muhawara ya tashi na ce musu. "Ku bani kuɗina!" "Me zaki yi da shi!?" "Ku bani kawai!" Haka dai muka wuce banki aka cire dubu dari biyu da hamsin, sannan na dawo gida da shi, ban d'aga idanun nayiwa Ya Hafiz magana ba.
Ban san ya aka yi na samu wata kwarin gwiwa ba, amma ina buƙatar hujjar da xan rabu da Ya Hafiz, shi yasa na dawo na gaji da barazanar Abba akan Mama da Yadiko, haka ya cigaba da iskanci kuma har lokacin Ya Sani an wuce da shi gidan gyaran hali, haka na cigaba da zama tsawon kwanaki.
Ranar da Ubangiji ya kawo min karshen duk wata damuwa, shine ranar Talata na tashi na daura abin karyawa, nawa iya ni cikina ni daya na daura, bayan na gama na zauna ina hutawa, sai ga Karimah. "Ke ina ruwan zafin da zamu karya?" Banza na bawa Ajiyarta ta fita a fusace lokacin na hada nawa na fito na wanke cokalin sai ga Ya Hafiz, yana zuwa ya ce min. "Ba dake ake magana ba yar dangi?" Ganin naki kula shi, har na shiga daki ya biyo ni ganin yadda na haɗa nawa na nufi wurin kofin yana ɗauka bai wata wata ba ya watsa min tafasasshen ruwan zafi a gadon bayana, ji nayi kamar dukka jikina ya matsa min, ga rigar jikina irin robar nan ne mai daukar zafi, yaga rigar nayi na watsa garin cire Braz dina na kwaso har da fatar bayana, zama nayi ina haki domin yau kan Allah ya kawo sanadin kenan, a hankali na d'ago kai na kalle shi, yadda nake kallonshi ya razana karshe fita yayi daga daga dakin, na dauki wayata na kira Ya Umar na ce mishi. "Don Allah ko zaka zo muje asibiti?" "Baki da lafiya ne? Gani nan don Allah ki jira gani nan!" Ai tun kafin ya iso Ya Hafiz ya gudu, yana shigowa yayi ta kwala min kira, a hankali na fito koda na iso gabanshi zubewa nayi a sume, haka yasa saka shi shiga tashin hankali, yadda na kifa tare da faduwa akan hannuna, shi yayi sanadin gocewar kashin hannuna, yadda fatar bayana ta bare jajjur ya bashi tsoro, haka ya riko ni, muka nufi asibiti.
Kiran Aunty Hindatu yayi ya gaya mata, itama tazo, kafin kace kwabo Aunty Raliya da take Jos ta iso, babu wanda ya sake ya gayawa su Mama da Yadiko. Kawai anyi shiru an barsu. Aunty Hindatu ta kanta ta koma zango ta dauko kuɗina tare da kayana ta kwaso min. Haka kwantar dani tsawon kwanaki ashirin ana wanke ciwon kafin aka sallame ni don ya kame. "Yanzu ina zaki?" "Jama'are na gaya musu shirina." Dama Ya ado yasan kome don haka ya ce na jira shi Aunty Munah da take River sai gata, don ta ce ba zata sake barin kallo ya wuce ta ba, Ya Abba daga Maiduguri ya dirko, kwana ɗaya muka kara gaba sai Jama'are. A gidan Goggo Alti muka fara sauka aka muka huta aka yi girki aka yi sallah sannan aka ci na nuna mata bayana da abinda ya faru ba kara da gaya mata gaskiya na gaji dari bisa dari ya goya min baya. Na nufi gidan Kakanmu. Da taimakon Yayuna muka isa gidan, na gaya mishi ya kira Yayansa da Hafiz domin nazo a raba auren ne har da Matarsa.
Kiri-kiri tsohon nan ya shiga fada wai an zuga ni. "Ba a zuga ni ba, a yzun na samu amsar tambayoyina, kai ne sanadin Hajja bakin cikinka ya kashe Hajja yanzu na fahimci yadda aka samu gawar Hajja, tabbas kai ka kashe Hajja sannan itama Dadah kayi sanadin daina ganinta karshe ta mutu bata gani. Imma ka kira Yaranka, ko kuma na kashe kaina kuma wallahi Yan uwana da hukuma ba zasu barka ba, mutuncin da kake da shi a fada sai ya zube, kimar da ka jima kana karewa zaka rasa. Zuwa gobe ka tara mu anan ko kuma jibi yan sanda su taraka a office ɗinsu. Kuma zan saka sunanka a cikin waɗanda suka kashe ni ba kai ba hatta Abba ba xan kyale shi ba." Daga haka na fito, ajiyar zuciya nake, amma definitely zuciyata ba zata iya daukar wannan kasadar ba, tsohon da nake ji yafi karfin na fada a fatar baki.
A daren Abba sai da ya kira Yayuna babu wnada ya dauki wayar, kai abin fa dole yasa aka hadu kamar yadda na fada din. *** A yau da nake tsaye a gaban Baban Jama'are, rike da jakata na zauna a gaban Baban Jama'are da kuma Malam Babba, tura kudin nayi a hankali. "Ya Hafiz ya biya sadakina a shekaru goma sha daya Naira dubu hamsin, yau na dawo mishi da dubu dari biyu,kawai abu daya nake bukata SAKI NA!" Mikewa yayi yana faɗin. "Hauka kike? Waye zai aure ki da wannan yanayin naki? Baki ga kina kama da dodo ba ne? Kambu ina ruwan kwatarkwashi, na ji xan sake ki shi waye ya gaya miki akwai wanda zai aure ki...." Tass aka wanke shi da mari, Yaya Adam kallonshi yayi cikin huci ya ce mishi. " Ni barista Adam Usman Umar Jama'are na tsaya mata, yau na kara yarda da cewa kai mugu ne hafiz laifi ne don ta nemi saki? Ashe dama wannan shine asalinka?" Baban Jamaarae ya ce mishi. "Na gode Adamu, na gode da ka wanke min raina, yau ba gobe ba ka sake ta ina alkaliya Hindatu?" Mikewa tayi ta dawo gaban jama'a, ta ce. "Baban Jama'are ni ba alkaliya ba ce, amma xan iya kiran alkalin ya shiga lamarin!" "Idan kuka kashe Auren Lubabatu ku sani sai dai ku nima mata wani Uban ba ni ba." Inji Babanmu. Da wani murmushi yake kallona, yana da wanda ya tsaya mishi. Murmushi nayi ina kallon kwayar idanunsa. "Idan ka kore ta, ina da inda zan ajiyeta. Hindatu ki kira mana alkali mu yi maganar da shi." "A'a su koma su sassanta kansu, idan abu ya ci tura sai mu kai gaba inji Baba Malam." "Wallahi wa Rabbul Ka'aba, ba zan sassanta da shi ba. Idan aka ce dole na koma gidansa zan koma amma ku sani zan mutu kuma zamu haɗu a gaban Ubangiji shine alkalin alkalai, ba zaku gane yadda nake mutuwa ba ne? Ba zaku gane yadda nake cutuwa ba ne?" Cire Hijab dina nayi na nuna musu hannuna da yake makale a wuyata. Na kuma kalli Aunty Inna na ce mata. "Zuge min zif din rigana!" Tana zugewa, na juya musu baya ruwan zafin da ya watsa min na shayi ne na ce musu. "Kace na tafi Baba zan tafi idan ka ce na mutu zan mutu, wannan shine abinda dan sonka ya min!" Kunya ce ta kama Ya Hafiz ya fara kame-kame yana faɗin. "Ba fa da gayya na mata ba, wallahi kawai na je zubar da." "Habibi kame-kame me kake kai fa kace ka gaji da ita gara ka sake ta, ina dalili mace ba haihuwa ba ka zauna da ita sai ciyar ta da ita kake yi, idan ka dawo da ita kuwa mutuwa zata yi da zama da kai domin an gama zugata. Mace sai kace rumfa. Kai ma dai da son rai kake, kasan ko ka ci gaba da zama da ita ba haihuwa zata yi ba tunda kai ne ka lalata mata mahaifa, gara ka sake ta kara gaba domin nima na sakata na wala" tana fadar haka ta juya ta bar parlourn, burinta ya cika ta fada fara ya sake ni yadda zata ji dad'inta ita ɗaya da Yaranta.
"Alhamdulillahi Ubangiji ya bata miji na gari, zaka sake ko sai na maka Allah ya isa!" Inji Baban Jama'are mahaifinsa. "Baba ina son matata, sharrin shaidan ne wallahi ban yi haka don na cutar da ita ba." Matsowa yayi gabana domin yanzu yasan tabbas za a raba shi da Lulu Kuma wannan zai kara hankad'o wasu abubuwan da ya aikata wanda haka yana fitowa kowa sai ya kusan tsine mishi "Luluna ki yi hakuri ki amince mu koma zamanmu!" Yadda yake roko da magiya zaka rantse ba shi ya gama cika baki idan ya sake ni sai na rasa majingina ba. Yadda ya gigice da Babanshi ya kara daka mishi tsawa Kakanmu Baba Malam ya ce mana. "Ku tashi ta koma dakinta." "Gaskiya ba zata koma ba, domin yanzu haka Lubnah tana ganin likitan ƙwaƙwalwa ne, saboda damuwar da take da shi ya shafi ƙwaƙwalwarta kowani lokaci zata iya haukacewa!" Inji Aunty Innah, kallona kowa ya koma yi cike da mamaki sai lokacin da hawaye yake zuba min. "Tabbas a yanzu haka ranar Monday zata ga babban likitan ƙwaƙwalwa anan Bauchi muna saka ran idan ya ganta zai daura ta akan magani!" Inji Ya Umar, Zare idanun Mama take zuciyarta yana wani irin bugawa. "Wani irin likitan ƙwaƙwalwa kuma?" Inji Yadiko, . "Kamar yadda kika ji Yadiko zamu mai da ta ganin likitan ƙwaƙwalwa, domin dole ta ga likita Lubnah da muka bashi ba ita ba ce wannan, idan kun kalle ta da kyau wannan bata da sake koma me yake damunta ba mu da dauka lokaci ya kure da zata kara." Ya Ado ya fada yana kallon agogon hannunsa, Baban Bauchi cikin isa irin nashi ya ce mana. "Idan kuka kashe mata aure ba dai gidana ba, kuma zan zare ku a cikin zuriar ta." "Kai sake ta, sannan na rungume Yaran Yaya Usman a madadin nawa, wallahi idan baka sake ta ba sai na maka Allah ya isa." Cikin fushi Hajiya Asiyah ta ce mishi. "Dalla sake ta, me za ayi da Macen da bata haihuwa me zaa yi da Macen da bata da amfani." Cikin faɗa Yadiko ta ce mata. "Kike fadar haka Hajiya Asiya? Kike fadar haka Hajiya Asiya? Rashin haihuwar waye sanadin mata haka? Ke Lubnah waye ya kawo miki maganin hana daukar ciki?" Kaina wani irin sarawa yake, hayaniyarsu saka min kaina juyawa yake. Kallon bakinsu nake domin motsinsa nake gani bana jin me suke cewa bakiɗaya. Lumshe idanuna nayi na bude a hankali, tare da dafe kaina. Jijiga Aunty Hindatu da nake kusa da ita tayi, na koma zan zube ta riko ni....... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu
*Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641
Posting Arewapen da Telegram
SHA BIYAR
Wannan sumar ya haifar da abubuwa dayawa, domin Mama ta tsaya a gefena tsawon wunin da nayi a gadon tana tare ni. Tashin hankalin da Ya Hafiz ya shiga abin har ya wuce tunanin kowa. Abu kamar wasa sai gashi lamarin ya wuce yadda ake tsammanin domin hajiya take kara jagula take al'amarin ta hanyar da aka yi wani rikici a cikin family akan aurena, sai da ta kai an rabu gida biyu wasu suna ganin kamar naki Ya Hafiz ne saboda Yan uwana sun zuga ni, Yayinda wasu suke tare da ni saboda ciwon da yake jikina suka ce ai tunda ya yarda da ya aikata ,sai gashi haka ya kawo rabuwar kuma kowa ya amince da a rabun, banda Abba da ya kafe shi da Baba Malam sai na koma.
Wasa wasa har tsawon kwanaki uku ina asibiti, yau Mama ta shirya tare da faɗin. "Zan tafi karbo takardanki, na gaji da ganin yadda kome yake faruwa shi Babanku ya dage ni ma kuwa ina tare dake babu wanda ya isa miki dole!" Gyada kai nayi ina mai cigaba da kwanciya, nasan cewa ina cikin tashin hankali, amma a kasan zuciyata ina jin kamar ban mishi adalci ba, anya Ya Hafiz ya cancanci haka? Bayan fitar ta sai ga Abba ya shigo, wani irin tsoro ne ya cika ni nayi baya ina zare idan, zama yayi. Gyara zama Babanmu yayi yana kallon yadda nake zaune a wurin guda, tunda ya shigo dakin, ya ga na kurawa window din idanu. "Lubabatu!" Ya kira sunana, a hankali na juyo ina kallonshi. "Nasan lafiyarki lau me yasa kike bawa Yan uwanki da mijinki wahala!" Kura mishi idanu nayi ina kallonshi. Turo kofar dakin Ya Ado da Ya Umar suka yi a tare, "me yasa kike bawa zuciyar kowa wahala?" "Baba bata da lafiya ka bar wannan maganar idan mun dawo ayi ta!" Inji Ya Umar da yake yana da zafin rai sosai. Rike shi Ya Ado yayi yana girgiza mishi kai. "Lubabatu Y'ata ce, akan me kuke kokarin shiga tsakaninmu?" "Saboda ka fifita zumunci akan Rayuwarta, ka rabata da Mahaifiyarta kada tazo ta ga halin da take ciki. Ka nisantata da kowa nata, Abba idan ka sake ta mutu a wannan yanayin Allah sai ya nuna maka iyakar...." Tass ya tsinkawa Ya Ado mari, a zuciye yayi waje." "Abba zan koma gidansa!" Juyawa yayi yana kallon yadda nake murmushi. "No Lulu kada ki mana haka." "A'a zan koma Ya Ado, zan koma saura me ya rage a rayuwata? Farin ciki sai dai wasu su yi, amma ni na san nayi hannun riga da shi, Ya Ado na gode sosai ka ce likita ya sallame ni kawai na koma dakina." Hankad'o kofar aka yi da karfi Mama ce tsaye tana huci. "Ba zaki koma ba, kin gama aurensa daga kotu muke ga takardanki." "Salamatu" "Sai me? Uwarshi ta kai kotu me ya rage? Ai dama albarkacin zumunci ne zaku kashe min Y'a Uwar da tafi ƙarfin Mijinta zaka yi tsammanin zata bar Lubnah ta zauna ne? An bashi kudin wanke muni me ake bukata?"
Shima kamar wanda aka wurgo shi ya ce mana. "Wallahi ban sake ta ba." "Kotu ta sake ta!" Inji Mama tana kara kallonshi. "Kaci albarkacin Ubanka, da sai na saka an maka abinda baka zata ba, Lubabatu kuwa ta haramta maka. Adamu kasan yadda zaku yi da ita zaman Bauchi ya kare kuma ka kuma kusantar inda Lubabatu take sai na saka an wulakanta min kai, idan kana jin rashin kunya da fitsara wannan cikin ta haifa min, lauya, magatakarda, Soja, da sojar kasa da na sama sun fika kwaya da tijara ahir dinka."
"Wallahi ban sake ta ba, ina son Matata kuma babu wanda! Ya isa raba ni da ita Baban Bauchi kana gani sun raba ni da Matata!" Ya dawo gabana ya ce min. "Luluna kina ganin sun raba mu? Luluna ki ce wani abu, ni ne Ya Hafiz dinki. Dube ni ni ne Hafiz ɗinki!" A hankali na zare hannuna a cikin nashi, zuciyata tana wani irin bugawa na ce mishi. "Alhamdulillahi Ubangiji da ka samar min yanci! Ka je na yafe maka kai da Karimcy ka je na bar muku kome na cikin gidan hatta suturata na yafe, Alhamdulillahi Ubangiji na gode maka!" Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka. Kuka nake da dukkan zuciyata.