Kenza eBookz

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 11

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 - Chapter 11

ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 11: ALAƘAR ZUCI BOOK 1 Chapter 11. Cikin irin haukar da ya saba ya ce min. "Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare…

4,197 words

Cikin irin haukar da ya saba ya ce min. "Idan baki dawo gare ni ba. Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!" Cikin fushi Mama ta ce mishi. "Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure kuwa wallahi sai tayi, ka fita kafin na kira a ci mutuncinka." "Lubnah ki dawo? Wallahi ki dawo ko kuma kina ji kina gani ki kare rayuwarki a wulakance! " Dariya Mama tayi tana faɗin. " Alhaji ka ji abinda danka yake faɗa? Ka ji yadda yake ihu bari na nuna mishi nima ina da fitsararru irinsa, ta leko waje tana faɗin. "Kai Adamu zo kayi min waje da wannan ɗan iskan ka nuna mishi yadda ake rashin kunya!" Ba Ya Ado ba bakiɗaya Yayuna maza suka yo dakin wani irin daukar amarya suka mishi, zuwa waje suka ajiye shi.. "idan ka sake zuwa inda Lubnah take gara ka kira kanka gawa domin sai munci Ubanka shege mara kunya dan iska!" Suka kore shi sannan suka dawo a lokacin Abba ya mike tsaye, kin yi yadda kike so da Yaranki ku je na sallame ku ke da ita Yar so dinku!" " Alhamdulillahi Masha Allah, na gode katuro min takardar da wuri domin ina gama idda zan yi aure in sha Allah! " Ashe maza ma na da kishi, cak Abba ya tsaya ya ce mata. " Uban waye ya ce zaki yi aure a shekarunki nan? " " Allah mana ya ce nayi koda ta dauki kwarinka! " " Kai Adamu ka gaya mata wallahi na dawo da ita kuma kada ta wuce yau bata koma dakinta ba, ita kuma kanwarku ba dai gidana ba. " Yadda Abba ya nuna baya bukatar ganina yasa min wani irin kunci, a hankali Mama ta d'ago hannu zata tab'a ni nayi maza na kare kaina, tare da cewa. "Don Allah ki yi hakuri!" Sake baki kowa na dakin yayi suna kallona har shi Abba da bai fita ba, juyowa yayi yana kallon yadda na kare fuskana. "Lubnah meke damunki! " Inji Ya Ado da ya tako gabana, " babu! " Na furta a hankali ina kallon Mama da itama mamaki ya kusan kashe ta. " Hafiz yana dukanki ne?" Rufe bakina nayi ina kallon Abba. " Gaya min dukarki yake yi?" Fadawa jikin Mama nayi na rufe idanuna, sake magana yayi ma kame-kame Mama ina ajiyar zuciya. " Wai a haka za a mai da ta wurinsa! Umar muje Bauchi a mai da ita asibiti she need treatment domin basu yadda ya dauka yana azabtar da ita ba. "

Kiransu Aunty Innah da Hindatu aka yi aka ce zaa koma Bauchi saboda mota daya aka dauko, a ranar aka bar Jama'aren, karfe tara na dare muka isa Bauchi, kai tsaya asibiti aka wuce da ni. Sai da muka isa asibiti bakiɗaya sai na kasa fita a motar, sai da suka fitar da ni daga motar, haka aka dauko keken marasa lafiya aka wuce da ni, zan iya cewa tun daga ranar sabon jinya ya same ni, hatta zuciyata sai da ta samu matsala.

Saboda nauyin damuwa dama can kaina ya jima da tabuwa, haka nayi ta jinya har wata guda kowa ya koma wurin aikinsa. Ya Umar da Tahir sai Sani da aka sake shi, Aunty Raliya tana zuwa a kai akai duba ni, da duk abinda tasan zan so.

* Flash back Abinda ya faruwa kuwa, tunda Hajiyar Ya Hafiz ta ga kudin da aka kawo tayi lissafinsa zai kara musu wani abu da yake mugaye ne, ita da Yaranta Nana da Firdausi suka shirya a kai ƙarar Lubnah kotu, yadda dole a amshi kudin da yardan Hafiz ko kada ya yarda idan suka karbi kudin daga baya sai ya ce bai yarda ba, sai kuwa Tijjani yaji maganar shine ya gayawa Baban Jama'are, shi kuma da ya tabbatar an kai maganar kotu, shine ya kira Ado ya gaya mishi, shi kuma ya tura Hindatu, tana zuwa ta tabbatar dama case ɗin a Bauchi ake son ayi shi, amma tunda sun kawo ba tare da wani dogon magana ba, aka tattauna saboda abin na family ne a office din alkali aka yi magana take alkali ya sake Lubnah tunda uwar shi bata bukatar Lubnah sannan koda ace uwarsa tana son Lubnah dole Hafiz ya kyaleta tunda abin har da irin wannan rayuwar. Ana. Fitowa daga office din Tijani ya kira shi ya gaya masa, sai ga shi har kotun ana ta jajjanta lamarin, ihu yayi ta yi yana faɗin bai sake ta ba, wallahi bai sake Lubnah ba. Koda Hajiyarshi ta bashi kudin wanke muni watsi da su yayi ya ce mata. "Duk abinda ya faru ke ce kika lalata min kome na, ina son Matata kika yi ta saka ni a gaba na cutar da ita, wallahi ba zan iya rabuwa da ita ba." Yayi ta rusa kuka har ya zo asibitin. Wanann shine abinda ya faru.

** A kwanakin da nayi ina jinya, babu wanda ya taba kira min sunan Ya Hafiz, nima kuma nayi ƙoƙarin danne tsoron da nake ji, sai dai kuma irin wannan tsoron baya barin Dan adam, domin abu ne da ruhi ya ginu akanshi, sai da ta kai ta kawo idan za a bude kofa da karfi sai na razana, ga wasu irin nightmare da nake yi,kamar dan mutu tsoro ya gama kassarani, karshe sai aka wayi gari amadadin jini na y sauka a'a jinina hawa yake kamar ana tula mishi gishiri, hatta likitan da yake duba ni sai da ya tambaye Mama ko tana bani wnai abincin da bai dace bane? Ta rantse mishi babu kome, shiru yayi kafin ya shiga tambayarta game da rayuwata kafin yau, bata boye mishi ba, amma yayi mamaki da ji ai ba a jima da kashe auren ba, don haka ya tafi da dare ina kwance ya shigo don Allah ya gani ko magana bana son yi ya shigo ya zauna tare da min tambayoyi, idanuna a rufe nake bashi amsa, abinda yayi matuƙar daure mishi kai, shine lokacin da ya mike ya matso zai duba ni domin ya ce na tashi zaune, wani baya da nayi saura kiris da na fado kasa. "Is ok ba zan miki kome ba,.amma ki kalle ni mana!" A dan tsorace na kalle shi nayi maza na rufe idanuna. "Hajiya haka take yi ne kullum!" Shiru tayi kafin ta ce mishi, "wani lokaci ba, musamman idan muna ta yawan baki masu zuwa gaishe ta!" "A dakatar dasu, su daina zuwa domin bata da lafiya sosai da sosai, jinya take bukata kafin ki tafi gida ku daura akan naku." Tabbas ni kaina nasan bani da lafiya, domin daga yadda nake razana da firgita.

Koda Yayuna suka zo Mama tayi musu bayani suka ga likita ya gaya musu halin da nake ciki, sai suke ganin kamar ba haka ba sai da Aunty Innah tazo ta fara musu bayani abinka da mai ilimin ta ce musu, ta gyara zama tana kallonsu kafin ta ce musu. "Lubnah tana bukatar kulawa a kowani irin Yanayi, Lubnah tana bukatar rayuwa me kyau no matter how tana bukatar faɗin ciki a ja ta a jiki." Sauke numfashi tayi tana kallon takardar hannunta ta ce musu. " Mun yarda da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Allah shi ya jarabci Lubnah da wannan laluran amma da ace tun farko da Hindatu ta fara min magana akan Lubnah zata samu wannan matsalar da tun lokacin aka kashe auren! " "Dalla Malama ki mana bayani kin sa zuciyata sai tsalle take idan ta dirko ta fashe fa? " Inji Tahir da ya gaji da maganar da take yana son Isa ga point din. "*GAD*" Ta furta muryanta yana rawa ta fara magana kamar haka. "GENERALIZED ANXIETY DISORDER, ake kiranshi a turance, cuta ce da take samun dan adam ta sanadin damuwa da tashin hankali tare da matsin lamba, wanda idan ta kai matakin chronic yake haifar da cutar hauka!" " Bama depression ba?" Inji Ya Umar, hawaye ne ya zubo mata ta cigaba da cewa "A yanzu ta shiga mataki na biyu ga cutar, wanda daga shi sai hauka. Yawan razana da miyagun mafarki. Tun ranar da Mama ta kai hannu zata ta b'ata ta razana, ya fara jin shakku, idan kun lura ana bude kofar zata zabura." Kuka ta saka a hankali. " Tana kokarin fita daga staage ta shiga wancan da shine zata fara hauka. Tun da na ga tana yawan dariya ko tayi ta zama shiru nayi fatan ya tsaya a haka ashe har ya isa wannan matakin. " " Kin ga ana warkewa ko ba a warkewa? " Inji Ya Umar, cikin shashekar kuka ta ce mishi. "Ana warkewa idan aka hadu da therapy." Shiru yayi kafin ya ce mata. "Yanzu taya zamu iya magance matsalar Lubnah amma wancan dan kutumar uban na Ganshi sai na kusan kashe shi!" Mama da take bakin kofar basu san ta fito ba ta ce mishi. "Me yayi da za a kashe shi? Shi bai yiwa lubnah kome ba, nice a matsayina na uwa na kashe Lubnah na sha ganin damuwa a cikin idanunta amma na rufe nawa idanun bana son na karanta. Balle har na samu damar cewa tayi hakuri da ace na karanta ai da yau yarinyar nan bata nakasa har haka ba taya zan yi da Lubnah?" Cikin kuka take magana, sanin cewa itama tana da laifi amma lokaci guda ta tsaya sai Yaran suka zagaye ta suna bata baki. Dakyar Mama tayi shiru.

Shigowa suka yi dakin, suka same ni kwance nayi rigingine, ina kallon sama ni kaina bana ce ga dalilin haka ba, amma na tsinci kaina da son kwanciya haka karar bude kofar yasa na rufe idanuna. "Auta!" Juyawa nayi ina kallonta. "Tashi ki ci abinci!" Duk yadda nake ji a zuciyata bana son ganin Mama tana damuwa balle yau ganin hawaye na zuba mata yasa na mike zaune. Abincin ta kawo min ta zauna a gefena tana mai diba ta bani a baki. Kallon cokalin nayi kafin na bude a hankali na amsa, hawaye na zuba mata tana bani ina ci, a hankali na kai hannuna saman fuskarta na goge mata. Murmushi tayi nima na mai da mata, na cigaba da amsa tana kuka har na kauda kaina domin idanuna yana cika da kwalla. Ruwa Aunty Innah ta bani na sha ina son Magana amma ban san me zance ba, a hankali na ce musu. "Amma ba zan koma gidan Ya Hafiz ba ko?" Ya Tahir ya matso gefena ya riko hannuna ya ce min. "Waye ya ce zaki koma gidan Hafiz?" Girgixa kai nayi matse hannuna yayi ya ce min. "Ki kwantar da hankalinki, babu inda zaki in sha Allah. Daga gidana babu wani wurin da zaki kin ji zaki zauna a gidana ko?" Gyada kai nayi ya ce min. "Kada ki kara tuna wani can da bai da amfani a rayuwarki da namu kin ji!"

Gyada kai nayi suka gaya min kowa ya shirya domin na zauna a gidanshi. Amma firstly lafiyata suke bukata domin sai da ita zan rayu. Tun daga ranar aka daura ni akan magani, idan Aunty Innah ta taso zata zo ta zauna tana kara tisa min karatun Alqur'ani da azkar. Haka yasa kullum ina cikin Alwala koda kuwa bani da tsarki ne, zuciyata ta samu nutswa. A cikin sati biyar da nayi a cikin babban asibitin Bauchi, duk wnada ya ganni sai ya san na samu nutswa sama da can baya.

* Hafiz

Ya gigice domin har Karimah sai da ya koreta, kamar zai yi hauka sannan kullum yana hanyar wurin Baban Bauchi, tare da rokon ya saka baki Lubnah ta dawo amma baban Bauchi ya ce yana kan ƙoƙarin ta dawo ya jira a sallamota, domin har ga Allah tausayi Hafiz yake ji, yadda ya gigice har Jama'are ya je gaban Baba Malam yana kuka wiiwii da yake shima Baba Malam ya ɗan ji haushin abin da Hafiz yayi amma da yake zuciyarsa muguwa ce sai gashi ya kira Baban Bauchi... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*

Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

SHA SHIDA

Da yake zuciyarsu ta cika da zalinci da mugunta, yadda yake shiga ba nan yake fita ba shi damuwarsa a maida Lubnah dakin Hafiz haka ne zai saka Hafiz ya samu nutsuwa, sai dai shi Baban Bauchi ya tabbatar mishi da cewa case ɗin bayana hannunsa yana hannun Baban Jama'are, wato mahaifin Hafiz, haka ya saka Hafiz a gaba har gaban mahaifinsa. Bayan sun zauna ba tare da dogon magana ba, ya ce ga abinda zai yi kuma Umarni ya bada ba ba kome ba. Shiru Baban Jama'are yayi tare da kallon Mahaifinsa. Sannan ya kalli Hafiz da yayi wani zuru-zuru. Ya ce mishi. "Baba ka tambaye tsakaninsa da Allah Lubabatu ta zalince? Idan ya ce eh yau ba sai gobe ba zata koma dakinsa idan kuma ya kasa ba ni amsar tambayoyin da zan mishi har abada ya rasa ta kenan." A matuƙar razane Hafiz yake kallon Mahaifinsa, ya kuma kalli Baba Malam, kamar ya ce. " Don Allah Baba Malam, ja saka baki wallahi abubuwan ba sauki." Gyara zama Baban Jama'are yayi ya ce mishi. " Wallahi warabbul ka'aba idan har ka tabbatar sau daya Lubabatu ta cutar da kai tow yau zata koma dakinka! " Wasu irin zufa ke karyo mishi yana sharewa suna kara karyowa. "Ka bawa Lubabatu maganin hana daukar ciki ko baka bata ba?" Baban Jama'are ya watsa mishi tambayar, kamar yayi kuka ya rike hannun Baba Malam. Yana me gyad'a. " Da bakinka zaka gaya min?" " Na bata" Hafiz ya fada yana shashekar kuka. Murmushi Baban Jama'are yayi yana kallon danshi, cikin wani irin yanayi na Tausayi me zagaye da bakin ciki. Ya ce mishi. "Ka bata kwayar yan shaye-shaye ko baka bata ba?" Cikin wani irin kuka ya ce mishi. "Na bata?" Cizon lips dinsa Baban Jama'are yayi yana jin idanunsa na cika da kwalla.. "ka sayar mata da gidanta ko baka sayar ba?" Kanshi a sunkuye ya ce mishi. "Na sayar Baba!" "Waye ya shiga tsakaninta da danginta?" Cikin wani irin gigita ya kalli Babansa ya ce mishi. "Baba ka gaya min ba zan same ta ba har abada, wallahi yanzu na tuba ina son Lubnah kamar yadda ta so ni a baya. Don Allah kada ka raba ni ita." Zuciyar Baban Jama'are yayi laushi amma abinda ya saka Hafiz saduda na karamin al'amari bane. "Na san halinka na san waye kai. Da ka girmama kanka da yau an wayi gari duniya ta girmama ka. Shi girmama ana nimansa ne tun daga yarinta Yaro ya yi abinda Manya suke yi sai ka ga girma ya shige shi. Da yau ka mu'amala Lubnah da adalci ina ga da yanxu kuna da Yara uku zuwa hudu, amma haka ka kashe ta kana ta kwashe duk abinda ta mallaka bayan ta tsaya maka, tayiwa Uwarka, tayi maka, tayiwa Yaranka, tayiwa yan uwanka, wacce irin son zuciya ce haka? Me tayi maka da zafi haka? Na zata kaf duniya idan akwai wanda zaka bawa kariya Lubnah ce, iyayenta suka maka riga da wando suka dauki yarsu mafi soyuwa suka baka, a lokacin akwai wani bawan Allah da ya zo yana sonta da gaskiya yarinyar nan ta juya baya ta ce bata son shi sai kai, yau an wayi gari ka gama lalata mata rayuwa, yau yarinya da bata wuce shekaru ashirin da shida tana zuwa da bakwai tana can tana fama da jinyar bakin cikin da kayi ta cusa mata, Hafiz ni na haife ka amma ni ma ban tsira daga kaidinka ba, me yasa sai Lubnah? Me tayi da zafi ka mata haka? " Hawaye ne yayi ta zubo mishi yana faɗin n. " Don Allah ka yi hakuri ka rufa min asiri, Lubabatu ita ce rayuwata, ita ce arzikina. Baba don Allah ka yafe min ka bani lubnah a karo na biyu." "Ba zan iya ba kayi hakuri, kaf duniya ni nake da iko da Adamu da Hindatu idan nace su dawo da ita zasu dawo da ita amma itama ina son ta shaki iskar yanci, ta san itama mace ce kuma mutum mai yanci, idan na ji labarin ka kuma d'ago maganar nan wallahi akan mahaifiyarka zan sauke shi. Kai na shiga tsakaninku da Lubnah har abada babu aure a tsakanin sai zumunci shima idan ta gadama idan na ji labarin wani abu ya faru sai ka gani a kwayar cin tuwonka!" "Yanzu ni ban isa ba! Yaron nan yayi nadama!" Inji baba Malam!, "Kayi hakuri Baba kai ikonka akanmu ne, Yaranmu kuwa ka barmu, akansu da ace tun farko ka amshi uzrin yarinyar nan da yau maganar bata dawo hannunmu ba, Baba ita gaskiya daya ce, don Allah ka bar yaran nan su dauki path din da kowa ya mishi duk wnada ya zalincin wani Allah ya bi masa hakkinsa." Rikicewa Hafiz yayi yana kuka yana rokon a bashi dama ɗaya. Babanshi kuwa ya ce ai yayi watsi da damarshi tun fil azal yanzu ya cigaba da hakuri kawai.

Wannan abin ya d'aga mishi haka, haka ya dawo wurin Hajiyarsu yayi ta kuka yana tambayarta me yasa tayi masa haka, me yasa ta shiga rayuwarshi da farko ya zata zai iya handle din matsalar sai ya fahimci ina kome ya lalace mishi, bai taɓa kawowa yana son Lubnah ba sai yanzu da ya rasata, haka yasa ya sha alwashin matukar bai same ta ba, har abada babu me samunta itama Hajiya ta kara tabbatarwa matukar basu dawo mishi da ita sai dai ta kare rayuwarta babu aure. Yadda suke kulla sharri matukar Lubnah bata dawo gare shi ba, abinda zasu mata sai ta zama abin tausayi. Wannan masifar da suke kulawa ya tsaya a tsakaninsu sannan itama Hajiyar zata je har Bauchi ta roke su idan suka ka ki kuwa sai dai su san yadda zasu da Lubnah. Wanann shi ne tsarin da suka yi, bayan sun manta da akwai Allah. ** Lubnah Rayuwa kamar littafi ne, yau idan wannan shafin ya bude maka gobe wani zai kara budewa, haka rayuwata ta shiga cikin jerin littattafan da ban san lokacin da na mallake su ba, kwanakina arba'in aka sallame ni, zuwa gidan Ya Tahir. Wanda shi ya fara nuna sha'awarsa akan na zauna a wurinsa. Aka gyara min dakina ba abinda ba a zuba min ba.

Tunda na dawo na samu nutsuwar zuciya da ruhi, shi yake bani magani ya kuma tsaya a kaina sai na ci abinci na sha maganin. Safe da yamma da rana kuma Matarshi tana bani. A hankali nutsuwa da kwanciyar hankali ya fara dawowa a rayuwata. Tseren da muka fara da kaddara ya dawo abu mafi sauƙin isowa. Mama gidan Ya Umar ta koma abinta, da suka mata maganar ta koma gidan Abba ta ce bata san da zancen ba, sosai Mama ta dauki wuta domin tafi kowa daukar zafi shi kanshi Abba sai da ta kai ta kawo yana shakkar mata magana, haka ya tafi har Jama'are yana samu Alhaji Ahmed Galadima babban wansu Mama ya roke shi ya saka baki Mama ya dawo, murmushi Yayi ya ce mishi ka zauna da ita tsawon shekaru arba'in ka san wacece ita ka je kai da kanka zata dawo! " Ba haka Abba ya so, Alhaji Ahmed Galadima ya tirsassa Mama ta koma sai gashi shima ya ce ya lallabata, kai karshe sai gashi ya kira Ya Ado tare da rokon shi da Yan uwansa su saka baki Uwarsu ta dawo dakinta. Ya ce mishi zasu mata magana in sha Allah.

Ai kuwa Ya Ado yana yiwa Mama magana ta ce ita fa ba inda zata koma ba sai dai yayi duk abinda zai yi, dukkanmu muka yi ta bata hakuri kafin ta amince ta koma amma shima Abba sai da yaji a jikinsa. Tsofaffin nan suna son junansu amma bakiɗaya sun koma kamar wasu kananan Yara sai wani jayayya suke. Haka muka cigaba da rayuwar a hankali ina ƙoƙarin zama mutum daga layin mahaukata zuwa jinsin mutane masu lafiya da cikakken hankali.

Sai da wata biyu kafin na fara jinin hailata domin shima daukewa yayi saboda tashin hankali, a wannan watan na fara kirga kwananki Iddana, da yake kwanaki biyar nake ina gamawa, na gayawa Aunty Hindatu da Aunty Innah, suka sani. Don sun ce idan yazo na gaya musu. Kamar da wasa na daina tunanin wani can Ya Hafiz, na daina tunanin kowa ni yanxu ai mazan tsoro suke ba ni, ba iya maza ba duk abinda za ayi tashin hankali da fada a kai take sai naji kamar zan mutu da tashin hankali. Shi yasa bana shiga ko hayaniyar Yaran Ya Tahir, suna fara zan gudu daki bana son tashin hankali ko yanayi sai naji kamar wani abu yana yawo a kaina. Haka yasa Uwar tana jin sun fara zata fara fada da kokarin kiran Babansu.

Wata hudu da mutuwar aure duk da ban gama idar ba, ranar na samu bakuntar Ruma Rabi'u Mai shanu ta zo min, Nafisa Sadi Gital, Hafsat Faruq Babaji, dukkansu Uku kowacce da Yaranta nayi mamakin da suka ji labarin ina gidan Ya Tahir.. "ladies a ina kuka ji ina nan gidan?" "Jalilah Kamil Jama'are ta gaya mana!" Lashe bakina nayi, sai kallon tausayi suke min. Yadda nake zaune kowa yasan yadda bana son kallon tausayi domin sai na fara jin wani irin tashin hankali. "Ku daina min kallon tausayi, ina da condition da mentally ill idan aka cigaba yanayin yana birkita min ƙwaƙwalwa Please." Yadda nayi maganar sai na ga suna kuka. Which mean sun san da haka, haka suka rungume ni tare sha faɗin. "Lulu in sha Allah zaki yi farin ciki, Ubangiji ya kawo lokacin farin cikin ne." Murmushi nayi ina shafa bayansu nace musu. "Alhamdulillahi Ubangiji ya bamu hakurin akan rayuwa." Daga nan jefi-jefi ina shiga hiran wani kuma nayi shiru nayi ta kallonsu kowacce take gaya min Yaranta da sauran nasarar da suka samu a lokacin suka bani shawarar idan na gama Idda na fara aiki, wani aiki zan yi? Ni da hayaniya yake d'aga min hankali, tow kadai nace musu anan suka wuce sai dare suka tafi bayan sun kawo min kayan alkhairi kala kala. Haka na yi ta shafa rayuwata a hankali har na gama iddana ina kuma ganin likita a kai a kai. A lokacin likitan shima yana jin dadin ganin yadda nake rayuwa cikin aminci da nutsuwa. Ranar da Ya Hafiz ya ji labarin na gama Idda, sai da ya kwanta a gadon Asibiti. Yayi ta surutu Matarshi ce aka raba shi da ita har da fisge-fisge, abin da ba dadin ji domin sai gashi kamar mai cutar farfadiya haka yake wasu abubuwan. Da na ji labarin na tausaya mishi amma idan na tuna yadda yaso kashe ni sai naji shi ba abin tausayi ba ne da ya samu wuri kashe ni zai yi da kwanaki na, gara da Allah ya yakin ce min shi da an barni da halina tabbas da na mutu.

Kwatsam ina zaune Aunty Innah ta nima min aikin koyarwa, wai ko dai rage min zaman da nake na kadaici, matata kuwa da Ya Hafiz ya rike sun karba aka sayar aka sauya min wata yar karama mai kyau, haka na fara zuwa aiki da ita. Bana shiga rayuwar kowa bana iya d'ago kai kalli mutum, asalima maza tsoro suke bani domin kallon Ya Hafiz nake su. Malamai mata ma sama-sama muke gaisawa.

Haka na cigaba da aikina yaran bani da matsala da su, musamman da suke ƙanana. Ina koya musu math, yadda na samu nutsuwa a yar wannan lokacin yasa hatta Yaran sun san bana son tashin hankali. Bana son magana bana son hayaniya. Sai Allah ya bani sa'a akansu yadda ko tari basu min nima da na fahimci sun fahimci halina, sai nake saya musu yar choco-choco ina bawa masu ƙoƙarin cikinsu, ina son Yara ina son ganinsu cikin farin ciki da walwala. Haka yasa yaran idan na shiga ajin sai su yi shiru kafin su mike su gaishe ni, sai na musu alama da da hannu suke zama na cigaba da musu karatu, kasancewar makarantar private ne sai Allah ya taimaka duk ranar Alhamis ina fita da su, PE physical education, saboda Yarar juma'a manya ke fita.

Yau da ya kasance Alhamis na isa Makarantar da wuri, nayi parking sannan na wuce staff office nayi sign sannan na nufi hanyar aji sai ga daya daga cikin malaman makaranta ya ce min. "Mrs Jama'are kina headmistress tana kiranki!" "Ok na gode!" Na juya na wuce office din, ina shiga da sallama idanuna ya fad'a cikin na...... *08130269641* [12/4, 10:51 AM] Firdausi Salis: *ALAƘAR ZUCI*

Ramlat Abdulrahman Manga Mai_Dambu

*Littafin nan na kudi ne akan 1500* *1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita* Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641

Posting Arewapen da Telegram

*Last Free pages*

SHA BAKWAI

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull